- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Makoki Makoki Makoki Mak Makoki 1 Wannan surar waƙa ce mai bin harufa bi da bi, ayoyin da suka fara da harufan Ibraniyanci bi da bi. Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki, birnin da a dā yake cike da mutane! Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa, wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe! Ita da take sarauniya a cikin larduna yanzu ta zama baiwa. Tana yin kuka mai zafi da dare, hawaye na gangara a kan kumatunta. A cikin masoyanta duka babu wanda ya yi mata ta’aziyya. Duk abokanta sun yashe ta; sun zama abokan gābanta. Bayan wahala da baƙin ciki, Yahuda ta tafi bauta. Ta zauna a cikin ƙasashe, ba tă samu wurin hutawa ba. Duk masu fafararta sun same ta sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai. Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki, gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya. Ba kowa a hanyoyin shiganta. Firistocinta suna gurnani, ’yan matana kuma suna wahala, kuma tana cikin shan wahala ƙwarai. Maƙiyanta sun zama shugabanninta; Abokan gābanta suna da kwanciyar rai. Ubangiji ya kawo mata ɓacin rai domin yawan zunubanta. ’Ya’yanta sun tafi bauta, a ƙarƙashin maƙiyanta. Diyar Sihiyona ba ta da sauran daraja. ’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi waɗanda suka rasa wurin kiwo; cikin rashin ƙarfi suka guje wa masu fafararsu. A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo Urushalima ta tuna da dukan dukiyar da take da ita a kwanakin dā can. Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta, ba wanda ya taimake ta. Maƙiyanta suka dube ta suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata. Urushalima ta yi zunubi ƙwarai saboda haka ta zama marar tsarki. Dukan masu martaba ta sun raina ta, gama sun ga tsiraicinta; ita ma da kanta tana nishi da ƙyar ta kuma juya baya. Ƙazantarta ta manne wa rigunanta; ba tă kula da nan gaba ba, fāɗuwarta kuwa babban abu ne; babu wanda zai yi mata ta’aziyya. “Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata, gama maƙiyi ya yi nasara.” Maƙiya ya kwashe dukiyarta duka; ta ga mutanen da ba su san Allah ba sun shiga wuri mai tsarkinta waɗanda ka hana su shiga taron jama’arka. Dukan mutanenta suna nishi da ƙyar suna neman burodi; sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci don kada su mutu da yunwa. Ubangiji, ka duba ka gani, gama an yashe ni.” “Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa? Ku duba ku gani. Ko akwai wata wahala kamar irin wadda nake sha, wadda Ubangiji ya auko mini a cikin zafin fushinsa? “Daga sama ya aiko da wuta, ya aiko ta cikin ƙasusuwana. Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna ya juyo da ni. Ya bar ni ni kaɗai, sumamme dukan yini. “Ya ɗaura zunubaina a wuyana; aka naɗe su a hannuwansa. Aka rataye su a wuyana Ubangiji ya kwashe ƙarfina. Ya bashe ni ga waɗanda suka fi ni ƙarfi. “Ubangiji ya ƙi duk mayaƙan da suke tare da ni; ya sa wata runduna ta tayar mini ta kuma tattake samarina. Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda kamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa. “Dalilin da ya sa nake kuka ke nan idanuna kuma suna ta zubar da hawaye. Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya, ba wanda zai sabunta ruhuna. ’Ya’yana sun zama fakirai domin maƙiyina ya yi nasara.” Sihiyona ta miƙa hannunta, amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya. Ubangiji ya umarta cewa maƙwabtansa za su zama maƙiyansa; Urushalima ta zama abar ƙyama a cikinsu. Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da ’yan matana duka sun tafi bauta. “Na kira abokaina amma sun yashe ni. Firistocina da dattawana sun hallaka a cikin birnin yayinda suke neman abinci don kada su mutu da yunwa. “Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki! Ina shan azaba a raina, ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata, domin na yi tawaye sosai. A waje takobi na kisa; a ciki kuma akwai mutuwa. “Mutane suna ji ina nishi da ƙyar, amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya. Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki; suna farin ciki da abin da ka yi. Ka kawo ranan nan da ka sanar domin su ma su zama kamar ni. “Bari ka ga muguntarsu duka; ka yi musu yadda ka yi mini domin dukan zunubansu. Nishina da yawa kuma zuciyata ta gaji.” 2 Wannan surar waƙa ce mai bin harufa bi da bi, ayoyin da suka fara da harufan Ibraniyanci bi da bi. Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyona da gizagizan fushi!2.1 Ko kuwa Yadda Ubangiji cikin fushinsa / ya yi da Diyar Sihiyona da wargi Ya jefar da darajar Isra’ila daga sama zuwa ƙasa; bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa ba a ranar fushinsa. Ubangiji ya hallakar da wurin zaman Yaƙub ba tausayi; A cikin fushinsa kuma zai rurrushe kagaran Diyar Yahuda. Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulki. A cikin zafin fushi ya fasa kowane ƙaho na Isra’ila. Ya janye hannun damansa sa’ad da maƙiyi ya zo. Ya yi ƙuna a cikin Yaƙub kamar wuta mai ƙone duk abin da yake kusa da ita. Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa; hannun damansa na shirye. Kamar maƙiyi, ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani; ya zuba fushinsa kamar wuta a kan tenti na Diyar Sihiyona. Ubangiji kamar maƙiyi ne; ya hallaka Isra’ila. Ya hallaka wurarenta duka ya kuma hallaka kagaranta. Ya ƙara yawan makoki da baƙin ciki wa Diyar Yahuda. Ya rushe haikalinsa kamar lambu; ya hallaka wurin yi masa sujada. Ubangiji ya sa Sihiyona ta manta da bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci; a cikin zafin fushinsa ya watsar da sarki da firist. Ubangiji ya ƙi bagadensa ya kuma yi wofi da haikalinsa. Ya ba maƙiyinta fadodinta; suka yi sowa a cikin gidan Ubangiji kamar a ranar da ake yin biki. Ubangiji ya ƙuduri niyya yă rushe bangon da yake kewaye da Diyar Sihiyona. Ya auna da igiyar awo bai fasa hallaka ta ba. Ya sa katanga da katanga duk suka lalace. Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa; ya kakkarya ƙarafanta. Sarakunanta da ’ya’yan sarakunanta duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe, babu sauran doka, annabawa kuma ba su samun wahayi daga wurin Ubangiji. Dattawan Diyar Sihiyona sun zauna shiru a ƙasa; suka kuma sa rigar buhu. ’Yan matan Urushalima suka sunkuyar da kawunansu ƙasa. Idanuna sun dushe don yawan kuka, raina na cike da baƙin ciki; zuciyata ta karaya domin mutanena sun hallaka, domin yara da jarirai suna suma a kan hanyoyi a cikin birni. Suna ce wa uwayensu, “Ina burodi da ruwan inabi?” Yayinda suke suma kamar mutanen da aka ji masu ciwo a cikin birni, sa’ad da suke mutuwa a hannuwan uwayensu. Me zan ce miki? Da me zan kwatanta ki, ke Diyar Urushalima? Da me zan misalta ki, yadda zan iya yi miki ta’aziyya, Ke Budurwa Diyar Sihiyona? Ciwonki yana da zurfi kamar teku. Wane ne zai iya warkar da ke? Wahayin annabawanki ƙarya ne kuma marasa amfani; ba su tona zunubanki ba yadda za su iya ceto ki daga bauta ba. Sun yi miki annabcin ƙarya marar amfani. Duk masu wucewa suna yi miki tafi na reni; suna yi wa Diyar Urushalima tsaki suna kaɗa kai suna cewa, “Wannan ne birnin da aka ce kyakkyawa ne, mai farantawa dukan duniya rai?” Maƙiyanki duka suna ta surutu game da ke; suna tsaki suna cizon haƙora suna cewa, “Mun hallaka ta. Wannan ce ranar da muke jira; yau mun gan ta.” Ubangiji ya yi abin da ya shirya; ya cika maganarsa, wadda ya umarta tun daɗewa. Ya jefar da ke ba tausayi, ya bari maƙiya sun yi nasara da ke, ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki. Zuciyar mutane ta yi kuka ga Ubangiji. Ya bangon Diyar Urushalima, bar hawayenki su zuba kamar rafi dare da rana; kada ki huta, kada idanunki su huta. Ki tashi, ki yi kuka cikin dare, dare na yi sai ki fara kuka; kina buɗewa Ubangiji zuciyarki. Ki ɗaga hannuwanki gare shi domin rayukan ’ya’yanki, waɗanda suka suma don yunwa a kan kowane titi. “Ka duba, ka gani ya Ubangiji. Wane ne ka taɓa yi wa haka? Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu, ’ya’yan da suka yi reno? Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa a cikin haikalin Ubangiji? “Matasa da tsofaffi duk suna kwanciya a cikin ƙurar tituna; an karkashe matasa da ’yan matana da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka; ka kashe su ba tausayi. “Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki, haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe. A ranar fushin Ubangiji ba mai tserewa ba wanda zai tsira; maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu, na kuma lura da su.” 3 Wannan surar waƙa ce; ayoyin kowane sakin layi sun fara da harufan Ibraniyanci bi da bi, kuma ayoyin cikin kowane sakin layi ya fara da harufa iri ɗaya. Ni ne mutumin da ya ga azaba ta wurin bulalar fushin Ubangiji. Ya kore ni, ya sa na yi tafiya a cikin duhu maimakon a cikin haske; ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini. Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana. Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni da baƙin ciki da kuma wahala. Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa. Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi. Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata. Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace. Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye, ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako. Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa. Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa. Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini. Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci. Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura. An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata. Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.” Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai. Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina. Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba. Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa. Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne. Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.” Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi; yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji. Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro. Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi. Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege. Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci. Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada. Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa. Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba. Bai yarda a tattake ’yan kurkuku a ƙasa ba, ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki, ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba? Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba? Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba? Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa? Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji. Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce, “Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba. “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi. Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka. Ka mai da mu tarkace da juji a cikin mutane. “Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana marar daɗi. Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.” Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena. Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa. Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani. Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina. Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu. Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami suka kuma jajjefe ni da duwatsu; ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa. Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi. Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.” Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.” Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina. Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya! Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini. Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai game da ni duk yini. Dube su! A zaune ko a tsaye, suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu. Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi. Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su. Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji. 4 Wannan surar waƙa ce mai bin harufa bi da bi, ayoyin da suka fara da harufan Ibraniyanci bi da bi. Zinariya ta rasa kyanta, hasken zinariya ya dushe! An warwatsar da tsarkakakkun duwatsu masu daraja a kan tituna. Dubi samarin Sihiyona masu daraja, waɗanda a dā darajarsu ta isa nauyin zinariya, yanzu ana ɗaukar su a matsayin tukwanen ƙasa, aikin maginin tukwane! Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji. Domin ƙishirwa harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu; yaran suna roƙo a ba su burodi, amma ba wanda ya ba su. Waɗanda a dā sukan ci abinci mai daɗi yanzu su ne masu bara a tituna. Waɗanda a dā suke sa kaya masu kyau yanzu suna kwance a kan tarin toka. Horon mutanena ya fi na Sodom girma, wadda aka hallaka farat ɗaya ba wani hannu da ya juya ya taimake ta. ’Ya’yan sarakunansu sun fi ƙanƙara haske sun kuma fi madara fari, jikunansu sun fi murjani ja, kyansu kamar shuɗin yakutu.4.7 Ko kuma lafis lazuli Amma yanzu sun fi dare duhu; ba a iya gane su a tituna. Fatar jikinsu ta manne da ƙasusuwansu; sun bushe kamar itace. Gara waɗanda aka kashe su da takobi da waɗanda suke mutuwa da yunwa; sun rame domin rashin abinci a gona. Da hannuwansu mata masu tausayi sun dafa yaransu, suka zama masu abinci sa’ad da aka hallaka mutanena. Ubangiji ya saki fushinsa; ya zuba zafin fushinsa. Ya hura wuta a Sihiyona ta kuma cinye harsashin gininta. Sarakunan duniya ba su gaskata ba, haka ma mutanen duniya, cewa magabta da maƙiya za su iya shiga ƙofofin Urushalima. Amma ya faru domin zunuban annabawanta da muguntar firistocinta, waɗanda suka zub da jinin masu adalci a cikinsu. Yanzu suna yawo barkatai a tituna kamar makafi. Sun ƙazantu da jini yadda ba wanda zai kuskura ya taɓa rigunansu. “Ku tafi! Ba ku da tsabta!” Haka mutane suke ihu suke ce musu. “Ku tashi daga nan! Ku tashi daga nan! Kada ku taɓa mu!” Sa’ad da suka gudu suna yawo, mutanen waɗansu ƙasashe suka ce, “Ba za su ci gaba da zama a nan ba.” Ubangiji kansa ya warwatsa su; ya daina duban su. Ba a ba firistoci girma, ba su ba dattawa gata. Idanunmu sun gaji, suna ta dubawa ko taimako zai zo; mu sa ido ko za mu ga ƙasar da za tă iya taimakon mu. Ana bin sawunmu, ba za mu iya tafiya kan tituna ba. Ƙarshenmu ya kusa, kwanakinmu sun ƙare, gama ƙarshenmu ya zo. Masu fafarar mu sun fi gaggafa mai firiya a sararin sama sauri; sun fafare mu a kan duwatsu suna fakon mu a jeji. Shafaffe na Ubangiji, numfashin ranmu, ya fāɗi cikin tarkonsu. Muna tunani cewa za mu iya rayuwa cikin sauran mutane a ƙarƙashin inuwarsa. Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom, ke mai zama a ƙasar Uz. Amma ke ma za a ba ki kwaf; za ki bugu ki zama tsirara. Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki. Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha. An ba wa baƙi gādonmu, gidajenmu kuma aka ba bare. Mun zama marayu marasa ubanni, uwayenmu kamar gwauraye. Dole mu sayi ruwan da muke sha; sai mun biya mu sami itace. Masu fafararmu sun kusa kama mu; mun gaji kuma ba dama mu huta. Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya don mu sami isashen abinci. Kakanninmu sun yi zunubi kuma ba sa nan yanzu, mu ne aka bari muna shan hukuncinsu. Bayi suna mulki a kanmu, kuma ba wanda zai ’yantar da mu daga hannuwansu. Muna samun burodi a bakin rayukanmu domin takobin da yake a jeji. Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, muna jin zazzaɓi domin yunwa. An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda. An rataye ’ya’yan sarakuna da hannuwansu; ba a ba wa dattawa girma. Samari suna faman yin niƙa; yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace. Dattawan sun bar ƙofar birnin, samari sun daina rera waƙa. Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki. Rawani ya fāɗi daga kanmu. Kaiton mu gama mun yi zunubi! Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi; domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe gama Tudun Sihiyona ya zama kufai, sai diloli ke yawo a wurin. Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada; kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani. Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe? Me ya sa ka yashe mu da jimawa? Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa.