- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Yowel
Yowel
Yowel
Yow
Yowel
Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.
Mamayar da fāra ta yi
Ku ji wannan, ku dattawa,
ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar.
Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku
ko a kwanakin kakanninku?
Ku faɗa wa ’ya’yanku,
bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu,
’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.
Abin da ɗango ya bari
fāri masu girma sun cinye;
abin da fāri masu girma suka bari,
burduduwa ta cinye;
abin da burduduwa ta bari sauran kwari1.4 A nan ma’anar kalmomin nan huɗu na Ibraniyanci da aka yi amfani da su da yake nuna fāra ba a san tabbatacciyar ma’anar ba. sun cinye.
Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka!
Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi;
ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi,
gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.
Wata al’umma ta mamaye ƙasata,
tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa;
tana da haƙoran zaki,
da zagar zakanya.
Ta mayar da kuringar inabina kango
ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena.
Ta ɓamɓare bayansu duka
ta kuma jefar da su
ta bar rassansu fari fat.
Ku yi makoki kamar budurwa1.8 Ko kuwa yarinya
a cikin tsummoki
tana baƙin ciki domin mijinta1.8 Ko kuwa wanda suka yi alkawarin aure na ƙuruciyarta.
Hadayun hatsi da hadayun sha
an yanke su daga gidan Ubangiji.
Firistoci suna makoki,
su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.
Filaye sun zama marasa amfani,
ƙasa ta bushe;1.10 Ko kuwa ƙasa tana makoki
an lalatar da hatsi,
sabon ruwan inabin ya bushe,
mai kuma ba amfani.
Ku fid da zuciya, ku manoma,
ku yi ihu, ku masu noma inabi;
ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir,
saboda an lalata girbin filaye.
Kuringar inabin ta bushe
itacen ɓaure kuma ya yi yaushi,
’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa,
dukan itatuwan filaye, sun bushe.
Tabbatacce farin cikin ’yan adam
ya bushe.
Kira don makoki
Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki;
ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade.
Zo, ku kwana saye da tsummoki,
ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima,
gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha
daga gidan Allahnku.
Ku yi shelar azumi mai tsarki;
ku kira tsarkakan taro.
Ku kira dattawa
da kuma dukan mazaunan ƙasar
zuwa gidan Ubangiji Allahnku,
ku kuma yi kuka ga Ubangiji.
Kaito saboda wannan rana!
Gama ranar Ubangiji ta kusa,
za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.1.15 Da Ibraniyanci Shaddai
Ba a yanke abinci
a idanunmu,
farin ciki da kuma murna
daga gidan Allahnmu ba?
Iri suna ta yanƙwanewa
a busasshiyar ƙasa1.17 ma’anar wannan kalma da Ibraniyanci ba ta da tabbas.
Ɗakunan ajiya sun lalace,
an rurrushe rumbunan hatsin,
gama hatsi ya ƙare.
Ji yadda dabbobi suke nishi!
Garkunan shanu sun ruɗe
saboda ba su da ciyawa,
har garkunan tumaki ma suna shan wahala.
A gare ka, ya Ubangiji, nake kira,
gama wuta ta cinye wurin kiwo
harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.
Har ma namun jeji suna haki gare ka;
rafuffuka sun bushe
wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.
Rundunar fāra
Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona;
ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki.
Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki,
gama ranar Ubangiji tana zuwa.
Tana gab da faruwa
rana ce ta baƙin duhu ƙirin,
ranar gizagizai ce baƙi ƙirin.
Babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi tana zuwa
kamar ketowar alfijir a kan duwatsu
yadda ba a taɓa ganin irinta ba,
ba kuwa za a ƙara ganin irinta ba har tsararraki masu zuwa.
A gabansu wuta tana ci,
a bayansu ga harshen wuta yana ci,
A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden,
a bayansu kuma jeji ne wofi,
babu abin da ya kuɓuce musu.
Suna da kamannin dawakai;
suna gudu kamar dokin yaƙi.
Da motsi kamar na kekunan yaƙi
sun tsallake ƙwanƙolin duwatsu,
kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka,
kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi.
Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba;
kowace fuska ta yanƙwane.
Sukan auka kamar jarumawa;
sukan hau katanga kamar sojoji.
Kowa yana takawa bisa ga tsari,
ba mai kaucewa.
Ba sa turin juna,
kowane yakan miƙe gaba.
Sukan kutsa cikin abokan gāba
ba mai tsai da su.
Sukan ruga cikin birni,
suna gudu a kan katanga.
Sukan hau gidaje,
sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi.
A gabansu duniya takan girgiza,
sararin sama kuma yakan jijjigu,
rana da wata su yi duhu,
taurari kuma ba sa ba da haske.
Ubangiji ya yi tsawa
wa shugaban mayaƙansa;
sojojinsa sun fi a ƙirge
masu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa.
Ranar Ubangiji da girma take;
mai banrazana.
Wa zai iya jure mata?
Ku kyakkece zuciyarku
“Ko yanzu”, in ji Ubangiji,
“Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku,
da azumi da kuka da makoki.”
Ku kyakkece zuciyarku
ba rigunanku ba.
Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,
gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma
mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,
yakan kuma janye daga aika da bala’i.
Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi
yă sa mana albarka
ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha
wa Ubangiji Allahnku.
A busa ƙaho a Sihiyona,
a yi shelar azumi mai tsarki,
a kira tsarkakan taro.
A tattara mutane;
ku tsarkake taron;
ku kawo dattawa wuri ɗaya;
ku kuma tara yara,
da waɗanda suke shan mama.
Bari ango yă bar ɗakinsa
amarya kuma lolokinta.
Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji,
su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade.
Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji.
Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya,
da abin ba’a a cikin al’ummai.
Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”
Amsar Ubangiji
Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsa
yă kuma ji tausayin mutanensa.
Ubangiji zai amsa2.18,19 Ko kuwa Ubangiji yă ji kishin / da kuma tausayawa / 19 Ubangiji ya amsa musu ya ce,
“Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai,
isashe da zai ƙosar da ku sosai;
ba kuma zan ƙara maishe ku
abin dariya ga al’ummai ba.
“Zan kori sojojin arewa nesa da ku,
in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma,
kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin teku2.20 Wato, Mediterraniyan.
da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum.2.20 wannan teku na Bahar Maliya ne
Warinsu kuma zai bazu;
ɗoyinsu zai tashi.”
Tabbatacce ya yi al’amura masu girma.2.20 Ko kuwa ya tashi. Tabbatacce ya yi abubuwa masu girma
Kada ki ji tsoro, ya ƙasa;
ki yi murna ki kuma yi farin ciki.
Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma.
Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji,
gama wuraren kiwo sun yi kore shar.
Itatuwa suna ba da ’ya’yansu;
itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.
Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona,
ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku,
gama ya ba ku
ruwan bazara cikin adalci.2.23 ko / mai koyar da gaskiya
Yakan aika muku yayyafi a yalwace,
na bazara da na kaka, kamar dā.
Masussukai za su cika da hatsi;
randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.
“Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru
waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa,
da kuma sauran fāra da tarin fāra2.25 Takamamme ma’anar kalmomin nan guda huɗu na Ibraniyancin da aka yi amfani da su a nan domin fāra babu wanda ya sani.
babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku.
Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi,
za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku,
wanda ya yi muku ayyukan banmamaki;
mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.
Sa’an nan za ku sani ina cikin Isra’ila,
cewa ni ne Ubangiji Allahnku,
babu wani kuma;
mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.
Ranar Ubangiji
“Daga baya kuma,
zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane.
’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,
tsofaffinku za su yi mafarkai,
matasanku za su ga wahayoyi.
Har ma a bisan bayina, maza da mata,
zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.
Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai
da kuma a kan duniya,
za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi.
Rana za tă duhunta
wata kuma yă zama jini
kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji.
Amma dukan waɗanda suka nemi
Ubangiji za su tsira.
Kamar yadda Ubangiji ya ce,
gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima
akwai ceto,
a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.
An shari’anta al’ummai
“A waɗancan kwanaki da kuma a wancan lokaci,
sa’ad da zan maido da arzikin Yahuda da Urushalima,
zan tattara dukan al’ummai
in kuma kawo su Kwarin Yehoshafat3.2 Yehoshafat yana nufin Ubangiji ya shari’anta; haka ma a aya 12.
Can zan yi musu shari’a
game da gādona, mutanena Isra’ila,
gama sun warwatsar da mutanena a cikin al’ummai
sun kuma raba ƙasata.
Sun jefa ƙuri’a a kan mutanena
suna kuma sayar da yara maza don karuwanci,
sun sayar da ’yan matan domin ruwan inabi
wanda za su sha.
“Yanzu mene ne damuwarku da ni, ya Taya da Sidon da kuma dukan mazaunan yankunan Filistiya? Kuna ƙoƙari ku sāka mini don abin da na yi ne? In kuna sāka mini ne, to, da gaggawa zan mayar muku da sakayya a kanku. Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku. Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urushalima ga mutanen Hellenawa, don ku aika da su nesa da ƙasarsu.
“Duba, zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, in kuma yi muku abin da kuka yi musu. Zan sayar da ’ya’yanku maza da mata ga mutanen Yahuda, su kuma za su sayar da su ga mutanen Sabenawa, al’umma da take nesa da ku.” Ubangiji ya faɗa.
Ku yi shelar wannan ga al’ummai.
Ku yi shirin yaƙi!
Ku tā da jarumawa!
Bari mayaƙa su ja kusa su kai hari.
Ku bubbuge garemaninku su zama takuba
da kuma laujenku su zama māsu.
Bari raunana su ce,
“Ni mai ƙarfi ne!”
Ku gaggauta, dukanku al’ummai daga kowane ɓangare,
ku tattaru a can.
Ka sauko da mayaƙanka, ya Ubangiji!
“Bari a tā da dukan al’ummai;
bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat
gama a can zan zauna
in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare.
Ku fito da lauje,
gama girbi ya nuna.
Ku zo, ku tattaka inabin,
gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika
randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba,
muguntarsu da girma take!”
Dubun dubbai
suna a cikin kwarin yanke shawara!
Gama ranar Ubangiji ta yi kusa
a cikin kwarin yanke shawara.
Za a duhunta rana da wata,
taurari kuma ba za su ba da haske ba.
Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona
tsawa kuma daga Urushalima;
duniya da sararin sama za su yi rawan jiki.
Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa,
mafaka ga mutanensa Isra’ila.
Albarka domin mutanen Allah
“Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku,
ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki.
Urushalima za tă zama mai tsarki;
baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba.
“A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi,
tuddai kuma za su malmalo madara;
dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa.
Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji
haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya.3.18 Ko kuwa kwarin Shittim
Amma Masar za tă zama kango,
Edom kuma hamada marar amfani,
saboda kama-karyar da aka yi wa mutanen Yahuda,
a ƙasar da aka zub da jinin marasa laifi.
Za a zauna a Yahuda har abada
Urushalima kuma daga tsara zuwa tsara.
Alhakin jininsu, wanda ban gafarta ba,
zan gafarta.”
Ubangiji yana zama a Sihiyona!