- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Zabura Zabura Zabura Zab Zabura LITTAFI NA ƊAYA Zabura 1–41 Zabura 1 Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a. Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana. Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara. Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa. Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai. Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka. Zabura 2 Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza? Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.” Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a. Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa, “Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.” Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne; yau na zama Mahaifinka. Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka. Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.” Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo; ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya. Ku bauta wa Ubangiji da tsoro ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki. Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi ku hallaka a abubuwan da kuke yi, gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya. Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi. Zabura 3 Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni! Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela3.2 Kalmar da ba a tabbatar da ma’anarta ba, mai bayyana sau da sau a cikin Zabura; mai yiwuwa kalma ce ta kiɗi. Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba. Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye. Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela Zabura 4 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka amsa mini sa’ad da na kira gare ka, Ya Allahna mai adalci. Ka ba ni sauƙi daga wahalata; ka ji tausayina ka kuma ji addu’ata. Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya? Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Sela Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa; Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi. Cikin fushinku kada ku yi zunubi; sa’ad da kuke kan gadajenku, ku bincike zukatanku ku kuma yi shiru. Sela Ku miƙa hadayun da suka dace ku kuma dogara ga Ubangiji. Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?” Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji. Ka cika zuciyata da farin ciki sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa. Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau. Zabura 5 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Busa. Ta Dawuda. Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji, ka ji ajiyar zuciyata. Ka saurare kukata na neman taimako, Sarkina da Allahna, gama gare ka nake addu’a. Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata; da safe na gabatar da bukatuna a gabanka in kuma jira da sa zuciya. Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne; gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta. Masu fariya ba za su iya tsaya a gabanka ba. Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba. Kakan hallaka masu yin ƙarya. Masu kisankai da mutane masu ruɗu Ubangiji yana ƙyama. Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma, zan shiga gidanka; da bangirma zan durƙusa ga haikalinka. Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka saboda abokan gābana, ka fayyace hanyarka a gabana. Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita; marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu. Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne; da harshensu suna faɗin ƙarya. Ka furta su masu laifi, ya Allah! Bari makircinsu yă zama fāɗuwarsu. Ka kore su saboda yawan zunubansu, saboda sun tayar maka. Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna; bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki. Ka buɗe kāriyarka a bisansu, domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka. Gama tabbatacce, ya Ubangiji, kakan albarkaci adalai; kakan kewaye su da tagomashinka kamar garkuwa. Zabura 6 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Bisa ga sheminit.6.0 mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce. Ta Dawuda. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka. Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo. Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe? Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka. Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari?6.5 Da Ibraniyanci Sheol Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye. Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana. Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata. Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata. Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan. Zabura 7 Wani shiggayiyon7.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce. ta Dawuda, wanda Ya Rera wa Ubangiji game da Kush mutumin Benyamin. Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka; ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na, in ba haka ba za su yayyage ni kamar zaki su ɓarke ni kucu-kucu ba tare da wani da zai cece ni ba. Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure aka kuwa sami laifi a hannuwana, in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana, to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini; bari yă tattake raina a ƙasa ya sa in kwana a ƙura. Sela Ka tashi, ya Ubangiji, cikin fushinka; ka tashi gāba da fushin abokan gābana. Ka farka, Allahna, ka umarta adalci. Bari taron mutane su taru kewaye da kai. Ka yi mulki a bisansu daga bisa; bari Ubangiji mai shari’ar mutane. Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina, bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka. Ya Allah mai adalci, wanda yake binciken tunani da zukata, ka kawo ƙarshen rikicin mugaye ka kuma sa adalai su zauna lafiya. Garkuwata shi ne Allah Mafi Ɗaukaka, wanda yake ceton masu tsabtar zuciya. Allah alƙali ne mai adalci, Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana. In mutum bai tuba ba, Allah zai wasa takobinsa; zai tanƙware yă kuma ɗaura bakansa. Ya shirya makamansa masu dafi; ya shirya kibiyoyinsa masu wuta. Wanda yake da cikin mugunta ya kuma ɗauki cikin damuwa yakan haifi ƙarya. Wanda ya haƙa rami yakan fāɗa cikin ramin da ya haƙa. Damuwar da ya ja yakan sāke nannaɗe a kansa; fitinarsa takan sauka a kansa. Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka. Zabura 8 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.8.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai. Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru. Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu, wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi? Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah8.5 Ko kuwa da rayayyun sama ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma. Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa, dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji, tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Zabura 99 Mai yiwuwa Zabura 9 da 10 tun ainihi waƙa guda ce, ɓangarori mai ƙunshe da layi masu yawa waɗanda suka fara da harufan Ibraniyancin da suke bin juna. A Seftuwajin zabura guda ce. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka. Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka; zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka. Abokan gābana sun ja da baya; suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka. Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi; ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci. Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye; ka shafe sunansu har abada abadin. Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu, ka tuttumɓuke biranensu; yadda ma ba aka ƙara tunaninsu. Ubangiji yana mulki har abada; ya kafa kujerarsa don shari’a. Zai hukunta duniya da adalci; zai yi mulkin mutane cikin gaskiya. Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala. Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba. Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona; yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata. Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala. Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini! Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa, don in furta yabanka cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka. Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu; aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye. An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa; an kama mugaye da aikin hannuwansu. Haggayiyon.9.16 Ko kuwa Tunani; mai yiwuwa salon kiɗi ne. Sela Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah. Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba, ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka. Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka. Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. Sela Zabura 1010 Mai yiwuwa Zabura 9 da 10 tun ainihi waƙa guda ce, ɓangarori mai ƙunshe da layi masu yawa waɗanda suka fara da harufan Ibraniyancin da suke bin juna. A Seftuwajin zabura guda ce. Don me, ya Ubangiji, kake tsaya can da nesa? Me ya sa kake ɓoye kanka a lokutan wahala? Cikin fariyarsa mugun mutum yakan cuci marasa ƙarfi, waɗanda yake kama cikin makircin da ya shirya. Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa; yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji. Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah; cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah. Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara; yana da girman kai kuma dokokinka suna nesa da shi; yakan yi wa dukan abokan gābansa duban reni. Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni; kullum zan yi murna ba zan taɓa shiga wahala ba.” Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana; wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa. Yakan yi kwanto kusa da ƙauyuka; daga kwanton yakan kashe marar laifi. Yana kallon waɗanda za su shiga hannunsa a ɓoye. Yakan yi kwanto a ɓoye kamar zaki. Yakan yi kwanto don yă kama marasa ƙarfi; yakan kama marasa ƙarfi yă ja su cikin ragarsa. Yakan ragargaza waɗanda suka shiga hannu, su fāɗi; sukan fāɗi a ƙarƙashin ƙarfinsa. Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta; ya rufe fuskarsa ba ya gani.” Ka tashi, Ubangiji! Ka hukunta miyagu, ya Allah. Kada ka manta da marasa ƙarfi. Don me mugun mutum zai ƙi Allah? Don me yakan ce wa kansa, “Allah ba zai nemi hakki daga gare ni ba”? Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki; kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu. Marar taimako kan danƙa kansa gare ka; kai ne mai taimakon marayu Ka karye hannun mugaye da kuma mugun mutum; ka nemi hakki daga gare shi saboda muguntar da ba za a gane ba. Ubangiji Sarkin har abada abadin ne; al’ummai za su hallaka daga ƙasarsa. Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala; kakan ƙarfafa su, ka kuma saurari kukansu, kana kāre marayu da waɗanda aka danne, domin mutum, wanda yake na duniya kada ƙara haddasa wata razana. Zabura 11 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda. A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka. Yaya za ku ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu. Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu; sun kuma ɗana kibiyoyinsu don su harbi mutanen kirki a zuciya daga cikin duhu. Sa’ad da aka tumɓuke tushe, me adali zai iya yi?” Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki; Ubangiji yana a kursiyinsa a sama. Yana kallon ’ya’yan mutane; idanunsa suna bincike su. Ubangiji yana bincike adalai, amma ransa yana ƙi mugaye da masu son rikici. A kan mugaye zai zuba garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu; iska mai zafi zai zama rabonsu. Gama Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar gaskiya masu adalci za su ga fuskarsa. Zabura 12 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit.12.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce. Zabura ta Dawuda. Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane. Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu. Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya, masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?” “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.” Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai. Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada. Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane. Zabura 13 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Har yaushe, ya Ubangiji? Za ka manta da ni har abada ne? Har yaushe za ka ɓoye fuskarka daga gare ni? Har yaushe zan yi kokawa da tunanina kuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata? Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina? Ka dube ni ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna. Ka ba da haske ga fuskata, ko in yi barci cikin mutuwa; abokin gābana zai ce, “Na sha ƙarfinsa,” kuma abokan gābana za su yi murna sa’ad da na fāɗi. Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa; zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka. Zan rera ga Ubangiji gama ya yi mini alheri. Zabura 14 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau. Ubangiji ya duba daga sama a kan ’yan adam don yă ga ko akwai wani da ya gane, wani wanda yake neman Allah. Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu; babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau, ba ko ɗaya. Masu aikata mugunta za su taɓa koyo. Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji? Ga su, tsoro ya sha kansu, gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai. Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza, amma Ubangiji ne mafakansu. Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna! Zabura 15 Zabura ta Dawuda. Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki? Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa, wanda yake ƙin mugun mutum amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji, yakan cika alkawarinsa ko da ma ya zafe shi, wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba. Zabura 16 Miktam ne16.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalma ta kiɗa ce. na Dawuda. Ka kiyaye ni, ya Allah, gama a cikinka nake samun mafaka. Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana; in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.” Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa, su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana. Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli. Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba ko in ambaci sunayensu da bakina. Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na; ka kiyaye rabona, Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi; tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa. Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara; ko da dare ma zuciyata kan koya mini. Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba. Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya, domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka. Zabura 17 Addu’a ce ta Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci; ka saurari kukata. Ka kasa kunne ga addu’ata, ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya. Bari fiffitawata tă zo daga gare ka; bari idanunka su ga abin da yake daidai. Ko ka duba zuciyata, ka kuma bincike ni da dare, ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba; na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba. Game da ayyukan mutane kuwa, ta wurin maganar leɓunanka na kiyaye kaina daga hanyoyin tashin hankali. Sawuna sun kama hanyoyinka ƙafafu kuwa ba za su yi santsi ba. Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini; ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata. Ka nuna mini girmar ƙaunarka mai banmamaki, kai da kake ceton waɗanda suke neman mafaka daga abokan gābansu da hannunka na dama. Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido; ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka daga mugaye waɗanda suke kai mini hari, daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni. Sun rufe zukatansu marar tausayi, da bakunansu suna magana da fariya. Sun sa mini ido, yanzu sun kewaye ni, a shirye suke, su jefa ni a ƙasa. Suna kama da zaki mai yunwan abinci, kamar babban zaki mai fako a maɓuya. Ka tashi, ya Ubangiji, ka yi arangama da su, ka durƙusar da su; ka cece ni daga mugaye ta wurin takobinka. Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan, daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne. Kakan cika yunwan waɗanda kake so; ’ya’yansu suna da isashe suna kuma ajiyar wadata wa ’ya’yansu. Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka. Zabura 18 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Ya rera ta ga Ubangiji kalmomin wannan waƙa sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa da kuma daga hannun Shawulu, ya ce, Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina. Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata. Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa kuɓuta daga abokan gābana. Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni; rigyawan hallaka sun sha kaina. Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni; tarkon mutuwa ya yi mini arangama. Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa. Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, tussan duwatsu sun girgiza; sun yi rawa domin ya yi fushi. Hayaƙi ya tashi daga kafan hancinsa; wuta mai ci daga bakinsa, garwashi wuta mai ci daga bakinsa. Ya buɗe sammai ya sauko; baƙaƙen gizagizai suna a ƙarƙashin ƙafafunsa. Ya hau kerubobi ya kuma yi firiya; ya yi shawagi a fikafikan iska. Ya mai da duhu abin rufuwarsa, rumfa kewaye da shi, baƙaƙen gizagizan ruwan sama na sarari, daga cikin hasken kasancewarsa gizagizai suka yi gaba, da ƙanƙara da kuma walƙiya. Ubangiji ya yi tsawa daga sama; muryar Mafi Ɗaukaka ya yi kāra. Ya harba kibiyoyinsa ya kuma watsar da abokan gāba, walƙiya mai girma ya fafare su. Kwarin teku sun bayyana tussan duniya sun bayyana a fili sa’ad da ka tsawata, ya Ubangiji, sa’ad da ka numfasa daga hancinka. Ya miƙa hannunsa daga sama ya kama ni; ya ja ni daga zurfin ruwaye. Ya cece ni daga abokin gābana mai ƙarfi, daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina. Sun yi arangama da ni a ranar masifa, amma Ubangiji ya zama mai taimakona. Ya fitar da ni zuwa wuri mai sarari; ya kuɓutar da ni, gama yana jin daɗina. Ubangiji ya yi haka da ni bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya ba ni lada. Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi mugunta ta wurin juyewa daga Allahna ba. Dukan dokokinsa suna a gābana; ban juye daga ƙa’idodinsa ba. Na kasance marar laifi a gabansa na kuma kiyaye kaina daga zunubi. Ubangiji ya ba ni lada bisa ga adalcina, bisa ga tsabtan hannuwana a gabansa. Ga mai aminci ka nuna kanka mai aminci, ga marar laifi ka nuna kanka marar laifi, ga mai tsabta ka nuna kanka mai tsabta, amma ga karkatacce, ka nuna kanka mai wayo. Kakan cece mai sauƙinkai amma kakan ƙasƙantar da masu girman kai. Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci; Allahna ya mai da duhu ya zama haske. Da taimakonka zan iya fāɗa wa runduna; tare da Allahna zan iya rinjayi katanga. Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji marar kuskure ne. Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi. Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba? Wane ne kuwa Dutse in ba Allahnmu ba? Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi ya kuma sa hanyarta ta zama cikakkiya. Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsaya a kan ƙwanƙoli. Ya horar da hannuwana don yaƙi; hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla. Ka ba ni garkuwar nasara, kuma hannunka na dama yana riƙe ni; ya sunkuya don ka mai da ni mai girma. Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina, don kada ɗiɗɗigena yă juya. Na bi abokan gābana na kuma cim musu; ban juya ba sai da na hallaka su. Na ragargaza su har ba za su iya tashi ba; sun fāɗi a ƙarƙashin ƙafafuna. Ka ƙarfafa ni da ƙarfi saboda yaƙi; ka sa abokan gābana suka rusuna mini. Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu, na kuma hallaka abokan gābana. Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba, ga Ubangiji, amma bai amsa ba. Na murƙushe su kamar ƙura mai laushi da iska ke kwashewa; na zubar da su kamar laka a tituna. Ka cece ni daga harin mutane; ka mai da ni kan al’ummai. Mutanen da ban sani ba sun zama bayina, da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya; baƙi suna rusuna a gabana. Duk sukan karai; suna zuwa da rawan jiki daga mafakansu. Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena! Girma ya tabbata ga Allah Mai cetona! Shi ne Allah mai sāka mini, wanda yake sa al’ummai a ƙarƙashina, wanda yakan cece ni daga abokan gābana. Ana girmama ka bisa abokan gābana; daga masu tā-da-na-zaune-tsaye ka kuɓutar da ni. Saboda haka zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Ubangiji; zan rera yabai ga sunanka. Yakan ba sarkinsa nasarori; yakan nuna alheri marar ƙarewa ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada. Zabura 19 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sammai suna shelar ɗaukakar Allah; sararin sama suna furta aikin hannuwansa. Kowace rana tana yin jawabi; kowane dare yana nuna sani. Ba magana, ba kalmar da aka hurta, ba wani amon da aka ji daga gare su. Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya, kalmominsu zuwa iyakokin duniya. A sammai Allah ya kafa tenti domin rana, wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa, kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere. Takan taso daga ƙarshen sammai ta kewaye zuwa wancan; babu abin da yake ɓuya wa zafinta. Dokar Ubangiji cikakkiya ce, takan wartsakar da rai. Farillan Ubangiji abin dogara ne, suna mai da hikima da sauƙi. Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne, suna ba da farin ciki ga zuciya. Umarnan Ubangiji haske ne suna ba da haske ga idanu. Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne. Sun fi zinariya daraja, fiye da zalla zinariya nesa; sun fi zuma zaƙi fiye da zuma daga kaki. Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka; a kiyaye su akwai lada mai girma. Wane ne zai iya rabe kurakuransa? Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa. Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci; kada ka bari su yi mulki a kaina. Ta haka zan zama marar laifi; marar laifi na babban tawaye. Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata su zama abin gamsuwa a gabanka, Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata. Zabura 20 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka. Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona. Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Sela Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara. Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka. Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa. Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu. Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram. Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira! Zabura 21 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi! Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela Ka marabce shi da yalwar albarka ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa. Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce; ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna. Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka. Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka ba zai jijjigu ba. Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka; hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka. A lokacin bayyanarka za ka sa su zama kamar wutar matoya. Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su, kuma wutarsa za tă cinye su. Za ka hallaka ’ya’yansu daga duniya, zuriyarsu kuma daga ’yan adam. Ko da yake suna shirya maka mugunta suna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba; gama za ka sa su juye bayansu sa’ad da ka auna su da bakan da ka ja. Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka; za mu rera mu kuma yabi ikonka. Zabura 22 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda. Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina? Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba, da dare kuma ban yi shiru ba. Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan; kai ne yabon Isra’ila. A gare ka ne kakanninmu suka sa bege; sun dogara ka kuwa cece su. Sun yi kuka gare ka suka kuma sami ceto; a gare ka suka dogara kuma ba su sha kunya ba. Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba, wanda mutane suke yi wa ba’a suka kuma rena shi. Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a; suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa, “Ya dogara ga Ubangiji; bari Ubangiji yă cece shi. Bari yă cece shi, da yake yana jin daɗinsa.” Duk da haka ka fitar da ni daga ciki; ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata. Daga haihuwa an jefa ni a kanka; daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna. Kada ka yi nesa da ni, gama wahala na kusa kuma babu wani da zai taimaka. Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka. Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama sun buɗe bakunansu a kaina. An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina. Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa. Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna. Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina. Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana. Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni. Ka ceci raina daga takobi, raina mai daraja daga ikon karnuka. Ka cece ni daga bakin zakoki; ka cece ni daga ƙahonin ɓauna. Zan furta sunanka ga ’yan’uwana; cikin taron masu sujada zan yabe ka. Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi! Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi! Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila! Gama bai rena ko yă ƙyale wahalar masu shan wuya ba; bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba amma ya saurari kukansa na neman taimako. Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro; a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina. Matalauta za su ci su ƙoshi; su da suke neman Ubangiji za su yabe shi, bari zukatanku su rayu har abada! Dukan iyakokin duniya za su tuna su kuma juya ga Ubangiji, kuma dukan iyalan al’ummai za su rusuna a gabansa, gama mulki na Ubangiji ne kuma yana mulki a bisa al’ummai. Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada; dukan waɗanda suka gangara zuwa ƙura za su durƙusa a gabansa, waɗanda ba za su iya bar kansu da rai ba. Zuriya masu zuwa za su yi masa hidima; za a faɗa wa zuriya na nan gaba game da Ubangiji. Za su yi shelar adalcinsa ga mutanen da ba a riga an haifa ba, gama ya aikata shi. Zabura 23 Zabura ta Dawuda. Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba, Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya, yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa,23.4 Ko kuwa ta kwarin mafi duhu duka ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya. Ka shirya mini tebur a gaban abokan gābana. Ka shafe kaina da mai; kwaf nawa ya cika har yana zuba. Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi dukan kwanakin raina, zan kuwa zauna a gidan Ubangiji har abada. Zabura 24 Zabura ta Dawuda. Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta; gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye. Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki? Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya. Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa. Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Sela Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga. Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi. Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga. Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela Zabura 2525 Wannan zabura waƙa ce, mai ayoyin da suke da harufan Ibraniyanci bi da bi. Ta Dawuda. A gare ka Ya Ubangiji, na miƙa raina. A gare ka na dogara, ya Allahna. Kada ka bari in sha kunya, ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina. Ba wanda yake sa bege a gare ka da zai taɓa shan kunya, amma za su sha kunya su da suke tayarwa babu dalili. Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji, ka koya mini hanyoyinka; ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini. Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma, gama suna nan tun dā. Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata da kuma hanyoyin tawayena; bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni, gama kai nagari ne, ya Ubangiji. Ubangiji nagari da mai adalci ne; saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa. Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa. Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka gafarta laifina, ko da yake mai girma ne. To wane ne mai tsoron Ubangiji? Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa. Zai ci kwanakinsa a wadace, kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar. Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa; yakan sa su san alkawarinsa. Idanuna kullum suna a kan Ubangiji, gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko. Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, gama na kaɗaice ina kuma wahala. Damuwoyin zuciyata sun ninka; ka ’yantar da ni daga wahalata. Ka dubi wahalata da kuma azabata ka ɗauke mini dukan zunubaina. Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru da kuma yadda suka ƙara ƙina! Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni; kada ka bari in sha kunya, gama na nemi mafaka daga gare ka. Bari mutunci da adalci su tsare ni, domin begena yana a kanka. Ka fanshi Isra’ila, ya Allah, daga dukan wahalarsu! Zabura 26 Ta Dawuda. Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi rayuwa marar zargi; Na dogara ga Ubangiji ba tare da kaucewa ba. Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni, ka bincike zuciyata da tunanina; gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka. Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya; na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye. Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji, ina shelar yabonka da ƙarfi ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki. Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji, wurin da ɗaukakarka ke zaune. Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi raina tare da masu son yin kisankai waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu, waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci. Amma na yi rayuwa marar zargi; ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai. Ƙafafuna suna tsaye daram; cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji. Zabura 27 Ta Dawuda. Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro? Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi. Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni, zuciyata ba za tă ji tsoro ba; ko da yake ya ɓarke a kaina, duk da haka zan ƙarfafa. Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa. Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse. Sa’an nan kaina zai ɗaukaka a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni; a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki; zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji; ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini. Zuciyata kan faɗa game da kai, “Nemi fuskarsa!” Fuskarka, Ubangiji, zan nema. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni, kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi; kai ne ka kasance mai taimakona. Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni, Ya Allah Mai cetona. Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni, Ubangiji zai karɓe ni. Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji; ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanya saboda masu danne ni. Kada ka ba da ni da sha’awar maƙiyina, gama masu shaidar ƙarya sun taso a kaina, suna numfasa tashin hankali. Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa zan ga alherin Ubangiji; a ƙasar masu rai. Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji. Zabura 28 Ta Dawuda. A gare ka nake kira, ya Ubangiji Dutsena; kada ka yi mini kunnen ƙashi. Gama in ka yi shiru, zan zama kamar waɗanda suka gangara rami. Ka ji kukata ta neman jinƙai yayinda nake kira ka don neman taimako, yayinda nake daga hannuwana wajen Wurinka Mafi Tsarki. Kada ka ja ni tare da mugaye, tare da masu yin mugunta, masu magana kamar ta alheri ce da maƙwabtansu amma suna riƙe da su a zukatansu. Ka sāka musu da ayyukansu da kuma don mugun aikinsu; ka sāka musu saboda abin da hannuwansu suka yi ka kuma mayar musu abin da ya dace da su. Da yake ba su kula da ayyukan Ubangiji da abin da hannuwansa suka yi ba, zai rushe su ba kuwa zai ƙara gina su ba. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya ji kukata na neman jinƙai. Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako. Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa. Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa, kagarar ceto domin shafaffensa. Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka; ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada. Zabura 29 Zabura ta Dawuda. Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa. Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa. Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye. Muryar Ubangiji mai iko ce; muryar Ubangiji da girma take. Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu. Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, Siriyon29.6 Wato, Dutsen Hermon kuma kamar ɗan jakin jeji. Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya. Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh. Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak29.9 Ko kuwa Ubangiji ya sa barewa ta haihu. ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!” Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada. Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama. Zabura 30 Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali.30.0 Kan magana, ko kuwa faɗa Ta Dawuda. Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba. Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni. Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami. Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki. Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe. Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.” Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro. A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira; a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai. “Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka? Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.” Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki, don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada. Zabura 31 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka bari in taɓa shan kunya; ka cece ni cikin rahamarka. Ka juye kunnenka gare ni, ka zo da sauri ka cece ni; ka zama dutsen mafakata, mafaka mai ƙarfi na cetona. Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata, saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni. Ka ’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini, gama kai ne mafakata. Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna; ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya. Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza; na dogara ga Ubangiji. Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikin ƙaunarka, gama ka ga azabata ka kuma san wahalar raina. Ba ka ba da ni ga abokin gāba ba amma ka sa ƙafafuna a wuri mai sarari. Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama ina cikin damuwa; idanuna sun gaji da baƙin ciki, raina da jikina sun tafke tilis. Baƙin ciki ya rufe raina shekaruna sun cika da nishi; ƙarfina ya karai saboda azaba, ƙasusuwana kuma sun gaji tiƙis. Saboda dukan abokan gābana, Na zama tamƙar abin reni na maƙwabtana; na zama abin tsoro ga abokaina, waɗanda suka gan ni a titi sukan gudu daga gare ni. An manta da ni sai ka ce na mutu; na zama kamar fasasshen kasko. Gama nakan ji raɗe-raɗen mutane masu yawa; akwai tsoro a kowane gefe; suna ƙulla maƙarƙashiya a kaina suna shirya su ɗauke raina. Amma na dogara gare ka, ya Ubangiji; na ce, “Kai ne Allahna.” Lokutana suna a hannuwanka; ka cece ni daga abokan gābana da kuma daga waɗanda suke fafara ta. Bari fuskarka ta haskaka a kan bawanka; ka cece ni da ƙaunarka marar ƙarewa. Kada ka bari in sha kunya, ya Ubangiji, gama na yi kuka gare ka; amma bari mugaye su sha kunya su kuma kwanta shiru a cikin kabari. Bari a rufe leɓunan ƙarairayinsu, gama da fariya da reni suna magana da girman kai a kan adalai. Alherinka da girma yake, wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka, wanda ka mayar a gaban mutane a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka. Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su daga makircin mutane; a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya daga harsuna masu zagi. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya nuna ƙaunarsa mai banmamaki gare ni sa’ad da aka yi mini kwanto kewaye da birni. Cikin tsorona na ce, “An yanke ni daga gabanka!” Duk da haka ka ji kukata na neman jinƙai sa’ad da na kira gare ka don taimako. Ku ƙaunaci Ubangiji, dukanku tsarkakansa! Ubangiji yakan adana amintattu, amma masu girman kai yakan sāka musu cikakke. Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa, dukanku masu sa bege a kan Ubangiji. Zabura 32 Ta Dawuda. Maskil32.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce. ne. Mai farin ciki ne shi wanda aka gafarta masa laifofinsa, wanda aka shafe zunubansa. Mai farin ciki ne mutumin da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa. Sa’ad da na yi shiru, ƙasusuwana sun yi ta mutuwa cikin nishina dukan yini. Gama dare da rana hannunka yana da nauyi a kaina; an shanye ƙarfina ƙaf sai ka ce a zafin bazara. Sela Sa’an nan na furta zunubina a gare ka ban kuwa ɓoye laifina ba. Na ce, “Zan furta laifofina ga Ubangiji.” Ka kuwa gafarta laifin zunubina. Sela Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka yayinda kake samuwa; tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso, ba za su kai wurinsa ba. Kai ne wurin ɓuyata; za ka tsare ni daga wahala ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi; Zan ba ka shawara in kuma lura da kai. Kada ka zama kamar doki ko doki, wanda ba su da azanci wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba. Azaban mugu da yawa suke, amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi. Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai; ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai! Zabura 33 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai; daidai ne masu gaskiya su yabe shi. Ku yabi Ubangiji da garaya; ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma. Ku rera masa sabuwar waƙa; ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki. Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya; yana da aminci cikin kome da yake yi. Ubangiji yana ƙaunar adalci duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa. Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa. Ya tattara ruwan teku cikin tuluna;33.7 Ko kuwa teku sai ka ce a tsibi ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya. Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji; bari dukan mutanen duniya su girmama shi. Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance; ya umarta, ya kuwa tsaya daram. Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane. Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai. Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta, mutanen da ya zaɓa don gādonsa. Daga sama Ubangiji ya duba ya kuwa ga dukan ’yan adam; daga mazauninsa yana lura da dukan waɗanda suke zama a duniya, shi da ya yi zukatan duka, wanda yake kula da kome da suke yi. Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa; ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa. Dogara a kan doki don ceto banza ne; duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto. Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa, don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa. Muna jiran Ubangiji da bege; shi ne taimakonmu da garkuwarmu. A cikinsa zukatanmu na farin ciki, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki. Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji, ko ma da muke sa begenmu a gare ka. Zabura 3434 Wannan zabura waƙa ce, mai ayoyin da suka fara da harufan Ibraniyanci bi da bi. Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi. Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana. Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki. Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare. Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro. Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya. Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa. Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su. Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi. Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa, gama masu tsoronsa ba sa rasa kome. Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa, amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau. Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni; zan koya muku tsoron Ubangiji. Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau, ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi. Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta. Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu; fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya. Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu. Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu. Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu; yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye. Mugunta zai kashe mugu; za a hukunta abokan gāban adalai. Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta. Zabura 35 Ta Dawuda. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni. Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni. Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa35.3 Ko kuwa ka kuwa tare hanya a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.” Bari waɗanda suke neman raina su sha kunya a kuma kunyatar da su; bari waɗanda suke shirya lalacewata su juya da baya su ruɗe. Bari su zama kamar yayi a gaban iska, mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu; bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi, mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu. Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalili kuma babu dalili suka haƙa mini rami, bari lalaci yă kama su ba zato, bari tarkon da suka ɓoye yă kama su, bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu. Sa’an nan raina zai cika da farin ciki a cikin Ubangiji in yi kuma murna a cikin cetonsa. Dukan raina zai ce, “Wane ne kamar ka, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu, matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.” Shaidu marasa imani sun fito; suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba. Suna sāka alherin da na yi musu da mugunta suka bar raina da nadama. Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa, nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata. Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna; masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba. Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa. Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a; Suna hararata da ƙiyayya. Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai? Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu, raina mai daraja daga waɗannan zakoki. Zan yi godiya cikin taro mai girma; cikin ɗumbun mutane zan yabe ka. Kada ka bar maƙaryatan nan, su yi farin ciki a kaina; kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, su ji daɗin baƙin cikina. Ba sa maganar salama sukan ƙirƙiro zage-zagen ƙarya a kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar. Sukan wage mini bakinsu suna cewa, “Allah yă ƙara! Da idanunmu mun gani.” Ya Ubangiji, ka ga wannan; kada ka yi shiru. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji. Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni! Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana. Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka, Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina. Kada ka bari su ce wa kansu, “Allah yă ƙara, dā ma abin da mun so ke nan!” Ko su ce, “Mun haɗiye shi.” Bari dukan waɗanda suke farin ciki a kaina a wahalata su sha kunya su kuma ruɗe; bari dukan waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni su sha kunya da wulaƙanci. Bari waɗanda suke murna saboda nasarata su yi sowa don farin ciki da murna; bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji, wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.” Harshena zai yi zancen adalcinka da kuma yabonka dukan yini. Zabura 36 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa. Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa. Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri. Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau. Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai. Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba. Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka. Suna biki a yalwar gidanka; kakan ba su sha daga rafin farin cikinka. Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai cikin haskenka mukan ga haske. Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka, adalcinka ga masu gaskiyar zuciya. Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini, ko hannun mugu ya kore ni. Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi, a zube, ba za su kuwa iya tashi ba! Zabura 3737 Wannan zabura waƙa ce, mai ayoyin da suka fara da harufan Ibraniyanci bi da bi. Ta Dawuda. Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta; gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu. Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya. Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka. Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan. Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya, gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka. Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu. Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala; kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai. Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar. A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe; ko ka neme su, ba za a same su ba. Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama. Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu; amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa. Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke. Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye. Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa; gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci. Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada. A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba; a kwanakin yunwa za su sami a yalwace. Amma mugaye za su hallaka, Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki, za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi. Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya, amma masu adalci suna bayar hannu sake; waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar, amma waɗanda ya la’anta, za a kore su. In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu; ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa. Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi. Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka. Ku juyo daga mugunta ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada. Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya, ’ya’yan mugaye za su hallaka. Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada. Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai. Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa; ƙafafunsa ba sa santsi. Mugaye suna fako suna jira masu adalci, suna ƙoƙari neman ransu; amma Ubangiji ba zai bar su a ikonsu ba ko ya bari a hukunta su sa’ad da aka kawo su shari’a ba. Ku sa zuciya ga Ubangiji ku kuma kiyaye hanyarsa. Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar, sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani. Na ga wani mugu, azzalumi, yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa, amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa; ko an neme shi, ba za a same shi ba. Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama. Amma za a hallaka dukan masu zunubi; za a yanke sa zuciya ta mugaye. Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala. Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su; yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su, domin sukan nemi mafaka daga gare shi. Zabura 38 Zabura ta Dawuda. Roƙo ne. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka. Gama kibiyoyinka sun soke ni, hannunka kuma ya fāɗo a kaina. Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina. Laifofina sun mamaye ni kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka. Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari saboda wawancina na zunubi. An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni; dukan yini ina ta kuka. Bayana yana fama da zazzaɓi; babu lafiya a jikina. Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni; ina nishi da wahala a cikin zuciyata. Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji; ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka. Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare, har ma haske ya rabu da idanuna. Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna; maƙwabtana ba sa zuwa kusa. Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu, waɗanda suke so su cuce ni suna zance lalatar da ni; yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya. Ni kamar kurma ne, wanda ba ya ji, kamar bebe, wanda ba ya iya buɗe bakinsa. Na zama kamar mutumin da ba ya ji, wanda bakinsa ba ya iya ba da amsa. Na dogara gare ka, ya Ubangiji; za ka amsa, ya Ubangiji Allahna. Gama na ce, “Kada ka bar su su yi farin ciki a kaina ko su yi kirari a kaina sa’ad da ƙafata ta yi santsi.” Gama ina gab da fāɗuwa, kuma cikin azaba nake kullum. Na furta laifina; na damu da zunubina. Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi; waɗanda suke kina ba dalili sun yi yawa. Waɗanda suke sāka alherina da mugunta, suna cin zarafina sa’ad da nake bin abin da yake daidai. Ya Ubangiji, kada ka yashe ni; kada ka yi nesa da ni, ya Allahna. Zo da sauri ka taimake ni, Ya Ubangiji Mai Cetona. Zabura 39 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zabura ta Dawuda. Na ce, “Zan lura da hanyoyina zan kuma kiyaye harshena daga zunubi; zan sa linzami a bakina muddin mugaye suna a gabana.” Na yi shiru, ban ce kome ba, Ko a kan abin da yake da kyau! Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi; zuciyata ta ƙara zafi a cikina. Kuma sa’ad da nake tunani, wuta ta yi ta kuna; sai na yi magana da harshena na ce, “Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata da kuma yawan kwanakina; bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri. Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai; yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka. Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum, har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela “Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa. Yana ta yawo, amma a banza ne kawai; yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba. “Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema? Begena yana a gare ka. Ka cece ni daga dukan laifofina; kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye. Na yi shiru; ba zan buɗe bakina ba, gama kai ne wanda ka aikata wannan. Ka ɗauke bulalarka daga gare ni; na ji jiki ta wurin bugun da hannunka ya yi mini. Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu; kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi, kowane mutum dai shaƙar iska ne. Sela “Ka ji addu’ata, ya Ubangiji, ka saurari kukata ta neman taimako; kada ka kurmance ga kukata. Gama ina zama tare da kai kamar baƙo, baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance. Ka kau da fuskarka daga gare ni, saboda in sāke yin farin ciki kafin in tafi in kuma rabu da nan.” Zabura 40 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Na jira da haƙuri ga Ubangiji; ya juya wurina ya kuma ji kukata. Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi, daga laka da taɓo; ya sa ƙafafuna a kan dutse ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya. Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji. Mai albarka ne mutumin da ya mai da Ubangiji abin dogararsa, wanda ba ya kula da masu girman kai, waɗanda suka juya ga allolin ƙarya. Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna, abubuwan banmamakin da ka aikata. Abubuwan da ka shirya mana. Ba wanda zai iya faɗa maka su; a ce zan yi magana in faɗe su, za su wuce gaban misali a furta. Hadaya da sadaka ba ka sha’awa, amma kunnuwana ka huda; hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata. Sa’an nan na ce, “Ga ni, na zo, kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi. Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna; dokar tana cikin zuciyata.” Na yi shelar adalcinka cikin babban taro; ba na rufe leɓunana, kamar yadda ka sani, ya Ubangiji. Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata; ina maganar amincinka da cetonka. Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka a gaban taron jama’arka mai girma ba. Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji; bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni. Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni; zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani. Sun fi gashin kaina yawa, har ma na fid da zuciya. Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji; Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni. Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan waɗanda suke neman lalacewata su koma baya da kunya. Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su sha mamaki saboda kunyar da za su sha. Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, Ubangiji mai girma ne!” Ni dai matalauci ne da mai bukata; bari Ubangiji yă tuna da ni. Kai ne taimakona da mai cetona; Ya Allahna, kada ka jinkirta. Zabura 41 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala. Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba. Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi. Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.” Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa, “Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?” Duk sa’ad da wani ya zo ganina, yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi; sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina. Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina; suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa, “Mugun ciwo ya kama shi; ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.” Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni. Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, ka tā da ni, don in sāka musu. Na sani kana jin daɗina, gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba. Cikin mutuncina ka riƙe ni ka sa ni a gabanka har abada. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, har abada abadin. Amin kuma Amin. LITTAFI NA BIYU Zabura 42–72 Zabura 4242 Cikin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci masu yawa Zabura 42 da 43, zabura guda ce. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Maskil42.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. ne na ’Ya’yan Kora maza. Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah. Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai. Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne? Hawayena ne sun zama abincina dare da rana, yayinda mutane suke ce da ni dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?” Waɗannan abubuwa ne nakan tuna sa’ad da nake faɗin abin da yake a raina, yadda dā nakan tafi tare da taron jama’a, ina bishe su a jere zuwa gidan Allah, da sowa ta farin ciki da kuma godiya a cikin taron biki. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna. Raina42.5,6 Kaɗan a cikin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci, Seftuwajin da Siriyak; yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci yabe shi domin taimakon cetonsa. 6 Ya Allahna, nawa yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar. Zurfi kan kira zurfi cikin rurin matsirgar ruwanka; dukan raƙuma da igiyoyi sun sha kaina. Da rana Ubangiji yakan nuna ƙaunarsa, da dare waƙarsa tana tare da ni, addu’a ga Allah na raina. Na ce wa Allah Dutsena, “Me ya sa ka manta da ni? Me zai sa in yi ta yawo ina makoki, a danne a hannun abokin gāba?” Ƙasusuwana suna jin jiki da wahala yayinda maƙiyana suna mini ba’a, suna ce mini dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?” Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna. Zabura 4343 Cikin rubuce-rubucen hannu masu yawa a Ibraniyanci Zabura 42 da 43 zabura guda ce. Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah, ka kuma nemi hakkina a kan al’ummai marasa sanin Allah. Ka kuɓutar da ni daga masu ruɗu da mugayen mutane. Kai ne Allah mafakata. Me ya sa ka ƙi ni? Me zai sa in yi ta yawo ina makoki, a danne a hannun abokin gāba? Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, bari su bishe ni bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki, zuwa wurin da kake zama. Sa’an nan zan tafi bagaden Allah, ga Allah, farin cikina da murnata. Zan yabe ka da garaya, Ya Allah, Allahna. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da Allahna. Zabura 44 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’ya’yan Kora maza. Maskil44.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. ne. Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah; kakanninmu sun faɗa mana abin da ka aikata a kwanakinsu, tun dā can. Da hannunka ka kori al’ummai ka kuma dasa kakanninmu; ka ragargaza mutanen ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka. Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar, ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba; hannun damanka ne, ƙarfin hannunka, da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su. Kai ne Sarkina da kuma Allahna, wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub. Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya; ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu. Ba na dogara ga bakana, takobina ba ya kawo nasara; amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu, ka sa abokan gābanmu suka sha kunya. A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini, kuma za mu yabi sunanka har abada. Sela Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu; ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu. Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba, kuma abokan gābanmu suka washe mu. Ka ba da mu a cinye kamar tumaki ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai. Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba babu wata riba daga sayar da su da ka yi. Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu, abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu. Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai; mutanen suna kaɗa mana kai. Dukan yini ina cikin wulaƙanci, fuskata kuma ta rufu da kunya saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina, saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa. Dukan wannan ya faru da mu, ko da yake ba mu manta da kai ba ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka. Zukatanmu ba su juya baya; ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba. Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin. Da a ce mun manta da sunan Allahnmu ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli, da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya? Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini; aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka. Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci? Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada. Me ya sa ka ɓoye fuskarka ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana? An kai mu ƙasa zuwa ƙura; jikunanmu sun manne da ƙasa. Ka tashi ka taimake mu; ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa. Zabura 45 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Lili.” Na ’ya’yan Kora maza. Maskil45.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Waƙar Aure. Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana yayinda nake rera ayoyina wa sarki; harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci. Kai ne mafi kyau cikin mutane an kuma shafe leɓunanka da alheri, da yake Allah ya albarkace ka har abada. Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi; ka rufe kanka da ɗaukaka da kuma daraja. Cikin darajarka ka hau zuwa nasara a madadin gaskiya, tawali’u da adalci; bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki. Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki; bari al’ummai su fāɗi ƙarƙashin ƙafafunka. Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin; sandar adalci zai zama sandar mulkinka. Kana ƙaunar abin da yake daidai kana kuma ƙin mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya sa ka a bisa abokanka ta wurin shafe ka da man farin ciki. Dukan rigunanka suna ƙanshin turaren mur da na aloyes, da na kashiya; daga kowace fadan da aka yi masa ado da hauren giwa kaɗe-kaɗen tsirkiya kan sa ka murna. ’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama; a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya. Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne, Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki. Sarki ya cika da sha’awar kyanki; ki girmama shi, gama shi ne maigidanki. Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki. Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun; an saƙa rigarta da zaren zinariya. Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki; abokanta budurwai suna biye da ita aka kuwa kawo su gare ka. Aka bi da su cikin farin ciki da murna; suka shiga fadan sarki. ’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka; za ka sa su yi mulki a duk fāɗin ƙasar. Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai; saboda haka al’ummai za su yabe ka har abada abadin. Zabura 46 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku, ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama. Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe. Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke. Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya. Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi46.9 Ko kuwa kekunan yaƙi da wuta. “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.” Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela Zabura 47 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki. Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya! Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu. Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni. Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai. Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi. Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki. Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai. Zabura 48 Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki. Kyakkyawa ce cikin tsayinta, abin farin cikin dukan duniya. Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon48.2 Zafon yana nufin dutse mai tsarki ko kuwa gefen arewa. ne Dutsen Sihiyona, birnin48.2 Ko kuwa duniya, Dutsen Sihiyona, a arewanci na Babban Sarki. Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta. Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni, sa’ad da suka yi gaba tare, sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro. Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda. Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje. Yadda muka ji, haka muka gani a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki, a cikin birnin Allahnmu. Allah ya sa ta zauna lafiya har abada. Sela Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa. Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci. Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki, ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukuntanka. Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta, ku ƙirga hasumiyoyinta, ku lura da katangarta da kyau, ku dubi fadodinta, don ku faɗe su ga tsara mai zuwa. Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe. Zabura 49 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku ji wannan, dukanku mutane; ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya, babba da yaro mai arziki da talaka. Bakina zai yi maganar hikima; magana daga zuciyata za tă ba da ganewa. Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina. Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni, waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu? Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi, kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa, da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa. Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu. Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu. Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa. Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. Sela Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada. Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru; gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba. Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara, zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba. Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa. Zabura 50 Zabura ta Asaf. Maɗaukaki, Allah, Ubangiji, ya yi magana ya kuma kira duniya daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa. Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau, Allah na haskakawa. Allahnmu yana zuwa ba kuwa zai yi shiru ba; wuta mai cinyewa a gabansa, babban hadari kuma ya kewaye shi. Ya kira sammai da suke bisa, da duniya, don yă shari’anta mutanensa. “Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.” Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. Sela “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana, Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku. Ni ne Allah, Allahnku. Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana. Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku, gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai. Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne. Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta. Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne? “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka, ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.” Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku? Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata. Kuna amfani da bakunanku don mugunta kuna kuma gyara harshenku don ruɗu. Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku. Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku. “Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah, ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku. Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa50.23 Ko kuwa gare shi kuma wanda ya lura da hanyarsa / zan nuna ceton Allah.” Zabura 51 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina. Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina. Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana. Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta. Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina. Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki; ka koya mini hikima a wuri can ciki. Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab; ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari. Bari in ji farin ciki da murna; bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki. Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina ka kuma shafe dukan kurakuraina. Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina. Kada ka fid da ni daga gabanka ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni. Ka mayar mini farin cikin cetonka ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni. Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka, masu zunubi kuma za su komo gare ka. Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah, Allahn da ya cece ni, harshena kuwa zai rera adalcinka. Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana, bakina kuwa zai furta yabonka. Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo; ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa. Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba. Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara; ka gina katangar Urushalima. Ta haka za a kasance da hadayu masu adalci, hadayun ƙonawa ɗungum don su faranta ka; sa’an nan za a miƙa bijimai a bagadenka. Zabura 52 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil52.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.” Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum? Me ya sa kake fariya dukan yini, kai da kake abin kunya a idanun Allah? Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu. Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri, ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu! Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka. Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka; zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela Masu adalci za su ga su ji tsoro; za su yi masa dariya, suna cewa, “Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!” Amma ni kamar itace zaitun ne ina haɓaka a gidan Allah; na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah har abada abadin. Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka. Zabura 53 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat.53.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Wani maskil53.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. na Dawuda. Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa, “Ba Allah.” Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau; babu wani mai aikata abu mai kyau. Allah yana duba daga sama a kan ’ya’yan mutane yă ga ko akwai wani wanda ya gane, wani wanda yake neman Allah. Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace; babu guda da yake aikata abu mai kyau, babu ko ɗaya. Masu aikata mugunta ba sa taɓa koyo? Suna cin mutanena kamar yadda ake cin burodi, ba sa kuma kira ga Allah. Ga shi fa, sun firgita don tsoro, ko da yake babu dalilin tsoro, gama Allah zai watsar da ƙasusuwan masu ƙinsa, za su sha kunya, gama Allah ya ƙi su. Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna! Zabura 54 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil54.0 Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce. ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?” Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka. Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina. Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni. Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su. Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau. Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana. Zabura 55 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil55.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. ta Dawuda. Ka ji addu’ata, ya Allah, kada ka ƙyale roƙona; ka ji ni ka kuma amsa mini. Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina, saboda danniyar mugaye. Gama sukan jawo mini wahala, suna jin haushina suna ƙina. Zuciyata tana wahala a cikina; tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina. Tsoro da rawan jiki sun kama ni; razana ta sha kaina. Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana! Ai, da na yi firiya na tafi na huta, da na tafi can da nisa na zauna a hamada; Sela da na hanzarta na tafi wurin mafakata, nesa da muguwar iska da hadiri.” Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu, gama na ga rikici da faɗa a cikin birni. Dare da rana suna yawo a kan katanga; mugun hali da zargi suna a cikinta. Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni; barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta. Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi. Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa, wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah. Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu. Amma na kira ga Allah, Ubangiji kuwa ya cece ni. Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata. Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni. Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, Sela mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah. Abokina ya kai wa abokansa hari; ya tā da alkawarinsa. Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun, duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa; kalmominsa sun fi mai sulɓi, duk da haka takuba ne zārarru. Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba. Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye zuwa cikin ramin lalacewa; masu kisa da mutane masu ruɗu ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba. Amma ni dai, na dogara gare ka. Zabura 56 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da murya “Kurciya a Itatuwan Oak Mai Nisa.” Ta Dawuda. Wani miktam.56.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Sa’ad da Filistiyawa suka kama shi a birnin Gat. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi; dukan yini suna matsa harinsu. Masu ɓata sunana suna bina dukan yini; da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu. Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka. Ga Allah wanda maganarsa nake yabo ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum mai mutuwa zai yi mini? Dukan yini sun yi ta juya maganata; kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni. Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina. Sam, kada ka bari su kuɓuce; cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai. Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka,56.8 Ko kuwa / ka sa hawayena a salkan ruwan inabinka ba a rubuce suke a cikin littafinka ba? Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni. Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa, ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini? Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah; zan miƙa hadayuna na godiya gare ka. Gama ka cece ni56.13 Ko kuwa raina daga mutuwa da kuma ƙafafun daga tuntuɓe, don in yi tafiya a gaban Allah cikin hasken rai.56.13 Ko kuwa a ƙasar masu rai Zabura 57 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.57.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce. Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka, ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni. Ya aika daga sama ya kuwa cece ni, yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; Sela Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa. Ina tsakiyar zakoki; ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane, mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi, waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi. Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya. Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna, damuwa ta sha ƙarfina. Sun haƙa rami a hanyata, amma su kansu suka fāɗa a cikinta. Sela Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe. Ka farka, raina! Ku farka, garaya da molo! Zan sa safe yă farka. Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai a cikin mutane. Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai; amincinka na kaiwa sarari. Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya. Zabura 58 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.58.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai? Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane? Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci, da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya. Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce; daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata. Dafinsu ya yi kamar dafin maciji, kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa, da ba ya jin muryar gardi, kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama. Ka kakkarya haƙoran a bakunansu, ya Allah; ka yayyage fiƙoƙin zakoki, ya Ubangiji! Bari su ɓace kamar ruwa mai wucewa; sa’ad da suka ja bakansu, bari kibiyoyinsu su murtsuke. Kamar katantanwun da suke narkewa yayinda suke tafiya, kamar jinjirin da aka haifa matacce, kada su ga hasken rana. Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa, ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye.58.9 Ma’anar Ibraniyancin wannan aya ba tabbatacce ba ne. Masu adalci za su yi murna sa’ad da aka rama musu, sa’ad da suka wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye. Sa’an nan mutane za su ce, “Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai; tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.” Zabura 59 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.59.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi. Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini. Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa. Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji. Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki! Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sela Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni. Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?” Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a. Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina. Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu, in ba haka mutanena za su manta. Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai, ka kuma kawar da su. Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi, ka cinye su da hasala, ka cinye su sarai. Sa’an nan za a sani a iyakar duniya cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. Sela Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni. Suna ta yawo neman abinci su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba. Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala. Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata. Zabura 60 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam60.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim60.0 Kan Magana. Wato, Arameyawan Arewa maso Yamma na Mesofotamiya. da Aram-Zoba,60.0 Kan magana, wato, Arameyawan Tsakiyar Suriya. da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu! Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa. Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu. Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. Sela Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta. Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Da nasara zan rarraba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot. Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne; Efraim shi ne hular kwanona, Yahuda kuma sandar mulkina. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.” Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom? Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu? Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattake abokan gābanmu. Zabura 61 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata. Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi. Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi. Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka. Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa. Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi. Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana. Zabura 62 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi. Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba. Har yaushe za ku tasar wa mutum guda? Dukanku ne za ku kā da shi wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga? Sun kintsa sosai su tumɓuke shi daga matsayinsa mai martaba; suna jin daɗi yin ƙarairayi. Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu, amma a zuciyarsu la’antawa suke yi. Sela Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne. Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba. Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne,62.7 Ko kuwa / Allah Mafi Ɗaukaka shi ne cetona da girmata shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata. Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. Sela Talakawa dai kamar shaƙar iska suke, Attajirai dai kamar shirim suke; in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne; dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai. Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu. Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji, “Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi, kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.” Zabura 63 Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa. Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka. Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka. Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana. Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka. A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare. Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka. Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni. Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya. Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji. Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata. Zabura 64 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna; ka tsare raina daga barazanan abokin gāba. Ka ɓoye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, daga daure dauren wannan taro masu aikata mugunta. Sukan wāsa harsunansu kamar takuba su harba kalmominsu kamar kibiyoyi masu kisa. Sukan yin kwanto su harbi marar laifi; sukan yi harbi nan da nan, ba tsoro. Sukan ƙarfafa juna a mugayen ƙulle-ƙullensu, sukan yi magana yadda za su ɓoye tarkunansu; su ce, “Wa zai gan su?”64.5 Ko kuwa mu Sukan yi ƙulle-ƙullen rashin adalci su ce, “Mun gama ƙulla cikakkiyar maƙarƙashiya tsab!” Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa. Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi; nan da nan za a buge su su fāɗi. Zai juya harshensu a kansu yă kuma kawo su ga hallaka; duk waɗanda suka gan su za su kaɗa kai, suna musu ba’a. Dukan mutane za su ji tsoro; za su yi shelar ayyukan Allah su kuma yi tunanin abin da ya aikata. Bari masu adalci su yi farin ciki a cikin Ubangiji su kuma nemi mafaka a gare shi; bari dukan masu gaskiya a zuciya su yabe shi! Zabura 65 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa. Yabo ya dace65.1 Ko kuwa kan jira; ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba a tabbatar ba. da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu Ya kai wanda yake jin addu’a a gare ka dukan mutane za su zo. Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu, ka gafarta65.3 Ko kuwa ka yi kafara domin laifofinmu. Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa ka kawo kusa don su zauna a filayenka! Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, na haikalinka mai tsarki. Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa, wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi, wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai. Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki. Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; kana azurta ta a yalwace. Rafuffukan Allah sun cika da ruwa don su ba mutane hatsi, don haka ne ka ƙaddara.65.9 Ko kuwa don haka ne ka shirya ƙasar Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta. Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka, amalankenka kuwa sun cika har suna zuba. Makiyayan hamada sun cika har suna zuba; tuddai sun rufu da murna. Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna kwari kuma sun cika da hatsi; suna sowa don farin ciki. Zabura 66 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura. Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya! Ku rera ɗaukaka ga sunansa; ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka! Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke! Ikonka da girma yake har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka. Dukan duniya sun rusuna a gabanka suna rera yabo gare ka, suna rera yabo ga sunanka.” Sela Ku zo ku ga abin da Allah ya yi, ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum! Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa. Yana mulki har abada ta wurin ikonsa, idanunsa suna duban al’ummai, kada ’yan tawaye su tayar masa. Sela Ku yabi Allahnku, ya mutane, bari a ji ƙarar yabonsa; ya adana rayukanmu ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi. Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa. Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu. Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa. Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa zan kuwa cika alkawurana gare ka, alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa sa’ad da nake cikin wahala. Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. Sela Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah; bari in faɗa muku abin da ya yi mini. Na yi kuka gare shi da bakina; yabonsa yana a harshena. Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba; amma tabbatacce Allah ya saurara ya kuma ji muryata a cikin addu’a. Yabo ga Allah, wanda bai ƙi addu’ata ba ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni! Zabura 67 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, Sela don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai. Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka. Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe. Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu. Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa. Zabura 68 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa; bari maƙiyansa su gudu a gabansa. Kamar yadda iska take hura hayaƙi, bari yă hura su haka; kamar yadda kaki kan narke a gaban wuta, bari mugaye su hallaka a gaban Allah. Amma bari adalai su yi murna su kuma yi farin ciki a gaban Allah; bari su yi murna da farin ciki. Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;68.4 Ko kuwa / ku shirya hanya wa shi da yake hawan ta hamada sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa. Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki. Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana. Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah, sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi, Sela duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama, a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra’ila. Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah; ka rayar da gādonka da ya gāji. Mutanenka suka zauna a cikinsa, kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta. Ubangiji ya yi umarni, mutane masu yawa ne suka yi shelarsa, “Sarakuna da mayaƙa suka gudu a gaggauce; cikin sansani mutane sun raba ganima. Har yayinda kuke barci a cikin garken tumaki, an dalaye fikafikan kurciya da azurfa, fikafikanta da zinariya mai ƙyalli.” Sa’ad da Maɗaukaki ya watsar da sarakuna a cikin ƙasa, sai ya zama kamar ƙanƙara ta sauka a kan Zalmon. Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne. Don me kuke duba da kishi, ya duwatsu masu wuyan hawa, a kan dutsen da Allah ya zaɓa yă yi mulki, inda Ubangiji kansa zai zauna har abada? Karusan Allah ninkin dubbai goma ne da kuma dubu dubbai; Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa. Sa’ad da ka hau bisa, ka bi da kamammu cikin tawagarka; ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga ’yan tawaye, don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. Sela Allahnmu shi ne Allah wanda yake ceto; daga Ubangiji Mai Iko Duka kuɓuta yake zuwa daga mutuwa. Tabbatacce Allah zai murƙushe kawunan abokan gābansa, rawanin gashi na waɗanda suke ci gaba cikin zunubansa. Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku, don ku wanke ƙafafunku a cikin jinin maƙiyanku, yayinda harsunan karnukanku su sami rabonsu.” Jerin gwanonka ya zo a bayyane, ya Allah, jerin gwanon Allahna da Sarkina zuwa cikin wuri mai tsarki. A gaba akwai mawaƙa, a bayansu akwai makaɗa; tare da su akwai ’yan mata suna bugan ganguna. Ku yabi Allah cikin taro mai girma; yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila. Ga ƙaramar kabilar Benyamin, suna jagorance su, ga babbar ƙungiya shugabannin Yahuda, ga kuma shugabannin Zebulun da na Naftali. Ka bayyana ikonka, ya Allah; ka nuna ƙarfinka, ya Allah, kamar yadda ka yi a dā. Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai. Ka tsawata wa naman jejin nan a cikin kyauro, garken bijimai a cikin ’yan maruƙan al’ummai. Ka ƙasƙantar, bari yă kawo sandunan azurfa. Ka watsar da al’ummai waɗanda suke jin daɗin yaƙi. Jakadu za su zo daga Masar; Kush za tă miƙa kanta ga Allah. Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, Sela gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya. Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari. Kai mai banmamaki ne, ya Allah, cikin wurinka mai tsarki; Allah na Isra’ila yakan ba da iko da kuma ƙarfi ga mutanensa. Yabo ya tabbata ga Allah! Zabura 69 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin.” Ta Dawuda. Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina. Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna. Waɗanda suke ƙina ba dalili sun fi gashin kaina yawa; da yawa ne abokan gābana babu dalili, su da suke nema su hallaka ni. An tilasta mini in mayar da abin da ban sata ba. Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba. Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki; bari waɗanda suke neman ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Allah na Isra’ila. Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata. Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana, bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza; gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina. Sa’ad da na yi kuka na kuma yi azumi dole in jimre da ba’a; sa’ad da na sanya rigunan makoki, mutane suna maishe ni abin dariya. Masu zama a ƙofa suna mini ba’a, na zama waƙa a bakin bugaggu da giya. Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji, a lokacin da ka ga dama; a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah, ka amsa mini da tabbacin ceto. Ka fid da ni daga laka, kada ka bari in nutse; ka cece ni daga waɗanda suke ƙina, daga rurin ruwaye. Kada ka bar rigyawa yă sha kaina ko zurfafa su haɗiye ni ko rami yă rufe bakinsa a kaina. Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka; cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni. Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka; ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala. Ka zo kusa ka kuɓutar da ni; ka fanshe ni saboda maƙiyana. Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya; dukan abokan gābana suna a gabanka. Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba. Sun sa abin ɗaci cikin abincina suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi. Bari teburin da aka shirya a gabansu yă zama musu tarko; bari yă zama sakamakon laifi da kuma69.22 Ko kuwa tarko / zumuncinsu kuma yă zama tarko. Bari idanunsu yă dushe don kada su gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada. Ka kwarara fushinka a kansu; bari fushinka mai zafi yă ci musu. Bari wurinsu yă zama kufai; kada ka bar wani yă zauna a tentunansu. Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni. Ka neme su da laifi a kan laifi; kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka. Bari a shafe su sarai daga littafin rai kada a kuma lissafta su tare da adalai. Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni. Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya. Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa. Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu! Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa. Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu, gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta, ’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can. Zabura 70 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Roƙo. Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni; Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni. Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan masu sha’awar gani lalacewata su juye baya da kunya. Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su juye baya saboda kunyansu. Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!” Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata; ka zo da sauri gare ni, ya Allah. Kai ne mai taimakona da mai cetona; Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri. Zabura 71 A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka taɓa sa in sha kunya. Ka kuɓutar da ni ka cece ni cikin adalcinka; ka juya kunnenka gare ni ka kuma cece ni. Ka zama dutsena da kagarata, inda kullum zan je. Ka ba da umarni a cece ni, gama kai ne dutsen ɓuyana da katangata. Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye, da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta. Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ƙarfin zuciyata tun ina yaro. Daga haihuwa na dogara gare ka; kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata. Kullayaumi zan yabe ka. Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci, amma kai ne katangata mai ƙarfi. Bakina ya cika da yabonka, ina furta darajarka dukan yini. Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa; kada ka yashe ni sa’ad da ƙarfina ya ƙare. Gama abokan gābana suna magana a kaina; waɗanda suke jira su kashe ni suna haɗa baki tare. Suna cewa, “Allah ya yashe shi; mu fafare shi mu kama shi, gama ba wanda zai kuɓutar da shi.” Kada ka yi nisa da ni, ya Allah; zo da sauri, ya Allahna, ka taimake ni. Bari masu zagina su hallaka da kunya; bari waɗanda suke so su cutar da ni su sha ba’a da kuma kunya. Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya; zan yabe ka sau da sau. Bakina zai ba da labarin adalcinka, zai yi maganar cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba. Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka; zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai. Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki. Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa. Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah, kai da ka yi manyan abubuwa. Wane ne kamar ka, ya Allah? Ko da yake ka sa na ga wahaloli, masu yawa da kuma masu ɗaci, za ka sāke mayar mini da rai; daga zurfafan duniya za ka sāke tā da ni. Za ka ƙara girmana ka sāke ta’azantar da ni. Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila. Leɓunana za su yi sowa don farin ciki sa’ad da na rera yabo gare ka, ni, wanda ka fansa. Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci dukan yini, gama waɗanda suka so su cutar da ni sun sha kunya suka kuma rikice. Zabura 72 Ta Solomon. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka. Zai72.2 Ko kuwa Bari yă; daidai da ayoyi 3-11 da kuma 17. shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya. Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci. Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece ’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya. Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai. Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa. A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata. Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi72.8 Wato, Yuferites zuwa iyakar duniya.72.8 Ko kuwa iyakar ƙasa Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura. Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai. Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa. Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako. Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa. Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa. Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini. Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar; bari yă cika bisan tuddai. Bari ’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon; bari yă bazu kamar ciyayi a gona. Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki. Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada; bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa. Amin kuma Amin. Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse. LITTAFI NA UKU Zabura 73–89 Zabura 73 Zabura ta Asaf. Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila, ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya. Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi; tafin ƙafana ya yi kusan zamewa. Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi. Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi. Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam. Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga. Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka. Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya. Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya. Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace.73.10 Ba a tabbatar da ma’anar Ibraniyancin da aka yi amfani da shi a wannan aya ba. Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?” Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa. Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi. Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya. Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe ’ya’yanka. Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama. Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka. Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya! Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai. Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi, na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka. Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana. Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka. Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai. Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada. Waɗanda suke nesa da kai za su hallaka; kakan hallaka dukan waɗanda suke maka rashin aminci. Amma game da ni, yana da kyau in kasance kusa da Allah. Na mai da Ubangiji Mai Iko Duka mafakata; zan yi shelar dukan ayyukanka. Zabura 74 Maskil 74.0 Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce. na Asaf. Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah? Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka? Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa, kabilar gādonka, wadda ka fansa, Dutsen Sihiyona, inda ka zauna. Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai, dukan wannan hallakar da abokin gāba ya yi wa wuri mai tsarki. Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu; suka kakkafa tutotinsu a matsayin alamu. Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura don yanka itatuwa a kurmi. Sun ragargaje dukan sassaƙar katako da gatura da kuma gudumarsu. Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus; suka ƙazantar da mazaunin Sunanka. Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!” Suka ƙone ko’ina aka yi wa Allah sujada a ƙasar. Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba; ba sauran annabawan da suka ragu, kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba. Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah? Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne? Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama? Ka fid da shi daga rigarka ka hallaka su! Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa; ka kawo ceto a kan duniya. Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka; ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye. Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada. Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka; ka busar da koguna masu ruwa. Yini naka ne, dare kuma naka ne; ka kafa rana da wata. Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya; ka yi rani da damina. Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji, yadda wawaye suka ɓata sunanka. Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji; kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba. Ka kula da alkawarinka, domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar. Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya; bari matalauta da mabukata su yabe sunanka. Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka; ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini. Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka, ihun abokan gābanka, waɗanda suke ci gaba da yi. Zabura 75 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Kada A Hallaka.” Zabura ta Asaf. Waƙa ce. Muna maka godiya, ya Allah, muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa; mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki. Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci; ni ne wanda yake shari’ar gaskiya. Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza, ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Sela Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’ ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku. Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama; kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ” Ba wani daga gabas ko yamma ko hamada da zai ɗaukaka mutum. Amma Allah ne mai yin shari’a, yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani. A hannun Ubangiji akwai kwaf cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji; yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa su sha shi tas. Game da ni dai, zan furta wannan har abada; zan rera yabo ga Allah na Yaƙub, wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.” Zabura 76 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce. A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila. Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona. A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa. Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa. A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi. Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi? Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit, sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka. Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro. Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa. Zabura 77 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Na Asaf. Zabura ce. Na yi kuka ga Allah don taimako; na yi kuka ga Allah don yă ji ni. Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji; da dare na miƙa hannuwa ba gajiya raina kuma ya ƙi yă ta’azantu. Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi; na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana. Sela ka hana idanuna rufewa; na damu ƙwarai har ba na iya magana. Na yi tunani kwanakin da suka wuce, shekarun da suka wuce da daɗewa; na tuna da waƙoƙina da dare. Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani. “Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba? Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci? Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” Sela Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan, shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.” Zan tuna da ayyukan Ubangiji; I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā. Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata. Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne. Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu? Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai; ka nuna ikonka a cikin mutane. Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka, zuriyar Yaƙub da Yusuf. Sela Ruwaye sun gan ka, ya Allah, ruwaye sun gan ka suka firgita; zurfafan gaske sun girgiza. Gizagizai sun sauko da ruwa, sararin sama suka buga tsawa; kibiyoyinka suka yi ta kai komo da walƙiya. Aka ji tsawanka a cikin guguwa, walƙiyarka ta haskaka duniya; duniya ta yi rawar jiki ta girgiza. Hanyarka ta bi ta cikin teku, hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye, duk da haka ba a ga sawunka ba. Ka bi da mutanenka kamar garke ta hannun Musa da Haruna. Zabura 78 Maskil 78.0 Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce. na Asaf. Ya mutanena, ku ji koyarwata; ku saurari kalmomin bakina. Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan dā, abin da muka ji muka kuma sani, abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana. Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba; za mu faɗa wa tsara mai zuwa ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji, ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata. Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu, don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu. Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa. Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba, masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa, waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba, waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba. Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna, suka juya da baya a ranar yaƙi; ba su kiyaye alkawarin Allah ba suka kuma ƙi su yi rayuwa ta wurin dokarsa. Suka manta da abin da ya aikata, abubuwan banmamakin da ya nuna musu. Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu a ƙasar Masar, a yankin Zowan. Ya raba teku ya kuma bi da su ciki; ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango. Ya bishe su da girgije da rana da kuma haske daga wuta dukan dare. Ya tsage duwatsu a cikin hamada ya kuma ba su ruwaye a yalwace kamar tekuna; ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga ya sa ruwa ya gudu kamar koguna. Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka. Da gangan suka gwada Allah ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi. Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada? Sa’ad da ya bugi dutse, ruwa ya ɓulɓulo, rafuffuka suka yi gudu a yalwace. Amma zai iya ba mu abinci? Zai iya tanada wa mutanensa nama?” Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila, gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa. Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sammai; ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci, ya ba su hatsin sama. Mutane suka ci burodin mala’iku; ya aika musu dukan abincin da za su iya ci. Ya saki iskar gabas daga sammai ya kuma saki iskar yamma ta wurin ikonsa. Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura, tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku. Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu, ko’ina kewaye da tentunansu. Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su, gama ya ba su abin da suka yi kwaɗayi. Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi, kai tun ma yana a bakunansu, fushin Allah ya ƙuna a kansu; ya karkashe waɗanda suka fi ƙiba a cikinsu, yana yankan matasan Isra’ila. Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi; duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba. Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa. A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi. Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu, cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu. Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki, suna masa ƙarya da harsunansu; zukatansu ba sa biyayya gare shi, ba su da aminci ga alkawarinsa. Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba. Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa. Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada suka kuma ɓata masa rai a jeji! Sau da sau suka riƙa gwada Allah; suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila. Ba su tuna da ikonsa, a ranar da ya fanshe su daga mai danniya, ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba. Ya mai da kogunansu suka zama jini; ba su iya sha daga rafuffuka ba. Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su, da kwaɗin da suka wahalshe su. Ya ba da hatsinsu ga fāra, amfanin gonakinsu ga ɗango. Ya lalace inabinsu da ƙanƙara itatuwan al’ul nasu kuma da jaura. Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara, tumakinsu ga aradun tsawa. Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa. Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba. Ya bugi kowane ɗan fari na Masar, mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham. Amma ya fitar da mutanensa kamar garke; ya bi da su kamar tumaki ta cikin hamada. Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro; amma teku ya cinye abokan gābansu. Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki, zuwa ƙasar tudun da hannunsa na dama ya kame. Ya kori al’ummai a gabansu ya rarraba ƙasashensu gare su a matsayin gādo; ya zaunar da kabilan Isra’ila a gidajensu. Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba. Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci, marar tabbas kamar tanƙwararren baka. Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu. Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya. Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane. Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba. Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa. Wuta ta cinye matasansu maza, ’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure; aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba. Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa, kamar yadda mutum kan farka daga buguwar ruwan inabi. Ya kori abokan gābansa; ya sa suka sha madawwamiyar kunya. Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba; amma ya zaɓi kabilar Yahuda, Dutsen Sihiyona, wanda ya ƙaunaci. Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa, kamar duniyar da ya kafa har abada. Ya zaɓi Dawuda bawansa ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki; daga kiwon tumaki ya kawo shi don yă kuma zama makiyayin mutanensa Yaƙub, na Isra’ila gādonsa. Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya; da hannuwa masu gwaninta ya bi da su. Zabura 79 Zabura ta Asaf. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai. Sun ba da gawawwakin bayinka kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama, nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya. Sun zubar da jini kamar ruwa ko’ina a Urushalima, kuma babu wani da zai binne matattu. Mun zama abin reni ga maƙwabta, abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu. Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne? Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta? Ka zuba fushinka a kan al’umman da ba su yarda da kai ba, a kan mulkokin da ba sa kira bisa sunanka; gama sun cinye Yaƙub suka lalatar da ƙasar zamansa. Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu; bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu, gama mun fid da zuciya sarai. Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, saboda ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu saboda sunanka. Don me al’ummai za su ce, “Ina Allahnsu yake?” A idanunmu, ka sanar wa al’ummai cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar. Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka; ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa. Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji. Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka, za mu yabe ka har abada; daga tsara zuwa tsara za mu yi ta ba da labarin yabonka. Zabura 80 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Lilin Alkawari.” Na Asaf. Zabura ce. Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka a gaban Efraim, Benyamin da Manasse. Ka tā da ƙarfinka; ka zo ka cece mu. Ka mai da mu, ya Allah; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu. Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka? Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf. Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu, kuma abokan gābanmu suna mana ba’a. Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu. Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi. Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa. Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa. Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi. Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa? Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa. Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi, saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka. An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka. Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka, ɗan mutum da ka renar wa kanka. Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka. Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu. Zabura 81 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.81.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Ta Asaf. Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub! Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga, ku kaɗa garaya da molo masu daɗi. Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata, da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu; wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila, farilla ta Allah na Yaƙub. Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf sa’ad da ya fito daga Masar. Muka ji yaren da ba mu fahimta ba. Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku; an ’yantar da hannuwansu daga kwando. Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba. Sela “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku, in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila! Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku; ba za ku rusuna ga baƙon allah ba. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi. “Amma mutanena ba su saurare ni ba; Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba. Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare don su bi dabararsu. “A ce mutanena za su saurare ni, a ce Isra’ila zai bi hanyoyina, da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu! Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki, hukuncinsu kuma zai dawwama har abada. Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau; da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.” Zabura 82 Zabura ta Asaf. Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”. “Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya. Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye. “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya. “Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne. Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.” Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne. Zabura 83 Waƙa ce. Zabura ta Asaf. Ya Allah, kada ka yi shiru; kada ka tsaya cik, ya Allah, kada ka daina motsi. Dubi yadda abokan gābanka suke fariya, dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu. Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka; suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so. Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma, don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.” Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare; suka haɗa kai gāba da kai, tentunan Edom da na mutanen Ishmayel, na Mowab da kuma na Hagirawa, Gebal, Ammon da Amalek, Filistiya, tare da mutanen Taya. Har Assuriya ma ta haɗa kai da su don ta ba da ƙarfi ga zuriyar Lot. Sela Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan, yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon, waɗanda suka hallaka a En Dor suka zama kamar juji a ƙasa. Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib, dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna, waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki wuraren kiwon Allah.” Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna, kamar yayin da iska take hurawa, kamar yadda wuta ke cin kurmi ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu, haka za ka kore su da iska mai ƙarfi ka kuma firgita su da guguwarka. Ka rushe fuskokinsu da kunya don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji. Bari su kasance cikin kunya da taƙaici; bari su hallaka cikin wulaƙanci. Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji, cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya. Zabura 84 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.84.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Na ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki! Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai. Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna. Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. Sela Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne. Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna. Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. Sela Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka. Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye. Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai. Ya Ubangiji Maɗaukaki, mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka. Zabura 85 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub. Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. Sela Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka. Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu. Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki? Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka? Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka. Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta. Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu. Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba. Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa, adalci kuma yă duba daga sama. Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta. Adalci na tafiya a gabansa yana shirya hanya domin ƙafafunsa. Zabura 86 Addu’ar Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma. Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka. Kai ne Allahna; ka ceci bawanka wanda ya dogara gare ka. Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini. Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina. Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; ka saurari kukata na neman jinƙai. A lokacin wahala zan yi kira gare ka, gama za ka amsa mini. A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji; babu ayyukan da za a kwatanta da naka. Dukan al’umman da ka yi za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji; za su kawo ɗaukaka ga sunanka. Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki; kai kaɗai ne Allah. Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji, zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka; ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba, don in ji tsoron sunanka. Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata; zan ɗaukaka sunanka har abada. Gama ƙaunarka da girma take gare ni; kai ka cece ni daga zurfafa, daga mazaunin matattu. Masu girman kai suna kai mini hari, ya Allah; ƙungiyar marasa imani suna neman raina, mutanen da ba su kula da kai ba. Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci. Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai; ka ba wa bawanka ƙarfi; ka ceci ni gama na bauta maka yadda mahaifiyata ta yi. Ka ba ni alamar alherinka, don abokan gābana su gani su kuma sha kunya, gama kai, ya Ubangiji, ka taimake ni ka kuma ta’azantar da ni. Zabura 87 Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki. Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub. Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, Sela “Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ” Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.” Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” Sela Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.” Zabura 88 Waƙa ce, Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannot88.0 Kan magana, mai yiwuwa muryar “Tsananin Baƙin Ciki.” maskil88.0 Kan magana, mai yiwuwa kalma waƙa ce. na Heman dangin Ezra. Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka. Bari addu’ata ta zo a gabanka; ka kasa kunne ga kukata. Gama raina yana cike da wahala rayuwata tana gab da kabari.88.3 Da Ibraniyanci Sheol An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami; ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne. An ware ni tare da matattu, kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari, waɗanda ba ka ƙara tunawa, waɗanda aka yanke daga taimakonka. Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa cikin zurfafa mafi duhu. Hasalarka tana da nauyi a kaina; ka turmushe ni da dukan raƙumanka. Sela Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka. Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? Sela Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne? An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira? Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka. Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni? Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya. Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni. Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum. Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa. Zabura 89 Maskil 89.0 Kan magana, mai yiwuwa kalmar waƙa ce. na Etan dangin Ezra. Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai. Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta. Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana, cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ” Sela Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji, amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka. Gama wane ne a sarari za a iya kwatanta da Ubangiji? Wane ne yake kamar Ubangiji a cikin talikan samaniya? Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro; shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi. Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka? Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka. Kana mulkin teku mai tumbatsa; sa’ad da raƙuma sun tashi, kakan kwantar da su. Ka ragargaza Rahab kamar waɗanda aka kashe; da hannunka mai ƙarfi ka watsar da abokan gābanka. Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta. Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka. Hannunka mai iko ne; hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka. Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka; ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka. Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji. Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini; suna samun ɗaukaka cikin adalcinka. Gama kai ne ɗaukakarsu da ƙarfinsu, kuma ta wurin alherinka ka ɗaukaka ƙahonka.89.17 ƙaho a nan na kwatanta mai ƙarfi. Tabbatacce, garkuwarmu ta Ubangiji ce, ta sarkinmu ce, da kuma ta Mai Tsarki na Isra’ila ce. Ka taɓa yin magana cikin wahayi, ga mutanenka masu aminci ka ce, “Na ba wa jarumi ƙarfi; na ɗaukaka saurayi daga cikin mutane. Na sami Dawuda bawana; da mai na mai tsarki na shafe shi. Hannuna zai kasance tare da shi; tabbatacce hannuna zai ƙarfafa shi. Babu abokin gāban da zai sa yă biya haraji; babu mugun mutumin da zai danne shi. Zan murƙushe maƙiyansa a gabansa in kashe dukan abokan gābansa. Amintacciya ƙaunata za tă kasance tare da shi, kuma ta wurin sunana za a ɗaukaka ƙahonsa. Zan sa hannunsa a bisa teku, hannunsa na dama a bisa koguna. Zai yi kira gare ni yă ce, ‘Kai ne Mahaifina, Allahna, Dutse mai cetona.’ Zan kuma naɗa shi ɗan farina, mafi ɗaukaka cikin sarakunan duniya. Zan ci gaba da ƙaunarsa har abada, alkawarina da shi ba zai taɓa fasa ba. Zan kafa zuriyarsa har abada, kursiyinsa muddin sammai suna nan. “In ’ya’yansa maza suka yashe dokata ba su kuwa bi ƙa’idodina ba, in suka take ƙa’idodina suka kuma kāsa kiyaye umarnaina, zan hukunta zunubinsu da sanda, laifinsu da bulala; amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba, ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba. Ba zan take alkawarina ba ko in canja abin da leɓunana suka ambata. Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba, cewa zuriyarsa za tă ci gaba har abada kuma kursiyinsa zai dawwama a gabana kamar rana; zai kahu har abada kamar wata, amintacciyar shaida a cikin sarari.” Sela Amma ka ƙi, ka yi ƙyama ka kuma yi fushi sosai da shafaffenka. Ka soke alkawarin da ka yi da bawanka ka kuma ƙazantar da rawaninsa a ƙura. Ka rurrushe dukan katangansa ka sa kagaransa suka zama kufai. Dukan waɗanda suka wuce sun washe shi; ya zama abin dariya wajen maƙwabtansa. Ka ɗaukaka hannun dama na maƙiyansa; ka sa dukan abokan gābansa suna farin ciki. Ka juye bakin takobinsa ba ka kuma taimake shi a cikin yaƙi ba. Ka kawo ƙarshen darajarsa ka kuma jefar da kursiyinsa ƙasa. Ka rage kwanakin ƙuruciyarsa; ka rufe shi da mayafin kunya. Sela Har yaushe, ya Ubangiji za ka ɓoye? Za ka ɓoye har abada ne? Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta? Ka tuna yadda raina mai wucewa ne. Gama ka halicce dukan mutane ba amfani! Wanda mutum ne zai rayu da ba zai ga mutuwa ba, ko yă cece kansa daga ikon kabari? Sela Ya Ubangiji, ina ƙaunar mai girma ta dā, wadda cikin amincinka ka rantse wa Dawuda? Ka tuna, Ubangiji, yadda aka yi wa bawanka ba’a, yadda na jimre a zuciyata da zage-zagen dukan al’ummai, zage-zagen da abokan gābanka suka yi mini, ya Ubangiji, da suka yi wa kowane matakin da shafaffenka ya ɗauka. Yabo ya tabbata ga Ubangiji har abada! Amin kuma Amin. LITTAFI NA HUƊU Zabura 90–106 Zabura 90 Addu’ar Musa Mutumin Allah. Ubangiji kai ne mazauninmu cikin dukan zamanai. Kafin a haifi duwatsu ko a fid da ƙasa da duniya, daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne. Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku ’ya’yan mutane.” Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare. Ka share mutane cikin barcin mutuwa; suna kama da sabuwa ciyawar safiya, ko da yake da safe takan yi sabuwar huda da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane. An cinye mu ta wurin fushinka mun kuma razana ta wurin hasalarka. Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka. Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka; mun gama shekarunmu da nishi. Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin, in muna da ƙarfi; duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai, gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare. Wa ya san ƙarfin fushinka? Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai. Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai, don mu sami zuciyar hikima. Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba? Ka ji tausayin bayinka. Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa, don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu. Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba, kamar yawan shekarun da muka ga wahala. Bari a nuna ayyukanka ga bayinka, darajarka ga ’ya’yansu. Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu. Zabura 91 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.91.1 Da Ibraniyanci Shaddai Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda nake dogara.” Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa. Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga. Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba, ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana. Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai. Za ka dai gan da idanunka yadda ake hukunta mugaye. In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata, to, babu wani mugun abin da zai same ka, ba masifar da za tă zo kusa da tentinka. Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka; za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse. Za ka taka zaki da gamsheƙa; za ka tattake babban zaki da maciji. Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana. Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi. Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.” Zabura 92 Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci. Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka, don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare, da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya. Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka. Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai! Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba, cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada. Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada. Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta. Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina. Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana. Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon; da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu. Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar, suna shela cewa, “Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.” Zabura 93 Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka; Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi. An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba. An kafa kursiyin tun da daɗewa; kana nan tun fil azal. Tekuna sun taso, ya Ubangiji, tekuna sun ta da muryarsu; tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa. Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye, mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku, Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne. Ƙa’idodinka suna nan daram; tsarki ya yi wa gidanka ado har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji. Zabura 94 Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa, Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka. Ka tashi, ya Alƙalin duniya; ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su. Har yaushe mugaye, ya Ubangiji har yaushe mugaye za su yi ta murna? Suna ta yin maganganun fariya; dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya. Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji; suna danne gādonka. Suna kashe gwauraye da kuma baƙi; suna kisan marayu. Suna ce, “Ubangiji ba ya gani; Allah na Yaƙub bai kula ba.” Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane; ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima? Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne? Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne? Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne? Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne? Ubangiji ya san tunanin mutum; ya san cewa tunaninsu banza ne. Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji, mutumin da ka koyar daga dokarka; kana ba shi sauƙi a lokacin wahala, sai har an haƙa rami wa mugaye. Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba; ba zai taɓa yashe gādonsa ba. Za a sāke kafa hukunci a kan adalci, kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi. Wane ne zai yi gāba da mugaye domina? Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina? Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba, da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa. Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni. Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina, ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina. Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai, wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar? Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa. Amma Ubangiji ya zama kagarata, Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka. Zai sāka musu saboda zunubansu yă kuma hallaka su saboda muguntarsu; Ubangiji Allahnmu zai hallaka su. Zabura 95 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu. Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa. Gama Ubangiji Allah mai girma ne, babban Sarki a bisa dukan alloli. A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne. Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa. Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu; gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa, “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba,95.8 Meriba yana nufin faɗa. kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa95.8 Massa yana nufin gwaji. a hamada, inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi. Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’ Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Zabura 96 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka. Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane. Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli. Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai. Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa. Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi. Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa. Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa; ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya. Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya. Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa; bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu. Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki; za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa. Zabura 97 Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna; bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki. Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi; adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa. Wuta tana tafiya a gabansa tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe. Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki. Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya. Sammai sun yi shelar adalcinsa, dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa. Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya, waɗanda suke fariya da gumaka, ku yi masa sujada, dukanku alloli! Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji. Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya; ana darjanta ka fiye da dukan alloli. Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta, gama yana tsaron rayukan amintattunsa yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye. An haskaka haske a kan masu adalci da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya. Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci, ku kuma yabi sunansa mai tsarki. Zabura 98 Zabura ce. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto. Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai. Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi; ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa, tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki. Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta. Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki; bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya. Zabura 99 Ubangiji yana mulki, bari al’ummai su yi rawan jiki; yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, bari duniya ta girgiza. Ubangiji mai girma yana a Sihiyona; an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai. Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana, shi mai tsarki ne. Sarki mai iko ne, yana ƙaunar adalci ka kafa gaskiya; a cikin Yaƙub ka yi abin da yake mai adalci da kuma daidai. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa; shi mai tsarki ne. Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu. Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije; ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su. Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa musu; ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa, ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki, gama Ubangiji Allahnmu mai tsarki ne. Zabura 100 Zabura ce. Don yin godiya. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya. Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki. Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa. Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa. Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai. Zabura 101 Ta Dawuda. Zabura ce. Zan rera wa ƙauna da adalcinka; gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo. Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi, yaushe za ka zo gare ni? Zan bi da sha’anin gidana da zuciya marar abin zargi Ba zan kafa a gaban idanuna 1 wani abu marar kyau ba. Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci; ba za su manne mini ba. Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta. Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba. Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima. Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana. Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji. Zabura 102 Addu’ar mutum mai shan wahala. Sa’ad da ya rasa ƙarfi ya kuma yi makoki a gaban Ubangiji. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri. Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta. Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci. Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai. Ni kamar mujiyar jeji ne, kamar mujiya a kufai. Na kwanta a faɗake; na zama kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki. Dukan yini abokan gābana suna tsokanata; waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana. Gama ina cin toka a matsayin abincina ina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye saboda fushinka mai girma, gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe. Kwanakina suna kamar inuwar yamma; na bushe kamar ciyawa. Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai. Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo. Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka; ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi. Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka. Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa. Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba. Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji, Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa, daga sama ya hangi duniya, don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.” Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima sa’ad da mutane da mulkoki suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada. Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina; ya gajartar da kwanakina. Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai. A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne. Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su. Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba. ’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.” Zabura 103 Ta Dawuda. Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki. Yabi Ubangiji, ya raina, kada kuma ka manta dukan alheransa, wanda yake gafarta dukan zunubai yake kuma warkar da dukan cututtuka, wanda ya fanshi ranka daga rami ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi, Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa. Ubangiji yana aikata adalci da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne. Ya sanar da hanyoyinsa wa Musa, ayyukansa ga mutanen Isra’ila. Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna. Ba zai yi ta zargi ba ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba; ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu. Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa; kamar yadda gabas yake daga yamma, haka ya cire laifofinmu daga gare mu. Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa, haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa; gama ya san yadda aka yi mu, ya tuna cewa mu ƙura ne. Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona; iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake. Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu, tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa. Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama, masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka. Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa, ku jarumawa masu yi masa aiki, waɗanda suke yin biyayya da maganarsa. Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama, ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa. Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa ko’ina a mulkinsa. Yabi Ubangiji, ya raina. Zabura 104 Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka. Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye. Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa yana hawa a kan fikafikan iska. Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa. Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba. Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu. Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu; suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu. Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba. Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka; yana gudu tsakanin duwatsu. Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji; jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu. Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan; suna rera cikin rassa. Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama; ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa. Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu, tsire-tsire domin mutum ya nome, suna fid da abinci daga ƙasa, ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna, mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske, abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa. Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai, al’ul na Lebanon da ya shuka. A can tsuntsaye suke sheƙunnansu; shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir. Manyan duwatsu na awakin jeji ne; tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema. Wata ne ke ƙididdigar lokuta, rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi. Ka yi duhu, sai ya zama dare, sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe. Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta suna kuma neman abincinsu daga Allah. Rana ta fito, sai suka koma shiru; suka koma suka kwanta a kogwanninsu. Mutum yakan tafi aikinsa, zuwa wurin aikinsa har yamma. Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka. Akwai teku, babba da kuma fāɗi, cike da halittun da suka wuce ƙirga, abubuwa masu rai babba da ƙarami. A can jiragen ruwa suna kai komo, kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can. Waɗannan duka suna dogara gare ka don ka ba su abincinsu a daidai lokaci. Sa’ad da ba su da shi, sai su tattara shi; sa’ad da ka buɗe hannunka, sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau. Sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai su razana; sa’ad da ka ɗauke numfashinsu, sai su mutu su kuma koma ga ƙura. Sa’ad da ka aika da Ruhunka, sai su halittu, su kuma sabunta fuskar duniya. Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada; bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa, shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana, wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi. Zan rera ga Ubangiji dukan raina; zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye. Bari tunanina yă gamshe shi, yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji. Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya mugaye kuma kada a ƙara ganinsu. Yabi Ubangiji, ya raina. Yabi Ubangiji.104.35 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; a cikin Seftuwajin wannan layi yana a farkon Zabura 105.1. Zabura 105 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi. Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata. Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki; bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki. Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum. Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi, mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar, Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa. Shi ne Ubangiji Allahnmu; kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya. Yana tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu, alkawarin da ya yi da Ibrahim, rantsuwar da ya yi wa Ishaku. Ya tabbatar da shi ga Yaƙub a matsayin ƙa’ida, Isra’ila a matsayin madawwamin alkawari, “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana a matsayin rabo za ka yi gādo.” Sa’ad da suke kima kawai, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta, suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga masarauta zuwa wata. Bai bar kowa yă danne su ba; saboda su, ya tsawata wa sarakuna, “Kada ku taɓa shafaffena; kada ku yi wa annabawa lahani.” Ya sauko da yunwa a kan ƙasa ya kuma lalace dukan tanadinsu na abinci; ya kuma aiki mutum a gabansu, Yusuf, da aka sayar a matsayin bawa. Suka raunana ƙafafunsa da sarƙa aka sa wuyansa cikin ƙarafa, sai abin da ya rigafaɗi ya cika sai da maganar Ubangiji ta tabbatar da shi mai gaskiya. Sarki ya aika aka kuma sake shi, mai mulkin mutane ya ’yantar da shi. Ya mai da shi shugaban gidansa, mai mulki a bisa dukan abin da ya mallaka, don yă umarci sarakunansa yadda ya ga dama yă kuma koya wa dattawa hikima. Sa’an nan Isra’ila ya shiga Masar; Yaƙub ya yi zama kamar baƙo a ƙasar Ham. Ubangiji ya mai da mutanensa suka yi ta haihuwa; ya sa suka yi yawa suka fi ƙarfin maƙiyansu, waɗanda ya juya zukatansu su ƙi mutanensa don su haɗa baki a kan bayinsa. Ya aiki Musa bawansa, da Haruna, wanda ya zaɓa. Suka yi mu’ujizansa a cikinsu, abubuwan mamakinsa a cikin ƙasar Ham. Ya aiko da duhu ya kuma sa ƙasar tă yi duhu, ba domin sun yi tawaye a kan maganarsa ba? Ya mai da ruwaye suka zama jini, ya sa kifayensu suka mutu. Ƙasarsu ta yi ta fid da kwaɗi, waɗanda suka haura cikin ɗakunan kwana na masu mulkinsu. Ya yi magana, sai tarin ƙudaje suka fito, cinnaku kuma ko’ina a ƙasar. Ya mai da ruwan samansu ya zama ƙanƙara, da walƙiya ko’ina a ƙasarsu; ya lalace inabinsu da itatuwan ɓaurensu ya ragargaza itatuwan ƙasarsu. Ya yi magana, sai fāri ɗango suka fito, fāran da ba su ƙidayuwa; suka cinye kowane abu mai ruwan kore a cikin ƙasarsu, suka cinye amfanin gonarsu Sa’an nan ya karkashe dukan ’yan fari a cikin ƙasarsu, nunan fari na dukan mazantakarsu. Ya fitar da Isra’ila, ɗauke da azurfa da zinariya, kuma daga cikin kabilansu babu wani da ya kāsa. Masar ta yi murna sa’ad da suka tafi, saboda tsoron Isra’ila ya fāɗo musu. Ya shimfiɗa girgije kamar mayafi, da kuma wuta don ta ba su haske da dare. Suka roƙa, ya kuwa ba su makware ya kuma ƙosar da su da abinci daga sama. Ya buɗe dutse, sai ruwa ya ɓulɓulo, kamar kogi ya gudu zuwa cikin hamada. Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki da ya ba wa bawansa Ibrahim. Ya fitar da mutanensa da farin ciki, zaɓaɓɓunsa da sowa ta farin ciki; ya ba su ƙasashen al’ummai, suka kuma sami gādon abin da waɗansu sun sha wahala a kai, don su kiyaye farillansa su kuma kiyaye dokokinsa. Yabo ga Ubangiji.105.45 Da Ibraniyanci Hallelu Ya Zabura 106 Yabi Ubangiji.106.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka kuma a aya 48. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji ko yă furta cikakken yabonsa? Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci, waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai. Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka, ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su, don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka, don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka in kuma shiga gādonka cikin yin yabo. Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta. Sa’ad da kakanninmu suke a Masar, ba su damu da mu’ujizanka ba; ba su tuna yawan alheranka ba, suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku. Duk da haka ya cece su saboda sunansa, don yă sanar da ikonsa mai girma. Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe; ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada. Ya cece su daga hannun maƙiyi; daga hannun abokin gāba ya fanshe su. Ruwaye suka rufe abokan gābansu; babu ko ɗaya da ya tsira. Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa suka kuma rera yabonsa. Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba. A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah. Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta. A sansani suka ji kishin Musa da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe. Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta binne iyalin Abiram. Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu; harshen wuta ya cinye mugaye. A Horeb suka yi ɗan maraƙi suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada. Suka sauke Ɗaukakarsu saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa. Suka manta da Allahn da ya cece su, wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar, mu’ujizai a ƙasar Ham ayyukan banrazana a Jan Teku. Don haka ya ce zai hallaka su, amma Musa, zaɓaɓɓensa, ya yi godo a gabansa don yă kau da hasalarsa daga hallaka su. Sai suka rena ƙasa mai ni’ima; ba su gaskata alkawarinsa ba. Suka yi gunaguni a tentunansu ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba. Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu cewa zai sa su mutu a cikin hamada, ya sa zuriyarsu su mutu a cikin al’ummai ya kuma watsar da su cikin dukan ƙasashe. Suka haɗa kai da Ba’al-Feyor suka kuma ci hadayun da aka miƙa wa allolin da ba su da rai; suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu. Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki, sai annobar ta daina. An ayana masa wannan a matsayin adalci har zamanai marar matuƙa masu zuwa. A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi, sai wahala ta zo wa Musa saboda su; saboda sun yi tayarwa a kan Ruhun Allah, har mugayen kalmomi suka fito daga leɓunan Musa. Ba su hallakar da mutanen yadda Ubangiji ya umarce su ba, amma suka yi cuɗanya da al’ummai suka ɗauki al’adunsu. Suka yi wa gumakansu sujada, waɗanda suka zama tarko gare su. Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu. Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu. Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi; ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa ya ji ƙyamar gādonsa. Ya miƙa su ga al’ummai, maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu. Abokan gābansu suka danne su suka sa su a ƙarƙashin ikonsu. Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu; saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi. Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su. Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu, ka kuma tattara mu daga al’ummai, don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya mu kuma ɗaukaka cikin yabonka. Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Bari dukan mutane su ce, “Amin!” Yabo ga Ubangiji. LITTAFI NA BIYAR Zabura 107–150 Zabura 107 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan, su da aka fansa daga hannun maƙiyi, su da ya tattara daga ƙasashe, daga gabas da yamma, daga arewa da kudu. Waɗansu sun yi ta yawo a jejin hamada, ba su sami hanya zuwa birnin da za su zauna ba. Sun ji yunwa da ƙishirwa, suka kuma fid da zuciya. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuma cece su daga damuwarsu. Ya bishe su ta miƙaƙƙiyar hanya zuwa birnin da za su zauna. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane, gama yana shayar da masu ƙishirwa yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau. Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai, ’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe, gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka. Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu. Ya fitar da su daga duhu da zurfin ɓaci rai ya tsintsinke sarƙoƙinsu. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane, gama ya farfashe ƙofofin tagulla ya kuma ragargaza ƙyamaren ƙarfe. Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu. Ba su so su ga abinci ba suka kuwa kai bakin mutuwa. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu. Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane. Bari su miƙa hadaya ta godiya su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki. Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye. Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku. Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama. Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa; a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai. Suka yi tangaɗi suna tuntuɓe kamar bugaggu; suka kuma kai ga ƙarshen dabararsu. Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa fitar da su daga damuwarsu. Ya kwantar da hadiri suka yi tsit; raƙuman ruwan teku suka yi shiru. Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta, ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane. Bari su ɗaukaka shi cikin taron mutane su kuma yabe shi cikin taron dattawa. Ya mai da koguna suka zama hamada, maɓulɓulai masu gudu suka zama ƙasa mai ƙishirwa, ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani, saboda muguntar waɗanda suka zauna a can. Ya mai da hamada ya zama tafkunan ruwa busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulai masu gudu; a can ya kai mayunwata su yi zama, ya kuma samo birnin da za su zauna. Suka yi shuka a gonaki suka dasa inabi suka kuma girbe amfani gona; ya albarkace su, yawansu kuma ya ƙaru, bai kuwa bar garkunansu suka ragu ba. Sa’an nan yawansu ya ragu, aka kuma ƙasƙantar da su ta wurin danniya, bala’i da kuma baƙin ciki; shi da yake kawo reni a kan manyan mutane ya sa suka yi ta yawo a cikin jejin da ba hanya. Amma ya fid da mabukata daga wahalarsu ya kuma ƙara iyalansu da tumakinsu. Masu yin gaskiya suka gani suka yi farin ciki amma dukan mugaye suka rufe bakunansu. Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji. Zabura 108 Waƙa ce. Zabura ta Dawuda. Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah; zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina. Ku farka, garaya da molo! Zan farkar da rana. Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai cikin mutane. Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai; amincinka ya kai sarari. A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai, bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya. Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta. Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Ciki nasara zan raba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot. Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne; Efraim shi hulan kwanona, Yahuda ne sandana na sarauta. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.” Wa zai kawo ni birni mai katanga? Wa zai jagorance ni zuwa Edom? Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu? Ka ba mu taimako a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattaka abokan gābanmu. Zabura 109 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Allah, wanda nake yabo, kada ka yi shiru, gama mugaye da masu ruɗu sun buɗe bakunansu a kaina; sun yi magana a kaina da harsunan ƙarya. Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni; sun tasar mini ba dalili. A maimakon ƙauna sun sāka mini da zargi, amma ni mutum ne mai addu’a. Sun sāka mini alheri da mugunta, ƙauna kuma da ƙiyayya. Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi; bari mai zargi yă tsaya a hannun damansa. Sa’ad da aka yi masa shari’a, bari a same shi da laifi, bari kuma addu’o’insa su hukunta shi. Bari kwanakinsa su zama kaɗan; bari wani yă ɗauki wurinsa na shugabanci. Bari ’ya’yansa su zama marayu matarsa kuma gwauruwa. Bari ’ya’yansa su zama masu yawo suna bara; bari a yi ta koransu daga gidajensu da suke kufai. Bari mai binsa bashi yă ƙwace dukan abin da yake da shi; bari baƙi su washe amfanin aikinsa. Bari kada kowa yă yi masa alheri ko yă ji tausayin marayunsa. Bari duk zuriyarsa su mutu, a shafe sunayensu daga tsara mai zuwa. Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji; bari kada a taɓa shafe zunubin mahaifiyarsa. Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji kullum, don yă sa a manta da su daga duniya. Gama bai taɓa yin tunanin yin alheri ba, amma ya tsananta wa matalauta da mabukata da kuma masu fid da zuciya har suka mutu. Yana jin daɗin la’antarwa, bari yă dawo a kansa; ba ya son sa albarka, bari kada kowa yă sa masa albarka. Ya sa la’antarwa kamar rigarsa; ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa, cikin ƙasusuwansa kamar mai. Bari tă zama kamar mayafin da aka ɗaura kewaye da shi, kamar ɗamara da aka ɗaura kewaye da shi har abada. Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji ga masu zargina, ga waɗanda suke mugayen maganganu a kaina. Amma kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi da ni da kyau saboda sunanka; ta alherin ƙaunarka, ka cece ni. Gama ni matalauci ne mai bukata kuma, zuciyata kuwa ta yi rauni a cikina. Na ɓace kamar inuwar yamma; ana kakkaɓe ni kamar fāra. Gwiwoyina suna mutuwa saboda azumi; jikina ya rame ba kuma ƙarfi. Na zama abin dariya ga masu zargina; sa’ad da suka gan ni, suka kaɗa kawunansu. Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; ka cece ni bisa ga ƙaunarka. Bari su san cewa hannunka ne, cewa kai ne, ya Ubangiji, ka yi shi. Za su iya la’anta, amma kai za ka sa albarka; sa’ad da suka tasar za su sha kunya, amma bawanka zai yi farin ciki. Masu zargina za su sha kunya za a rufe su da kunya kamar mayafi. Da bakina zan ɗaukaka Ubangiji sosai; cikin babban taro zan yabe shi. Gama yana tsaya a hannun damar mai bukata, don yă cece ransa daga waɗanda suke hukunta shi. Zabura 110 Ta Dawuda. Zabura ce. Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka. Rundunarka za su so yin yaƙi a ranarka ta yaƙi. Saye cikin ɗaukaka mai tsarki, daga cikin ciki na safiya za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.110.3 Ko kuwa / samarinka za su zo gare ka kamar raba Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.” Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa. Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya. Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya; saboda haka zai ɗaga kansa sama. Zabura 111111 Wannan Zabura waƙa ce, layinta sun fara da jerin harufan Ibraniyanci bi da bi. Yabi Ubangiji.111.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro. Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu. Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada. Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma. Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada. Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai. Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne. Tsayayyu ne har abada abadin, ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya. Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa. Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo. Zabura 112112 Wannan Zabura waƙa ce, layinta sun fara da jerin harufan Ibraniyanci bi da bi. Yabi Ubangiji.112.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa. ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka. Wadata da arziki suna a cikin gidansa, adalcinsa zai dawwama har abada. Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya, mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.112.4 Ko kuwa / gama Ubangiji mai alheri ne, mai tausayi da kuma mai adalci. Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya. Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba; za a tuna da mai adalci har abada. Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji. Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa. Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa112.9 Ƙaho a nan yana nufin girma. sama da bangirma. Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi, zai ciza haƙora yă kuma lalace; sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe. Zabura 113 Yabi Ubangiji.113.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya, haka ma a aya 9. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji. Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji. Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa, wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya? Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka; ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu. Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji. Zabura 114 Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe, Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa. Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya; duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki. Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya, ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki? Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub, wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa. Zabura 115 Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba amma ga sunanka yă sami ɗaukaka, saboda ƙaunarka da amincinka. Me ya sa al’ummai suke cewa, “Ina Allahnsu?” Allahnmu yana a sama; yana yin duk abin da ya ga dama. Amma gumakansu azurfa da zinariya ne, da hannuwan mutane suka yi. Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani; suna da kunnuwa, amma ba sa ji, hanci, amma ba sa jin ƙanshi suna da hannuwa, amma ba sa iya taɓa kome, ƙafafu, amma ba sa iya tafiya; ba sa iya ce wani abu da maƙogwaronsu. Masu yinsu za su zama kamar su, haka kuma zai kasance da duk wanda ya dogara da su. Ya gidan Isra’ila, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu. Ya gidan Haruna, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu. Ku da kuke tsoronsa, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu. Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu. Zai albarkace gidan Isra’ila, zai albarkace gidan Haruna, zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji, manya da ƙanana duka. Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru, da ku da ’ya’yanku. Bari Ubangiji yă albarkace ku, shi Mahalicci sama da ƙasa. Saman sammai na Ubangiji ne, amma ya ba da duniya ga mutum. Ba matattu ba ne masu yabon Ubangiji, waɗanda suke gangara zuwa wurin da ake shiru; mu ne masu ɗaukaka Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Yabi Ubangiji.115.18 Da Ibraniyanci Hallelu Ya Zabura 116 Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata; ya ji kukata ta neman jinƙai. Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai. Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni, wahalar kabari sun zo a kaina; na cika da wahala da ɓacin rai. Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!” Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci; Allahnmu yana cike da tausayi. Ubangiji yana tsare masu tawali’u; sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni. Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka. Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe, don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai. Na gaskata, saboda haka na ce, “An azabtar da ni ƙwarai.” Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.” Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni? Zan daga kwaf na ceto in kuma kira ga sunan Ubangiji. Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa. Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa. Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi. Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji. Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa, a filayen gidan Ubangiji, a tsakiyarki, ya Urushalima. Yabi Ubangiji.116.19 Da Ibraniyanci Hallelu Ya Zabura 117 Yabi Ubangiji, dukanku al’umma; ku ɗaukaka shi, dukanku mutane. Gama ƙaunarsa da girma take gare mu, amincin Ubangiji kuma madawwami ne har abada. Yabi Ubangiji.117.2 Da Ibraniyanci Hallelu Ya Zabura 118 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. Bari Isra’ila yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” Bari gidan Haruna yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni. Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai yi mini? Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona. Zan yi nasara a kan abokan gābana. Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum. Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga sarakuna. Dukan al’ummai sun kewaye ni, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su. Sun kewaye ni a kowane gefe, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su. Sun rufe ni kamar ƙudan zuma, amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta; a cikin sunan Ubangiji na hallaka su. An ture ni baya na kusa fāɗuwa, amma Ubangiji ya taimake ni. Ubangiji ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona. Sowa ta farin ciki da nasara sun fito a cikin tentunan adalai, “Hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa! An ɗaga hannun dama na Ubangiji sama; hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!” Ba zan mutu ba amma zan rayu, zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi. Ubangiji ya hore ni sosai, amma bai ba da ni ga mutuwa ba. Buɗe mini ƙofofin adalci; zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji. Wannan ne ƙofar Ubangiji inda adalai za su shiga. Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini; ka zama mai cetona. Zabura Dutsen da magina suka ƙi ya zama mai amfani; Ubangiji ne ya yi haka, kuma abu mai daraja ne a idanunmu. Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta. Ya Ubangiji, ka cece mu; Ya Ubangiji, ka ba mu nasara. Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji. Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka. Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade. Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya; kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka. Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada. Zabura 119119 Wannan Zabura waƙa ce, ayoyin kowane layi sun fara da irin harufan ɗaya na Ibraniyanci. א Alef Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji. Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu. Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa. Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su. Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana! Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka. Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci. Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum. ב Bet Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta? Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka. Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka. Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata don kada in yi maka zunubi. Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka. Da leɓunana na ba da labarin dukan dokokin da suka fito bakinka. Na yi farin ciki da bin farillanka yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa. Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka. Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba. ג Gimel Ka yi alheri ga bawanka, zan kuwa rayu; zan yi biyayya da maganarka. Ka buɗe idanuna don in iya gani abubuwan banmamaki a cikin dokarka. Ni baƙo ne a duniya; kada ka ɓoye mini umarnanka. Zuciyata ta ƙosa saboda marmari don dokokinka koyaushe. Ka tsawata wa masu fariya, waɗanda suke la’anta waɗanda kuma suka kauce daga umarnanka. Ka cire mini ba’a da reni, gama ina kiyaye farillanka. Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna, bawanka zai yi tunani a kan ƙa’idodinka. Farillanka ne abin farin cikina; su ne mashawartana. ד Dalet An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura; ka kiyaye raina bisa ga maganarka. Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini; ka koya mini ƙa’idodinka. Bari in gane koyarwar farillanka; sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka. Raina ya gaji da baƙin ciki; ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka. Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu; ka yi mini alheri ta wurin dokokinka. Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka. Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya. Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka ’yantar da zuciyata. ה He Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe. Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata. Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki. Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba. Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka. Ka cika alkawarinka ga bawanka, saboda a ji tsoronka. Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro, gama dokokinka nagari ne. Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka. ו Waw Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji, cetonka bisa ga alkawarinka; sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka. Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka. Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin. Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka. Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba, gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu. Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka. ז Zayin Tuna da maganarka ga bawanka, gama ka ba ni bege. Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce alkawarinka yana kiyaye raina. Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba, amma ban rabu da dokar ba. Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji, na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu. Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka. Ƙa’idodinka su ne kan waƙata a duk inda na sauka. Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka. Wannan shi ne na saba yi, ina yin biyayya da farillanka. ח Het Kai ne rabona, ya Ubangiji; na yi alkawarin in kiyaye maganarka. Na nemi fuskarka da dukan zuciyata; ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka. Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka. Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka. Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi, ba zan manta da dokokinka ba. Da tsakar dare nakan tashi in gode maka saboda dokokinka masu adalci. Ni aboki ne ga duk mai tsoronka, ga duk wanda yake bin farillanka. Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka. ט Tet Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji. Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka. Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka. Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka. Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata. Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka. Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka. Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu. י Yod Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka. Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka. Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni. Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka. Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina. Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka. Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni, waɗanda suka gane da farillanka. Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka, don kada in sha kunya. כ Kaf Raina ya tafke da marmari don cetonka, amma na sa zuciyata a maganarka. Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka; Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?” Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba. Har yaushe bawanka zai yi ta jira? Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini? Masu girman kai sun haƙa mini rami, sun ƙetare dokarka. Dukan umarnanka abin dogara ne; ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili. Sun kusa gama da ni a duniya, amma ban bar bin farillanka ba. Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka, zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka. ל Lamed Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai. Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama. Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima. Da ba don dokarka ce farin cikina ba, da na hallaka a cikin azabana. Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina. Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka. Mugaye suna jira su hallaka ni, amma zan yi ta tunani a kan farillanka. Ga duk cikakke na ga kāsawa; amma umarnanka ba su da iyaka. מ Mem Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini. Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni. Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka. Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka. Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka. Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini. Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina! Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba. נ Nun Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata. Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci. Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka. Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji, ka kuwa koya mini dokokinka. Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana, ba zan manta da dokarka ba. Mugaye sun kafa mini tarko, amma ban kauce daga farillanka ba. Farillanka su ne gādona har abada; su ne farin cikin zuciyata. Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka har ƙarshe. ס Samek Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka. Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna! Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata. Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci. Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne. Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti; saboda haka nake ƙaunar farillanka. Naman jikina na rawan jiki don tsoronka; na cika da tsoron dokokinka. ע Ayin Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai; kada ka ni a hannun masu danne ni. Ka tabbatar da lafiyar bawanka; kada ka bar masu girman kai su danne ni. Idanuna sun gaji, da jiran cetonka, da jiran alkawarinka mai adalci. Ka yi da bawanka bisa ga ƙaunarka ka kuma koya mini ƙa’idodinka. Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi don in gane farillanka. Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji; ana karya dokarka. Saboda ina ƙaunar umarnanka fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla, saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau, na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba. פ Fe Farillanka masu banmamaki ne; saboda haka nake yin biyayya da su. Fassarar maganganunka sukan ba da haske; sukan ba da ganewa ga marar ilimi. Ina hakkin da bakina a buɗe, ina marmarin umarnanka. Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, yadda kullum ka yi wa waɗanda suke ƙaunar sunanka. Ka bi da sawuna bisa ga maganarka; kada ka bar zunubi yă mallake ni. Ka fanshe ni daga mutane masu danniya, don in yi biyayya da farillanka. Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka ka kuma koya mini ƙa’idodinka. Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka. צ Tsade Mai adalci ne kai, ya Ubangiji, dokokinka kuma daidai ne. Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne; su kuma abin dogara ne ƙwarai. Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka. An gwada alkawuranka sarai, bawanka kuwa yana ƙaunarsu. Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni, ba na manta da farillanka. Adalcinka dawwammame ne dokar kuma gaskiya ce. Wahala da damuwa suna a kaina, amma umarnanka su ne farin cikina. Farillanka daidai ne har abada; ka ba ni ganewa don in rayu. ק Kof Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji, zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka. Na yi kira gare ka; ka cece ni zan kuwa kiyaye farillanka. Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako; na sa zuciyata a maganarka. Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka. Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka. Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa, amma suna nesa da dokarka. Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji, kuma dukan umarnanka gaskiya ne. Tun tuni na koyi daga farillanka cewa ka kafa su su kasance har abada. ר Resh Ka dubi wahalata ka cece ni, gama ban manta da dokarka ba. Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni, ka cece rai na kamar yadda ka alkawarta! Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka. Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji; ka kiyaye raina bisa ga dokokinka. Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini, amma ban rabu da farillanka ba. Na dubi marasa aminci da ƙyama, gama ba sa yin biyayya da maganarka. Dubi yadda nake ƙaunar farillanka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga ƙaunarka. Dukan maganganunka gaskiya ne; dukan dokokinka masu adalci madawwami ne. ש Sin da Shin Masu mulki suna tsananta mini ba dalili, amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka. Ina farin ciki da alkawarinka kamar yadda wani kan sami ganima mai girma. Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya amma ina ƙaunar dokarka. Sau bakwai a rana ina yabonka saboda dokokinka masu adalci. Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe. Ina jiran cetonka, ya Ubangiji, ina kuma bin umarnanka. Ina biyayya da farillanka, gama ina ƙaunarsu ƙwarai. Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka, gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka. ת Taw Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji; ka ba ni ganewa bisa ga maganarka. Bari roƙona yă zo gabanka; ka cece ni bisa ga alkawarinka. Bari leɓunana su cika da yabonka, gama ka koya mini ƙa’idodinka. Bari harshena yă rera game da maganarka, gama dukan umarnanka masu adalci ne. Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni, gama na zaɓi farillanka. Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji, dokarka kuwa ita ce farin cikina. Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni. Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya. Ka nemi bawanka, gama ban manta da umarnanka ba. Zabura 120 Waƙar haurawa. Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara. Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara? Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya. Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar! Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama. Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi. Zabura 121 Waƙar haurawa. Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo? Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa. Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba; tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci. Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka; rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare. Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka; Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma. Zabura 122 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.” Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima. An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda. A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila. A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda. Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya. Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.” Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.” Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki. Zabura 123 Waƙar haurawa. Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama. Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa. Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa. Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya. Zabura 124 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce, da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana, sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai; da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu. Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba. Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira. Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa. Zabura 125 Waƙar haurawa. Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona, wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada. Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, haka Ubangiji ya kewaye mutanensa yanzu da har abada kuma. Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance a kan ƙasar da take rabon adalai ba, domin kada masu adalci su yi amfani da hannuwansu su aikata mugunta. Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu, ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu. Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta. Salama tă kasance tare da Isra’ila. Zabura 126 Waƙar haurawa. Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki. Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.” Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki. Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb. Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki. Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna. Zabura 127 Waƙar haurawa. Ta Solomon. In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza. Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna. ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi. Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya. Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a. Zabura 128 Waƙar haurawa. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa. Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka. Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka. Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji. Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima, bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila. Zabura 129 Waƙar haurawa. Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce, sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba. Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi. Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye. Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya. Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma; da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa. Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.” Zabura 130 Waƙar haurawa. Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Ya Ubangiji, ka ji muryata. Bari kunnuwanka su saurara ga kukata ta neman jinƙai. In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai, Ya Ubangiji, wa zai tsaya? Amma tare da kai akwai gafartawa, saboda haka ake tsoronka. Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata. Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya. Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa. Shi kansa zai fanshi Isra’ila daga dukan zunubansu. Zabura 131 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina. Amma na haƙura na kuma kwantar da raina; kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa, kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina. Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma. Zabura 132 Waƙar haurawa. Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda da kuma dukan irin wuyan da ya jimre. Ya yi rantsuwa ga Ubangiji ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa, “Ba zan shiga gidana ko in kwanta a gado ba, ba zan ba wa idanuna barci ba, ba gyangyaɗi wa idanuna, sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.” Mun ji haka a Efrata, muka yi ƙaro da shi a filayen Ya’ar,132.6 Wato, Kiriyat Yeyarim,132.6 Ko kuwa mun ji game da shi a Efrata, mun same shi a filayen Ya’ar. (Kuma babu alamar keɓewa kewaye da ayoyi 7-9) “Bari mu tafi wurin zamansa; bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa, ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka. Bari a suturta firistocinka da adalci; bari tsarkakanka su rera don farin ciki.” Saboda Dawuda bawanka, kada ka ƙi shafaffenka. Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka, in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari da farillan da na koya musu, to ’ya’yansu maza za su zauna a kan kursiyinka har abada abadin.” Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa, “Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin; a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta, zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa; matalautanta za su ƙoshi da abinci. Zan suturta firistocinta da ceto, tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki. “A nan zan sa ƙaho132.17 Ƙaho a nan yana nufin wani mai ƙarfi, wato, sarki. ya yi girma wa Dawuda in kuma kafa fitila saboda shafaffena. Zan suturta abokan gābansa da kunya, amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.” Zabura 133 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya! Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai, yana gangarawa a gemu, yana gangarawa a gemun Haruna, har zuwa wuyan rigunansa. Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada. Zabura 134 Waƙar haurawa. Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji. Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji. Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona. Zabura 135 Yabi Ubangiji.135.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a ayoyi 3 da 21. Yabi sunan Ubangiji; yabe shi, ku bayin Ubangiji, ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji, cikin filayen gidan Allahnmu. Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne; rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau. Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa, Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja. Na san cewa Ubangiji yana da girma, cewa shugabanmu ya fi dukan alloli girma. Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu. Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya; yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa. Ya kashe ’ya’yan fari na Masar, ’ya’yan fari na mutane da na dabbobi. Ya aiko da alamu da abubuwan banmamaki a tsirkiyarku, ya Masar, a kan Fir’auna da kuma dukan bayinsa. Ya bugi al’ummai masu yawa ya kuma karkashe manyan sarakuna, Sihon sarkin Amoriyawa, Og sarkin Bashan da kuma dukan sarakunan Kan’ana, ya kuma ba da ƙasarsa kamar abin gādo, abin gādo ga mutanensa Isra’ila. Sunanka, ya Ubangiji, dawwammame ne har abada, sanin da aka yi maka, ya Ubangiji, yana nan cikin dukan zamanai. Gama Ubangiji zai nuna cewa mutanensa ba su da laifi ya kuma ji tausayin bayinsa. Gumakan al’ummai azurfa ne da zinariya, da hannuwan mutane suka yi. Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani; suna da kunnuwa, amma ba sa ji, ba kuwa numfashi a bakunansu. Waɗanda suka yi su za su zama kamar su, haka kuma zai zama da dukan waɗanda suke dogara gare su. Ya gidan Isra’ila, yabi Ubangiji; Ya gidan Haruna, yabi Ubangiji; Ya gidan Lawi, yabi Ubangiji; ku da kuke tsoronsa, yabi Ubangiji. Yabo ya tabbata ga Ubangiji daga Sihiyona, gare shi wanda yake zama a Urushalima. Yabi Ubangiji. Zabura 136 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ku yi godiya ga Allahn alloli. Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji. Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu Ƙaunarsa madawwamiya ce. Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko; Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku; Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ya buge manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya karkashe manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Sihon sarkin Amoriyawa Ƙaunarsa madawwamiya ce. Da kuma Og sarkin Bashan, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya kuma ba da ƙasarsu gādo, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Gādo ga bawansa Isra’ila; Ƙaunarsa madawwamiya ce. Shi wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ya kuma ’yantar da mu daga abokan gābanmu, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda kuma ke ba da abinci ga kowace halitta. Ƙaunarsa madawwamiya ce. Ku yi godiya ga Allah na sama. Ƙaunarsa madawwamiya ce. Zabura 137 A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona. A can a kan rassan itatuwa muka rataye garayunmu, gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!” Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji a baƙuwar ƙasa? In na manta da ke, ya Urushalima, bari hannuna na dama manta da iyawarsa. Bari harshena yă manne wa rufin bakina in ban tuna da ke ba, in ban so Urushalima farin cikin mafi girma ba. Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi a ranar da Urushalima ta fāɗi. Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta, A ragargaza ta har tushenta!” Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka, mai farin ciki ne wanda ya sāka miki saboda abin da kika yi mana, shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu. Zabura 138 Ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; a gaban “alloli” zan rera yabo. Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki zan kuma yabi sunanka saboda ƙaunarka da amincinka, saboda ka ɗaukaka a bisa kome sunanka da kuma maganarka. Sa’ad da na kira, ka amsa mini; ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni. Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji, sa’ad da suka ji maganganun bakinka. Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji, gama ɗaukakar Ubangiji da girma take. Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu, amma tun da nesa ya san masu girman kai. Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala, kana kiyaye raina; ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana, da hannunka na dama ka cece ni. Ubangiji zai cika manufarsa a kaina; ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada, kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka. Zabura 139 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni. Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa. Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina. Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji. Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina. Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana, ya fi ƙarfi in gane. Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan gudu in tafi daga gabanka? In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can. In na tashi a fikafikan safiya, in na sauka a gefe mai nisa na teku, can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam. In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni haske kuma zai zama dare kewaye da ni,” duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba; dare zai haskaka kamar rana, gama duhu ya yi kamar haske gare ka. Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata. Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai. Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba sa’ad da aka yi ni asirce. Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya. Idanunka sun ga jikina marar fasali; dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka kafin ɗayansu yă kasance. Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah! Yawansu ba su da iyaka! A ce zan iya ƙirgansu, za su fi yashin teku yawa. Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu. Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah! Ku rabu da ni, ku masu kisankai! Suna magana game da kai da mugun nufi; maƙiyanka suna ɗaukan sunanka a banza. Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji, ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba? Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai; na ɗauke su abokan gābana. Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata; ka gwada ni ka kuma san damuwata. Duba ko akwai wani laifi a cikina, ka bishe ni a madawwamiyar hanya. Zabura 140 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici, masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu suna kuma kawo yaƙi kullum. Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu. Masu girman kai sun sa mini tarko; sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu sun kuma shirya mini tarko a hanyata. Sela Ya Ubangiji, na ce maka, “Kai ne Allahna.” Ka ji kukata ta neman jinƙai, ya Ubangiji. Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi, wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi. Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji; kada ka bar shirinsu su yi nasara, in ba haka ba za su yi fariya. Sela Bari kawunan waɗanda suka kewaye ni su rufu da masifun da leɓunansu suka jawo. Bari garwashin wuta yă zubo a kansu; bari a jefar da su cikin wuta, cikin rami mai zurfi, kada su sāke tashi. Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar; bari masifa ta farauci mutane masu rikici. Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci yana kuma yi wa mabukata adalci. Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka. Zabura 141 Zabura ta Dawuda. Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira. Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa; bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma. Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana. Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu, ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka tare da mutane masu aikata mugunta; kada ka bari in ci abincinsu. Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne; bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina. Kaina ba zai ƙi shi ba, duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka. Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne. Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa, haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.” Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka; a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa. Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini, daga tarkon da mugaye suka sa. Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu, amma bari ni in zo in wuce lafiya. Zabura 142 Maskil ne142.0 Kan maganar, mai yiwuwa kalmar waƙa ce. ta Dawuda. Sa’ad da yake cikin kogo. Addu’a ce. Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji; na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai. Na kawo gunagunina a gabansa; a gabansa na faɗa wahalata. Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina, kai ne wanda ya san hanyata. A hanyar da nake tafiya mutane sun kafa mini tarko. Duba ta damata ka gani; babu wanda ya kula da ni. Ba ni da mafaka; babu wanda ya kula da raina. Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Na ce, “Kai ne mafakata, rabona a ƙasar masu rai.” Ka saurari kukata, gama ina cikin matsananciyar bukata; ka cece ni daga waɗanda suke fafarata, gama sun fi ni ƙarfi sosai. Ka ’yantar da ni daga kurkuku, don in yabi sunanka. Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni saboda alherinka gare ni. Zabura 143 Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, ka ji addu’ata, ka saurari kukata don neman jinƙai; cikin amincinka da adalcinka ka amsa mini. Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a, gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka. Abokin gāba yana fafarata, ya murƙushe ni har ƙasa; ya sa ina zama a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu tun tuni. Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina zuciyata ta damu ƙwarai. Na tuna da kwanakin baya na yi tunani a kan dukan ayyukanka na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi. Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji; ƙarfina ya ƙare. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami. Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa, gama na sa zuciyata a gare ka. Ka nuna mini hanyar da zan bi, gama a gare ka na miƙa raina. Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka. Ka koya mini in yi nufinka, gama kai ne Allahna; bari nagarin Ruhunka yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina; a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala. A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana; ka hallaka dukan maƙiyana, gama ni bawanka ne. Zabura 144 Ta Dawuda. Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana don yaƙi, yatsotsina don faɗa. Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata, katangata da mai cetona, garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi, wanda ya sa mutane a ƙarƙashina. Ya Ubangiji, wane ne mutum da ka kula da shi, ɗan mutum da har za ka yi tunaninsa? Mutum yana kama da numfashi; kwanakinsa suna wucewa kamar inuwa. Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko; ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi. Ka aiko da walƙiya ka watsar da abokan gāba; ka karɓa kibiyoyinka ka sa su gudu. Ka miƙa hannunka daga bisa; ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga manyan ruwaye, daga hannuwan baƙi waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne. Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah; a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi, ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara, wanda ya cece bawansa Dawuda. Daga takobin kisa. Ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga hannuwan baƙi waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne. Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su, ’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai da sassaƙa don adon fada. Rumbunanmu za su cika da kowane irin tanadi. Tumakinmu za su ƙaru ninki dubu, ninki dubu goma-goma a filayenmu; shanunmu za su ja kaya masu nauyi.144.14 Ko kuwa manyanmu za su kahu daram Ba za a sami tashin hankali a katangarmu ba, ba zuwan zaman bauta, ba jin kukan damuwa a titunanmu. Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka; masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji. Zabura 145145 Wannan Zabura waƙa ce, ayoyin waɗanda suka (haɗa da aya 13b) sun fara da irin harufa ɗaya bayan ɗaya na Ibraniyanci. Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda. Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin. Kowace rana zan yabe ka in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin. Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum. Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara; za su yi magana game da manyan ayyukanka. Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja, zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki. Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro, zan kuma yi shelar manyan ayyukanka. Za su yi bikin yalwar alherinka suka kuma rera adalcinka da farin ciki. Ubangiji mai alheri da kuma tausayi, mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna. Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi. Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka. Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka za su kuma yi zancen ikonka, saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka da ɗaukakar darajar mulkinka. Mulkinka madawwamin mulki ne, sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai. Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi. Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa. Idanun kowa yana dogara gare ka, kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace. Ka buɗe hannunka ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai. Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi. Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya. Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su. Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa, amma dukan mugaye zai hallaka su. Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji. Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki har abada abadin. Zabura 146 Yabi Ubangiji.146.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 10. Yabi Ubangiji, ya raina. Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina; zan rera yabo ga Allahna muddin raina. Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna, ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto. Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa; a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza. Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa. Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada. Yakan biya bukatun mutanen da aka danne ya kuma ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku, Ubangiji yakan ba wa makafi ido, Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa, Ubangiji yana ƙaunar masu adalci. Ubangiji yana tsaron baƙi yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa, amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye. Ubangiji yana mulki har abada, Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani. Yabi Ubangiji. Zabura 147 Yabi Ubangiji.147.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 20. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi! Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta. Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu. Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna. Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka. Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa. Rera wa Ubangiji waƙar godiya; ku kada garaya ga Allahnmu. Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai. Yakan tanada wa shanu abinci da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira. Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki, balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum; Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa, waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa. Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona. Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki. Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau. Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri. Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka. Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko? Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su; yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu. Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila. Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji. Zabura 148 Yabi Ubangiji.148.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 14. Yabi Ubangiji daga sammai, yabe shi a bisa sammai. Yabe shi, dukanku mala’ikunsa, yabe shi, dukanku rundunarsa na sama. Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa. Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su. Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba. Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku, walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa, ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul, namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya, sarakunan duniya da dukan al’ummai, ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya, samari da ’yan mata, tsofaffi da yara. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka; darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai. Ya tayar wa mutanensa ƙaho,148.14 Ƙaho a nan na nuna wani mai ƙarfi, wato, sarki. yabon dukan tsarkakansa, na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa. Yabi Ubangiji. Zabura 149 Yabi Ubangiji.149.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 9. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka. Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu. Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya. Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto. Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu. Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu, don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane, don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe, don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji. Zabura 150 Yabi Ubangiji.150.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 6. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa. Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa. Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo, yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa, yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai. Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.