- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Rut Rut Rut Rut Rut Na’omi ta rasa mijinta da ’ya’yanta maza A kwanakin da mahukunta suke mulki1.1 A gargajiyance alƙalai an yi yunwa a ƙasar, sai wani mutum daga Betlehem a Yahuda tare da matarsa da ’ya’yansu maza biyu, suka tafi su yi zama na ɗan lokaci a ƙasar Mowab. Sunan mutumin, Elimelek ne, sunan matarsa Na’omi; sunayen ’ya’yan nan nasu biyu, su ne Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Betlehem ta Yahuda. Suka kuwa tafi Mowab suka zauna a can. To, Elimelek mijin Na’omi ya rasu, aka bar ta da ’ya’yanta maza biyu. Suka auri mata Mowabawa, sunan ɗaya Orfa ɗayan kuma Rut. Bayan sun zauna a can kamar shekara goma, sai Malon da Kiliyon suka mutu su ma, aka kuma bar Na’omi babu ’ya’yanta maza biyu da kuma mijinta. Na’omi da Rut sun dawo Betlehem Sa’ad da ta ji a Mowab cewa Ubangiji ya zo don yă taimaki mutanensa ta wurin tanada musu da abinci, sai Na’omi tare da surukanta suka shirya su koma gida daga can. Tare da surukanta biyu suka bar inda suka zauna suka kuma kama hanya da za tă komar da su zuwa ƙasar Yahuda. Sai Na’omi ta ce wa surukanta biyu, “Ku koma, kowannenku, zuwa gidan mahaifiyarta. Bari Ubangiji yă nuna muku alheri yadda kuka nuna wa matattun nan da kuma gare ni. Bari Ubangiji yă sa kowannenku ta sami hutu a gidan wani miji.” Sa’an nan ta sumbace su suka kuma yi kuka da ƙarfi suka ce mata, “Za mu tafi tare da ke zuwa ga mutanenki.” Amma Na’omi ta ce, “Ku koma gida, ’ya’yana mata. Don me za ku tafi tare da ni? Zan ƙara samun waɗansu ’ya’ya maza da za su zama mazanku ne? Ku koma gida ’ya’yana mata; na tsufa ainun da zan sāke samun wani miji. Ko ma na yi tsammani har yanzu ina da bege, ko ma na sami miji a wannan dare na kuma haifi ’ya’ya maza, za ku jira sai sun yi girma? Za ku ci gaba da kasance babu aure saboda su? A’a, ’ya’yana mata. Ina da baƙin ciki ƙwarai fiye da ku, domin hannun Ubangiji ya yi gāba da ni!” A kan wannan suka sāke ɓarke da kuka. Sa’an nan Orfa ta sumbaci surukarta ta yi bankwana, amma Rut ta manne mata. Sai Na’omi ta ce, “Duba, ’yar’uwanki ta koma zuwa ga mutanenta da kuma allolinta. Ki koma tare da ita.” Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna. Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.” Sa’ad da Na’omi ta gane cewa Rut ta ƙudura tă tafi tare da ita, sai ta daina nema tă koma. Saboda haka matan biyu suka ci gaba da tafiya sai da suka isa Betlehem. Da suka isa Betlehem, sai dukan garin ya ruɗe saboda su, matan kuwa suka ce, “Na’omi ce wannan kuwa?” Ta ce musu, “Kada ku kira ni Na’omi.1.20 Na’omi yana nufin mai daɗi; haka ma a aya 21. Ku kira ni Mara1.20 Mara yana nufin ɗaci. gama Maɗaukaki1.20 Da Ibraniyanci an rubuta Shaddai ne a nan. ya sa raina ya yi ɗaci sosai. In tafi cikakke, amma Ubangiji ya dawo da ni ba kome. Don me kuke kirana Na’omi? Ubangiji ya wahalshe1.21 Ko kuwa ba da shaida gāba da ni. ni, Maɗaukaki ya kawo mini masifa.” Na’omi fa ta koma daga Mowab tare da Rut mutuniyar Mowab, surukarta, suka kai Betlehem a lokacin da ake fara girbin sha’ir. Rut ta sadu da Bowaz To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz. Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.” Na’omi ta ce mata, “Ki je, ’yata.” Saboda haka ta tafi ta fara kala a gonaki a bayan masu girbi. Sai ya zamana, ta sami kanta tana aiki a gonar da take ta Bowaz, wanda yake daga dangin Elimelek. Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “Ubangiji yă kasance tare da ku!” Sai suka amsa, “Ubangiji yă albarkace ka!” Sai Bowaz ya tambayi shugaban masu girbinsa, “Wace yarinya ce wannan?” Shugaban ya amsa, “Ita ce mutuniyar Mowab da ta zo daga Mowab tare da Na’omi. Ta ce, ‘Ina roƙo a bar ni in bi bayan masu girbin in yi kala.’ Haka ta shiga cikin gonar ta kuwa yi aiki tun da safe har zuwa yanzu, sai ɗan hutun da ta yi kaɗan.” Saboda haka Bowaz ya ce wa Rut, “’Yata, ki saurare ni. Kada ki tafi ki yi kala a wani gona, kada kuma ki tafi daga nan. Ki tsaya nan tare da ’yan matana bayi. Ki lura da gonar da mutanena suke girbi, ki bi su tare da ’yan matana. Na riga na faɗa wa mazan kada su taɓa ke. Kuma duk sa’ad da kika ji ƙishirwa, ki tafi ki ɗebo ruwa daga tulunan da mazan suka cika.” Jin haka, sai ta rusuna da fuskata har ƙasa ta ce, “Me ya sa na sami irin wannan tagomashi a idanunka da har ka lura da ni, ni da nake baƙuwa?” Bowaz ya amsa, “An faɗa mini duka game da abin kika yi domin surukarki tun mutuwar mijinki, yadda kika bar mahaifinki da mahaifiyarki da kuma ƙasarki kika zo ki yi zama da mutanen da ba ki taɓa sani ba. Bari Ubangiji yă sāka maka saboda abin da ka yi. Bari Ubangiji, Allah na Isra’ila yă sāka maka a yalwace, a ƙarƙashin fikafikan da ka sami mafaka.” Ta ce, “Bari in ci gaba da samun tagomashi a idanunka ranka yă daɗe. Ka ta’azantar da ni ka kuma yi wa baranyarka magana mai alheri ko da yake ban kai matsayi ɗaya daga cikin bayinka ’yan mata ba.” A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.” Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa. Da ta tashi don tă yi kala, sai Bowaz ya yi umarni wa samarinsa cewa, “Ko ta tara daga cikin dammuna, kada ku wulaƙanta ta. Ku kuma riƙa zarar mata waɗansu daga dammunan don ta ɗauka, kada ku kwaɓe ta.” Saboda haka Rut ta yi kala a gonar har yamma. Sa’an nan ta sussuka hatsin sha’ir da ta kalata ta sami kamar efa.2.17 Wato, kusan bushel uku bisa biyar (Kamar lita 22) Ta ɗauka ta koma gari sai surukarta ta ga yawan abin da ta kalato. Rut kuma ta fitar da ragowar abin da ta ci bayan ta ƙoshi ta ba ta. Surukarta ta tambaye ta, “Ina kika yi kala a yau? Ina kika yi aiki? Albarka ta tabbata ga mutumin nan ta ya lura da ke!” Sai Rut ta faɗa wa surukarta game da wurin wanda ta yi ta aiki. Ta ce, “Sunan mutumin da na yi aiki da shi a yau Bowaz ne.” Sai Na’omi ta ce wa surukarta, “Ubangiji yă yi masa albarka! Bai daina nuna alheri ga masu rai da matattu ba.” Ta ƙara da cewa, “Wannan mutum danginmu ne na kusa; shi ɗaya daga cikin danginmu mai fansa.” Sa’an nan Rut mutuniyar Mowab ta ce, “Ya ma ce mini, ‘Ki riƙa bin ma’aikatana sai sun ƙare yin girbin dukan hatsina.’ ” Na’omi ta ce wa Rut surukarta, “Zai fi miki kyau, ’yata ki riƙa tafiya da ’yan matansa, domin a gonar wani dabam mai yiwuwa a yi miki lahani.” Saboda haka Rut ta tsaya kusa da bayi mata na Bowaz don tă yi kala sai da girbin sha’ir da na alkama suka ƙare. Ta kuwa zauna tare da surukarta. Rut da Bowaz a masussuka Wata rana Na’omi surukar Rut ta ce mata, “’Yata, bai kamata in nema miki gida,3.1 Da Ibraniyanci an rubuta in sami miki hutu ne a nan. inda za a tanada miki da kyau? Bowaz wanda kike aiki da bayinsa ’yan mata ba danginmu ne na kusa ba? Da daren yau zai sussuka sha’ir nasa a masussuka. Ki yi wanka ki fesa turare, ki kuma sa tufafinki mafi kyau. Sa’an nan ki gangara zuwa masussuka, amma kada ki bari yă san cewa kina a can sai ya gama ci da sha. Sa’ad da ya kwanta, ki lura da inda yake kwance. Sa’an nan ki tafi ki buɗe ƙafafunsa ki kwanta. Zai faɗa miki abin da za ki yi.” Rut ta amsa ta ce “Zan yi abin da kika faɗa.” Saboda haka ta gangara zuwa masussuka ta kuma yi dukan abin da surukarta ta ce ta yi. Sa’ad da Bowaz ya gama ci da sha yana kuma cikin farin ciki, sai ya tafi ya kwanta a ƙarshen tarin hatsi. Rut kuwa ta sulalle ta je ta buɗe ƙafafunsa ta kwanta. Da tsakar dare sai wani abu ya firgitar da mutumin, ya kuwa juya sai ya tarar da mace kwance a ƙafafunsa. Sai ya yi tambaya ya ce, “Ke wace ce?” Ta amsa ta ce, “Ni ce baranyarka Rut, ka rufe ni ta mayafinka da yake kai dangi, mai fansa ne na kusa.” Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji yă albarkace ki ’yata. Wannan alheri ya fi wannan da kika nuna da farko. Ba ki gudu kin bi saurayi, mai arziki ko matalauci ba. Yanzu kuwa ’yata kada ki ji tsoro. Zan yi miki dukan abin da kika roƙa. Dukan ’yan’uwana na gari sun san cewa ke mace ce mai halin kirki. Ko da yake gaskiya ne ni dangi ne na kusa, amma akwai dangi mai fansa mafi kusa fiye da ni. Ki kwana a nan, da safe kuwa in yana so yă fansa, to, da kyau, sai yă fansa. Amma in ba ya niyya, tabbatacce, na rantse da Ubangiji mai rai zan yi. Ki kwanta a nan sai da safe.” Saboda haka ta kwanta a ƙafafunsa sai da safe, amma ta tashi kafin a gane wani, sai ya ce, “Kada ki bar wani yă san cewa mace ta zo masussuka.” Ya kuma ce, “Ki kawo gyalenki da kika yafa ki shimfiɗa shi a nan.” Sa’ad da ta yi haka, sai ya zuba mudu shida na sha’ir ya sa mata a kai. Sa’an nan ya3.15 Da yawa cikin rubuce-rubucen hannun Ibraniyanci, yawancin rubuce-rubucen Ibraniyanci, Bulget da na Siriyak suna da ita ce a nan. koma gari. Sa’ad da Rut ta koma wurin surukarta Na’omi ta tambaye ta “Yaya aka yi ’yata?” Sai ta faɗa mata dukan abin da Bowaz ya yi mata ta kuma ƙara da cewa, “Ya ba ni waɗannan mudu shida na sha’ir, yana cewa, ‘Kada ki koma wurin surukarki hannu wofi.’ ” Sai Na’omi ta ce, “Ki jira, ’yata, sai kin ga abin da zai faru. Gama mutumin ba zai huta ba sai an warware batun a yau.” Bowaz ya auri Rut Ana cikin haka Bowaz ya haura zuwa ƙofar gari ya tafi ya zauna a can. Sa’ad da dangi mai fansan da ya yi zance ya iso, Bowaz ya ce, “Zo nan abokina ka zauna.” Saboda haka ya ratso ya zauna. Bowaz kuwa ya kira dattawa guda goma na garin ya ce, “Ku zauna a nan,” suka kuwa zauna. Sa’an nan ya ce wa dangin nan mai fansa, “Na’omi, wadda ta dawo daga Mowab, tana so ta sayar da filin da yake na ɗan’uwanmu Elimelek. Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka4.4 Da yawa cikin rubuce-rubucen hannun Ibraniyanci, Seftuwajin, Bulget da na Siriyak, yawancin rubuce-rubucen Ibraniyanci, suna da shi ne a nan. yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.” Sai ya ce, “Zan fansa.” Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi4.5 Da Ibraniyanci, Bulget da na Siriyak, Na’omi, ka saya Rut mutuniyar Mowab gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.” Da jin haka, sai dangin nan mai fansa ya ce, “To, ba zan iya fanshe shi ba don kada in yi wa nawa mallakar rauni. Za ka iya fanshe shi wa kanka. Ni dai ba zan iya ba.” (To, a kwanakin can a Isra’ila, domin a tabbatar da fansa da kuma musayar da mallaka, mutum zai cire takalminsa ya ba wa ɗayan. Wannan ita ce hanyar tabbatar da al’amarin a hukumance a cikin Isra’ila.) Saboda haka dangin nan mai fansa ya ce wa Bowaz, “Saye shi wa kanka.” Sai ya cire takalminsa. Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon. Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!” Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem. Ta wurin ’ya’yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace, bari iyalinka yă zama kamar na Ferez, wanda Tamar ta haifa wa Yahuda.” Na’omi ta sami yaro Sai Bowaz ya ɗauki Rut ta kuwa zama matarsa. Sa’an nan ya kwana da ita, Ubangiji kuma ya sa ta yi ciki, ta haifi ɗa. Mata suka ce wa Na’omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda a wannan rana bai bar ki ba tare da dangi mai fansa ba. Allah yă sa yă zama sananne a dukan Isra’ila! Zai sabunta rayuwarki yă adana ki a tsufanki. Gama surukarki wadda take ƙaunarki wadda kuma take mafi kyau gare ki fiye da ’ya’ya maza bakwai, ta haife shi.” Sai Na’omi ta ɗauki yaron, ta kwantar da shi a cinyarta ta kuma kula da shi. Matan da suke zama a wurin suka ce, “Na’omi ta sami yaro.” Suka kuwa ba shi suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, mahaifin Dawuda. Ga asalin zuriyar Ferez. Ferez shi ne mahaifin Hezron, Hezron ya haifi Ram, Ram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,4.20 Kaɗan daga cikin rubuce-rubucen Ibraniyanci waɗansu rubuce-rubucen Seftuwajin da Bulget (dubi kuma aya 21 da kuma Seftuwajin na 1Tar 2.11); yawancin rubuce-rubucen Ibraniyanci suna da Salma ne. Salmon ya haifi Bowaz, Bowaz ya haifi Obed, Obed ya haifi Yesse, Yesse kuwa ya haifi Dawuda.