- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Nahum
Nahum
Nahum
Nah
Nahum
Jawabi game da Ninebe a littafin wahayin Nahum, mutumin Elkosh.
Fushin Ubangiji a kan Ninebe
Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya kuma.
Ubangiji Allah mai kishi ne, mai ɗaukar fansa kuma.
Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa,
yakan ci gaba da fushi a kan abokan gābansa.
Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai iko duka kuma.
Ubangiji ba zai bar masu zunubi babu horo ba.
Hanyarsa tana cikin guguwa da kuma hadari,
gizagizai kuwa su ne ƙurar ƙafafunsa.
Yakan tsawata wa teku yă kuma busar da shi;
yakan sa dukan koguna su kafe.
Bashan da Karmel sun yi yaushi
tohon Lebanon kuma ya koɗe.
Duwatsu suna rawan jiki a gabansa
tuddai kuma sun narke.
Duniya da dukan abin da yake cikinta
suna rawan jiki a gabansa.
Wa zai iya tsaya wa fushinsa?
Wa yake da ikon jimre wa zafin hasalarsa?
Ana zuba fushinsa kamar wuta;
aka kuma ragargaza duwatsu a gabansa.
Ubangiji nagari ne,
mafaka kuma a lokacin wahala.
Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,
amma da ambaliyar ruwa
zai kawo Ninebe ga ƙarshe;
zai fafari maƙiyansa zuwa cikin duhu.
Dukan abin da suke ƙullawa game da Ubangiji1.9 Ko kuwa Mene ne ku maƙiya kuke ƙullawa a kan Ubangiji? Shi zai kawo ga ƙarshe;
wahala ba za tă sāke komowa ƙaro na biyu ba.
Za su sarƙafe a ƙaya,
za su kuma bugu da ruwan inabinsu;
za a laƙume su kamar busasshiyar ciyawa.1.10 ma’anar kalman nan Ibraniyanci babu tabbas.
Daga cikinki, ya Ninebe wani ya fito
wanda ya ƙulla wa Ubangiji makirci
yana ba da mugayen shawarwari.
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Ko da yake sun yi tarayya, suna kuma da yawa,
za a yanke su, a kawar a su.
Ko da yake na ba ki azaba, ya Yahuda,
ba zan ƙara ba ki azaba ba.
Yanzu zan karya karkiyarsu daga wuyanki
in kuma tsittsinke sarƙar da suka ɗaura ki.”
Ubangiji ya ba da umarni game da ke Ninebe,
“Ba za ki sami zuriyar da za tă ci gaba da sunanki ba.
Zan rurrushe siffofin da kuka sassaƙa da kuma gumakan da kuka ƙera
gumakan da suke a cikin haikalin allolinku.
Zan shirya kabarinki,
domin ke muguwa ce.”
Duba, can a bisa duwatsu,
ga ƙafafu mai kawo labari mai daɗi,
wanda yake shelar salama!
Ki yi bukukkuwanki, ya Yahuda,
ki kuma cika wa’adodinki.
Mugaye ba za su ƙara mamaye ki ba;
domin za a hallaka su ƙaƙaf.
Ninebe za tă fāɗi
Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe.
Ki tsare mafaka,
ki yi gadin hanya
ki sha ɗamara
ki tattaro dukan ƙarfinki!
Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub,
kamar ta Isra’ila,
ko da yake masu washewa sun washe su
suka kuma lalatar da inabinsu.
Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne;
jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura.
Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya
a ranar da aka shirya su;
ana kaɗa māsu da bantsoro.2.3 Da Ibraniyanci; Seftuwajin da Siriyak / mahayan dawakai suna kai da kawowa
Kekunan yaƙi sun zabura a tituna,
suna kai da kawowa a dandali.
Suna walƙiya kamar tocila
suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.
Ninebe ta tattara rundunarta,
duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu.
Sun ruga zuwa katangan birnin,
sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata.
An buɗe ƙofofin rafuffukan
sai wurin ya rurrushe.
An umarta2.7 Ma’anar kalmar da Ibraniyanci babu tabbas. cewa birnin
za tă tafi bauta, za a kuma yi gaba da su.
Bayi ’yan mata suna kuka kamar tattabaru
suna buga ƙirjinsu.
Ninebe tana kama da tafki,
wanda ruwanta yana yoyo.
Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,”
amma ba wanda ya waiga.
A washe azurfa;
a washe zinariya;
dukiyarsu ba ta da iyaka,
arzikinsu kuma ba ya ƙarewa.
Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta!
Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa,
jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare!
Ina kogon zakokin nan yake yanzu,
inda suka ciyar da ’ya’yansu,
inda zaki da zakanya sukan shiga,
da ’ya’yansu, ba mai damunsu
Zaki ya kashe abin da ya ishe ’ya’yansa
ya kuma murɗe wuyan dabbobi
ya cika wurin zamansa da abin da ya kama
ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.
“Ina gāba da ke,”
in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Zan ƙone kekunan yaƙinki,
takobi kuma zai fafare ’ya’yan zakokinki.
Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba.
Ba kuwa za a ƙara jin
muryar ’yan saƙonki ba.”
Kaiton Ninebe
Kaiton birni mai zub da jini,
wadda take cike da ƙarairayi,
cike da ganima,
wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala!
Ku ji karar bulala
da kwaramniyar ƙafafu,
da sukuwar dawakai
da girgizar kekunan yaƙi!
Mahaya dawakai sun kunno kai,
takuba suna walƙiya,
māsu kuma suna ƙyali;
ga ɗumbun da aka kashe
ga tsibin matattu,
gawawwaki ba iyaka,
mutane suna tuntuɓe da gawawwaki,
duk saboda yawan sha’awace-sha’awacen karuwa,
mai daɗin baki, uwargidan maita,
wadda ta ɓad da al’ummai ta wurin karuwancinta
ta kuma ɓad da mutane ta wurin maitancinta.
“Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Zan kware fatarinki a idonki.
Zan nuna wa al’ummai tsiraicinki,
masarautai kuma kunyarki.
Zan watsa miki ƙazanta,
in yi miki wulaƙanci
in kuma mai da ke abin reni.
Duk wanda ya gan ki zai gudu daga gare ki yana cewa,
‘Ninebe ta lalace, wa zai yi makoki domin ta?’
Ina zan sami wani wanda zai yi miki ta’aziyya?”
Kin fi Tebes3.8 Ibraniyanci Ba Amon ne
da take a bakin Nilu,
da ruwa yake kewaye da ita?
Rafi shi ne kāriyarta,
ruwanta kuma katanga.
Kush3.9 Wato, yankin Nilu na Bisa da kuma Masar su ne ƙarfinta marar iyaka;
Fut da Libiya suna cikin mataimakanta.
Duk da haka an tafi da ita
ta kuma tafi bauta.
Aka fyaɗa ƙanananta da ƙasa
aka yayyanka su gunduwa-gunduwa a kan kowane titi.
Aka jefa ƙuri’a a kan manyan mutanenta,
aka daure manyan mutanenta da sarƙoƙi.
Ke ma za ki bugu,
za ki ɓuya.
Ki kuma nemi mafaka daga wurin abokin gāba.
Dukan kagarunki suna kama da itatuwan ɓaure
da ’ya’yansu da suka nuna.
Da an girgiza,
sai ɓaure su zuba a bakin mai sha.
Dubi mayaƙanki,
duk mata ne!
Ƙofofin ƙasarki
a buɗe suke ga abokan gābanki,
wuta ta cinye madogaransu.
Ki ja ruwa gama za a kewaye ki da yaƙi.
Ki ƙara ƙarfin kagaranki!
Ki kwaɓa laka,
ki sassaƙa turmi
ki gyara abin yin tubali!
A can wuta za tă cinye ki;
takobi zai sare ki,
kuma kamar fāra, za a cinye ki.
Ki riɓaɓɓanya kamar fāra,
ki riɓaɓɓanya kamar fārin ɗango!
Kin ƙara yawan masu kasuwancinki
har sai da suka fi taurarin sama.
Amma kamar fāra sun cinye ƙasar
sa’an nan suka tashi, suka tafi.
Masu tsaronki suna kama da fāri ɗango,
shugabanninki sun yi cincirindo kamar fārin ɗango
da suka sauka a kan bango a rana mai sanyi,
amma da rana ta fito, duk za su tashi su tafi,
ba kuma wanda ya san inda suka nufa.
Ya sarkin Assuriya, makiyayanka3.18 Ko kuwa masu mulki sun yi barci;
manyan mutanenka sun kwanta su huta.
An watsar da mutanenka a cikin duwatsu,
ba wanda zai tattaro su.
Ba abin da zai warkar da rauninka;
rauninka ya yi muni.
Duk wanda ya ji labarinka
zai tafa hannuwansa saboda farin cikin fāɗuwarka,
gama wane ne bai ji
jiki a hannunka ba?