- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Ayuba
Ayuba
Ayuba
Ayu
Ayuba
Gabatarwa
A ƙasar Uz akwai wani mutum mai suna Ayuba. Mutum ne marar laifi kuma mai adalci; yana tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta. Yana da ’ya’ya maza bakwai da ’yan mata uku, yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa.
’Ya’yansa maza sukan yi biki a gidajensu, wannan yă yi yă ba wancan, sai su kira ’yan’uwansu mata ukun su ci, su sha tare. Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa ’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi.
Gwajin Ayuba na farko
Wata rana mala’iku1.6 Da Ibraniyanci ’ya’yan Allah maza suka kawo kansu gaban Ubangiji, Shaiɗan1.6 Shaiɗan yana nufin mai zargi. shi ma ya zo tare da su. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?”
Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”
Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.”
Sai Shaiɗan ya amsa ya ce, “Haka kawai Ayuba yake tsoron Allah? Ba ka kāre shi da iyalinsa gaba ɗaya da duk mallakarsa ba? Ka Albarkaci ayyukan hannunsa yadda dabbobinsa duk sun cika ko’ina. Ka ɗan miƙa hannunka ka raba shi da duk abin da yake da shi, ba shakka zai la’anta ka kana ji, kana gani.”
Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.”
Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji.
Wata rana lokacin da ’ya’yan Ayuba suke cikin biki a gidan babban ɗansa, sai ɗan aika ya zo wurin Ayuba ya ce masa, “Shanu suna huɗa, jakuna kuma suna kiwo nan kusa, sai Sabenawa suka auka musu suka kwashe su suka tafi, suka karkashe masu yi maka aiki duka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Wutar Allah ta sauko daga sama ta ƙona dukan tumaki da masu lura da su, wato, bayinka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa sun auka wa raƙumanka sun kwashe su duka, suka kuma karkashe masu yi maka aiki, ni kaɗai ne na tsira na zo in gaya maka!”
Yana cikin magana, sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “’Ya’yanka maza da mata suna biki, suna ci suna sha a gidan babban ɗanka, sai wata iska mai ƙarfi daga hamada ta auka ta rushe gidan, gidan kuwa ya fāɗi a kan ’ya’yanka ya kashe su, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada ya ce,
“Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata,
tsirara kuma zan koma.
Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa;
yabo ya tabbata ga Ubangiji.”
Cikin wannan duka Ayuba bai yi wa Allah zunubi ta wurin ba shi laifi ba.
Gwajin Ayuba na biyu
Wata rana kuma mala’iku suka sāke kawo kansu gaban Ubangiji, sai Shaiɗan shi ma ya zo tare da su yă nuna kansa a gabansa. Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?”
Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”
Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah ba ruwansa da mugunta. Kuma har yanzu bai fasa zama mai aminci ba duk da wahalar da ka sa na bari ka ba shi ba tare da wani dalili ba.”
Shaiɗan ya amsa ya ce, “Fata don fata! Mutum zai iya rabuwa da duk abin da yake da shi domin ransa. Ka ɗan taɓa lafiyar jikinsa ka gani ba shakka zai la’anta ka kana ji kana gani.”
Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.”
Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa. Sai Ayuba ya ɗauki kaskon tukunya yana ta sosa ƙurajen da shi, yayinda yake zaune cikin toka.
Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!”
Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?”
A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.
Abokan Ayuba uku
Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi. Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu, sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki.
Ayuba ya yi magana
Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi. Ayuba ya ce,
“A hallaka ranar da aka haife ni,
da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’
Bari ranan nan ta zama duhu;
kada Allah yă kula da ita;
kada rana tă yi haske a wannan rana.
Bari duhu da inuwa mai duhu ta sāke rufe ta;
gizagizai kuma su rufe ta;
duhu kuma ya rufe haskenta.
Bari duhu mai yawa yă rufe daren nan;
kada a haɗa ta cikin kwanakin shekara,
ko kuma cikin kwanakin watanni.
Bari daren yă zama marar amfani;
kada a ji wata sowa ta farin ciki.
Bari waɗanda suke la’anta ranaku su la’anta wannan rana
su waɗanda suke umartar dodon ruwa.
Bari taurarinta na safe su zama duhu;
bari ranar tă yi ta jiran ganin haske
amma kada tă gani,
gama ba tă hana uwata ɗaukar cikina,
don ta hana ni shan wahalan nan ba.
“Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni,
ko kuma in mutu sa’ad da ana haihuwata ba?
Me ya sa aka haife ni,
aka tanada nono na sha na rayu?
Da yanzu ina kwance cikin salama;
da ina barcina cikin salama
tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa,
waɗanda suka gina wa kansu wuraren da yanzu duk sun rushe,
da shugabanni waɗanda suke da zinariya,
waɗanda suka cika gidajensu da azurfa.
Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba,
kamar jaririn da bai taɓa ganin hasken rana ba.
A wurin mugaye za su daina yin mugunta,
gajiyayyu kuma za su huta.
Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin;
an sake su ba za su sāke jin ana tsawata masu ba.
Manyan da ƙanana suna a can,
bawa kuma ya sami ’yanci daga wurin maigidansa.
“Don me ake ba da haske ga waɗanda suke cikin ƙunci,
rai kuma ga masu ɗacin rai
ga waɗanda suke neman mutuwa amma ba su samu ba,
waɗanda suke nemanta kamar wani abu mai daraja a ɓoye,
waɗanda suke farin ciki
sa’ad da suka kai kabari?
Don me aka ba mutum rai,
mutumin da bai san wani abu game da kansa ba,
mutumin da Allah ya kange shi.
Baƙin ciki ya ishe ni maimakon abinci;
ina ta yin nishi ba fasawa;
Abin da nake tsoro ya faru da ni;
abin da ba na so ya same ni.
Ba ni da salama, ba natsuwa;
ba ni da hutu, sai wahala kawai.”
Elifaz
Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
“In wani ya yi maka magana, za ka ji haushi?
Amma wa zai iya yin shiru?
Ka tuna yadda ka yi wa mutane da yawa magana,
yadda ka ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi.
Maganarka ta ƙarfafa waɗanda suka yi tuntuɓe;
ka ƙarfafa gwiwoyin da suka rasa ƙarfinsu.
Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya;
wahala ta sa ka rikice.
Ashe bai kamata ka dogara ga Allahnka ba,
amincinka kuma yă zama begenka?
“Ka duba ka gani yanzu. Wane marar laifi ne ya taɓa hallaka?
Ko an taɓa hallaka masu adalci?
Na kula cewa waɗanda suke huɗa gonar mugunta,
da waɗanda suke shuka mugunta, su ne suke girbe mugunta.
A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su,
cikin fushinsa yakan hallaka su.
Zakoki suna ruri suna gurnani;
duk da haka an karya haƙoran manyan zakoki.
Zakoki suna mutuwa domin ba dabbar da za su kashe su ci,
’ya’yan zakanya kuma sun watse.
“Asirce aka gaya mini maganan nan,
da ƙyar kunnuwana suka iya ji.
Cikin mafarki da tsakar dare,
lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan.
Tsoro da fargaba suka kama ni
har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa.
Wani iska ya taɓa mini fuska,
sai tsigar jikina ta tashi.
Ya tsaya cik,
amma ban iya sani ko mene ne ba.
Wani abu ya tsaya a gabana,
na kuma ji murya.
‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci,
ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki?
In Allah bai yarda da bayinsa ba,
in ya sami mala’ikunsa da laifi,
to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka,
waɗanda da ƙura aka yi harsashensu,
waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu!
Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su;
farat ɗaya, su mutu har abada.
Ba a tuge igiyar tentinsu,
don su mutu ba tare da hikima ba?’
“Ka yi kira in kana so, amma wa zai amsa maka?
Wurin waɗanne tsarkaka za ka juya?
Fushi yana kashe wawa,
ƙyashi kuma yana kashe marar azanci.
Ni ma na ga wawa yana cin gaba,
amma nan da nan gidansa ya zama la’ananne.
’Ya’yansa suna cikin hatsari,
ba wanda zai tsaya musu a gaban alƙali,
mayunwata sun kwashe girbinsa,
har abubuwan da suke cikin ƙaya,
masu jin ƙishirwa kuma suna zuba ido ga dukiyarsa.
Gama ba daga cikin ƙasa wahala take fitowa ba,
ko kuma bala’i daga ƙasa.
Duk da haka an haifi mutum don wahala ne,
kamar yadda ba shakka tartsatsin wuta yake tashi.
“Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah;
zan gaya masa damuwata.
Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa,
mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa.
Yana zuba ruwan sama a ƙasa;
yana zuba ruwa a gonaki.
Yana ɗaukaka masu sauƙinkai,
yana kāre waɗanda suke makoki.
Yana dagula shirye-shiryen masu wayo
don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi.
Yana kama masu wayo cikin wayonsu,
yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba.
Da rana sukan yi karo da duhu;
da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke.
Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi;
yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.
Saboda haka matalauta suna da bege,
rashin gaskiya kuma ta yi shiru.
“Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure;
saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.
Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon;
ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.
Zai cece ka daga bala’o’i guda shida;
har bakwai ma ba abin da zai same ka.
Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa,
a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.
Zai kāre ka daga ɓata suna,
kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo.
Za ka yi wa hallaka da yunwa dariya;
kuma ba ka bukata ka ji tsoron manyan namun jeji.
Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki,
kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai.
Za ka zauna lafiya a cikin tenti naka,
za ka ƙirga kayanka za ka samu kome na nan.
Za ka san cewa ’ya’yanka za su zama da yawa,
zuriyarka kuma kamar ciyawa a ƙasa.
Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu,
kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi.
“Mun yi nazarin wannan, kuma gaskiya ne.
Saboda haka ka ji, ka kuma yi amfani da shi.”
Ayuba
Sa’an nan Ayuba ya amsa,
“Da kawai za a iya auna wahalata
a kuma sa ɓacin raina a ma’auni!
Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi,
shi ya sa nake magana haka.
Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina,
ruhuna yana shan dafinsa;
fushin Allah ya sauka a kaina.
Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci,
ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?
Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba,
ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai?
Na ƙi in taɓa shi;
irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya.
“Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu,
da ma Allah zai biya mini bukatata,
wato, Allah yă kashe ni,
yă miƙa hannunsa yă yanke raina!
Da sai in ji daɗi
duk zafin da nake sha
ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.
“Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya?
Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri?
Da ƙarfin dutse aka yi ni ne?
Ko jikina tagulla ne?
Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne,
yanzu da aka kore nasara daga gare ni?
“Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki
ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.
Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba,
kamar rafin da yakan bushe da rani,
kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara,
yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,
amma da rani sai yă bushe,
lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin.
Ayari sukan bar hanyarsu;
sukan yi ta neman wurin da za su sami ruwa, su kāsa samu har su mutu.
Ayarin Tema sun nemi ruwa,
matafiya ’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu.
Ransu ya ɓace, domin sun sa zuciya sosai;
sa’ad da suka kai wurin kuwa ba su sami abin da suka sa zuciyar samu ba.
Yanzu kuma kun nuna mini ba ku iya taimako;
kun ga abin bantsoro kuka tsorata.
Ko na taɓa cewa, ‘Ku ba da wani abu a madadina,
ko na roƙe ku, ku ba da wani abu domina daga cikin dukiyarku,
ko kuma kun taɓa kuɓutar da ni daga hannun maƙiyina,
ko kun taɓa ƙwato ni daga hannun marasa kirki’?
“Ku koya mini, zan yi shiru;
ku nuna mini inda ban yi daidai ba.
Faɗar gaskiya tana da zafi!
Amma ina amfanin gardamar da kuke yi?
Ko kuna so ku gyara abin da na faɗi ne,
ku mai da magana wanda yake cikin wahala ta zama ta wofi?
Kukan yi ƙuri’a a kan marayu
ku kuma sayar da abokinku.
“Amma yanzu ku dube ni da kyau,
zan yi muku ƙarya ne?
Ku bi a hankali, kada ku ɗora mini laifi;
ku sāke dubawa, gama ba ni da laifi.
Ko akwai wata mugunta a bakina?
Bakina ba zai iya rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba?
“Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya?
Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne?
Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi,
ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi.
Saboda haka rabona shi ne watanni na zama banza,
kowane dare kuwa sai ɓacin rai nake samu.
Lokacin da na kwanta ina tunani, ‘Har sai yaushe zan tashi?’
Gari ya ƙi wayewa, ina ta jujjuyawa har safe.
Jikina duk tsutsotsi da ƙuraje sun rufe shi,
fatar jikina ta ruɓe tana fitar da ruwan miki.
“Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri,
za su kawo ga ƙarshe ba bege.
Ka tuna, ya Allah, raina numfashi ne kawai;
idanuna ba za su taɓa sāke ganin farin ciki ba.
Idanun da suke ganina yanzu ba za su sāke ganina ba;
za ku neme ni amma ba za ku same ni ba.
Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi,
haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba.
Ba zai taɓa zuwa gidansa ba;
ba za a sāke san da shi ba.
“Saboda haka ba zan yi shiru ba;
zan yi magana cikin ɓacin raina,
zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina.
Ni teku ne, ko kuwa dodon ruwa,
don me kake tsaro na?
Lokacin da nake zato zan sami salama
in na kwanta a gadona don in huta,
duk da haka kana ba ni tsoro da mafarke-mafarke,
kana tsorata ni da wahayi.
Na gwammace a shaƙe ni in mutu
maimakon in kasance cikin wannan jiki.
Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada.
Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani.
“Mene ne mutum har da ka kula da shi haka,
har ka mai da hankali a kansa,
har kake duba shi kowace safiya,
kake kuma gwada shi koyaushe?
Ba za ka ɗan daina kallo na ba
ko ka rabu da ni na ɗan lokaci?
In na yi zunubi, me na yi maka,
kai mai lura da mutane?
Don me ka sa ni a gaba?
Na zame maka kaya mai nauyi ne?
Me ya sa ba za ka gafarta mini laifofina ba?
Gama na kusa kwantawa cikin ƙasa;
za ka neme ni,
amma ba za ka same ni ba.”
Bildad
Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,
“Har yaushe za ka gama faɗa waɗannan abubuwa?
Maganganunka ba su da amfani.
Allah ba mai shari’ar gaskiya ba ne?
Ko Maɗaukaki yakan yi abin da ba daidai ba?
Lokacin da ’ya’yansa suka yi masa zunubi,
yakan bar su su sha wahalar da zunubi yake kawowa.
Amma in za ka dubi Allah
ka roƙi Maɗaukaki,
in kai mai tsarki ne, kuma mai adalci,
ko yanzu ma zai taimake ka,
yă mayar maka iyalinka da farin cikinka.
Ko da yake za ka fara da kaɗan,
duk da haka za ka gama da samu mai yawa.
“Tambayi na gaba da kai
ka ji abin da iyayenka suka koya
gama jiya kaɗai aka haife mu ba mu san kome ba,
kuma kwanakinmu a duniya masu wucewa ne.
Ba za su bishe ka su kuma gaya maka abin da za ka yi ba?
Ba za su yi magana daga cikin hikimar da suke da ita ba?
Ko kyauro zai iya yi girma a wurin da ba ruwa?
Ko za tă taɓa iya yin girma ba tare da ruwa ba?
Yayinda take girma ba a yanka ta,
takan mutu da sauri fiye da ciyawa.
Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah;
waɗanda ba su da Allah, ba su da bege.
Abin da yake dogara a kai ba shi da ƙarfi;
abin da yake dogara a kai yanar gizo ce.
Ya jingina ga yanar gizo, amma ba ta tare shi,
sun kama ta, amma ba za tă taimake su tsayawa ba.
Yana kama da shukar da aka ba ta ruwa sosai lokacin da akwai rana sosai,
tana yaɗuwa da kyau;
shukar tana bin yaɗuwa, jijiyoyinta suna nannaɗe duwatsu,
suna neman wurin da za su kama sosai a cikin duwatsu.
Amma lokacin da aka tuge shukar daga wurin da take,
wurin ba zai san da ita kuma ba, wurin zai ce, ‘Ban taɓa ganin ki ba.’
Ba shakka shukar ta mutu ke nan,
kuma waɗansu za su tsiro a wurin.
“Ba shakka, Allah ba ya ƙin marar laifi,
ko kuma yă ƙarfafa masu aikata mugunta.
Sai dai yă cika bakinka da dariya,
yă sa ka yi sowa ta murna.
Maƙiyanka za su sha kunya,
za a kawar da tentin mugaye.”
Ayuba
Sai Ayuba ya amsa,
“Lalle, na san wannan gaskiya ne.
Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?
Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi,
ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.
Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa.
Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?
Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani
kuma yana juya su cikin fushinsa.
Yana girgiza ƙasa,
yana girgiza harsashenta.
Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske;
yana hana taurari yin haske.
Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai
ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.
Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza,
da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.
Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa,
mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.
Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni;
ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce.
Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu?
Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’
Allah ba ya danne fushinsa;
ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su.
“Ta yaya zan iya yin faɗa da shi?
Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi?
Ko da yake ba ni da laifi, ba zan iya amsa masa ba;
sai dai roƙon jinƙai zan iya yi ga mahukuncina.
Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini,
ban yarda cewa zai saurare ni ba.
Zai sa hadari yă danne ni
yă ƙara mini ciwona ba dalili.
Ba zai bari in yi numfashi ba,
sai dai yă ƙara mini azaba.
In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne!
In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?
Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi;
in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.
“Ko da yake ba ni da laifi,
ban damu da kaina ba;
na rena raina.
Ba bambanci; shi ya sa na ce,
‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’
Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa,
yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.
Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye,
yakan rufe idanun masu shari’a.
In ba shi ba wa zai yi wannan?
“Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri;
suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu.
Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro,
kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.
‘In na ce zan manta da abin da yake damu na,
zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’
duk da haka ina tsoron duk wahalata,
domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.
Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi,
duk ƙoƙarina a banza yake.
Ko da na wanke jikina duka da sabulu,
na wanke hannuwana kuma da soda,
duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri,
yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.
“Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa,
har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a.
In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu,
ya ɗora hannunsa a kanmu tare,
wani wanda zai sa Allah yă daina duka na,
don yă daina ba ni tsoro.
Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba,
amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.
“Na gaji da rayuwa;
saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi
yadda raina yake jin ba daɗi.
Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni,
amma ka gaya mini laifin da na yi maka.
Kana jin daɗin ba ni wahala,
don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka,
yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?
Idanunka irin na mutum ne?
Kana gani yadda mutum yake gani ne?
Kwanakinka kamar na mutane ne,
ko shekarunka kamar na mutane ne
da za ka neme ni da laifi
ka hukunta ni?
Ko da yake ka san ba ni da laifi,
kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.
“Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni.
Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?
Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu.
Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?
Ba kai ka zuba ni kamar madara ba,
na daskare kamar cuku.
Ka rufe ni da tsoka da fata,
ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?
Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri,
kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.
“Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka,
na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.
In na yi zunubi kana kallo na
kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.
Idan ina da laifi, kaitona!
Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba,
gama kunya ta ishe ni
duk ɓacin rai ya ishe ni.
In na ɗaga kaina, za ka neme ni kamar zaki
ka sāke nuna al’ajabin ikonka a kaina.
Kana sāke kawo sababbin waɗanda za su ba da shaida a kaina
kana ƙara haushinka a kaina;
kana ƙara kawo mini hari.
“Me ya sa ka fito da ni daga cikin uwata?
Da ma na mutu kafin a haife ni.
Da ma ba a halicce ni ba,
da na mutu tun daga cikin cikin uwata na wuce zuwa kabari!
’Yan kwanakina ba su kusa ƙarewa ba ne?
Ka rabu da ni don in ɗan samu sukuni na ɗan lokaci
kafin in koma inda na fito,
ƙasa mai duhu da inuwa sosai,
zuwa ƙasa mai duhun gaske,
da inuwa da hargitsi,
inda haske yake kamar duhu.”
Zofar
Sa’an nan Zofar mutumin Na’ama ya amsa,
“Duk surutun nan ba za a amsa maka ba?
Ko mai surutun nan marar laifi ne?
Ko maganganun nan naka marasa amfani za su sa mutane su yi maka shiru?
Ba wanda zai kwaɓe ka lokacin da kake faɗar maganar da ba daidai ba?
Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne
kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’
Da ma Allah zai yi magana,
yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba
yă kuma buɗe maka asirin hikima,
gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu.
Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka.
“Ko za ka iya gane al’amuran Allah?
Ko za ka iya gane girman asirin Maɗaukaki?
Sun fi nisan sama tudu, me za ka iya yi?
Sun fi zurfin kabari zurfi, me za ka sani?
Tsayinsu ya fi tsawon duniya
da kuma fāɗin teku.
“In ya zo ya kulle ka a kurkuku
ya ce kai mai laifi ne, wa zai hana shi?
Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya;
kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?
Amma daƙiƙin mutum ba ya taɓa zama mai hikima
kamar dai a ce ba a taɓa haihuwar ɗan aholaki horarre.
“Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka,
ka kuma miƙa hannuwanka gare shi,
in ka kawar da zunubin da yake hannunka,
ba ka bar zunubi ya kasance tare da kai ba
shi ne za ka iya ɗaga fuskarka ba tare da jin kunya ba;
za ka tsaya da ƙarfi kuma ba za ka ji tsoro ba.
Ba shakka za ka manta da wahalolinka,
za ka tuna da su kamar yadda ruwa yake wucewa.
Rayuwarka za tă fi hasken rana haske,
duhu kuma zai zama kamar safiya.
Za ka zauna lafiya, domin akwai bege;
za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.
Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro,
da yawa za su zo neman taimako a wurinka.
Amma idanun mugaye ba za su iya gani ba,
kuma ba za su iya tserewa ba;
begensu zai zama na mutuwa.”
Ayuba
Sai Ayuba ya amsa,
“Ba shakka ku ne mutanen nan,
hikima za tă mutu tare da ku!
Amma ni ma ina da hankali kamar ku;
ba ku fi ni ba.
Wane ne bai san duk waɗannan abubuwan ba?
“Na zama abin dariya ga abokaina,
ko da yake na yi kira ga Allah ya kuwa amsa mini,
duk da haka suka yi mini riya ko da yake ni mai adalci ne kuma marar laifi!
Mutanen da ba su da damuwa suna jin daɗin ganin waɗanda
suke dab da fāɗuwa.
Amma wurin zaman ’yan fashi yana nan ba mai damunsu,
waɗanda kuma suke saɓa wa Allah suna zamansu lafiya,
har ma da masu ɗaukar allahnsu a hannuwansu.
“Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka,
ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.
Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka,
ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.
Wane ne cikin waɗannan bai san
cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?
Ran kowace halitta yana a hannunsa,
haka kuma numfashin dukan ’yan adam.
Ko kunne ba ya gwada kalmomi
kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci?
Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba?
Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?
“Allah ne mai iko da kuma hikima,
shawara da ganewa nasa ne.
Abin da ya rushe ba a iya ginawa ba;
in ya kulle mutum ba a iya buɗe shi a sake shi ba.
Idan ya hana ruwan sama, za a yi fări;
in kuma ya saki ruwa za a yi ambaliya.
Shi ne mai ƙarfi da kuma mai nasara;
mai ruɗi da wanda aka ruɗa, duk nasa ne.
Yakan sa mashawarta su zama marasa hikima
yă kuma sa wawaye su zama masu shari’a.
Yana cire sarƙar da sarakuna suka ɗaura
yă kuma ɗaura musu wata tsumma a kwankwaso.
Yakan ƙasƙantar da firistoci
yă kuma tumɓuke masu ikon da aka kafa tun da daɗewa.
Yana sa amintattun mashawarta su yi shiru
yakan kawar da hikimar dattawa.
Yakan sa masu iko su ji kunya
yă kuma ƙwace ƙarfin masu ƙarfi.
Yana buɗe abubuwan da suke cikin duhu
yă kuma kawo haske a wuraren da ba haske;
yana sa al’ummai su zama manya, sai kuma yă hallaka su;
yana sa al’ummai su ƙasaita, yă kuma watsar da su.
Yana hana shugabannin duniya ganewa;
Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata.
Suna lallube cikin duhu ba haske;
yă sa su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.
“Idanuna sun ga waɗannan duka,
kunnuwana sun ji sun kuma gane.
Abin da kuka sani, ni ma na sani;
ba ku fi ni ba.
Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki,
in kai kukana wurin Allah kai tsaye.
Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi;
ku likitocin wofi ne, dukanku!
In da za ku yi shiru gaba ɗaya!
Zai zama muku hikima.
Ku ji gardamata yanzu;
ku ji roƙon da zai fito daga bakina.
Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah?
Ko za ku yi ƙarya a madadinsa?
Ko za ku nuna masa sonkai?
Ko za ku yi gardama a madadinsa?
In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi?
Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane?
Ba shakka zai kwaɓe ku
in kun nuna sonkai a ɓoye.
Ko ikonsa ba ya ba ku tsoro?
Tsoronsa ba zai auka muku ba?
Duk surutanku kamar toka suke;
kāriyarku na yimɓu ne.
“Ku yi shiru zan yi magana;
sa’an nan abin da zai same ni yă same ni.
Don me na sa kaina cikin hatsari
na yi kasada da raina?
Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance;
ba shakka zan kāre kaina a gabansa
lalle wannan zai kawo mini kuɓuta
gama ba wani marar tsoron Allah da zai iya zuwa wurinsa!
Ku saurara da kyau ku ji abin da zan faɗa;
bari kunnuwanku su ji abin da zan ce.
Yanzu da na shirya ƙarata,
na san za a ce ba ni da laifi.
Ko wani zai ce ga laifin da na yi?
In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu.
“Kai dai biya mini waɗannan bukatu biyu kawai ya Allah,
ba zan kuwa ɓoye daga gare ka ba;
Ka janye hannunka nesa da ni,
ka daina ba ni tsoro da bantsoronka.
Sa’an nan ka kira ni, zan kuwa amsa,
ko kuma ka bar ni in yi magana sai ka amsa mini.
Abubuwa nawa na yi waɗanda ba daidai ba, kuma zunubi ne?
Ka nuna mini laifina da zunubina.
Don me ka ɓoye mini fuskarka;
ka kuma sa na zama kamar maƙiyinka?
Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa?
Ko za ka bi busasshiyar ciyawa?
Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni;
ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata.
Ka daure ƙafafuna da sarƙa;
kana kallon duk inda na taka
ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna.
“Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu,
kamar rigar da asu ya cinye.
“Mutum haihuwar mace
kwanakinsa kaɗan ne, kuma cike da wahala.
Yana tasowa kamar fure yana kuma shuɗewa;
kamar inuwa, ba ya daɗewa.
Za ka zura ido a kan irin wannan ne?
Za ka kawo shi gaba don ka yi masa shari’a?
Wane ne zai iya kawo abin da yake da tsarki daga cikin abu marar tsarki?
Babu!
An lissafta kwanakin mutum;
ka riga ka ɗibar masa watanni,
ka yi masa iyaka, ba zai iya wuce iyakar ba.
Saboda haka ka kawar da kanka daga gare shi,
ka rabu da shi har sai ya cika lokacinsa kamar mutumin da aka ɗauki hayarsa.
“Aƙalla itace yana da bege.
In an sare shi, zai sāke tsira,
zai tohu da kyau.
Ko da jijiyoyin itacen sun tsufa a cikin ƙasa
kuma kututturensa ya mutu a cikin ƙasa.
Daga ya ji ƙanshin ruwa zai tohu
yă yi tsiro kamar shuka.
Amma mutum yana mutuwa a bizne shi;
daga ya ja numfashinsa na ƙarshe, shi ke nan.
Kamar yadda ruwa yake bushewa a teku ko a gaɓar rafi
sai wurin yă bushe,
haka mutum zai kwanta ba zai tashi ba;
har sai duniya ta shuɗe
mutane ba za su farka ba, ba za su tashi daga barcinsu ba.
“Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabari
ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce!
In da za ka keɓe mini lokaci
sa’an nan ka tuna da ni!
In mutum ya mutu, ko zai sāke rayuwa?
In haka ne zan daure
kwanakin da nake shan wahala har su wuce.
Za ka kira zan kuwa amsa maka;
za ka yi marmarin abin da hannunka ya halitta.
Ba shakka a lokacin ne za ka lura da matakaina
amma ba za ka kula da zunubaina ba.
Za a daure laifofina a cikin jaka;
za ka rufe zunubaina.
“Amma kamar yadda manyan duwatsu suke fāɗuwa
su farfashe su kuma gusa daga wurarensu,
yadda ruwa yakan zaizaye duwatsu
ruwa mai ƙarfi kuma yă kwashe turɓayar ƙasa,
haka kake barin mutum ba bege.
Ka sha ƙarfinsa gaba ɗaya, sai ya ɓace,
ka sauya yanayinsa ka kuma kore shi.
Ko an martaba ’ya’yansa maza, ba zai sani ba;
Ko an wulaƙanta su, ba zai gani ba.
Zafin jikinsa kaɗai yake ji
yana kuka wa kansa ne kaɗai.”
Elifaz
Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
“Mutum mai hikima zai amsa da surutai marasa kan gado
ko yă cika cikinsa da iskar gabas?
Ko zai yi gardama da maganganun wofi
maganganu marasa amfani?
Amma ka ma rena Allah
ka hana a yi addu’a gare shi.
Zunubanka ne suke gaya maka abin da za ka ce;
kana magana kamar mai wayo.
Bakinka zai kai ka yă baro, ba nawa ba;
maganar bakinka za tă juya a kanka.
“Kai ne mutum na farko da aka fara haihuwa?
Ko kai ne aka fara halitta kafin tuddai?
Kana sauraron shawarar Allah?
Ko kana gani kai kaɗai ne mai hikima?
Me ka sani da ba mu sani ba?
Wane fahimi kake da shi da ba mu da shi?
Masu furfura da tsofaffi suna gefenmu
mutanen da sun girme babanka.
Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba.
Maganarsa mai laushi ba tă ishe ka ba?
Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka,
kuma don me idanunka suke haske,
har kake fushi da Allah
kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka?
“Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki,
ko kuma mace ta haife shi, har yă iya zama mai adalci?
In Allah bai nuna amincewa ga tsarkakansa ba,
in har sammai ba su da tsarki a idonsa,
mutum fa, wanda yake da mugunta da lalacewa,
wanda yake shan mugunta kamar ruwa!
“Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani;
bari in gaya maka abin da na gani,
abin da masu hikima suka ce,
ba tare da sun ɓoye wani abu da suka samu daga wurin iyayensu ba
(waɗanda su ne masu ƙasar
kafin baƙi su shigo ƙasar).
Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala,
wahala kaɗai zai yi ta sha.
Ƙara mai bantsoro za tă cika kunnuwansa
’yan fashi za su kai masa hari.
Yana jin tsoron duhu
domin za a kashe shi da takobi.
Yana ta yawo, abinci don ungulaye;15.23 Ko kuwa yawo, neman abinci
ya san ranar duhu tana kusa.
Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi,
kamar sarkin da yake shirin yaƙi,
domin ya nuna wa Allah yatsa
ya rena Allah Maɗaukaki,
ya tasar masa da faɗa
da garkuwa mai kauri da kuma ƙarfi.
“Ko da yake fuskarsa ta cika da kumatu
kuma yana da tsoka ko’ina,
zai yi gādon garuruwan da suka lalace,
da kuma gidajen da ba wanda yake zama a ciki,
gidajen da sun zama tarkace.
Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za tă dawwama ba,
abin da ya mallaka kuma ba zai bazu a ƙasar ba.
Ba zai tsere wa duhu ba;
wuta za tă ƙona rassansa,
kuma numfashi daga bakin Allah zai hallaka shi.
Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani
domin ba zai samu wani abu ba daga ciki.
Kafin lokacinsa yă cika, za a gama biyansa duka,
kuma rassansa ba za su ba da amfani ba.
Zai zama kamar itacen inabi wanda ’ya’yansa suka kakkaɓe kafin su nuna,
kamar itacen zaitun zai zubar da furensa.
Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da ’ya’ya,
wuta kuma za tă ƙona tenti na masu son cin hanci.
Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta;
cikinsu yana cike da ruɗami.”
Ayuba
Sai Ayuba ya amsa,
“Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan;
dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!
Dogayen surutanku ba sa ƙare ne?
Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?
Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi
in da kuna cikin halin da nake;
zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi,
in kaɗa muku kaina.
Amma bakina zai ƙarfafa ku;
ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku.
“Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi;
in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.
Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni;
ka ɓata gidana gaba ɗaya.
Ka daure ni, ya kuma zama shaida;
yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.
Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa
yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni;
ya zura mini ido.
Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni;
suka yi mini ba’a
suka haɗu suka tayar mini.
Allah ya bashe ni ga mugayen mutane,
ya jefa ni hannun mugaye.
Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai;
amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya;
ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;
maharbansa sun kewaye ni.
Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata
har jini ya zuba a ƙasa.
Ya ji mini rauni a kai a kai
ya auko mini kamar mai yaƙi.
“Ina makoki saye da tsummoki
na ɓoye fuskata a cikin ƙura.
Fuskata ta yi ja don kuka
idanuna sun kukumbura;
duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba
kuma addu’ata mai tsabta ce.
“Ya duniya, kada ki ɓoye jinina;
bari yă yi kuka a madadina!
Ko yanzu haka shaidata tana sama;
wanda zai tsaya mini yana sama.
Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne
yayinda nake kuka ga Allah;
a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah
kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
“Shekaru kaɗan suka rage
in kama hanyar da ba a komawa.
Na karaya,
kwanakina sun kusa ƙarewa,
kabari yana jirana.
Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni;
idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini.
“Ya Allah, ka ba ni abin da ka yi mini alkawari.
Wane ne zai kāre ni?
Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba,
saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.
In mutum ya juya wa abokansa baya don a ba shi wata lada
’ya’yansa za su makance.
“Allah ya sa na zama abin da kowa yake magana a kai
wanda kowa yake tofa wa miyau a fuska.
Idanuna ba sa gani sosai don baƙin ciki;
jikina ya zama kamar inuwa kawai
Mutanen da suke masu adalci wannan abu ya ba su tsoro;
marasa laifi sun tayar wa marasa tsoron Allah.
Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu,
waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi.
“Amma ku zo dukanku, ku sāke gwadawa!
Ba zan sami mutum ɗaya mai hikima ba a cikinku.
Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci
haka kuma abubuwan da zuciyata take so.
Mutanen nan sun juya rana ta zama dare.
A tsakiyar duhu suka ce, ‘Haske yana kusa.’
In kabari ne begen da nake da shi kaɗai,
in na shimfiɗa gadona a cikin duhu,
In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’
tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’
To, ina begena yake?
Wane ne zai iya ganin wani bege domina?
Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne?
Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?”
Bildad
Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,
“Yaushe za ka gama maganganun nan?
Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.
Don me muke kamar shanu a wurinka,
ka ɗauke mu mutanen wofi?
Kai da ka yayyage kanka don haushi,
za a yashe duniya saboda kai ne?
Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?
“An kashe fitilar mugu;
harshen wutarsa ya daina ci.
Wutar cikin tentinsa ta zama duhu;
fitilar da take kusa da shi ta mutu.
Ƙarfin takawarsa ya ragu;
dabararsa ta ja fāɗuwarsa.
Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga,
yana ta yawo a cikin ragar.
Tarko ya kama ɗiɗɗigensa;
tarko ya riƙe shi kam.
An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa;
an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.
Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe
yana bin shi duk inda ya je.
Masifa tana jiransa;
bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.
Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa;
ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.
An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa
aka sa shi tsoro sosai.
Wuta ta cinye tentinsa;
farar wuta ta rufe wurin da yake zama.
Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa
rassansa sun mutu a sama.
An manta da shi a duniya;
ba wanda yake ƙara tunawa da shi.
An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu,
an kore shi daga duniya.
Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa,
ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.
Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi;
tsoro ya kama mutanen gabas.
Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake,
haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”
Ayuba
Sai Ayuba ya amsa,
“Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba
ku kuma murƙushe ni da maganganunku?
Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni,
kuna kai mini hari na rashin kunya.
In gaskiya ne na yi laifi,
kuskurena ya rage nawa.
In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina
kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne,
sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba
ya kewaye ni da ragarsa.
“Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba;
ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba.
Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba;
ya rufe hanyata da duhu.
Ya cire darajar da nake da ita,
ya kuma cire rawani daga kaina.
Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare;
ya tuge begen da nake da shi kamar itace.
Yana jin haushina
ya lissafta ni cikin maƙiyansa.
Rundunarsa ta zo da ƙarfi;
suka kafa sansani kewaye da ni,
suka zagaye tentina.
“Ya raba ni da ’yan’uwana maza;
abokaina sun zama baƙi gare ni.
Dangina sun tafi;
abokaina na kurkusa sun manta da ni.
Waɗanda sukan ziyarce ni,
da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo.
Na kira bawana, amma bai amsa ba,
ko da yake na roƙe shi da bakina.
Numfashina yana ɓata wa matata rai;
’yan’uwana sun ƙi ni.
Har ’yan yara suna rena ni;
in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.
Duk abokaina sun yashe ni;
waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.
Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi,
da ƙyar na tsira.
“Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina,
gama hannun Allah ya sauko a kaina.
Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi?
Ba ku gaji da yagar fatata ba?
“Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna,
da an rubuta su a littafi,
a rubuta su da ƙarfe a kan dutse
don su dawwama har abada!
Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai,
kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.
Kuma bayan an hallaka fatata,
duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.
Zan gan shi da kaina
da idanuna, Ni, ba wani ba ne.
Zuciyata ta cika da wannan tunani!
“In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini,
tun da shi ne tushen damuwa,’
sai ku ma ku ji tsoron takobin;
gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi,
sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.”
Zofar
Sai Zofar mutumin Na’ama ya amsa,
“Tunanin da ya dame ni ya sa dole in amsa
domin abin ya dame ni sosai.
Na ji wani zargin da ka yi mini na reni,
kuma yadda na gane, shi ya sa zan ba da amsa.
“Ba shakka ka san yadda abin yake tuntuni,
tun da aka sa mutum cikin duniya,
mugun mutum bai taɓa daɗewa ba,
farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne.
Ko da ya ƙasaita ya kai sararin sama,
kansa kuma yana taɓa gizagizai.
Zai hallaka har abada, kamar bayan gidansa;
waɗanda suka gan shi za su ce, ‘Ina yake?’
Kamar mafarki haka zai ɓace, ba za a ƙara ganinsa ba
zai ɓace kamar wahayi da dare.
Idon da ya gan shi ba zai ƙara ganinsa ba;
wurin zamansa ba zai sāke ganinsa ba.
Dole ’ya’yansa su mayar wa matalauta abin da ya kamata;
dole hannuwansa su mayar da dukiyarsa.
Jin ƙarfi da ya cika ƙasusuwansa
zai kwantar da shi a cikin ƙura.
“Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa
kuma yana ɓoye ta a harshensa,
ko da yake ba zai iya rabuwa da ita ba,
yana kuma ajiye ta a bakinsa,
duk da haka abincin da ya ci zai zama da tsami a cikin cikinsa;
zai zama kamar dafin maciji a cikinsa.
Zai haras da dukiyar da ya haɗiye;
Allah zai sa cikinsa yă haras da su.
Zai sha dafin maciji;
sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.
Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka
masu kwarara da zuma da madara ba.
Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu,
ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba.
Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala;
ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba.
“Ba shakka ba zai samu abin da yake ƙoƙarin samu ba,
dukiyarsa ba za tă cece shi ba.
Ba abin da ya ragu da zai ɗauka;
arzikinsa ba zai dawwama ba.
Yana cikin samun arziki, ɓacin rai zai auka masa;
ƙunci mai ƙarfi zai zo masa.
Lokacin da ya cika cikinsa,
Allah zai zuba fushinsa a kansa,
zai daddaka shi.
Ko da yake yana guje wa makamin ƙarfe,
kibiya mai bakin tagulla za tă huda shi.
Zai zāre ta daga bayansa,
tsinin zai fita daga hantarsa;
tsoro zai cika shi;
duhu kawai yake jiran dukiyarsa.
Wutar da ba a fifita ba za tă cinye shi
ta kuma ƙona duk abin da ya rage a tentinsa.
Sammai za su fallasa laifinsa;
duniya za tă yi gāba da shi.
Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa,
ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah.
Abin da Allah zai sa yă faru da mugu ke nan,
gādon da Allah ya ba shi ke nan.”
Ayuba
Sai Ayuba ya amsa,
“Ku saurare ni da kyau;
bari wannan yă zama ta’aziyyar da za ku ba ni.
Ku ba ni zarafi in yi magana,
bayan na gama sai ku yi ba’arku.
“A wurin mutum ne na kawo kukana?
Don me ba zan kāsa haƙuri ba?
Ku dube ni, ku kuma yi mamaki;
ku rufe bakina da hannunku.
Lokacin da na yi tunanin wannan,
sai in ji tsoro; jikina yă fara rawa.
Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa,
suna kuma ƙaruwa da iko?
Suna ganin ’ya’yansu suna girma,
suna ganin jikokinsu suna tasowa a kan idanunsu.
Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba.
Kuma Allah ba ya ba su horo.
Shanunsu ba sa fasa haihuwa;
suna haihuwa ba sa yin ɓari.
Suna aika ’ya’yansu kamar garke;
’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle.
Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya;
suna jin daɗin busar sarewa.
Suna yin rayuwarsu cikin arziki
kuma su mutu cikin salama.
Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’
Ba ma so mu san hanyoyinka.
Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa?
Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?
Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba
saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
“Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa?
Sau nawa bala’i yake auka masa,
ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?
Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska,
ko kuma kamar ƙura da iskar hadari take kwashewa?
An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’
Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!
Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka;
bari yă sha daga fushin Maɗaukaki.
Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya
sa’ad da kwanakinsa suka ƙare?
“Wani zai iya koya wa Allah ilimi
tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?
Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi
da kwanciyar hankali,
jikinsa ɓulɓul,
ƙasusuwansa da alamar ƙarfi.
Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai,
bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba.
Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa,
kuma tsutsotsi za su cinye su.
“Na san duk abin da kuke tunani,
yadda za ku saɓa mini.
Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan,
tenti wurin da mugaye suke zama?’
Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba?
Ba ku kula da labaransu,
cewa an kāre mugu daga ranar bala’i,
an kāre shi daga ranar fushi?
Wane ne yake gaya masa abin da ya yi?
Wane ne yake rama abin da ya yi?
Za a bizne shi a kabari,
a kuma yi tsaron kabarinsa.
Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali;
dukan jama’a suna binsa,
da yawa kuma suna gabansa.
“Saboda haka ta yaya za ku iya yi mini ta’aziyya
da surutan banzan nan naku? Babu wani abu cikin amsarku sai ƙarya!”
Elifaz
Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
“Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah?
Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?
Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne?
Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?
“Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka
ya kuma bari haka yă same ka?
Ba muguntarka ce ta yi yawa ba?
Ba zunubanka ne ba iyaka ba?
Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili;
ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara.
Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba
kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.
Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa,
mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka.
Ka kori gwauraye hannu wofi,
ka kuma karya ƙarfin marayu.
Shi ya sa kake kewaye da tarkuna,
shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka.
An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani,
shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka.
“Ba Allah ne a can sama ba?
Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama!
Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani?
A cikin duhu ne yake shari’a?
Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu
lokacin da yake takawa a cikin sammai.’
Za ka ci gaba da bin tsohuwar hanyar
da mugayen mutane suka bi?
An ɗauke su kafin lokacinsu yă cika,
ruwa ya share tushensu.
Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu!
Me Maɗaukaki zai yi mana?’
Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau,
saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
“Masu adalci suna gani ana hallaka mugaye, suna jin daɗi;
marasa laifi suna yi musu ba’a, suna cewa,
‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu,
wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’
“Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa;
ta haka ne arziki zai zo maka.
Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa
kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka.
In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke.
In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.
Ka jefar da zinariyarka a ƙasa,
ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,
sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka,
zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.
Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki
daga wurin Maɗaukaki,
ku kuma ɗaga idanunku ga Allah
Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka,
kuma za ka cika alkawuranka.
Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki,
haske kuma zai haskaka hanyarka.
Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’
Sa’an nan zai ceci masu tawali’u.
Zai ceci wanda ma yake mai laifi,
wanda zai tsirar da shi ta wurin tsabtar hannuwanka.”
Ayuba
Sa’an nan Ayuba ya amsa,
“Ko a yau, ina kuka mai zafi;
hannunsa yana da nauyi duk da nishin da nake yi.
Da a ce na san inda zan same shi;
da a ce zan iya zuwa wurin da yake zama!
Zan kai damuwata wurinsa
in yi gardama da shi.
Zan nemi in san abin da zai ce mini,
in kuma auna abin da zai ce mini.
Zai yi gardama da ni da ikonsa mai girma?
Babu, ba zai zarge ni da laifi ba.
Mai adalci ne zai kawo ƙara a wurinsa,
kuma zan samu kuɓuta daga wurin mai shari’an nan har abada.
“Amma in na je gabas, ba ya wurin;
in na je yamma, ba zan same shi ba.
Sa’ad da yake aiki a arewa, ba ni ganinsa;
sa’ad da ya juya zuwa kudu, ba na ganinsa.
Amma ya san hanyar da nake bi;
sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya.
Ƙafafuna suna bin ƙafafunsa kurkusa;
na bi hanyarsa ba tare da na juya ba.
Ban fasa bin dokokin da ya bayar ba;
na riƙe maganarsa da muhimmanci fiye da abincin yau da gobe.
“Amma ya tsaya shi kaɗai, kuma wa ya isa yă ja da shi?
Yana yin abin da yake so.
Yana yi mini abin da ya shirya yă yi mini,
kuma yana da sauran irinsu a ajiye.
Shi ya sa na tsorata a gabansa;
sa’ad da na yi tunanin wannan duka, nakan ji tsoronsa.
Allah ya sa zuciyata ta yi sanyi;
Maɗaukaki ya tsorata ni.
Duk da haka duhun bai sa in yi shiru ba,
duhun da ya rufe mini fuska.
“Domin me Maɗaukaki ba zai sa ranar shari’a ba?
Don me waɗanda suka san shi suke faman samun irin ranakun nan?
Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su;
suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su.
Suna ƙwace wa marayu jakunansu
suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi.
Suna ture matalauta daga hanya
suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye.
Kamar jakunan jeji a hamada,
matalauta suna aikin neman abinci
gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu.
Suna girbi a gonakin da ba nasu ba,
suna yin kala a gonar inabi ta mugaye.
Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara;
ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi.
Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu,
sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa.
Ana ƙwace jinjiri mai shan mama;
ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.
Don ba su da tufafi suna yawo tsirara;
suna dakon dammunan hatsi
amma duk da haka suna cikin shan yunwa.
Suna matse zaitun a cikin kunyoyi
suna kuma matse ruwan inabi daga ’ya’yan inabi, duk da haka suna fama da ƙishi.
Ana jin nishin masu mutuwa daga birni,
kuma rayukan waɗanda aka ji musu rauni suna kuka suna kira don taimako.
Amma bai ba wani laifi ba.
“Akwai waɗanda suke yi wa haske tawaye,
waɗanda ba su san hanyoyinsa ba
ko kuma ba su taɓa bin hanyoyinsa ba.
Sa’ad da hasken yini ya tafi, mai kisankai yakan tashi;
yă je yă kashe matalauta da masu bukata;
a cikin dare yake shigowa kamar ɓarawo.
Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai;
yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’
sai kuma yă ɓoye fuskarsa.
Cikin duhu mutane suna fasa gidaje,
amma da rana sukan kulle kansu;
ba sa so wani abu yă haɗa su da haske.
Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu;
suna abokantaka da razanar duhu.
“Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa;
gefen ƙasar da suke, an la’anta ta,
yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu.
Kamar yadda zafi da fări suke shanye ƙanƙarar da ta narke,
haka kabari zai ƙwace waɗanda suka yi zunubi.
Waɗanda suka haife su za su manta da su,
tsutsotsi za su cinye su;
ba za a sāke tunawa da mugaye ba
amma an sare su kamar itace.
Suna cutar macen da ba ta da ɗa,
suna nuna wa gwauruwa rashin alheri.
Amma Allah cikin ikonsa yakan kawar da masu ƙarfi,
ko da yake sun yi ƙarfi, ba su da tabbacin rayuwa.
Mai yiwuwa zai bar su su zauna cikin kwanciyar hankali,
amma idanunsa suna kansu.
Sukan samu cin nasara na ɗan lokaci,
amma kuma za su ɓace; za su fāɗi
a tattara su kamar sauran; za a datse su kamar kan hatsi.
“In wannan ba haka ba ne,
wane ne zai shaida ƙarya nake yi har yă ƙi yarda da maganata?”
Bildad
Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,
“Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa;
yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.
Za a iya ƙirga rundunarsa?
A kan wane ne ba ya haska haskensa?
Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?
Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?
In har wata da taurari
ba su da tsarki a idanunsa,
mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.
Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”
Ayuba
Sai Ayuba ya amsa,
“Yadda ka taimaki marar ƙarfi!
Yadda ka ceci marar ƙarfi!
Ka ba marar hikima shawara!
Ka nuna kana da ilimi sosai.
Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu?
Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka?
“Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye
da dukan mazauna cikin ruwaye.
Mutuwa tsirara take a gaban Allah;
haka kuma hallaka take a buɗe.
Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari;
ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.
Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa,
duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.
Ya rufe fuskar wata,
ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,
ya zāna iyakar fuskar ruwa
a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.
Madogaran sama sun girgiza,
saboda tsawatawarsa.
Da ikonsa ya kwantar da teku;
da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.
Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau
da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.
Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa.
Kaɗan kawai muke ji game da shi!
Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”
Ayuba kuwa ya ci gaba da magana,
“Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata,
Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.
Muddin ina da rai a cikina
kuma numfashin Allah yana cikin hancina,
bakina ba zai faɗi mugun abu ba,
harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.
Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba;
har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.
Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba;
lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina.
“Bari maƙiyana su zama kamar mugaye,
masu gāba da ni kuma su zama kamar marasa adalci.
Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi,
lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa?
Ko Allah yana sauraron kukansa
lokacin da ƙunci ya auko masa?
Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki?
Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?
“Zan koya muku game da ikon Allah;
ba zan ɓoye hanyoyin Maɗaukaki ba.
Duk kun ga wannan ku da kanku
saboda haka me ya sa kuke maganganun nan marasa ma’ana?
“Ga abin da mugaye za su samu
gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki.
Kome yawan ’ya’yansa, takobi za tă gama da su;
zuriyarsa ba za su taɓa samun isashen abinci ba.
Waɗanda suka tsira annoba za tă kashe su,
kuma gwaurayensu ba za su yi kukan mutuwarsu ba.
Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa,
tufafi kuma kamar tarin ƙasa,
abin da ya tara masu adalci za su sa
marasa laifi za su raba azurfarsa.
Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo,
kamar bukkar mai tsaro.
Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan;
lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi.
Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa;
Da dare iska za tă tafi da shi.
Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare;
za tă share shi daga wurinsa.
Za tă murɗe shi ba tausayi,
lokacin da yake guje wa ikon iskar.
Zai tafa hannu yă yi tsaki
yă kawar da shi daga wurinsa.”
Akwai ramin azurfa
akwai kuma wurin da ake tace zinariya.
Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe,
ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse.
Mutum ya kawo ƙarshen duhu;
yakan bincike zuzzurfar iyaka,
yana neman duwatsu a wuri mafi duhu.
Nesa da inda mutane suke zama,
yakan huda rami yă yi abin lilo,
a wurin da mutane ba sa bi.
Cikin ƙasa inda ake samun abinci,
a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta;
akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta,
akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta.
Tsuntsu mai farauta bai san hanyarta ba,
ba shahon da ya taɓa ganin ta.
Manyan namun jeji ba su taɓa binta ba,
ba zakin da ya taɓa binta.
Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu,
yă kuma tumɓuke tushen duwatsu.
Yana tona rami a cikin duwatsu
idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun.
Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa
yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske.
Amma a ina ne za a iya samun hikima?
Ina fahimta take zama?
Mutum bai gane muhimmancinta ba,
ba a samunta a ƙasar masu rai.
Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”;
teku ya ce, “Ba ta wurina.”
Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta,
ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.
Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir,
ko sauran duwatsu masu daraja ba.
Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba,
ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.
Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya;
farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.
Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba,
zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba.
“To, daga ina ke nan hikima ta fito?
Ina fahimta take zama?
An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai,
har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.
Hallaka da mutuwa suna cewa,
‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’
Allah ya gane hanyar zuwa wurinta.
Shi ne kaɗai ya san inda take zama,
Gama yana ganin iyakar duniya
kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.
Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura,
ya kuma auna ruwaye.
Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka
da kuma hanya domin walƙiya,
sai ya dubi hikima ya auna ta;
ya tabbatar da ita, ya gwada ta.
Ya kuma ce wa mutum,
‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima,
kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”
Ayuba ya ci gaba da jawabinsa,
“Da ma ina nan lokacin da ya wuce baya can,
kwanakin da Allah yake lura da ni,
lokacin da fitilarsa take haske a kaina
na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa.
Kwanakin da nake tasowa,
lokacin da abokantakar Allah ta sa wa gidana albarka,
lokacin da Maɗaukaki yana tare da ni,
kuma ’ya’yana suna kewaye da ni,
lokacin da ake zuba madara a inda nake takawa,
duwatsu kuma suna ɓulɓulo mini man zaitun.
“Sa’ad da na je ƙofar birni na zauna
a bainin jama’a,
matasan da suka gan ni sukan ja gefe
tsofaffi kuma suka tashi tsaye;
sarakuna suka yi shiru
suka rufe bakunansu da hannuwansu;
Muryar manya ta yi tsit
harshensu ya manne a rufin bakunansu.
Duk wanda ya ji ni ya yaba mini
waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni,
domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako,
da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.
Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka.
Na faranta wa gwauruwa zuciya.
Na yafa adalci ya zama suturata;
gaskiya ita ce rigata da rawanina.
Ni ne idon makafi
kuma ƙafa ga guragu.
Ni mahaifi ne ga masu bukata;
na tsaya wa baƙo.
Na karya ƙarfin mugaye
na ƙwato waɗanda suke riƙe da haƙoransu.
“Na yi tunani cewa, ‘Zan mutu a cikin gidana,
kwanakina da yawa kamar turɓayar ƙasa.
Jijiyoyina za su kai cikin ruwa,
kuma raɓa za tă kwanta a rassana dukan dare.
Ɗaukakata za tă kasance tare da ni garau,
bakana koyaushe sabo ne a hannuna.’
“Mutane suna mai da hankali su saurare ni,
suna yin shiru don su ji shawarata.
Bayan da na yi magana, ba su ƙara ce kome ba.
Maganata ta shige su.
Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama.
Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara.
Sa’ad da na yi musu murmushi da ƙyar sukan yarda;
hasken fuskata yana da daraja a gare su.
Na zaɓar masu inda za su bi na kuma zauna kamar sarkinsu;
na zauna kamar sarki a cikin rundunansu;
ina nan kamar mai yi wa masu makoki ta’aziyya.
“Amma yanzu suna yi mini ba’a
waɗanda na girme su,
waɗanda iyayensu maza ba su isa
su zama karnukan kiwon garken tumakina ba.
Ina amfani ƙarfin hannuwansu gare ni,
tun da ba su da sauran kuzari?
Duk sun rame don rashi da yunwa,
suna yawo a gaigayar ƙasa
a kufai da dare.
A cikin jeji suna tsinkar ganyaye marasa daɗi,
jijiyoyin itacen kwakwa ne abincinsu.
An kore su daga cikin mutanensu,
aka yi musu ihu kamar ɓarayi.
An sa dole su zauna a kwazazzabai da kuma
cikin kogunan duwatsu da kuma cikin ramummuka cikin ƙasa.
Suka yi ta kuka kamar dabbobi a jeji,
suka taru a ƙarƙashin sarƙaƙƙiya.
Mutane marasa hankali marasa suna,
an kore su daga ƙasar.
“Yanzu kuma ’ya’yansu maza su suke yi mini ba’a cikin waƙa
na zama abin banza a gare su.
Suna ƙyamata suna guduna;
suna tofa mini miyau a fuska.
Yanzu da Allah ya kunce bakana ya ba ni wahala
sun raba ni da mutuncina.
A hannun damana ’yan tā-da-na-zaune-tsaye sun tayar;
sun sa tarko a ƙafafuna,
sun yi shirin hallaka ni.
Sun ɓata mini hanyata;
sun yi nasara cikin hallaka ni,
ba tare da wani ya taimake su ba.
Suka nufo ni daga kowane gefe;
suka auko mini da dukan ƙarfinsu.
Tsoro ya rufe ni;
an kawar mini mutuncina kamar da iska,
dukiyata ta watse kamar girgije.
“Yanzu raina yana ƙarewa;
kwanakin wahala sun kama ni.
Dare ya huda ƙasusuwana;
ina ta shan azaba ba hutawa.
A cikin girman ikonsa Allah ya zama kamar riga a jikina;
ya shaƙe ni kamar wuyan rigata.
Ya jefa ni cikin laka,
na zama ba kome ba sai ƙura da toka.
“Na yi kuka gare ka ya Allah, amma ba ka amsa mini ba.
Na tashi tsaye, amma sai ka dube ni kawai.
Ka dube ni ba tausayi;
Ka kai mini hari da ƙarfin hannunka.
Ka ɗaga ni sama ka ɗora ni a kan iska;
ka jujjuya ni cikin hadari.
Na san za ka sauko da ni ga mutuwa
zuwa wurin da kowane mai rai zai je.
“Ba shakka ba mai ɗora hannu a kan mutumin da yake cikin wahala.
Lokacin da ya yi kukan neman taimako a cikin wahalarsa.
Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba?
Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba?
Duk da haka sa’ad da nake begen abu mai kyau,
mugun abu ne ya zo;
Sa’ad da nake neman haske, sai duhu ya zo.
Zuciyata ba tă daina ƙuna ba;
ina fuskantar kwanakin wahala.
Na yi baƙi ƙirin, amma ba rana ce ta ƙona ni ba.
Na tsaya a cikin mutane, na kuma yi kuka don taimako.
Na zama ɗan’uwan diloli,
na zama abokan mujiyoyi.
Fatar jikina ta yi baƙi tana ɓarewa;
jikina yana ƙuna da zazzaɓi.
Garayata ta zama ta makoki,
sarewata kuma ta zama ta kuka.
“Na yi alkawari da idanuna
kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.
Gama mene ne rabon mutum daga Allah a sama,
gādonsa daga Maɗaukaki a sama?
Ba masifa ba ne domin mugaye,
hallaka kuma ga waɗanda suka yi ba daidai ba?
Bai ga hanyoyina ba ne
bai ƙirga kowace takawata ba?
“In da na yi tafiya cikin rashin gaskiya
ko kuma ƙafata ta yi sauri zuwa yin ƙarya,
Bari Allah yă auna a kan ma’auni na gaskiya
zai kuma san cewa ni marar laifi ne.
In takawata ta kauce daga hanya,
in zuciyata ta bi abin da idanuna ke so,
ko kuma in hannuwana suna da laifi;
bari waɗansu su ci abin da na shuka,
kuma bari a tuge amfanin gonata.
“In sha’awar mace ya shiga mini zuciya,
ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
sai matata ta niƙa hatsin wani
kuma waɗansu maza su kwana da ita.
Gama wannan zai zama abin kunya,
zunubin da za a yi shari’a a kai.
Wuta ce take ƙuna har ta hallakar;
za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.
“In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu,
sa’ad da suke da damuwa da ni,
me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni?
Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?
Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba?
Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?
“In na hana wa matalauta abin da suke so,
ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,
in na ajiye burodina don kaina kaɗai,
ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,
amma tun suna tasowa na lura da su,
kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa.
In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura,
ko wani mai bukata da ba shi da riga,
kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba
don na yi masa sutura da gashin tumakina,
in na ɗaga hannuna don in cuci maraya,
domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,
bari hannuna yă guntule daga kafaɗata,
bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.
Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah,
kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba.
“In na dogara ga zinariya
ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’
in na yi fahariya don yawan dukiyata,
arzikin da hannuwana suka samu.
In na dubi rana cikin haskenta,
ko kuma wata yana tafiyarsa,
zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye,
hannuna kuma ya sumbace su.
Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan
don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.
“In na yi murna domin mugun abu ya faru da maƙiyina;
ko kuma domin wahala ta same shi,
ban bar bakina yă yi zunubi
ta wurin la’anta shi ba,
in mutanen gidana ba su taɓa cewa,
‘Wane ne bai ƙoshi da naman Ayuba ba?’
Ba baƙon da ya taɓa kwana a titi,
gama koyaushe ƙofata tana buɗe domin matafiya,
in na ɓoye zunubina yadda mutane31.33 Ko kuwa yadda Adamu ya yi suke yi,
ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata,
domin ina tsoron taron mutane
kuma ina tsoron wulaƙancin da dangina za su yi mini,
sai na yi shiru kuma ban fita waje ba.
(“Kash, da ina da wanda zai ji ni!
Na sa hannu ga abin da na faɗa don kāre kaina,
bari Maɗaukaki yă amsa mini; bari mai tuhumata da laifi yă yi ƙarata a rubuce.
Ba shakka sai in ɗora a kafaɗata,
zan aza a kaina kamar rawani.
Zan ba shi lissafin duk abin da na taɓa yi;
zan zo gabansa kamar ɗan sarki.)
“In ƙasata tana kuka da ni
kunyoyinta duk sun cika da hawaye,
in na kwashe amfaninta ban biya ba
ko kuma na kashe masu ita,
bari ƙaya ta fito a maimakon alkama
ciyawa kuma a maimakon sha’ir.”
Maganar Ayuba ta ƙare.
Elihu
Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne. Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba. Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi. Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka. Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata.
Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce,
“Ni ƙarami ne a shekaru,
ku kuma kun girme ni;
shi ya sa na ji tsoro
na kāsa gaya muku abin da na sani.
Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana;
ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’
Amma ruhun da yake cikin mutum,
numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.
Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba,
ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba.
“Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni;
ni ma zan gaya muku abin da na sani.
Na jira sa’ad da kuke magana,
na ji muhawwararku
lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa,
na saurare ku da kyau.
Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi;
ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.
Kada ku ce, ‘Mun sami hikima;
Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’
Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba
kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba.
“Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa;
kalmomi sun kāsa musu.
Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru,
yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa.
Ni ma zan faɗi nawa;
ni ma zan faɗi abin da na sani.
Gama ina cike da magana,
kuma ruhun da yake cikina yana iza ni;
a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba,
kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa.
Dole in yi magana in sami lafiya;
dole in buɗe baki in ba da amsa.
Ba zan nuna wa wani sonkai ba,
ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba;
gama da a ce na iya daɗin baki,
da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni.
“Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce;
ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa.
Zan yi magana;
kalmomina suna dab da fitowa daga bakina.
Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata;
bakina zai faɗi gaskiyar abin da na sani.
Ruhun Allah ne ya yi ni;
numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.
Ka amsa mini in za ka iya;
ka yi shirin fuskanta ta.
Ni kamar ka nake a gaban Allah;
ni ma daga ƙasa aka yi ni.
Kada ka ji tsorona,
ba abin da zai fi ƙarfinka.
“Amma ka faɗa na ji,
na ji daidai abin da ka faɗa,
‘ni mai tsarki ne marar zunubi;
ina da tsabta kuma ba ni da laifi.
Duk da haka Allah ya same ni da laifi;
ya ɗauke ni maƙiyinsa,
ya daure ƙafafuna da sarƙa;
yana tsaron duk inda na bi.’
“Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba,
gama Allah ya fi mutum girma.
Don me ka yi masa gunaguni
cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?
Gama Allah yana magana,
yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya
ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.
A cikin mafarki, cikin wahayi da dare,
sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane
lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,
mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu
yă razana su da gargaɗinsa,
don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba
a kuma hana su daga girman kai,
don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami,
a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.
“Ko kuma mutum yă sha horo
ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,
yadda zai ji ƙyamar abinci,
har yă ƙi son abinci mafi daɗi.
Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki
kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.
Ransa yana matsawa kusa da rami,
ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.
Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci,
ɗaya daga cikin dubu,
da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,
yă yi masa alheri yă ce,
‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami,
na samu fansa dominsa.’
Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri;
za tă zama kamar lokacin da yake matashi.
Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa,
yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna;
Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.
Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce,
‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai,
amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.
Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami,
kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’
“Allah ya yi wa mutum duk waɗannan,
sau biyu, har ma sau uku.
Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami,
don hasken rai ya haskaka a kansa.
“Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni;
ka yi shiru zan yi magana.
In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini;
yi magana, domin ina so in ’yantar da kai.
Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni;
yi shiru, zan kuma koya maka hikima.”
Sa’an nan Elihu ya ce,
“Ku ji maganata, ku masu hikima;
ku saurare ni, ku masu ilimi.
Gama kunne yana rarrabe magana
kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci.
Bari mu zaɓi abin da yake daidai,
bari mu koyi abin da yake mai kyau tare.
“Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi,
amma Allah ya hana mini hakkina.
Ko da yake ina da gaskiya,
an ɗauke ni maƙaryaci;
ko da yake ba ni da laifi,
kibiyoyinsa sun ji mini ciwo wanda ba ya warkewa.’
Wane mutum ne kamar Ayuba,
wanda yake shan ba’a kamar ruwa?
Yana abokantaka da masu aikata mugunta;
yana cuɗanya da mugaye.
Gama ya ce, ‘Ba ribar da mutum zai samu
lokacin da yake ƙoƙari yă faranta wa Allah zuciya.’
“Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa.
Ko kaɗan Allah ba ya mugunta,
Maɗaukaki ba ya kuskure.
Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi;
yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo.
Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba,
Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba.
Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya?
Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya?
In nufinsa ne
ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa,
’yan adam duka za su hallaka tare,
mutum kuma zai koma ƙasa.
“In kana da ganewa sai ka saurari wannan;
ka saurari abin da zan ce.
Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki?
Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi?
Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’
ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’
wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki
kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta,
gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.
Suna mutuwa nan take, a cikin tsakiyar dare;
an girgiza mutanen amma sun wuce;
an taɓa manya amma ba da hannun mutum ba.
“Idanunsa suna kan al’amuran mutane;
yana ganin tafiyarsu duka.
Babu wuri mai duhu, babu inuwa mai duhu,
inda masu aikata mugunta za su ɓoye.
Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane,
har da za su zo gabansa don yă shari’anta su.
Ba tare da tambaya ba yana ragargaza masu iko,
yă kuma sa waɗansu a wurinsu.
Gama yana sane da abubuwan da suke yi,
yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su.
Yana ba su horo, don muguntarsu,
inda kowa zai gan su,
domin sun juya daga binsa,
kuma ba su kula da hanyoyinsa ba.
Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa
yadda ya kai ga jin kukan masu bukata.
Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi?
In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi?
Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka,
yana hana wanda bai san Allah ba yă yi mulki,
ya hana shi sa wa mutane tarko.
“A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi,
amma ba zan sāke saɓa wa wani ba.
Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba;
in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’
Ya kamata Allah yă yi maka bisa ga abin da ka ce ne,
sa’ad da ka ƙi ka tuba?
Dole kai ka zaɓa, ba ni ba;
yanzu ka gaya mini abin da ka sani.
“Mutane masu ganewa za su ce,
masu hikima waɗanda suka ji ni za su ce mini,
‘Ayuba ya yi magana cikin rashin sani;
maganganunsa na marar hikima ne.’
Kash, da za a gwada Ayuba har ƙarshe,
domin yana ba da amsa kamar mugun mutum.
Ya ƙara tawaye a kan zunubansa;
ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu
ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.”
Sai Elihu ya ce,
“Ko kana tsammani wannan gaskiya ne?
Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’
Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita,
kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’
“Zan so in ba ka amsa
kai tare da abokanka.
Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani;
ku dubi gizagizai a samanku.
In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah?
In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa?
In kuna da adalci, me kuka ba shi,
ko kuma me ya karɓa daga hannunku?
Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai,
adalcinku kuma yakan shafi ’yan adam ne kaɗai.
“Mutane suna kuka don yawan zalunci;
suna roƙo don taimako daga hannu mai ƙarfi.
Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni,
mai ba da waƙoƙi cikin dare,
wanda ya fi koya mana fiye da dabbobin duniya
ya kuma sa muka fi tsuntsayen cikin iska hikima.’
Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako
domin girman kan mugaye.
Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi;
Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.
Ta yaya zai saurara sosai ko zai saurara
lokacin da kake cewa ba ka ganinsa,
cewa ka kawo ƙara a wurinsa
kuma dole ka jira shi.
Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsa
ko kaɗan ba ya kula da mugunta.
Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai;
yana ta yawan magana ba tare da sani ba.”
Elihu ya ci gaba,
“Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan,
zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah.
Daga nesa na sami sanina;
zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne.
Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne;
mai cikakken sani yana tare da kai.
“Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane;
shi mai girma ne cikin manufarsa.
Ba ya barin mugaye da rai
sai dai yana ba waɗanda ake tsanantawa hakkinsu.
Ba ya fasa duban masu adalci;
yana sa su tare da sarakuna
yana ɗaukaka su har abada.
Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi,
ƙunci kuma ya daure su,
yana gaya musu abin da suka yi,
cewa sun yi zunubi da girman kai.
Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su
su tuba daga muguntarsu.
In sun yi biyayya suka bauta masa,
za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata
shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya.
Amma in ba su saurara ba,
za su hallaka da takobi
kuma za su mutu ba ilimi.
“Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi;
ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa.
Suna mutuwa tun suna matasa,
cikin ƙazamar rayuwar karuwanci.
Amma yana kuɓutar da masu wahala;
yana magana da su cikin wahalarsu.
“Yana so yă rinjaye ka daga haƙoran ƙunci,
zuwa wuri mai sauƙi inda ba matsi
zuwa teburinka cike da abincin da kake so.
Amma yanzu an cika ka da hukuncin da ya kamata a yi wa mugaye;
shari’a da kuma gaskiya sun kama ka.
Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki;
kada ka bar toshiya ta sa ka juya.
Dukiyarka
ko dukan yawan ƙoƙarinka
sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci?
Kada ka yi marmari dare yă yi,
don a fitar da mutane daga gidajensu.
Ka kula kada ka juya ga mugunta,
abin da ka fi so fiye da wahala.
“An ɗaukaka Allah cikin ikonsa.
Wane ne malami kamar sa?
Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi,
ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’
Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa,
waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa.
Dukan ’yan adam sun gani;
mutane sun hanga daga nesa.
Allah mai girma ne,
ya wuce ganewarmu!
Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
“Yana sa ruwa yă zama tururi
yă zubo daga sama.
Gizagizai suna zubo da raɓarsu
kuma ruwan sama yana zubowa ’yan adam a wadace.
Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai
yadda yake tsawa daga wurin zamansa?
Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi,
tana haskaka zurfin teku.
Haka yake mulkin al’ummai
yana kuma tanada abinci a wadace.
Yana cika hannuwansa da walƙiya
kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi.
Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa;
ko shanu sun san da zuwansa.
“Wannan ya sa gabana ya fāɗi,
zuciyata ta yi tsalle.
Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa,
tsawar da take fita daga bakinsa.
Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai
ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya.
Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo;
Ya tsawata da muryarsa mai girma.
Sa’ad da ya sāke yin tsawa
ba ya rage wani abu.
Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi;
yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.
Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’
ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’
Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa,
ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.
Dabbobi sun ɓoye;
sun zauna cikin kogunansu.
Guguwa tana fitowa daga inda take,
sanyi kuma daga iska mai sanyi.
Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara
sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.
Yana cika gizagizai da lema;
yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.
Bisa ga bishewarsa suke juyawa
a kan fuskar duniya,
suna yin dukan abin da ya
umarce su su yi.
Yana aiko da ruwa domin horon mutane,
ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.
“Ka saurari wannan Ayuba;
ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.
Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai
ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka?
Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama,
waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani.
Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da
iska mai sanyi take hurawa,
ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi
da ƙarfi kamar madubi?
“Gaya mana abin da ya kamata mu ce masa;
ba za mu iya kawo ƙara ba domin duhunmu.
Ko za a gaya masa cewa ina so in yi magana?
Ko wani zai nemi a haɗiye shi?
Yanzu ba wanda zai iya kallon rana,
yadda take da haske a sararin sama
bayan iska ta share ta.
Yana fitowa daga arewa da haske na zinariya,
Allah yana zuwa da ɗaukaka mai ban al’ajabi.
Maɗaukaki ya fi ƙarfin ganewarmu,
shi babban mai iko ne, mai gaskiya da babban adalci,
ba ya cutar mutum.
Saboda haka, mutane suke girmama shi,
ko bai kula da waɗanda suke gani su masu hikima ba ne?”
Ubangiji ya yi magana
Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,
“Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata
da surutan wofi?
Ka sha ɗamara kamar namiji;
zan yi maka tambaya,
za ka kuwa amsa mini.
“Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya?
Gaya mini, in ka sani.
Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani!
Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?
A kan me aka kafa tushenta,
ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,
yayinda taurarin safe suke waƙa tare
dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.
“Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi,
lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.
Lokacin da na yi wa gizagizai riga
na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,
sa’ad da na yi masa iyaka na
sa masa ƙofofi da wurin kullewa.
Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai,
ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?
“Ko ka taɓa ba safiya umarni
ko kuma ka sa asuba ta fito,
don ta kama gefen duniya
ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?
Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi;
ta fito a fili kamar riga.
An hana mugaye haskensu,
hannun da suka ɗaga an karya shi.
“Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku,
ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku?
Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa?
Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa?
Ko ka gane fāɗin duniya?
Gaya mini, in ka san wannan duka.
“Ina ne hanyar zuwa gidan haske?
Kuma a ina duhu yake zama?
Ko za ka iya kai su wurarensu?
Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama?
Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin!
Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa.
“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara
ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara
waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala,
domin kwanakin yaƙi da faɗa?
Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya,
ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?
Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa,
da kuma hanyar walƙiyar tsawa
don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin
jeji inda ba mai zama ciki
don a ƙosar da wurin da ya bushe
a sa ciyawa ta tsiro a can?
Ruwan sama yana da mahaifi?
Wa ya zama mahaifin raɓa?
Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara?
Wane ne ya haifi jaura daga sammai
lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse,
lokacin da saman ruwa ya daskare?
“Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta?
Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?
Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu
ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?
Ka san dokokin sammai?
Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?
“Za ka iya tsawata wa gizagizai
ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa?
Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa?
Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’
Wane ne yake cika zuciya da hikima
ko kuma yake ba zuciya ganewa?
Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai?
Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai
sa’ad da ƙura ta yi yawa
ta daskare a wuri ɗaya?
“Za ka iya farauto wa zakanya nama,
ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu.
Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu,
ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu?
Wane ne yake ba hankaka abinci
lokacin da ’ya’yansa suke kuka ga Allah,
kuma suna yawo don rashin abinci?
“Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa?
Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?
Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu?
Ka san lokacin da suke haihuwa?
Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu;
naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu.
’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji;
sukan tafi ba su dawowa.
“Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi?
Wane ne yake kunce igiyoyinsu?
Na sa jeji yă zama gidansa
ƙasar gishiri kuma ta zama wurin zamansa.
Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari;
ba ya jin tsawar mai tuƙa shi.
Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa
yana neman kowane ɗanyen abu mai ruwan ciyawa.
“Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci?
Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare?
Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya?
Zai yi maka buɗar gonarka?
Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa?
Za ka bar masa nauyin aikinka?
Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida
yă tattara shi a masussuka?
“Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki
amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.
Tana sa ƙwai nata a ƙasa
kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,
ba tă damu ko za a taka su a fasa su,
ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.
Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba
ba tă damu da wahalar da ta sha ba.
Gama Allah bai ba ta hikima ba
ko kuma iya fahimta.
Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu
tana yi wa doki da mai hawansa dariya.
“Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa
kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa?
Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra,
ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa.
Yana takawa da ƙarfi
yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi.
Yana yi wa tsoro dariya
ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.
Kwari a baka yana lilo a gabansa
kibiya da māshi suna wuce kansa.
Yana kartar ƙasa da ƙarfi;
ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho.
Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’
Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa,
da ihun shugabannin yaƙi.
“Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya
take kuma baza fikafikanta zuwa kudu?
Ko da umarninka ne shaho yake firiya
ya kuma yi sheƙarsa a can sama?
Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare;
cikin duwatsu ne wurin zamansa.
Daga can yake neman abincinsa;
idanunsa suna gani daga nesa.
’Ya’yansa suna shan jini,
inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.”
Ubangiji ya ce wa Ayuba,
“Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki?
Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.”
Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
“Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka?
Na rufe bakina da hannuna.
Na yi magana sau ɗaya amma ba ni da amsa,
sau biyu, amma ba zan ƙara cewa kome ba.”
Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa,
“Ka tashi tsaye ka tsaya da ƙarfi kamar namiji;
zan yi maka tambaya
kuma za ka amsa mini.
“Ko za ka ƙi yarda da shari’ata?
Za ka ba ni laifi don ka nuna kai marar laifi ne?
Ko hannunka irin na Allah ne,
kuma ko muryarka za tă iya tsawa kamar ta Allah?
Sai ka yi wa kanka ado da ɗaukaka da girma,
ka yafa daraja da muƙami.
Ka saki fushinka,
ka dubi dukan wani mai girman kai ka wulaƙanta shi.
Ka dubi duk wani mai girman kai ka ƙasƙantar da shi,
ka tattake mugaye a inda ka tsaya.
Ka bizne su duka tare
ka rufe fuskokinsu a cikin kabari.
Sa’an nan ni kaina zan shaida maka cewa
hannun damanka zai iya cetonka.
“Dubi dorina,
wadda na halicce ku tare
kuma ciyawa take ci kamar sa.
Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta
ikonta yana cikin tsokar cikinta.
Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul;
jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya.
Ƙasusuwanta bututun tagulla ne,
haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe.
Tana ta farko cikin ayyukan Allah,
Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi.
Tuddai su suke tanada mata abinci
a inda duk namun jeji suke wasa.
Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus
ta ɓuya cikin kyauro da fadama.
Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji,
itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba;
ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa.
Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo,
ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta?
“Ko za ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kamar kifi
ko kuma ka daure harshenta da igiya?
Za ka iya sa igiya a cikin hancinta
ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya?
Za tă ci gaba da roƙonka ka yi mata jinƙai?
Ko za tă yi maka magana a hankali?
Za tă yi yarjejjeniya da kai
don ka ɗauke ta tă zama baiwa gare ka dukan kwanakin ranta?
Za ka yi wasa da ita kamar yadda za ka yi da tsuntsu?
Ko za ka daure ta da tsirkiya domin bayinka mata?
’Yan kasuwa za su saye ta
ko za su raba ta a tsakaninsu?
Ko za ka iya huda fatarta da kibiya
ka kuma huda kansa da māsu?
In ka ɗora hannunka sau ɗaya a kanta
za ka tuna da yaƙin da ba za ka sāke yi ba!
Duk ƙoƙarin kama ta banza ne;
ganin ta kawai abin tsoro ne.
Ba wanda ya isa yă tsokane ta.
Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni?
Wane ne yake bi na bashi da dole in biya?
Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne.
“Ba zan daina magana game da gaɓoɓinta ba
ƙarfinta da kuma kyan kamanninta ba.
Wa zai iya tuɓe mata mayafinta?
Wa zai iya shiga tsakanin ɓawonta.
Wa zai iya buɗe ƙofofin bakinta?
Haƙoranta ma abin tsoro ne?
An rufe bayanta da jerin garkuwoyi
aka manne su sosai.
Suna kurkusa da juna yadda
da ƙyar iska take iya wucewa tsakani.
An haɗa su da juna
sun mannu da juna kuma ba za a iya raba su ba.
Numfashinta yana fitar da wuta;
idanunta kamar hasken zuwan safe.
Wuta tana fitowa daga bakinta;
tartsatsin wuta suna fitowa,
Hayaƙi yana fitowa daga hancinta
kamar daga tukunya mai tafasa a kan wutar itace.
Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta,
harshen wuta yana fita daga bakinta.
Akwai ƙarfi a cikin wuyanta;
razana tana wucewa a gabanta.
Namanta yana da kauri a manne da juna;
naman yana da tauri ba ya matsawa.
Ƙirjinta yana da ƙarfi kamar dutse,
da ƙarfi kamar dutsen niƙa.
Sa’ad da ta tashi, manya suna tsorata;
suna ja da baya.
Takobi ba ta iya yankanta,
kibiya ko māshi ba sa iya huda ta.
Ƙarfe kamar kara ne a wurinta
tagulla kuma kamar ruɓaɓɓen katako ne a wurinta.
Māsu ba su sa ta tă gudu;
jifar majajjawa kamar na ciyawa ne gare ta.
Kulki a gare ta kamar ciyawa ne,
tana dariyar wucewar māshi.
Cikinta yana rufe a ɓawo masu ƙarfi,
tana kabtar ƙasa in tana tafiya.
Tana sa zurfin kogi yă tafasa kamar tukunya,
ta kuma sa teku yă zama kamar tukunyar man shafawa.
A bayanta ya bar haske
kamar zurfin ruwan da yana kumfa.
Ba wani abu kamar ta a duniya,
halitta marar tsoro.
Tana rena duk masu girman kai.
Ita take mulki kan duk masu girman kai.”
Ayuba
Sa’an nan Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
“Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa;
ba wanda zai iya ɓata shirinka.
Ka yi tambaya, ‘Wane ne wannan da ya ƙi karɓar shawarata shi marar ilimi?’
Ba shakka na yi magana game da abubuwan da ban gane ba,
abubuwan ban al’ajabi da sun fi ƙarfin ganewata.
“Ka ce, ‘Saurara yanzu, zan kuma yi magana
zan tambaye ka,
kuma za ka amsa mini.’
Kunnuwana sun ji game da kai
amma yanzu na gan ka.
Saboda haka na rena kaina
na kuma tuba cikin ƙura da toka.”
Ƙarshen magana
Bayan Ubangiji ya gaya wa Ayuba waɗannan abubuwa, ya ce wa Elifaz mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokanka guda biyu domin ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi. Saboda haka yanzu sai ku ɗauki bijimai guda bakwai, da raguna bakwai, ku je wurin bawana Ayuba ku miƙa hadaya ta ƙonawa domin kanku. Bawana Ayuba zai yi muku addu’a zan kuwa karɓi addu’arsa in bi da ku nisa da wawancinku. Ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba yadda bawana Ayuba ya yi ba.” Saboda haka Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa da Zofar mutumin Na’ama, suka yi abin da Ubangiji ya gaya masu; Ubangiji kuma ya karɓi addu’ar Ayuba.
Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu. Dukan ’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya.
Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu. Ya kuma haifi ’ya’ya maza bakwai, mata uku. ’Yar farko ya kira ta Yemima, ta biyun Keziya ta ukun Keren-Haffuk. Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza.
Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu. Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.