- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Firistoci Firistoci Firistoci Fir Firistoci Hadaya ta ƙonawa Ubangiji ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin Tentin Sujada ya ce, “Yi magana da Isra’ilawa ka ce musu, ‘Duk sa’ad da waninku ya kawo hadaya ga Ubangiji, ku kawo hadayarku ta dabba daga garkenku ta shanu ko kuwa daga tumakinku. “ ‘In hadaya ta ƙonawar daga shanu ne, sai yă miƙa namiji marar lahani. Dole yă kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă zama yardajje ga Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya ta ƙonawar, za a kuwa karɓa a madadinsa don a yi kafara dominsa. Zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji, Haruna kuwa da ’ya’yansa maza firist, za su kawo jinin su kuma yafa shi a kan bagaden a kowane gefe a mashigin Tentin Sujada. Zai feɗe hadaya ta ƙonawar, yă yayyanka shi gunduwa-gunduwa. ’Ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su hura wuta a bagade, su kuma shirya itace a kan wutar. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su shirya gunduwa-gunduwar haɗe da kan da kuma kitsen a kan itace mai cin wuta wanda yake a kan bagaden. Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. “ ‘In hadaya ta ƙonawar daga garke ne, ko na tumaki, ko na awaki, zai miƙa namiji ne marar lahani. Zai yanka shi a gefen arewa na bagaden a gaban Ubangiji, ’ya’yan Haruna firistoci kuwa za su yayyafa jinin dabbar a bagaden a kowane gefe. Zai yanka shi gunduwa-gunduwa, firist kuwa zai shirya su haɗe da kan, da kuma kitsen a kan itace mai cin wutar da yake a kan bagade. Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. “ ‘In hadaya ga Ubangiji ɗin, hadaya ta ƙonawa ta tsuntsaye ce, zai miƙa kurciya ko ’yar tattabara. Firist zai kawo ta bagade, yă murɗe wuyan tsuntsun yă ƙone shi a kan bagade; zai tsiyaye jininsa tsuntsun a gefen bagaden. Amma zai ɗauki kayan cikin tsuntsun da gashin yă zubar da su a gefen bagaden a wajen gabas a wurin zuba toka. Zai tsaga shi biyu a tsaka, amma ba zai raba shi ba. Firist ɗin zai ɗibiya shi a bisa itacen da yake bisa bagaden, yă ƙone shi. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Hadaya ta hatsi “ ‘Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, hadayarsa za tă zama gari mai laushi ne. Zai zuba mai a kai, yă sa turare a kansa yă kai wa ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci. Firist zai ɗiba gari mai laushin a tafin hannu da kuma man, tare da dukan turaren, yă ƙone wannan a sashen tunawa a kan bagade, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta. “ ‘In kuka kawo toyayyen hadayar gari da aka yi daga matoya, zai ƙunshi gari mai laushi, toyayye ba tare da yisti ba, gauraye kuma da mai, ko kuwa ƙosai da aka yi ba tare da yisti ba, aka kuma kwaɓa da mai. In an toya hadaya ta garinku a kasko, sai a yi shi da gari mai laushi haɗe da mai, ba kuwa da yisti ba. A gutsuttsura shi, a zuba mai a kansa, hadaya ce ta hatsi. In hadayarku ta hatsin da aka dafa ne a tukunya, sai a yi shi da gari mai laushi da kuma mai. A kawo hatsin da aka yi da waɗannan abubuwa ga Ubangiji; a ba wa firist wanda zai ɗauka yă kai bagade. Zai fid da sashen tunawa daga hadaya ta gari, yă ƙone shi a kan bagade kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Sauran hadaya ta garin za tă zama ta Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayun da aka yi ga Ubangiji ta wuta. “ ‘Kowace hadaya ta garin da kuka kawo ga Ubangiji, dole a yi shi ba tare da yisti ba, gama ba za ku ƙone wani yisti, ko zuma a cikin hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta ba. Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta ’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba. A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku. “ ‘In kuka kawo hadaya ta gari na ’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta. A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi. Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Hadaya ta salama “ ‘In hadayar wani mutum, hadaya ta salama ce,3.1 Al’adance; hadaya ta zumunci; haka ma a ayoyi 3, 6 da 9. ya kuma miƙa ’yar dabba daga garke, ko namiji ko ta mace ce, sai yă miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Ubangiji. Yă kuma ɗibiya hannunsa bisa kan hadayarsa, yă yanka ta a mashigin Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna waɗanda suke firistoci za su yayyafa jinin a kan bagade a kowane gefe. Daga hadaya ta zumuncin da zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta; wato, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki ko kuwa da sun shafe su, da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji. ’Ya’yan Haruna za su ƙone shi a kan bagade a bisa hadaya ta ƙonawa wadda take a kan itacen da yake cin wuta, kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. “ ‘In ya miƙa dabba ce daga garke a matsayin hadaya ta salama ga Ubangiji, zai miƙa namiji ko ta mace marar lahani. In ya miƙa ɗan rago ne, zai kawo shi a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannu a kan hadayarsa, yă yanka shi a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jinin dabbar a kowane gefe na bagade. Daga hadaya ta zumuncin zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, kitsen, ƙibabbiya wutsiyar gaba ɗaya da ya yanka gab da ƙashin gadon baya, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, ko kuwa da suka shafe su, da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji. Firist zai ƙone su a kan bagade kamar hadayar abinci, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. “ ‘In yana miƙa akuya ce, zai kawo ta a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jininta a kowane gefe na bagade. Daga abin da zai miƙa sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, dukan kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su, da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji. Firist zai ƙone su a kan bagade kamar abinci, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi. Dukan kitsen na Ubangiji ne. “ ‘Wannan dawwammamiyar farilla ce ga tsararraki masu zuwa, a inda za ku zauna. Ba za ku ci wani kitse ko wani jini ba.’ ” Hadaya ta zunubi (Firistoci 6.24-30) Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da wani ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji, “ ‘In shafaffen firist ya yi zunubi, ya jawo wa jama’a laifi, dole yă kawo wa Ubangiji ɗan bijimi marar lahani a matsayin hadaya don zunubi saboda zunubin da ya yi. Zai kawo bijimin a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. Zai ɗibiya hannunsa a kan bijimin, yă kuma yanka shi a gaban Ubangiji. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗiba jinin bijimin yă kai cikin Tentin Sujada. Yă tsoma yatsarsa a cikin jinin, yă kuma yafa sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen wuri mai tsarki. Sa’an nan firist ɗin zai zuba jinin a ƙahonin bagaden turare masu ƙanshi da suke a gaban Ubangiji a Tentin Sujada. Sauran jinin bijimin zai zuba a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada. Zai cire dukan kitsen daga bijimin hadaya don zunubi, kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su, da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta, waɗanda zai cire tare da ƙodoji. Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin yă ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya. Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da hanjinsa, wato, dukan sauran bijimi, dole yă ɗauke su zuwa waje da sansani zuwa wani wuri mai tsabta inda ake zub da toka, yă ƙone shi a itacen da yake cin wuta a tarin toka. “ ‘In dukan jama’ar Isra’ilawa suka yi zunubi ba da gangan ba, har suka aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake jama’ar ba su san batun ba, duk da haka sun yi laifi. Sa’ad da suka gane da zunubin da suka aikata, dole taron su kawo ɗan bijimi a matsayin hadaya don zunubi, su kawo shi a gaban Tentin Sujada. Dattawan jama’a za su ɗibiya hannuwansu a kan bijimin a gaban Ubangiji, sai a yanka bijimin a gaban Ubangiji. Sa’an nan shafaffen firist zai ɗibi jinin bijimi zuwa cikin Tentin Sujada. Zai tsoma yatsarsa cikin jini yă kuma yayyafa shi a gaban Ubangiji sau bakwai a gaban labule. Zai zuba jinin a ƙahonin bagaden da suke gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Zai zuba sauran jinin a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada. Zai cire dukan kitsen daga gare shi yă ƙone a kan bagade, yă kuma yi da wannan bijimi kamar yadda ya yi da bijimi na hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsu, za a kuwa gafarta musu. Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a. “ ‘Sa’ad da shugaba ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta, to, ya yi laifi. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo bunsuru marar lahani a matsayin hadayarsa. Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun yă kuma yanka shi a inda ake yankan hadayar ƙonawa a gaban Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsarsa yă sa a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade. Zai ƙone dukan kitse a kan bagade kamar yadda ya ƙone kitsen hadaya ta salama. Ta haka firist zai yi kafara saboda zunubin mutumin, za a kuwa gafarta masa. “ ‘In wani memba a cikin jama’a ya yi zunubi ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo akuya marar lahani a matsayin hadayarsa domin zunubin da ya yi. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin da yatsarsa yă zuba a ƙahoni a bagaden hadaya ta ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a ƙasan bagade. Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa. “ ‘Idan kuwa daga cikin ’yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo ’yar tunkiya marar lahani. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta hadaya don zunubi a inda ake yankan hadayar ƙonawa. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubin da yatsarsa yă zuba a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade. Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist ɗin zai yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa. “ ‘Mutum zai yi zunubi in bai yi magana ba sa’ad da ya ji ana shelar neman shaida game da wani abin da ya gani ko kuwa ya ji, alhakin zai zauna a wuyansa. “ ‘Ko kuwa in mutum ya taɓa wani abin da yake mai ƙazanta, ko gawar naman jeji marar tsabta, ko na shanu marar tsabta, ko na halittu marasa tsabtan da suke motsi a ƙasa; ko da yake bai sani ba, ya ƙazantu ke nan, kuma ya yi laifi. Ko kuwa in ya taɓa rashin tsabta na mutane, wani abin da zai sa shi rashin tsabta; ko da yake bai sani ba, sa’ad da ya gane, zai zama mai laifi. Ko kuwa in mutum bai yi tunani ba, ya yi rantsuwar yin wani abu, ko mai kyau ko marar kyau; ko da yake bai sani ba, duk da haka sa’ad da ya gane zai zama mai laifi. Sa’ad da wani yana da laifi a kowanne cikin waɗannan hanyoyi, dole yă furta a hanyar da ya yi zunubin kuma don zunubin da ya yi, dole yă kawo wa Ubangiji tunkiya ko akuya daga garke kamar hadaya don zunubi; firist kuwa zai yi kafara dominsa da kuma domin zunubinsa. “ ‘In ba zai iya kawo tunkiyar ba, sai yă kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ga Ubangiji a matsayin hakki don zunubinsa, ɗaya domin hadaya don zunubi ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Zai kawo su wa firist, wanda da fari zai miƙa ɗaya domin hadaya don zunubi. Zai murɗe kan daga wuyanta, ba tare da tsinke kan gaba ɗaya ba, zai kuma yayyafa jinin hadaya don zunubin a gefen bagade; a tsiyaye sauran jinin kuma a gindin bagade. Hadaya ce ta zunubi. Firist zai miƙa ɗayan matsayin hadaya ta ƙonawa bisa ga yadda aka tsara, yă kuma yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa. “ ‘In ba zai iya kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ba, sai yă kawo humushin garwan5.11 Wato, mai yiwuwa kamar kwata 2 (kamar lita 2) gari mai laushi domin hadaya don zunubi. Ba lalle ba ne yă sa mai ko turare a kansa, saboda wannan hadaya ce ta zunubi. Zai kawo wa firist, firist kuwa zai ɗiba da hannu don yă kasance abin tunawa, sai yă ƙone a bisan bagaden kamar hadayar da ake ƙona da wuta ga Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsa saboda dukan waɗannan zunuban da ya yi, za a kuwa gafarta masa. Sauran hadayar za tă zama ta firist, kamar yadda yake bisa ga hadaya ta gari.’ ” Hadaya ta laifi (Firistoci 7.1-10) Ubangiji ya ce wa Musa, “Sa’ad da mutum ya ci amana, ya kuma yi zunubi ba da gangan ba dangane da wani cikin abubuwa masu tsarki na Ubangiji, zai kawo ga Ubangiji rago daga garke wanda ba shi da lahani saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimata kuɗinsa bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Hadaya ce ta laifi. Dole yă biya abin da ya kāsa yi dangane da abubuwa masu tsarki, yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar abin a kan wannan sa’an nan yă ba wa firist. Firist kuwa zai yi kafara dominsa da ragon hadaya don laifi. Za a kuwa gafarta masa. “In mutum ya yi zunubi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake bai sani ba, shi mai laifi ne. Za a kuwa nemi hakki daga gare shi. Zai kawo wa firist rago daga garke, marar lahani. Za a kimanta tamanin rago daidai da tamanin hadaya don laifi. Firist kuwa zai yi kafara don kuskuren da mutumin ya yi ba da saninsa ba, za a gafarta masa. Hadaya ce ta laifi, ya yi laifi na5.19 Ko kuwa ya yi cikakkiyar kafara saboda nasa abin da ya yi marar kyau ga Ubangiji.” (Ƙidaya 5.5-10) Ubangiji ya ce wa Musa, “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin, ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi, sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta. Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa. A matsayin hakki kuwa, dole yă kawo wa firist, wato, ga Ubangiji, hadaya rago marar lahani kuma wanda aka kimanta tamaninsa daga garke don laifinsa. Ta haka firist zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.” Hadaya ta ƙonawa (Fitowa 29.38-43; Ƙidaya 28.1-8) Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ba Haruna da ’ya’yansa maza wannan umarni, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za tă kasance a bagade dukan dare, sai da safe, kuma dole a bar wutar tă yi ta ci a bisa bagaden. Sa’an nan firist zai sa rigunarsa ta lilin da kuma rigar lilin da ake sa a ciki, sa’an nan yă kwashe tokan hadaya ta ƙonawa da wuta da ta ci a kan bagaden, yă sa kusa da bagaden. Sa’an nan yă tuɓe waɗannan rigunan yă sa waɗansu, sa’an nan yă ɗauki tokar yă kai waje da sansani zuwa inda yake da tsabta. Dole a bar wutar da take bisa bagaden tă yi ta ci; kada tă mutu. Kowace safiya firist zai ƙara itacen wuta, yă shirya hadaya ta ƙonawa a bisa wutar yă kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a kansa. Dole a bar wutar tă ci gaba da ci a bisa bagade; kada tă mutu. Hadaya ta gari “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin hadaya ta gari. ’Ya’yan Haruna za su kawo ta a gaban Ubangiji, a gaban bagaden. Firist zai ɗiba garin hadayar mai laushin wanda aka zuba masa mai da kuma turare cike da tafin hannu. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa. Haruna da ’ya’yansa maza za su ci sauran, amma za a ci shi ba tare da yisti ba a tsattsarkan wuri; za su ci shi a harabar Tentin Sujada. Ba za a toya shi da yisti ba; na ba su yă zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi. Kowane ɗa namiji cikin zuriyar Haruna zai iya cinsa. Wannan rabonsa ne na kullum na hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta. Wannan madawwamiyar doka ce cikin zamananku duka. Duk abin da ya taɓa hadayun zai tsarkaka.’ ”6.18 Ko kuwa Duka wanda ya taɓa su dole yă kasance mai tsarki haka ma a aya 27. Ubangiji ya kuma ce wa Musa, “Wannan ne hadayar da Haruna da ’ya’yansa maza za su kawo ga Ubangiji a ranar da za a naɗa su firistoci,6.20 Ko kuwa kowane humushin garwan gari mai laushi a matsayin hadaya ta gari na kullum, rabinsa da safe, rabinsa kuma da yamma. A shirya shi da mai a kwanon tuya, a kawo shi kwaɓaɓɓe sosai, a miƙa shi hadaya ta gari dunƙule-dunƙule6.21 Ba a tabbatar da ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba. don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Duk wanda aka naɗa daga ’ya’yan Haruna yă zama firist a madadinsa, shi ne zai miƙa wannan hadayar ga Ubangiji. Zai ƙone hadayar ƙurmus. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce har abada. Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ƙurmus, ba za a ci ba.” Hadaya ta zunubi (Firistoci 4.1,2) Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin hadaya don zunubi. Za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji a inda ake yankan hadaya ta ƙonawa; dole tă kasance mai tsarki. Firist da ya miƙa ta zai ci, za a ci ta a tsattsarkan wuri, a harabar Tentin Sujada. Duk abin da ya taɓa wani sashe na naman, zai zama da tsarki, kuma in wani jini ya ɗiga a riga, dole ka wanke shi a tsattsarkan wuri. Dole a farfashe tukunyar lakar da aka dafa naman a ciki; amma in an dafa a tukunyar tagulla, sai a kankare tukunyar, a kuma ɗauraye da ruwa. Kowane namiji a iyalin firistoci zai iya ci; gama abu ne mafi tsarki. Amma duk wata hadaya don zunubi wadda aka kawo jininta cikin Tentin Sujada don a yi kafara a Wuri Mai Tsarki, ba za a ci ba. A maimako haka za a ƙone ta ɗungum. Hadaya don laifi (Firistoci 5.14-19) “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi na hadaya don laifi, hadaya ce tsattsarka. Za a yanka hadaya don laifi a inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, za a kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagade. Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji biyu da kitsen da yake a bisansu kusa da kwiɓi, da kuma rufin hanta, wanda za a cire tare da ƙodoji. Firist zai ƙone su a kan bagade, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Hadaya ce don laifi. Kowane da namiji cikin iyalin firistoci zai iya ci. Sai a tsattsarkan wuri ne za a ci; gama abu mafi tsarki ne. “ ‘Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ƙa’ida hanyar yinsu iri ɗaya ce. Su ɗin na firist da ya yi kafara da su ne. Firist da ya miƙa hadaya ta ƙonawa domin wani, zai iya ajiye fatar wa kansa. Kowace hadaya ta garin da aka toya a tanda, ko aka dafa a tukunya ko a kan kaskon tuya, na firist da ya miƙa ta ne, kuma kowace hadaya ta gari wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, ita ma, ta dukan ’ya’ya Haruna ne maza. Hadaya don salama “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodin hadaya don zumuncin da mutum zai iya miƙa ga Ubangiji. “ ‘In ya miƙa hadayar a matsayin hadaya ta godiya ce, to, zai miƙa ta tare da burodi mai kauri marar yisti, wanda aka kwaɓa da mai, da burodi marar kauri, wanda aka shafa wa mai, da kuma burodi mai kauri da aka yi da gari mai laushi wanda aka kwaɓa sosai da mai. Tare da hadayarsa don zumunci ta godiya, zai miƙa dunƙulen burodin da aka yi da yisti. Zai kuma kawo ɗaya daga kowace a matsayin hadaya, baiko ne ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist da ya yafa jinin hadaya ta salama ne. Za a ci wannan nama na hadaya don zumunci ta godiya a ranar da aka miƙa ta, kada yă bar wani abu daga naman yă kwana. “ ‘In hadayarsa cika wa’adin rantsuwa ce ko kuwa ta yardar rai ce, sai a ci hadayar a ranar da ya miƙa ta, amma za a iya cin duk abin da ya rage kashegari. Duk naman hadayar da ya rage har kwana uku, dole a ƙone shi. Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami albarkar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci kuwa ya yi laifi. “ ‘Ba za a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki ba; dole a ƙone shi. Game da sauran nama, kowa da yake mai tsarki zai iya ci. Amma in wani wanda ba shi da tsarki ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a fid da mutumin daga cikin mutanensa. Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a fid da mutumin daga cikin mutanensa.’ ” An hana cin kitse da kuma jini Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Kada ku ci wani kitsen shanu, ko na tumaki, ko kuwa na awaki. Za a iya yin wani amfani da kitsen dabbar da ta mutu mushe, ko kitsen dabbar da namun jeji su yayyaga, amma kada a kuskura a ci. Duk wanda ya ci kitsen dabbar da aka miƙa ta wuta ga Ubangiji, za a fid da shi daga mutanensa. Kuma duk inda kuke zama, ba za ku ci jinin wani tsuntsu ko na dabba ba. Duk wanda ya ci jini, za a fid da mutumin daga mutanensa.’ ” Rabo don firist Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Duk wanda ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama. Da hannuwansa zai kawo hadayar da za a ƙona ga Ubangiji; zai kawo kitsen tare da ƙirjin, yă kuma kaɗa ƙirjin a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Firist zai ƙone kitsen a bisa bagade, amma ƙirjin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza. Za ku ba da cinya ta dama ta hadaya don zumuncinku ga firist a matsayin baiko. Ɗan Haruna da ya miƙa jini da kitsen hadaya ta salama, zai ɗauki cinyar tă zama rabonsa. Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ” Wannan shi ne sashen hadayar da aka ba wa Haruna da ’ya’yansa maza, hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta, tun ranar da aka gabatar da su don su yi wa Ubangiji hidima a matsayin firist. A ranar da aka keɓe su, Ubangiji ya umarta cewa Isra’ilawa su ba da wannan a gare su a matsayin rabonsu na kullum, a dukan tsararraki masu zuwa. Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, hadaya don zunubi, hadaya don laifi, hadaya ta naɗi da kuma hadaya ta salama, waɗanda Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai, a Hamadar Sinai, a ranar da ya umarci Isra’ilawa su kawo hadayunsu ga Ubangiji. Naɗin Haruna da ’ya’yansa maza (Fitowa 29.1-37) Ubangiji ya ce wa Musa, “Kawo Haruna da ’ya’yansa maza, ka ɗauki rigunansu, man keɓewa, bijimi domin hadaya don zunubi, ’yan raguna biyu da kuma kwandon da yake da burodi marar yisti, ka kuma tara dukan jama’a a ƙofar Tentin Sujada.” Sai Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi, jama’a kuwa suka taru a ƙofar Tentin Sujada. Sai Musa ya ce wa jama’ar, “Ga abin da Ubangiji ya umarta a yi.” Sa’an nan Musa ya kawo Haruna da ’ya’yansa maza gaba, ya kuma wanke su da ruwa. Ya sa wa Haruna taguwa, ya ɗaura igiya kewaye da shi, ya sa masa riga, ya sa masa efod. Ya kuma ɗaura masa efod wanda aka yi masa saƙar gwaninta. Ya sa masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirjin. Sai ya naɗa masa rawani, daga gaban rawanin ya sa allon zinariya, wato, kambi tsattsarka, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Sa’an nan Musa ya ɗauki man keɓewa ya keɓe tabanakul da kuma kowane abin da yake cikinsa, ta haka ya tsarkake su. Ya yayyafa mai a kan bagade sau bakwai, yana keɓe bagade da dukan kayayyaki, da daro, da abin da yake tsaya a kai, don yă tsarkake su. Ya zuba man keɓewa a kan Haruna, ya kuma keɓe shi don yă tsarkake shi. Sa’an nan ya kawo ’ya’yan Haruna maza, ya sa musu taguwoyi, ya ɗaɗɗaura igiyoyi kewaye da su, ya kuma sa musu huluna yadda Ubangiji ya umarce shi. Sa’an nan ya miƙa bijimi domin hadaya don zunubi, sai Haruna da ’ya’yansa suka ɗibiya hannuwansu a bijimin. Musa ya yanka bijimin ya ɗauki jinin, ya sa yatsarsa ya zuba a dukan ƙahonin bagade don yă tsarkake bagaden. Ya zuba sauran jinin a gindin bagade. Ta haka ya tsarkake shi don yă yi kafara dominsa. Musa ya ɗebo dukan kitsen da yake kewaye da kayan ciki, da kuma wanda ya rufe hanta, da ƙodojin, da kuma kitsensu, ya kuma ƙone su a kan bagade. Amma bijimin da fatarsa da namansa da kuma ƙashinsa ya ƙone su a bayan sansani, yadda Ubangiji ya umarce shi. Sa’an nan ya miƙa ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, sai Haruna da ’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan rago. Sa’an nan Musa ya yanka ɗan ragon, ya kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagaden. Ya yanka ragon gunduwa-gunduwa ya ƙone kan, ya kuma ƙone gunduwa-gunduwan da kitsen. Ya wanke kayan cikin da ƙafafun a ruwa, ya kuma ƙone dukan ragon a bisa bagade kamar hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi. Sai ya miƙa ɗayan ɗan ragon, ɗan ragon naɗin, sai Haruna da ’ya’yansa maza suka ɗibiya hannuwansu a kan ɗan ragon. Musa kuwa ya yanka ɗan ragon ya ɗibi jinin ya sa leɓatun kunnen dama na Haruna, ya kuma sa a babbar yatsarsa ta hannun dama da kuma a babbar yatsar ƙafarsa ta dama. Musa ya kuma kawo ’ya’yan Haruna gaba, ya sa jini a leɓatun kunnuwansu na dama, ya kuma sa a manyan yatsotsinsu na hannun dama da kuma a manyan yatsotsinsu na ƙafafunsu na dama. Sa’an nan ya yayyafa jinin a kowane gefen bagade. Ya ɗibi kitsen, da wutsiya mai kitse, da kuma dukan kitsen da ke kewaye da kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, ƙodoji biyu da kitsensu da kuma cinya ta dama. Sa’an nan daga cikin kwandon burodi marar yisti wanda yake a gaban Ubangiji, ya ɗauko dunƙulen burodi, da kuma guda da aka yi da mai, da kuma ƙosai; ya sa waɗannan a sassan kitsen, da kuma a cinya ta dama. Ya sa waɗannan a hannuwan Haruna da ’ya’yansa, suka kuma kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Sa’an nan Musa ya karɓe su daga hannuwansu ya ƙone a bagade a bisa hadaya ta ƙonawa a matsayin hadaya ta naɗi, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Ya kuma ɗauki ƙirjin; rabon Musa na ɗan ragon naɗi, ya kaɗa shi a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, yadda Ubangiji ya umarce shi. Sai Musa ya ɗibi man keɓewa da jini daga bagade, ya yayyafa su a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan ’ya’yansa da rigunansu, don yă tsarkake Haruna da rigunansa da kuma ’ya’yansa da rigunansu. Sai Musa ya ce wa Haruna da ’ya’yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar Tentin Sujada, ku kuma ci shi a can tare da burodi daga kwandon naɗi, yadda na umarta, cewa,8.31 Ko kuwa aka umarce ni ‘Haruna da ’ya’yansa maza za su ci shi.’ Sa’an nan ku ƙone sauran naman da kuma burodin. Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada har kwana bakwai, sai ranakun naɗi suka cika, gama naɗinku zai ɗauki kwana bakwai. Abin da aka yi a yau umarni ne daga Ubangiji don yin kafara saboda ku. Dole ku kasance a ƙofar Tentin Sujada dare da rana har kwana bakwai, ku kuma yi abin da Ubangiji yake bukata, don kada ku mutu; gama abin da aka umarce ni ke nan.” Saboda haka Haruna da ’ya’yansa maza suka yi kome da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa. Firistoci sun kama aikinsu A rana ta takwas, Musa ya kira Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dattawan Isra’ila. Ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki ɗan maraƙi domin hadayarka don zunubi da kuma ɗan rago domin hadaya ta ƙonawa, dukan biyu su kasance marar lahani, ka miƙa su a gaban Ubangiji. Sa’an nan ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ku ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi, da ɗan maraƙi bana ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya marasa lahani, don hadaya ta ƙonawa, da bijimi da rago don hadayun salama, a yi hadaya da su ga Ubangiji, da hadaya ta gari da aka kwaɓa da mai, gama yau Ubangiji zai bayyana a gare ku.’ ”9.4 Kalmar Ibraniyanci za tă iya haɗa namiji da ta mace; haka ma a ayoyi 18 da 19. Suka ɗauki abubuwan da Musa ya umarta zuwa gaban Tentin Sujada, sai dukan jama’a suka zo kusa suka tsaya a gaban Ubangiji. Sa’an nan Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarce ku ku yi, domin ɗaukakar Ubangiji za tă bayyana gare ku.” Musa ya ce wa Haruna, “Matsa kusa da bagaden, ka miƙa hadayarka don zunubi, da hadayarka ta ƙonawa, ka yi kafara don kanka da kuma don jama’a. Ka kuma kawo hadayar jama’a, ka yi kafara dominsu kamar yadda Ubangiji ya umarta.” Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa. ’Ya’yan Haruna maza suka kawo masa jinin, ya kuma tsoma yatsarsa a cikin jinin ya zuba cikin ƙahonin bagade; sauran jinin kuwa ya zuba a gindin bagaden. A kan bagaden, ya ƙone kitsen, ƙodojin, da abin da ya rufe hanta, daga hadaya don zunubi, yadda Ubangiji ya umarci Musa. Naman da fatar kuwa ya ƙone waje da sansanin. Sa’an nan ya yanka hadaya ta ƙonawa. ’Ya’yan Haruna maza suka miƙa masa jinin, ya kuwa yayyafa shi a kowane gefe na bagaden. Suka miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa-gunduwa, haɗe da kan, ya kuwa ƙone su a bisa bagaden. Sai ya wanke kayan ciki da ƙafafun, ya kuwa ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Sa’an nan Haruna ya kawo hadayar da take domin mutane. Ya ɗauki akuya ta hadaya don zunubin mutane, ya yanka shi, ya miƙa shi domin hadaya don zunubi kamar yadda ya yi da na farko. Ya kawo hadaya ta ƙonawa ya kuma miƙa ta yadda aka tsara. Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗiba a tafi hannu ya ƙone a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa ta safe. Haruna ya yanka maraƙin da ragon a matsayin hadaya ta salama domin mutane. ’Ya’yansa maza suka miƙa masa jinin, ya kuwa yayyafa shi a kowane gefe na bagade. Amma sashen kitsen maraƙin da na ragon, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki, da ƙodoji da kuma kitsen da ya rufe hanta, suka shimfiɗa waɗannan a kan ƙirjin, sa’an nan Haruna ya ƙone kitsen a kan bagade. Sai Haruna ya kaɗa ƙirjin da kuma cinyar dama a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa, kamar yadda Musa ya umarta. Sa’an nan Haruna ya ɗaga hannuwansa wajen mutane ya sa musu albarka. Da yake ya miƙa hadaya don zunubi, hadaya ta ƙonawa da kuma hadaya ta salama, sai ya sauka. Sai Musa da Haruna suka shiga cikin Tentin Sujada. Da suka fita, sai suka sa wa mutane albarka; sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutane. Sai wuta ta fito daga gaban Ubangiji ta cinye hadaya ta ƙonawa da sassan kitsen a kan bagaden. Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suna farin ciki, suka fāɗi rubda ciki, suka yi sujada. Mutuwar Nadab da Abihu ’Ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka ɗauki farantansu, suka sa wuta a ciki, suka zuba turare a kai; suka kuma miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba. Sai wuta ta fito daga Ubangiji ta cinye su, suka kuma mutu a gaban Ubangiji. Sai Musa ya ce Haruna, “Ga abin da Ubangiji yake nufi sa’ad da ya ce, “ ‘A cikin waɗanda suka kusace ni za a tabbata ni mai tsarki ne; a fuskar dukan mutane za a kuwa girmama ni.’ ” Haruna ya yi shiru. Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan, ’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki ’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.” Sai suka zo suka ɗauke su, suna nan cikin taguwoyinsu, zuwa waje da sansani yadda Musa ya umarta. Sa’an nan Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza, “Kada ku bar gashin kanku barkatai,10.6 Ko kuwa Kada ku buɗe kawunanku kada kuma ku yage tufafinku, don kada ku mutu. Yin haka zai jawo fushin Ubangiji a kan dukan jama’a. Amma dangoginku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya hallaka da wuta. Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada ko kuwa ku mutu, domin man Shafan Ubangiji yana kanku.” Saboda haka suka yi kamar yadda Musa ya faɗa. Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce, “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa. Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta, za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.” Musa ya ce wa Haruna da Eleyazar da Itamar ’ya’yansa maza da suka ragu, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji ku ci ba tare da yisti ba, a gefen bagaden, gama tsattsarka ne. Ku ci shi a tsattsarkan wuri, gama rabonka ne da na ’ya’yanka daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji; gama haka aka umarce ni. Amma kai da ’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma ’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa. Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da ’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.” Sa’ad da Musa ya nemi sani game da akuyar hadaya don zunubi, ya kuwa gane cewa an ƙone shi, sai ya yi fushi da Eleyazar da kuma Itamar, ’ya’yan Haruna maza da suka ragu, ya kuma yi tambaya, “Me ya sa ba ku ci hadaya don zunubi a cikin wuri mai tsarki ba? Mafi tsaki ne; an ba ku ne don a ɗauke laifin jama’a ta wurin yin kafara saboda su a gaban Ubangiji. Da yake ba a kai jininsa cikin wuri mai tsarki ba, ya kamata ku ci akuyar a wuri mai tsarki, kamar yadda na umarta.” Sai Haruna ya amsa wa Musa, “Yau sun miƙa hadayarsu don zunubi da kuma hadayarsu ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?” Da Musa ya ji haka, sai ya gamsu. Abinci mai tsabta da marar tsabta (Maimaitawar Shari’a 14.3-21) Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ku ce wa Isra’ilawa, ‘Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci. Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa. “ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku. Rema, ko da yake tana tuƙa, duk da haka ba ta da rababben kofato; saboda haka namanta haram ne gare ku. Zomo, ko da yake yana tuƙa, duk da haka ba shi da rababben kofato; saboda haka namansa haram ne gare ku. Alade, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, saboda haka namansa haram ne gare ku. Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawwakinsu, gama haram ne gare ku. “ ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori. Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku. Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu. Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa. “ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu, shirwa, da duk wani irin baƙin shirwa, kowane irin hankaka, mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho, ƙaramin ƙururu, babba da jaka, zalɓe, kazar ruwa, kwasakwasa, da ungulu, shamuwa, kowane irin jinjimi, katutu da kuma jamage.11.19 Cikakkun sunayen waɗansu tsuntsaye, ƙwari da dabbobi a wannan sura ba tabbatattu ba ne. “ ‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku. Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle. Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu. Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku. “ ‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana. Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma. “ ‘Kowace dabbar da ba ta da rababben kofato ko ba ta tuƙa, haram ce gare ku; duk wanda ya taɓa gawarsu zai ƙazantu. Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma. Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku. “ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa, da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo. Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma. Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka. In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar. Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne. Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu. Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu. In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta. Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku. “ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma. “ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba. Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa. Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. “ ‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa. Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’ ” Tsabtaccewa bayan haihuwa Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta. A rana ta takwas, za a yi wa yaron kaciya. Sa’an nan dole macen ta jira kwana talatin don a tsabtacce ta daga zub da jini. Ba za tă taɓa wani abu mai tsarki, ko ta je wuri mai tsarki ba sai kwanakin tsabtaccewarta sun cika. In ta haifi ’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta. “ ‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko ’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi. Firist zai miƙa su a gaban Ubangiji don yă yi kafara dominta, sa’an nan tă tsabtacce daga zub da jininta. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin macen da ta haifi ɗa namiji ko ’ya ta mace. In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’ ” Ƙa’idodi game cututtukan fatar jiki Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Sa’ad da wani yana da kumburi, ko ɓamɓaroki, ko tabo a fatar jikinsa da zai iya zama cutar fatar jiki,13.2 A al’adance kuturta; an yi amfani da ma’anar kalmar Ibraniyancin nan don cututtuka dabam-dabam da yake shafan fatar jiki, ba lalle kuturta ba; haka ma a ko’ina a cikin wannan sura. dole a kawo shi ga Haruna firist, ko kuwa ga ɗaya a cikin ’ya’yansa maza13.2 Ko kuwa zuriya wanda yake firist. Firist zai bincika mikin da yake a fatar mai cutar, in gashin a mikin ya juya ya zama fari, mikin kuma ya zama kamar ya fi zurfin fatar jiki, wannan cutar kuturta ce. Sa’ad da firist ya bincike shi, zai furta shi marar tsarki. In tabon a fata jikinsa fari ne amma bai zama ya fi zurfin fatar jikin ba, gashin a cikinsa kuma bai juya ya zama fari ba, firist ɗin zai kaɗaice mai cutar na kwana bakwai. A rana ta bakwai firist zai bincike shi, in kuwa ya ga cewa mikin bai canja ba, bai kuwa yaɗu a fatar jikin ba, zai kaɗaice shi na waɗansu ƙarin kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin firist zai sāke bincike shi, in kuwa mikin ya bushe bai kuwa yaɗu a fatar jikin ba, firist ɗin zai furta shi mai tsarki; ƙurji ne kawai. Dole mutumin yă wanke rigunansa, zai kuma tsarkaka. Amma in ƙurjin ya yaɗu a fatar jikinsa bayan ya nuna kansa ga firist don a furta shi tsarkake, dole yă sāke bayyana a gaban firist. Firist ɗin zai bincike shi, in ƙurjin ya yaɗu a fatar jikinsa, zai furta shi marar tsarki; cuta ce mai yaɗuwa. “Sa’ad da wani yana da cutar fatar jiki, dole a kawo shi ga firist. Firist zai bincike shi, in kuwa farin kumburi a fatar jikin ya juyar da gashin fari in kuma akwai sabon miki a kumburi, to, cutar fatar jikin ne mai ƙarfi kuma firist zai furta shi marar tsarki. Ba zai kaɗaice shi ba, domin ya riga ya zama marar tsarki. “In cutar ta fashe ko’ina a fatar jiki, har iyakar ganin firist, ta rufe dukan fatar jikin mai fama da cutar, daga kai har zuwa ƙafa, firist zai bincike shi, in cutar ta riga ta rufe dukan jikinsa, zai furta wannan mutum tsarkakakke ne. Da yake ya juya fari fat, tsarkakakke ne. Amma sa’ad da sabon miki ya bayyana a jikinsa, zai furta shi marar tsarki. Sa’ad da firist ɗin ya ga sabon miki, zai furta shi marar tsarki. Sabon mikin marar tsarki, yana da cuta mai yaɗuwa. A ce sabon mikin ya canja ya juya fari, dole yă je wurin firist. Firist zai bincike shi, in kuma mikin ya juya ya zama fari, firist zai furta mai cutar tsarkakakke; to, zai zama tsarkakakke. “Sa’ad da wani yana da kumburi a fatar jikinsa ya kuma warke, kuma a inda ƙurjin yake, wani farin kumburi ko tabo ja-ja, fari-fari ya bayyana, dole yă gabatar da kansa ga firist. Firist zai bincike shi, in kuma ya zama ya fi fatar jiki zurfi kuma gashinsa ya juya ya zama fari, firist ɗin zai furta shi marar tsarki. Cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu a inda ƙurjin yake. Amma in sa’ad da firist ya bincike shi, ya tarar babu farin gashi a ciki, kuma bai yi zurfi fiye da fatar jikin ba, ya kuma bushe, sai firist ɗin ya kaɗaice shi har kwana bakwai. In yana yaɗuwa a cikin fatar jikin, firist zai furta shi marar tsarki; cuta mai yaɗuwa ce. Amma in tabon bai canja ba, bai kuma yaɗu ba, tabo ne kawai daga ƙurji, kuma firist zai furta shi tsarkakakke. “Sa’ad da wani yana da ƙuna a fatar jikinsa, wurin kuwa ya yi ja-ja, ko fari-fari, ko kuwa farin tabo ya bayyana a sabon miki na ƙunan, firist zai bincike tabon, idan kuma gashin a cikinsa ya juya ya zama fari, kuma ya yi zurfi fiye da fatar jikin, cuta ce mai yaɗuwa da ta fasu daga ƙunan. Firist zai furta shi marar tsarki; cuta ce mai yaɗuwa. Amma in firist ɗin ya bincike shi bai kuwa ga wani farin gashi a wurin ba, in kuma bai yi zurfi fiye da fatar jikin ba, ya kuma bushe, to, firist ɗin zai kaɗaice shi na kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin firist zai bincike shi, in kuma cutar tana yaɗuwa a cikin fatar jikin, firist ɗin zai furta shi marar tsarki, cutar fatar jiki ce mai yaɗuwa. In kuma wurin bai canja ba, bai kuma yaɗu cikin fatar jikin ba amma ya bushe, kumburi ne daga ƙuna, firist ɗin kuwa zai furta shi tsarkakakke; tabo ne kawai daga ƙuna. “In namiji ko ta mace tana da miki a kai ko kuwa a gemu, firist zai bincike mikin, in ya yi zurfi fiye da fatar jiki, gashin ya zama rawaya, ya kuma zama siriri, firist zai furta wannan mutum marar tsarki; ƙaiƙayi ne, cuta mai yaɗuwa ce na kai ko na gemu. Amma in, sa’ad da firist ya bincika wannan irin mikin, bai yi zurfi fiye da fatar jiki ba kuma babu baƙin gashi a cikinsa, firist ɗin zai kaɗaice mutum mai fama da cutar, kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin firist zai bincika mikin in kuwa ƙaiƙayin bai bazu ba, ba rawayan gashi kuma a ciki, babu zurfin da yake fiye da fatar jiki, dole a yi masa aski, sai dai ba zai aske wurin cutar ba, kuma firist zai kaɗaice shi kwana bakwai. A rana ta bakwai firist zai bincike ƙaiƙayin, idan bai bazu a fatar jikin ba, bai kuma yi zurfin fiye da fatar jikin ba, firist ɗin zai furta shi tsarkakakke. Dole kuma yă wanke rigunansa, zai kuwa zama tsarkakakke. Amma in ƙaiƙayin ya yaɗu a cikin fatar jikin bayan aka furta shi tsarkakakke, firist ɗin zai bincike shi, in kuma ƙaiƙayin ya yaɗu a fatar jikin, firist ɗin ba ya bukatar neman ganin rawayan gashi; mutumin marar tsarki ne. In fa a ganinsa bai canja ba kuma baƙin gashi ya fito a cikinsa, ƙaiƙayin ya warke ke nan. Mutumin tsarkakakke ne, firist ɗin kuwa zai furta shi tsarkakakke. “Sa’ad da namiji ko ta mace tana da farare wurare a fatar jiki, firist ya bincika su, in kuma wuraren toka-toka ne, to, ƙurji marar lahani ne ya faso a fatar jikin; wannan mutum tsarkakakke. “Mutumin da ya rasa gashi kansa ya zama mai sanƙo ke nan, duk da haka mutumin tsattsarka ne. In ya rasa gashin goshinsa yana kuma da sanƙo a goshinsa, shi tsarkakakke ne. Amma in yana da miki ja-ja da ya yi fari a sanƙonsa ko a goshinsa, cuta mai yaɗuwa ce take fasuwa a kai ko a goshin. Sai firist ya bincike shi, in kuma kumburarren miki a kansa ko goshinsa ja-ja da fari-fari kamar cutar fatar jiki mai yaɗuwa ne, mutumin ya kamu da cutar kuma marar tsarki ne. Firist ɗin zai furta mutumin marar tsarki saboda mikin da yake a kansa. “Mutum mai wannan cuta mai yaɗuwa dole yă sa yagaggun riguna, yă kuma bar gashin kansa ba gyara, yă rufe sashe ƙasa na fuskarsa, sa’an nan yă riga cewa, ‘Marar tsarki! Marar tsarki!’ Muddin yana da cutar zai ci gaba da kasance marar tsarki. Dole yă yi zama shi kaɗai; dole yă yi zama waje da sansani. Ƙa’idodi game da cutar fatar jiki a riguna “In akwai cutar fatar jiki a riguna, duk wani rigar ulu ko na lilin, duk wani kayan zare, ko saƙa na lilin, ko ulu, duk wani kayan fata, ko wanda aka yi da fata, in kuma cutar a cikin rigar, ko fatar, ko kayan saƙan kore-kore ne, ko ja-ja, to, cutar fatar jiki da ake samu a riguna ce mai yaɗuwa, kuma dole a nuna wa firist. Firist ɗin zai bincike cutar fatar jikin da take a rigar, yă kuma kaɗaice kayan da abin ya shafe shi kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin zai bincike shi, in cutar rigar ta yaɗu, ko a tariyar zaren, ko a wadarin, ko a fatar, ko kuwa a duk abin da ake amfani da shi, to wannan muguwar cutar riga ce; kayan marar tsarki ne. Dole yă ƙone rigar, ko tariyar zaren, ko kayan da aka saƙa na ulu ko lilin, ko kuwa na kaya da aka yi da fatar, wanda cutar ta fāɗa wa, domin cutar rigar muguwa ce, dole a ƙone kayan. “Amma in sa’ad da firist ya bincike shi, cutar rigar ba ta yaɗu a rigar, ko a tariyar zare, ko a kayan da aka saƙa, ko a kayan da aka yi da fata ba, zai umarta cewa a wanke kayan da cutar ta shafa. Sa’an nan zai kaɗaice shi na waɗansu kwana bakwai. Bayan an wanke kayan da cutar ta shafa, firist zai bincike shi, in kuwa cutar rigar ba tă canja yadda take ba, ko da yake ba tă yaɗu ba, marar tsarki ce. In sa’ad da firist ya bincike shi, cutar rigar ta bushe bayan da aka wanke kayan, sai yă yage sashen da cutar ta shafa na rigar, ko fatar, ko tariyar zaren, ko kuwa na kayan da aka saƙa. Amma in ya sāke bayyana a rigar, ko a tariyar zaren, ko a kayan da aka saƙa, ko a kayan da aka yi da fatar, to, yana yaɗuwa ke nan, kuma dole a ƙone duk abin da yake da cutar rigar da wuta. Rigar, ko tariyar zare, ko kayan da aka saƙa, ko kuwa duk kayan da aka yi da fatar da aka wanke, aka kuma fid da cutar rigar, dole a sāke wanke shi, zai kuwa zama tsarkakakke.” Waɗannan su ne ƙa’idodi game da cutar fatar jiki na rigar ulu, ko rigar lilin, tariyar zare, ko kayan da aka saƙa, ko kuwa duk wani abin da aka yi da fata, don furta su tsarkakakke, ko kuwa marar tsarki. Tsabtaccewa daga cutar fatar jiki mai yaɗuwa Ubangiji ya ce wa Musa, “Waɗannan su ne ƙa’idodi domin mutumin da yake da cuta a lokacin tsabtaccewarsa, sa’ad da aka kawo shi ga firist. Firist zai fita waje da sansani ya bincike shi. In mutumin ya warke daga cutar fatar jiki mai yaɗuwa, firist zai umarta a kawo tsuntsaye biyu masu rai, masu tsabta da itacen al’ul, jan ƙyalle da kuma hizzob saboda mutumin da za a tsabtacce. Sa’an nan firist zai umarta a kashe ɗaya daga cikin tsuntsayen a bisa ruwa mai kyau a tukunyar laka. Zai ɗauki tsuntsu mai rai ya tsoma shi tare da itacen al’ul, jan ƙyalle da kuma hizzob cikin jinin tsuntsun da aka yanka a bisa ruwa mai kyau. Sau bakwai zai yayyafa wa mutumin da za a tsabtacce daga cutar mai yaɗuwa ya kuma furta shi tsarkakakke. Sa’an nan ya saki tsuntsu mai rai ɗin ya tafi. “Dole mutumin da aka tsabtaccen ya wanke rigunansa, ya aske dukan gashinsa ya kuma yi wanka; sa’an nan zai tsabtacce. Bayan wannan zai iya zo cikin sansani, amma dole yă tsaya waje da tentinsa kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin dole yă aske dukan gashinsa; dole yă aske kansa, gemunsa, gashin girarsa da sauran gashinsa. Dole yă wanke rigunansa ya kuma yi wanka, zai kuwa tsabtacce. “A rana ta takwas dole yă kawo ɗan rago da ’yar tunkiya bana ɗaya, kowane marar lahani, tare da rabin garwan gari mai laushi haɗe da mai domin hadaya ta gari, da kuma moɗa ɗaya na mai. Firist da ya furta shi tsarkakakke zai miƙa da wanda za a tsabtaccen da kuma hadayunsa a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. “Sa’ad da firist zai ɗauki ɗaya daga cikin ragunan ya kuma miƙa shi kamar hadaya don laifi, tare da moɗan mai; zai kaɗa su a gaban Ubangiji kamar hadaya kaɗawa. Zai yanka ɗan ragon a tsattsarkan wuri inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Gama yadda hadaya ta zunubi ta firist ne, haka hadaya domin laifi ma, hadaya ce mafi tsarki. Firist ɗin zai ɗiba jinin hadaya don laifin ya zuba a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsabtacce, a babbar yatsar hannunsa na dama a kuma a babbar yatsar ƙafa damansa. Firist ɗin zai ɗiba daga moɗan mai ɗin ya zuba a tafin hannunsa na hagu, ya tsoma yatsarsa ta dama cikin man da yake a tafin hannunsa, kuma da yatsar zai yayyafa man a gaban Ubangiji sau bakwai. Firist zai sa sauran mai da yake cikin tafinsa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsabtacce, a babbar yatsarsa na dama da kuma a babbar yatsar ƙafarsa ta dama, a bisa jinin hadaya don laifin. Sauran man a tafin hannunsa firist zai sa a kan wanda za a tsabtaccen ya kuma yi kafara dominsa a gaban Ubangiji. “Sa’an nan firist ɗin zai miƙa hadaya don zunubi ya kuma yi kafara saboda wannan da za a tsabtacce daga rashin tsarkinsa. Bayan haka, firist zai yanka hadaya ta ƙonawa ya miƙa ta a bagade, tare da hadaya ta gari, ya kuma yi kafara dominsa, zai kuwa tsabtacce. “In kuwa mutumin matalauci ne ba zai iya samu waɗannan ba, to, dole yă ɗauki ɗan rago guda kamar hadaya don laifi a kaɗa don a yi kafara dominsa, tare da humushin garwa gari mai laushi haɗe da mai don hadaya ta gari, da moɗa na mai, da kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, wanda zai iya samu, ɗaya domin hadaya don zunubi ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. “A rana ta takwas dole yă kawo su domin tsabtaccewarsa ga firist a ƙofar Tentin Sujada, a gaban Ubangiji. Firist zai ɗauki ɗan rago na hadaya don laifi tare da moɗa na mai, ya kaɗa su a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Zai yanka ɗan rago domin hadaya don laifi ya kuma ɗibi jinin ya sa a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsabtaccen, a babban yatsar hannun damansa da kuma a babban yatsar ƙafarsa na dama. Firist zai zuba man a tafin hannunsa na hagu, da yatsarsa na dama zai yayyafa man daga tafinsa sau bakwai a gaban Ubangiji. Daga cikin man da yake a tafinsa zai zuba a wuri da ya zuba jinin hadaya don laifi, a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsabtaccen, a babban yatsar hannun damansa da kuma a babban yatsar ƙafa damansa. Sauran man da yake cikin tafinsa firist ɗin zai zuba a kan wannan da za a tsabtaccen don a yi kafara dominsa a gaban Ubangiji. Sa’an nan zai miƙa kurciyoyi ko tattabarai, waɗanda mutumin zai iya, ɗaya14.31 Seftuwajin da Siriyak; Da Ibraniyanci kamar yadda mutumin zai iya, ɗaya kamar hadaya don zunubi ɗayan kuma kamar hadaya ta ƙonawa, tare da hadaya ta gari. Ta haka firist zai yi kafara a gaban Ubangiji a madadin wanda za a tsabtacce.” Waɗannan su ne ƙa’idodi domin mutumin da yake da cutar fatar jiki wanda kuma ba zai iya samun abubuwan hadaya ta kullum domin tsabtaccewarsa ba. Tsabtaccewa daga riga mai cutar fatar jiki Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Sa’ad da kuka shiga ƙasar Kan’ana, wadda nake ba ku kamar gādonku, na kuma sa yaɗuwa cutar fatar jiki a riga a cikin gida a wannan ƙasa, dole maigidan ya tafi ya faɗa wa firist ya ce, ‘Na ga wani abu da ya yi kamar cutar fatar jikin da take a riga a cikin gidana.’ Firist zai umarci a fitar da kome a gidan kafin ya shiga ya bincike cutar fatar jiki da take a rigar, saboda babu abin da yake gidan da za a furta marar tsarki ne. Bayan haka firist zai shiga ya dudduba gidan. Zai bincike cutar fatar jiki da take a riga a bangaye, in kuma yana da tabon kore-kore ko ja-ja da suka bayyana da suka yi zurfi fiye da saman bangon, firist ɗin zai fita a bakin ƙofar gidan ya rufe ta na kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin firist zai dawo don yă dudduba gidan. In cutar fatar jiki da take a riga ta yaɗu a bangayen, zai umarta a ciccire duwatsun da suke da cutar a zubar a wuri marar tsarki waje da birnin. Dole yă sa a kankare duka shafen bangon cikin gidan a kuma zuba kayan da aka kankare a wurin marar tsarki waje da birnin. Sai su ɗebi waɗansu duwatsu su sa a wuraren da suka ciccire waɗancan, su kuma ɗiba sabon laka su yi shafen gidan. “In cutar fatar jiki da take ta rigar ta sāke bayyana a gidan bayan an ciccire duwatsu aka kankare gidan aka kuma yi shafe, firist zai je ya bincika shi, in kuwa cutar ta bazu a gidan, to, muguwar cuta ce; gidan marar tsarki ne. Dole a rushe gidan, a fid da duwatsun, katakai da kuma dukan shafen daga birnin zuwa wuri marar tsarki. “Duk wanda ya shiga gidan yayinda aka rufe shi zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya kwana ko ya ci abinci a gidan dole yă wanke rigunansa. “Amma in firist ya zo ya bincika gidan kuma cutar fatar jiki da take ta rigar ba tă bazu ba bayan an yi wa gidan shafe, zai furta gidan tsarkakakke, domin cutar ta tafi. Don a tsabtacce gidan, zai ɗauki tsuntsaye biyu da itacen al’ul, jan ƙyalle da hizzob. Zai yanka ɗaya daga cikin tsuntsayen a bisa ruwa mai kyau a cikin tukunyar laka. Sa’an nan zai ɗauki itacen al’ul, hizzob, jan ƙyalle da kuma tsuntsu mai ran ya tsoma su cikin jinin tsuntsun da aka yanka da kuma cikin ruwa mai kyau, ya yayyafa wa gida sau bakwai. Zai tsabtacce gidan da jinin tsuntsun, ruwa mai kyau, tsuntsu mai ran, itacen al’ul, hizzob da kuma jan ƙyalle. Sa’an nan zai saki tsuntsu mai rai ɗin a fili waje da birnin ya tafi. Ta haka zai yi kafara saboda gidan, gidan kuwa zai zama tsarkakakke.” Waɗannan su ne ƙa’idodi saboda duk wani cuta mai yaɗuwa, don ƙaiƙayi, don cutar fatar jiki da take a riga ko a cikin gida, da kuma don kumburi, ɓamɓaroki ko tabo, don a tabbatar sa’ad da wani abu mai tsarki da marar tsarki. Waɗannan su ne ƙa’idodi domin cutar fatar jiki mai yaɗuwa da cutar fatar jikin da take a riga. Mugunyar da ke sa ƙazantuwa Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Yi wa Isra’ilawa magana, ku ce musu, ‘Duk sa’ad da wani namiji yake ɗiga daga azzakarinsa, wannan ɗiga marar tsarki ne. Ko ɗigar ta ci gaba da fitowa daga azzakarinsa ko an tsere ta, za tă sa mutumin yă zama marar tsarki. Ga yadda ɗigarsa za tă kawo ƙazantuwa, “ ‘Duk gadon da mutumin mai ɗigar ya kwanta a kai, zai zama marar tsarki, kuma duk abin da ya zauna a kai, zai zama marar tsarki. Duk wanda ya taɓa gadonsa dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma. Duk wanda ya zauna a inda wannan mai ɗiga ya zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma. “ ‘Duk wanda ya taɓa jikin mai ɗiga, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. “ ‘In mai ɗiga ya tofa miyau a kan wani wanda yake tsarkakakke, dole tsarkakakken nan yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. “ ‘Kowane sirdi da mai ɗigar ya zauna a kai zai ƙazantu, kuma duk wanda ya taɓa wani abu cikin abubuwan da suke a ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har yamma; duk wanda ya ɗauki abubuwan nan dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma. “ ‘Duk wanda mai ɗiga ya taɓa ba tare da ya wanke hannuwansa da ruwa ba, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. “ ‘Dole a farfashe tukunya lakar da mutumin ya taɓa, kuma dole a ɗauraye duk wani abin da aka yi da katako wanda ya taɓa da ruwa. “ ‘Sa’ad da aka tsabtacce mai ɗigar, zai ɗauki kwana bakwai don tsabtaccewarsa; dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka mai tsabta, zai kuwa zama tsarkakakke. A rana ta takwas dole yă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, yă zo gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada, yă ba da su ga firist. Firist ɗin zai miƙa su, ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mai ɗigar. “ ‘Sa’ad da namiji ya ɗigar maniyyi, dole yă wanke jikinsa gaba ɗaya da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma. Dole a wanke duk riga ko fatar da yake da maniyyin a kansa da ruwa, zai kuma ƙazantu har yamma. Sa’ad da namiji ya kwana da mace ya kuwa zub da maniyyi, dole dukansu biyu su yi wanka, za su kuma ƙazantu har yamma. “ ‘Sa’ad mace take al’adarta ta ƙa’ida, rashin tsabtarta ta al’adar zai ɗauki kwana bakwai, kuma duk wanda ya taɓa ta, zai ƙazantu har yamma. “ ‘Duk abin da ta kwanta a kai a lokacin al’adarta zai ƙazantu, kuma duk abin da ta zauna a kai zai ƙazantu. Duk wanda ya taɓa gadonta dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. Duk wanda ya taɓa wani abin da ta zauna a kai, dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. Ko gado ne, ko kuwa wani abin da ta zauna a kai, sa’ad da wani ya taɓa shi, zai ƙazantu har yamma. “ ‘In namiji ya kwana da ita, al’adarta kuwa ta taɓa shi, zai ƙazantu na kwana bakwai; duk kuma gadon da ya kwanta a kai, zai ƙazantu. “ ‘Idan mace tana ɗigar jini na tsawon kwanaki, ban da kwanakin ganin al’adarta, ko kuwa idan al’adarta ya wuce yawan kwanakin da ya kamata, to, za tă ƙazantu daidai kamar na kwanakin al’adar da ta saba yi. Wato, muddin tana cikin ɗiga, ta zama mai ƙazanta. Duk gadon da ta kwanta yayinda ta ci gaba da ɗiga zai zama marar tsarki, kamar yadda gadonta yake a lokacin al’adarta, kuma duk abin da ta zauna a kai zai zama marar tsarki, kamar yadda yake a lokacin al’adarta. Duk wanda ta taɓa su zai zama marar tsarki; dole yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma. “ ‘Sa’ad da aka tsabtacce ta daga ɗigarta, dole tă ɗauki kwana bakwai, bayan haka za tă zama mai tsarki. A rana ta takwas, dole tă ɗauki kurciyoyi biyu ko tattabari biyu ta kawo su ga firist a bakin ƙofar Tentin Sujada. Firist zai miƙa ɗaya saboda hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara dominta a gaban Ubangiji saboda ƙazantar ɗigarta. “ ‘Ta haka za ka tsarkake Isra’ilawa daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da wurin zamana wanda yake tsakiyarsu.’ ” Waɗannan su ne ƙa’idodi a kan wanda yake ɗiga, da wanda yake zubar da maniyyi, ƙa’idodi ne kuma ga mace wadda take al’ada, ga namiji ko macen da take ɗiga, ga kuma namijin da ya kwana da mace marar tsarki. Ranar kafara Ubangiji ya yi magana da Musa bayan mutuwar ’ya’yan Haruna biyu maza waɗanda suka mutu sa’ad da suka kusaci Ubangiji. Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan’uwanka Haruna, kada yă riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule koyaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada yă mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin. “Ga yadda Haruna zai shiga wuri mai tsarki, zai zo da ɗan bijimi domin hadaya don zunubi da kuma rago domin hadaya ta ƙonawa. Zai sa toguwar lilin mai tsarki, tare da ɗan ciki na lilin; zai yi ɗamara da igiya kewaye da shi, yă kuma sa hular lilin. Waɗannan su ne riguna masu tsarki; saboda haka dole yă yi wanka kafin yă sa su. Zai ɗauki bunsurai biyu daga jama’ar Isra’ilawa na hadaya don zunubi da ɗan rago don hadaya ta ƙonawa. “Haruna zai miƙa bijimi hadaya don zunubinsa yă kuma yi kafara don kansa da gidansa. Sa’an nan zai ɗauki bunsurai biyu yă miƙa su a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Haruna zai jefa ƙuri’a don awaki biyun ɗin, ƙuri’a ɗaya domin Ubangiji, ɗayan kuma don azazel16.8 Wato, akuya don cirewa; Ibraniyanci azazel, haka ma a ayoyi 10 da 26. Haruna zai kawo akuyar da ƙuri’a ta fāɗi a kai wa Ubangiji yă miƙa ta na hadaya don zunubi. Amma za a miƙa akuyar da aka zaɓa ta wurin ƙuri’a a matsayi ta azazel da rai a gaban Ubangiji don a yi amfani da ita don kafara ta wurin korinta zuwa cikin jeji kamar azazel. “Haruna zai kawo bijimi domin hadayarsa ta zunubi don yă yi kafara wa kansa da kuma domin gidansa, zai kuma yanka bijimin domin nasa hadaya don zunubi. Zai ɗauki faranti cike da garwashin wuta daga bagade a gaban Ubangiji, yă kuma cika hannunsa biyu da turare mai ƙanshin da aka niƙa yă kai su bayan labule. Zai sa turaren a wuta a gaban Ubangiji, hayaƙin turaren kuwa zai rufe murfin kafarar a bisa Akwatin Alkawari, don kada yă mutu. Zai ɗibi jinin bijimin da yatsarsa yă yayyafa a gaban murfin kafarar; sa’an nan yă yayyafa jinin da yatsarsa sau bakwai a gaban murfin kafarar. “Sa’an nan zai yanka akuya na hadaya don zunubi saboda mutane, yă kai jinin bayan labule, yă yi da shi yadda ya yi da jinin bijimin. Zai yayyafa shi a kan murfin kafarar da kuma a gabansa. Ta haka zai yi kafara domin Wuri Mafi Tsarki saboda ƙazantar tawayen Isra’ilawa, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka zai yi saboda Tentin Sujada wanda yake a cikinsu a tsakiyar ƙazantarsu. Kada kowa yă kasance a Tentin Sujada daga lokacin da Haruna ya shiga don yă yi kafara a Wuri Mafi Tsarki har sai ya fita, bayan ya yi kafara domin kansa, gidansa da kuma dukan jama’ar Isra’ila. “Sa’an nan zai fita zuwa bagade da yake a gaban Ubangiji, yă yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimi da na akuya yă zuba a ƙahonin bagade. Zai yayyafa jinin a kan bagade da yatsarsa sau bakwai, yă tsabtacce shi yă kuma tsarkake shi daga ƙazantar Isra’ilawa. “Sa’ad da Haruna ya gama yin kafara domin Wuri Mafi Tsarki, Tentin Sujada da kuma bagade, sai yă kawo akuya mai rai. Haruna zai ɗibiya hannuwansa a kan akuya mai ran, yă furta a kansa dukan mugunta da tawayen Isra’ilawa, dukan zunubansu, yă kuma sa su a kan akuyan. Zai kori akuyan zuwa cikin jeji a hannun mutumin da aka ba shi aikin yin haka. Akuyan zai ɗauka a kansa dukan zunubansu zuwa kaɗaitaccen wuri, a can mutumin zai sake shi a jeji. “Sa’an nan Haruna zai shiga Tentin Sujada yă tuɓe rigunansa na lilin da ya sa, kafin yă shiga Wuri Mafi Tsarki, zai kuma bar su a can. Zai yi wanka a tsattsarkan wuri yă sa rigunarsa na kullum. Sa’an nan zai fita yă miƙa hadaya ta ƙonawa domin kansa da hadaya ta ƙonawa domin mutane, don yă yi kafara domin kansa da kuma domin mutane. Zai kuma ƙone kitsen hadaya don zunubi a kan bagade. “Dole mutumin da ya saki akuya na azazel yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka; bayan haka zai iya shiga sansani. Dole a ɗauki jini, fata, nama da kuma ƙashin bijimi da akuyan hadaya don zunubi, waɗanda aka kawo jininsu cikin Wuri Mafi Tsarki don kafara, a kai waje da sansani a ƙone. Dole mutumin da ya ƙone su yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, bayan haka zai iya shiga sansani. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare ku. A rana ta goma ga wata na bakwai, dole ku yi mūsu kanku,16.29 Ko kuwa dole ku yi azumi; haka ma a aya 31. ba kuwa za ku yi wani aiki ba, ko da mutum baƙo ne a cikinku ko kuwa ɗan ƙasa, gama a wannan rana za a yi kafara dominku, don a tsarkake ku. Sa’an nan a gaban Ubangiji, za a tsarkake ku daga dukan zunubanku. Asabbaci ne don hutawa, kuma dole ku yi mūsun kanku; wannan dawwammamiyar farilla ce. Firist da aka keɓe aka kuma naɗa don yă gāji mahaifinsa a matsayin babban firist ne zai yi kafara. Zai sa rigunan lilin masu tsarki yă yi kafara domin Wuri Mafi Tsarki, Tentin Sujada da bagade, da kuma saboda firistoci da kuma dukan jama’ar Isra’ila. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce gare ku. Za a riƙa yin kafara sau ɗaya a shekara saboda dukan zunuban Isra’ilawa.” Aka kuma yi haka, yadda Ubangiji ya umarci Musa. An hana cin jini Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji ya umarta. Duk mutumin Isra’ilan da ya yanka sa,17.3 Kalmar Ibraniyanci ta ƙunshi namiji da ta macen sa ne. ɗan rago ko akuya a sansani ko waje da shi a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa. Wannan ya zama haka saboda Isra’ilawa su kawo wa Ubangiji hadayun da suke yi a filaye. Dole su kawo su ga firist, wato, ga Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, su miƙa su a matsayin hadayun salama. Firist zai yayyafa jinin a bagaden Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, yă kuma ƙone kitsen kamar ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare su wa tsararraki masu zuwa.’ “Faɗa musu, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko wani baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka kuma bai kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă miƙa shi ga Ubangiji ba, dole a raba wannan mutum da mutanensa. “ ‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa. Gama ran halitta yana a cikin jinin, kuma na ba da shi gare ku don kafara a kan bagade, jini ne yake kafara saboda ran mutum. Saboda haka na ce wa Isra’ilawa, “Babu waninku da zai ci jini, babu wani baƙon da yake zama a cikinku da zai ci jini.” “ ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa, domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.” “ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake. Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’ ” Jima’in da aka hana Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi wa Isra’ilawa magana ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku. Kada ku yi yadda suke yi a Masar inda da kuke zama, kuma ba a ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan’ana inda nake kawo ku ba. Kada ku yi yadda suke yin abubuwa. Dole ku kiyaye dokokina kuma ku lura ku bi farillaina. Ni ne Ubangiji Allahnku. Ku kiyaye farillaina da dokokina, gama mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada wani ya kusaci wani dangi na kusa don yă yi jima’i. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwana da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce; kada ka yi jima’i da ita. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar mahaifinka, wannan zai ƙasƙantar da mahaifinka. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwarka, ko ’yar mahaifinka ko ’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanka ko ’yar ’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita ’yar’uwarka ce. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifinka, ita dangin mahaifinka ne na kusa. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifiyarka, domin ita dangin mahaifiyarka ce na kusa. “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ɗan’uwan mahaifinka ta wurin kusaci matarsa don ka yi jima’i da ita, ita bābarka ce. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ne; kada ka yi jima’i da ita. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗan’uwanka; wannan zai ƙasƙanta ɗan’uwanka. “ ‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma ’yarta. Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanta ko ’yar ’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne. “ ‘Kada ka auri ’yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai. “ ‘Kada ka kusaci mace don ka yi jima’i da ita a lokacin ƙazantar al’adarta. “ ‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita. “ ‘Kada ku ba da wani daga cikin ’ya’yanku don a yi hadaya wa18.21 Ko kuwa don a tura cikin wuta Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne. “ ‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne. “ ‘Kada ku ƙazantar da kanku da wani daga cikin waɗannan, domin haka al’umman da zan kora a gabanku suka ƙazantu. Har ƙasar ma ta ƙazantu, saboda haka na hukunta ta saboda zunubinta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta. Amma dole ku kiyaye farillaina da kuma dokokina. Kada haifaffe ɗan ƙasa da baƙin da suke zama a cikinku yă yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, gama mutanen da suka zauna a wannan ƙasa kafin ku sun aikata dukan waɗannan abubuwa, suka kuma ƙazantu. Kuma in kuka ƙazantar da ƙasar, za tă amayar da ku kamar yadda ta amayar da al’umman da suka riga ku. “ ‘Duk wanda ya yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, dole a fid da mutumin daga cikin mutanensa. Ku kiyaye umarnaina kuma kada yi ku wata al’ada mai banƙyamar da aka yi kafin ku zo kuma kada ku ƙazantar da kanku da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Dokoki iri-iri Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne. “ ‘Dole kowannenku yă girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku juyo ga gumaka, ko ku yi wa kanku allolin da aka yi zubi da ƙarfe. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta yadda za tă karɓu a madadinku. Za a ci ta a ranar da kuka miƙa ta, ko kuwa a kashegarin; duk abin da ya rage har kwana ta uku dole a ƙone shi. In aka ci ta a rana ta uku, marar tsabta ce, ba kuma za a karɓe ta ba. Duk wanda ya ci ta zai zama da laifi domin ya ƙazantar da abin da yake da tsarki ga Ubangiji, dole a raba mutumin nan da mutanensa. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku. Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku yi sata. “ ‘Kada ku yi ƙarya. “ ‘Kada ku ruɗe juna. “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana. “ ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya. “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa. “ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji. “ ‘Ku kiyaye farillaina. “ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu. “ ‘In wani ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda aka yi wa wani alkawari amma bai fanshe ta ba, ko kuwa ba a ’yantar da ita ba, dole a yi hukuncin da ya dace. Duk da haka ba za a kashe su ba, domin ba a ’yantar da ita ba. Dole mutumin da ya kwana da ita yă kawo rago a ƙofar Tentin Sujada domin hadaya don laifi ga Ubangiji. Da ragon hadaya don laifin ne firist zai yi kafara saboda mutumin a gaban Ubangiji saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta zunubinsa. “ ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai ’ya’ya na ci, ku ɗauki ’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci.19.23 Da Ibraniyanci marasa kaciya Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba. A shekara ta huɗu, dukan ’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji. Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin ’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku ci wani abinci tare da jini a cikinsa. “ ‘Kada ku yi duba ko sihiri. “ ‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku. “ ‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta. “ ‘Ku kiyaye Asabbacina, ku kuma girmama wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji. “ ‘Sa’ad da baƙo yana zama tare da ku a ƙasarku, kada ku wulaƙanta shi. Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar. “ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da kuma dukan dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.’ ” Hukuntai don zunubi Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikin Isra’ila da ya miƙa20.2 Ko kuwa miƙa hadaya; haka ma a ayoyi 3 da 4. wani daga cikin ’ya’yansa wa Molek, dole sa kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi. Zan yi gāba da wannan mutum, zan kuma raba shi da mutanensa; gama ta wurin miƙa ’ya’yansa ga Molek, ya ƙazantar da wuri mai tsarkina, ya kuma ƙazantar da sunana mai tsarki. In mutanen ƙasar suka kau da idanunsu sa’ad da wannan mutum ya miƙa ’ya’yansa ga Molek, suka kāsa kashe shi, zan yi gāba da wannan mutum da iyalinsa, zan raba shi da kuma duk waɗanda suka bi shi cikin karuwanci ga Molek daga mutanensu. “ ‘Zan yi gāba da mutumin da ya juyo ga masu duba da bokaye, don yă yi karuwanci ta wurin bin su, zan kuma raba shi daga mutanensa. “ ‘Ku tsarkake kanku, ku kuma zama da tsarki, gama Ni ne Ubangiji Allahnku. Ku kiyaye farillaina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.20.8 Ko kuwa wanda ya tsarkake ku; Ko kuwa wanda ya keɓe masu tsarki “ ‘In wani ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi. Domin ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, alhakin jininsa zai zauna a kansa. “ ‘In mutum ya yi zina da matar wani, da matar maƙwabcinsa, dole a kashe su biyu da suka yi zinan. “ ‘In mutum ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa. Dole a kashe shi da macen, alhakin jininsu zai zauna a kansu. “ ‘In mutum ya kwana da matar ɗansa, dole a kashe su biyun. Abin da suka yi haram ne; alhakin jininsu zai zauna a kansu. “ ‘In mutum ya kwana da mutum kamar yadda ake kwana da mace, su biyun sun yi abin ƙyama. Dole a kashe su, alhakin jininsu zai zauna a kansu. “ ‘In mutum ya auri ’ya da mahaifiyarta, mugun abu ne. Da shi da su, dole a ƙone su da wuta, saboda kada mugun abu yă kasance a cikinku. “ ‘In mutum ya yi jima’i da dabba, dole a kashe shi, dole kuma ku kashe dabbar. “ ‘In mace ta kusaci dabba don tă yi jima’i da ita, ku kashe macen da dabbar. Dole a kashe su; alhakin jininsu zai zauna a kansu. “ ‘In mutum ya auri ’yar’uwarsa, ko ’yar mahaifinsa, ko kuwa ta mahaifiyarsa, suka kuma yi jima’i, abin kunya ne. Dole a raba su a idanun mutanensu. Ya ƙasƙantar da ’yar’uwarsa kuma za a nemi hakki daga gare shi. “ ‘In mutum ya kwana da mace a lokacin al’adarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama’arsu, gama sun karya ƙa’idodi a kan rashi tsarki. “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifiyarka, ko ta mahaifinka, gama wannan zai ƙasƙantar da dangi na kurkusa, dukanku za ku ɗauki laifin. “ ‘In mutum ya kwana da bābarsa, ya ƙasƙantar da kawunsa ke nan. Hakkin zai kasance a kansu, za su mutu babu ’ya’ya. “ ‘In mutum ya auri matar ɗan’uwansa, aikin rashin tsabta ne, ya ƙasƙantar da ɗan’uwansa ke nan. Za su mutu babu ’ya’ya. “ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da dokokina duka, don kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku. Kada ku yi zama bisa ga al’adun al’umman da zan kora a gabanku. Domin sun aikata dukan waɗannan abubuwa, na yi ƙyamarsu. Amma na faɗa muku, “Za ku mallaki ƙasarsu, zan ba ku ita gādo, ƙasa mai zub da madara da zuma.” Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga al’ummai. “ ‘Saboda haka sai ku bambanta tsakanin dabbobi masu tsarki da marasa tsarki, da kuma tsakanin tsuntsaye masu tsarki da marasa tsarki. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wata dabba, ko tsuntsu, ko wani abin da yake rarrafe a ƙasa, waɗanda na keɓe a matsayi marasa tsarki a gare ku. Ku zama tsarkakakke gare ni, gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, na kuma keɓe ku daga al’ummai don ku zama nawa. “ ‘Namiji, ko ta macen da yake mai duba, ko maita a cikinku dole a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu; alhakin jininsu zai zauna a kansu.’ ” Dokoki domin firistoci Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da firistoci, ’ya’yan Haruna maza, ka ce musu, ‘Kada firist yă ƙazantar da kansa saboda wani cikin mutanensa da suka mutu, sai dai na danginsa na kusa, kamar mahaifiyarsa ko mahaifinsa, ɗansa ko ’yarsa, ɗan’uwansa, ko ’yar’uwarsa da ba tă riga ta yi aure ba, wadda take dogara gare shi, da yake ba ta da miji, saboda ita zai iya ƙazantar da kansa. Kada yă ƙazantar da kansa saboda mutanen da suke da dangantakar da shi ta wurin aure, ta yin haka zai ƙazantar da kansa. “ ‘Kada firistoci su aske kansu ƙwal ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsage jikunansu. Dole su kasance masu tsarki ga Allahnsu, kada kuma su ɓata sunan Allahnsu. Domin sukan miƙa hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta, abincin Allahnsu, saboda haka sai su kasance da tsarki. “ ‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu. An ɗauke su da tsarki, domin suna miƙa abincin Allahnku. An ɗauka su masu tsarki gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, Ni wanda ya mai da ku masu tsarki. “ ‘In ’yar firist ta ɓata kanta ta wurin zama karuwa, ta kunyatar da mahaifinta ke nan; dole a ƙone ta da wuta. “ ‘Babban firist, wanda yake ɗaya cikin ’yan’uwansa wanda aka shafe da mai a kansa, wanda kuma aka naɗa don yă sa rigunan firistoci, kada yă bar gashin kansa buzu-buzu, ko ya kyakketa rigunansa. Ba zai shiga inda akwai gawa ba. Kada yă ƙazantar da kansa, ko ma ta mahaifinsa ce ko ta mahaifiyarsa. An keɓe shi domina, kada yă ƙazantar da kansa, kada kuwa yă ɓata Tentin Sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce. Ni ne Ubangiji. “ ‘Dole macen da zai aura ta kasance budurwa. Ba zai auri matan da mijinta ya mutu, ko macen da mijinta ya rabu da ita, ko macen da ta ɓata kanta ta wurin karuwanci ba, sai dai yă auri budurwa daga cikin mutanensa, don kada yă ƙazantar da ’ya’yansa a cikin mutanensa. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da shi mai tsarki.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Haruna cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani yă zo kusa domin yă miƙa hadaya ta ci gare ni. Duk mai lahani, ko makaho, ko gurgu, ko mai naƙasa, ko mai wani lahani a jiki; ko mai karyayyen ƙafa, ko mai karyayyen hannu, ko mai ƙusumbi, ko wada, ko wanda yake da lahani a ido, ko mai cuta mai sa ƙaiƙayi, ko mai kirci, ko wanda aka daƙe, ba zai yi kusa domin yă miƙa hadaya ba. Ba zuriyar Haruna firist, mai lahanin da zai zo kusa don yă miƙa hadayun da aka yi ga Ubangiji da wuta. Da yake yana da lahani, ba zai zo kusa don yă miƙa abincin Allahnsa ba. Zai iya cin abinci mafi tsarki na Allahnsa, haka ma abinci mai tsarki; duk da haka saboda lahaninsa, ba zai yi kusa da labule, ko yă yi kusa da bagade don kada yă ƙazantar da wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji wanda yake mai da su masu tsarki.’ ” Sai Musa ya faɗa wannan wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa. Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, su lura da tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka keɓe gare ni da bangirma, saboda ba za su ƙazantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Ubangiji. “Faɗa musu cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, in wani zuriyarku ya ƙazantu, duk da haka ya kusaci tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka keɓe ga Ubangiji, dole a raba wannan mutum daga gabana. Ni ne Ubangiji. “ ‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga, da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta, duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har yamma, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka tukuna. Sa’ad da rana ta fāɗi, zai zama tsarkakakke, bayan wannan kuwa zai iya cin tsarkakakkun hadayu, gama abincinsa ne. Kada yă ci wani abin da ya mutu mushe, ko wanda namun jeji suka yayyaga, don kada yă ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji. “ ‘Firistoci za su kiyaye umarnaina don kada su yi laifi su mutu saboda sun rena su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da su masu tsarki. “ ‘Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake yana zama tare da su, ko kuwa an ɗauke shi yana yin musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba. Amma in firist ya sayi bawa da kuɗi, ko kuwa in an haifi bawan a gidansa, wannan bawan zai iya cin tsattsarkan abincin. In ’yar firist ta auri wani da ba firist ba, ba za tă ci wani tsarkakakkun sadaka ba. Amma idan ’yar firist ta zama gwauruwa ko sakakkiya, ba ta da ’ya’ya, ta kuwa dawo don tă zauna a gidan mahaifinta kamar matashiya, za tă iya cin abincin. “ ‘In wani ya ci tsarkakakken abinci cikin kuskure, dole yă maido wa firist hadayar, yă kuma ƙara kashi ɗaya bisa biyar na tamanin abin. Firist ɗin ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun hadayun da Isra’ilawa suka kawo ga Ubangiji ta wurin barinsu su ci tsarkakakkun hadayu, ta yin haka su jawo wa kansu laifin da zai bukaci biya ba. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.’ ” Hadayun da ba a yarda da su ba Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa magana ka ce musu, ‘In waninku, ko mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a Isra’ila, ya kawo kyauta don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko don yă cika alkawari, ko kuwa a matsayin hadaya ta yardar rai, dole ku miƙa dabba namiji marar lahani, daga shanu, tumaki, ko awaki, domin yă zama yardajje a madadinku. Kada ku kawo wani abu mai lahani, domin ba zai zama yardajje ba a madadinku. Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta salama daga garken shanu, ko na tumaki, ga Ubangiji don yă cika wani alkawari na musamman, ko hadaya ta yardar rai, dole yă zama marar lahani, ko tabo, don yă zama yardajje. Kada ku miƙa wa Ubangiji dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko masu gundumi, ko masu ɗiga, ko masu susa, ko masu kirci. Kada ku sa wani daga cikin waɗannan a bisa bagade a matsayin hadaya, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Za ku iya miƙa hadaya ta yardar rai da maraƙi, ko tunkiya mai naƙasa, ko marar cikakken lafiya, amma ba za tă zama yardajje don cika alkawarin da aka yi ba. Ba za ku miƙa wa Ubangiji dabbar da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa ba. Ba za ku kuma karɓi irin waɗannan dabbobi daga hannun baƙi ku miƙa su a matsayin abinci ga Allahnku ba. Ba za su zama yardajje a madadinku ba, domin sun naƙasa, suna kuma da lahani.’ ” Ubangiji ya ce wa Musa, “Sa’ad da aka haifi ɗan maraƙi, tunkiya, ko akuya, sai yă kasance da mahaifiyarsa kwana bakwai. Daga rana ta takwas zuwa gaba, zai zama yardajje hadaya, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Kada a yanka saniya, ko tunkiya da ɗanta rana ɗaya. “Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, ku miƙa ta a yadda za tă zama yardajje a madadinku. Dole a ci hadayar a ranar; kada a bar saura sai da safe. Ni ne Ubangiji. “Ku kiyaye dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji. Kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Dole Isra’ilawa su gane Ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji, wanda ya keɓe ku a matsayin tsarkaka da kuma wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.” Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga ƙayyadaddun bukukkuwa, ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji, da za ku sanar wa mutane su riƙa kiyayewa, su zama lokutan tarurruka masu tsarki. Asabbaci “ ‘Akwai kwanaki shida da za ku iya yin aiki, amma rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, rana mai tsarki ga jama’a. Kada ku yi wani aiki a ko’ina kuke da zama, Asabbaci ne ga Ubangiji. Bikin Ƙetarewa da Burodi Marar Yisti (Ƙidaya 28.16-25) “ ‘Waɗannan su ne bukukkuwan da Ubangiji ya kafa da tsarkakakkun taron jama’a za su yi a ƙayyadaddun lokuta. Bikin Ƙetarewar Ubangiji, zai fara da yamma a ranar goma sha huɗu na wata na fari. A rana ta goma sha biyar na wannan wata, za a fara Bikin Burodi Marar Yisti na Ubangiji. Za ku yi kwana bakwai kuna cin burodi marar yisti. A rana ta fari, ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. Kwana bakwai za ku miƙa hadaya ga Ubangiji da wuta. A rana ta bakwai ɗin ku yi taro mai tsarki, ba za ku kuwa yi aiki na kullum ba.’ ” ’Ya’yan fari na itatuwa Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, kuka kuma girbe amfanin gonarta, sai ku kawo wa firist damin hatsi na farko da kuka girbe. Zai kaɗa damin a gaban Ubangiji domin yă zama yardajje a madadinku; firist ɗin zai kaɗa shi a kashegarin Asabbaci. A ranar da kuka kaɗa damin, dole ku miƙa hadaya ta ƙonawa na ɗan rago bana ɗaya, marar lahani ga Ubangiji, tare da hadaya ta gari mai laushi, humushi biyu haɗe da mai, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, da kuma abin sha kwalaba ɗaya na ruwan inabi. Ba za ku ci wani burodi, ko gasasshen hatsi, ko sabon hatsi ba, sai ran nan da kuka kawo wannan hadaya ga Allahnku. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa, a duk inda kuke zama. Bikin Makoni (Ƙidaya 28.26-31) “ ‘Daga kashegarin Asabbaci, ranar da kuka kawo dami don hadaya ta kaɗawa, ku ƙirga cikakku makoni bakwai. Ku ƙirga kwana hamsin har zuwa kashegarin Asabbaci na bakwai, sa’an nan ku miƙa hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji. Daga ko’ina kuke da zama, ku kawo dunƙule biyu na humushin gari mai laushi da aka tuya da yisti, a matsayin hadaya ta kaɗawa ta ’ya’yan fari na itatuwa ga Ubangiji. Tare da wannan, ku miƙa ’yan raguna bakwai, kowanne bana ɗaya-ɗaya marar lahani, bijimi da kuma raguna biyu. Za su zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, tare da hadayunsu na hatsi, da hadayunsu na sha, hadaya da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Sa’an nan ku miƙa bunsuru ɗaya na hadaya don zunubi, da ’yan raguna biyu, kowanne bana ɗaya-ɗaya, don hadaya ta salama. Firist zai kaɗa ’yan raguna biyun a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, tare da burodin sababbin ’ya’yan fari na itatuwan. Tsarkaken hadaya ce ga Ubangiji ga firist. A wannan rana za ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Bikin busar ƙahoni (Ƙidaya 29.1-6) Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar farko ga wata na bakwai, za tă zama ranar hutu, rana ce ta tuni da yin taro mai tsarki na sujada da za a fara busar ƙaho. Kada ku yi aiki na kullum, amma ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.’ ” Ranar kafara (Ƙidaya 29.7-11) Ubangiji ya ce wa Musa, “Rana ta goma ta wata bakwai, za tă zama Ranar Kafara. Sai ku yi taro mai tsarki don ku yi mūsun kanku ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. Kada ku yi aiki a ranar, gama Ranar Kafara ce, sa’ad da za a yi kafara saboda ku a gaban Ubangiji Allahnku. Duk wanda bai yi mūsun kansa a wannan rana ba, dole a raba shi daga mutanensa. Zan hallaka duk wani da ya yi aiki a wannan rana daga mutanensa. Sam ba za ku yi wani aiki ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce, wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama. Asabbaci ne na hutu dominku, kuma dole ku yi mūsun kanku. Daga yamman rana ta tara ga wata, har zuwa yamma na biye, za ku kiyaye Asabbacinku.” Bikin tabanakul (Ƙidaya 29.12-40) Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘A ranar goma sha biyar ga wata na bakwai, za a fara Bikin Tabanakul na Ubangiji, zai kuma ɗauki kwana bakwai. A ranar farko za tă zama ta taro mai tsarki, kada ku yi aiki na kullum. Kwana bakwai za ku miƙa hadayun da aka yi da wuta ga Ubangiji, a rana ta takwas, ku yi taro mai tsarki, ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. Wannan ranar rufewar taro ce; kada ku yi aiki na kullum. (“ ‘Waɗannan su ne bukukkuwan da Ubangiji ya kafa, waɗanda za ku yi a matsayin tsarkakakkun taro, don kawo hadayun da aka yi da wuta ga Ubangiji, hadayu na ƙonawa da hadayu na hatsi, sadaka da kuma hadayu na sha, da ake bukata kowace rana. Waɗannan hadayu, ƙari ne a kan waɗannan na Asabbatan Ubangiji, haɗe kuma da kyautanku, da kome da kuka yi alkawari, da kuma hadayu yardar ran da za ku ba wa Ubangiji.) “ ‘Saboda haka, farawa daga ranar goma sha biyar ga watan bakwai, bayan kun tara hatsin gona, ku yi bikin Ubangiji kwana bakwai; rana ta fari, rana hutu ce, rana ta takwas kuma rana hutu ce. A rana ta fari, za ku ɗebi zaɓaɓɓun ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, da rassan dabino, rassa masu ganye, da kuma ganyayen itacen wardi na rafi, ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, kwana bakwai. Za ku kiyaye bikin nan har kwana bakwai a kowace shekara ga Ubangiji. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsarraraki masu zuwa, ku kiyaye ta a wata na bakwai. Ku zauna a bukkoki kwana bakwai. Dukan ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa, za su zauna a bukkoki don zuriyarku tă san cewa na sa Isra’ilawa suka zauna a bukkoki sa’ad da na fitar da su daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Saboda haka Musa ya sanar wa Isra’ilawa ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji. Mai da burodi, shiryayye a gaban Ubangiji (Fitowa 27.20,21) Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai na zaitun da aka matse, don ƙuna fitilun yadda harshen wutar ba zai taɓa mutuwa ba. Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa. Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji. “Ɗauki gari mai laushi a gasa dunƙulen burodi goma sha biyu, a yi amfani da humushi biyu na garwan gari don kowace burodi. A shirya su jeri biyu, guda shida a kowane jeri a kan teburin da aka yi da zinariya zalla, a gaban Ubangiji. Za a zuba turare a kowane layin dunƙulen burodin don yă kasance abin tunawa a bisa burodin. Turaren zai ƙone a madadin burodin don yă zama kamar hadayar da aka miƙa da wuta ga Ubangiji. Za a shirya wannan gurasa a gaban Ubangiji kowane Asabbaci, a madadin Isra’ilawa a matsayin madawwamin alkawari. Wannan burodin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza, waɗanda za su ci a tsattsarkan wuri, gama sashe ne mafi tsarki na rabonsu na kullum na hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji.” A Jajjefi mai saɓo da duwatsu To, ɗan wata mutuniyar Isra’ila wanda mahaifinsa mutumin Masar ne, ya je cikin Isra’ilawa, sai faɗa ta tashi tsakaninsa da wani mutumin Isra’ila a cikin sansani. Ɗan mutuniyar Isra’ila ya saɓi Sunan Ubangiji, ya kuma la’ana shi, saboda haka aka kawo shi wa Musa. (Sunan mahaifiyarsa Shelomit ne, ’yar Dibri na kabilar Dan.) Suka sa shi a gidan tsaro sai lokacin da nufin Ubangiji ya nuna musu abin da za su yi da shi. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kai mai saɓon nan waje da sansani. Duk waɗanda suka ji maganar da mai saɓon nan ya yi su ɗibiya hannuwansu a kansa, taron jama’a kuwa gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wanda ya zagi Allahnsa, alhakin zai rataya a wuyansa, duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji, dole a kashe shi. “ ‘Duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi. Duk wanda ya kashe dabbar wani, dole yă biya, rai domin rai. Duk wanda ya yi wa maƙwabcinsa rauni, sai a yi masa abin da ya yi; karaya don karaya, ido don ido, haƙori don haƙori. Kamar yadda ya yi wa wani rauni, shi ma a yi masa. Duk wanda ya kashe dabba, dole yă biya, amma duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi. Za ku kasance da doka iri ɗaya wa baƙo da kuma wa haifaffen ɗan ƙasa. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ” Sai Musa ya yi wa Isra’ilawa magana, suka kuwa kai mai saɓon waje da sansani, suka jajjefi shi da duwatsu. Isra’ilawa suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa. Shekara ta Asabbaci (Maimaitawar Shari’a 15.1-11) Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce, “Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji. Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu. Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi. Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu. Duk abin da gonar ta ba da amfani a shekara ta Asabbaci, zai zama abinci gare ku, wa kanku, bayinku maza da mata, da ma’aikatan da kuka ɗauka aiki, da kuma waɗanda ba zama ɗinɗinɗin suke yi tare da ku ba, haka ma zai zama abinci domin dabbobinku, da kuma namun jeji a ƙasarku. Duk abin da ƙasar ta bayar za a ci. Murnar cika shekarar hamsin “ ‘Ku ƙirga asabbatai bakwai na shekaru bakwai, sau bakwai. Gama asabbatai bakwai na shekaru bakwai za su yi daidai da shekaru arba’in da tara. Sa’an nan a busa ƙaho a ko’ina, a rana ta goma ga wata na bakwai; a Ranar Kafara, a busa ƙaho a dukan ƙasarku. Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa. Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba. Gama shekara ce ta murna, za tă kuma zama mai tsarki a gare ku, ku dai ci abin da aka ɗauka kai tsaye daga gonaki. “ ‘A wannan Shekara ta Murna, kowa zai koma ga mallakarsa. “ ‘In ka sayar da gona wa wani daga mutanen ƙasarka, ko ka saya wata gona daga gare shi, kada ku cuci juna. Sa’ad da mutum ya sayi fili daga abokin zamansa, kuɗin zai kasance bisa ga yawan shekara hamsin ta murna da suka wuce, da kuma bisa ga yawan shekarun noma da suka rage kafin wata shekara hamsin ta murna. Idan shekarun suna da yawa, sai ku kara kuɗin filin, idan kuma shekarun ba su da yawa, sai ku rage kuɗin filin, gama ainihin abin da ake sayar maka shi ne yawan hatsin. Kada ku cuci juna, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Ku bi farillaina, ku kuma yi hankali ga kiyaye dokokina, za ku kuwa zauna lafiya a ƙasar. Sa’an nan ƙasar za tă ba da amfaninta, za ku kuwa ci ku ƙoshi, ku kuma zauna lafiya. Mai yiwuwa ku ce, “Me za mu ci a shekara ta bakwai in ba mu yi shuki ko girbin hatsinmu ba?” Zan aika muku da irin albarka a shekara ta shida har da ƙasar za tă ba da amfani isashe na shekara uku. Yayinda kuke shuki a shekara ta takwas, za ku kasance da raguwa hatsi na shekarar da ta wuce, za ku kuma ci gaba da ci daga gare shi har girbin shekara ta tara yă shigo. “ ‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma ’yan haya nawa. Ko’ina a ƙasar da kuke da mallaka, dole ku tanadar da dama fansar ƙasar. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta, ya kuma sayar da mallakarsa, sai danginsa na kusa yă je yă fanshi abin da mutumin ƙasarsa ya sayar. In mutumin ba shi da wanda zai fansa masa ita, shi kansa kuwa ya wadace, ya kuma sami isashen halin fansarta, sai yă lasafta yawan shekarun da aka yi tun da an sayar da filin. Kuɗin filin zai dangana ga yawan shekarun da suka rage kafin shekara hamsin ta murna da za tă zo; sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa. Amma in bai sami halin sāke biyansa ba, abin nan da ya sayar zai ci gaba da zama mallakar mai sayan, sai Shekara ta Murna. Za a maido masa da ita a Shekara ta Murna, sa’an nan zai iya koma ga mallakarsa. “ ‘In mutum ya sayar da gida a birni mai katanga, yana da izini yă fanshe shi a ƙarshen shekara guda, bayan ya sayar da shi. In ba a fanshe shi a ƙarshen shekara ba, gidan da yake a birni mai katanga, zai zama mallakar na ɗinɗinɗin na mai sayan da kuma zuriyarsa. Ba za a mai da shi a Shekara ta Murna ba. Amma za a ɗauki gidaje a ƙauyuka marasa katanga kewaye da su daidai da gonaki. Za a iya fanshe su, a kuma mayar da su a Shekara ta Murna. “ ‘Kullum, Lawiyawa suna da izini su fanshi gidajensu a biranen Lawiyawa waɗanda suka mallaka. Saboda haka ana iya fansa mallakar Lawiyawa, wato, gidan da aka sayar a duk birnin da yake nasu, za a kuma mayar a Shekara ta Murna, gama gidaje a biranen Lawiyawa, mallakar Isra’ilawa ne. Amma kada a sayar da filayen kiwo na waɗannan birane; mallakarsu ce, ta ɗinɗinɗin. “ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku. Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku. Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, don in ba ku ƙasar Kan’ana in kuma zama Allahnku. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta a cikinku, ya kuma sayar da kansa gare ku, kada ku sa yă yi kamar bawa. Amma a ɗauke shi a matsayin ma’aikacin da aka ɗauka aiki, ko mazaunan da ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, sai yă yi muku aiki sai Shekara ta Murna. Sa’an nan a sake shi da ’ya’yansa, yă kuma koma ga danginsa da mallakar kakanninsa. Gama Isra’ilawa bayina ne, waɗanda na saya daga Masar, kada a sayar da su a matsayin bayi. Kada ku gwada musu azaba, amma ku ji tsoron Allahnku. “ ‘Bayinku maza da mata, za su zo daga al’ummai da suke kewaye da ku, daga gare su za ku iya saya bayi. Za ku iya saya waɗansu mutanen da ba sa zama ɗinɗinɗin a cikinku, da kuma membobin danginsu da aka haifa a ƙasarku. Za ku iya ba da su ga ’ya’yanku a matsayin kayan gādo, za ku kuma iya mai da su bayi dukan rayuwarsu, amma kada ku yi mulki a bisa ’yan’uwanku Isra’ilawa da tsanani. “ ‘In baƙo, ko wani da yake zama ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, ya wadace, ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku kuwa ya talauta, ya kuma sayar da kansa ga baƙon da yake zama a cikinku, ko memba na dangin baƙon, yana da izini samun fansa, bayan ya sayar da kansa. Ɗaya daga cikin danginsa zai iya fansarsa. Kawu ko yaron ɗan’uwan mahaifin wannan mutum, ko kuwa wani dangi a cikin zuriyarsa, zai iya fanshe shi. Ko kuma in ya azurta, zai iya fansar kansa. Da shi da mai sayansa, za su ƙirga lokaci daga shekarar da ya sayar da kansa har zuwa Shekara ta Murna. Farashin sakinsa zai dangana a kuɗin da ake biyan ma’aikacin da aka ɗauka aiki, na yawan shekarun ne. In shekaru sun ragu, dole yă biya don fansarsa da kuɗi mai yawa fiye da wanda aka saye shi. In shekarun sun rage kaɗan ne kafin Shekara ta Murna, sai yă yi lissafin wannan, yă kuma biya fansarsa daidai wa daida. Sai a yi da shi kamar ma’aikacin da aka ɗauka aiki, daga shekara zuwa shekara; dole ku tabbata mai shi bai mallake shi da tsanani ba. “ ‘Ko ma ba a fanshe shi a ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ba, sai a sake shi da ’ya’yansa a Shekara ta Murna, gama Isra’ilawa nawa ne a matsayin bayi. Su bayina ne waɗanda na saya daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku. Lada don biyayya “ ‘Kada ku yi gumaka, ko ku kafa siffa, ko al’amudi wa kanku, kada kuma ku sa sassaƙaƙƙun duwatsu a ƙasarku don ku rusuna musu. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Ku kiyaye Asabbataina, ku kuma ba wa wuri mai tsarkina girma. Ni ne Ubangiji. “ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina, zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu. Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku. “ ‘Zan ba ku salama a ƙasar, za ku kuwa kwanta, kuma babu wani da zai tsorata ku. Zan kori mugayen namun jeji daga ƙasar, takobi kuma ba zai ratsa cikin ƙasarku ba. Za ku kori abokan gābanku, za su kuwa fāɗi a kaifin takobi a gabanku. Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku. “ ‘Zan dube ku da idon rahama, in kuma sa ku riɓaɓɓanya ku kuma ƙaru, zan kiyaye alkawarina da ku. Za ku ci gaba da cin girbin bara, har ku fitar da shi don ku sami wurin saboda sabo. Zan kafa wurin zamana a cikinku, ba zan kuma yi ƙyamarku ba. Zan yi tafiya a cikinki in kuma zama Allahnku, za ku kuwa zama mutanena. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar don kada ku ƙara zama bayi ga Masarawa; na karya sandunan wahalarku, na kuma bar ku ku yi tafiya a sake. Hukunci don rashin biyayya “ ‘Amma in za ku kasa kunne gare ni, ku kuma aikata dukan waɗannan umarnai, in kuka kuma ƙi farillaina, kuka yi ƙyamar dokokina, kuka kuma kāsa kiyaye umarnaina, har kuka karya alkawarina, to, zan yi muku wannan. Zan kawo muku abin bantsoro, cututtuka da zazzaɓin da zai lalatar da idonku, yă kuma sa ranku a wahala. Za ku shuka iri a banza, domin abokan gābanku ne za su ci. Zan yi gāba da ku har abokan gābanku su ci ku a yaƙi, su waɗanda suke ƙinku za su yi mulki a kanku, za ku gudu ba tare da wani yana korinku ba. “ ‘In bayan dukan wannan, ba ku saurare ni ba, zan hukunta ku saboda zunubanku har sau bakwai. Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma tă zama kamar tagulla. Ƙarfinku zai ƙare a banza domin ƙasarku ba za tă ba da hatsi ba, balle itatuwan ƙasar su ba da ’ya’ya. “ ‘In kuka ci gaba da tayar mini, kuka ƙi ku saurare ni, zan ninka wahalolinku sau bakwai, yadda ya dace da zunubanku. Zan aika da mugayen namun jeji a kanku, za su kuwa kashe ’ya’yanku, su hallaka shanunku, su rage yawanku, ku zama kaɗan. Wannan zai sa a rasa mutane a kan hanyoyinku. “ ‘In duk da waɗannan abubuwa, ba ku yarda da gyaran da nake yi muku ba, kuka ci gaba da yin adawa da ni, zan yi adawa da ku, zan kuma aukar muku saboda zunubanku har sau bakwai. Zan kawo takobi a kanku don in yi ramuwa saboda karya alkawarin da kuka yi. Sa’ad da kuka janye zuwa cikin biranenku, zan aika da annoba a cikinku, za a kuwa ba da ku ga hannun abokan gāba. Sa’ad da na yanke abincinku, mata goma za su dafa abinci a murhu ɗaya, za su kuma rarraba abincin a ma’auni. Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba. “ ‘In duk da haka kuka ci gaba da ƙin saurare ni, kuka ci gaba da yin adawa da ni, cikin fushina, sai in yi adawa da ku, in kuma hukunta ku saboda zunubanku har sau bakwai. Za ku ci naman ’ya’yanku maza da na ’ya’yanku mata. Zan rurrushe dukan masujadanku, in yanke bagadanku na turare, in yi tarin gawawwakinku a kan gumakanku, zan kuma yi ƙyamarku. Zan mai da biranenku kango, in lalace wuraren tsarkinku, ba zan kuma shaƙi ƙanshi hadayunku ba. Zan mai da ƙasarku kango har abokan gābanku da suke zama a wurin su yi mamaki. Zan watsar da ku cikin al’ummai, in kuma ja takobina in kore ku. Ƙasarku za tă zama kufai, biranenku kuma su zama kango. Sa’an nan ƙasar za tă ji daɗin hutun shekarun Asabbacinta, a dukan lokutan da take kango, ku kuwa kuna a ƙasar abokan gābanku, sa’an nan ƙasar za tă huta ta ji daɗin asabbatanta. A dukan lokutan da take kango, ƙasar za tă sami hutun da ba tă samu a lokutan asabbatan da kuke zama a cikinta ba. “ ‘Ga waɗanda za su ragu kuwa, zan cika zukatansu da tsoro a ƙasashen abokan gābansu har motsin ganyen da iska ta hura zai sa su ruga da gudu. Za su yi gudu kamar suna gudu daga takobi ne, za su kuma fāɗi, ko da yake babu wanda yake korinsu. Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake babu wanda yake korinsu. Ta haka ba za ku iya tsaya a gaban abokan gābanku ba. Za ku mutu a cikin al’ummai, ƙasar abokan gābanku za tă cinye ku. Sauranku da suka ragu za su lalace a ƙasashen abokan gābansu saboda zunubansu; da kuma saboda zunuban kakanninsu. “ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni, waɗanda suka sa na yi adawa da su har da na aika da su ƙasar abokan gābansu, sa’ad da suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, suka kuma biya hukuncin zunubansu, zan tuna da alkawarina da Yaƙub, da alkawarina da Ishaku, da kuma alkawarina da Ibrahim, zan tuna da ƙasar. Gama za su gudu su bar ƙasar, ƙasar kuwa ta ji daɗin asabbatanta yayinda take kango muddin ba su ciki. Za su biya hukuncin zunubansu domin sun ƙi dokokina, suka kuma yi ƙyamar farillaina. Duk da haka, sa’ad da suke a ƙasar abokan gābansu, ba zan ƙi su, ko in yi ƙyamarsu, in hallaka su ƙaƙaf, har in karya alkawarina da su ba. Ni ne Ubangiji Allahnsu. Amma saboda su, zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu, waɗanda na fitar da su daga Masar a idon al’ummai, don in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.’ ” Waɗannan su ne farillai, da dokoki, da kuma ƙa’idodin da Ubangiji ya kafa a Dutsen Sinai, tsakaninsa da Isra’ilawa ta wurin Musa. Fansar abin da yake na Ubangiji Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Duk sa’ad da mutum ya yi rantsuwa ta musamman zai keɓe wani ga Ubangiji, ta wurin biyan kuɗaɗen fansa, ga yadda ma’aunin biyan zai kasance, mutum mai shekara tsakanin ashirin da sittin, za a biya azurfa hamsin. Mace kuma za a biya azurfa talatin. Saurayi mai shekara tsakanin biyar da ashirin, za a biya azurfa ashirin, yarinya kuma azurfa goma. Yaro mai shekara tsakanin wata ɗaya da shekara biyar, za a biya azurfa biyar, ’yar yarinya kuma azurfa uku. Namijin da ya fi shekara sittin, za a biya azurfa goma sha biyar, mace kuma azurfa goma. In mai alkawarin matalauci ne da ba zai iya biyan ƙayyadadden abin da aka tsara ba, sai yă tafi wurin firist, shi firist kuma yă duba yadda mutumin da ya yi alkawarin zai iya biya. Sa’an nan mutumin zai biya abin da firist ya faɗa. “ ‘In abin da ya yi alkawarin yardajje ne a matsayin hadaya ga Ubangiji, wannan dabbar da aka bayar ga Ubangiji, za tă zama mai tsarki. Kada yă yi musayarta ko yă yi musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau; in lalle ne yă yi musayar dabbar da wata, to, duk wannan da kuma wanda zai yi musayar da ita za su zama masu tsarki. In abin da ya yi alkawari dabba ce marar tsarki, wadda ba yardajje ba ce, a matsayin hadaya ga Ubangiji, dole a kai dabbar wa firist, wanda zai yanke hukunci dacewarta, ko mai kyau ce, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama. In mai shi yana so yă fanshi dabbar, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta. “ ‘In mutum ya miƙa gidansa a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji, firist zai daidaita dacewar ko mai kyau ne, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama. In mutumin da ya keɓe gidansa ya fanshe shi, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar, gidan kuma zai zama nasa. “ ‘In wani ya keɓe wa Ubangiji wani sashe daga cikin gonarsa ta gādo, sai yă kimanta kuɗin gonar daidai da yawan irin da za a iya shuka a gonar. Za a kimanta kuɗin a kan shekel hamsin na irin sha’ir. In ya keɓe gonarsa a Shekara ta Murna, darajar da aka kimanta za tă zauna. Amma in ya keɓe gonar bayan Shekara ta Murnan, firist zai kimanta darajar bisa ga yawan shekarun da suka rage har zuwa Shekara ta Murna mai zuwa, sai a rage darajar da aka kimanta a kanta. In mutumin da ya keɓe gonar, yana so yă fanshe ta, to, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta, gonar kuwa tă zama nasa. In kuma bai fanshe gonar ba, ko kuwa in ya sayar wa wani dabam, ba za a taɓa fanshe ta ba. Sa’ad da aka saki gonar a Shekara ta Murna, za tă zama mai tsarki, a matsayin gonar da aka miƙa ga Ubangiji, za tă zama mallakar firistoci. “ ‘In mutum ya keɓe gonar da ya saya, wadda take ba sashe na gonar iyali ba, ga Ubangiji, firist zai kimanta darajarta har Shekara ta Murna, dole kuma mutumin yă biya darajarta a ranar, a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji. A Shekara ta Murna ɗin, gonar za tă dawo ga mutumin da aka saye ta daga wurinsa, wanda yake mai gonar. A kimanta kowace daraja bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, gera ashirin ga shekel. “ ‘Ba wani da zai iya keɓe ɗan farin dabba, da yake ɗan fari ya riga ya zama na Ubangiji, ko na saniya, ko na tunkiya, na Ubangiji ne. In tana cikin dabbobin da suke marasa tsarki, zai iya saye ta a darajar da aka kimanta, yă ƙara da kashi ɗaya bisa biyar na darajarta. In bai fanshe ta ba, sai a sayar da ita a darajar da aka kimanta. “ ‘Amma babu abin da mutum ya mallaka, ya kuma keɓe ga Ubangiji, ko mutum ne, ko dabba, ko ganar iyali da za a sayar, ko a fansa; kome da aka keɓe a wannan hanya, mafi tsarki ne ga Ubangiji. “ ‘Babu wani da aka keɓe don hallaka da za a fansa; dole a kashe shi. “ ‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji. In mutum ya fanshi wani zakansa, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar. Ushirin gaba ɗaya na garken shanu, da na tumaki, kowane kashi ɗaya bisa goma na dabbar da ta wuce ƙarƙashin sandan mai kiwo, za tă zama mai tsarki ga Ubangiji. Kada kuwa ya zaɓa mai kyau daga marar kyau, ko yă yi musaya. In ya yi musaya kuwa, dabbar da wadda ya musayar, za su zama masu tsarki, ba kuma za a fanshe su ba.’ ” Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai saboda Isra’ilawa.