- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Karin Magana Karin Magana Karin Magana K Mag Karin Magana Gabatarwa, manufa da kuma kan magana Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila. Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo; don ganewa kalmomi masu zurfi; don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali, kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace; don sa marar azanci yă yi hankali, yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa, bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu, bari masu tunani kuma su sami jagora, don su fahimci karin magana da kuma misalai, kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima. Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye1.7 Kalmomin Ibraniyancin da aka rubuta wawa a cikin Littafi Karin Magana, da kuma ko’ina a cikin Tsohon Alkawari sau da yawa, yana nufin wani wanda ya rasa cikakken ɗa’a ne. sun rena hikima da horo. Gargaɗi don a rungumi hikima Jan kunne game da jaraba Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka. Za su zama kayan ado don su inganta ka da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado. Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda. In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi; mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami; za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima; ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato” ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu; gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi, suna saurin yin kisankai. Ba shi da amfani a kafa tarko a idanun dukan tsuntsaye! Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko; ba sa kama kome, sai rayukansu! Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau; ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu. Jan kunne game da ƙin hikima Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi, tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a; tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu,1.21 Da Ibraniyanci; Seftuwajin / a bisa katanga tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari. “Har yaushe ku da kuke marasa azanci1.22 Kalmar Ibraniyancin da aka rubuta marar azanci a cikin Littafin Kari Magana gaba ɗaya tana nufin marar ɗa’a da kuma wanda yana aikata mugunta ne. za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi? Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina. Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna, da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba, Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku, sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba, da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata, za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu. Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su, rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su; amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.” Ribar ɗa’ar hikima Ɗana, in ka yarda da kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka, kana kasa kunne ga abin da yake na hikima, kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi, in kuma ka kira ga tsinkaya ka kuma kira da ƙarfi don ganewa, in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya, to, za ka gane tsoron Ubangiji ka kuma sami sanin Allah. Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito. Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya, shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi, gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata yana kuma tsare hanyar amintattunsa. Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau. Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai. Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora. Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci, waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu, waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci, waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu. Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta, wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.2.17 Ko kuwa alkawarin Allahnta Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu. Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai. Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai. Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar, marasa laifi kuma za su kasance a cikinta; amma za a fid da mugaye daga ƙasar, za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta. Ƙarin ribar hikima Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka, gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata. Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka. Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane. Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka; cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.3.6 Ko kuwa zai nuna maka hanyoyi Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta. Wannan zai ba wa jikinka lafiya yă kuma adana ƙasusuwanka. Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka; ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi. Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa, domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi. Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi, gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya. Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita. Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma. Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi, dukan hanyoyinta kuma salama ne. Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta; waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka. Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya, ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke; ta wurin sani aka rarraba zurfafa, gizagizai kuma suka zubo raɓa. Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira, kada ka bar su su rabu da kai; za su zama rai a gare ka, abin adon da zai gyara wuyanka. Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya, ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba; sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi. Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya ko lalacin da yakan auka wa mugaye, gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko. Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka. Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu. Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai. Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba. Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu. Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi. La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye, amma yakan albarkaci gidan adali. Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri. Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya. Hikima ce mafi girma duka Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi. Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata. Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata, ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu. Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su. Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai. Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi. Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka. Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.” Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa. Na bishe ka a hanyar hikima na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi. Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe; sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba. Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce; ka tsare shi sosai, gama ranka ne. Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye. Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka. Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani. Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su. Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka. Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne; ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe. Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa, ka saurara sosai ga kalmomina. Kada ka bari su rabu da kai, ka kiyaye su a cikin zuciyarka; gama rai ne ga waɗanda suke nemansu da kuma lafiya ga dukan jikin mutum. Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka, gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne. Ka kau da muguwar magana daga bakinka; ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka. Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka. Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai. Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta. Gargaɗi a kan zina Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata ka saurara da kyau ga kalmomin basirata, don ka ci gaba da yin kome daidai leɓunanka za su adana sani. Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma, maganarta tana da sulɓi fiye da mai; amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya, mai ci kamar takobi mai kaifi biyu. Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa; sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari. Ba ta wani tunanin rayuwa; hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa. Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta, don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu da kuma shekarunku ga wani marar imani, don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam. A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi, sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye. Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara! Ban yi biyayya da malamaina ba ko in saurari masu koyar da ni. Na zo gab da hallaka gaba ɗaya a tsakiyar dukan taron.” Ku sha ruwa daga tankinku, ruwa mai gudu daga rijiyarku. In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje, rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a? Bari su zama naka kaɗai, don kada ka raba da baƙi. Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka, bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka. Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum. Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali? Don me za ka rungume matar wani? Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji, yana kuma lura da dukan hanyoyinsa. Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi; igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan. Zai mutu saboda rashin ɗa’a yawan wawancinsa zai sa yă kauce. Gargaɗi a kan wawanci Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi, in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani, in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko, to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka! Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma. Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko. Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima! Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki, duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi. Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku? Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi. Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki, wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa, wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi, duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi, zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta, mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa. Gargaɗi a kan zina Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka. Ka ɗaura su a zuciyarka har abada; ka ɗaura su kewaye da wuyanka. Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana. Gama waɗannan umarnai fitila ne, wannan koyarwa haske ne, kuma gyare-gyaren horo hanyar rayuwa ce, suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a daga sulɓin harshen mace marar aminci. Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta. Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta, mazinaciya kuma takan farauci ranka. Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa ba tare da rigunansa sun ƙone ba? Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba? Haka yake da wanda ya kwana da matar wani; babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci. Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa. Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa. Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali; duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne. Dūka da kunya ne za su zama rabonsa, kuma kunyarsa za tă dawwama. Gama kishi kan tā da hasalar miji, kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa. Ba zai karɓi duk wata biya ba; zai ƙi cin hanci, kome yawansu. Gargaɗi A kan mazinaciya Ɗana, ka kiyaye kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka. Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu; ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka. Ka daure su a yatsotsinka; ka rubuta su a allon zuciyarka. Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,” ka kuma kira fahimi danginka; za su kiyaye ka daga mazinaciya, daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali. A tagar gidana na leƙa ta labule mai rammuka. Sai na gani a cikin marasa azanci, na lura a cikin samari, wani matashi wanda ba shi da hankali. Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta, yana tafiya a gefen wajen gidanta da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa, yayinda duhun dare yana farawa. Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi, saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi. (Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya, ƙafafunta ba sa zama a gida; wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali, tana yawo a kowace kusurwa.) Sai ta kama shi ta rungume shi da duban soyayya a fuskarta ta ce, “Ina da hadaya ta salama a gida; yau zan cika alkawarina. Saboda haka na fito don in sadu da kai; na neme ka na kuma same ka! Na lulluɓe gadona da lili masu launi dabam-dabam daga Masar. Na yayyafa turare a gadona da mur, aloyes da kuma kirfa. Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe; bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna! Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa. Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.” Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta. Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa. Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta. Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa. Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira. Kiran hikima Hikima ba ta yin kira ne? Fahimi ba ya tā da muryarsa ne? A ƙwanƙoli a kan hanya, inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta; kusa da ƙofofin shiga cikin birni, a mashigai, ta tā da murya, “Gare ku, ya mutane, nake kira; na tā da muryata ga dukan ’yan adam. Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali; ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi. Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa; na buɗe leɓunana don in faɗa abin da yake daidai. Bakina yana magana abin da yake gaskiya, gama leɓunana sun ƙi mugunta. Dukan kalmomin bakina suna da adalci; babu waninsu da ya karkace ko kuwa ƙarya ne. Ga mai tunani dukansu daidai ne; ba su da laifi ga waɗanda suke da sani. Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa, sani a maimakon zinariya zalla, gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja, kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita. “Ni, hikima, ina zama tare da hankali; ina da sani da iya rarrabewa. Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana. Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne; ina da fahimi da kuma iko. Ta wurina sarakuna suke mulki masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci; ta wurina sarakuna suke mulki, da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya. Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, kuma waɗanda suke nemana sukan same ni. Tare da ni akwai wadata da girmamawa, dukiya da wadata masu dawwama. ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla; amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau. Ina tafiya a hanyar adalci, a kan hanyoyin gaskiya, ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata ina sa wuraren ajiyarsu su cika. Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa, kafin ayyukansa na tuntuni; an naɗa ni tun fil azal, daga farko, kafin duniya ta kasance. Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni, sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa; kafin a kafa duwatsu a wurarensu, kafin tuddai ma, an haife ni, kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya. Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa, sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram, sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya. A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa. Na cika da murna kowace rana, kullum ina farin ciki a gabansa, ina farin ciki da dukan duniyarsa ina murna da ’yan adam. “Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina. Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima; kada ku ƙyale ta. Mai albarka ne wanda ya saurare ni; yana tsaro kullum a ƙofofina, yana jira a ƙofar shigata. Gama duk wanda ya same ni ya sami rai zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji. Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa; dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.” Gayyatar hikima da gayyatar wawanci Hikima ta gina gidanta; ta yi ginshiƙansa bakwai. Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta; ta kuma shirya teburinta. Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira daga wurare masu tsayi na birnin. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!” Tana faɗa wa marasa hankali. “Ku zo, ku ci abincina da ruwan inabin da na gauraye. Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi. “Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci. Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka; ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka. Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima; ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa. “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne. Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa, za a kuwa ƙara wa ranka shekaru. In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada; in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala.” Wawancin mace a bayyane yake; ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani. Takan zauna a ƙofar gidanta, a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni, tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali. “Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!” Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba. Karin maganar Solomon Karin maganar Solomon. Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki. Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa. Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu. Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya. Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya. Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani, amma rikici kan sha bakin mugu. Tunawa da mai adalci albarka ne amma sunan mugu zai ruɓe. Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni amma surutun wawa kan kai ga lalaci. Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi. Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki surutun wawa kuma kan zo da lalaci. Bakin adali maɓulɓulan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa. Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi. Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi, amma bulala domin bayan marasa azanci ne. Mai hikima kan yi ajiyar sani, amma bakin wawa kan gayyaci lalaci. Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci. Hakkin adalai kan kawo musu rai, amma albashin mugaye kan kawo musu hukunci. Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai, amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce. Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne. Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne. Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani. Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci. Albarkar Ubangiji kan kawo wadata, ba ya kuma ƙara wahala a kai. Wawa yakan ji daɗi halin mugunta, amma mutum mai fahimi kan ji daɗin hikima. Abin da mugu ke tsoro shi ne zai same shi; abin da adali ke bukata yakan sami biyan bukata. Sa’ad da hadiri ya taso, yakan watsar da mugaye, amma adalai za su tsaya daram har abada. Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi. Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai, amma akan gajartar da shekarun mugaye. Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki, amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome. Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta. Ba za a taɓa tumɓuke masu adalci ba, amma mugaye ba za su ci gaba da kasance a ƙasar ba. Bakin adalai kan fitar da hikima, amma za a dakatar da mugun harshe. Leɓunan adalai sun san abin da ya dace, amma bakunan mugaye sun san abin da yake mugu ne kawai. Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa. Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo, amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai. Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su, amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi. Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi, amma adalci kan yi ceto daga mutuwa. Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu, amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu. Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su, amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace. Sa’ad da mugu ya mutu, sa zuciyarsa kan hallaka; dukan abin da ya sa zuciya daga ikonsa ba ya amfana kome. Akan kuɓutar da mai adalci daga wahala, sai ta dawo wa mugu a maimako. Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta. Sa’ad da adali ya yi nasara, birnin kan yi farin ciki; sa’ad da mugu ya hallaka, akwai sowa ta farin ciki. Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita, amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin. Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci, amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa. Gulma yakan lalace yarda, amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri. Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara. Duk wanda ya ɗauki lamunin wani tabbatacce zai sha wahala, amma duk wanda ya ƙi ya sa hannu a ɗaukar lamuni ba ruwansa. Mace mai hankali na samu bangirma, amma azzalumai za su sami dukiya. Mutumin kirki kan ribance kansa, amma mugu kan kawo wa kansa wahala. Mugun mutum kan sami albashin ƙarya amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce. Mutum mai adalci da gaske yakan sami rai, amma shi da ya duƙufa ga aikata mugunta kan tarar da mutuwarsa. Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi. Ka tabbata da wannan. Mugaye ba za su tafi babu hukunci ba, amma waɗanda suke masu adalci za su tafi babu hukunci. Kamar zinariya a hancin alade haka kyan mace wadda ba ta da hankali. Sha’awar adalai kan ƙare kawai a aikata alheri, amma sa zuciyar mugaye kan ƙarasa kawai a fushi. Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye; wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci. Mutum mai kyauta zai azurta; shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi. Mutane kan la’anci mai ɓoye hatsi yana jira ya yi tsada, amma albarka kan zauna a kan wanda yake niyya ya sayar. Duk mai nema alheri kan sami alheri, amma mugu kan zo wa wanda yake nemansa. Duk wanda ya dogara ga arzikinsa zai fāɗi, amma adali zai yi nasara kamar koren ganye. Duk wanda ya kawo wahala wa iyalinsa zai gāji iska kawai, kuma wawa zai zama bawan masu hikima. ’Ya’yan itacen adali itacen rai ne, kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne. In masu adalci sun sami abin da ya dace da su a duniya, yaya zai zama ga marasa sanin Allah da kuma masu zunubi! Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani, amma duk mai ƙin gyara wawa ne. Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji, amma Ubangiji yakan hukunta mai son yin wayo. Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta, amma ba za a tumɓuke adali ba. Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne, amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa. Shirye-shiryen masu adalci daidai ne, amma shawarar mugaye ruɗu ne. Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai, amma jawabin masu aikata gaskiya kan kuɓutar da su. Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu, amma gidan masu adalci kan tsaya daram. Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa, amma mutane marasa azanci akan rena su. Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa da ka mai da kanka kai wani ne alhali kuwa ba ka da abinci. Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa, amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta. Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne. Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane, amma saiwar masu adalci kan haɓaka. Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi, amma adali kan kuɓuta daga wahala. Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau tabbatacce yadda aikin hannuwansa suke ba shi lada. Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara. Wawa kan nuna fushinsa nan take, amma mai la’akari kan ƙyale zargi. Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya, amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne. Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa. Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada, amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai. Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki. Ba wani lahanin da zai sami masu adalci, amma mugaye suna da nasu cike da wahala. Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya. Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa, amma zuciyar wawa kan yi ta tallar wawanci. Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta. Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum, amma maganar alheri kan faranta masa rai. Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa. Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta, amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci. A hanyar adalci akwai rai; a wannan hanya akwai rashin mutuwa. Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa, amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi. Daga abin da ya fito leɓunan mutum ne mutum kan ji daɗin abubuwa masu kyau, amma marar aminci yakan ƙosa ya tā-da-na-zaune-tsaye. Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa, amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci. Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai. Adali yana ƙin abin da yake ƙarya, amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci. Adalci yakan lura da mutum mai mutunci, amma mugunta takan sha kan mai zunubi. Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome, wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai. Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa, amma matalauci ba ya jin barazana. Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai, amma fitilar mugaye mutuwa take. Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara. Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa. Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo, amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai. Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa, amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada. Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne, mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa. Fahimta mai kyau kan sami tagomashi, amma hanyar marar aminci tana da wuya. Kowane mai azanci yakan nuna sani, amma wawa yakan yi tallen wawancinsa. Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala, amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa. Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya, amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma. Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai, amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta. Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima, amma abokin wawaye zai yi fama da lahani. Rashin sa’a kan fafare mai zunubi, amma wadata ce ladar adali. Mutumin kirki kan bar gādo wa ’ya’ya ’ya’yansa, amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci. Gonar matalauci za tă iya ba da abinci a yalwace, amma rashin adalci kan share shi tas. Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba, amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi. Masu adalci sukan ci isashen abinci, amma cikin mugaye na fama da yunwa. Mace mai hikima kan gina gidanta, amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa. Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji, amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi. Maganar wawa kan kawo sanda a bayansa, amma leɓunan masu hikima kan tsare su. Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome, amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito. Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu, amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi. Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome, amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira. Ka guji wawa, gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba. Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu, amma wautar wawaye ruɗu ne. Wawaye kan yi ba’a a gyaran zunubi, amma fatan alheri yana samuwa a cikin masu aikata gaskiya. Kowace zuciya ta san ɓacin ranta, kuma babu wani dabam da zai yi rabon jin daɗinsa. Za a rushe gidan mugu, amma tentin mai aikata gaskiya zai haɓaka. Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa. Ko cikin dariya zuciya takan yi ciwo, kuma farin ciki kan iya ƙarasa a baƙin ciki. Marasa bangaskiya za su sami sakamako cikakke saboda hanyoyinsu, kuma mutumin kirki zai sami lada saboda nasa. Marar azanci kan gaskata kome, amma mai la’akari kan yi tunani game da matakinsa. Mai hikima kan ji tsoron Ubangiji ya kuma guji mugunta, amma wawa yana da girman kai yakan yi kome da garaje. Mutum mai saurin fushi yakan yi ayyukan wauta, akan kuma ƙi mai son nuna wayo. Marar azanci kan gāji wauta, amma mai la’akari kan sami rawanin sani. Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki, mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai. Maƙwabta sukan gudu daga matalauta, amma masu arziki suna da abokai da yawa. Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata. Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci. Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai. Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu, amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai. Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka, amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne. Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka, kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka. Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai yakan juye mutum daga tarkon mutuwa. Yawan mutane shi ne ɗaukakar sarki, amma in ba tare da mabiya ba sarki ba kome ba ne. Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili. Zuciya mai salama kan ba jiki rai, amma kishi kan sa ƙasusuwa su yi ciwo. Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne. Sa’ad bala’i ya auku, mugaye kan fāɗi, amma ko a mutuwa masu adalci suna da mafaka. Hikima tana a zuciyar mai azanci, kuma ko a cikin wawaye takan sa a santa. Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane. Sarki yakan yi murna a kan bawa mai hikima, amma bawa marar kunya kan jawo fushinsa. Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi. Harshen mai hikima kan yi zance mai kyau a kan sani, amma bakin wawa kan fitar da wauta. Idanun Ubangiji suna a ko’ina, suna lura da masu aikata mugunta da masu aikata alheri. Harshen da ya kawo warkarwa shi ne itacen rai, amma harshe mai ƙarya kan ragargaza zuciya. Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa, amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci. Gidan adali yana da dukiya mai yawa, amma albashin mugaye kan kawo musu wahala. Leɓunan masu hikima sukan baza sani; ba haka zukatan wawaye suke ba. Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye, amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi. Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci. Horo mai tsanani yana jiran duk wanda ya bar hanya; wanda ya ƙi gyara zai mutu. Mutuwa da Hallaka suna nan a fili a gaban Ubangiji, balle fa zukatan mutane! Mai yin ba’a yakan ƙi gyara; ba zai nemi shawara mai hikima ba. Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske, amma ciwon zuciya kan ragargaza rai. Zuciya mai la’akari kan nemi sani, amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi. Dukan kwanakin mutumin da ake danniya fama yake yi, amma zuciya mai farin ciki yana yin biki kullum. Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala. Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take. Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa. An tare hanyar rago da ƙayayyuwa, amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce. Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa, amma wawa yakan rena mahaifiyarsa. Wauta kan sa mutum marar azanci ya yi farin ciki, amma mai basira kan kiyaye abin da yake yi daidai. Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara. Mutum yakan yi farin ciki a ba da amsar da take daidai, kuma ina misali a yi magana a lokacin da ya dace! Hanyar rai na yin jagora ya haura wa masu hikima don ta kiyaye shi daga gangarawa zuwa kabari. Ubangiji yakan rushe gidan mai girman kai amma yakan kiyaye iyakokin gwauruwa daidai. Ubangiji yana ƙyamar tunanin mugaye, amma waɗanda suke da tunani masu tsabta yakan ji daɗinsu. Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa, amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu. Zuciyar mai adalci takan auna amsoshinta, amma bakin mugu yakan fitar da mugunta. Ubangiji yana nesa da mugaye amma yakan ji addu’ar adalai. Fuska mai fara’a takan kawo farin ciki ga zuciya, kuma labari mai daɗi na kawo lafiya ga ƙasusuwa. Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba. Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan, amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira. Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima, kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa. Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke, amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo. Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi, amma Ubangiji yakan auna manufofi. Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara. Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa, har ma da mugaye domin ranar masifa. Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba. Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi; ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta. Sa’ad da hanyoyin mutum sun gamshi Ubangiji, yakan sa abokan gāban mutumin ma su zauna lafiya da shi. Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya. ’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa. Leɓunan sarki kan yi magana kamar ta wurin ikon Allah, kuma bai kamata bakinsa ya yi kuskure a yanke shari’a ba. Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne; dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne. Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau, gama an kafa kujerar sarauta ta wurin adalci ne. Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya; sukan darjanta mutumin da yake faɗin gaskiya. Fushin sarki ɗan saƙon mutuwa ne, amma mai hikima yakan faranta masa rai. Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan; tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara. Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya, ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa! Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta; duk wanda yake lura da hanyarsa yakan lura da ransa. Girmankai yakan zo kafin hallaka, girman kai yakan zo kafin fāɗuwa. Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu sauƙinkai, da ka raba ganima da masu girman kai. Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara, kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji. Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai, kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni. Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi, amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye. Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa, kuma leɓunansa kan inganta umarni. Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma, mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa. Akwai hanyar da ta yi kamar daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa. Marmarin cin abinci yakan yi wa ɗan ƙodago aiki; yunwarsa kan sa ya ci gaba. Mutumin banza yakan ƙulla mugunta, kuma jawabinsa yana kama da wuta mai ƙuna. Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa. Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau. Duk wanda ya ƙyifce da idonsa yana ƙulla maƙarƙashiya ce; duk wanda ya murguɗa leɓunansa yana niyya aikata mugunta ke nan. Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci. Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi, ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane. Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne. Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai. Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya. Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi. Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne; duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi. Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu. Leɓunan basira ba su dace da wawa ba, ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya! Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi; ko’ina ya juye, yakan yi nasara. Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa. Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari. Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah; za a aika manzo mutuwa a kansu. Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa. In mutum ya sāka alheri da mugunta, mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba. Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke. Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu. Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa, da yake ba shi da sha’awar samun hikima? Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi. Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci. Duk mai son faɗa yana son zunubi, duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka. Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba; duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala. Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki babu farin ciki ga mahaifin wawa. Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa. Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce don yă lalace yin adalci. Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima, amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya. Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa da ɓacin rai ga wanda ya haife shi. Ba shi da kyau a hukunta marar laifi, ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu. Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne. Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa. Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai; yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai. Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa. Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo, haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo. Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye, amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu. Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri ko ka hana wa marar laifi adalci. Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa, bakinsa kuma kan gayyaci dūka. Bakin wawa lalatar da kansa yake yi leɓunansa kuma tarko ne ga ransa. Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke; sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum. Wanda yake ragwanci a aikinsa ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa. Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi; masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya. Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga; suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba. Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai, amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa. Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara, wannan wauta ce da kuma abin kunya. Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo, amma in ya karai, to, tasa ta ƙare. Zuciya mai la’akari kan nemi sani; kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya. Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa yakan kuma kai shi a gaban babban mutum. Wanda ya fara mai da jawabi yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai wani ya fito ya yi masa tambaya tukuna. Jefa ƙuri’a kan daidaita tsakanin masu faɗa ta kuma ajiye masu faɗan a rabe. Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada. Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika; girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi. Harshe yana da ikon rai da mutuwa, kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa. Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji. Matalauci kan yi roƙo da taushi, amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya. Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa. Gara matalauci wanda yake marar laifi da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne. Ba shi da kyau ka kasance da niyya babu sani, ko ka kasance mai garaje ka ɓace hanya. Wautar mutum kan lalatar da ransa, duk da haka zuciyarsa kan ba wa Ubangiji laifi. Wadata kan kawo abokai da yawa, amma abokin matalauci kan bar shi. Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba. Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki, kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne. ’Yan’uwan matalauci sukan guje shi, balle abokansa, su ma za su guje shi. Ko da yake matalaucin yana binsu yana roƙo, ba zai sam su ba. Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa; duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba. Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka. Bai dace da wawa ya yi rayuwa cikin jin daɗi ba, haka ya fi muni bawa ya yi mulki a kan sarki! Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi. Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa. Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne, mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa. Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne, amma mace mai basira daga Ubangiji ne. Ragwanci kan jawo zurfin barci, mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa. Duk wanda ya bi umarnai kan tsare ransa, amma duk wanda ya ƙi binsu zai mutu. Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi. Ka hori ɗanka, gama yin haka akwai sa zuciya; kada ka goyi baya lalacewarsa. Dole mai zafin rai yă biya tara; in ka fisshe shi sau ɗaya, to, sai ka sāke yin haka. Ka kasa kunne ga shawara ka kuma yarda da umarni, a ƙarshe kuwa za ka yi hikima. Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum, amma manufar Ubangiji ce takan cika. Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa;19.22 Ko kuwa Haɗamar mutum ita ce rashin kunyarsa gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci. Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai. Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi. Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa! Ka bulale mai ba’a, marasa azanci kuwa za su yi la’akari; ka tsawata wa mai basira, zai kuwa ƙara sani. Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci. In ka daina jin umarni, ɗana, za ka kuwa kauce daga kalmomin sani. Mai shaidar da yake malalaci yana wa shari’a ba’a ne, bakin mugaye kuma na haɗiye mugunta. An shirya tara saboda masu ba’a ne, dūka kuma saboda bayan wawaye. Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne; duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne. Fushin sarki yana kama da rurin zaki; duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa. Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa. Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome. Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne, amma mutum mai basira yakan jawo su. Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne, amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda. Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi; masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa. Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a, yakan ga dukan mugunta da idanunsa. Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki; ni mai tsabta ne marar zunubi kuma”? Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka. Akan san ƙananan yara ta ayyukansu, ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta. Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani, Ubangiji ne ya yi su duka. Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci. “Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya; sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki. Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace, amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja. A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci. Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi, amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi. Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara; in kana yaƙi, ka sami bishewa. Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu. In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu. Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba. Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!” Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka. Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba, da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba. Ubangiji ne yake bi da matakan mutum, Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa? Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa. Sarki mai hikima yakan gane mugunta; ya hukunta su ba tausayi. Fitilar Ubangiji kan bincika zuciyar mutum takan bincika lamirinsa. Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya; ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe. Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu, furfura ita ce darajar tsofaffi. Naushi da rauni kan share mugunta, dūka kuma kan tsabtacce lamiri. A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne wanda yake bi da shi duk inda ya so. Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke, amma Ubangiji yakan auna zuciya. Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya. Girmankai da fariya, su ne fitilar mugaye, wannan kuwa zunubi ne! Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci. Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko. Rikicin mugaye zai yi gāba da su, gama sun ƙi su yi abin da yake daidai. Hanyar mai laifi karkatacciya ce, amma halin marar laifi sukan aikata gaskiya. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina. Mugun mutum yakan zaƙu ya aikata mugunta; maƙwabcinsa ba ya samun jinƙai daga gare shi. Sa’ad da aka hukunta mai ba’a marasa azanci suka yi wayo; sa’ad da aka yi wa mai hikima umarni yakan sami sani. Mai Adalci kan lura da gidan mugu kan kuma zama sanadin lalacin mugu. In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba. Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani. Sa’ad da aka yi adalci, yakan kawo farin ciki ga mai adalci amma fargaba ga masu aikata mugunta. Mutumin da ya kauce daga hanyar fahimi kan zo ga hutu a ƙungiyar matattu. Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci; duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba. Mugu kan zama abin fansa don adali, marar aminci kuma don mai aikata gaskiya. Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali. A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau, amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi. Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa. Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai. Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa. Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa; yana yin abubuwa da girmankai ainun. Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki. Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake. Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi! Mai ba da shaidar ƙarya zai hallaka, kuma duk wanda ya saurare shi zai hallaka har abada.21.28 Ko kuwa / amma kalmomin mai biyayya za su ci gaba da kasancewa Mugun mutum kan yi tsayin daka, amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi. Babu hikima, babu tunani, babu shirin da zai yi nasara a kan Ubangiji. Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne. An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa; tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya. Mawadaci da matalauci suna da abu guda. Ubangiji ne Mahaliccinsu duka. Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka, amma marar azanci kan yi ta tafiya yă kuma sha wahala. Sauƙinkai da tsoron Ubangiji sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai. A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko, amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu. Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi, kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba. Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne. Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala, za a kuma hallaka sandar fushinsa. Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta. Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare. Duk mai son tsabtar zuciya wanda kuma jawabinsa mai alheri ne zai zama aminin sarki. Idanun Ubangiji na lura da sani, amma yakan ƙi kalmomin marar aminci. Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!” Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi; duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki. Wauta tana da yawa a zuciyar yara, amma sandar horo zai kore ta nesa da su. Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta. Maganganu Masu Hikima Faɗi 1 Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima; ka yi amfani da abin da nake koyarwa, gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka. Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji, ina koya maka yau, har kai ma. Ban rubuta maka maganganu talatin ba, maganganun shawara da sani, ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai, saboda ka iya ba da amsa daidai ga duk wanda ya aike ka? Faɗi 2 Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a, gama Ubangiji zai yi magana dominsu zai kuwa washe waɗanda suka washe su. Faɗi 3 Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi, in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko. Faɗi 4 Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi; gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma. Faɗi 5 Kada ka matsar da shaidar kan iyakar da kakanninka suka kafa. Faɗi 6 Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa? Zai yi wa sarakuna hidima; ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba. Faɗi 7 Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki, ka lura sosai da abin da yake gabanka, ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka in kai mai ci da yawa ne. Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi gama wannan abinci ruɗu ne. Faɗi 8 Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa. Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa. Faɗi 9 Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi; gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin.23.7 Ko kuwa gama yadda yake tunani a cikinsa, haka yake; Ko kuwa gama yadda ya sa a bikin, haka yake Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai. Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza. Faɗi 10 Kada ka yi magana da wawa, gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a. Faɗi 11 Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā ko ka ɗiba gonar marayu, gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi; zai kuwa yi magana dominsu. Faɗi 12 Ka mai da hankali ga umarni ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani. Faɗi 13 Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba. Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa. Faɗi 14 Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce, to, zuciyata za tă yi murna; cikin cikina zai yi farin ciki in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai. Faɗi 15 Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi. Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba. Faɗi 16 Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima, ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai. Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci, gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki. Faɗi 17 Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa. Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; ka nemi hikima, horo da fahimi. Mahaifin adali yana da farin ciki sosai; duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa. Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki! Faɗi 18 Ɗana, ka ba ni zuciyarka bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina, gama karuwa rami ne mai zurfi mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce. Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza. Faɗi 19 Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu? Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi. Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro! A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa. Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa. Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa. Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?” Faɗi 20 Kada ka yi ƙyashin mugaye, kada ka yi sha’awar ƙungiyarsu; gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne. Faɗi 21 Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta; ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja. Faɗi 22 Mutum mai hikima yana da iko sosai, kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi; don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa. Faɗi 23 Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa. Faɗi 24 Duk mai ƙulla mugunta za a ɗauka shi mai kuta hargitsi ne. Makircin wawa zunubi ne, mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a. Faɗi 25 In ba ka da ƙarfi a lokacin wahala, ka tabbatar kai marar ƙarfi ne sosai! Ka kuɓutar da waɗanda ake ja zuwa inda za a kashe su; ka riƙe waɗanda suke tangaɗi zuwa wajen yanka. In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba? Faɗi 26 Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau; zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka. Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai; in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba. Faɗi 27 Kada ka kwanta kana fako kamar ɗan iska don ƙwace gidan adali, kada ka ƙwace masa wurin zama; gama ko da adali ya fāɗi sau bakwai, yakan tashi kuma, amma bala’i kan kwantar da mugaye. Faɗi 28 Kada ka yi dariya sa’ad da abokin gāba ya fāɗi; sa’ad da ya yi tuntuɓe, kada ka yi farin ciki, in ba haka ba in Ubangiji ya gani ba zai amince ba ya kuma juye fushinsa daga gare shi. Faɗi 29 Kada ka ji tsoro saboda masu mugunta ko ka yi ƙyashin mugaye, gama mugu ba shi da zuciya ta nan gaba, kuma fitilar mugaye za tă mutu. Faɗi 30 Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana, kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa, gama za a tura waɗannan biyu zuwa hallaka nan da nan, kuma wa ya sani irin bala’in da za su iya kawowa? Ƙarin maganganun hikima Waɗannan ma maganganun masu hikima ne, Nunan sonkai a shari’a ba shi da kyau. Duk wanda ya ce wa mai laifi, “Ba ka da laifi”, mutane za su la’ance shi al’umma kuma za tă ce ba a san shi ba. Amma zai zama da lafiya ga duk waɗanda suka hukunta masu laifi, kuma babban albarka zai zo a kansu. Amsa da take ta gaskiya tana kamar sumba a leɓuna. Ka gama aikinka ka kuma shirya gonakinka; bayan haka, ka gina gidanka. Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba, ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu. Kada ka ce, “Zan yi masa kamar yadda ya yi mini; zan rama abin da wannan mutum ya yi mini.” Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci; ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe. Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari. Ƙarin karin maganar Solomon Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara. Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne. Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi, haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika. Ka tace azurfa sai kayan su fito don maƙerin azurfa; ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci. Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki, kada kuma ka nemi wa kanka wuri a cikin manyan mutane; gara ya ce maka, “Ka hauro nan,” da a ƙasƙantar da kai a gaban wani mai makami. Abin da ka gani da idanunka kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya? In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama, kada ka tona asirin wani, in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba. Kalmar da aka faɗa daidai tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa. Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa. Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika; ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi. Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama haka mutumin da yake fariya a kan kyautan da ba ya bayarwa. Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki, magana mai hankali kan karye ƙashi. In ka sami zuma, ka sha isashe kawai, in ya yi yawa, za ka yi amai. Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka yawan ganinka zai sa ya ƙi ka. Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa. Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa haka yake ga mai dogara da marasa aminci a lokacin wahala. Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi, ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa, haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki. In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci; in yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa, Ubangiji kuma zai sāka maka. Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi. Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina. Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji haka yake da jin labari mai daɗi daga ƙasa mai nisa. Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace haka yake da mai adalci wanda ya miƙa wuya ga mugaye. Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa, haka ma ba shi da kyau ka nemi girma wa kanka. Kamar birni da katangarsa sun rushe haka yake da mutumin da ba ya iya danne fushinsa. Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa bai dace da wawa ba. Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya, haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take. Bulala don doki, linzami don jaki, sanda kuma don bayan wawaye! Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa. Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne. Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa. Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas haka karin magana yake a bakin wawa. Kamar ɗaura dutse a majajjawa haka yake da girmama wawa. Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu haka karin magana yake a bakin wawa. Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa. Kamar yadda kare kan koma ga amansa, haka wawa kan maimaita wautarsa. Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne. Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya, zaki mai faɗa yana yawo a tituna!” Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa, haka rago yake jujjuya a gadonsa. Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa. Rago yana gani yana da hikima fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu. Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa. Kamar yadda mahaukaci yake harbin cukwimai ko kibiyoyi masu dafi haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!” In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba. Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta, haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa. Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi; sukan gangara can cikin cikin mutum. Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba haka leɓuna masu mugun zuciya. Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa, amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi, gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa. Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya, duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro. In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki; in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa. Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai, daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna. Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba. Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba; wani dabam, ba leɓunanka ba. Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce, amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi. Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi? Gara tsawatawar da ake yi a fili da ƙaunar da ake yi a ɓoye. Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi! Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi. Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa haka yake da mutumin da ya bar gidansa. Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya, gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki. Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa. Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya; zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini. Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce, marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani. A karɓe rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci. In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe, za a ɗauka shi a matsayin la’ana. Mace mai fitina kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa; hana ta yana kamar yin ƙoƙari tsai da iska ne ko yin ƙoƙarin cafke mai a tafin hannunka. Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum. Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi. Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take, haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin. Mutuwa da Hallaka27.20 Da Ibraniyanci Sheol da Abaddon ba sa ƙoshi, haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu. Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba. Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka; domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara. Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai, gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki. Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata. Mugu yakan gudu ko babu wanda yake korarsa, amma adalai suna da ƙarfin hali kamar zaki. Sa’ad da ƙasa ta yi tayarwa, takan kasance da masu mulki da yawa, amma mai fahimi da sani kan mai da zaman lafiya. Mai mulkin da ya danne talakawa yana kama da ruwan saman da ya lalatar da hatsi. Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi, amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai. Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne. Duk wanda ya kiyaye doka ɗa ne mai la’akari, amma wanda yake abokantaka da masu zari yakan jawo wa mahaifinsa kunya. Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri. In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka ko addu’arsa ma abar ƙyama ce. Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta zai fāɗa cikin tarkonsa amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau. Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa, amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai. Sa’ad da adalai suka yi nasara, kowa yakan yi biki; amma sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya. Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai. Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah, amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala. Kamar rurin zaki ko sanɗar beyar haka mugun mutum mai mulki a kan mutane marasa ƙarfi yake. Mugu mai mulki ba shi da azanci, amma duk wanda yake ƙin ƙazamar riba yakan yi tsawon rai. Mutumin da laifin kisa ya yi ta damunsa zai zama mai gudu don tsoro har mutuwa; kada wani ya taimake shi. Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya, amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan. Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace, amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe. Mutum mai aminci zai cika da albarka, amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci. Nuna sonkai ba shi da kyau, duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa. Mai rowa yana alla-alla ya yi arziki bai san cewa talauci ne ke jiransa ba. Duk wanda ya tsawata wa wani mutum zai sami yabo a ƙarshe fiye da wanda yake mai daɗin baki. Duk wanda ya yi wa mahaifin ko mahaifiyarsa sata ya kuma ce, “Ai, ba laifi ba ne” abokin mai hallakarwa ne shi. Mai haɗama yakan jawo tā-da-na-zaune-tsaye, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai yi nasara. Duk mai dogara ga kansa wawa ne, amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya. Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba, amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa. Sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya; amma sa’ad da mugu ya hallaka, adali kan ci gaba cikin arziki da lafiya. Mutumin da ya ci gaba da taurinkai bayan an kwaɓe shi ba da daɗewa ba zai hallaka ba makawa. Sa’ad da masu adalci suke cin nasara, mutane kan yi farin ciki sa’ad da mugaye suke mulki, mutane kan yi nishi. Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa. Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar. Duk wanda yake wa maƙwabcinsa daɗin baki yana sa wa ƙafafunsa tarko ne. Mugun mutum tarko ne ta wurin zunubinsa, amma mai adalci zai iya rera ya kuma yi murna. Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa, amma mugaye ba su da wannan damuwa. Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi. In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa, wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba. Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya. Wawa yakan nuna fushinsa a fili, amma mai hikima kan kanne fushinsa. In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye. Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya. Ubangiji ne yake ba dukansu gani. In sarki yana hukunta talakawa da adalci kursiyinsa kullum zai kasance lafiya. Sandar gyara kan ba da hikima, amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa. Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa, amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane. Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama; zai ba ka farin cikin da kake so. Inda ba wahayi, mutane kan kangare; amma masu albarka ne waɗanda suke kiyaye doka. Ba a yi wa bawa gyara ta wurin magana kawai; ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba. Ka ga mutum mai yin magana da garaje? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi. In mutum ya yi wa bawansa shagwaɓa tun yana yaro, zai jawo baƙin ciki a ƙarshe. Mutum mai cika fushi yakan tā da faɗa, mai zafin rai kuma kan yi zunubai masu yawa. Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa. Duk wanda yake abokin ɓarawo abokin gāban kansa ne; yana jin sa yana ta rantsuwa, amma bai isa ya ce kome ba. Jin tsoron mutum tarko ne, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya. Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki, amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci. Masu adalci suna ƙyamar masu rashin gaskiya; mugaye sukan yi ƙyamar masu aikata gaskiya. Maganganun Agur Maganganun Agur ɗan Yake, magana ce horarriya.30.1 Ko kuwa Yake na Massa Wannan mutum ya furta wa Itiyel da kuma ga Ukal, “Ni ne mafi jahilci a cikin mutane; ba ni da fahimi irin na mutum. Ban koyi hikima ba, ba ni kuma da sani game da Mai Tsarkin nan, Wane ne ya taɓa haura zuwa sama ya dawo? Wane ne ya tattara iska a tafin hannuwansa? Wane ne ya nannaɗe ruwaye a cikin rigarsa? Wane ne ya kafa dukan iyakokin duniya? Mene ne sunansa, da kuma sunan ɗansa? Faɗa mini in ka sani! “Kowace maganar Allah ba ta da kuskure; shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi. Kada ka ƙara ga maganarsa, in ba haka ba zai tsawata maka ya kuma nuna kai maƙaryaci ne. “Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji; kada ka hana ni kafin in mutu. Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna. “Kada ka baza ƙarairayi game da bawa ga maigidansa, in ba haka ba, zai la’ance ka, za ka kuwa sha wahala a kan haka. “Akwai waɗanda sukan zagi mahaifinsu ba sa kuma sa wa mahaifiyarsu albarka; waɗanda sukan ɗauka su tsarkaka ne a ganinsu alhali kuwa ƙazamai ne su; waɗanda kullum idanunsu masu kallon reni ne, waɗanda kallon da suke yi na daurin gira ne; waɗanda haƙoransu takuba ne waɗanda kuma muƙamuƙansu tarin wuƙaƙe ne don su cinye matalauta daga duniya da kuma mabukata daga cikin mutane. “Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’ Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa, ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa, da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’ “Idon da yake yi wa mahaifi ba’a, wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya, hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido, ungulai za su cinye su. “Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu, yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace. “Ga yadda mazinaciya take yi. Takan ci ta share bakinta ta ce, ‘Ban yi wani abu marar kyau ba.’ “Akwai abubuwa uku da duniya kan yi rawan jiki, abubuwa huɗu da ba ta iya jurewa, bawan da ya zama sarki, wawan da ya ƙoshi da abinci, macen da ba a ƙauna wadda ta sami miji, da kuma baiwar da ta ɗauki matsayin uwargijiyarta. “Akwai abubuwa huɗu a duniya da suke ƙanana, duk da haka suna da hikima ƙwarai. Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani; remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai, duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu; fāra ba su da sarki, duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma; ana iya kama ƙadangare da hannu, duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna. “Akwai abubuwa uku da suke jan jiki da kuma taƙama a tafiyarsu abubuwa huɗu waɗanda suke kwarjini da taƙama a tafiyarsu, zaki mai ƙarfi a cikin namun jeji, wanda ba ya ratse wa kowa; zakara mai taƙama, da bunsuru, da kuma sarki mai sojoji kewaye da shi. “In ka yi wauta ka kuma ɗaukaka kanka, ko kuwa wani yana ƙulla maka mugunta, ka dāfa hannunka a bisa bakinka! Gama kamar yadda kaɗaɗɗen madara takan kawo mai, murɗa hanci kuma takan sa a yi haɓo, haka tsokanar fushi takan kawo faɗa.” Maganganun Sarki Lemuwel Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriya31.1 Ko kuwa na Lemuwel sarkin Massa, waɗanda mahaifiyarsa ta koya masa, “Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina! Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!31.2 Ko kuwa / amsar addu’o’ina Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata, ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna. “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel, ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi, ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa, don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta, su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu. A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala; bari su sha su manta da talaucinsu kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu. “Yi magana domin bebaye, domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu. Yi magana a kuma yi shari’ar adalci; a tsare hakkin talakawa da masu bukata.” Maganar ƙarshe. Mace Mai Halin Kirki 31.10 Ayoyi 10-31 suna bin juna layi-layi, kowace aya na farawa da harufan Ibraniyanci bi da bi. Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai. Mijinta yana da cikakken amincewa da ita kuma ba ya rasa wani abu mai daraja. Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakin ranta. Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki. Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa. Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi. Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi. Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta. Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare. Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta. Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata. Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri. Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya. Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari. Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara. Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa. Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta. Tana lura da sha’anin gidanta kuma ba ta cin abincin ƙyuya. ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka; haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa, “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo, amma ke kin fi su duka.” Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe; amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce. Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta, bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.