- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Zakariya Zakariya Zakariya Zak Zakariya Kira don komawa ga Ubangiji A wata na bakwai na shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo. Ubangiji ya yi fushi sosai da kakanninku. Saboda haka ka gaya wa mutanen, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku komo gare ni,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘ni kuma zan komo gare ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka ce musu, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku juya daga mugayen hanyoyinku da mugayen abubuwan da kuke yi.’ Amma ba su saurara ba, ko ma su kula da ni, in ji Ubangiji. Yanzu ina kakanninku suke? Annabawan kuma fa, sun rayu har abada ne? Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku? “Sa’an nan suka tuba suka ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’ ” Mutumin a cikin itatuwan ci-zaƙi 7-8 A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato, watan Shebat, a shekara ta biyu ta Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Zakariya ɗan Berekiya ɗan Iddo. Da dare, na ga wahayi, a gabana kuwa ga mutum a kan jan doki! Yana tsaye a cikin itatuwa masu furanni, a bayansa a cikin itatuwan ci-zaƙi, a bayansa kuwa akwai dawakai masu ruwan ja, ruwan ƙasa-ƙasa da kuma ruwan fari. Sai na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan ranka yă daɗe?” Mala’ikan da yake magana da ni ya amsa ya ce, “Zan nuna maka mene ne su.” Sai mutumin da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin ya yi bayani cewa, “Su ne waɗanda Ubangiji ya aika ko’ina a duniya.” Sai suka ce wa mala’ikan da yake tsaye cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun ratsa ko’ina a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.” Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Maɗaukaki, har yaushe za ka ci gaba da ƙi nuna wa Urushalima da kuma garuruwan Yahuda jinƙai, waɗanda kake fushi da su shekarun nan saba’in?” Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa. Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona, amma ina fushi da ƙasashen da suke ji suna zaman lafiya, na ɗan yi fushina kawai, amma sai suka ƙara musu masifar.’ “Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Zan komo Urushalima da jinƙai, a can ne za a sāke gina gidana. Za a kuma miƙe ma’auni a bisa Urushalima,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’ ” Ƙahoni huɗu da maƙera huɗu Sa’an nan na dubi sama a gabana kuwa sai ga ƙahoni huɗu! Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, “Mene ne waɗannan?” Ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima.” Sa’an nan Ubangiji ya nuna mini maƙera guda huɗu. Na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan suke zuwa yi?” Ya amsa ya ce, “Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta.” Mutum riƙe da ma’auni Sa’an nan na ɗaga kai sai na ga mutum a tsaye riƙe da ma’auni a hannunsa! Sai na yi tambaya, na ce, “Ina za ka?” Ya amsa mini ya ce, “Zan je in auna Urushalima, in ga yadda fāɗinta da tsawonta suke.” Sai mala’ikan da yake yi mini magana ya tafi, sai wani mala’ika ya zo ya same shi ya ce masa, “Yi gudu, gaya wa saurayin can cewa, ‘Urushalima za tă zama birni marar katanga domin mutane da dabbobi masu yawa ƙwarai za su kasance a cikinta. Ni da kaina ne zan zama katangar wuta kewaye da birnin, in kuma zama darajarta,’ in ji Ubangiji. “Zo! Zo! Ku gudu daga ƙasar arewa,” in ji Ubangiji, “gama na warwatsa ku a kusurwoyi huɗu na sama,” in ji Ubangiji. “Zo, ya ke Sihiyona! Ku tsere, ku masu zama a cikin Diyar Babilon!” Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Bayan ya ɗaukaka ni, ya kuma aiko ni ga ƙasashen da suka washe ku gama duk wanda ya taɓa ku ya taɓa ƙwayar idonsa ne. Ba shakka zan tā da hannuna a kansu domin bayinsu su washe su. Sa’an nan za ku san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni. “Ki yi sowa ki yi murna, ya ke Diyar Sihiyona. Gama ina zuwa, zan zauna a cikinki,” in ji Ubangiji. “Ƙasashe da yawa za su haɗa kai da Ubangiji a ranan nan, za su kuma zama mutanena. Zan zauna a cikinku, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. Ubangiji zai gāji Yahuda a matsayin rabonsa a cikin ƙasa mai tsarki zai kuma sāke zaɓi Urushalima. Ku yi tsit a gaban Ubangiji, dukanku ’yan adam, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.” Tufafi masu tsabta don babban firist Sa’an nan ya nuna mini Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji, Shaiɗan3.1 Shaiɗan yana nufin mai zargi. kuma yana tsaye a damansa don yă tuhume shi. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsawata maka, Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima, ya tsawata maka! Ashe, mutumin nan ba shi ne sandar da take ƙonewa da aka ciro daga cikin wuta ba?” Yanzu an sa wa Yoshuwa tufafi masu dauda sa’ad da yake tsaye a gaban mala’ikan. Mala’ikan ya ce wa waɗanda suke tsaye a gabansa, “Ku cire masa tufafinsa masu dauda.” Sai ya ce wa Yoshuwa, “Duba, na ɗauke zunubanka, zan sa maka tufafi masu tsada.” Sai na ce, “Sa masa rawani mai tsabta a kansa.” Aka sa masa rawani mai tsabta a kansa aka kuma sa masa tufafi yayinda mala’ikan Ubangiji yake tsaye a wurin. Mala’ikan Ubangiji ya yi wa Yoshuwa wannan gargaɗi. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘In za ka yi tafiya a hanyoyina ka kuma kiyaye abubuwan da nake so, za ka zama shugaban haikalina, ka kuma lura da ɗakunan shari’ata, zan kuma ba ka wuri cikin waɗannan da suke tsaye a nan. “ ‘Ka saurara, ya babban firist Yoshuwa, kai da abokanka da suke zaune a gabanka, ku da kuke alamun abubuwan da za su zo. Zan kawo bawana, wanda yake Reshe. Dubi dutsen da na ajiye a gaban Yoshuwa! Akwai idanu bakwai3.9 Ko kuwa sassa a kan wannan dutse guda, zan kuma yi rubutu a kansa,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘zan kuma kawar da zunubin ƙasan nan a rana ɗaya. “ ‘A wannan rana kowannenku zai gayyaci maƙwabcinsa yă zauna a ƙarƙashin itacen inabi da kuma na ɓaure,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.” Wurin ajiye fitilan zinariya da itatuwan zaitun biyu Sai mala’ikan da ya yi magana da ni ya komo ya farkar da ni, kamar yadda ake farkar da mutum daga barcinsa. Ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Na amsa, na ce, “Na ga wurin ajiye fitilan zinariya da kwano a kai, da kuma fitilu bakwai a kansa, da butocin kai wa fitilu mai guda bakwai. Akwai kuma itatuwan zaitun guda biyu a gefensa, ɗaya a gefen dama na kwanon ɗaya kuma a gefen hagunsa.” Na tambayi mala’ikan da ya yi magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?” Sai ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?” Na amsa, na ce, “A’a, ranka yă daɗe.” Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ” Sai maganar Ubangiji ta zo mini, “Hannuwan Zerubbabel sun kafa harsashin haikalin nan; hannuwansa ne kuma za su gama ginin. Sa’an nan ne za ka san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni zuwa wurinka. “Wa ya rena ranar ƙananan abubuwa? Mutane za su yi murna sa’ad da suka ga igiyar gwaji a hannun Zerubbabel. “Waɗannan guda bakwai ɗin su ne idanun Ubangiji, masu jujjuyawa cikin dukan duniya.” Sai na tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan itatuwan zaitun guda biyu tsaye a hagu da kuma daman wurin ajiye fitilan fitilu?” Na sāke tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan rassa biyun nan na zaitun a gefen bututu biyu na zinariya da suke zuba man zinariya?” Ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?” Na ce, “A’a, ranka yă daɗe.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne biyun da aka shafe don4.14 ko kuwa biyun da suke kawo mai su kuma su yi wa Ubangiji dukan duniya hidima.” Naɗaɗɗen littafi mai firiya Na sāke dubawa sai ga naɗaɗɗen littafi mai firiya a gabana! Sai ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Sai na amsa na ce, “Na ga naɗaɗɗen littafi mai firiya, tsawonsa ƙafa talatin da fāɗinsa kuma ƙafa goma sha biyar.”5.2 Da Ibraniyanci tsawonsa kamu ashirin, fāɗinsa kuma kamu goma (tsawonsa wajen mita 9, fāɗinsa kuma wajen mita huɗu da rabi). Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya. Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ” Mace a cikin kwando Sai mala’ikan da yake mini magana ya zo gaba ya ce mini, “Duba ka gani ko mene ne wannan da yake fitowa.” Na tambaya na ce, “Mene ne?” Ya amsa ya ce, “Kwando ne na awo.”5.6 Da Ibraniyanci efa ne; haka ma a ayoyi 7-11. Ya ƙara da cewa, “Wannan shi ne laifin5.6 ko kuwa bayyanuwar mutanen a duk fāɗin ƙasar.” Sa’an nan aka ɗaga murfin dalman, a ciki kuwa ga mace zaune! Ya ce, “Wannan mugunta ce,” ya kuma tura ta cikin kwandon ya rufe da murfin dalman, ya kuma danna da dutse. Na ɗaga idona sama, sai ga mata biyu a gabana, iska tana hura fikafikansu! Suna da fikafikai kamar na shamuwa, suka kuma ɗaga kwandon sama. Na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Ina za ku kai kwandon?” Ya amsa ya ce, “Zuwa ƙasar Babiloniya5.11 Da Ibraniyanci Shinar. Shinar tsohon sunan Babilon ne. Bisa ga Far 11, a wurin ne mutanen dā suka gina gini mai tsayi na saɓo ga Allah, wanda Ubangiji ya sauka ya dagula harsunansu. don a gina masa haikali. Sa’ad da aka gama ginin, za a ajiye shi a ciki.” Kekunan yaƙi huɗu Na sāke ɗaga kai sama, sai ga kekunan yaƙi guda huɗu a gabana suna fitowa tsakanin duwatsu guda biyu, duwatsun tagulla! Karusa ta farko tana da jajjayen dawakai, ta biyu kuma baƙaƙen dawakai, ta ukun farare dawakai, ta huɗu kuma dawakai masu ɗigo-ɗigo a dukan jikinsu, dukansu kuwa ƙarfafa. Sai na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?” Mala’ikan ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu na sama, waɗanda suka fito daga wurin Ubangiji na dukan duniya. Wannan mai baƙaƙen dawakai zai nufi wajen ƙasar arewa, mai fararen dawakai zai nufi wajen yamma, sai kuma mai dawakai masu ɗigo-ɗigo a jiki zai nufi wajen kudu.” Da ƙarfafa dawakan suka fito, sai suka yi marmari su ratsa dukan duniya. Sai ya ce, “Ku ratsa dukan duniya!” Saboda haka suka ratsa dukan duniya. Sai ya kira ni ya ce, “Duba, waɗanda suka nufi wajen ƙasar arewa sun ba wa Ruhuna hutu a ƙasar arewa.” Rawani domin Yoshuwa Maganar Ubangiji ta zo mini, ta ce, “Ka karɓi azurfa da zinariya daga masu zaman bauta Heldai, Tobiya, Yedahiya, waɗanda suka iso daga Babilon. A ranar kuma ka je gidan Yosiya ɗan Zefaniya. Ka ɗauki azurfar da zinariyar ka yi rawani, ka ɗora shi a kan babban firist, Yoshuwa ɗan Yehozadak. Ka ce masa ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ga mutumin da sunansa ne Reshe, zai kuma ratse daga inda yake yă gina haikalin Ubangiji. Shi ne zai gina haikalin Ubangiji, za a kuma martaba shi da daraja, zai kuma zauna yă yi mulki a kan kursiyinsa. Zai zama firist a kan kursiyinsa. Kuma a tsakanin biyun za a sami zaman lafiya.’ Za a ba Heldai,6.14 Da Siriyak da Ibraniyanci Helem Tobiya, Yedahiya da kuma Hen6.14 Ko kuwa da kuma mai alheri ɗan Zefaniya kamar abin tunawa a cikin haikalin Ubangiji. Waɗanda suke nesa za su zo su taimaka gina haikalin Ubangiji, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku. Wannan zai faru in kuka yi biyayya sosai ga Ubangiji Allahnku.” Gaskiya da jinƙai, ba azumi ba A shekara ta huɗu ta Sarki Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa Zakariya a rana ta huɗu ta watan tara, wato, watan Kisleb. Mutanen Betel sun aika Sharezer da Regem-Melek, tare da mutanensu su nemi tagomashin Ubangiji ta wurin tambayar firistocin da kuma annabawan gidan Ubangiji Maɗaukaki, “Ko ya kamata in yi makoki da azumi a wata na biyar, yadda na yi a shekaru masu yawa?” Sai maganar Ubangiji Maɗaukaki ta zo mini ta ce, “Ka tambayi dukan mutanen ƙasar da firistoci cewa, ‘Sa’ad da kuka yi makoki da azumi a wata na biyar da na bakwai dukan shekaru saba’in nan, a ainihi saboda ni kuka yi azumi? Kuma sa’ad da kuke ci kuke sha, ba kanku kuke yi wa shagali ba? Ashe, ba kalmomin da Ubangiji ya faɗi ke nan ta bakin annabawan farko ba sa’ad da Urushalima da garuruwan da suke kewaye da ita suke hutawa, suke cikin wadata, akwai kuma mutane a Negeb da yammancin gindin tuddai?’ ” Sai maganar Ubangiji ta sāke zuwa wa Zakariya cewa, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna. Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’ “Amma suka ƙi su saurara; da taurinkai suka juya bayansu suka kuma toshe kunnuwansu. Suka taurare zukatansu kamar dutse, suka ƙi jin abin da doka ko kuma maganar Ubangiji Maɗaukaki take faɗi wadda ya aika ta wurin Ruhunsa ta wurin annabawan farko. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ji fushi ƙwarai. “ ‘Sa’ad da na yi kira, ba su saurara ba; saboda haka sa’ad da suka kira, ba zan saurara ba,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘Na warwatsar da su da guguwa a cikin dukan ƙasashe, inda suka zama baƙi. Aka bar ƙasar ta zama kango bayansu, da har ba mai shiga ko fita. Haka suka sa ƙasan nan mai daɗi ta zama kango.’ ” Ubangiji ya yi alkawari zai albarkaci Urushalima Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa gare ni. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ina kishin Sihiyona ƙwarai; ina kuma cike da kishi dominta.” Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Tsofaffi maza da mata za su sāke zauna a titunan Urushalima, kowanne da sanda a hannu saboda tsufa. Titunan birnin za su cika da samari da ’yan mata suna wasa.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mai yiwuwa ya zama da mamaki ga raguwar wannan mutanen da suke nan a lokacin, amma zai zama abin mamaki gare ni ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Zan ceci mutanena daga ƙasashen gabas da yamma. Zan komo da su su zauna a Urushalima; za su zama mutanena, ni kuwa zan zama amintaccen Allahnsu mai adalci.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku da yanzu kuke jin maganan nan da annabawa suka faɗi, waɗanda suke a nan lokacin da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji Maɗaukaki, bari hannuwanku su zama da ƙarfi don a gama gina haikalin. Kafin wannan lokaci babu albashi domin mutum ko dabba. Ba wanda yake iya sakewa yă yi hidimominsa saboda maƙiya, domin na sa kowa yă zama maƙiyi maƙwabcinsa. Amma yanzu ba zan yi da waɗanda raguwar mutane yadda na yi da na dā ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Iri zai yi girma da kyau, kuringa za tă ba da ’ya’yanta, ƙasa za tă ba da hatsi, sama kuma za tă ba da raɓa. Zan ba da duk waɗannan abubuwa su zama gādo ga raguwar mutanen nan. Kamar yadda kuka zama abin la’ana a ƙasashe, ya Yahuda da Isra’ila, haka zan cece ku, za ku kuma zama albarka. Kada ku ji tsoro, sai dai ku bar hannuwanku su zama da ƙarfi.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Kamar dai yadda na yi niyyar kawo muku bala’i, in kuma ƙi jin tausayi sa’ad da kakanninku suka ba ni haushi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, kada ku ji tsoro “saboda a yanzu na yi niyya in sāke yi wa Urushalima da Yahuda abu mai kyau. Abubuwan da za ku yi ke nan. Ku gaya wa juna gaskiya, ku kuma dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunanku na shari’arku; kada ku ƙulla wa maƙwabtanku mugunta, kuma kada ku so yin rantsuwa ta ƙarya. Ina ƙyamar waɗannan duka,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. Maganar Ubangiji Maɗaukaki ta sāke zuwa wurina. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Azumin wata na huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai da na watan goma za su zama lokutan farin ciki da murna da kuma bukukkuwa na murna ga Yahuda. Saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Mutane da yawa da kuma mazaunan birane da yawa har yanzu za su zo, mazaunan wani birni za su je wurin mazaunan wani birni su ce, ‘Bari mu je nan da nan mu roƙi Ubangiji mu kuma nemi Ubangiji Maɗaukaki. Ni kaina zan je.’ Mutane da yawa kuma da al’ummai masu ƙarfi za su zo Urushalima su nemi Ubangiji Maɗaukaki su kuma roƙe shi.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “A kwanakin nan, mutane goma daga kabilu da al’ummai za su riƙe rigar mutumin Yahuda guda su ce, ‘Bari mu tafi tare da kai, domin mun ji cewa Allah yana tare da ku.’ ” Hukunci a kan abokan gāban Isra’ila Annabci. Maganar Ubangiji tana gāba da ƙasar Hadrak za tă kuma sauko a kan Damaskus, gama idanun dukan mutane da na kabilan Isra’ila suna a kan Ubangiji9.1 Ko kuwa Damaskus. Gama idon Ubangiji yana a kan dukan mutane, haka ma a kan kabilan Isra’ila,, da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita, da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai. Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi; ta tara azurfa kamar ƙasa, zinariya kuma kamar tarin shara a tituna. Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta, zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku, wuta kuma za tă cinye ta. Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro; Gaza za tă yi birgima cikin azaba, haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya. Gaza za tă rasa sarkinta za a kuma gudu a bar Ashkelon. Baƙi za su mallaki Ashdod, kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa. Zan kawar da jini daga bakinsu, zan kuma cire abincin da aka haramta daga tsakanin haƙoransu. Waɗanda za a bari za su zama na Allahnmu, su kuma zama shugabanni a Yahuda, Ekron kuma za tă zama kamar Yebusiyawa. Amma zan kāre gidana daga sojoji masu kai da kawowa. Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba, gama yanzu ina tsaro. Zuwan sarkin Sihiyona Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka. Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim, da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima, za a kuma karya bakan yaƙi. Zai yi shelar salama ga al’ummai. Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku, daga Kogi9.10 Wato, Yuferites kuma zuwa ƙarshen duniya.9.10 Ko kuwa ƙarshen ƙasa Ke kuma, saboda jinin alkawarina da ke, zan ’yantar da ’yan kurkukunki daga rami marar ruwa. Ku koma maɓuya, ya ku ’yan kurkuku masu sa zuciya; ko yanzu ma na sanar cewa zan mayar muku ninki biyu. Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana, in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya. Zan tā da ’ya’yanki maza, ya Sihiyona, gāba da ’ya’yanki, ya Girka, in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi. Ubangiji zai bayyana Sa’an nan Ubangiji zai bayyana a bisansu; kibiyarsa za tă wulga kamar walƙiya. Ubangiji Mai Iko Duka zai busa ƙaho; zai taho ta cikin guguwa daga kudu, Ubangiji Maɗaukaki kuma zai tsare su. Za su hallakar su kuma yi nasara da duwatsun majajjawa. Za su sha su yi kururuwa kamar sun sha ruwan inabi; za su cika kamar kwanon da ake amfani don a yayyafa jini a kusurwoyin bagade. Ubangiji Allahnsu zai cece su a wannan rana gama su mutanensa ne da kuma garkensa. Za su haska a cikin ƙasarsa kamar lu’ulu’u a rawani. Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa! Hatsi zai sa samari su yi murna, sabon ruwan inabi kuma zai sa ’yan mata su yi farin ciki. Ubangiji zai lura da Yahuda Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara; Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari. Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa. Gumaka suna maganganun ruɗu, masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya, suna faɗa mafarkan ƙarya suna ba da ta’aziyyar banza. Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi. “Ina fushi da makiyayan, zan kuma hukunta shugabannin; gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura da garkensa, wato, gidan Yahuda, zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi. Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito, daga gare shi za a samu abin kafa tenti, daga gare shi za a sami bakan yaƙi, daga gare shi za a sami kowane mai mulki. Tare za su10.4,5 Ko kuwa mai mulki, dukansu tare. 5 Su zama kamar mutane masu ƙarfi suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi. Domin Ubangiji yana tare da su, za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai. “Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yusuf. Zan maido da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar ban taɓa ƙinsu ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu zan kuma amsa musu. Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi, zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi. ’Ya’yansu za su gani su yi murna; zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji. Zan ba da alama in kuma tattara su. Ba shakka zan fanshe su; za su yi yawa kamar yadda suke a dā. Ko da yake na warwatsa su cikin mutane, duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni. Su da ’ya’yansu za su rayu, za su kuwa komo. Zan komo da su daga Masar in kuma tattara su daga Assuriya. Zan kawo su Gileyad da Lebanon, har wuri yă kāsa musu. Za su ratsa cikin tekun wahala; zan kwantar da raƙuman teku dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe. Za a ƙasƙantar da Assuriya, sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita. Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,” in ji Ubangiji. Buɗe ƙofofinki, ya Lebanon, don wuta ta cinye itatuwan al’ul naki. Yi kuka, ya itacen fir, gama itacen al’ul ya fāɗi; itatuwa masu daraja sun lalace! Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan; an sassare itatuwan babban kurmi! Ku ji kukan makiyaya; an ɓata musu wuraren kiwonsu masu ciyayi! Ku ji rurin zakoki; an lalatar da jejin Urdun! Makiyaya biyu Ga abin da Ubangiji Allahna ya ce, “Yi kiwon garken tumakin da za a yanka. Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba. Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.” Saboda haka na yi kiwon garken da za a yanka, musamman garken da ake zalunta. Sai na ɗauki sanduna biyu na kira ɗaya Tagomashi, ɗaya kuma Haɗinkai, sai na yi kiwon garken. Cikin wata guda na kawar da makiyayan nan uku. Garken suka ƙi ni, na kuwa gaji da su na ce, “Ba zan zama makiyayinku ba. Bari masu mutuwa su mutu, masu hallaka kuma su hallaka. Bari waɗanda suka ragu su ci naman juna.” Sai na ɗauki sandana mai suna Tagomashi na karya shi, na janye alkawarin da na yi da dukan al’ummai. An janye shi a ranan nan, saboda haka garken da yake cikin wahala masu kallona sun san cewa maganar Ubangiji ce. Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin. Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji. Sai na karya sandana na biyu mai suna Haɗinkai, ta haka na karya ’yan’uwantakar da take tsakanin Yahuda da Isra’ila. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na wawan makiyayi. Gama zan tā da makiyayi a ƙasar wanda ba zai kula da ɓatattu, ko yă nemi ƙanana, ko yă warkar da waɗanda suka ji ciwo, ko kuma ciyar da masu lafiya ba, sai dai zai ci naman keɓaɓɓun tumaki, yă farfasa kofatonsu. “Kaito ga banzan makiyayin nan, wanda ya bar garken! Bari takobi yă sare hannunsa da idonsa na dama! Bari hannunsa yă shanye gaba ƙaf, idonsa na dama kuma yă makance sarai!” Za a hallaka abokan gāban Urushalima Annabci, maganar Ubangiji game da Isra’ila. Ubangiji, wanda ya shimfiɗa sammai, wanda ya kafa harsashin duniya, wanda kuma ya yi ruhun mutum a cikinsa ya ce, “Zan sa Urushalima ta zama kwaf mai sa mutanen da suke a dukan kewayenta, jiri. Yaƙi zai kewaye Urushalima har yă shafi Yahuda ma. A ranan nan, sa’ad da duk al’umman duniya za su tayar mata, zan sa Urushalima ta zama dutsen da ba a iya matsarwa ga dukan al’ummai. Duk waɗanda suka yi ƙoƙari su matsar da shi za su ji ciwo. A ranan nan zan sa kowane doki yă tsorata, mai hawan dokin kuma yă haukace,” in ji Ubangiji. “Zan sa idanuna in tsare gidan Yahuda, amma zan makantar da dukan dawakan al’ummai. Sa’an nan shugabannin Yahuda za su ce a cikin zukatansu, ‘Mutanen Urushalima suna da ƙarfi domin Ubangiji Maɗaukaki shi ne Allahnsu.’ “A ranan nan zan sa shugabannin Yahuda su zama kamar tukunyar wuta a tarin itacen wuta; kamar harshen wuta a dammunan hatsi. Za su ƙone dukan mutanen da suke kewaye da su hagu da dama, amma babu abin da zai taɓa mutanen Urushalima. Ubangiji zai ceci wuraren zaman Yahuda da farko, don kada darajar gidan Dawuda da mazaunan Urushalima su fi na Yahuda daraja. A ranan nan Ubangiji zai kiyaye waɗanda suke zama a Urushalima, domin marasa ƙarfi a cikinsu su zama kamar Dawuda, gidan Dawuda kuma zai zama kamar Allah, kamar mala’ikan Ubangiji da yake tafiya a gabansu. A ranan nan zan fito don in hallaka dukan al’umman da suka yaƙi Urushalima. Makoki saboda wannan da suka soki “Zan kuma zubo wa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima ruhun alheri da na addu’a. Za su dube ni, wannan da suka soke shi, za su kuma yi makoki dominsa kamar yadda mutum yakan yi makokin mutuwar ɗansa tilo, su kuma yi baƙin ciki ƙwarai kamar yadda mutum yakan yi baƙin ciki don ɗan fari. A ranan nan kuka a Urushalima zai yi yawa kamar kukan Hadad Rimmon a filin Megiddo. Ƙasar za tă yi makoki, kowane iyali zai yi makoki a ware, tare da matansu su ma a ware, iyalin gidan Dawuda da matansu, iyalin gidan Natan da matansu, iyalin gidan Lawi da matansu, iyalin gidan Shimeyi da matansu, dukan sauran iyalan kuma da matansu. Tsarkakewa daga zunubi “A ranan nan za a buɗe maɓulɓulan ruwa zuwa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima, don a tsarkake su daga zunubi da rashin tsabta. “A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar. In kuma wani ya yi annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa’ad da yake yin annabci, iyayensa za su soke shi da takobi. “A ranan nan kowane annabi zai ji kunyar annabcin wahayinsa. Ba zai sa rigar annabci mai gashi ba don yă yi ruɗu. Zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne. Ni manomi ne; ƙasa ce nake samun abin zaman gari tun ina matashi.’13.5 Ko kuwa manomi; wani mutum ya sayar da a ƙuruciyata In wani ya tambaye shi, ‘Waɗanne miyaku ne haka a jikinka13.6 Ko kuwa miyaku a tsakanin hannuwanka?’ Zai amsa yă ce, ‘Miyakun da aka yi mini a gidan abokaina ne.’ An bugi makiyayin, tumakin suka watse “Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina, mutumin da yake kusa da ni sosai!” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kashe makiyayin, sai tumakin su watse, in kuma tayar wa ƙananan. A cikin ƙasar duka,” in ji Ubangiji, “kashi biyu bisa uku za a buge su su hallaka; duk da haka za a bar kashi ɗaya bisa uku a cikinta. Wannan kashi ɗaya bisa ukun zan kawo in sa a cikin wuta; zan tace su kamar azurfa in gwada su kamar zinariya. Za su kira bisa sunana zan kuwa amsa musu; zan ce, ‘Su mutanena ne,’ za su kuma ce, ‘Ubangiji ne Allahnmu.’ ” Ubangiji zai zo yă yi mulki Ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba muku ganimar da aka washe daga gare ku. Zan tara dukan al’ummai su yaƙi Urushalima; za a ci birnin da yaƙi, za a washe gidaje, a kuma yi wa mata fyaɗe. Rabin birnin zai je bauta, amma ba za a kwashe sauran mutanen daga birnin ba. Sa’an nan Ubangiji zai fita yă yi yaƙi da waɗannan al’ummai, kamar yadda yake yaƙi a ranar yaƙi. A ranan nan ƙafafunsa za su tsaya a kan Dutsen Zaitun, gabas da Urushalima, za a kuma tsage Dutsen Zaitun kashi biyu daga gabas zuwa yamma, yă zama babban kwari, rabin dutsen zai matsa zuwa wajen arewa, rabi kuma zai matsa zuwa wajen kudu. Za ku gudu ta wajen kwarin dutsena, gama zai miƙe har zuwa Azel. Za ku gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa14.5 Ko kuwa 5 Za a tare kwarin dutsena a kuma miƙe shi har zuwa Azel. Za a tare shi yadda aka tare saboda girgizar ƙasa a kwanakin Uzziya sarkin Yahuda. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo, tare da duk masu tsarki. A ranan nan ba za a kasance da haske ko sanyi ba, ko hazo mai duhu ba. Za tă zama rana ce ta musamman, ba yini ko dare, rana da take sananne ga Ubangiji. Sa’ad da yamma ta yi, za a yi haske. A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku14.8 Wato, Bahar Rum rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum,14.8 Wato, Bahar Maliya a damina da rani. Ubangiji zai sama sarki bisa dukan duniya. A ranan nan za a kasance da Ubangiji ɗaya, ba wani suna kuma sai nasa. Ƙasar gaba ɗaya daga Geba zuwa Rimmon, kudu da Urushalima, za tă zama kamar Araba. Amma Urushalima za tă kasance a wurinta, daga Ƙofar Benyamin zuwa sashen Ƙofa ta Farko, zuwa Ƙofar Kusurwa, daga kuma Hasumiyar Hananel zuwa wurin matsin ruwan inabin sarki. Za a zauna a cikinka; ba za a ƙara hallaka ta ba. Urushalima za tă zauna lafiya. Ga bala’in da Ubangiji zai bugi dukan al’umman da suka yi yaƙi da Urushalima. Fatar jikinsu za tă ruɓe tun suna tsaye a ƙafafunsu, idanunsu za su ruɓe a cikin kwarminsu, harsunansu kuma zai ruɓe a cikin bakunansu. A ranan nan Ubangiji zai sa maza su cika da tsoro ƙwarai. Kowane mutum zai kama hannun ɗan’uwansa, za su kai wa juna hari. Yahuda ma za tă yi yaƙi a Urushalima. Za a tattara dukiyar al’umman da suke kewaye, za a tara zinariya da azurfa masu yawan gaske tare da tufafi. Irin wannan bala’i zai auko wa dawakai da alfadarai, raƙuma da jakuna, da kuma dukan dabbobi a wannan sansani. Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul. In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji14.18 Ko kuwa sashe, sai Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba. Wannan ne zai zama hukuncin Masar da kuma na dukan al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba. A ranan nan za a rubuta TSARKI GA Ubangiji a jikin ƙararrawar dawakai, kuma tukwanen dahuwa a gidan Ubangiji za su zama kamar kwanoni masu tsarki a gaban bagade. Kowace tukunya a Urushalima da Yahuda za tă zama mai tsarki ga Ubangiji Maɗaukaki, kuma duk wanda ya zo don miƙa hadaya zai ɗauki waɗansu tukwane yă yi dahuwa da su. A ranan nan kuwa, ba Bakan’ane14.21 Ko kuwa mai ciniki da zai ƙara kasance a gidan Ubangiji Maɗaukaki.