- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Ru’uya ta Yohanna Ru’uya ta Yohanna Ru’uya ta Yohanna R Yoh Ru’uya ta Yohanna Gabatarwa Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna, wanda ya shaida dukan abin da ya gani, wato, maganar Allah da kuma shaidar Yesu Kiristi. Mai albarka ne wanda yake karanta waɗannan kalmomin annabci, masu albarka ne kuma waɗanda suke jinsu, suke kuma sa abin da aka rubuta a ciki a zuciya, domin lokaci ya yi kusa. Gaisuwa da yabo Daga Yohanna, Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya. Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa, da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya. Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa, ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin. “Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.” Bari yă zama haka nan! Amin. “Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.” Wani kama da Ɗan Mutum Ni, Yohanna, ɗan’uwanku da kuma abokin tarayyarku cikin wahala da mulki, da kuma haƙurin jimrewa da suke namu cikin Yesu, ina can tsibirin Fatmos saboda maganar Allah da kuma saboda shaidar Yesu. A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho, wadda ta ce, “Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.” Sai na juya don in ga muryar da take magana da ni. Da na juya kuwa sai na ga alkukan fitilu bakwai na zinariya. A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,”1.13 Dubi Dan 7.13. saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa. Kansa da kuma gashin fari ne fat kamar ulu, fari kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kuwa kamar harshen wuta. Sawunsa sun yi kamar tagullar da take haske cikin matoya, muryarsa kuma ta yi kamar muryar ruwaye masu gudu. A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta. Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe. Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades. “Saboda haka, ka rubuta abin da ka gani, abin da yake yanzu, da abin da zai faru nan gaba. Asirin taurari bakwai da ka gani a hannuna na dama da kuma na alkukan fitilu bakwai na zinariya shi ne, Taurarin bakwai ɗin nan, mala’ikun ikkilisiyoyi bakwai ne; alkukan fitilu bakwai ɗin nan kuma ikkilisiyoyi bakwai ne. Zuwa ga ikkilisiya a Afisa “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya. Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne. Kai kam ka daure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba. Duk da haka ina riƙe da wannan game da kai. Ka watsar da ƙaunarka ta farko. Ka tuna da matsayinka a dā kafin ka fāɗi! Ka tuba ka kuma yi ayyukan da ka yi da fari. In ba ka tuba ba, zan zo wajenka in ɗauke wurin ajiye fitilanka daga inda yake. Sai dai kana da wannan abu mai kyau. Ka ƙi ayyukan Nikolaitawa da ni ma nake ƙi. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah. Zuwa ga ikkilisiya a Simirna “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai. Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne. Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan. Zuwa ga ikkilisiya a Fergamum “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Fergamum, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin wannan wanda yake da takobi mai kaifi biyu. Na san inda kake da zama, inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku, inda Shaiɗan yake zama. Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci. Haka ma kana da waɗanda suke riƙe da koyarwar Nikolaitawa. Saboda haka ka tuba! In ba haka ba, zan zo wajenka ba da daɗewa ba in yaƙe su da takobin bakina. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen. Zuwa ga ikkilisiya a Tiyatira “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Tiyatira, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin Ɗan Allah, wanda idanunsa suna kama da harshen wuta wanda kuma ƙafafunsa suna kama da tagullar da aka goge. Na san ayyukanka, ƙaunarka da bangaskiyarka, hidimarka da daurewarka, kuma cewa kana yin abubuwa a yanzu fiye da abin da ka yi da farko. Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka. Na ba ta lokaci tă tuba daga fasikancinta, amma ba ta da niyya. Don haka zan jefa ta a kan gadon wahala, zan kuma sa waɗanda suke zina da ita, su sha azaba ƙwarai, sai dai in sun tuba daga hanyoyinta. Zan kashe ’ya’yanta. Sa’an nan dukan ikkilisiyoyi za su san cewa ni ne mai bincika zukata da tunani, zan kuwa sāka wa kowannenku gwargwadon ayyukansa. Yanzu, ina ce wa sauranku da kuke a Tiyatira, ku da ba ku riƙe da koyarwarta ba kuma ba ku koyi abin da suke kira zurfafan asiran Shaiɗan, ‘Ba zan ƙara muku wani nauyi ba. Sai dai ku riƙe abin da kuke da shi har sai na zo.’ Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai. ‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’2.27 Zab 2.9 kamar yadda na karɓi iko daga Ubana. Zan kuma ba shi tauraron asubahi. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Zuwa ga ikkilisiya a Sardis “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Sardis, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake riƙe da ruhohi bakwai na Allah da kuma taurari bakwai. Na san ayyukanka; ana ganinka kamar rayayye, amma kai matacce ne. Ka farka! Ka ƙarfafa abin da ya rage wanda kuma yake bakin mutuwa, don ban ga ayyukanka cikakke ne ba a gaban Allahna. Saboda haka, ka tuna fa, abin da ka karɓa ka kuma ji; ka yi biyayya da shi, ka kuma tuba. Amma in ba ka farka ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san lokacin da zan zo maka ba. Duk da haka kana da mutane kima cikin Sardis waɗanda ba su ɓata tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni, saye da fararen tufafi, don sun cancanta. Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Zuwa ga ikkilisiya a Filadelfiya “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Filadelfiya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake mai tsarki da kuma gaskiya, wanda yake riƙe da mabuɗin Dawuda. Abin da ya buɗe ba mai rufewa, abin da kuma ya rufe ba mai buɗewa. Na san ayyukanka. Duba, na sa a gabanka buɗaɗɗen ƙofa wadda ba mai iya rufewa. Na san cewa kana da ɗan ƙarfi, duk da haka ka kiyaye maganata ba ka kuwa yi mūsun sunana ba. Zan sa waɗanda suke na majami’ar Shaiɗan, waɗanda suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai maƙaryata, zan sa su zo su fāɗi a ƙasa a gabanka su kuma shaida cewa na ƙaunace ka. Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya. Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka. Duk wanda ya ci nasara zan mai da shi ginshiƙi a haikalin Allahna. Ba kuwa zai sāke barin wurin ba. Zan rubuta a kansa sunan Allahna da kuma sunan birnin Allahna, sabuwar Urushalima, wadda take saukowa daga sama daga Allahna; ni kuma zan rubuta a kansa sabon sunana. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Zuwa ga ikkilisiya a Lawodiseya “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Lawodiseya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomina Amin, amintaccen mashaidi mai gaskiya, da kuma mai mulkin halittar Allah. Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi! Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina. Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara. Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani. Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba. Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.” Kursiyi a sama Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.” Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa. Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin. Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu. Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah. Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya. Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama. Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa, “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’ wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.” Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa, “Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.” Naɗaɗɗen littafi da kuma Ɗan Ragon Sa’an nan na ga a hannun damar wannan wanda yake zaune a kursiyin naɗaɗɗen littafi da rubutu a ciki da wajensa an kuma hatimce shi da hatimai bakwai. Na kuma ga wani babban mala’ika yana shela da babbar murya cewa, “Wa ya cancanta yă ɓalle hatiman nan yă kuma buɗe naɗaɗɗen littafin?” Amma ba wani a sama ko a ƙasa ko a ƙarƙashin ƙasan da ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin ko ma yă duba cikinsa. Na yi ta kuka domin ba a iya samun wanda ya cancanta yă buɗe naɗaɗɗen littafin ko yă duba cikinsa ba. Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.” Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya. Ya zo ya karɓi naɗaɗɗen littafin daga hannun dama na wannan wanda yake zaune a kursiyin. Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. Suka rera sabuwar waƙa, “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin ka kuma buɗe hatimansa, domin an kashe ka, da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah, daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma. Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.” Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. Da babbar murya suka rera, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!” Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, sun tabbata har abada abadin!” Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada. Hatimai Na kalli yayinda Ɗan Ragon ya buɗe hatimin farko na hatimai bakwai ɗin nan. Sai na ji ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai ya yi magana da murya mai kama da tsawa ya ce, “Zo!” Na duba, can kuwa a gabana ga wani farin doki! Mai hawansa yana riƙe da baka, aka kuma ba shi rawani, ya yi sukuwa ya fito kamar mai nasara da ya kutsa don nasara. Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na biyun, sai na ji halitta mai rai na biyu ya ce, “Zo!” Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yă ɗauke salama daga duniya yă kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi. Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na uku, sai na ji halitta mai rai na uku ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga wani baƙin doki! Mai hawansa yana riƙe da abubuwan awo guda biyu a hannunsa. Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!” Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na huɗu, sai na ji muryar halitta mai rai na huɗu ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga ƙodaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya. Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi. Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su. Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini, taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi. Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa. Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan! Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?” An yi wa 144,000 hatimi Bayan wannan, na ga mala’iku huɗu, a tsaye a kusurwoyi huɗu na duniya, suna tsare iskoki huɗu na duniya, domin su hana wani iska hurawa a bisan ƙasa ko a bisan teku ko a bisa wani itace. Sai na ga wani mala’ika yana zuwa daga gabas, yana da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya wa mala’ikun nan huɗu da aka ba su iko su cuci ƙasa da teku ya ce, “Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.” Sai na ji yawan waɗanda aka sa musu hatimi. Su 144,000 daga dukan kabilan Isra’ila. Daga kabilar Yahuda mutum 12,000 ne aka sa musu hatimin, daga kabilar Ruben mutum 12,000, daga kabilar Gad mutum 12,000, daga kabilar Asher mutum 12,000, daga kabilar Naftali mutum 12,000, daga kabilar Manasse mutum 12,000, daga kabilar Simeyon mutum 12,000, daga kabilar Lawi mutum 12,000, daga kabilar Issakar mutum 12,000, daga kabilar Zebulun mutum 12,000, daga kabilar Yusuf mutum 12,000, daga kabilar Benyamin mutum 12,000. Babban taro sanye da fararen tufafi Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa, “Ceto na Allahnmu ne, wanda yake zaune a bisan kursiyi, da kuma na Ɗan Ragon.” Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, suna cewa, “Amin! Yabo da ɗaukaka, da hikima da godiya da girma da iko da ƙarfi sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin. Amin!” Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi su wane ne, daga ina kuma suka fito?” Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. Saboda haka, “suna a gaban kursiyin Allah suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa; kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu. ‘Ba za su sāke jin yunwa ba; ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba. Rana ba za tă buga su ba,’ ko kuma kowane irin zafin ƙuna. Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu; ‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’ ‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ” Hatimi na bakwai da kaskon zinariya Sa’ad da ya buɗe hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kusan rabin sa’a. Sai na ga mala’iku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai. Wani mala’ika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yă miƙa tare da addu’o’in dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin. Hayaƙin turaren tare da addu’o’in tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun mala’ikan. Sai mala’ikan ya ɗauki kaskon, ya cika shi da wuta daga bagaden, ya kuma wurga shi bisan duniya; sai aka yi ta yin tsawa, ƙararraki, walƙiya, da kuma girgizar ƙasa. Ƙahoni Sai mala’iku bakwai ɗin nan da suke da ƙahoni bakwai suka shirya don su busa su. Mala’ika na fari ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta haɗe da jini, aka kuma wurga su bisan duniya. Kashi ɗaya bisa uku na duniya ya ƙone, kashi ɗaya bisa uku na itatuwa suka ƙone, dukan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone. Mala’ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai ga wani abu kamar babban dutse mai cin wuta, aka jefa cikin teku. Kashi ɗaya bisa uku na teku ya zama jini, kashi ɗaya bisa uku na halittu masu rai da suke cikin tekun suka mutu, kashi ɗaya bisa uku kuma na jiragen ruwa kuma suka hallaka. Mala’ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa. Mala’ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare. Yayinda nake kallo, sai na ji gaggafar da take tashi sama a tsakiyar sararin sama ta yi kira da babbar murya ta ce, “Kaito! Kaito! Kaiton mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala’ikun nan uku suke shirin busawa!” Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya. Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani. Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum. Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu. Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane. Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki. Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi. Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar. Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon.9.11 Abaddon da kuma Afolliyon suna nufin Maihallakarwa. Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa. Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah. Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.” Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam. Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu. Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa. Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu. Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni. Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba. Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba. Mala’ika da ƙaramin naɗaɗɗen littafi Sai na ga wani babban mala’ika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta. Yana riƙe da ɗan ƙaramin naɗaɗɗen littafi, wanda yake a buɗe a hannunsa. Ya kafa ƙafarsa ta dama a kan teku ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa, ya kuma yi ihu da ƙarfi kamar rurin zaki. Da ya yi ihun, sai muryoyin tsawan nan bakwai suka yi magana. Sa’ad da tsawan nan bakwai kuwa suka yi magana, ina dab da rubutawa; amma na ji wata murya daga sama ta ce, “Rufe abin da tsawan nan bakwai suka faɗa kada ka rubuta.” Sai mala’ikan da na gani na tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama. Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri! Amma a ranakun da mala’ika na bakwai na dab da busa ƙahonsa, za a cika asirin Allah, kamar yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.” Sai muryar da na ji daga sama ta sāke magana da ni ta ce, “Tafi, ka karɓi naɗaɗɗen littafin da yake a buɗe a hannun mala’ikan da yake tsaye bisa teku da ƙasa.” Sai na je wajen mala’ikan na ce masa yă ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yă yi tsami, amma ‘a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.’ ” Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun mala’ikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma sa’ad da na cinye, cikina ya yi tsami. Sa’an nan aka ce mini, “Dole ne ka sāke yin annabci game da mutane masu yawa, al’ummai, harsuna da kuma sarakuna.” Shaidu biyu Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can. Sai dai kada ka haɗa da harabar waje; kada ka auna ta, domin an ba da ita ga Al’ummai. Za su tattaka birni mai tsarki har watanni 42. Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.” Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za tă fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu. Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so. To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su. Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu. Kwana uku da rabi mutane daga kowace jama’a, kabila, harshe da kuma al’umma za su yi ta kallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su. Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya. Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su. Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna kallo. A wannan sa’a aka yi wata babbar girgizar ƙasa kashi ɗaya bisa goma kuma na birnin ya rushe. Aka kashe mutane dubu bakwai a girgizar ƙasar, waɗanda suka tsira kuwa suka ji tsoro suka ɗaukaka Allah na sama. Kaito na biyu ya wuce; kaito na uku yana zuwa ba da daɗewa ba. Ƙaho na bakwai Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.” Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, suna cewa, “Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki, wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā, domin ka karɓi ikonka mai girma ka kuma fara mulki. Al’ummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo. Lokaci ya yi don a shari’anta matattu, da kuma don sākawa wa bayinka annabawa da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka, ƙarami da babba, don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.” Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma. Mace da ƙaton maciji Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta. Tana da ciki ta kuma yi kuka mai zafi yayinda take gab da haihuwa. Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa. Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi. Ta haifi ɗa, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al’ummai da sandar ƙarfe. Aka fyauce ɗanta zuwa wurin Allah da kuma kursiyinsa. Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260. Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani. Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama. Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya. Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin ’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa. Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa. Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai, da ku da kuke zaune a cikinsu! Amma kaiton duniya da kuma teku, gama Iblis ya sauko gare ku! Ya cika da fushi, domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.” Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji. Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba. Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya. Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa. Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu. Dabbar daga teku Macijin kuwa13.1 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na baya-bayan nan suna da Na kuma ne a nan ya tsaya a bakin teku. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga teku. Tana da ƙahoni goma da kawuna bakwai, da kuma rawani goma a ƙahoninta, a kowane kai kuwa akwai sunan saɓo. Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma. Ɗaya daga cikin kawunan dabbar ya yi kamar yana da raunin da zai iya kashe shi, amma raunin nan da zai iya kashe shi ya riga ya warke. Dukan duniya ta yi mamaki ta kuma bi dabbar. Mutane suka yi wa macijin sujada domin ya ba wa dabbar ikonsa, suka yi wa dabbar sujada, suka kuma yi tambaya cewa, “Wane ne yake kama da dabban nan? Wa zai iya yaƙe ta?” Aka ba wa dabbar baki don ta faɗi kalmomin girman kai da na saɓo ta kuma yi amfani da ikonta har watanni arba’in da biyu. Ta buɗe bakinta don tă yi wa Allah saɓo, ta kuma ɓata sunansa da kuma mazauninsa da na waɗanda suke zama a sama. Aka ba ta iko tă yaƙi tsarkaka tă kuma ci nasara a kansu. Aka kuma ba ta iko bisa kowace kabila, jama’a, harshe da kuma al’umma. Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada, dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba.13.8 Ko kuwa rubutacce daga halittar duniya a littafin rai na Ɗan Ragon da aka yanka Duk mai kunne ji, bari yă ji. Duk wanda aka ƙaddara ga bauta, ga bauta zai tafi. Duk wanda aka ƙaddara za a kashe da takobi, da takobin za a kashe shi. Wannan yana bukata haƙuri da aminci a gefen tsarkaka. Dabba daga ƙasa Sai na ga wata dabba tana fitowa daga ƙasa. Tana da ƙahoni biyu kamar ɗan rago, amma ta yi magana kamar maciji. Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta. Ta kuma yi manyan ayyuka da kuma alamu masu banmamaki, har ta sa wuta ta sauko daga sama zuwa ƙasa a gaban idon mutane. Saboda alamun nan da aka ba ta iko tă yi a madadin dabban nan ta fari, sai ta ruɗi mazaunan duniya. Ta umarce su su kafa siffa don girmama dabbar da aka ji mata rauni da takobi duk da haka ta rayu. Aka ba ta iko tă ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don tă yi magana tă kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada. Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta. Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yă lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666. Ɗan Ragon da 144,000 Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu. Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu. Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya. Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon. Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne. Mala’iku uku Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.” Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.” Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.” Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu. Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu. Girbin duniya Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum”14.14 Dubi Dan 7.13. tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa. Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.” Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya. Wani mala’ika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi. Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin ’ya’yan inabin sun nuna.” Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah. Aka tattake su a wurin matsin inabi a bayan gari, jini kuwa ya yi ta gudana daga wurin matsin inabi tsayinsa ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300. Mala’iku bakwai da annobai bakwai Na ga wata babbar alama mai banmamaki a sama, mala’iku bakwai da annobai bakwai na ƙarshe, na ƙarshe, domin da su ne fushin Allah ya cika. Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa, “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki, ya Ubangiji Maɗaukaki. Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya, ya Sarkin zamanai. Wane ne ba zai ji tsoronka, yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji? Gama kai kaɗai ne mai tsarki. Dukan al’ummai za su zo su yi sujada a gabanka, gama an bayyana ayyukan adalcinka.” Bayan wannan sai na duba, a cikin sama kuwa sai ga haikali, wato, tabanakul na Shaida, a buɗe. Daga cikin haikalin mala’iku bakwai tare da annobai bakwai suka fito. Suna saye da tufafin lilin masu tsabta masu walƙiya, suna kuma saye da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu. Sai ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai, ya ba wa mala’iku bakwai nan kwanonin zinariya bakwai cike da fushin Allah, wanda yake raye har abada abadin. Aka kuma cika haikalin da hayaƙi daga ɗaukakar Allah da kuma daga ikonsa, kuma ba wanda ya iya shiga haikalin sai da aka cika annobai bakwai nan na mala’iku bakwai. Kwanoni bakwai na fushin Allah Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.” Mala’ika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada. Mala’ika na biyu ya juye kwanonsa a bisan teku, sai tekun ya zama jini kamar na mataccen mutum, kuma kowane abu mai rai da yake cikin tekun ya mutu. Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini. Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce, “Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai, kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan; gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka, ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.” Na kuma ji bagaden ya amsa, “I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki, hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.” Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta. Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi. Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi. Mala’ika na shida ya juye kwanonsa a bisan babban kogin Yuferites, sai ruwansa ya shanye don a shirya hanya saboda sarakuna daga Gabas. Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan. Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki. “Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.” Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon. Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!” Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce. Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa. Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba. Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai. Babilon, karuwa a kan dabbar Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.” Sa’an nan mala’ikan ya ɗauke ni cikin Ruhu zuwa hamada. A can na ga mace zaune a kan wata jan dabbar da aka rufe da sunayen saɓo tana kuma da kawuna bakwai da ƙahoni goma. Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. Sunan da aka rubuta a goshinta asiri ne, Babilon mai girma mahaifiyar karuwai da kuma na abubuwa masu banƙyama na duniya. Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu. Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai. Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka asirin macen nan da dabbar da take hawa, wadda take da kawuna bakwai da ƙahoni goma. Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo. “Wannan yana bukata hankali da kuma hikima. Kawuna bakwai nan tuddai bakwai ne da macen take zama a kai. Sarakuna bakwai ne kuma. Biyar sun fāɗi, ɗaya yana nan, ɗayan kuma bai zo ba tukuna; amma sa’ad da ya zo, zai kasance na ɗan lokaci. Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta. “Ƙahonin nan goma da ka gani sarakuna goma ne da ba su riga sun karɓi mulki ba, amma waɗanda na sa’a guda za su karɓi iko a matsayin sarakuna tare da dabbar. Suna da manufa guda za su kuma ba wa dabbar ikonsu da kuma sarautarsu. Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna, tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.” Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna. Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta. Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu tă yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika. Macen da ka gani ita ce babban birnin da yake mulki a bisan sarakunan duniya.” Makoki a kan Babilon Bayan wannan sai na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa. Ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi. Ta zama gidan aljanu da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu, wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama. Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.” Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fita daga cikinta, mutanena, don kada zunubanta su shafe ku, don kada wata annobarta ta same ku; gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta. Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku; ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi. Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata. Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta. A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce, ‘Ina zama kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’ Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata, mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta zai cinye ta, gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta. “Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita. Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’ “Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi; kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane. “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’ Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki su ce, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai! Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa. Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’ Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’ “Ki yi murna a kanta, ya sama! Ku yi murna, ku tsarkaka! Ku yi murna, ku manzanni da annabawa! Allah ya hukunta shi saboda abin da ya yi muku.” Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce, “Da wannan irin giggitawa za a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa, ba za a ƙara ganin ta ba. Ba za a ƙara jin ƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙaho a cikinki ba. Ba za a ƙara samun ma’aikaci na kowace irin sana’a a cikinki kuma ba. Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙa a cikinki kuma ba. Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa a cikinki ba. Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba. Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya. Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce. A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka, da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.” Halleluya sau uku a kan fāɗuwar Babilon Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa, “Halleluya! Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu, gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma. Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta. Ya rama jinin bayinsa a kanta.” Suka sāke tā da murya suka ce, “Halleluya! Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.” Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce, “Amin, Halleluya!” Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku da kuke bayinsa, ku da kuke tsoronsa, babba da yaro!” Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki. Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta. Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta ta sanya.” (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.) Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.” Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.” Mahayi a kan farin doki Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi. Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi. Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin. Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki. A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji. Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah, don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.” Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa. Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu. Shekaru dubu Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu. Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci. Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu. (Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko. Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu. Hallakar Shaiɗan Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku. Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su. Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin. An shari’anta matattu Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan. Sabuwar sama da sabuwar duniya Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.” Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.” Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.” Ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.” Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah. Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar lu’ulu’u mai daraja sosai, kamar yasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi. Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma mala’iku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila. Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma. An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon. Mala’ikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa. Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke. Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga ma’aunin mutum, wanda mala’ikan ya yi amfani da shi. An yi katangar da yasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi yasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu, na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya yasin, na goma sha biyu kuma ametis. Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin. Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin. Al’ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin. Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba. Za a kawo ɗaukaka da girmar al’ummai a cikin birnin. Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon. An maido da Eden Sai mala’ikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon, yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ’ya’ya goma sha biyu, yana ba da ’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne. Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima. Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin. Yohanna da Mala’ikan Mala’ikan ya ce mini, “Waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa, ya aiki mala’ikansa, don yă nuna wa bayinsa abubuwan da za su faru nan ba da daɗewa ba.” “Ga shi! Ina zuwa da wuri! Mai albarka ne wanda yake kiyaye kalmomin annabcin da suke cikin wannan littafi.” Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!” Sa’an nan ya gaya mini cewa, “Kada ka rufe kalmomin annabcin littafin nan, domin lokaci ya yi kusa. Duk mai yin laifi yă ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yă ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yă ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yă ci gaba da yin abin da yake da tsarki.” Maganar ƙarshe. Gayyata da gargaɗi “Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe. “Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi. Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta. “Ni, Yesu, na aiko mala’ikana ya ba ka wannan shaida saboda ikkilisiyoyi. Ni ne Tushe da kuma Zuriyar Dawuda, da kuma Tauraron Asubahi mai haske.” Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yă zo; duk mai bukata kuma, yă ɗibi ruwan rai kyauta. Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi. Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan. Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan. Shi da ya shaida waɗannan abubuwa ya ce, “I, ina zuwa da wuri.” Amin. Zo, Ubangiji Yesu! Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da mutanen Allah. Amin.