- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Mika
Mika
Mika
Mik
Mika
Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.
Ku ji, ya ku mutane duka,
ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki,
bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku,
daga haikalinsa mai tsarki.
Hukunci a kan Samariya da kuma Urushalima
Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa;
zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya.
Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa,
kamar kaki a gaban wuta,
kwaruruka kuma za su ɓace,
kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.
Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub,
da kuma zunuban gidan Isra’ila ne.
Mene ne laifin Yaƙub?
Shin, ba Samariya ba ce?
Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda?
Shin, ba Urushalima ba ce?
“Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji,
wurin noman inabi.
Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari
in kuma bar harsashin gininta a bayyane.
Za a ragargaje dukan allolinta;
za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta;
zan lalatar da dukan gumakanta.
Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su,
ga karuwanci kuma za su koma.”
Kuka da Makoki
Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka;
zan yi tafiya ba takalmi, zan tuɓe, in kuma yi tafiya tsirara.
Zan yi kuka kamar dila,
in yi baƙin ciki kamar mujiya.
Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne;
ya bazu har Yahuda.
Ya ma kai bakin ƙofar mutanena,
har ma Urushalima da kanta.
Kada a faɗe shi a Gat;1.10 Gat ya yi kamar Ibraniyanci na faɗin wani abu.
kada ma a yi kuka.1.10 Da Ibraniyanci; Seftuwajin iya nufin ba a Akko ba ya yi kamar Ibraniyanci na kuka.
A maimako haka, a yi birgima a cikin ƙura
a Bet-Leyafra1.10 Bet Ofra yana nufin gidan laka..
Ku wuce tsirara da kuma kunya,
ku mazaunan Shafir1.11 Shafir yana nufin jin daɗi..
Bet-Ezel tana makoki
domin babu wani daga Za’anan1.11 Za’anan ya yi kamar Ibraniyanci na fito waje.
da ya fito don yă taimaka.
Mazaunan Marot1.12 Marot ya yi kamar Ibraniyanci na ɗaci
sun ƙosa su ga alheri,
amma Ubangiji ya sauko da azaba,
har zuwa ƙofar Urushalima.
Ku da kuke zama a Lakish,1.13 Lakish ya yi kamar Ibraniyanci na ƙungiya.
ku ɗaura wa dawakai kekunan yaƙi.
Gama ku kuka fara yin zunubi
a Sihiyona,
gama an sami laifofin Isra’ila
a cikinku.
Saboda haka za ku ba da kyautan bankwana
ga Moreshet Gat.
Garin Akzib1.14 Akzib yana nufin yaudara. zai zama abin yaudara
ga sarakunan Isra’ila.
Ku mazaunan Maresha1.15 Maresha ya yi kamar Ibraniyanci na mai nasara.
Ubangiji zai kawo wanda zai ci ku da yaƙi.
Sarakunan Isra’ila
za su gudu zuwa Adullam.
Ku aske kanku ƙwal don makoki,
ku yi wa kanku ƙwalƙwal kamar ungulu.
Gama za a ja ’ya’yan da kuke farin ciki
a kai su bauta.
Shirin mutum da na Allah
Taku ta ƙare, ku da kuke shirya makirci,
ku da kuke ƙulle-ƙullen mugunta a kan gadonku!
Da gari ya waye sai ku fita ku aikata mugunta
domin ikon aikatawa yana hannunku.
Kukan yi ƙyashin gonaki ku kuma ƙwace su,
ku yi ƙyashin gidaje ku kuma ƙwace.
Kukan zalunci mutum, ku ƙwace masa gidansa,
har ku ƙwace masa gādonsa.
Saboda haka, Ubangiji ya ce,
“Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i,
yadda ba za ku iya ceton kanku ba.
Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba,
gama zai zama lokacin bala’i ne.
A wannan rana mutane za su yi muku ba’a
za su yi muku gwalo da wannan waƙar makoki,
‘An lalatar da mu sarai;
an rarraba mallakar mutanena.
Ya ɗauke shi daga gare ni!
Ya miƙa filayenmu ga maciyan amanarmu.’ ”
Saboda haka ba za ku kasance da wani a taron jama’ar Ubangiji
da zai raba ƙasar ta wurin jefa ƙuri’a ba.
Annabawan ƙarya
“Kada ku yi annabci” in ji annabawansu.
“Kada ku yi annabci game da waɗannan abubuwa;
abin kunya ba zai same mu ba.”
Daidai ne a ce, ya gidan Yaƙub,
“Ruhun Ubangiji yana fushi ne?
Yana yin irin waɗannan abubuwa?”
“Ashe, maganata ba tă amfane
wanda ayyukansa suke daidai ba?
Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi
kamar magabci.
Kun tuɓe riga mai tsada
daga waɗanda suke wucewa ba tare da kun damu ba,
sai ka ce mutanen da suke komowa daga yaƙi.
Kun kori matan mutanena
daga gidajensu masu daɗi.
Kuka kawar da albarkata har abada
daga wurin ’ya’yansu.
Ku tafi, ku ba ni wuri!
Gama wannan ba wurin hutunku ba ne,
gama ya ƙazantu,
ya zama kangon da ya wuce gyara.
In maƙaryaci da mazambaci ya zo ya ce,
‘Zan yi muku annabci ku sami wadataccen ruwan inabi da barasa,’
zai dai zama annabin da ya dace da wannan mutane ne!
An yi alkawarin ’yantarwa
“Tabbatacce zan tattara ku duka, ya gidan Yaƙub;
zan tattara ku raguwar Isra’ila.
Zan kawo su wuri ɗaya kamar
tumaki a cikin garke,
kamar garke a wajen kiwonsa;
wurin zai cika da mutane.
Wanda ya fasa ƙofa ya buɗe, shi zai haura yă yi musu jagora,
za su fashe bangon su fita.
Sarkinsu zai wuce gabansu,
Ubangiji kuma zai kasance a gaba.”
An Tsawata wa Shugabanni da Annabawa
Sa’an nan na ce,
“Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub,
ku masu mulkin gidan Isra’ila.
Ya kamata ku san shari’a,
ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta,
ku da kuke feɗe mutanena
kuke tuge nama daga ƙasusuwansu;
ku da kuke cin naman mutanena,
ku feɗe fatar jikinsu
kuke kakkarya ƙasusuwansu,
kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya,
kamar naman da za a sa a dafa.”
Sa’an nan za su kira ga Ubangiji,
amma ba zai amsa musu ba.
A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su
saboda irin muguntar da suka yi.
Ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“Game da annabawa
masu ɓad da mutanena,
in wani ya ciyar da su,
sai su ce akwai ‘salama’
amma in bai ciyar da su ba,
a shirye suke su kai masa hari.
Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba,
kuma duhu, ba tare da duba ba.
Rana za tă fāɗi wa annabawa,
yini kuma zai zama musu duhu.
Masu gani za su ji kunya,
masu duba kuma za su ji taƙaici.
Dukansu za su rufe fuskokinsu
gama ba amsa daga Allah.”
Amma game da ni, ina cike da iko
ta wurin Ruhun Ubangiji
da kuma adalci da ƙarfi,
don a sanar da Yaƙub laifofinsa,
ga Isra’ila kuma zunubinsa.
Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub,
ku masu mulkin gidan Isra’ila,
ku da kuke ƙyamar gaskiya,
kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya;
kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini,
Urushalima kuma ta wurin mugunta.
Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne,
firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su,
annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi.
Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa,
“Ba Ubangiji yana tare da mu ba?
Ba bala’in da zai zo mana.”
Don haka, saboda ku,
za a nome Sihiyona kamar gona,
Urushalima kuma ta zama tarin juji,
tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.
Dutsen Ubangiji
A kwanakin ƙarshe
za a kafa dutsen haikalin Ubangiji
yă zama babba a cikin duwatsu.
Za a ɗaga shi sama da tuddai,
mutane kuma za su riƙa ɗunguma zuwa gare shi.
Al’ummai da yawa za su zo su ce,
“Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji,
zuwa gidan Allah na Yaƙub.
Zai koya mana hanyoyinsa,
don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.”
Doka za tă fita daga Sihiyona,
maganar Ubangiji kuma daga Urushalima.
Zai shari’anta tsakanin mutane
yă kuma sulhunta tsakanin manyan al’ummai nesa da kuma kusa.
Har su mai da takubansu su zama garemani,
māsunsu kuma su zama wuƙaƙen askin itace.
Al’umma ba za tă ɗauki takobi gāba da wata al’umma ba,
ko a yi horarwa don yaƙi.
Kowa zai zauna a tushen kuringar inabinsa
da tushen ɓaurensa,
kuma ba wanda zai tsoratar da su,
gama Ubangiji Maɗaukaki ne ya faɗa.
Dukan al’ummai za su iya tafiya
a cikin sunan allolinsu;
mu dai za mu yi tafiya a cikin sunan Ubangiji
Allahnmu har abada abadin.
Shirin Ubangiji
“A wannan rana,” in ji Ubangiji,
“zan tattara guragu;
zan kuma tara masu zaman bauta,
da waɗanda na sa suka damu.
Zan mai da guragu su zama raguwa,
waɗanda aka kora, su zama al’umma mai ƙarfi.
Ubangiji zai yi mulkinsu a Dutsen Sihiyona
daga wannan rana da kuma har abada.
Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke,
Ya mafaka4.8 Ko kuwa tudu Diyar Sihiyona,
za a maido miki da mulkinki na dā,
sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.”
Don me yanzu kike kuka da ƙarfi,
ba ki da sarki ne?
Masu shawararki sun hallaka ne,
da zafi ya cika ki kamar mace mai naƙuda?
Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona,
kamar macen da take naƙuda,
don yanzu dole ki bar birni
ki kafa sansani a filin Allah.
Za ki tafi Babilon;
a can za a kuɓutar da ki.
A can ne Ubangiji
zai fanshe ki daga hannun maƙiyanki.
Amma yanzu al’ummai da yawa
suna gāba da ke.
Suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita,
bari mu zuba wa Sihiyona ido.”
Amma ba su san
tunanin Ubangiji ba;
ba su fahimci shirinsa ba,
shi da ya tattara su kamar dammuna a masussuka.
“Ki tashi ki yi sussuka, ya Diyar Sihiyona,
gama zan ba ki ƙahonin ƙarfe;
zan ba ki kofatan tagulla
domin ki ragargaje al’ummai masu yawa.”
Za ki ba Ubangiji dukan dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba,
wadatarsu kuma ga Ubangiji dukan duniya.
An yi alkawarin mai mulki daga Betlehem
Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa,5.1 Ko kuwa Ƙara ƙarfin katangarki, ya katangan birni
gama an kewaye mu da yaƙi.
Za su bugi kumatun mai mulkin
Isra’ila da sandar ƙarfe.
“Amma ke, Betlehem ta Efrata,
ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki5.2 Ko kuwa masu mulki a Yahuda,
daga cikinki wani zai zo domina
wanda zai yi mulkin Isra’ila,
wanda asalinsa5.2 Da Ibraniyanci fitowa daga
tun fil azal ne.”5.2 Ko kuwa daga madawwamin kwanaki
Saboda haka za a yashe Isra’ila
har sai wadda take naƙuda ta haihu
sauran ’yan’uwansa kuma sun dawo
su haɗu da Isra’ilawa.
Zai tsaya yă yi kiwon garkensa
da ƙarfin Ubangiji,
cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa.
Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa
za tă kai har ƙarshen duniya.
Zai kuma zama salamarsu.
Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari
suka tattake kagarunmu,
za mu tā da makiyaya bakwai,
har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su.
Za su yi mulkin5.6 Ko kuwa ragargaza ƙasar Assuriya da takobi,
ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi.5.6 Ko kuwa Nimrod a bakin ƙofofinta
Zai cece mu daga hannun Assuriyawa
sa’ad da suka kawo wa ƙasarmu hari
suka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu.
Raguwar Yaƙub za tă kasance
a tsakiyar mutane masu yawa
kamar raɓa daga Ubangiji,
kamar yayyafi a kan ciyawa,
wanda ba ya jiran mutum
ko kuma yă dakata wa ɗan adam.
Raguwar Yaƙub za tă kasance tare da al’ummai,
a cikin mutane masu yawa,
kamar zaki a cikin sauran namun jeji,
kamar ɗan zaki cikin garken tumaki,
wanda yake tattaka yă kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu,
ba kuwa wanda zai cece su.
Za a ɗaga hannunka cikin nasara a kan abokan gābanka,
za a hallaka maƙiyanka duka.
“A wannan rana,” in ji Ubangiji
“Zan hallaka dawakanku daga cikinku,
in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.
Zan hallaka biranen ƙasarku
in yi rugu-rugu da dukan katangunku.
Zan kawar da maitarku,
ba za a ƙara yin sihiri ba.
Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa
da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku,
nan gaba ba za ku ƙara rusuna
wa aikin hannuwanku ba.
Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku5.14 Wato, alamar alliyar Ashera
in kuma rurrushe biranenku.
Zan yi ramuwa cikin fushi da hasala
a kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba.”
Damuwar Ubangiji a kan Isra’ila
Ku saurari abin da Ubangiji ya ce,
“Tashi ku gabatar da ƙararku a gaban duwatsu;
bari tuddai su ji abin da kuke so ku faɗa.
“Ku saurara, ya ku duwatsu game da tuhumar da Ubangiji yake muku,
ku ji, ku daɗaɗɗun tushin duniya.
Gama Ubangiji yana da ƙara a kan mutanensa;
yana tuhumar Isra’ila.
“Ya ku mutanena, me na yi muku?
Ta yaya na nawaita muku? Ku amsa mini.
Na fito da ku daga ƙasar Masar
na kuma ’yantar da ku daga ƙasar bauta.
Na aika da Musa yă jagorance ku,
haka ma Haruna da Miriyam.
Ya ku mutanena, ku tuna
abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla
da kuma amsar da Bala’am ɗan Beyor ya bayar.
Ku tuna da tafiyarku daga Shittim zuwa Gilgal,
don ku san ayyukan adalcin Ubangiji.”
Da me zan zo a gaban Ubangiji
in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah?
Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa,
da ɗan maraƙi bana ɗaya?
Ubangiji zai ji daɗin hadayar raguna dubbai
da kuma rafuffukan mai dubbai goma?
Zan ba da ɗan farina ne don laifina,
ko ’ya’yan jikina domin zunubin raina?
Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.
Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa
shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai
ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.
Laifin Isra’ila da kuma hukunci
Ku saurara! Ubangiji yana kira ga birni,
a ji tsoron sunana kuwa hikima ce,
“Ku kasa kunne ga sandan nan da kuma wannan wanda ya naɗa.6.9 Ma’anar Ibraniyanci na wannan layin babu tabbas.
Har yanzu zan manta, ya muguwar gida
da dukiyarki da kika samu a muguwar hanya
zan kuma manta da bugaggen mudun awo6.10 Efa mudun awo ne na busasshen abu. wanda ake zargi?
Zan kuɓutar da mutumin da yake da ma’auni na rashin gaskiya,
da kuma buhun ma’aunan ƙarya?
Attajiranta masu fitina ne;
mutanenta kuma maƙaryata ne
harsunansu kuwa suna yaudara.
Saboda haka, zan hallaka ku
in lalace ku saboda zunubanku.
Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba,
cikinku zai zama babu kome6.14 Ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma babu tabbas.
Za ku tattara amma ba za ku yi ajiyar kome ba,
gama abin da kuka yi ajiya zan ba wa takobi.
Za ku yi shuki amma ba za ku girba ba;
za ku matse zaitun amma ba za ku yi amfani da mai wa kanku ba,
za ku tattaka ’ya’yan inabi amma ba za ku sha ruwan inabin ba.
Kuna kiyaye ƙa’idodin Omri
da dukan ayyukan gidan Ahab
kun kuma bi al’adunsu.
Saboda haka, zan maishe ku kufai
in mai da ku abin dariya a cikin mutane,
za ku sha reni a wurin al’ummai.”6.16 Seftuwajin; da Ibraniyanci suna da abin zargi ga mutanena ne a nan
Baƙin cikin Isra’ila
Tawa ta ƙare!
Ina kama da wanda yake tattara ’ya’yan itatuwa
a lokacin kalar ’ya’yan inabi;
babu sauran nonon inabin da za a tsinka a ci,
babu kuma ’ya’yan ɓaure na farko-farkon da raina yake marmari.
An kawar da masu tsoron Allah daga ƙasar;
babu sauran mai adalcin da ya rage.
Dukan mutane suna kwanto don su zub da jini;
kowa yana farautar ɗan’uwansa da tarko.
Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta;
shugabanni suna nema a ba su kyautai,
alƙalai suna nema a ba su cin hanci,
masu iko suna faɗar son zuciyarsu,
duk suna ƙulla makirci tare.
Mafi kyau a cikinsu yana kama da ƙaya,
mafi gaskiyarsu ya fi shingen ƙaya muni.
Ranar da Allah zai ziyarce ku ta zo,
ranar da masu gadinku za su hura ƙaho.
Yanzu ne lokacin ruɗewarku.
Kada ka yarda da maƙwabci;
kada ka sa begenka ga abokai.
Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka,
ka yi hankali da kalmominka.
Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne,
diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta,
matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta,
abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.
Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji,
ina sauraron Allah Mai Cetona;
Allahna kuwa zai ji ni.
Isra’ila za tă tashi
Kada ku yi farin ciki, ku maƙiyana!
Ko da yake na fāɗi, zan tashi.
Ko da yake na zauna a cikin duhu,
Ubangiji zai zama haskena.
Domin na yi masa zunubi,
zan fuskanci fushin Ubangiji,
har sai ya dubi batuna
ya kuma tabbatar da ’yancina.
Zai kawo ni zuwa wurin haske;
zan ga adalcinsa.
Sa’an nan maƙiyina zai gani
yă kuma sha kunya,
shi da yake ce da ni
“Ina Ubangiji Allahnka?”
Zai gani, yă kuma ji kunya.
Ko yanzu ma za a tattake shi
kamar taɓo a tituna.
Ranar gina katangarka tana zuwa,
a ranar za a fadada iyakokinka.
A wannan rana mutane za su zo gare ka
daga Assuriya da kuma biranen Masar,
daga Masar ma har zuwa Yuferites
daga teku zuwa teku,
kuma daga dutse zuwa dutse.
Duniya za tă zama kufai saboda mazaunanta,
saboda ayyukansu.
Addu’a da yabo
Ka yi kiwon mutanenka da sandarka,
garken gādonka,
wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi,
a ƙasa mai kyau ta kiwo,7.14 Ko kuwa a tsakiyar Karmel
bari su yi kiwo a Bashan da Gileyad
kamar a kwanakin dā.
“Kamar a kwanakin da kuka fito daga Masar,
zan nuna musu al’ajabaina.”
Al’ummai za su gani su kuma ji kunya,
za a kuma ƙwace musu dukan ikonsu.
Za su kama bakinsu
kunnuwansu kuma za su zama kurame.
Za su lashi ƙura kamar maciji,
kamar dabbobi masu rarrafe a ƙasa.
Za su fito daga maɓuyarsu da rawan jiki,
za su juya cikin tsoro ga Ubangiji Allahnmu
su kuma ji tsoronku.
Wane ne Allah kamar ka,
wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?
Ba ka zama mai fushi har abada
amma kana marmari ka nuna jinƙai.
Za ka sāke jin tausayinmu;
za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka
ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.
Za ka yi wa Yaƙub aminci,
ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim,
kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu
tun a kwanankin dā.