- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Irmiya Irmiya Irmiya Irm Irmiya Kalmomin Irmiya ɗan Hilkiya, ɗaya daga cikin firistoci a Anatot a yankin Benyamin. Maganar Ubangiji ta zo gare shi a shekara ta goma sha uku ta sarautar Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda, da kuma a zamanin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, har zuwa watan biyar na shekara goma sha ɗaya na Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, sa’ad da aka kai mutanen Urushalima zaman bauta. Kiran Irmiya Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san1.5 Ko kuwa zaɓe ka, kafin a haife ka, na keɓe ka; na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.” Sai na ce, “Kayya, Ubangiji Mai Iko Duka, ban iya magana ba; ni ɗan yaro ne kawai.” Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka,” in ji Ubangiji. Sai Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina ya ce mini, “Yanzu na sa kalmomina a bakinka. Duba, yau na naɗa ka a kan al’ummai da mulkoki don ka tumɓuke ka kuma rusar, ka hallaka ka kuma kakkaɓe, ka gina ka kuma shuka.” Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Me ka gani, Irmiya?” Sai na amsa na ce, “Na ga reshen itacen almon.” Ubangiji ya ce mini, “Daidai ne ka gani, gama ina lura in ga cewa maganata ta cika.” Maganar Ubangiji ta sāke zo mini cewa, “Me ka gani?” Na amsa na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, tana juyewa daga arewa.” Ubangiji ya ce mini, “Daga arewa za a zubo masifa a kan dukan mazaunan ƙasar. Ina shirin kiran dukan mutanen masarautar arewanci,” in ji Ubangiji. “Sarakunansu za su zo su kafa kursiyoyinsu a mashigin ƙofofin Urushalima; za su zo su kewaye dukan katangarta su kewaye dukan garuruwan Yahuda. Zan furta hukunci a kan mutanena saboda muguntarsu na yashe ni, suna ƙona turare ga waɗansu alloli suna kuma bauta wa abin da hannuwansu suka yi. “Ka kintsa kanka! Ka tashi tsaye ka faɗa musu abin da na umarce ka. Kada su firgita ka, in ba haka ba zan firgita ka a gabansu. Yau na mai da kai birni mai katanga, ginshiƙin ƙarfe da bangon tagulla don ka tsaya gāba da dukan ƙasar, ya kuma yi gāba da sarakunan Yahuda da fadawan, da firistoci da kuma mutanenta. Za su yi yaƙi da kai amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, zan kuma kiyaye ka,” in ji Ubangiji. Isra’ila ya yashe Allah Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Tafi ka yi shela a kunnuwar Urushalima cewa, “ ‘Na tuna da amincin ƙuruciyarki, yadda kamar amarya kika ƙaunace ni kika kuma bi ni cikin hamada, cikin ƙasar da ba a yi shuka ba. Isra’ila tsattsarka ce ga Ubangiji, nunan fari na girbinsa; dukan waɗanda suka cinye ta an same su da laifi, masifa kuwa ta same su,’ ” in ji Ubangiji. Ka saurari maganar Ubangiji, ya gidan Yaƙub, dukanku zuriyar gidan Isra’ila. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Wane laifi ne kakanninku sun same ni da shi, da suka tsaya nesa da ni? Sun bi gumakan banza su kansu suka kuma zama banza da kansu. Ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji, wanda ya fitar da su daga Masar ya bishe su cikin jeji cikin hamada da kwazazzabai ƙasa mai fări da kuma duhu, ƙasar da ba kowa mai ratsa ta ba kowa kuma mai zama a cikinta?’ Na kawo ku zuwa ƙasa mai albarka don ku ci amfaninta da abubuwa masu yalwar da take bayarwa. Amma kuka zo kuka ƙazantar da ƙasata kuka kuma mai da gādona abin ƙyama. Firistoci ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji ba.’ Waɗanda suke amfani da doka ba su san ni ba; shugabanni suka yi mini tawaye. Annabawa suka yi annabci ta wurin Ba’al, suna bin gumakan banza. “Saboda haka ina sāke tuhumarku,” in ji Ubangiji. “Zan kuma tuhumi ’ya’ya ’ya’yanku. Ku ƙetare zuwa tsibiran Kittim2.10 Wato, Saifurus da tsibiran wajen yamma ku gani, ku aika zuwa Kedar ku duba da kyau; ku ga ko an taɓa yin wani abu haka. Akwai wata al’ummar da ta canja allolinta? (Duk da haka su ba alloli ba ne sam.) Amma mutanena sun musayar da ɗaukakarsu da gumakan banza. Ku girgiza saboda wannan, ya sammai, ku kuma razana don tsoro mai girma,” in ji Ubangiji. “Mutanena sun aikata zunubai guda biyu. Sun rabu da ni, ni da nake maɓulɓular ruwan rai, sun kuma haƙa tankunan ruwansu, tankuna ruwan da suka fashe da ba za su iya riƙe ruwa ba. Isra’ila bawa ne, bawa ne ta wurin haihuwa? Me ya sa ya zama ganima? Zakoki sun yi ruri; sun yi masa ruri. Sun lalatar da ƙasarsa; an ƙone garuruwansa aka kuma watse daga ciki. Haka ma, mutanen Memfis2.16 Da Ibraniyanci Nof da Tafanes sun aske rawanin kanka2.16 Ko kuwa fasa ƙoƙon kansa Ba kai ne ba ka jawo wa kanka ba ta wurin rabuwa da Ubangiji Allahnka sa’ad da ya bi da kai a hanya? To, me ya sa za ka Masar don shan ruwa daga Shihor?2.18 Wato, reshen Nilu Kuma me ya sa za ka Assuriya don shan ruwa daga Kogi?2.18 Wato, Yuferites Muguntarka za tă hukunta ka; jan bayanka zai tsawata maka. Sai ka lura ka kuma gane yaya mugu da kuma ɗaci suke a gare ka sa’ad da ka rabu da Ubangiji Allahnka kuma ba ka tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Tun da daɗewa ka karya karkiyarka ka kuma tsintsinke sarƙoƙinka; sai ka ce, ‘Ba zan bauta maka ba!’ Tabbatacce, a kan kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane ɗanyen itace ka kwanta kamar karuwa. Na shuka ka kamar zaɓaɓɓen inabi iri mai kyau da kuma wanda za a dogara a kai. Yaya kuma ka juya kana gāba da ni ka lalace, ka zama inabin jeji? Ko da yake ka wanke kanka da sabulu ka yi amfani da sabulu mai yawa, duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. “Yaya za ka ce, ‘Ban ƙazantu ba; ban bi Ba’al ba’? Duba yadda ka yi a cikin kwari; ka ga abin da ka yi. Kai kamar makwaɗaciyar raƙuma ce mai zafin gudu kana gudu nan da can, kamar jakar jejin da ta saba da hamada, mai busar iska cikin son barbaranta sa’ad da take son barbara wa zai iya hana ta? Jakin da yake nemanta, ba ya bukatar wahalar da kansa; a lokacin barbara za a same ta. Kada ka yi gudu har ƙafafunka su zama ba takalma maƙogwaronka kuma ya bushe. Amma sai ka ce, ‘Ba amfani! Ina ƙaunar baƙin alloli kuma dole in bi su.’ “Kamar yadda akan kunyatar da ɓarawo sa’ad da aka kama shi, haka gidan Isra’ila zai sha kunya, su, sarakunansu da shugabanninsu, firistocinsu da kuma annabawansu. Kuna ce wa itace, ‘Kai ne mahaifina,’ ga dutse kuma, ‘Kai ne ka haife ni.’ Sun juye mini bayansu ba fuskokinsu ba; duk da haka sa’ad da suna cikin wahala, sukan ce, ‘Zo ka cece mu!’ To ina allolin da kuka yi wa kanku? Bari su zo in suna iya cetonku sa’ad da kuke cikin wahala! Gama kuna da alloli masu yawa kamar yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda. “Me ya sa kuke tuhumana? Dukanku kun yi mini tawaye,” in ji Ubangiji. “A banza na hukunta mutanenku; ba su yi gyara ba. Takobinku ya cinye annabawanku kamar zaki mai jin yunwa. “Ku na wannan zamani, ku saurari maganar Ubangiji. “Na zama wa Isra’ila hamada ne ko ƙasa mai babban duhu? Me ya sa mutanena suke cewa, ‘Muna da ’yanci mu yi ta yawo; ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’? Budurwa za tă manta da kayan adonta amarya ta manta da kayan adon aurenta? Duk da haka mutanena sun manta da ni, kwanaki ba iyaka. Kuna da azanci sosai a bin masoya! Kai, ko mafiya muni cikin mata tana iya koya daga hanyoyinku. A rigunanku mutane kan sami jinin matalauta marasa laifi, ko da yake ba ku kama su suna fasawa su shiga ba. Duk da haka kuna cewa, ‘Ba ni da laifi; ba ya fushi da ni.’ Amma zan zartar da hukunci a kanku domin kun ce, ‘Ban yi zunubi ba.’ Don me kuke yawo da yawa haka, kuna ta canjin hanyoyinku? Masar za tă kunyata ku yadda kuka sha kunya a wurin Assuriya. Za ku kuma bar wurin da hannuwanku a kanku, gama Ubangiji ya ƙi waɗanda kuka amince da su; ba za ku zama abin taimako a gare su ba. “In mutum ya saki matarsa ta kuwa bar shi ta auri wani mutum, zai iya komo da ita kuma? Ƙasar ba za tă ƙazantu gaba ɗaya ba? Amma kun yi rayuwa kamar karuwa da masoya masu yawa yanzu za ki komo wurina?” In ji Ubangiji. “Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani. Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba? A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki, kin zauna kamar makiyayi3.2 Ko kuwa mutumin Arab a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da karuwancinki da muguntarki. Saboda haka an hana yayyafi, kuma babu ruwan bazara da ya sauka. Duk da haka kina da irin kallon da karuwa takan yi; kin ƙi ki ji kunya. Yanzu ba kin kira ni, ‘Mahaifina, abokina daga ƙuruciyata ba, kullum za ka riƙa fushi? Hasalarka za tă ci gaba har abada ne?’ Haka kike magana, amma kina aikata dukan muguntar da kika iya yi.” Isra’ila marar aminci A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can. Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba, ’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani. Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina. Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace. Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci. Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa, “ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba, gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji, ‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba. Ki dai yarda da laifinki kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye, kin watsar da alheranki ga baƙin alloli a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ ” in ji Ubangiji. “Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi. A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba. A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo. “Ni kaina na faɗa, “ ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza in ba ki ƙasa mai daɗi, gādo mafi kyau da wata al’umma.’ Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’ ba za ki ƙara rabuwa da bina ba. Amma kamar mace marar aminci ga mijinta, haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji. An ji kuka a filayen tuddai, kuka da roƙon mutanen Isra’ila, domin sun lalace hanyoyinsu sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu. “Ku komo, mutane marasa bangaskiya; zan warkar da ku daga ja da bayanku.” “I, za mu zo wurinka, gama kai ne Ubangiji Allahnmu. Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai da duwatsu banza ne; tabbatacce a wurin Ubangiji Allahnmu ne akwai ceton Isra’ila. Daga ƙuruciyarmu allolin kunya sun cinye mu amfanin wahalar kakanninmu garkunan tumakinsu da na awakinsu, yaransu maza da mata. Bari mu kwanta mu sha kunya, bari kuma kunyarmu ta rufe mu. Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi, da mu da kakanninmu; daga ƙuruciyarmu har yă zuwa yau ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba.” “In za ka komo, ya Isra’ila, ka komo gare ni,” in ji Ubangiji. “In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabana ba ka ƙara karkace ba, kuma in cikin gaskiya da adalci ka rantse, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ to al’ummai za su sami albarka ta wurinsa kuma a cikinsa za su ɗaukaka.” Ga abin da Ubangiji yana ce wa mutanen Yahuda da kuma na Urushalima. “Ku nome ƙasarku kuma kada ku yi shuka cikin ƙayayyuwa. Ku yi wa kanku kaciya ga Ubangiji ku yi wa zukatanku kaciya, ku mutanen Yahuda da mutanen Urushalima, in ba haka ba hasalata za tă sauko ta ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci ba wanda zai kashe ta. Masifa daga Arewa “Ku yi shela a Yahuda ku kuma furta a Urushalima ku ce, ‘Ku busa ƙaho a ko’ina a ƙasar!’ Ku tā da murya da ƙarfi ku ce, ‘Ku tattaru! Bari mu gudu zuwa birane masu katanga!’ Ku tā da tuta don zuwa Sihiyona! Ku gudu ku nemi mafaka ba tare da jinkiri ba! Gama ina kawowa masifa daga arewa, mummunan hallaka kuwa.” Zaki ya fito daga ruƙuƙinsa; mai hallakarwar al’ummai ya kama hanya. Ya bar wurinsa don yă lalace ƙasarku. Garuruwanku za su zama kufai babu mazauna. Saboda haka ku yafa tufafin makoki, ku yi makoki da kuka, gama fushin Ubangiji bai juye daga gare mu ba. “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “sarki da shugabanni za su fid da zuciya, firistoci za su razana, annabawa kuma za su yi mamaki.” Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka, yaya ka ruɗi mutanen nan da kuma Urushalima gaba ɗaya haka ta wurin cewa, ‘Za ku zauna lafiya,’ sa’ad da takobi yana a maƙogwaronmu.” A lokacin za a faɗa wa mutanen nan da kuma Urushalima cewa, “Iska mai zafi daga tuddan hamada za tă hura zuwa wajen mutanena, amma ba don ta sheƙe ko ta rairaye; ba; iska mafificin ƙarfi da ta fito daga gare ni.4.12 Ko kuwa ta zo ta wurin umarnina Yanzu na zartar da hukuncina a kansu.” Duba! Yana zuwa kamar gizagizai, kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa, dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaiton mu! Mun shiga uku! Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki ki sami ceto. Har yaushe za ki zauna riƙe da mugayen tunani? Murya ta shela daga Dan, tana furtawa masifa daga tuddan Efraim. “A faɗa wa al’ummai wannan, a furta wannan game Urushalima. ‘Sojoji masu ƙawanya suna zuwa daga ƙasa mai nisa, suna tā da kirarin yaƙi a kan biranen Yahuda. Sun kewaye ta kamar masu gadin fili, domin ta yi mini tawaye,’ ” in ji Ubangiji. “Halinki da ayyukanki sun kawo wannan a kanki. Hukuncinki ke nan. Yana da ɗaci! Ya soke ki har zuciyarki!” Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi. Masifa kan masifa; dukan ƙasar ta zama kufai. Cikin ɗan lokaci aka rurrushe tentuna nawa, mafakata ba zato. Har yaushe zan dubi tutar yaƙi in kuma ji karar ƙaho? “Mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Su ’ya’ya ne marasa azanci; ba su da fahimi. Suna da dabarar aikata mugunta; ba su san yadda za su aikata alheri ba.” Na dubi duniya, na ga cewa marar siffa ce babu kome; sammai kuma, haskensu ya tafi. Na dubi duwatsu, sai na ga suna makyarkyata; dukan tuddai kuwa suna lilo. Na duba, sai na ga ba kowa; kowane tsuntsu a sarari da ya tsere. Na duba, sai na ga ƙasa mai amfani ta zama hamada; dukan garuruwanta sun zama kufai a gaban Ubangiji, a gaban zafin fushinsa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dukan ƙasar za tă zama kufai, ko da yake ba zan hallaka ta gaba ɗaya ba. Saboda haka duniya za tă yi kuka sammai a bisa kuma za su yi duhu, domin na yi magana kuma ba zan fasa ba, na yanke shawara ba kuwa zan janye ba.” Da jin motsin mahayan dawakai da maharba kowane gari ya ruga da gudu. Waɗansu suka shiga kurmi; waɗansu suka hau cikin duwatsu. Dukan garuruwan sun fashe tas; babu wani da yake zama a ciki. Me kike yi, ya wadda aka ragargaza? Me ya sa kika sanya mulufi kika sa kayan adon zinariya? Me ya sa kika sa wa idanunki tozali? Kin yi kwalliyarki a banza. Masoyanki sun bar ki; suna neman ranki. Na ji kuka kamar na mace mai naƙuda, nishi kamar na wadda take haihuwa ɗanta na fari, kukan Diyar Sihiyona tana haki, da ƙyar take numfashi, tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina! Na suma; an ba da raina ga masu kisana.” Ba ko ɗaya da yake da adalci “Ku yi ta kai da kawowa a titunan Urushalima, ku dudduba ko’ina ku kuma lura, ku bincika cikin dandalinta. Ko za ku sami mutum guda wanda yake aikata adalci wanda yake kuma son bin gaskiya, sai in gafarta wa wannan birni. Ko da yake suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ duk da haka suna rantsuwar ƙarya.” Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya? Ka buge su, amma ba su ji zafi ba; ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara. Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse suka ƙi su tuba. Na yi tunani, “Waɗannan ne kawai matalauta; su wawaye ne, gama ba su san hanyar Ubangiji ba, ko abubuwan da Allahnsu yake bukata ba. Saboda haka zan tafi wurin shugabanni in yi musu magana; tabbatacce sun san hanyar Ubangiji, da abubuwan da Allahnsu yake bukata.” Amma da nufi guda su ma suka karye karkiyar suka tsintsinke sarƙoƙin. Saboda haka zaki daga kurmi zai fāɗa musu, kyarkeci kuma daga hamada zai cinye su, damisa za tă yi musu ƙawanya kusa da garuruwansu yă yayyage duk wanda ya kuskura ya fita, gama tawayensu da girma yake jan bayansu kuma yana da yawa. “Me zai sa in gafarta muku? ’Ya’yanku sun yashe ni sun yi rantsuwa da allolin da ba alloli ba ne. Na biya musu dukan bukatunsu, duk da haka suka yi zina suka tattaru a gidajen karuwai. An ciyar da su sosai, kamar ƙosassun ingarmu, masu jaraba, kowanne yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa. Ba zan hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’ummar nan ba? “Ku ratsa cikin gonakin inabinta ku cinye su, amma kada ku hallaka su gaba ɗaya. Ku kakkaɓe rassanta, gama waɗannan mutane ba na Ubangiji ba ne. Gidan Isra’ila da gidan Yahuda sun zama marasa aminci gaba ɗaya gare ni” in ji Ubangiji. Sun yi ƙarya a kan Ubangiji; sun ce, “Ba zai yi kome ba! Ba wata masifar da za tă same mu; ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba. Annabawa holoƙo ne kawai maganar kuwa ba ta cikinsu; saboda haka bari abin da suke faɗi ya koma kansu.” Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Domin mutanen sun yi waɗannan maganganu, zan mai da maganata a bakinku wuta waɗannan mutane kuwa su zama itacen da za tă ci. Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba. Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne; dukansu jarumawa ne. Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku, za su cinye ’ya’yanku maza da mata; za su cinye garkunan tumakinku da na awakinku, za su cinye ’ya’yan inabinku da na ɓaurenku. Da takobi za su hallaka biranenku masu katanga. “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki,” in ji Ubangiji, “ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Sa’ad da kuma mutanen suka yi tambaya, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi dukan wannan gare mu?’ Sai ka amsa musu, ‘Yadda kuka yashe ni kuka kuma bauta wa baƙin alloli a ƙasarku, haka yanzu za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ “Ka sanar da wannan ga gidan Yaƙub ka yi shelarsa a Yahuda. Ku ji wannan, ku wawaye marasa azanci, waɗanda suke da idanu amma ba sa gani, waɗanda suke da kunnuwa amma ba sa ji. Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba? Na sa yashi ya zama iyakar teku, madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba. Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba; za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba. Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma ’yan tawaye ne; sun kauce suka kuma rabu da ni. Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu, wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara, wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’ Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa; zunubanku sun hana ku samun alheri. “A cikin mutanena an sami mugaye waɗanda suke kwanton ɓauna kamar masu sa tarko wa tsuntsaye kamar waɗanda suke kafa tarko don su kama mutane. Kamar keji cike da tsuntsaye, gidajensu sun cika da ruɗu; sun yi arziki suka kuma zama masu iko suka kuma yi ƙiba, suka yi bul-bul. Mugayen ayyukansu ba su da iyaka; ba sa wa marayu shari’ar adalci, ba sa kāre ’yancin matalauta. Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’umma kamar wannan ba? “Abin banmamaki da bantsoro ya faru a ƙasar. Annabawa suna annabcin ƙarya, firistoci suna mulki da ikon kansu, mutanena kuma suna son haka. Amma me za ku yi a ƙarshe? Abokan gāba sun kewaye Urushalima “Ku gudu neman mafaka, mutanen Benyamin! Ku gudu daga Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa! Ku ba da alama a Bet-Hakkerem! Gama masifa tana zuwa daga arewa, mummunar hallaka ce kuwa. Zan hallaka Diyar Sihiyona, kyakkyawa da kuma mai laulayi. Makiyaya da garkunansu za su taso mata; za su kafa tentunansu kewaye da ita, kowanne yana lura da sashensa.” “Mu shirya don yaƙi da ita! Ku tashi, bari mu fāɗa mata da tsakar rana! Amma, kaito, rana tana fāɗuwa, inuwar yamma kuwa sai ƙaran tsawo take. Saboda haka ku tashi, bari mu fāɗa mata da dare mu rurrushe kagaranta!” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku sassare itatuwan ku tula ƙasa kewaye da Urushalima. Dole a hukunta wannan birni; saboda ya cika da zalunci. Kamar yadda rijiya takan ba da ruwarta, haka birnin yake da muguntarsa. Ana jin labarin rikici da hallaka a cikinsa; ciwonsa da mikinsa kullum suna a gabana. Ki ji gargaɗi, ya Urushalima, ko kuwa in juya daga gare ki in mai da ƙasarki kufai don kada wani ya zauna a cikinta.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Bari su yi kalan raguwar Isra’ila a yi kalan sarai yadda ake yi wa inabi; ka sāke miƙa hannunka a kan rassan, kamar mai tattara inabi.” Ga wa zan yi magana in kuma gargaɗar? Wa zai saurare ni? Kunnuwansu sun toshe6.10 Da Ibraniyanci marar kaciya don kada su ji. Maganar Ubangiji ta zama abin zargi a gare su; ba sa jin daɗinta. Amma ina cike da fushin Ubangiji, kuma ba na iya kannewa. “Ka kwararo shi a kan yara a titi da kuma a kan samarin da suka tattaru; za a kama miji da mata a cikinsa, tsofaffi da suka tsufa tukub. Za a ba da gidajensu ga waɗansu, tare da gonakinsu da matansu, sa’ad da na miƙa hannuna gāba da waɗanda suke zama a ƙasar,” in ji Ubangiji. “Daga ƙarami zuwa babba, dukansu masu haɗama ne don riba; har da annabawa da firistoci, dukansu suna aikata rashin gaskiya. Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali kuwa ba lafiya. Suna jin kunyar halinsu na banƙyama? A’a, ba sa jin kunya sam; ba su ma san yadda za su soke kai ba. Saboda haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za a hamɓarar da su sa’ad da na hukunta su,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba; ku nemi hanyoyin dā, ku tambaya inda hanyar mai kyau take, ku yi tafiya a kanta, za ku kuwa sami hutu wa rayukanku. Amma kun ce, ‘Ba za mu bi ta ba.’ Na naɗa muku masu tsaro a kanku na kuma ce, ‘Ku saurari karan ƙaho!’ Amma kuka ce, ‘Ba za mu saurara ba.’ Saboda haka ku, ya al’ummai; ku lura Ya shaidu, abin da zai faru da su. Ki ji, ya duniya. Zan kawo masifa a kan waɗannan mutane, sakayyar ƙulle-ƙullensu, domin ba su saurari maganata ba suka kuma ƙi dokata. Babu riba a kawo mini turare daga Sheba ko rake mai zaƙi daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba; ba na jin daɗin sadakokinku.” Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Zan sa abin tuntuɓe gaban mutanena. Mahaifi da ’ya’yansa maza za su yi tuntuɓe a kan juna; maƙwabci da abokansa za su hallaka.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Duba, sojoji suna zuwa daga ƙasar arewa; babbar al’umma ce ta yunƙuro daga iyakokin duniya. Suna riƙe da baka da māshi; mugaye ne kuma marasa tausayi. Motsinsu kamar ƙugin teku ne yayinda suke hawan dawakansu; suna zuwa a jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi don su fāɗa miki, ya Diyar Sihiyona.” Mun ji labari a kansu, hannuwanmu kuwa suka yi laƙwas. Azaba ta kama mu, zafi kamar na mace mai naƙuda. Kada ku fita zuwa gonaki ko ku yi tafiya a hanyoyi, gama abokin gāba yana da takobi, kuma akwai razana ko’ina. Ya mutanena, ku sanya tufafin makoki ku yi birgima a toka; ku yi kuka mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, gama nan da nan mai hallakarwa zai auko mana. “Na maishe ka mai jarrabawar ƙarfe mutanena ne kuwa ƙarfen, don ka lura ka kuma gwada hanyoyinsu. Su duka masu taurinkai ne, ’yan tawaye, suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da ƙarfe; dukansu lalatattu ne. Mazuga yana zuga da ƙarfi don yă ƙone dalma da wuta, amma tacewa yana tafiya a banza; ba a fitar da mugaye. Ana ce da su azurfar da aka ƙi, gama Ubangiji ya ƙi su.” Banzancin addinin ƙarya (Irmiya 26.1-6) Maganar da ta zo wa Irmiya ke nan daga Ubangiji. “Ka tsaya a ƙofar gidan Ubangiji, a can kuwa ka yi shelar wannan saƙo. “ ‘Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi don yin sujada ga Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allahna Isra’ila, yana cewa ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, zan kuwa bar ku ku zauna a wannan wuri. Kada ku dogara ga maganganun nan na ruɗarwa cewa, “Wannan shi ne haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji!” In dai kuka canja hanyoyinku da ayyukanku kuma kuna aikata adalci da junanku, in ba ku zalunci baƙo, maraya ko gwauruwa ba kuma in ba ku zub da jinin marar laifi a wannan wuri ba, in kuma ba ku bi waɗansu alloli da za su cuce ku ba, to, zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasar da na ba kakanninku har abada abadin. Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani. “ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba, sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama? Wannan gidan da ake kira da Sunana ya zama kogon ’yan fashi ne a gare ku? Amma ina kallo! In ji Ubangiji. “ ‘Yanzu ku fita zuwa Shilo inda na fara maishe shi wurin zama don Sunana, ku ga abin da na yi masa saboda muguntar mutanen Isra’ila. Yayinda kuke yin dukan waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji, na yi muku magana sau da sau, amma ba ku ji ba; na kira ku, amma ba ku amsa ba. Saboda haka, abin da na yi wa Shilo shi ne yanzu zan yi wa gidan da ake kira da Sunana, haikalin da kuka dogara a kai, wurin da na ba ku da kuma kakanninku. Zan kore ku daga gabana, kamar yadda na yi ga dukan ’yan’uwanku, mutanen Efraim.’ “Saboda haka kada ka yi addu’a don wannan mutane ko ka yi wani kuka ko roƙo dominsu, gama ba zan ji ka ba. Ba ka gani abin da suke yi a biranen Yahuda da kuma a titunan Urushalima? Yara sukan tara itace, iyaye suka hura wuta, mata kuma sukan kwaɓa kullu don su yi wa Sarauniyar Sama waina. Sukan miƙa hadayun sha ga waɗansu alloli don su tsokane ni in yi fushi. Amma ni ne suke tsokana? In ji Ubangiji Ashe, ba kansu ne suke cuta, suna kunyata kansu ba? “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa fushina da hasalata za su kwarara a wannan wuri, a kan mutum da dabba, a kan itatuwan fili da a kan amfanin gona, za su yi ta kuna, ba kuwa za a kashe ba. “ ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa ci gaba, ku ƙara hadayun ƙonawarku da sauran sadakoki ku kuma yi ta cin naman! Gama sa’ad da na fitar da kakanninku daga Masar na kuma yi musu magana, ban ba su dokoki kawai game da hadayun ƙonawa da sadakoki ba, amma na ba su wannan umarni cewa ku yi mini biyayya, zan kuwa zama Allahnku ku kuma ku zama mutanena. Ku yi tafiya cikin dukan hanyoyin da na umarce ku, don ku zauna lafiya. Amma ba su saurara ba, ba su kuwa kula ba; a maimako, suka bi shawarar kansu da ta taurare muguwar zukatansu. Su ja da baya a maimakon yin gaba. Daga lokacin da kakanninku suka bar Masar har yă zuwa yau, kullum na yi ta aikan bayina annabawa. Amma ba su saurare ni ba, ba su kula ba. Sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.’ “Sa’ad da ka faɗa musu wannan duka, ba za su saurare ka ba; sa’ad da ka kira su, ba za su amsa ba. Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Wannan ce al’ummar da ba tă yi biyayya ga Ubangiji Allahnta ba, ba kuwa ta karɓi gyara ba. Gaskiya ta ƙare; ta ɓace gaba ɗaya daga leɓunansu. “ ‘Ku aske gashin kanku ku zubar; ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi ’yan zamanin nan ya kuma rabu da su saboda fushin da suka ba shi. Kwarin kisa “ ‘Mutanen Yahuda sun yi mugunta a gabana, in ji Ubangiji. Sun kafa gumakansu masu banƙyama a gidan da ake kira da Sunana suka ƙazantar da shi. Sun gida masujadan Tofet a Kwarin Ben Hinnom don miƙa ’ya’yansu maza da mata a wuta, abin da ban yi umarni ba, ba kuwa yi tunaninsa ba. Saboda haka ku yi hankali, kwanaki suna zuwa in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara kira wurin Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma Kwarin Kisa, gama za su binne matattu a Tofet sai har ba sauran wuri. Sa’an nan gawawwakin wannan mutane za su zama abinci ga tsuntsayen sama da kuma namun jeji, ba za a kuwa sami wani da zai kore su ba. Zan kawo ƙarshen muryar murna da farin ciki da muryar amarya da ango a garuruwan Yahuda da kuma a titunan Urushalima, gama ƙasar za tă zama kufai. “ ‘A wancan lokaci, in ji Ubangiji, za a fitar da ƙasusuwan sarakuna da na shugabannin Yahuda, ƙasusuwan firistoci da na annabawa, da kuma ƙasusuwan mutanen Urushalima daga kaburbura. Za a shimfiɗa su a rana da wata da kuma dukan taurarin sammai, waɗanda suka ƙaunata suka kuma bauta wa, waɗanda suka bi suka nemi shawarar suka kuma yi wa sujada. Ba za a tattara su ko a binne su ba, amma za su zama kamar juji a jibge a ƙasa. Duk inda na kore su zuwa, dukan waɗanda suka ragu na wannan muguwar al’umma za su gwammaci mutuwa da rai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’ “Fada musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Sa’ad da mutane suka fāɗi, ba sa tashi ne? Sa’ad da mutum ya kauce, ba ya dawowa? To, me ya sa waɗannan mutane suka kauce? Me ya sa Urushalima kullum take kaucewa? Sun manne wa ƙarya; suka ƙi su dawo. Na saurara sosai, amma ba su faɗi wata maganar kirki ba. Ba wanda ya tuba daga muguntarsa, sai ma cewa yake, “Me na yi?” Kowa ta kai-ta-kai yake kamar dokin da ya kutsa kai a fagen fama. Ko shamuwa ta sararin sama ma takan san lokutan da aka tsara mata, kurciya, mashirare da kuma zalɓe sukan lura da lokacin ƙauransu. Amma mutanena ba su san abubuwan da Ubangiji yake bukata ba. “ ‘Yaya za ku ce, “Muna da hikima, gama muna da dokar Ubangiji,” alhali alƙalamin ƙarya na magatakarda ya yi ƙarya? Za a kunyatar da masu hikima; za su yi fargaba a kuma kama su. Da yake sun ƙi maganar Ubangiji, wace irin hikima kuka ce kuke da ita? Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu gonakinsu kuma ga waɗansu da suka ci da yaƙi. Tun daga ƙarami har zuwa babba, kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba; har da annabawa da firistoci ma, kowannensu yana ƙarya. Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, “Lafiya, Lafiya,” alhali kuwa ba lafiya. Sukan ji kunyar halin banƙyamarsu kuwa? Sam, ba su da kunya ko kaɗan; ba su ma san yadda za su ji kunya ba. Saboda haka sukan fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za su fāɗi sa’ad da aka hukunta su, in ji Ubangiji. “ ‘Zan ƙwace girbinsu, in ji Ubangiji. Ba a za sami inabi a kuringa ba. Ba za a sami ’ya’ya a itacen ɓaure ba, ganyayensu kuwa za su bushe. Abin da na ba su za a ƙwace.’ ” Me ya sa muke zama a nan? Mu tattaru! Mu gudu zuwa birane masu katanga mu mutu a can! Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa ya kuma ba mu ruwan dafi mu sha, domin mun yi masa zunubi. Mun sa zuciya ga salama amma ba lafiya, mun sa zuciya ga lokacin warkarwa amma sai ga razana. Daga Dan ana jin tirjin dawakan abokin gāba; da jin haniniyar ingarmunsu dukan ƙasar ta girgiza. Sun zo su cinye ƙasar da kome da yake cikinta, birni da dukan mazaunanta. “Duba, zan aika macizai masu dafi a cikinku, kāsā, waɗanda ba su da maƙari, za su kuwa sassare ku,” in ji Ubangiji. Ya mai ta’aziyyata a cikin baƙin ciki, zuciyata ta ɓaci ƙwarai. Ka saurari kukan mutanena daga ƙasa mai nisa suna cewa, Ubangiji ba ya a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya can ne kuma?” “Me ya sa suka tsokane ni da gumakansu har na yi fushi, da baƙin gumakansu marasa amfani?” “Girbi ya wuce, damuna ta ƙare, ba a kuwa cece mu ba.” Da yake an ragargazar da mutanena, an ragargaza ni ke nan; na yi kuka, tsoro ya kama ni. Ba magani ne a Gileyad? Ba likita ne a can? To, me ya sa ba warkarwa wa raunin mutanena? Da ma kaina maɓulɓulan ruwa ne idanuna kuma maɓulɓulan hawaye! Da sai in yi kuka dare da rana saboda mutanena da aka kashe. Da ma a hamada ina da wurin da matafiye za su sauka, don in bar mutanena in tafi in bar su; gama dukansu mazinata ne, taron mutane marasa aminci. “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, don su harba ƙarya; ba da gaskiya ba ne suke nasara a cikin ƙasar. Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan; ba su san ni ba,” in ji Ubangiji. “Ka yi hankali da abokanka; kada ka amince da ’yan’uwanka. Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne, kowane aboki kuma mai kushe ne. Aboki kan ruɗi aboki, ba mai faɗar gaskiya. Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya; sun gajiyar da kansu da yin zunubi. Kai9.6 Wato, Irmiya (jam’i na mutum guda a Ibraniyanci) kana zama a tsakiyar ruɗu; cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,” in ji Ubangiji. Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ga shi zan tace in kuma gwada su, gama me kuwa zan yi saboda zunubin mutanena? Harshensu kibiya ce mai dafi; yana magana da ruɗu. Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa, amma a zuciyarsa ya sa masa tarko. Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in ɗau fansa a kan irin al’umma kamar wannan ba?” Zan yi kuka in yi kururuwa saboda duwatsu in kuma yi makoki game da wuraren kiwon hamada. Sun zama kango ba wanda yake bi cikinta, ba a kuma jin kukan shanu. Tsuntsaye sararin sama sun gudu namun jeji ma duk sun watse. “Zan mai da Urushalima tsibin kufai, wurin zaman diloli; zan kuma lalace garuruwan Yahuda saboda haka ba wanda zai zauna a can.” Wane mutum ne yana da isashiyar hikimar fahimtar wannan? Wa Ubangiji ya umarta da zai iya yin bayani? Me ya sa aka lalace ƙasar ta zama kufai kamar hamada da ba wanda zai iya ratsa ta? Ubangiji ya ce, “Domin sun bar dokata, wadda na sa a gabansu; ba su yi biyayya da ni ko su bi dokata ba. A maimako, sun bi taurin zuciyarsu; suka bi Ba’al, yadda kakanninsu suka koya musu.” Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Ga shi zan sa wannan mutane su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwan dafi. Zan watsar da su a cikin al’ummai da su da kakanninsu ba su sani ba, zan kuma fafare su da takobi sai na hallaka su.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku lura yanzu! Ku kira mata masu makoki su zo ku aika wa gwanaye a cikinsu su zo. Bari su zo da sauri su yi kuka a kanmu sai idanunmu sun cika da hawaye giranmu kuma su jiƙe sharkaf. An ji karar kuka daga Sihiyona cewa, ‘Duba yadda muka lalace! Duba irin babban kunyar da muka sha! Dole mu bar ƙasar domin gidajenmu sun lalace.’ ” Yanzu, ya mata, ku ji maganar Ubangiji; ku buɗe kunnuwanku ga maganar bakina. Ku koya wa ’yan matanku yadda za su yi kuka; ku koya wa juna makoki. Mutuwa ta haura ta tagoginmu ta kuma shiga katangarmu; ta karkashe ’ya’ya a tituna ta kuma karkashe samari a dandali. Ka ce, “Ga abin da Ubangiji ya furta, “ ‘Gawawwakin mutane za su fāɗi kamar juji a fili, kamar hatsin da aka yanka a bayan mai girbi, da ba mai tara su.’ ” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa, amma bari shi wanda yake taƙama ya yi taƙama da wannan, cewa ya fahimci ya kuma san ni, cewa ni ne Ubangiji, wanda yake yin alheri, gaskiya da kuma adalci a duniya, gama a waɗannan ne nake jin daɗi,” in ji Ubangiji. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya kawai a jiki, Masar, Yahuda, Edom, Ammon, Mowab da dukan waɗanda suke zaune a hamada a wurare masu nisa.9.26 Ko kuwa hamada da kuma waɗanda suke hawan gashi kai ta goshinsu Gama dukan waɗannan al’ummai marasa kaciya ne, har dukan gidan Isra’ila ma marasa kaciya ne a zuciya.” Allah da kuma gumaka Ku ji abin da Ubangiji yana ce muku, ya gidan Isra’ila. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ku koyi hanyoyin al’ummai ko ku razana game da alamun sararin sama, ko da yake al’ummai sun razana saboda su. Gama al’adun mutane banza ne; sukan yanke itace daga kurmi, sai mai sassaƙa yă sassaƙa shi da gizago. Sukan yi masa ado da azurfa da kuma zinariya; sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi, don kada yă fāɗi. Kamar dodon gona cikin gonar kabewa, haka gumakansu ba sa iya magana; dole a yi ta ɗaukansu domin ba za su iya tafiya ba. Kada ku ji tsoronsu; ba za su iya yi wa wani lahani ba ba sa iya yin wani abin kirki.” Babu wani kamar ka, ya Ubangiji; kai mai girma ne, kuma sunanka yana da girma da kuma iko. Wane ne ba zai girmama ka ba, Ya Sarkin al’ummai? Tsoronka wajibi ne. A cikin dukan masu hikima na al’ummai kuma cikin dukan mulkokinsu, babu kamar ka. Dukansu marasa azanci ne wawaye; gumakan itacen banza ne suke koya musu. An kawo ƙeraren azurfa daga Tarshish zinariya kuma daga Ufaz. Abin da gwani da maƙerin zinariya suka yi sa’an nan aka yi masa ado da mulufi da shunayya dukan aikin gwanaye. Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya; shi ne Allah mai rai, madawwamin sarki. Sa’ad da ya yi fushi, ƙasa takan girgiza; al’ummai ba sa iya jure da hasalarsa. “Ka faɗa musu wannan, ‘Waɗannan alloli, waɗanda ba su yi sammai da ƙasa ba, za su hallaka daga duniya da kuma daga ƙarƙashin sammai.’ ”10.11 Wannan sashe na wannan aya yana a harshen Arameya ne. Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa. Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi; yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya. Yakan aiki walƙiya da ruwan sama ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa. Kowa marar azanci ne, marar ilimi; kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa. Siffofinsa ƙarya ne; ba su da numfashi a cikinsu. Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne; Sa’ad da hukuncinsu ya yi za su lalace. Shi da yake Rabon Yaƙub ba kamar waɗannan yake ba, gama shi ne Mahaliccin abubuwa duka, har da Isra’ila, kabilar gādonsa Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. Hallaka mai zuwa Ku tattara kayayyakinku don ku bar ƙasar, ku da kuke zaune a wurin da aka kewaye da yaƙi. Gama haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan lokaci zan jefar da waɗanda suke zaune a ƙasar; zan kawo damuwa a kansu domin a kama su.” Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini! Raunina ba mai warkewa ba ne! Duk da haka na ce wa kaina, “Wannan ciwona ne, dole kuma in jure da shi.” An lalatar da tentina; dukan igiyoyinsa sun tsintsinke. ’Ya’yana maza sun bar ni ba sa nan; ba wanda aka bari da zai kafa tentina ko ya kafa mini mafaka. Makiyaya marasa azanci ne kuma ba sa neman nufin Ubangiji; saboda haka ba sa nasara dukan garkensu kuwa ya watse. Ku saurara! Rahoto yana zuwa babban hargitsi daga ƙasar arewa! Zai mai da garuruwan Yahuda kufai, mazaunin diloli. Addu’ar Irmiya Na sani, ya Ubangiji, cewa ran mutum ba nasa ba ne; ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba. Ka yi mini gyara, Ubangiji, amma fa da adalci kaɗai ba cikin fushinka ba, don kada ka wofinta ni. Ka zuba hasalarka a kan al’umman da ba su san ka ba, a kan mutanen da ba sa kira bisa sunanka. Gama sun cinye Yaƙub; sun cinye shi gaba ɗaya suka kuma lalace wurin zamansa. An take alkawari Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji. “Ka saurari zancen wannan alkawari ka kuma faɗe su ga mutanen Yahuda da kuma waɗanda suke zaune a Urushalima. Ka faɗa musu cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa, ‘La’ananne ne wanda bai kula da zancen alkawarin nan ba, zancen da na umarci kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga cikin tanderun narkewar ƙarfe.’ Na ce, ‘Ku yi mini biyayya ku kuma aikata kowane abin da na umarce ku, za ku kuwa zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku. Sa’an nan zan cika rantsuwar da na yi wa kakanni-kakanninku, da zan ba su ƙasa mai zub da madara da kuma zuma’ ƙasar da kuka mallaka a yau.” Sai na amsa na ce, “Amin, Ubangiji.” Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuda da titunan Urushalima duka cewa, ‘Su saurari zancen alkawarin nan, su aikata. Daga lokacin da na fitar da kakanni-kakanninku daga Masar har yă zuwa yau, na gargaɗe su sau da sau, ina cewa, “Ku yi mini biyayya.” Amma ba su kasa kunne ko su saurara ba, a maimako, sai suka bi taurinkai na mugayen zukatansu. Saboda haka na kawo musu dukan la’anonin alkawarin da na riga na umarce su, su bi amma ba su kiyaye ba.’ ” Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Akwai maƙarƙashiya a cikin mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima. Sun koma ga zunuban kakanni kakanninsu, waɗanda suka ƙi su saurari maganata. Suka bi waɗansu alloli don su bauta musu. Da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda duk sun take alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu. Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan kawo masifa a kansu wadda ba za su iya tsere mata ba. Ko da yake suna kuka gare ni, ba zan saurare su ba. Garuruwan Yahuda da mutanen Urushalima za su tafi su yi kuka ga allolin da suke ƙona wa turare, amma ba za su taimake su ba sam sa’ad da masifar ta auku. Kuna da alloli masu yawa yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda; kuma bagadan da kuka yi don ƙona turare wa allahn nan Ba’al abin kunya sun yi yawa kamar titunan Urushalima.’ “Kada ka yi addu’a domin wannan mutane ko ka miƙa wani roƙo ko kuka dominsu, domin ba zan saurara ba sa’ad da suka kira gare ni a lokacin ƙuncinsu. “Mene ne ƙaunatacciyata take yi a haikali da yake ta yin ƙulle-ƙullen mugayen makircinta tare da mutane masu yawa? Tsarkakar nama zai iya kawar da hukuncinki? Sa’ad da kike yin muguntarki sa’an nan ki yi farin ciki.”11.15 Ko kuwa Ko tsarkakan nama zai kawar da hukuncinki? Sa’an nan ki yi farin ciki Ubangiji ya kira ki itacen zaitun mai inuwa kyakkyawa mai ’ya’ya masu kyau. Amma da ƙugin babbar hadari zai cinna masa wuta, rassansa za su kakkarye. Ubangiji Maɗaukaki, wanda ya dasa ki, ya furta miki masifa, domin gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda sun aikata mugunta suka kuma tsokane ni in yi fushi ta wurin ƙona wa Ba’al turare. An shirya wa Irmiya maƙarƙashiya Domin Ubangiji ya bayyana mini maƙarƙashiyarsu, na santa, gama a wannan lokaci ya nuna mini abin da suke yi. Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.” Amma, ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake yin shari’a da adalci kake gwada zuciya da kuma tunani, ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, gama a gare ka na danƙa maganata. “Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka suna kuma cewa, ‘Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji in ba haka za ka mutu a hannunmu’ saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘Zan hukunta su. Samarinsu za su mutu ta wurin takobi, ’ya’yansu maza da mata kuwa ta wurin yunwa. Babu raguwar da za a bar musu, domin zan kawo masifa a kan mutanen Anatot a shekarar hukuncinsu.’ ” Damuwar Irmiya Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji, sa’ad da na kawo ƙara a gabanka. Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka. Me ya sa mugaye suke nasara? Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa? Ka dasa su, sun kuwa yi saiwa; sun yi girma suna ba da ’ya’ya. Kullum sunanka yana a bakinsu amma kana nesa da zuciyarsu. Duk da haka ka san ni, ya Ubangiji; kana ganina ka kuma gwada tunanina game da kai. Ka ja su kamar tumakin da za a yanka! Ka ware su don ranar yanka! Har yaushe ƙasar za tă kasance busasshiya12.4 Ko kuwa ƙasar za tă yi makoki ciyawar kowane fili ta bushe? Domin waɗanda suke zaune cikinta mugaye ne, dabbobi da tsuntsaye sun hallaka. Ban da haka ma, mutane suna cewa, “Ba zai ga abin da yake faruwa da mu ba.” Amsar Allah “In ka yi tsere da mutane a ƙafa suka kuma gajiyar da kai, yaya za ka yi gasa da dawakai? In ka yi tuntuɓe a lafiyayyiyar ƙasa,12.5 Ko kuwa In ka dogara a lafiyayyiyar ƙasa ƙaƙa za ka yi a kurmin12.5 Ko kuwa a rigyawar Urdun? ’Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka; sun tā da kuka mai ƙarfi a kanka. Kada ka amince da su, ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai. “Zan yashe gidana, in rabu da gādona; Zan ba da wadda nake ƙauna a hannuwan abokan gābanta. Gādona ya zama mini kamar zaki a kurmi. Yana mini ruri; saboda haka na ƙi shi. Ashe, gādona bai zama mini kamar dabbare dabbaren tsuntsu mai cin nama da sauran tsuntsaye masu cin nama suka kewaye shi da faɗa ba? Tafi ka tattaro dukan namun jeji; ka kawo su su ci. Makiyaya masu yawa za su lalace gonar inabina su tattake gonata; za su mai da gonata mai kyau kango marar amfani. Za tă zama kango, busasshiya da kuma kango a gabana; ƙasar duka za tă zama kango domin ba wanda ya kula. A kan dukan tsaunukan nan na hamada masu hallakarwa za su zo, gama takobin Ubangiji zai ci daga wannan iyaka ƙasa zuwa wancan; ba wanda zai zauna lafiya. Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa; za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba. Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe saboda zafin fushin Ubangiji.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Game da dukan mugayen maƙwabtana waɗanda suka ƙwace gādon da na ba wa mutanena Isra’ila kuwa, zan tumɓuke su daga ƙasashensu zan kuma tumɓuke gidan Yahuda daga cikinsu. Amma bayan na tumɓuke su, zan sāke jin tausayi in komo da kowannensu zuwa gādonsa da kuma ƙasarsa. In kuma suka koyi al’amuran mutanena sosai suka kuma yi rantsuwa da sunana, suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye’ kamar yadda sun taɓa koya wa jama’ata yin rantsuwa da Ba’al, sa’an nan za su kahu a cikin jama’ata. Amma duk al’ummar da ba tă saurara ba, zan tumɓuke ta ɗungum in kuma hallaka ta,” in ji Ubangiji. Abin ɗamara na lilin Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Tafi ka sayo abin ɗamara na lilin ka sha ɗamara da shi, amma kada ka bari yă taɓa ruwa.” Saboda haka na sayo abin ɗamara, yadda Ubangiji ya umarce ni, na kuwa sha ɗamara da shi. Sai maganar Ubangiji ta zo mini sau na biyu cewa, “Ka ɗauki abin ɗamara da ka sayo, wanda ka ɗaura, ka tafi yanzu zuwa Fera13.4 Ko kuwa mai yiwuwa Yuferites; haka ma a ayoyi 5-7 ka ɓoye shi a cikin kogon dutse.” Saboda haka na tafi na ɓoye shi a Fera, yadda Ubangiji ya ce mini. Bayan ’yan kwanaki sai Ubangiji ya ce mini, “Tafi yanzu zuwa Fera ka ɗauko abin ɗamara da na ce maka ka ɓoye a can.” Sai na tafi Fera da haka na ɗauko abin ɗamara daga wurin da na ɓoye shi, amma abin ɗamara yanzu ya lalace ya zama ba shi da amfani sam. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Haka zan lalatar da alfarmar Yahuda da yawan alfarmar Urushalima. Waɗannan mugayen mutane, waɗanda suka ƙi saurari maganata, waɗanda suka biye wa taurin zuciyarsu suka bi waɗansu alloli don su bauta su kuma yi musu sujada, za su zama kamar wannan abin ɗamara gaba ɗaya marasa amfani! Gama kamar yadda abin ɗamara kan kame gindin mutum tam, haka zan daure dukan gidan Isra’ila da dukan gidan Yahuda gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘domin su zama jama’a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.’ Salkunan ruwan inabi “Faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi.’ In kuwa suka ce maka, ‘Ba mu san cewa ya kamata a cika kowace salkar ruwan inabi da ruwan inabi ba?’ Sai ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan cika dukan waɗanda suke zama a ƙasar da buguwa, har ma da sarakunan da suke zama a kursiyin Dawuda, firistoci, annabawa da dukan waɗanda suke zaune a Urushalima. Zan fyaɗe su a kan juna, iyaye da ’ya’yansu maza, in ji Ubangiji. Tausayi ko jinƙai, ko juyayi ba zai hana ni hallaka su ba.’ ” Barazanar kwashewa zuwa zaman bauta Ku ji ku kuma saurara, kada ku yi girman kai, gama Ubangiji ya yi magana. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku kafin ya kawo duhu, kafin ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan tuddai masu duhu. Za ku sa zuciya ganin haske amma zai mai da shi duhu mai kauri ya kuma canja shi zuwa duhu baƙi ƙirin. Amma in ba ku saurara ba, zan yi kuka a ɓoye saboda girmankanku; idanuna za su yi kuka mai zafi, suna zub da hawaye ƙwarai, domin zan kwashe garken Ubangiji zuwa zaman bauta. Ka faɗa wa sarki da kuma mahaifiyar sarauniya cewa, “Ku sauko daga kursiyinku, gama rawaninku na ɗaukaka za su fāɗi daga kawunanku.” Za a kulle biranen da suke a Negeb, kuma babu wanda zai buɗe su. Za a kwashe dukan Yahuda zuwa zaman bauta, za a kwashe su tas. Ku tā da idanunku ku ga waɗanda suke zuwa daga arewa. Ina garken da aka ba ku tumakin da kuke taƙama a kai? Me za ku ce sa’ad da Ubangiji ya naɗa muku waɗanda ku kanku kuka koya musu a matsayi abokai na musamman? Ashe, azaba ba za tă auko muku kamar na mace mai naƙuda ba? In kuma kuka tambaye kanku “Me ya sa wannan ya faru da mu?” Wannan kuwa saboda yawan zunubanku ne ya sa fatarinku ya yage aka kuma wahalshe jikinku. Mutumin Habasha13.23 Da Ibraniyanci Mutumin Kush (mai yiwuwa mutum daga yankin Bisa na Nilu). zai iya canja launin fatar jikinsa ko damisa ta canja dabbare dabbarenta? Ba za ku iya yin alheri ku da kuka saba da yin mugunta ba. “Zan watsar da ku kamar yayin da iskar hamada take hurawa. Rabonku ne wannan, sashen da na auka muku,” in ji Ubangiji “domin kun manta da ni kuka kuma dogara ga allolin ƙarya. Zan kware fatarinku sama ya rufe fuskarku don a iya ga tsiraicinku zinace zinacenku da haniniya kamar dawakai, karuwancinku na bankunya! Na ga ayyukanku na banƙyama a kan tuddai da kuma a filaye. Kaitonki, ya Urushalima! Har yaushe za ki ci gaba da rashin tsarki?” Fari, yunwa da takobi Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa, “Yahuda tana makoki biranenta suna fama; suna kuka saboda ƙasar, kuka kuma tana tasowa daga Urushalima. Manyan mutane suna aika bayinsu su ɗebo ruwa a maɓulɓulai amma babu ruwa. Suka dawo da tulunansu haka nan; da kunya da kuma ƙasƙanci, da kawunansu a rufe. Ƙasa ta tsattsage saboda babu ruwan sama a ƙasar; manoma sun sha kunya suka kuma rufe kawunansu. Har barewa a kurmi ma ta gudu ta bar ’ya’yan da ta haihu sababbi saboda babu ciyawa. Jakan jeji suna tsaye a kan tuddai suna haki kamar diloli; idanunsu sun kāsa gani saboda rashin makiyaya.” Ko da yake zunubanmu suna ba da shaida a kanmu, Ya Ubangiji, ka yi wani abu saboda sunanka. Gama jan bayanmu ya yi yawa; mun yi maka zunubi. Ya kai, Sa Zuciyar Isra’ila, Mai Cetonsa a lokutan wahala, me ya sa kake yi kamar baƙo a ƙasar, kamar matafiyi wanda yake shirya wuri don yă kwana gari ya waye ya wuce? Me ya sa kake yi kamar mutumin da aka far masa kwasam ba zato, kamar jarumi marar ƙarfin ceto? Kana a cikinmu, ya Ubangiji, da sunanka ake kiranmu; kada ka yashe mu! Ga abin da Ubangiji ya ce game da wannan mutane, “Suna son yawace-yawace ƙwarai; ba sa hana ƙafafunsu yawo. Saboda haka Ubangiji bai yarda da su ba; yanzu zai tuna da muguntarsu zai kuma hukunta su saboda zunubansu.” Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu’a domin zaman lafiyar mutanen nan. Ko da yake suna azumi, ba zan saurari kukansu ba, ko da yake suna miƙa hadayun ƙonawa da hadayun gari, ba zan yarda da su ba. A maimako zan hallaka su da takobi, yunwa da annoba.” Amma na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, annabawa sun riƙa ce musu, ‘Ba za ku ga takobi ko ku yi fama da yunwa ba. A maimako, zan ba ku madawwamiyar salama.’ ” Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne. Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su. Mutanen da suke musu annabcin kuwa za a kore su zuwa titunan Urushalima saboda yunwa da kuma takobi. Babu wanda zai binne su, ko ya binne matansu, ko ’ya’yansu maza da mata. Zan aukar musu da masifar da ya dace da su. “Ka yi musu wannan magana, “ ‘Bari idanuna su yi ta zub da hawaye dare da rana kada su daina; saboda ’yata budurwa, mutanena, sun sha wahalar babban rauni, an yi musu bugu mai ragargazawa. In na shiga cikin ƙasar, na ga waɗanda takobi ya kashe; in na shiga cikin birni, na ga waɗanda suke fama da yunwa. Da Annabi da firist duk sun tafi ƙasar da ba su sani ba.’ ” Ka ƙi Yahuda ɗungum ke nan? Kana ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu don kada mu warke? Mun sa zuciya ga salama babu abin alherin da ya zo, mun sa rai ga lokacin warkarwa amma sai ga razana. Ya Ubangiji, mun gane da muguntarmu da kuma laifin kakanninmu; tabbatacce mun yi maka zunubi. Saboda sunanka kada ka ƙi mu; kada ka ƙasƙantar da kursiyoyinka mai ɗaukaka. Ka tuna da alkawarinka da mu kada ka tā da shi. Akwai wani daga cikin gumaka marasa amfani na al’ummai da ya kawo ruwan sama? Sararin sama kansu sukan yi yayyafi? A’a, kai ne, ya Ubangiji Allahnmu. Saboda haka sa zuciyarmu tana a kanka, gama kai ne kake yi wannan duka. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi! In kuma suka tambaye ka, ‘Ina za mu tafi?’ Sai ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Waɗanda aka ƙaddara ga mutuwa, ga mutuwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga takobi, ga takobi za su; waɗanda aka ƙaddara ga yunwa, ga yunwa za su; waɗanda aka ƙaddara ga zaman bauta, ga zaman bauta za su.’ “Zan aika musu da iri masu hallakarwa guda huɗu,” in ji Ubangiji, “takobi zai kashe, karnuka za su kwashe, tsuntsaye da namun jeji kuma su cinye su kuma hallaka. Zan sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya saboda abin da Manasse ɗan Hezekiya sarkin Yahuda ya aikata a Urushalima. “Wa zai ji tausayinki, ya Urushalima? Wa zai yi makoki dominki? Wa zai dakata ya tambayi lafiyarki? Kin ƙi ni,” in ji Ubangiji. “Ki ci gaba da ja da baya. Ta haka zan ɗibiya hannuwana a kanki in hallaka ki; ba zan ƙara nuna miki jinƙai ba. Zan sheƙe ki da abin sheƙewa a ƙofofin birnin ƙasar. Zan kawo baƙin ciki da hallaka a kan mutanena, gama ba su canja hanyoyinsu ba. Zan ƙara yawan gwaurayensu su fi yashin teku yawa. Da tsakar rana zan kawo mai hallakarwa a kan iyaye mata na samarinsu; farat ɗaya zan kawo musu wahala da razana. Mahaifiya ’ya’ya bakwai za tă suma ta ja numfashinta na ƙarshe. Ranarta zai fāɗi tun lokacin bai yi ba; za tă sha kunya a kuma wulaƙanta ta. Zan sa a kashe raguwa da takobi a gaban abokan gābansu,” in ji Ubangiji. Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni, mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi! Ban ba da bashi ko in ci bashi ba, duk da haka kowa yana zagina. Ubangiji ya ce, “Tabbatacce zan cece ka don alheri; tabbatacce zan sa abokan gābanka su yi roƙo gare ka a lokacin masifa da kuma lokacin wahala. “Mutum zai iya karye ƙarfe ƙarfe daga arewa, ko tagulla? “Dukiyarku da arzikinku zan ba da su ganima, babu tara, saboda duka zunubanku ko’ina a ƙasar. Zan bautar da ku ga abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina zai yi ƙuna kamar wuta da za tă yi ƙuna a kanku.” Ka gane, ya Ubangiji; ka tuna da ni ka kuma lura da ni. Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini. Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni; ka tuna yadda na sha zagi saboda kai. Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su; suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna, gama ana kirana da sunanka, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki. Ban taɓa zauna a cikin ’yan tawaye ba, ban taɓa yi murna da su ba; na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina ka kuma sa na cika da haushi. Me ya sa wahalata ba ta ƙarewa mikina kuma ba ya warkuwa? Za ka zama mini kamar rafi mai yaudara ne, kamar maɓulɓulan da ta kafe ne? Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “In ka tuba, zan maido da kai don ka bauta mini; in ka ambaci maganganu masu kyau, ba marasa kyau ba, za ka zama kakakina. Bari wannan mutane su juyo gare ka, amma kada ka juye gare su. Zan mai da kai katanga ga wannan mutane, katanga mai ƙarfi na tagulla; za su yi yaƙi da kai amma ba za su yi nasara a kanka ba, gama ina tare da kai don in kuɓutar in kuma cece ka,” in ji Ubangiji. “Zan cece ka daga hannuwan mugaye in ɓamɓare ka daga hannun marasa tausayi.” Ranar masifa Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Kada ka yi aure ka haifi ’ya’ya maza da mata a wannan wuri.” Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da ’ya’ya maza da matan da aka haifa a wannan ƙasa da kuma game da matan da suke iyayensu da suke mazan da iyayensu. “Za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi kuka dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba, amma za a bar su a juji. Takobi da yunwa ne za su hallaka su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji na duniya.” Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ka shiga gidan da akwai abincin makoki; kada ka tafi ka yi makoki ko ka nuna juyayi, domin na janye albarkata, ƙaunata da tausayina daga wannan mutane,” in ji Ubangiji. “Manya da ƙanana duka za su mutu a wannan ƙasa. Ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi makokinsu ba, kuma ba wanda zai tsaga kansa ko ya aske kansa saboda su. Ba wanda zai ba da abinci don yă ta’azantar da waɗanda suke makoki saboda matattu, kai, ko saboda mahaifi ko mahaifiya ma ba kuwa wani da zai ba da abin sha don yă ta’azantar da su. “Kada kuma ka shiga gidan da ake biki ka zauna don ci da sha. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa a idanunka da kuma a kwanakinka zan kawo ƙarshen muryar farin ciki da murna da kuma muryoyin amarya da ango a wannan wuri. “Sa’ad da ka faɗa wa waɗannan mutane wannan duka suka kuma tambaye ka, ‘Me ya sa Ubangiji ya ƙaddara irin wannan babban masifa a kanmu? Wace mugunta muka yi? Wane zunubi muka aikata wa Ubangiji Allahnmu?’ Sai ka ce musu, ‘Wannan ya zama haka domin kakanninku sun rabu da ni,’ in ji Ubangiji, ‘suka bi waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Suka rabu da ni, ba su kuwa kiyaye dokata ba. Amma kun yi laifi fiye da kakanninku. Duba yadda kowannenku yana bin taurin muguwar zuciyarsa a maimakon yin mini biyayya. Saboda haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasar da ku da kakanninku ba ku taɓa sani ba, a can kuwa za ku bauta wa waɗansu alloli dare da rana, gama ba zan nuna muku tagomashi ba.’ “Amma fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga Masar,’ amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su.’ Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba wa kakanninsu. “Amma yanzu zan aiko a kira masunta masu yawa su zo,” in ji Ubangiji, “za su kuma kama su. Bayan wannan zan aiko a kira mafarauta su zo, su farauce su daga kowane dutse da tudu da kuma daga kogwannin duwatsu. Idanuna suna a kan dukan hanyoyinsu; ba a ɓoye suke daga gare ni, kuma zunubansu ba a ɓoye suke a idanuna ba. Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, suka kuma cika abin gādona da gumakansu na banƙyama.” Ya Ubangiji, ƙarfina da katangana, mafakata a lokacin damuwa, gare ka al’ummai za su zo daga iyakokin duniya su ce, “Kakanninmu ba su mallaki kome ba sai allolin ƙarya, gumakan banza da ba su yi musu amfani ba. Mutane kan yi allolinsu ne? I, amma waɗannan ba alloli ba ne!” “Saboda haka zan koya musu a wannan lokaci zan koya musu ikona da ƙarfina. Sa’an nan za su sani cewa sunana Ubangiji ne. “An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe, an rubuta da tsinin dutse, a kan allunan zukatansu da kuma a kan ƙahonin bagadansu. Har ’ya’yansu ma sun tuna bagadansu da ginshiƙan Asheransu kusa da itatuwa masu duhuwa da kuma a kan tuddai masu tsayi. Dutsena a ƙasar da17.2,3 Ko kuwa tuddai 3 da duwatsun ƙasar. Naku dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinku za a ba da su ganima, tare da masujadanku na kan tuddai, saboda zunubi ko’ina a ƙasarku. Saboda laifinku za ku rasa gādon da na ba ku. Zan bautar da ku ga abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, domin kun husata ni, zai kuwa ci har abada.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum, wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya. Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango; ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba. Za su zauna a busassun wuraren hamada, a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa. “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji. Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.” Zuciya ta fi kome ruɗu ta fi ƙarfin warkewa. Wa zai iya gane ta? “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya in gwada tunani, don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa, bisa ga ayyukansa.” Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba. A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi, a ƙarshe kuma zai zama wawa. Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko, shi ne wuri mai tsarkinmu. Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila, duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya. Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura domin sun yashe Ubangiji, maɓulɓular ruwan rai. Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke; ka cece ni zan kuwa cetu, gama kai ne nake yabo. Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take? Bari tă cika yanzu!” Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba; ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba. Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka. Kada ka zama mini abin razana; kai ne mafakata a ranar masifa. Bari masu tsananta mini su sha kunya, amma ka kiyaye ni daga shan kunya; bari su tsorata, amma ka kiyaye ni da razana. Ka kawo musu ranar masifa; ka hallaka su da hallaka riɓi biyu. Kiyaye Asabbaci da tsarki Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima. Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima. Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku. Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba. Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba, sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada. Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji. Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ” A gidan mai ginin tukwane Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji. “Ka gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, a can zan ba ka saƙona.” Sai na gangara zuwa gidan mai ginin tukwane, na gan shi yana aiki a na’urar ginin tukwanen. Amma tukunyar da yake ginawa ta lalace a hannuwansa, sai mai ginin tukwanen ya sāke gina wata tukunya dabam, yana gyara ta yadda ya ga dama. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila. A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki, in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata. In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta, in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata. “Yanzu fa, sai ka faɗa wa mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa ga shi! Ina shirya muku masifa ina ƙirƙiro dabara a kanku. Saboda haka ku juya daga mugayen hanyoyinku, kowannenku, ku canja hanyoyinku da kuma ayyukanku.’ Amma za su amsa su ce, ‘Ba amfani. Za mu ci gaba da shirye-shiryenmu; kowannenmu zai bi taurin muguwar zuciyarsa.’ ” Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tattambaya a cikin al’ummai. Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu mafi banƙyama. Dusar ƙanƙarar Lebanon ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon? Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa sun taɓa daina gudu? Duk da haka mutanena sun manta da ni; sun ƙone turare wa gumaka marasa amfani, waɗanda suka sa su tuntuɓe a al’amuransu a hanyoyin dā. Sun sa suka yi tafiya a ɓarayin hanyoyi a hanyoyin da ba a gina ba. Ƙasarsu za tă zama kufai, abin reni har abada; dukan waɗanda suka wuce za su yi mamaki su kaɗa kai. Kamar iska daga gabas zan warwatsa su a gaban abokan gābansu; zan juya musu bayana, ba zan nuna musu fuskata ba a ranar masifarsu.” Suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya; gama koyarwar doka da firist ya yi ba za tă ɓace ba, haka ma shawara daga mai hikima da kuma magana daga annabawa. Saboda haka ku zo, mu fāɗa masa da harsunanmu kada mu saurari wani abin da zai faɗa.” Addu’ar Irmiya Ka saurare ni, ya Ubangiji ka ji abin da masu zargina suke cewa! Ya kamata a sāka wa alheri da mugunta? Duk da haka sun haƙa mini rami. Ka tuna cewa na tsaya a gabanka na kuma yi magana a madadinsu don ka janye fushinka daga gare su. Saboda haka ka kawo wa ’ya’yansu yunwa; ka miƙa su ga ikon takobi. Bari matansu su zama marasa ’ya’ya da gwauraye; bari a kashe mazansu, a kuma kashe samarinsu da takobi a yaƙi. Bari a ji kuka daga gidajensu sa’ad da ka kawo masu hari a kansu farat ɗaya, gama sun haƙa rami don su kama ni suka kuma kafa tarko wa ƙafafuna. Amma Ya Ubangiji, ka san duk maƙarƙashiyarsu, na neman su kashe ni. Kada ka gafarta musu laifofinsu ko ka shafe zunubansu daga gabanka. Bari a tumɓuke su a gabanka; ka yi da su sa’ad da kake fushi. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tafi ka sayo tulu a wurin mai ginin tukwane. Ka ɗauki waɗansu dattawan jama’a da kuma na firistoci ku fita zuwa Kwarin Ben Hinnom, kusa da mashigin Ƙofar Kasko. A can ka furta maganganun da na faɗa maka, ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya sarakunan Yahuda da kuma mutanen Urushalima. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku saurara! Zan kawo masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa. Gama sun yashe ni suka kuma mai da wannan wuri ya zama na baƙin alloli; sun ƙone hadayu a cikinsa wa allolin da ko su ko kakanninsu ko sarakunan Yahuda ba su taɓa sani ba, suka kuma cika wannan wuri da jini marasa laifi. Suka gina masujadai na kan tudu na Ba’al don su ƙona ’ya’yansu maza a cikin wuta a matsayin hadaya ga Ba’al abin da ban umarta ba, ban ambata ba, bai kuma zo mini ba. Saboda haka ku lura, kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara ce da wannan wuri Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma za su ce da shi Kwarin Kisa. “ ‘A wannan wuri zan lalace19.7 Ibraniyanci na lalace ya yi kamar Ibraniyanci na tulu (dubi ayoyi 1 da 10). dabarun Yahuda da na Urushalima. Zan sa a kashe su da takobi a gaban abokan gābansu, a hannuwan waɗanda suke neman ransu, zan kuma ba da gawawwakinsu su zama abinci ga tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji. Zan ragargazar da wannan birni in mai da shi abin reni, duk wanda ya wuce zai yi mamaki ya kuma yi tsaki saboda dukan masifunsa. Zan sa su ci naman ’ya’yansu maza da mata, za su kuma ci naman juna a lokacin damuwar ƙawanya da abokan gāban da suke neman ransu za su yi musu.’ “Sa’an nan ka fasa tulun yayinda waɗanda suka tafi tare da kai suna duba, ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa zan farfasa wannan al’umma da wannan birni kamar yadda aka farfasa wannan tulu mai ginin tukwane ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne matattu a Tofet har sai ba sauran wuri. Ga abin da zan yi wa wannan wuri da waɗanda suke zaune a nan, in ji Ubangiji. Zan mai da wannan birni kamar Tofet. Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’ ” Sa’an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don yă yi annabci, ya tsaya a filin haikalin Ubangiji ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa wannan birni da ƙauyukan da suke kewayensa kowace masifar da na furta a kansu, domin sun yi taurinkai, ba su kuwa saurari maganata ba.’ ” Irmiya da Fashhur Da firist nan Fashhur ɗan Immer, babban ma’aikaci a cikin haikalin Ubangiji, ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan abubuwa, sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka aka kuma sa shi a turu a Ƙofar Bisa na Benyamin a haikalin Ubangiji. Kashegari, sa’ad da Fashhur ya fitar da shi daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashhur ba, amma ya ba ka suna Magor-Missabib.20.3 Magor-Missabib yana nufin razana ta kowace fuska. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi. Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon. Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ” Damuwar Irmiya Ya Ubangiji, ka ruɗe20.7 Ko kuwa rarrashe ni, na kuwa ruɗu; ka fi ni ƙarfi, ka kuwa yi nasara. Na zama abin dariya dukan yini; kowa yana yi mini ba’a. Duk sa’ad da na yi magana, nakan tā da murya ina furta hargitsi da hallaka. Haka maganar Ubangiji ta kawo mini zagi da reni dukan yini. Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba ba zan ƙara yin magana da sunansa ba,” sai in ji maganarsa a cikina kamar wuta, wutar da aka kulle a ƙasusuwana. Na gaji da danne ta a cikina; tabbatacce ba zan iya ba. Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa, “Razana ta kowace fuska! Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!” Dukan abokaina suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa, “Mai yiwuwa a ruɗe shi; sai mu yi nasara a kansa mu ɗau fansa a kansa.” Amma Ubangiji yana tare da ni kamar babban jarumi; saboda haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe ba kuwa za su yi nasara ba. Za su fāɗi su kuma sha mummunar kunya; ba za a taɓa manta da rashin bangirmansu ba. Ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake gwada adali kana bincika zuciya duk da tunani, bari in ga sakayyarka a kansu, gama a gare ka na miƙa damuwata. Ku rera ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji! Ya kuɓutar da ran mabukaci daga hannuwan mugaye. La’ananniya ce ranar da aka haife ni! Kada ranar da mahaifiyata ta haife ni ta zama mai albarka! La’ananne ne mutumin da ya kawo wa mahaifina labari, wanda ya sa shi ya yi murna cewa, “An haifa maka yaro, ɗa namiji!” Bari mutumin ya zama kamar garuruwan da Ubangiji ya tumɓuke ba tausayi. Bari yă ji kuka da safe kururuwan yaƙi kuma da tsakar rana. Gama bai kashe ni a cikin ciki ba, da ma ya sa cikin mahaifiyata ya zama kabarina, cikinta ya fadada har abada. Me ya sa na ma fito daga cikin ciki in ga wahala da baƙin ciki in kuma ƙare kwanakina da kunya? Allah ya ƙi amsa roƙon Zedekiya Magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji sa’ad da Sarki Zedekiya ya aiki Fashhur ɗan Malkiya da firist Zefaniya ɗan Ma’asehiya gare shi. Suka ce masa, “Yanzu ka roƙi mana Ubangiji saboda Nebukadnezzar21.2 Da Ibraniyanci Nebukadrezzar, wanda Nebukadnezzar ne wani suna; a nan da kuma sau da dama a Irmiya da Ezekiyel. sarkin Babilon yana kawo mana yaƙi. Wataƙila Ubangiji zai yi mana waɗansu abubuwa banmamaki kamar a lokacin baya don yă janye daga gare mu.” Amma Irmiya ya amsa musu ya ce, “Ku faɗa wa Zedekiya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yake cewa ina shirin juya kayan yaƙin da suke a hannuwanka a kanka, waɗanda kake amfani don ka yaƙi sarki Babilon da kuma Babiloniyawa21.4 Ko kuwa Kaldiyawa; haka ma a aya 9 waɗanda suka kewaye katangar birnin, zan kuwa tsiba kayan yaƙinka a tsakiyar birnin nan. Ni da kaina zan yi yaƙi da kai da miƙaƙƙen hannu mai ƙarfi cikin fushi da hasala mai girma. Zan kashe waɗanda suke zaune a wannan birni, mutane da dabbobi za su kuwa mutu da muguwar annoba. Bayan wannan, in ji Ubangiji, zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da kuma mutanen wannan birni waɗanda suka tsira daga annoba, takobi da kuma yunwa, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Zai kashe su da takobi; ba zai ji tausayinsu ko ya yi musu jinƙai ko ya yi juyayinsu ba.’ “Bugu da ƙari, ka faɗa wa mutanen cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ga shi na sa a gabanku hanyar rai da hanyar mutuwa. Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba. Amma duk wanda ya fita ya miƙa kansa ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye ku zai rayu; zai kuɓutar da ransa. Na ƙudura in yi wa wannan birni lahani ba alheri ba, in ji Ubangiji. Za a ba da shi a hannuwan sarki Babilon, zai kuwa hallaka shi da wuta.’ “Ban haka ma, ka faɗa wa gidan sarauta na Yahuda cewa, ‘Ku saurari maganar Ubangiji; Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ku yi gaskiya kowace safiya; ku kuɓuta daga hannun mai danniya wannan da aka yi wa fashi in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci babu wanda zai kashe ta. Ina gāba da ku, mazaunan Urushalima, ku da kuke zama a bisa wannan kwari kan dutsen da yake a fili, in ji Ubangiji ku da kuke cewa, “Wa zai iya yaƙe mu? Wa zai iya shiga mafakarmu?” Zan hukunta ku gwargwadon ayyukanku, in ji Ubangiji. Zan sa wuta a kurminku da za tă cinye kome da yake kewaye da ku.’ ” Hukunci a kan mugayen sarakunan Yahuda Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka gangara zuwa fadan sarkin Yahuda ka yi shelar wannan saƙo a can ka ce, ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya sarkin Yahuda, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda, kai, da fadawanka da mutanenka waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri. Gama in ka lura da bin waɗannan umarnai, to, sarakunan da suke zaune a gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan fada, suna hawan kekunan yaƙi da dawakai, fadawansu da mutanensu suna musu rakiya. Amma in ba ku kiyaye waɗannan umarnai ba, in ji Ubangiji, na rantse da kaina cewa wannan fada za tă zama kufai.’ ” Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da wannan fadar sarkin Yahuda, “Ko da yake kina kamar Gileyad a gare ni, kamar ƙwanƙolin Lebanon, tabbatacce zan maishe ki hamada, kamar garuruwan da ba mazauna. Zan aika da mai hallakarwa a kanki, kowane mutum da makamansa, za su kuma yayyanka gumaguman al’ul na ki masu kyau su jefa su cikin wuta. “Mutane daga al’ummai da yawa za su ratsa cikin wannan birni su kuma tambayi juna suna cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’ Amsar kuwa za tă zama, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada suka kuma bauta wa waɗansu alloli.’ ” Kada ku yi kuka domin sarkin da ya mutu ko ku yi makoki saboda rashinsa; a maimako, ku yi kuka mai zafi saboda wanda aka kai zaman bauta, domin ba zai ƙara dawowa ba ko ya ƙara ganin ƙasarsa ta haihuwa. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shallum22.11 A kan kuma kira shi Yehoyahaz ɗan Yosiya, wanda ya gāji mahaifinsa a matsayin sarkin Yahuda amma bai bar wurin nan ba, “Ba zai ƙara dawowa ba. Zai mutu a inda suka kai shi zaman bauta; ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.” “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya, yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza ba ya biyansu wahalarsu. Yana cewa, ‘Zan gina wa kaina babban fada da manyan ɗakuna.’ Ta haka sai ya yi musu manyan tagogi ya manne musu al’ul ya yi musu ado kuma da ruwan ja. “Wannan zai mai da kai sarki ne in kana da al’ul a kai a kai? Mahaifinka bai kasance da abinci da abin sha ba? Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai saboda haka kome ya kasance da lafiya da shi. Ya kāre muradin matalauta da mabukata, ta haka kome ya tafi masa daidai. Ba abin da ake nufi da ba san ni ke nan ba?” In ji Ubangiji. “Amma idanunka da zuciyarka sun kahu kawai a kan ƙazamar riba, da a kan zub da jinin marar laifi da kuma a kan danniya da zalunci.” Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, “Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’ Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’ Za a binne shi kamar jaki za a ja shi a ƙasa a jefar a bayan ƙofofin Urushalima.” “Ka haura zuwa Lebanon ka yi kuka, bari a ji muryarka a Bashan, yi kuka daga Abarim, gama an murƙushe dukan abokanka. Na ja maka kunne sa’ad da kake zama lafiya, amma sai ka ce, ‘Ba zan saurara ba!’ Wannan halinka ne tun kana matashi; ba ka yi mini biyayya ba. Iska za tă koro dukan makiyayanka abokanka kuma za su tafi zaman bauta. Sa’an nan za ka sha kunya a kuma walaƙanta ka saboda dukan muguntarka. Kai da kake zama a ‘Lebanon,’22.23 Wato, fada a cikin Urushalima (duba 1Sar 7.2) kai da kake sheƙa a gine-ginen al’ul za ka yi nishi sa’ad da zafi ya auka maka, zafi kamar na mace mai naƙuda! “Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “ko kai, Yehohiyacin22.24 Da Ibraniyanci Koniya, wani suna na Yehohiyacin; haka ma a 28. ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda, ka zama zoben hatimin dama a hannuna na dama, zan kwaɓe ka. Zan ba da kai ga waɗanda suke neman ranka, waɗanda kake tsoro, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da kuma ga Babiloniyawa. Zan jefar da kai da mahaifiyar da ta haife ka zuwa wata ƙasa, inda babu ɗayanku da aka haifa a wurin, a can kuma za ka mutu. Ba za ka ƙara dawo ƙasar da kake marmarin dawowa ba.” Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya, abin da babu wanda yake so? Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba? Ya ke ƙasa, ƙasa, ƙasa, ki ji maganar Ubangiji! Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka rabu da wannan mutum sai ka ce marar ’ya’ya, mutumin da ba zai yi nasara a rayuwarsa ba, gama babu zuriyarsa da za tă yi nasara babu wani da zai zauna a kursiyin Dawuda ko ya ƙara yin mulkin Yahuda.” Reshen adalci “Kaiton makiyayan da suka hallakar suka kuma warwatsar da tumakin makiyayanta!” In ji Ubangiji. Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana ce wa makiyayan da suke lura da mutanena, “Domin kun watsar da garkena kuka kuma kore su ba ku kuma lura da su ba, zan kawo hukunci a kanku saboda muguntar da kuka yi,” in ji Ubangiji. “Ni kaina zan tattara raguwar garkena daga ƙasashen da na kore su zuwa zan kuma dawo da su ga makiyayansu, inda za su yi ta haihuwa su riɓaɓɓanya. Zan sa makiyaya a kansu waɗanda za su lura da su, ba za su ƙara jin tsoro ko razana ba, ba kuwa waninsu da zai ɓace,” in ji Ubangiji. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan tā da wa Dawuda23.5 Ko kuwa tā da daga zuriyar Dawuda Reshen adalci, Sarki wanda zai yi mulki da hikima ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar. A cikin zamaninsa za a ceci Yahuda Isra’ila kuma zai zauna lafiya. Sunan da za a kira shi ke nan, Ubangiji Adalcinmu. “Saboda haka fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da mutanen ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da Isra’ila daga Masar ba,’ amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da zuriyar Isra’ila daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashen da ya yashe su.’ Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu.” Annabawa masu ƙarya Game da annabawa kuwa, Zuciyata ta karai; dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa. Na zama kamar wanda ya bugu, kamar mutumin da ruwan inabi ya sha kansa, saboda Ubangiji da kuma maganarsa mai tsarki. Ƙasar ta cika da mazinata; saboda la’ana23.10 Ko kuwa saboda waɗannan abubuwa ƙasar ta zama kango23.10 Ko kuwa ƙasar yana kuka makiyaya a hamada ta bushe. Annabawa suna bin mugayen muradu suna kuma amfani da ƙarfinsu a hanyar marar kyau. “Annabi da firist dukansu biyu marasa sanin Allah ne; har ma a cikin haikalina na tarar da muguntarsu,” in ji Ubangiji. “Saboda haka hanyarsu za tă yi santsi; za a jefar da su cikin duhu a can kuwa za su fāɗi. Zan kawo musu masifa a shekarar da za a hukunta su,” in ji Ubangiji. “A cikin annabawan Samariya na ga wannan abin banƙyama. Suna annabci ta wurin Ba’al suna ɓad da mutanena Isra’ila. A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.” Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da annabawa, “Zan sa su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwa mai dafi, domin daga annabawan Urushalima rashin sani Allah ya bazu ko’ina a ƙasar.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Kada ku saurari abin da annabawan suke muku annabci; suna cika ku da sa zuciyar ƙarya. Suna maganar wahayi daga tunaninsu, ba daga bakin Ubangiji ba. Suna cin gaba da ce wa waɗanda suka rena ni, Ubangiji ya ce za ku zauna lafiya.’ Ga duka waɗanda suke bin taurin zukatansu kuwa sukan ce, ‘Babu lahanin da zai same ku.’ Amma wane ne a cikinsu ya taɓa tsaya a majalisar Ubangiji yă ga ko ya ji maganarsa? Wa ya saurari ya kuma ji maganarsa? Ga shi, hadarin Ubangiji zai taso cikin hasala guguwa tana kaɗawa a kan kawunan mugaye. Fushin Ubangiji ba zai kau ba sai ya aikata nufin zuciyarsa. A kwanakin masu zuwa za ku gane sarai. Ban aiki waɗannan annabawa ba, duk da haka sun tafi da saƙonsu; ban yi musu magana ba, duk da haka sun yi annabci. Amma da a ce sun tsaya a majalisata, da sun yi shelar maganata ga mutanena sun kuma juyar da su daga mugayen hanyoyinsu da kuma daga mugayen ayyukansu. “Ni ɗin Allah na kusa ne kawai,” in ji Ubangiji, “ba Allah na nesa ba? Akwai wanda zai iya ɓuya a lungu har da ba zan iya ganinsa ba?” In ji Ubangiji “Ban cika sama da ƙasa ba?” In ji Ubangiji. “Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’ Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu? Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada. Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji. “Maganata ba wuta ba ce,” in ji Ubangiji, “kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse? “Saboda haka,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke satar maganganuna daga juna. I,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke kaɗa harsunansu sa’an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya furta.’ Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji. “Sa’ad da waɗannan mutane, ko annabi ko firist, ya tambaye ka, ‘Mece ce maganar23.33 Ko kuwa nawaya (dubi Seftuwajin da Bulget) Ubangiji?’ Ka ce musu, ‘Wace magana?23.33 Da Ibraniyanci; Seftuwajin da Bulget Ku ne nawayar. (Ibraniyanci na faɗar Ubangiji da nawaya sun yi kama da juna.) Zan yashe ku, in ji Ubangiji.’ In annabi ko firist ko da wani dabam ya ce, ‘Wannan ne abin da Ubangiji yake cewa,’ zan hukunta wannan mutum da kuma gidansa. Ga abin da kowannenku yana cin gaba da ce wa abokinsa ko danginsa, ‘Mece ce amsar Ubangiji?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’ Amma kada ku ƙara ambatar ‘maganar Ubangiji’ domin kowace maganar mutum kan zama maganarsa. Ta haka kukan lalace maganar Allah mai rai, Ubangiji Maɗaukaki, Allahnmu. Ga abin da za ku ci gaba da faɗa wa annabi, ‘Mece ce amsar Ubangiji gare ka?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’ Ko da yake kuna cewa, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ga abin da Ubangiji yana cewa kuna amfani da kalmomi, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ko da yake na ce muku kada ku ce, ‘Wannan ce maganar Ubangiji.’ Saboda haka, tabbatacce zan manta da ku in kuma jefar da ku daga gabana tare da birnin da na ba ku da kuma kakanninku. Zan kawo muku madawwamiyar kunya, kunya ta har abada wadda ba za a taɓa manta ba.” Kwanduna biyu na ’ya’yan ɓaure Bayan Nebukadnezzar ya kwashi Yekoniya24.1 Da Ibraniyanci Yekoniya, wani suna na Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da fadawa, da masu sana’a da masu zane zanen Yahuda daga Urushalima zuwa Babilon zaman bauta, Ubangiji ya nuna mini kwanduna biyu na ’ya’yan ɓaure ajiye a gaban haikalin Ubangiji. Kwando guda yana da ’ya’yan ɓaure masu kyau sosai, kamar waɗanda suka nuna da wuri; ɗayan kwandon kuma yana da ’ya’yan ɓaure marasa kyau, sun yi muni har ba a iya ci. Sa’an nan Ubangiji ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani, Irmiya?” Na ce, “’Ya’yan ɓaure. Masu kyau ɗin suna da kyau sosai, amma munanan sun yi muni har ba a iya ci.” Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar ’ya’yan ɓauren nan masu kyau, haka zan kula da mutanen Yahuda waɗanda aka kwaso waɗanda na fisshe su daga wannan wuri zuwa ƙasar Babiloniyawa24.5 Ko kuwa Kaldiyawa Idanuna za su kula da su don kyautatawarsu, zan kuma komo da su wannan ƙasa. Zan gina su ba zan rushe su ba; zan dasa su ba kuwa zan tumɓuke su ba. Zan ba su zuciya don su san ni, cewa ni ne Ubangiji. Za su zama mutanena, zan zama Allahnsu, gama za su komo gare ni da dukan zuciyarsu. “ ‘Amma kamar ’ya’yan ɓauren nan marasa kyau, waɗanda sun yi muni har ba a iya ci,’ in ji Ubangiji, ‘haka zan yi da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da sauran mutanen da suka tsira a Urushalima, ko suna a wannan ƙasa ko suna zama a Masar. Zan mai da su abin ƙyama da masifa ga dukan mulkokin duniya, abin zargi da abin karin magana, abin ba’a da abin la’ana a duk inda zan kore su zuwa. Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu sai an hallaka su sarai daga ƙasar da na ba su da kuma kakanninsu.’ ” Shekaru saba’in na zaman bauta Magana ta zo wa Irmiya game da dukan mutanen Yahuda a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wadda ta kasance shekara ta fari ta Nebukadnezzar sarkin Babilon. Saboda haka Irmiya annabi ya ce wa dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima. Shekaru ashirin da uku, daga shekara ta goma sha uku ta Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda har zuwa wannan rana, maganar Ubangiji ta zo mini na kuma yi muku magana sau da sau, amma ba ku saurara ba. Ko da yake Ubangiji ya aika dukan bayinsa annabawa gare ku sau da sau, ba ku saurara ba, ba ku kuma kula ba. Sun ce, “Ku juye yanzu, kowannenku, daga mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa iya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku da kuma kakanninku har abada abadin. Kada ku bi waɗansu alloli don ku bauta ku kuma yi musu sujada; kada ku tsokane ni in yi fushi da abin da hannuwanku suka yi. Sa’an nan ba zan kawo muku lahani ba.” “Amma ba ku saurare ni ba,” in ji Ubangiji, “kun tsokane ni da abin da kuka yi da hannuwanku, kuka kuma kawo lahani wa kanku.” Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Domin kun ƙi ku saurara ga maganata, zan kira dukan mutanen arewa da bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon,” in ji Ubangiji, “zan kuma kawo su su yi gāba da wannan ƙasa da mazaunanta da kuma gāba da dukan al’ummai da suke kewaye. Zan hallaka su sarai in kuma mai da su abin bantsoro da abin dariya, za su kuma zama kufai har abada. Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila. Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in. “Amma sa’ad da shekaru saba’in ɗin suka cika, zan hukunta sarkin Babilon da kuma al’ummarsa, ƙasar Babiloniyawa, saboda laifinsu,” in ji Ubangiji, “in kuma mai da ita kango har abada. Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abubuwan na yi magana a kanta, dukan abubuwan da aka rubuta a wannan littafi, abubuwan da Irmiya kuma ya yi annabci a kan dukan al’ummai. Su kansu al’ummai da sarakuna masu yawa za su bautar da su; zan sāka musu bisa ga ayyukansu da aikin hannuwansu.” Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa mini, “Ka karɓi kwaf ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha. Sa’ad da suka sha, za su yi ta tangaɗi su kuma yi hauka saboda takobin da zan aika a cikinsu.” Saboda haka na karɓi kwaf daga hannun Ubangiji na sa dukan al’ummai waɗanda ya aiko ni wurinsu su sha. Urushalima da garuruwan Yahuda, sarakunan da fadawanta, don su mai da su kufai da kuma abin bantsoro da ba’a da la’ana, yadda suke a yau; Fir’auna sarkin Masar, ma’aikatansa, fadawansa da dukan mutanensa, da dukan baƙin da suke can; dukan sarakunan Uz; dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod); Edom, Mowab da Ammon; dukan sarakunan Taya da Sidon; sarakunan bakin teku a ƙetaren teku; Dedan, Tema, Buz da dukan waɗanda suke a manisantan wurare; dukan sarakunan Arabiya da dukan sarakunan baƙin da suke zama a hamada; dukan sarakunan Zimri, Elam da Mediya; da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya. Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha. “Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’ Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha! Ga shi, na sa masifa tă yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana, kuna gani za ku tafi ba hukunci? Ba za ku tafi ba hukunci ba, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’ “Yanzu ka yi annabcin dukan waɗannan maganganu a kansu ka kuma ce musu, “ ‘Ubangiji zai yi ruri daga bisa; zai yi tsawa daga mazauninsa mai tsarki ya kuma yi ruri da ƙarfi a kan ƙasarsa. Zai yi ihu kamar waɗanda suke matsin ’ya’yan inabi, yi ihu a kan dukan waɗanda suke zaune a duniya. Hayaniya za tă taso har iyakar duniya, gama Ubangiji zai kawo tuhume-tuhume a kan al’ummai; zai kawo shari’a a kan dukan ’yan adam ya kuma kashe mugaye da takobi,’ ” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Duba! Masifa tana yaɗuwa daga al’umma zuwa al’umma; hadari mai girma yana tasowa daga iyakar duniya.” A lokacin waɗanda Ubangiji ya kashe za su kasance a ko’ina, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi kuka dominsu, ba za a tattara su don a binne ba, amma za su zama kamar juji da an tsiba a ƙasa. Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya; ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke. Gama lokacin da za a yanka ku ya zo; za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau. Makiyaya ba za su sami wurin da za su gudu su tafi ba, shugabannin garke ba za su sami wurin kuɓuta ba. Ji kukan makiyaya, kururuwan shugabannin garke, gama Ubangiji yana hallaka wurin kiwo. Rafi mai gudu a hankali zai zama kango saboda zafin fushin Ubangiji. Kamar zaki zai bar wurin ɓuyarsa, ƙasarsu kuma za tă zama kufai saboda takobin masu danniya da kuma saboda zafin fushin Ubangiji. An yi wa Irmiya barazanar mutuwa (Irmiya 7.1-15) A farkon sarautar Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo daga wurin Ubangiji, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka tsaya a filin gidan Ubangiji ka kuma yi magana ga dukan mutanen garuruwan Yahuda waɗanda suka zo sujada a gidan Ubangiji. Ka faɗa musu kome da na umarce ka; kada ka bar wata magana. Wataƙila su saurara kowanne kuma ya juyo daga mugun hanyarsa. Sa’an nan in yi juyayi in kuma janye masifar da nake shirin kawo a kansu saboda muguntar da suka aikata. Ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, in ba ku saurare ni, ku kuma bi dokata, wadda na sa a gabanku ba, in kuma ba ku saurari maganganun bayina annabawa, waɗanda na aika muku sau da sau ba (ko da yake ba ku saurara ba), to, sai in mai da gidan nan kamar Shilo, birnin nan kuma abin la’ana a cikin al’umman duniya.’ ” Firistoci, annabawa da dukan mutane suka ji Irmiya yana waɗannan maganganu a gidan Ubangiji. Amma da Irmiya ya gama faɗar wa dukan mutanen abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa, sai firistoci, annabawa da dukan mutane suka kama shi suka ce, “Mutuwa za ka yi! Me ya sa ka yi annabci da sunan Ubangiji cewa wannan gida zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kango da hamada?” Sai duk mutane suka tattaru kewaye da Irmiya a cikin gidan Ubangiji. Da fadawan Yahuda suka ji haka, sai suka haura daga fada zuwa gidan Ubangiji suka zazzauna a wuraren zamansu a mashigin Sabuwar Ƙofar gidan Ubangiji. Sa’an nan firistoci da annabawa suka ce wa fadawan da dukan mutane, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa gama ya yi annabci gāba da wannan birni. Ku kun ji da kunnuwanku!” Sai Irmiya ya ce wa dukan fadawa da kuma dukan mutane, “Ubangiji ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan gida da wannan birni dukan abin da na faɗa. Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku. Game da ni dai, ina a hannuwanku; ku yi duk abin da kuka ga ya yi kyau, ya kuma dace a gare ku. Ku tabbata dai, cewa in kuka kashe ni, za ku jawo wa kanku alhakin jini marar laifi a kanku da a kan birnin nan da kuma a kan masu zama a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.” Sai fadawa da dukan mutane suka ce wa firistoci da annabawa. “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.” Waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka zo gaba suka ce wa dukan taron jama’a, “Mika mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya ce wa dukan mutanen Yahuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “ ‘Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za tă zama tsibin juji, ƙwanƙolin dutsen haikali kuwa zai zama kurmi.’26.18 Mik 3.12 “Hezekiya sarkin Yahuda ko kuwa wani a Yahuda ya kashe shi? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji ya nemi tagomashinsa ba? Ubangiji kuwa bai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kansu ba? Muna gab da jawo wa kanmu muguwar masifa!” (To, fa, Uriya ɗan Shemahiya daga Kiriyat Yeyarim wani mutum ne wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji; ya yi annabci irin abu ɗaya gāba da wannan birni da wannan ƙasa yadda Irmiya ya yi. Da sarki Yehohiyakim da dukan fadawansa da ma’aikatansa suka ji wannan magana, sai sarki ya nemi a kashe shi. Amma Uriya ya ji wannan shiri sai ya gudu zuwa Masar don tsoro. Sarki Yehohiyakim ya aiki Elnatan ɗan Akbor zuwa Masar, tare da waɗansu mutane. Suka dawo da Uriya daga Masar suka kawo shi wurin Sarki Yehohiyakim, wanda ya kashe shi da takobi aka kuma jefar da gawarsa a makabartar talakawa.) Bugu da ƙari, Ahikam ɗan Shafan ya goyi bayan Irmiya, saboda haka ba a ba da shi ga mutane don su kashe shi ba. Yahuda ya bauta wa Nebukadnezzar A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji. Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda. Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan. Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama. Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa. Dukan al’ummai za su bauta masa da ɗansa da kuma jikansa har sai har lokacin ƙasarsa ya kai; sa’an nan al’ummai masu yawa da kuma manyan sarakuna za su kasance a ƙarƙashinsa. “ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa. Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’ Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka. Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ” Na ba da wannan saƙo guda ga Zedekiya sarkin Yahuda. Na ce, “Ka rusunar da wuyanka a ƙarƙashin sarkin Babilon; ka bauta masa da kuma mutanensa, za ka kuwa rayu. Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba? Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku. ‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’ ” Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne. Kada ku saurare su. Ku bauta wa sarkin Babilon, za ku kuwa rayu. Don me wannan birni zai zama kufai? In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima, I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa game da abubuwan da aka bari a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da Urushalima, ‘Za a kwashe su zuwa Babilon a can kuwa za su kasance sai ranar da na neme su,’ in ji Ubangiji. ‘Sa’an nan zan komo da su in maido da su wannan wuri.’ ” Hananiya annabin ƙarya A wata na biyar na wannan shekara, shekara ta huɗu, a farkon sarautar Zedekiya sarkin Yahuda, sai annabi Hananiya ɗan Azzur, wanda ya fito daga Gibeyon, ya zo wurina a gidan Ubangiji a gaban firistoci da kuma dukan mutane, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Zan karya karkiyar sarkin Babilon. Cikin shekaru biyu zan komo da dukan kayayyakin gidan Ubangiji da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe daga wannan wuri ya kai Babilon. Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da kuma dukan sauran masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suka tafi Babilon,’ in ji Ubangiji, ‘gama zan karya karkiyar sarkin Babilon.’ ” Sai annabi Irmiya ya amsa wa annabi Hananiya a gaban firistoci da kuma dukan mutane waɗanda suke tsaye a gidan Ubangiji. Ya ce, “Amin! Ubangiji yă sa yă zama haka! Ubangiji yă cika maganar da ka yi annabci ta wurin komo da kayayyakin gidan Ubangiji da kuma dukan masu zaman bauta zuwa wannan wuri daga Babilon. Duk da haka, ka saurari abin da zan faɗa a kunnenka da kuma a kunnen duka mutane, Daga farko fari annabawan da suka riga ka da ni sun yi annabcin yaƙi, masifa da annoba a kan ƙasashe masu yawa da kuma manyan mulkoki. Amma annabin da ya yi annabcin salama shi za a ɗauka a matsayin wanda Ubangiji ya aika in har abin da ya furta ya zama gaskiya.” Sai annabi Hananiya ya cire karkiya daga wuyar annabi Irmiya ya karya ta, ya ce a gaban dukan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘A haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar sarkin Babilon daga wuyan dukan al’ummai a cikin shekaru biyu.’ ” Da wannan, annabi Irmiya ya yi tafiyarsa. Ba a daɗe ba bayan annabi Hananiya ya karya karkiya daga wuyan annabi Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Je ka faɗa wa Hananiya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka karya karkiyar katako, amma a wurinsa za ka sami karkiyar ƙarfe. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa zan sa karkiyar ƙarfe a wuyan dukan waɗannan al’ummai don in sa su bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon, za su kuwa bauta masa. Zan ma sa shi ya mallaki namun jeji.’ ” Sa’an nan annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka saurara, Hananiya! Ubangiji bai aike ka ba, duk da haka ka lallashe wannan al’umma su dogara ga ƙarya. Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Ina shirin kawar da kai daga fuskar duniya. A wannan shekara za ka mutu, domin ka yi wa’azin tawaye a kan Ubangiji.’ ” A wata na bakwai na wannan shekara, annabi Hananiya ya mutu. Wasiƙa zuwa ga masu zaman bauta Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon. (Wannan ya faru bayan Sarki Yekoniya da mahaifiyar sarauniya, shugabannin fada da kuma dukan shugabannin Yahuda da Urushalima, gwanayen sana’a da masu sassaƙa suka tafi zaman bauta daga Urushalima.) Ya ba da wasiƙar ta hannun Eleyasa ɗan Shafan da Gemariya ɗan Hilkiya, waɗanda Zedekiya sarkin Yahuda ya aika wurin Sarki Nebukadnezzar a Babilon. Wasiƙar ta ce, Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ga dukan waɗanda aka kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon. “Ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar. Ku yi aure ku kuma haifi ’ya’ya maza da mata; ku nemi mata wa ’ya’yanku maza, ku kuma ba da ’ya’yanku mata ga aure, saboda su ma za su haifi ’ya’ya maza da mata. Ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu. Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.” I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Kada ku bar annabawa da masu sihiri a cikinku su ruɗe ku. Kada ku saurari mafarkan da dā kuke ƙarfafa su su yi. Suna muku annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri. Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku. Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.” Za ku iya ce, “Ubangiji ya tā da annabawa saboda mu a Babilon.” Amma ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarki, wanda yake zaune a kursiyin Dawuda da kuma dukan mutanen da suka ragu a wannan birni, ’yan’uwanku waɗanda ba su tafi tare da ku zuwa zaman bauta ba. I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu zan kuma sa su zama kamar ɓaure marar amfani da suka yi munin da ba a iya ci. Zan fafare su da takobi, yunwa da annoba zan kuma sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya da kuma abin la’ana da abin bantsoro, abin dariya da abin reni, a cikin dukan al’umman da aka kore su zuwa. Gama ba su saurari maganata ba,” in ji Ubangiji, “maganar da na aika gare su sau da sau ta bayina annabawa. Ku kuma masu zaman bauta ba ku saurara ba,” in ji Ubangiji. Saboda haka, ku ji maganar Ubangiji, dukanku masu zaman bauta waɗanda na aika daga Urushalima zuwa Babilon. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa game da Ahab ɗan Kolahiya da Zedekiya ɗan Ma’asehiya, waɗanda suke muku annabcin ƙarya da sunana. “Zan ba da su ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai kuwa kashe su a gaban idanunku. Saboda su, dukan masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suke a Babilon za su yi amfani da wannan la’ana cewa, ‘Ubangiji ka yi da mu kamar Zedekiya da Ahab waɗanda sarkin Babilon ya ƙone da wuta.’ Gama sun aikata munanan abubuwa a Isra’ila; sun yi zina da matan maƙwabtansu kuma da sunana suka yi ƙarya, waɗanda ban faɗa musu su yi ba. Na san wannan kuma ni shaida ne ga haka,” in ji Ubangiji. Saƙo ga Shemahiya Faɗa wa Shemahiya mutumin Nehelam, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka aika da wasiƙu da sunanka ga dukan mutane a Urushalima, zuwa ga Zefaniya ɗan Ma’asehiya firist da kuma ga sauran firistoci. Ka ce wa Zefaniya, Ubangiji ya naɗa ka firist a wurin Yehohiyada don ka lura da gidan Ubangiji; ya kamata ka sa kowane mahaukaci wanda yake yi kamar annabi cikin turu da kuma a kangi. To, me ya sa ba ka tsawata wa Irmiya daga Anatot, wanda yana ɗauka kansa annabi a cikinku ba? Ya aiko mana da saƙonsa a Babilon cewa zai ɗauki lokaci ƙwarai. Saboda haka ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar.’ ” Zefaniya firist kuwa, ya karanta wasiƙar annabi Irmiya. Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ka aika da wannan saƙo zuwa ga dukan masu zaman bauta cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa game da Shemahiya, mutumin Nehelam. Domin Shemahiya ya yi muku annabci, ko da yake ban aike shi ba, ya kuma sa kuka gaskata ƙarya, ga abin da Ubangiji yana cewa, tabbatacce zan hukunta Shemahiya mutumin Nehelam da zuriyarsa. Ba zai kasance da wani da ya rage a cikin wannan mutane ba, ba kuwa zai ga abubuwa alherin da zan yi wa mutanena ba, in ji Ubangiji, domin ya yi wa’azin tawaye a kaina.’ ” Maidowa da Isra’ila Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ka rubuta a cikin littafi dukan maganganun da na yi maka. Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan komo da mutanena Isra’ila da Yahuda daga bauta in kuma maido da su ga ƙasar da na ba wa kakanninsu mallaka,’ in ji Ubangiji.” Ga kalmomin Ubangiji da ya yi game da Isra’ila da Yahuda, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ana jin kukan tsoro, razana, ba salama ba. Ku tambaya ku ji. Namiji zai iya haifi ’ya’ya? To, me ya sa kuke ganin kowane mai ƙarfi da hannuwansa a kwankwaso kamar mace mai naƙuda, kowace fuska ta koma fari? Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma! Babu kamar ta. Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub, amma za a cece shi daga cikinta. “ ‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan karya karkiya daga wuyansu zan kuma cire musu kangi; baƙi ba za su ƙara bautar da su ba. A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji Allahnsu Dawuda sarkinsu kuwa, wanda na tayar musu. “ ‘Saboda haka kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila,’ in ji Ubangiji. ‘Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nesa, zuriyarka daga ƙasar zaman bautansu. Yaƙub zai sami salama da zaman lafiya, kuma ba wanda zai sa ya ji tsoro. Ina tare da kai zan kuma cece ka,’ in ji Ubangiji. ‘Ko da yake na hallakar da dukan al’umma gaba ɗaya a inda na warwatsa ku, ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba. Zan hore ku amma da adalci kaɗai; ba zan ƙyale ku ku tafi gaba ɗaya ba hukunci ba.’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Mikinku marar warkewa ne, raunin da kuka ji ya sha ƙarfin warkarwa. Babu wanda zai yi roƙo saboda damuwarku, ba magani domin mikinku babu warkarwa dominku. Dukan abokanku sun manta da ku; ba su ƙara kulawa da ku. Na buge ku kamar yadda abokin gāba zai yi na kuma hukunta ku yadda mai mugunta zai yi, domin laifinku da girma yake zunubanku kuma da yawa suke. Me ya sa kuke kuka a kan mikinku, wahalarku da ba ta da magani? Domin laifinku da girma yake da kuma zunubanku masu yawa na yi muku waɗannan abubuwa. “ ‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi; dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta. Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su; dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima. Amma zan mayar muku da lafiya in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji, ‘domin ana ce da ku yasassu, Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub in kuma ji tausayin wuraren zamansa; za a sāke gina birnin a kufansa, fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita. Daga gare su waƙoƙi za su fito na godiya da kuma sowa ta farin ciki. Zan riɓaɓɓanya su, ba za su kuwa ragu ba; zan kawo musu ɗaukaka, ba kuwa za a ƙasƙanta su ba. ’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dā jama’arsu kuma za su kahu a gabana; zan hukunta duk wanda ya zalunce su. Shugabansu zai zama ɗaya daga cikinsu; mai mulkinsu zai taso daga cikinsu. Zan kawo shi kusa zai kuma zo kusa da ni, gama wane ne zai miƙa kansa don yă yi kusa da ni?’ In ji Ubangiji. ‘Saboda haka za ku zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnku.’ ” Ga shi, hadarin Ubangiji zai fasu cikin hasala, iskar guguwa mai hurawa a kan kawunan mugaye. Fushi mai zafi na Ubangiji ba zai kawu ba sai ya cika manufofin zuciyarsa gaba ɗaya. A kwanaki masu zuwa za ku gane wannan. “A lokacin nan, zan zama Allah na dukan kabilan Isra’ila, za su kuma zama mutanena,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Mutanen da suka tsere wa takobi za su sami tagomashi a hamada; zan zo don in ba da hutu ga Isra’ila.” Ubangiji ya bayyana mana a dā,31.3 Ko kuwa Ubangiji ya bayyana mana tun daga nesa yana cewa, “Na ƙaunace ku da madawwamiyar ƙauna; na janye ku da ƙauna marar iyaka. Zan sāke gina ki za ki kuwa sāke ginuwa, ya Budurwar Isra’ila. Za ki kuma ɗauki ganganki ki fita don ki yi rawa da masu farin ciki. Za ki sāke dasa gonakin inabi a kan tussan Samariya; manoma za su yi shuka a kansu su kuma ji daɗin amfaninsu. Za a yi ranar da matsara za su tā da murya a kan tuddan Efraim su ce, ‘Ku zo, bari mu haura Sihiyona, zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku rera don farin ciki wa Yaƙub; ku yi sowa don al’ummai da suke nesa. Ka sa a ji yabanku, ku kuma ce, ‘Ya Ubangiji ka ceci mutanenka, raguwar Isra’ila.’ Ga shi, zan kawo su daga ƙasar arewa in tattara su daga iyakar duniya. A cikinsu makafi da guragu za su kasance, mata masu ciki da matan da suke naƙuda; jama’a mai yawan gaske za su komo. Za su zo da kuka; za su yi addu’a yayinda nake komo da su. Zan bishe su kusa da rafuffukan ruwa a miƙaƙƙiyar hanya inda ba za su yi tuntuɓe ba, domin ni ne mahaifin Isra’ila, Efraim kuma ɗan farina ne. “Ku ji maganar Ubangiji, ya al’ummai; ku yi shelarta a gaban teku masu nesa cewa, ‘Shi wanda ya watsar da Isra’ila zai tattara su zai kuma lura da garkensa kamar makiyayi.’ Gama Ubangiji zai fanshi Yaƙub zai cece su daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi. Za su zo su yi sowa don farin ciki a ƙwanƙolin Sihiyona; za su yi farin ciki cikin yalwar Ubangiji hatsi, sabon ruwan inabi da mai, ’ya’yan garken tumaki da na shanu. Za su zama kamar gonar da aka yi wa banruwa, ba za su ƙara yin baƙin ciki ba. ’Yan mata za su yi rawa su kuma yi murna, haka ma samari da tsofaffi. Zan mai da makokinsu farin ciki; zan ta’azantar da su in kuma sa su yi farin ciki a maimakon baƙin ciki. Zan ƙosar da firistoci da yalwa, mutanena kuma za su cika da yalwa,” in ji Ubangiji. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “An ji murya daga Rama, makoki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka domin ’ya’yanta ta kuma ƙi a ta’azantar da ita domin ’ya’yanta ba su.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Hana muryarki kuka da kuma idanunki hawaye, gama za a sāka wa aikinki,” in ji Ubangiji. “Za su komo daga ƙasar abokin gāba. Saboda haka akwai sa zuciya domin nan gaba,” in ji Ubangiji. “’Ya’yanki za su komo ƙasarsu. “Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa, ‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji, na kuwa horu. Ka mayar da ni, zan kuwa dawo, domin kai ne Ubangiji Allahna. Bayan na kauce, sai na tuba; bayan na gane, sai na sunkuyar da kaina. Na ji kunya da ƙasƙanci domin ina ɗauke da kunyar ƙuruciyata.’ Efraim ba ƙaunataccen ɗana ba ne, ɗan da nake jin daɗinsa? Ko da yake sau da dama ina maganar gāba a kansa, duk da haka nakan tuna da shi. Saboda haka zuciyata tana marmarinsa; ina da jinƙai mai girma dominsa,” in ji Ubangiji. “Ki kafa alamun hanya; ki sa shaidun bishewa. Ki lura da babbar hanya da kyau, hanyar da kika bi. Ki komo, ya Budurwar Isra’ila, ki komo zuwa garuruwanki. Har yaushe za ki yi ta yawo, Ya ’ya marar aminci? Ubangiji zai ƙirƙiro sabon abu a duniya mace za tă kewaye31.22 Ko kuwa za tă fita neman; ko za tă kāre namiji.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Sa’ad da na komo da su daga bauta mutane a ƙasar Yahuda da cikin garuruwanta za su sāke yi amfani da waɗannan kalmomi. ‘Ubangiji ya albarkace ka, ya mazauni mai adalci, ya tsarkakan dutse.’ Mutane za su zauna tare a Yahuda da dukan garuruwansa, manoma da waɗanda suke yawo da garkunansu. Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi.” A kan wannan na farka na duba kewaye. Barcina ya yi mini daɗi. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan kafa gidan Isra’ila da gidan Yahuda da ’ya’yan mutane da na dabbobi. Kamar yadda na lura da su don su tumɓuke su kuma rusar, su lalatar, su hallaka su kuma kawo masifa, haka zan lura da su don su gina su kuma dasa,” in ji Ubangiji. “A waɗannan kwanaki mutane ba za su ƙara ce, “ ‘Ubanni suka ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya suka mutu ba.’ A maimako, kowa zai mutu saboda zunubinsa; duk wanda ya ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoransa ne za su mutu. “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda. Ba zai zama kamar alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu ba sa’ad da na kama su da hannu na bishe su daga Masar, domin sun take alkawarina, ko da yake na zama miji a gare su,” in ji Ubangiji. “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba, ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin duk za su san ni, daga ƙaraminsu har zuwa babba,” in ji Ubangiji. “Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya kafa rana don tă yi haske a yini shi da ya sa wata da taurari su yi haske da dare, shi da yake dama teku don raƙuman ruwansa su yi ruri Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. “In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,” in ji Ubangiji, “to, sai zuriyar Isra’ila ta daina zama al’umma a gabana.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In a iya auna sammai a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan saboda dukan abin da suka yi,” in ji Ubangiji. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da za a sāke gina wannan birni domina daga Hasumiyar Hananel zuwa Ƙofar Kusurwa. Ma’auni zai miƙe daga can ya nausa kai tsaye zuwa tudun Gareb sa’an nan ya juya zuwa Gowa. Dukan kwarin da ake zubar da toka da kuma gawawwaki, da dukan lambatun da suke can har zuwa Kwarin Kidron a gabas zuwa kusurwar Ƙofar Doki, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke birnin ko a rushe shi ba.” Irmiya ya sayi fili Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji a shekara ta goma ta Zedekiya sarkin Yahuda, wanda ya kasance shekara ta goma sha takwas ta Nebukadnezzar. Sojojin sarkin Babilon a lokacin suna ƙawanya wa Urushalima annabi Irmiya kuwa yana a tsare a sansanin matsara a fadar Yahuda. Zedekiya sarkin Yahuda fa ya sa shi a kurkuku yana cewa, “Don me kake yin annabci? Ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga sarkin Babilon, zai kuwa cinye ta. Zedekiya sarkin Yahuda ba zai kuɓuta daga hannuwan Babiloniyawa32.4 Ko kuwa Kaldiyawa; haka ma a ayoyi 5, 24, 25, 28, 29 da 43 ba amma tabbatacce za a ba da shi ga sarkin Babilon, zai kuwa yi masa magana fuska da fuska ya kuma gan shi da idanunsa. Zai kai Zedekiya Babilon, inda zai zauna har sai ya magance shi, in ji Ubangiji. In ka yi yaƙi da Babiloniyawa, ba za ka yi nasara ba.’ ” Irmiya ya ce, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, Hananel ɗan Shallum ɗan’uwan mahaifinka zai zo wurinka ya ce, ‘Saya filina a Anatot, domin a matsayinka na dangi na kurkusa hakkinka ne kuma kai ya wajaba ka saye shi.’ “Sa’an nan, kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa, sai ga Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina ya zo wurina a sansanin matsara ya ce, ‘Saya filina a Anatot a yankin Benyamin. Da yake hakkinka ne ka fanshe shi ka kuma mallake shi, ka sayo shi wa kanka.’ “Sai na gane cewa wannan maganar Ubangiji ce; saboda haka sai na saye filin a Anatot daga hannun Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina na kuma auna masa shekel goma sha bakwai na azurfa. Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna shekel a ma’auni. Na ɗauki takardar ciniki, takardar da aka rubuta sharuɗan a ciki, da kuma takardar da ba a liƙe ba, na kuma ba wa Baruk ɗan Neriya, ɗan Masehiya, wannan takarda a gaban Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina da kuma a gaban shaidun da suka sa hannu a takardan ciniki da kuma a gaban dukan Yahudawan da suke zaune a sansanin matsaran. “A gabansu na yi wa Baruk waɗannan umarnai cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka ɗauki waɗannan takardun ciniki, wanda aka liƙe da wanda ba a liƙe ba, ka sa su a cikin tulun yumɓu don kada su lalace. Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa za a sāke saye gidaje, filaye da gonakin inabi a wannan ƙasa.’ “Bayan na ba da takardun ciniki ga Baruk ɗan Neriya, sai na yi addu’a ga Ubangiji na ce, “A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka. Kakan nuna ƙauna ga dubbai amma kakan hukunta ’ya’ya saboda laifin ubanninsu a bayansu. Ya mai girma da kuma Allah mai iko, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki, manufofinka da girma suke, ayyukanka kuma masu girma ne. Idanunka suna a buɗe ga dukan hanyoyin mutane; kakan sāka wa kowa gwargwadon halinsa yadda ya dace. Ka aikata ayyukan banmamaki da kuma al’ajabai a Masar ka kuma ci gaba da su har yă zuwa yau, a Isra’ila da kuma a cikin dukan ’yan adam, ka kuma sami sunan da har yanzu yake naka. Ka fitar da mutanenka Isra’ila daga Masar da alamu da abubuwa banmamaki, ta wurin hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi tare da banrazana mai girma. Ka ba su wannan ƙasa da ka rantse za ka ba wa kakanni kakanninsu, ƙasa mai zub da madara da zuma. Suka shiga suka mallake ta, amma ba su yi maka biyayya ba, ba su kuma bi dokarka ba; ba su yi abin da ka umarce su ba. Saboda haka ka kawo masifa a kansu. “Duba yadda aka gina mahaurai don a kame birni. Saboda takobi, yunwa da annoba, za a ba da birnin ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye shi da yaƙi. Abin da ka faɗa ya faru, yadda kake gani yanzu. Ko da yake za a ba da birnin ga Babiloniyawa, kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka ce mini, ‘Saye fili da azurfa ka kuma sa a shaida cinikin.’ ” Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ni ne Ubangiji Allah na dukan ’yan adam. Akwai wani abin da ya gagare ni? Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga Babiloniyawa da kuma ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, wanda zai yaƙe ta. Babiloniyawan da suke yaƙi da wannan birni za su zo ciki su cinna masa wuta; tare da gidaje inda mutane suka tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙona turare a rufin ɗakuna wa Ba’al suka zub da hadayun sha wa waɗansu alloli. “Mutanen Isra’ila da na Yahuda ba abin da suka yi sai mugunta a gabana daga ƙuruciyarsu; tabbatacce, mutanen Isra’ila ba su yi kome ba sai dai tsokane ni da abin da hannuwansu suka yi, in ji Ubangiji. Daga ranar da aka gina ta har zuwa yanzu, wannan birni ta tā da fushina da hasalata da dole a kawar da ita daga gabana. Mutanen Isra’ila da na Yahuda sun tsokane ni ta wurin dukan muguntar da suka aikata su, sarakunansu da fadawansu, firistocinsu da annabawa, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima. Sun juya mini bayansu ba fuskokinsu ba; ko da yake na koyar da su sau da sau, ba su saurara ko bi horo na ba. Sun kafa gumakansu na banƙyama a cikin haikalina wanda ake kira da sunana, sun kuwa ƙazantar da shi. Sun gina masujadai kan tudu wa Ba’al a Kwarin Ben Hinnom don su miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ga Molek, ko da yake ban taɓa umarce su ba, bai kuma zo mini cewa su yi abin banƙyama irin wannan ba ta haka suka sa Yahuda ya yi zunubi. “Kana cewa game da wannan birni, ‘Ta wurin takobi, yunwa da annoba za a ba da shi ga sarkin Babilon’; amma ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa tabbatacce zan tattara su daga dukan ƙasashen da na kore su zuwa cikin fushina da hasalata mai girma; zan komo da su wurin nan in sa su zauna lafiya. Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu. Zan ba su zuciya ɗaya da aiki ɗaya, don kullum su ji tsorona domin amfaninsu da kuma amfanin ’ya’yansu a bayansu. Zan yi madawwamin alkawari da su. Ba zan taɓa barin aikata musu alheri ba, zan kuma iza su su ji tsorona, don kada su ƙara juya daga gare ni. Zan yi farin ciki a yin musu alheri, tabbatacce zan su dasa a wannan ƙasa da dukan zuciyata da dukan raina. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, yadda na kawo dukan wannan masifa a kan wannan mutane, haka zan ba su wadatar da na yi musu alkawari. Za a sāke sayi filaye a wannan ƙasa da kuka ce, ‘Kango ce, ba mutane ko dabbobi, gama an ba da ita ga Babiloniyawa.’ Za a sayi filaye da azurfa, a kuma sa hannu a takardan ciniki, a liƙe a kuma shaida a yankin Benyamin, a ƙauyukan kewayen Urushalima, a garuruwan Yahuda da kuma a garuruwan ƙasar tudu, na yammancin gindin dutse da na Negeb, domin zan maido da wadatarsu, in ji Ubangiji.” Alkawarin Maidowa Yayinda Irmiya yana a tsare a sansanin matsara, sai maganar Ubangiji ta zo masa sau na biyu cewa, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci duniya, Ubangiji wanda ya siffanta ta ya kuma kafa ta, Ubangiji ne sunansa. ‘Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.’ Gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa game da gidaje a wannan birni da fadodin Yahuda da aka rurrushe domin a yi amfani da su a kan mahaurai da kuma takobi a yaƙi da Babiloniyawa. ‘Za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata. Zan ɓoye fuskata wa wannan birni saboda dukan muguntarsu. “ ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya. Zan komo da Yahuda da Isra’ila daga bauta zan kuma sāke gina su kamar yadda suke a dā. Zan tsarkake su daga dukan zunubin da suka yi mini zan kuma gafarta musu dukan zunubansu na yin mini tawaye. Sa’an nan birnin nan za tă sa in zama sananne, farin ciki, yabo da girma a gaban dukan al’ummai a duniya da suka ji abubuwa masu kyau da na yi mata; za su kuma yi mamaki su kuma yi rawan jiki saboda yalwar wadata da salamar da na ba ta.’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Kuna cewa game da wannan wuri, “Kango ne, babu mutane ko dabbobi.” Duk da haka a cikin garuruwan Yahuda da titunan Urushalima da aka yashe, inda ba mutane ko dabbobi, za a sāke jin sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘A wannan wuri, kango da babu mutane ko dabbobi, cikin dukan garuruwansa za a sāke kasance da wurin kiwo don makiyaya su hutar da garkunansu. A cikin garuruwan ƙasar tudu, garuruwan yammancin gindin dutse da na Negeb, a yankin Benyamin, a cikin ƙauyuka kewayen Urushalima da kuma a cikin garuruwan Yahuda, garkuna za su sāke bi a ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,’ in ji Ubangiji. “ ‘Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan cika alkawarin alheri da na yi wa gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda. “ ‘A waɗannan kwanaki da kuma a wannan lokaci zan tā da Reshe mai adalci daga zuriyar Dawuda; zai yi abin da yake daidai da kuma gaskiya a ƙasar. A kwanakin nan zan ceci Yahuda Urushalima kuma za tă zauna lafiya. Sunan da za a kira ta shi ne, Ubangiji Adalcinmu.’ Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra’ila ba, ba kuwa firistoci waɗanda suke Lawiyawa za su rasa mutumin da zai ci gaba da tsaya a gabana don miƙa hadayun ƙonawa, ya ƙona hadayun hatsi ya kuma miƙa sadakoki ba.’ ” Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ka tā da alkawarina na rana da kuma alkawarina na dare, har dare da rana ba za su ƙara bayyana a ƙayyadaddun lokutansu ba, to, sai a tā da alkawarina da Dawuda bawana da alkawarina da Lawiyawan da suke firistoci masu hidima a gabana, Dawuda kuma ba zai ƙara kasance da zuriyar da za tă yi mulki. Zan sa zuriyar Dawuda bawana da kuma Lawiyawan da suke hidima a gabana su yi yawa kamar taurarin sararin sama da kuma yashin bakin tekun da ba a iya ƙidaya.’ ” Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ba ka lura ba cewa waɗannan mutane suna cewa, ‘Ubangiji ya ƙi masarautai33.24 Ko kuwa iyalai biyu da ya zaɓa’? Saboda haka suka rena mutanena ba sa ƙara ɗaukansu a matsayin al’umma. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ban kafa alkawarina game da rana da kuma game da dare ba in kuma gyara dokokin sama da duniya ba, to zan ƙi zuriyar Yaƙub da na Dawuda bawana ba zan kuma zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza ya yi mulki a kan zuriyar Ibrahim, Ishaku da Yaƙub ba. Gama zan mayar da wadatarsu33.26 Ko kuwa zan komo da su daga bauta in kuma yi musu jinƙai.’ ” Gargaɗi ga Zedekiya Yayinda Nebukadnezzar sarkin Babilon da dukan sojojinsa da kuma dukan mulkokinsa da mutanen masarautar da yake mulki suna yaƙi da Urushalima da dukan garuruwan da suke kewaye, sai wannan magana ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi wurin Zedekiya sarkin Yahuda ka faɗa masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga sarkin Babilon, zai kuwa ƙone ta. Ba za ka tsere daga hannunsa ba amma tabbatacce za a kama ka a kuma ba da kai gare shi. Za ka ga sarkin Babilon da idanunka, zai kuwa yi magana da kai fuska da fuska. Za ka kuwa tafi Babilon. “ ‘Duk da haka ka ji alkawarin Ubangiji, ya Zedekiya sarkin Yahuda. Ga abin da Ubangiji yake cewa game da kai. Ba za ka mutu ta takobi ba; za ka mutu cikin salama. Yadda mutane suka ƙuna wutar jana’iza don girmama kakanninka, sarakunan da suka riga ka, haka za su ƙuna wuta don girmama da kuma makokinka suna cewa, “Kaito, ya maigida!” Ni kaina na yi wannan alkawari, in ji Ubangiji.’ ” Sa’an nan annabi Irmiya ya faɗi dukan wannan wa Zedekiya sarkin Yahuda, a Urushalima, yayinda sojojin sarkin Babilon suna yaƙi da Urushalima da sauran garuruwan Yahuda waɗanda suka ragu, Lakish da Azeka. Waɗannan su ne birane masu katanga kaɗai a Yahuda. Maganar ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Sarki Zedekiya ya yi yarjejjeniya da duka mutane a Urushalima ya yi shelar ’yanci wa bayi. Kowa ya ’yantar da bayinsa da suke Ibraniyawa, maza da mata; kada kowa ya riƙe bawa wanda yake mutumin Yahuda. Saboda haka dukan fadawa da mutane suka yi yarjejjeniyar cewa za su ’yantar da bayinsu maza da mata ba za su kuwa ƙara riƙe su bayi ba. Suka yarda, suka kuma sake su. Amma daga baya suka canja ra’ayoyinsu suka maido bayinsu suka kuma sāke bautar da su. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa na yi alkawari da kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga ƙasar bauta. Na ce, ‘A kowace shekara ta bakwai dole kowannenku yă ’yantar da duk wani ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa wanda aka sayar masa. Bayan ya yi muku hidima shekaru shida, dole ku bar shi yă tafi ’yantacce.’34.14 M Sh 15.12 Amma kakanninku ba su saurare ni ba, ba su ji ni ba. Bai daɗe ba da kuka tuba, kuka kuma yi abin da yake mai kyau a idona. Kowannenku ya yi shelar ’yanci ga ɗan’uwansa. Kun ma yi yarjejjeniya a gabana a gidan da ake kira da Sunana. Amma yanzu kun juya kun kuma ɓata sunana; kowannenku ya mayar da bayi maza da matan da kuka ’yantar su tafi inda suka ga dama. Kun sāke tilasta su su zama bayinku. “Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, kun yi mini rashin biyayya; ba ku yi shelar ’yanci don ’yan’uwanku ba. Saboda haka yanzu na yi muku shelar ’yanci in ji Ubangiji, ’yanci ga mutuwa ta takobi, annoba da kuma yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga sauran mulkokin duniya. Mutanen da suka keta alkawarina da ba su cika sharuɗan alkawarin da suka yi a gabana ba, zan yi da su kamar ɗan maraƙin da suka yanka biyu suka bi ta tsakiyarsa. Shugabannin Yahuda da Urushalima, fadawa, firistoci da kuma dukan mutanen ƙasar waɗanda suka bi tsakanin ɗan maraƙin da aka yanka, zan ba da su ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namun jeji. “Zan ba da Zedekiya sarkin Yahuda da fadawansa ga abokan gābansu waɗanda suke neman ransu, ga sojojin sarkin Babilon, waɗanda suke janye daga gare ku. Zan yi umarni, in ji Ubangiji, zan kuma komo da su wannan birni. Za su kuwa yi yaƙi da ita, su ƙwace ta su kuma ƙone ta. Zan kuma mai da garuruwan Yahuda kufai don kada wani ya zauna a can.” Mutanen Rekab Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji a lokacin mulkin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda. “Ka tafi wurin iyalin Rekabawa ka gayyace su su zo a ɗaya daga cikin ɗakunan da suke gefe a gidan Ubangiji ka kuma ba su ruwan inabi su sha.” Sai na tafi don in kawo Ya’azaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da ’yan’uwansa da kuma dukan ’ya’yansa maza, dukan iyalin Rekabawa. Na kawo su cikin gidan Ubangiji, a cikin ɗakin ’ya’yan Hanan ɗan Igdaliya maza mutumin Allah. Ɗakin ne kusa da ɗakin fadawa, wanda yake bisa na Ma’asehiya ɗan Shallum mai tsaron ƙofa. Sai na ajiye ƙwarya cike da ruwan inabi da waɗansu kwaf a gaban iyalin Rekabawan na kuma ce musu, “Ku sha ruwan inabin.” Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi. Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’ Mun yi biyayya da kome da kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu. Mu ko matanmu ko ’ya’yanmu maza da mata ba mu taɓa shan ruwan inabi ba ba mu kuma gina gidaje mu zauna a ciki ba ko mu yi gonakin inabi, gonaki ko hatsi ba. Mun yi rayuwarmu a cikin tentuna mun kuma yi biyayya ƙwarai da kowane abin da kakanmu Yehonadab ya umarce mu. Amma da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasan nan hari, sai muka ce, ‘Ku zo, dole mu tafi Urushalima don mu tsira daga Babiloniyawa da kuma sojojin Arameyawa.’ Saboda haka ne muke a Urushalima.” Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi ka faɗa wa mutanen Yahuda da kuma mutanen Urushalima cewa, ‘Ba za ku koyi darasi ku kuma yi biyayya da maganata ba?’ In ji Ubangiji. ‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba. Sau da sau na aika dukan bayina annabawa gare ku. Suka ce, “Kowannenku ya juyo daga mugayen hanyoyinsa ya sabunta ayyukansa; kada yă bi waɗansu alloli don yă bauta musu. Ta haka za ku zauna a cikin ƙasar da na ba ku da kuma kakanninku.” Amma ba ku saurara ba, ba ku kuwa ji ni ba. Zuriyar Yehonadab ɗan Rekab sun yi biyayya da umarnin da kakansu ya ba su, amma waɗannan mutane ba su yi mini biyayya ba.’ “Saboda haka, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa Yahuda da kuma kowane mutumin da yake zama a Urushalima kowace masifar da na ambata a kansu. Na yi musu magana, amma ba su saurara ba; na kira su, amma ba su amsa ba.’ ” Sai Irmiya ya ce wa iyalin Rekabawa, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kun yi biyayya da umarnin kakanku Yehonadab kuka kuma kiyaye dukan umarnansa kuka yi kome bisa ga tsari.’ Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Yehonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa mutumin da zai yi mini hidima ba.’ ” Yehohiyakim ya ƙone littafin Irmiya A shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji cewa, “Ka ɗauki littafi ka rubuta dukan maganganun da na yi maka game da Isra’ila, Yahuda da kuma dukan sauran al’ummai daga lokacin da na fara maka magana a mulkin Yosiya har zuwa yanzu. Wataƙila sa’ad da mutanen Yahuda suka ji game da kowace masifar da na shirya in auka musu, kowa ya juya daga muguwar hanyarsa; sa’an nan in gafarta musu muguntarsu da kuma zunubinsu.” Saboda haka Irmiya ya kira Baruk ɗan Neriya, yayinda Irmiya yake fadar dukan waɗannan maganganun da Ubangiji ya faɗa masa, Baruk ya rubuta su a littafin. Sai Irmiya ya ce wa Baruk, “An hana ni, ba zan tafi haikalin Ubangiji ba. Saboda haka ka tafi gidan Ubangiji a ranar azumi ka karanta wa mutane daga littafin maganar Ubangiji da na shibta maka ka rubuta. Ka karanta su ga dukan mutanen Yahuda waɗanda suka zo daga garuruwansu. Wataƙila za su kawo kukansu a gaban Ubangiji, kowanne kuma ya juya daga muguwar hanyarsa, gama fushi da hasalar da Ubangiji ya furta a kan mutanen nan yana da girma.” Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya ce ya yi; a haikalin Ubangiji kuwa ya karanta maganar Ubangiji daga littafin A watan tara na shekara ta biyar ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, an yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji ga dukan mutanen Urushalima da waɗanda suka zo daga garuruwan Yahuda. Daga ɗakin Gemariya ɗan Shafan magatakarda, wanda yake a fili na bisa a mashigin Sabuwar Ƙofar haikali, Baruk ya karanta wa dukan mutane a haikalin Ubangiji maganar Irmiya daga littafin. Sa’ad da Mikahiya ɗan Gemariya, ɗan Shafan, ya ji dukan maganar Ubangiji daga littafin, sai ya sauka zuwa ɗakin magatakarda a fada, inda dukan fadawa suke zaune, Elishama magatakarda, Delahiya ɗan Shemahiya, Elnatan ɗan Akbor, Gemariya ɗan Shafan, Zedekiya ɗan Hananiya, da dukan sauran fadawa. Bayan Mikahiya ya faɗa musu kome da ya ji Baruk ya karanta wa mutane daga littafin, sai dukan fadawan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya ce wa Baruk, “Ka zo tare da littafin da ka karanta wa mutane.” Saboda haka Baruk ɗan Neriya ya tafi wurinsu tare da littafin a hannunsa. Suka ce masa, “Zauna, ka karanta mana littafin.” Sai Baruk ya karanta musu littafin. Da suka ji dukan maganar, sai suka dubi juna a firgice suka ce wa Baruk, “Dole mu sanar da dukan maganan nan ga sarki.” Sa’an nan suka ce wa Baruk, “Faɗa mana yadda ka yi ka rubuta dukan wannan. Irmiya ne ya yi maka shibtar ta?” Baruk ya amsa ya ce, “I, shi ne ya faɗa mini dukan wannan magana, na kuwa rubuta su a takarda.” Sa’an nan fadawan suka ce wa Baruk, “Kai da Irmiya ku je ku ɓuya. Kada ku bari wani ya san inda kuke.” Bayan da suka ajiye littafin a ɗakin Elishama magatakarda, sai suka tafi wurin sarki a fili suka sanar da shi kome. Sai sarki ya aiki Yehudi ya kawo littafin daga ɗakin Elishama magatakarda ya kuma karanta wa sarki da kuma dukan fadawan da suke tsaye kusa da shi. A watan tara ne sarki kuwa yana zaune a gidansa na rani, wuta kuwa tana ci a kasko a gabansa. Duk sa’ad da Yehudi ya karanta sashi uku ko huɗu na littafin, sai sarkin ya sa wuƙa ya yanke su, ya zuba a wutar da take ci a kasko, da haka ya ƙone dukan littafin. Sai sarki da dukan masu yin masa hidima waɗanda suke jin maganan nan ba su firgita ba, balle su keta rigunansu. Ko da yake Elnatan, Delahiya da Gemariya sun roƙi sarki kada yă ƙone littafin, bai saurare su ba. A maimakon haka, sai sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, Serahiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel su kama Baruk marubuci da Irmiya annabi. Amma Ubangiji ya ɓoye su. Bayan sarki ya ƙone littafin da ya ƙunshi maganar da Baruk ya rubuta daga shibtar Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Ka ɗauki wani littafi ka rubuta a kansa dukan maganar da littafi na farin ya ƙunsa, wanda Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone. Ka kuma faɗa wa Yehohiyakim sarkin Yahuda cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka ƙone wancan littafin ka kuma ce, “Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle sarkin Babilon zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?” Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim sarkin Yahuda. Ba zai kasance da wani wanda zai zauna a kan gadon sarautar Dawuda ba; za a jefar da gawarsa ta sha zafi da rana da dare kuma ta sha matsanancin sanyi. Zan hukunta shi da kuma ’ya’yansa da masu hidimarsa saboda muguntarsu; zan kawo kowace masifar da na furta a kansu da kuma waɗanda suke zama a Urushalima da na Yahuda, domin sun ƙi su saurara.’ ” Sai Irmiya ta ɗauko wani littafi ya ba wa Baruk ɗan Neriya marubuci, kuma yayinda Irmiya yake shibtawa, Baruk ya rubuta a littafin dukan maganar da take a littafin da Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone. Ya kuma ƙara ire-iren maganganun nan a kansu. Irmiya a kurkuku Nebukadnezzar sarkin Babilon ya naɗa Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda; ya yi mulki a madadin Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim. Shi da masu yin masa hidima da mutanen ƙasar ba su kula da maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya annabi ba. Sai sarki Zedekiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya tare da firist nan Zefaniya ɗan Ma’asehiya da wannan saƙo cewa, “Ina roƙonka ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnmu saboda mu.” To, fa, Irmiya ya sami ’yancin kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a riga an sa shi a kurkuku ba. Sojojin Fir’auna suka fita daga Masar, sa’ad da Babiloniyawa waɗanda suke ƙawanya wa Urushalima suka ji labari game da su, sai suka janye daga Urushalima. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya annabi cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aika a neme ni cewa, ‘Sojojin Fir’aunan da suka fito su taimake ka, za su koma ƙasarsu, Masar. Sa’an nan Babiloniyawa za su koma su yaƙi wannan birni su ci ta su kuma ƙone shi.’ “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku ruɗe kanku, kuna tsammani, ‘Tabbatacce Babiloniyawa sun bar mu.’ Ba za su bari ba! Ko da a ce za ku ci dukan sojojin Babiloniyawan da suke yaƙi da ku har raunana ne kawai aka bari a tentunansu, za su fito su ƙone wannan birni.” Bayan sojojin Babiloniyawa suka janye daga Urushalima saboda sojojin Fir’auna, sai Irmiya ya bar birnin don yă je yankin Benyamin ya sami rabon mallaka a cikin mutane a can. Amma sa’ad da ya kai Ƙofar Benyamin, sai hafsa mai tsaro, wanda ake kira Iriya ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama shi ya kuma ce, “Kana gudu daga Babiloniyawa ne!” Sai Irmiya ya ce, “Ba gaskiya ba ce, ba na gudu daga Babiloniyawa.” Amma Iriya bai saurare shi ba; a maimako, ya kama Irmiya ya kawo shi wurin fadawa. Suka yi fushi da Irmiya suka sa aka yi masa dūka aka kuma jefa shi cikin kurkuku a gidan Yonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku. Aka sa Irmiya a can cikin kurkuku, inda ya kasance kwanaki masu yawa. Sa’an nan Sarki Zedekiya ya aika a kawo shi aka kuma kawo shi fada, inda ya tambaye shi a kaɗaice ya ce, “Akwai wata magana daga Ubangiji?” Irmiya ya amsa ya ce, “I, za a ba da kai ga sarkin Babilon.” Sai Irmiya ya ce wa Sarki Zedekiya, “Wane laifi na yi maka ko fadawanka ko kuwa wannan mutane, da ka sa aka jefa ni cikin kurkuku? Ina annabawanka waɗanda suka yi maka annabci suna cewa, ‘Sarkin Babilon ba zai yaƙe ka ko wannan ƙasa ba’? Amma yanzu, ranka yă daɗe, sarkina, ka saurara. Bari in kawo kukata a gabanka. Kada ka mai da ni gidan Yonatan magatakarda, in ba haka zan mutu a can.” Sarki Zedekiya ya yi umarni a ajiye Irmiya a sansanin matsara a kuma ba shi burodi daga titin masu gashin burodi kowace rana sai duka burodi a birnin ya ƙare. Saboda haka Irmiya ya zauna a sansanin matsara. An jefa Irmiya a rijiya marar ruwa Shefatiya ɗan Mattan, Gedaliya ɗan Fashhur, Yukal38.1 Da Ibraniyanci Yukal, wani sunan Yukal ɗan Shelemiya da Fashhur ɗan Malkiya ya ji abin da Irmiya yana faɗa wa dukan mutane sa’ad da ya ce, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Duk wanda ya zauna a wannan birni zai mutu ta takobi, yunwa ko annoba, amma duk wanda ya je wurin Babiloniyawa38.2 Ko kuwa Kaldiyawa; haka ma a ayoyi 18, 19 da 23 zai rayu. Zai tsira da ransa, ya rayu.’ Kuma ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Tabbatacce za a ba da wannan birni ga sojojin sarkin Babilon, wanda zai ci shi.’ ” Sai fadawa suka ce wa sarki, “Ya kamata a kashe wannan mutum. Yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran mutane, ta wurin abubuwan da yake faɗa musu. Wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan sai dai wahala.” “Yana a hannuwanku” Sarki Zedekiya ya amsa. “Sarki ba zai iya yin kome ya hana ku ba.” Saboda haka suka kama Irmiya suka sa a rijiyar da ba ruwa a ciki ta Malkiya, ɗan sarki, wadda take a sansanin matsara. Suka saukar da Irmiya cikin rijiyar da ba ruwa da igiya; babu ruwa a cikinta, sai laka, Irmiya ya nutse cikin laka. Amma Ebed-Melek mutumin Kush,38.7 Mai yiwuwa daga yankin Nilu na Bisa wani hafsa38.7 Ko kuwa wani bābā a fada, ya ji cewa sun sa Irmiya a rijiyar da ba ruwa. Yayinda sarki yana zama a Ƙofar Benyamin, Ebed-Melek ya fita daga fadar ya ce masa, “Ranka yă daɗe sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu a duk abin da suka yi wa Irmiya annabi. Sun jefa shi cikin rijiyar da ba ruwa, inda zai mutu da yunwa gama ba sauran wani burodi a birnin.” Sai sarki ya umarce Ebed-Melek mutumin Kush, “Ka ɗauko mutane talatin daga nan ku fid da Irmiya annabi daga rijiyar kafin ya mutu.” Saboda haka Ebed-Melek ya ɗauki mutane tare da shi suka shiga ɗaki a ƙarƙashin baitulmali a cikin fada. Ya ɗauko waɗansu tsofaffin tsummoki da tsofaffi riguna daga can ya kuma zurara su da igiya wa Irmiya a cikin rijiyar. Ebed-Melek mutumin Kush ya ce wa Irmiya, “Ka sa waɗannan tsummoki da tsofaffin rigunan a hammatarka, ya zarga igiya.” Irmiya ya yi haka, suka kuma ja shi sama da igiya suka fid da shi daga rijiyar. Irmiya kuwa ya zauna a sansanin matsara. Zedekiya ya sāke yi wa Irmiya tambayoyi Sai Sarki Zedekiya ya aika a kawo Irmiya annabi, ya sa aka kawo shi a ƙofa ta uku ta haikalin Ubangiji. Sai sarki ya ce wa Irmiya, “Zan tambaye ka wani abu, kada ka ɓoye mini wani abu.” Irmiya ya ce wa Zedekiya, “In na ba ka amsa, ba za ka kashe ni ba? Ko da na ba ka shawara, ba za ka saurare ni ba.” Amma Sarki Zedekiya ya yi wannan rantsuwa a kaɗaice ga Irmiya cewa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya ba mu numfashi, ba zan kashe ka ko in ba da kai ga waɗanda suke neman ranka ba.” Sa’an nan Irmiya ya ce wa Zedekiya, “Ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon, za a bar ka da rai ba za a kuma ƙone wannan birni ba; da kai da iyalinka za ku rayu. Amma in ba ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon ba, za a ba da wannan birni ga Babiloniyawa za su kuma cinna mata wuta; kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba.’ ” Sarki Zedekiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawan da suka tafi wurin Babiloniyawa, gama Babiloniyawa mai yiwuwa su ba da ni gare su su kuma wulaƙanta ni.” Irmiya ya ce, “Ba za su ba da kai ba, ka yi biyayya ga Ubangiji ta wurin yin abin da na faɗa maka. Ta haka zai zama maka da amfani, za ka kuwa rayu. Amma in ka ƙi miƙa wuya, ga abin da Ubangiji ya bayyana mini. Za a fitar da dukan matan da suka ragu a fadan sarkin Yahuda wa hafsoshin sarkin Babilon. Waɗannan mata za su ce maka, “ ‘Sun ruɗe ka suka kuma rinjaye ka, waɗannan abokanka. Ƙafafunka sun nutse a cikin laka; abokanka sun yashe ka.’ “Za a kawo dukan matanka da ’ya’yanka wa Babiloniyawa. Kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba amma za su sa sarkin Babilon zai kama ka; za a kuma ƙone wannan birni.38.23 Ko kuwa za ka kuma sa wannan birni yă Sai Zedekiya ya ce wa Irmiya, “Kada ka bar wani ya san wannan zance, in ba haka ba za ka mutu. In fadawa suka ji cewa na yi magana da kai, suka kuma zo wurinka suka ce, ‘Faɗa mana abin da ka faɗa wa sarki da kuma abin da sarki ya faɗa maka; kada ka ɓoye mana, in ba haka za mu kashe ka,’ sai ka ce musu cewa, ‘Na roƙi sarki kada yă mai da ni gidan Yonatan in mutu a can.’ ” Dukan fadawa kuwa suka zo wurin Irmiya suka tambaye shi, ya kuma faɗa musu dukan abin da sarki ya umarce shi ya faɗa. Saboda haka ba su ƙara ce masa kome ba, gama ba wanda ya ji zance da suka yi da sarki. Irmiya kuwa ya zauna a sansanin masu gadi har ranar da aka ci Urushalima da yaƙi. Fāɗuwar Urushalima (Irmiya 52.4-16; 2 Sarakuna 25.1-12) Ga yadda aka ci Urushalima, A shekara ta tara ta Zedekiya sarkin Yahuda, a wata na goma, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fita yaƙi da Urushalima da dukan sojojinsa ya kuma yi mata ƙawanya. A rana ta tara ga watan huɗu a shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya, sai aka huda katanga. Sa’an nan dukan fadawan sarkin Babilon suka shiga suka zazzauna a Ƙofar Tsakiya. Wato, Nergal-Sharezer na Samgar-Nebo, Sarsekim wani babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da dukan sauran fadawan sarkin Babilon. Sa’ad da Zedekiya sarkin Yahuda da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu; suka bar birnin da dare ta hanyar lambun sarki, ta ƙofar da take tsakanin katanga biyu, suka nufi waje Araba.39.4 Ko kuwa Kwarin Urdun Amma sojojin Babiloniyawa suka bi su, suka ci wa Zedekiya a filayen Yeriko. Suka kama shi suka kai shi wurin Nebukadnezzar a Ribla a ƙasar Hamat, inda aka yanke masa hukunci. A can Ribla sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idanunsa aka kuma kashe dukan manyan mutanen Yahuda. Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya ya kuma buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babilon. Sai Babiloniyawa suka cinna wa fadar da kuma gidajen mutane wuta suka farfasa katangar Urushalima. Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya kwashi mutanen da suka rage a birnin zuwa zaman bauta a Babilon, tare da waɗanda suka riga suka tafi wurinsa, da kuma sauran mutanen. Amma Nebuzaradan shugaban matsaran ya bar waɗansu matalauta a ƙasar Yahuda, su da ba su da kome; a lokacin kuwa ya ba su gonakin inabi da kuma filaye. To, fa, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ba da wannan umarnai game da Irmiya ta wurin Nebuzaradan shugaban matsaran sarki cewa, “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.” Saboda haka Nebuzaradan shugaban matsara, Nebushazban babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da sauran hafsoshin sarkin Babilon suka aika aka kawo Irmiya daga filin matsar. Suka miƙa shi ga Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, don yă kai shi gidansa. Saboda haka ya zauna a can a cikin mutanensa. Yayinda aka kulle Irmiya a sansanin matsara, maganar Ubangiji ta zo masa cewa, “Tafi ka faɗa wa Ebed-Melek mutumin Kush, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ina gab da cika maganata a kan wannan birni ta wurin masifa, ba wadata ba. A lokacin za tă cika a idanunka. Amma zan kuɓutar da kai a wannan rana, in ji Ubangiji; ba zan ba da kai ga waɗanda kake tsoronsu ba. Zan cece ka; ba za ka mutu ta wurin takobi ba amma za ka tsira da ranka, domin ka dogara gare ni, in ji Ubangiji.’ ” An ’yantar da Irmiya Sai magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya sake shi a Rama. Ya sami Irmiya a daure da sarƙoƙi a cikin sauran kamammu daga Urushalima da kuma Yahuda waɗanda ake kaiwa zaman bauta a Babilon. Sa’ad da shugaban matsaran ya sami Irmiya sai ya ce masa, “Ubangiji Allahnka ya sa wannan masifa saboda wannan wuri. Yanzu kuma Ubangiji ya cika shi; ya yi kamar yadda ya faɗa. Dukan wannan ya faru domin kun yi zunubi ga Ubangiji ba ku kuwa yi masa biyayya ba. Amma yau ina ’yantar da kai daga sarƙoƙin da suke a hannuwanka. Zo mu tafi Babilon, in kana so, zan kuwa lura da kai; amma in ba ka so, kada ka zo. Ga shi, dukan ƙasar tana a gabanka; ka tafi duk inda ka so.” Amma, kafin Irmiya yă juya yă tafi,40.5 Ko kuwa Irmiya ya amsa Nebuzaradan ya ƙara da cewa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, wanda sarkin Babilon ya naɗa a kan garuruwan Yahuda, ka zauna da shi a cikin mutane, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga dama.” Sa’an nan shugaban ya ba shi abinci da kuma kyauta sai ya bar shi ya tafi. Saboda haka Irmiya ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa ya zauna tare da shi a cikin mutanen da aka bari a ƙasar. An yi wa Gedaliya kisan gilla Sa’ad da dukan shugabannin hafsoshin tare da mutanen da suke a karkara suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya ɗan Ahikam gwamna a kan ƙasar ya kuma sa shi ya lura da maza, mata da ’ya’yan da suke mafi talauci a ƙasar da waɗanda ba a kwashe zuwa zaman bauta a Babilon ba, sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan da Yonatan ’ya’yan Kareya, da Serahiya ɗan Tanhumet maza, ’ya’yan Efai maza, mutumin Netofa, da Yezaniya40.8 Da Ibraniyanci Yezaniya, wani suna na Ya’azaniya ɗan mutumin Ma’aka da mutanensu. Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, ya yi rantsuwa don yă tabbatar musu da mutanensu. Ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Babiloniyawa.40.9 Ko kuwa Kaldiyawa; haka ma a aya 10 Ku zauna a ƙasar ku bauta wa sarkin Babilon, zai kuma yi muku amfani. Ni kaina zan zauna a Mizfa in zama wakilinku a gaban Babiloniyawa waɗanda za su zo wurinmu, amma ku girbe ruwan inabi, ’ya’yan itatuwa na kaka, da mai, ku zuba su a tulunan ajiyarku, ku kuma zauna a garuruwan da kuka ci.” Sa’ad da dukan Yahudawan da suke a Mowab, Ammon, Edom da sauran ƙasashe suka ji cewa sarkin Babilon ya bar raguwa a Yahuda ya kuma naɗa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan gwamna a kansu, sai suka dawo ƙasar Yahuda, wurin Gedaliya a Mizfa, daga dukan ƙasashen da suke a warwatse. Suka girbe ruwan inabi a yalwace da ’ya’yan itatuwan kaka. Yohanan ɗan Kareya da dukan manyan sojoji da suke a karkara suka zo wurin Gedaliya a Mizfa suka ce masa, “Ba ka san cewa Ba’alis sarkin Ammonawa ya aiki Ishmayel ɗan Netaniya ya ɗauke ranka ba?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam bai gaskata su ba. Sai Yohanan ɗan Kareya ya yi wa Gedaliya a Mizfa magana a asirce ya ce, “Bari in tafi in kashe Ishmayel ɗan Netaniya, ba kuwa wanda zai sani. Me zai sa ya ɗauke ranka ya watsar da dukan Yahudawan da suka taru kewaye da kai har waɗanda suka ragu na Yahuda su hallaka?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohanan ɗan Kareya, “Kada ka yi irin wannan abu! Abin da kake faɗa game da Ishmayel ba gaskiya ba ne.” A wata na goma sha bakwai sai Ishmayel ɗan Netaniya, ɗan Elishama, wanda yake mai jinin sarauta yake kuma ɗaya daga cikin hafsoshin sarki, ya zo tare da mutum goma wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa. Yayinda suke ci tare a can, sai Ishmayel ɗan Netaniya da mutum goma waɗanda suke tare da shi suka kashe Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da takobi, suka kashe wannan da sarkin Babilon ya naɗa a matsayin gwamna a kan ƙasar. Ishmayel ya kuma kashe dukan Yahudawan da suke tare da Gedaliya a Mizfa, haka ma ya yi da sojojin Babiloniyawan da suke can. Kashegari bayan an kashe Gedaliya, kafin wani ya san abin da ya faru, sai ga mutane tamanin daga Shekem, Shilo da Samariya suka zo da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage, suka kawo hadayun gari da turare tare da su a gidan Ubangiji. Ishmayel ɗan Netaniya ya fito daga Mizfa don yă sadu da su. Sa’ad da ya sadu da su, sai ya ce, “Ku zo wurin Gedaliya ɗan Ahikam.” Da suka shiga cikin birni, sai Ishmayel ɗan Netaniya da mutanen da suke tare da shi suka karkashe su suka zubar a rijiya. Amma goma daga cikinsu suka ce wa Ishmayel, “Kada ka kashe mu, muna da alkama da sha’ir, mai da kuma zuma, a ɓoye a gona.” Saboda haka ka bar mu kada ka kashe mu tare da sauran. To, rijiyar da ya zubar da gawawwakin mutanen da ya kashe tare da ta Gedaliya ita ce wadda Sarki Asa ya haƙa a matsayin kāriya saboda Ba’asha sarkin Isra’ila. Ishmayel ɗan Netaniya ya cika ta da gawawwaki. Ishmayel ya mai da dukan sauran mutanen da suke Mizfa bayi ’ya’yan sarki mata tare da dukan sauran da aka bari a can, waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Ishmayel ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya tashi don yă haye zuwa wurin Ammonawa. Sa’ad da Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka ji dukan laifofin da Ishmayel ɗan Netaniya ya aikata, sai suka kwashe dukan mutanensu suka tafi don su yaƙi Ishmayel ɗan Netaniya. Suka iske shi kusa da babban tafki a Gibeyon. Sa’ad da dukan mutanen da suke tare da Ishmayel suka ga Yohanan ɗan Kareya da shugabannin sojojin da suke tare da shi, sai suka yi farin ciki. Dukan mutanen da Ishmayel ya kame a Mizfa suka juya, suka tafi wurin Yohanan ɗan Kareya. Amma Ishmayel ɗan Netaniya da mutanensa takwas suka tsere daga Yohanan suka gudu zuwa wurin Ammonawa. Gudu zuwa Masar Sai Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojojin da suke tare da shi suka bi da dukan waɗanda suka tsira daga Mizfa waɗanda ya karɓe daga Ishmayel ɗan Netaniya bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato, sojoji, mata, yara da fadawan da ya kawo daga Gibeyon Sai suka ci gaba, suka dakata a Gerut Kimham kusa da Betlehem a kan hanyarsu zuwa Masar don su kuɓuce wa Babiloniyawa. Sun ji tsoronsu domin Ishmayel ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wanda sarkin Babilon ya naɗa gwamna a kan ƙasar. Sa’an nan dukan shugabannin sojoji, haɗe da Yohanan ɗan Kareya da Yezaniya42.1 Ibraniyanci; Seftuwajin (dubi kuma Irm 43.2) Azariya ɗan Hoshahiya, da dukan mutane daga ƙarami zuwa babba, suka zo wurin Irmiya annabi suka ce masa, “Muna roƙonka ka ji kukanmu ka kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda dukan wannan raguwar mutane. Gama kamar yadda kake gani yanzu, ko da yake dā muna da yawa, yanzu ɗan kaɗan muka rage. Ka yi addu’a cewa Ubangiji Allahnka zai faɗa mana inda za mu tafi da kuma abin da za mu yi.” Sai Irmiya ya amsa ya ce, “Na ji ku, tabbatacce zan yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yadda kuka roƙa; zan faɗa muku duk abin da Ubangiji ya faɗa ba kuwa zan ɓoye muku kome ba.” Sa’an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji ya zama shaida na gaskiya da kuma aminci a kanmu in ba mu yi bisa da duk abin da Ubangiji Allahnka ya aike ka ka faɗa mana ba. Ko ya gamshe mu ko bai gamshe mu ba, za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu, ga wanda muke aikan ka, saboda ya zama mana da amfani, gama za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu.” Bayan kwana goma sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya. Saboda haka ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi da dukan jama’a daga ƙarami zuwa babba. Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni gare shi don in gabatar da kukanku, yana cewa, ‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku. Kada ku ji tsoron sarkin Babilon, wanda kuke tsoro a yanzu. Kada ku ji tsoronsa, in ji Ubangiji, gama ina tare da ku zan kuma cece ku daga hannuwansa. Zan nuna muku jinƙai don yă nuna muku jinƙai ya kuma maido da ku ƙasarku.’ “Amma fa, in kuka ce, ‘Ba za mu zauna a wannan ƙasa ba,’ ta haka kuka kuma nuna rashin biyayya ga Ubangiji Allahnku, in kuma kuka ce, ‘A’a, za mu tafi mu zauna a Masar, inda ba za mu ga yaƙi ko mu ji ƙarar ƙaho ko mu ji yunwa ba,’ to, ku ji maganar Ubangiji, ya raguwar Yahuda. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In kun ƙudura ku tafi Masar kuka kuma tafi kun zauna a can, takobin da kuke tsoro zai same ku a can, kuma yunwar da kuke tsoro za tă bi ku zuwa Masar, a can kuwa za ku mutu. Tabbatacce, duk waɗanda suka ƙudura suka tafi Masar su zauna a can za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba; ba ko ɗayansu zai tsira ko ya kuɓuta wa masifar da zan aukar a kansu.’ Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama abin la’ana da abin tsoro, abin ƙyama da abin ba’a; ba za ku ƙara ganin wannan wuri ba.’ “Ya ku raguwar Yahuda, Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku je Masar.’ Ku tabbatar da wannan. Na gargaɗe ku yau cewa in kun yi kuskure42.20 Ko kuwa kun yi kuskure a zukatanku sa’ad da kuka aike ni wurin Ubangiji Allahnku kuka kuma ce, ‘Yi mana addu’a ga Ubangiji Allahnmu; ka faɗa mana duk abin da ya faɗa za mu kuwa aikata.’ Na faɗa muku yau, amma har yanzu ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku cikin dukan abin da ya aiko ni in faɗa muku ba. Saboda haka yanzu, ku tabbatar da wannan. Za ku mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba a wurin da kuke so ku tafi ku zauna.” Sa’ad da Irmiya ya gama faɗa wa mutane dukan maganar Ubangiji Allahnsu, duk abin da Ubangiji ya aike shi ya faɗa musu, Azariya ɗan Hoshahiya da Yohanan ɗan Kareya da dukan masu ɗaga kai suka ce wa Irmiya, “Kana ƙarya ne! Ubangiji Allahnmu bai aike ka ka ce, ‘Kada ku tafi Masar don ku zauna a can.’ Amma Baruk ɗan Neriya yana zuga ka a kanmu don ka ba da mu ga Babiloniyawa, don su kashe mu ko su kai mu zaman bauta a Babilon.” Saboda haka Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da dukan mutane suka yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da su zauna a ƙasar Yahuda. A maimako, Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe raguwar Yahuda waɗanda suka dawo su zauna a ƙasar Yahuda daga dukan al’umman inda aka kora su. Suka kuma kwashe dukan maza, mata da yara da ’ya’yan sarki mata waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari tare da Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da Irmiya annabi da kuma Baruk ɗan Neriya. Saboda haka suka shiga Masar cikin rashin biyayya ga Ubangiji suka tafi har can Tafanes. A Tafanes maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, “Yayinda Yahudawa suna kallo, ka ɗauki waɗansu manyan duwatsu tare da kai ka kuma binne su cikin yumɓu a tubalin dakalin ƙofar shiga fadar Fir’auna a Tafanes. Sa’an nan ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, zan aika wa bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon, zan kuma sa kursiyinsa a kan waɗannan duwatsun da na binne a nan; zai fadada bukkar mulkinsa a bisansu. Zai zo ya yaƙi Masar, ya kawo mutuwa ga waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa, zaman bauta ga waɗanda aka ƙaddara musu zaman bauta, da kuma takobi ga waɗanda aka ƙaddara su mutu ta takobi. Zai43.12 Ko kuwa Zan sa wuta wa haikalan allolin Masar; zai ƙone haikalansu yă kuma kwashe allolinsu bayi. Kamar yadda makiyayi yakan yafa mayafinsa kewaye da shi, haka zai yafa Masar kewaye da kansa ya kuma tashi a wurin babu abin da ya same shi. A can cikin haikalin rana43.13 Ko kuwa a Heliyofolis a Masar zai rushe al’amudan duwatsu yă kuma ƙone haikalan allolin Masar.’ ” Masifa domin bautar gumaka Wannan maganata zo wa Irmiya game da dukan Yahudawa masu zama a Masar ta Ƙasa, a Migdol, Tafanes da Memfis, da kuma a Masar ta Bisa. “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa kun ga masifa mai girmar da na kawo a kan Urushalima da kuma a kan dukan garuruwan Yahuda. A yau sun zama hamada da kuma kango saboda muguntar da suka aikata. Sun tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙone turare da kuma ta wurin bauta wa waɗansu allolin da su ko ku ko kakanninku ba su taɓa sani ba. Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’ Amma ba su saurara ko su kasa kunne ba; ba su juye daga muguntarsu ko su daina ƙone turare wa waɗansu alloli ba. Saboda haka, fushina mai ƙuna ya fāɗo a kan garuruwan Yahuda da kuma titunan Urushalima na kuma mai da su kufai da suke a yau. “To, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa don me kuka kawo irin masifa mai girma haka a kanku ta wurin warewa daga Yahuda maza da mata, yara da jarirai, kun kuma bar kanku babu raguwa? Me ya sa kuka tsokane ni in yi fushi saboda abin da hannuwanku suka yi, kuna ƙone turare wa waɗansu alloli a Masar, inda kuka zo don ku zauna? Za ku hallakar da kanku ku kuma mai da kanku abin la’ana da abin zargi da abin ba’a a cikin dukan al’umman duniya. Kun manta mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakuna da sarauniyoyin Yahuda da mugayen ayyukanku, da na matanku a cikin Yahuda da kan titunan Urushalima? Har yă zuwa yau ba su ƙasƙantar da kansu ko su nuna bangirma, ko su kiyaye dokata da ƙa’idodin da na sa a gabanku da kakanninku ba. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa na ƙudura in aukar muku da masifa in kuma hallaka dukan Yahuda. Zan ɗauke raguwar Yahuda waɗanda suka ƙudurta su je Masar su zauna a can. Duk za su hallaka a Masar; za su mutu ta wurin takobi ko su mutu da yunwa. Daga ƙarami zuwa babba, za su mutu ta wurin takobi ko yunwa. Za su zama abin zarge da abin tsoro, abin la’ana da abin ba’a. Zan hukunta waɗanda suke zama a Masar da takobi, yunwa da annoba, yadda na hukunta Urushalima. Babu wani daga raguwar Yahuda wanda ya tafi Masar da zai kuɓuta ko ya tsira har ya komo zuwa ƙasar Yahuda, wadda za su yi marmari su komo su zauna; babu wani da zai komo sai dai ’yan gudun hijira.” Sai dukan mazan da suka san cewa matansu suna ƙone turare wa waɗansu alloli, tare da dukan matan da suke a nan babban taro, da kuma dukan mutanen da suke zama a Masar ta Ƙasa da ta Bisa, suka ce wa Irmiya, “Ba za mu saurari saƙon da ka yi mana magana a sunan Ubangiji ba! Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa. Amma tun da muka daina ƙone turare ga Sarauniyar Sama da kuma miƙa mata hadayun sha, muka rasa kome muna ta mutuwa ta wurin takobi da yunwa.” Matan suka ƙara da cewa, “Sa’ad da muka ƙone turare ga Sarauniyar Sama muka kuma miƙa mata hadayun sha, mazanmu ba su san muna yin waina kamar siffarta muna kuma miƙa mata hadayun sha ba?” Sai Irmiya ya ce wa dukan mutanen, maza da mata, waɗanda suke ba shi amsa, Ubangiji bai tuna ya kuma yi tunani game da turaren da aka ƙone a garuruwan Yahuda da kan titunan Urushalima wanda ku da kakanninku, sarakunanku da fadawanku da mutanen ƙasar ba ne? Sa’ad da Ubangiji bai iya jurewa da mugayen ayyukanku da kuma abubuwa banƙyama da kuka aikata ba, sai ƙasarku ta zama abin la’ana da kufai babu mazauna yadda yake a yau. Domin kun ƙone turare kuka kuma yi wa Ubangiji zunubi ba ku kuma yi masa biyayya ko ku kiyaye dokarsa ko ƙa’idodinsa ko farillansa ba, wannan masifa ta aukar muku, yadda yanzu kuka gani.” Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane, har da mata, “Ku saurari maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda a Masar. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’ “To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku! Amma ku ji maganar Ubangiji, dukan Yahudawan da suke zama a Masar, ‘Na rantse da sunana,’ in ji Ubangiji, ‘cewa babu wani daga Yahuda wanda yake zama a ko’ina a Masar zai ƙara kira bisa sunana ko ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji Mai Iko Duka yana raye.” Gama ina lura da su don lahani, ba alheri ba; mutanen Yahuda da suke a Masar za su hallaka ta wurin takobi da yunwa sai dukansu sun hallaka. Waɗanda suka kuɓuta wa takobi suka komo zuwa ƙasar Yahuda daga Masar za su zama kima kawai. Sa’an nan dukan raguwar Yahuda waɗanda suka zo don su yi zama a Masar za su san maganar wane ne za tă tabbata, tawa ko tasu. “ ‘Wannan zai zama alama a gare ku cewa zan hukunta ku a wannan wuri,’ in ji Ubangiji, ‘saboda ku san cewa barazanata ta lahani a kanku tabbatacce za tă cika.’ Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan bayar da Fir’auna Hofra sarkin Masar ga abokan gābansa waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zedekiya sarkin Yahuda ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, abokin gāban da ya nemi ransa.’ ” Saƙo zuwa ga Baruk Ga abin da Irmiya annabi ya faɗa wa Baruk ɗan Neriya a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, bayan Baruk ya rubuta maganar da Irmiya ya shibta masa a kan littafi cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana ce maka, Baruk. Ka ce, ‘Kaitona! Ubangiji ya ƙara baƙin ciki da wahalata; na gaji da nishe-nishe ban kuma huta ba.’ ” Ubangiji ya ce, “Ka faɗa masa wannan, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan rushe abin da na gina in kuma tumɓuke abin da na dasa, a duk fāɗin ƙasar. Ya kamata ka nemi manyan abubuwa wa kanka? Kada ka neme su. Gama zan aukar da masifa a kan dukan mutane, in ji Ubangiji, amma duk inda ka tafi zan bar ka ka kuɓutar da ranka.’ ” Saƙo game da Masar Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da al’ummai. Game da Masar. Ga saƙo game da sojojin Fir’auna Neko sarkin Masar, wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ci da yaƙi a Karkemish a Kogin Yuferites a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda. “Ku shirya garkuwoyinku, manya da ƙanana, ku kuma fito don yaƙi! Ku shirya dawakai, ku sa musu sirdi! Ku tsaya a wurarenku saye da hulunan kwano a kai! Ku wasa māsunku, ku yafa kayan yaƙinku! Me nake gani? Sun tsorata, suna ja da baya, an ci jarumawansu. Suna gudu da sauri ba waiwayawa, akwai razana a kowane gefe,” in ji Ubangiji. “Masu saurin gudu ba sa iya gudu haka ma masu ƙarfi ba sa iya kuɓuta. A arewa ta Kogin Yuferites sun yi tuntuɓe sun fāɗi. “Wane ne wannan mai tashi kamar Nilu, kamar koguna masu tafasar ruwaye? Masar tana tashi kamar Nilu, kamar koguna masu tafasa. Tana cewa, ‘Zan tashi in rufe duniya; zan hallakar da birane da kuma mutanensu.’ Ku yi sukuwar hauka, ya dawakai! Ku tashi a guje, ya mahayan kekunan yaƙi! Ku yi ta fitowa, ya jarumawa, mutanen Kush da kuma Ludim masu riƙon garkuwoyi, mutanen Lidiya, masu iya jan baka. Amma wannan rana ta Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki ranar ɗaukar fansa, gama ɗaukar fansa a kan maƙiyansa. Takobi zai yi ta ci sai ya gamsu, sai ya kashe ƙishirwansa da jini. Gama Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, zai miƙa hadaya a ƙasar arewa kusa da Kogin Yuferites. “Ki haura Gileyad ki samo magani, Ya Budurwa ’Yar Masar. Amma kin riɓanya magani a banza; ba magani dominki. Al’ummai za su ji game da kunyar da kika sha; kukanki zai cika duniya. Jarumi zai yi tuntuɓe a kan wani; dukansu biyu za su fāɗi tare.” Ga saƙon da Ubangiji ya yi wa Irmiya annabi game da zuwan Nebukadnezzar sarkin Babilon don yă yaƙi Masar. “Ka yi shelar wannan a Masar, ka kuma furta shi a Migdol; ka yi shelarsa kuma a Memfis da Tafanes. ‘Ku ɗauki matsayinku ku kuma shirya, gama takobi na cin waɗanda suke kewaye da ku.’ Me zai sa a wulaƙanta jarumawanka haka? Ba za su iya tsayawa ba, gama Ubangiji zai ture su ƙasa. Za su yi ta tuntuɓe; za su fāɗi akan juna. Za su ce, ‘Mu tashi, mu koma zuwa wurin mutanenmu da kuma ƙasashenmu, daga takobin masu danniya.’ A can za su tā da murya su ce, ‘Fir’auna sarkin Masar mai yawan surutu ne kawai; ya bar zarafi ya wuce masa.’ “Muddin ina raye,” in ji Sarki, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki, “wani zai ɓullo wanda yake kamar Tabor a cikin duwatsu, kamar Karmel kusa da teku. Ku tattara kayanku don shirin zuwa zaman bauta, ku da kuke zama a Masar, gama Memfis za tă zama kufai ta zama kango, babu mazauna. “Masar kyakkyawar karsana ce, amma bobuwa tana zuwa a kanta daga arewa. Sojojin da ta yi hayarsu a cikinta suna kamar ’yan maruƙa masu kitse. Su ma za su juya su kuma gudu gaba ɗaya, ba za su iya tsayawa ba, gama ranar masifa tana zuwa a kansu, lokacin da za su sha hukunci. Masar za tă yi huci kamar macijin da yake gudu yayinda abokin gāba yana matsowa da ƙarfi; za su fāɗo mata gatura kamar mutanen da suke saran itatuwa. Za su sari kurminta,” in ji Ubangiji, “ko da yake yana maƙare da itatuwa. Sun fi fāra yawa, ba su ƙidayuwa. Za a kunyatar da Diyar Masar, da aka bashe ga mutanen arewa.” Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ina gab da kawo hukunci a kan allahn Amon na Tebes,46.25 Da Ibraniyanci No a kan Fir’auna, a kan Masar da allolinta da sarakunanta, da kuma a kan waɗanda suka dogara ga Fir’auna. Zan ba da su ga waɗanda suke neman ransu, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da fadawansa. Amma daga baya, Masar za tă kasance da mazauna kamar dā,” in ji Ubangiji. “Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila. Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nisa, zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yaƙub zai sāke kasance cikin salama, rai kwance, babu kuma wanda zai sa ya ji tsoro. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana, gama ina tare da kai,” in ji Ubangiji. “Ko da na hallaka dukan al’ummai sarai inda na kora ka, ba zan hallaka ka sarai ba. Zan hore ka amma da adalci kaɗai; ba zan bar ka ba hukunci ba.” Saƙo game da Filistiyawa Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa; za su zama kogi mai rigyawa. Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta, garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu. Mutane za su yi kuka; dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa da jin motsin takawar kofatan dawakai, da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba da motsin ƙafafunsu. Ubanni ba za su juye don su taimaki ’ya’yansu ba; hannuwansu za su yi laƙwas. Gama rana ta zo da za a hallaka Filistiyawa a kuma datse dukan waɗanda suka ragu waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon. Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa, raguwa daga bakin tekun Kaftor. Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki; Ashkelon zai yi shiru. Ya raguwar da suke zama a fili, har yaushe za ku tsattsage kanku? “Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji sai yaushe za ka huta? Ka koma kubenka; ka huta, ka yi shiru.’ Amma ta yaya zai huta sa’ad da Ubangiji ya umarta, sa’ad da ya umarta shi don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?” Saƙo game da Mowab Game da Mowab. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace. Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta; katagar48.1 Ko kuwa / Misgab za tă sha kunya ta kuma wargaje. Ba za a ƙara yabi Mowab ba; a Heshbon48.2 Da Ibraniyanci na Heshbon ya yi kamar Ibraniyanci na maƙarƙashiya. mutane za su shirya mata maƙarƙashiya. ‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’ Ke kuma, ya Madmen48.2 Sunan garin Mowab nan Madmen ya yi kamar Ibraniyanci na yi shiru. za ki yi shiru; takobi zai fafare ki. Saurari kuka daga Horonayim, kukan risɓewa mai girma da hallaka. Za a karye Mowab; ƙanananta za su yi kuka. Sun haura hanyar zuwa Luhit, suna kuka mai zafi yayinda suke tafiya; a hanyar da ta gangara zuwa Horonayim suna kuka a kan hallakar da aka ji. Ku gudu! Ku gudu don tserar da ranku; ku zama kamar kurmi48.6 Ko kuwa kamar Arower a hamada. Da yake kun dogara ga ayyukanku da arzikinku, ku ma za a kwashe ku bayi, Kemosh zai tafi bauta, tare da firistocinsa da fadawansa. Mai hallakarwa zai aukar wa kowane gari, kuma ba wani garin da zai kuɓuta. Kwari zai lalace tudu kuma ya hallaka, domin Ubangiji ya faɗa. Ku sa gishiri a kan Mowab, gama za tă zama kango;48.9 Ko kuwa Ku ba wa Mowab fikafikai, don tă tashi tă tafi garuruwanta za su zama kufai, ba mazauna a cikinsu. “La’ananne ne shi wanda yake sake a yin aikin Ubangiji! La’ananne ne wanda ya janye takobinsa daga zub da jini! “Mowab ta kasance cikin kwanciyar rai tun ƙuruciyarta, kamar ruwan inabin da aka bari lis, ba a juya daga tulu zuwa wani tulu ba ba tă tafi bauta ba. Saboda haka tana da ɗanɗanonta, kuma ƙanshinta bai canja ba. Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan aika da mutanen da za su tuntsurar da tuluna, su kuma zubar da ita waje. Za su bar tulunan ba kome a ciki su kuma farfashe tulunanta. Sa’an nan Mowab za tă ji kunyar Kemosh, yadda gidan Isra’ila ya ji kunya sa’ad da suka dogara ga Betel. “Yaya za ku ce, ‘Mu jarumawa ne, mutane masu ƙarfi a yaƙi?’ Mowab za tă hallaka a kuma kai wa garuruwanta hari; samarinta kyawawa za su gangara cikin mayanka,” in ji Sarki, wanda sunansa Ubangiji Maɗaukaki ne. “Fāɗuwar Mowab ta yi kusa; bala’inta zai auku nan da nan. Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta, duk waɗanda suka san shahararta; ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye, dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’ “Sauko daga darajarku ku zauna a busasshiyar ƙasa, Ya mazaunan Diyar Dibon, gama shi mai hallaka Mowab zai haura a kanku zai kuma lalace biranenku masu kagarai. Ku tsaya a bakin hanya ku duba, ku da kuke zama a Arower. Ku tambayi mutumin da yake gudu da macen da take tserewa, tambaye su, ‘Me ya faru?’ An kunyata Mowab, gama ta wargaje. Ku yi kuka ku kuma tā da murya! Ku yi shela kusa da Arnon cewa an hallaka Mowab. Hukunci ya zo wa tudu, zuwa Holon, Yahza da Mefa’at, zuwa Dibon, Nebo da Bet-Dibilatayim, zuwa Kiriyatayim, Bet-Gamul da Bet-Meyon, zuwa Keriyot da Bozra zuwa dukan garuruwan Mowab, nesa da kusa. An karye ƙahon Mowab; an karye hannunta,” in ji Ubangiji. “Ku bugar da ita domin ta tayar wa Ubangiji. Bari Mowab tă yi ta birgima a cikin amanta; bari tă zama abin dariya. Isra’ila ma bai zama abin dariya a gare ki ba? Ba a kama shi cikin ɓarayi, har kaɗa kai na ba’a kike yi a duka sa’ad da kike magana game da shi? Ku bar garuruwanku ku zauna a cikin duwatsu, ku da kuke zama a Mowab. Ku zama kamar kurciyar da take sheƙarta a bakin kogo. “Mun ji labarin girman kan Mowab mun ji alfarma girmankanta da kumburinta girmankanta da fariyarta da renin zuciyarta. Na san alfarmanta amma a banza ne,” in ji Ubangiji, “kuma taƙamarta ba ya cimma kome. Saboda haka zan yi kuka a kan Mowab gama dukan Mowab zan yi kuka, Zan yi gurnani don mutanen Kir Hareset. Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka Ya kuringar Sibma. Rassanki sun kai har teku; sun kai har tekun Yazer. Mai hallakarwa ya fāɗo a kan ’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna. Farin ciki da murna su ɓace daga lambunan itatuwa da kuma gonakin Mowab. Na dakatar da malalar ruwan inabi daga wurin matsi; ba wanda zai matse su da ihun farin ciki. Ko da yake akwai sowa sowar ba ta farin ciki ba ce. “Muryar kukansu na tashi daga Heshbon zuwa Eleyale da Yahaz, daga Zowar har zuwa Horonayim da Eglat Shelishiya, gama har ruwan Nimrim ma sun bushe. A Mowab zan kawo ƙarshen waɗanda suke miƙa hadayu a masujadan kan tudu suna kuma ƙone turare ga allolinsu,” in ji Ubangiji. “Saboda haka zuciyata na makoki don Mowab kamar busa; tana makoki kamar busa saboda mutanen Kir Hareset. Arzikin da suka samu ta ƙare. An aske kowane kai aka kuma yanke kowane gemu aka kuma sa wa kowane kwankwaso rigar makoki. A kan dukan rufi a Mowab da kuma a dandalin jama’a babu wani abu sai kuka gama na karye Mowab kamar tulun da babu mai so,” in ji Ubangiji. “Duba yadda aka ragargazar ta ita! Duba yadda suke kuka! Duba yadda Mowab ta juya bayanta da kunya! Mowab ta zama abin ba’a abin tsoro ga dukan waɗanda suke kewaye da ita.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ga shi! Gaggafa tana firiya zuwa ƙasa, tana shimfiɗa fikafikanta a kan Mowab. Za a ci Keriyot48.41 Ko kuwa Birane a kuma kame kagarai. A wannan rana zukatan jarumawan Mowab za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda. Za a hallakar da Mowab a matsayin al’umma domin ta tayar wa Ubangiji. Razana da rami da tarko suna jiranku, Ya mutanen Mowab,” in ji Ubangiji. “Duk wanda ya gudu daga razana zai fāɗa cikin rami, duk wanda ya haura daga rami zai fāɗa cikin tarko; gama zan kawo wa Mowab shekarar hukuncinta,” in ji Ubangiji. “A ƙarƙashin Heshbon masu gudun hijira suna tsaye ba mai taimako, gama wuta ta mutu daga Heshbon, harshen wuta daga tsakiyar Sihon; ta ƙone goshin Mowab, ƙoƙon kai na ’yan tayarwa masu surutu. Kaitonki, ya Mowab! Mutanen Kemosh sun hallaka; an kai ’ya’yanki maza daurin talala ’ya’yanki mata zaman bauta. “Duk da haka zan maido da wadatar Mowab a kwanaki masu zuwa,” in ji Ubangiji. A nan hukuncin Mowab ya ƙare. Saƙo game da Ammon Game da Ammonawa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Isra’ila ba shi da ’ya’ya maza ne? Ba shi da magāda ne? To, me ya sa Molek49.1 Ko kuwa sarkinsu; Da Ibraniyanci malkam; haka ma a aya 3. ya mallaki Gad? Me ya sa mutanensa suka zama a garuruwansa? Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi kirarin yaƙi a kan Rabba ta Ammonawa; zai zama tarin juji, za a sa wuta a ƙauyukan da suke kewayenta. Sa’an nan Isra’ila zai kori waɗanda suka kore shi,” in ji Ubangiji. “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai! Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba! Ku sa tufafin makoki; ku ruga nan da can a cikin katanga, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da kuma fadawansa. Me ya sa kuke taƙama da kwarurukanku, taƙama da kwarurukanku masu amfani? Ya ke diya marar aminci, kin dogara a wadatarki kika kuma ce, ‘Wa zai iya fāɗa mini?’ Zan kawo razana a kanki daga waɗanda suke kewaye da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Za a kore kowannenku, babu wani da zai tattara masu gudun hijira. “Duk da haka, daga baya, zan maido da wadatar Ammonawa,” in ji Ubangiji. Saƙo game da Edom Game da Edom. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Babu sauran hikima a Teman ne? Shawara ta ɓace daga masu basira ne? Hikimarsu ta ruɓe ne? Ku juya ku gudu, ku ɓuya a cikin kogwanni masu zurfi, ku da kuke zama a Dedan, gama zan kawo masifa a kan Isuwa a lokacin da zan hukunta shi. In masu tsinkar ’ya’yan inabi suka zo maka, ba za su rage ’ya’yan inabi kaɗan ba? In ɓarayi suka zo da dare, ba za su sata abin da kawai suke bukata ba? Amma zan washe Isuwa sarai; zan bubbuɗe wuraren ɓuyarsa, don kada yă ɓoye kansa. ’Ya’yansa, danginsa da maƙwabtansa za su hallaka, ba kuwa zai ƙara kasancewa ba. Ka bar marayunka; zan tsare ransu. Gwaurayenka kuma za su dogara a gare ni.” Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In waɗanda ba su dace su sha kwaf ɗin ba suka sha shi, me ya sa za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, sai ka sha shi. Na rantse da kaina,” in ji Ubangiji, “cewa Bozra za tă zama kufai da kuma abin tsoro, abin dariya da abin la’ana; kuma dukan garuruwanta za su kasance kufai har abada.” Na ji saƙo daga Ubangiji cewa; an aiki jakada zuwa ga al’ummai ya ce, “Ku tattara kanku don ku fāɗa mata! Ku tashi don yaƙi!” “Yanzu zan mai da kai ƙanƙani a cikin al’ummai abin reni a cikin mutane. Tsoron da ka sa ake ji da kuma girman kan zuciyarka ya ruɗe ka, kai da kake zama a kogon dutse, kai da kake kan tudu. Ko da yake ka gina wa kanka sheƙa can bisa kamar na gaggafa, daga can zan sauko da kai ƙasa,” in ji Ubangiji. “Edom za tă zama abin tsoro; dukan wanda ya wuce zai giggice ya yi tsaki saboda dukan mikinta. Kamar yadda aka tumɓuke Sodom da Gomorra, tare da garuruwan da suke maƙwabtaka da su,” in ji Ubangiji, “haka ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta. “Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai kyau, zan kori Edom daga ƙasarta nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa don wannan? Wane ne yake kama da ni kuma wa zai kalubalance ni? Kuma wane makiyayi ne zai yi gāba da ni?” Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Edom, abin da ya nufa wa waɗanda suke zama a Teman. Za a ja ƙanana na garken tumaki a tafi; zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su. Amon fāɗuwarsu zai sa ƙasa ta girgiza; za a kuma ji muryar kukansu a Jan Teku. Duba! Gaggafa tana firiya tana kuma saukowa, tana buɗe fikafikanta a bisa Bozra. A wannan rana zukatan jarumawan Edom za su zama kamar macen da take naƙuda. Saƙo game da Damaskus Game da Damaskus. “Hamat da Arfad sun giggice, gama sun ji mummunar labari. Suna damuwa, sun damu kamar tekun da baya hutu. Damaskus ta karai ta juya don ta gudu tsoro kuma ya kama ta; wahala da zafi sun kama ta, zafi kamar na mace mai naƙuda. Me ya sa ba a tafi aka bar sanannen birnin nan ba, birnin da nake jin daɗi? Tabbatacce, samarinta za su fāɗi a tituna; dukan sojojinta za su yi shiru a wannan rana,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan cinna wa katangar Damaskus wuta; za tă ci kagaran Ben-Hadad.” Saƙo game da Kedar da Hazor Game da Kedar da mulkokin Hazor, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fāɗa wa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tashi, ku fāɗa wa Kedar ku kuma hallaka mutanen Gabas. Za a ƙwace tentunansu da garkunansu; za a tafi da mafakanta tare da dukan kayayyakinsu da raƙumansu. Mutane za su yi musu ihu, ‘Razana ko’ina!’ “Ku yi maza ku gudu! Ku zauna a kogo masu zurfi, ku da kuke zama a Hazor,” in ji Ubangiji. “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya shirya muku maƙarƙashiya; ya ƙulla maƙarƙashiya a kanku. “Ku tashi ku kuma fāɗa wa al’umma da sauƙi wadda take zama da ƙarfin hali,” in ji Ubangiji, “al’ummar da ba ta da ƙofofi ko ƙyamare; mutanenta suna zama su kaɗai. Za a washe raƙumansu, garkunansu mai girma za su zama ganima. Zan watsar da waɗanda suke a wurare masu nesa a ko’ina zan kuma kawo musu masifa a kowane gefe,” in ji Ubangiji. “Hazor za tă zama mazaunin diloli, kufai har abada. Ba wanda zai zauna a can; ba wanda zai zauna a cikinta.” Saƙo game da Elam Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Elam, a farkon mulkin Zedekiya sarkin Yahuda. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ga shi, zan karye ƙarfin Elam, zaunannen ƙarfinsu. Zan kawo a kan Elam a kusurwoyi huɗu daga kusurwoyi huɗu na duniya; zan watsar da su zuwa kusurwoyi huɗu, kuma ba al’ummar da masu gudun hijirar Elam ba za su kai ba. Zan ragargaza Elam a gaban maƙiyansu, a gaban waɗanda suke neman ransu; zan kawo masifa a kansu, da zafin fushina,” in ji Ubangiji. “Zan runtume su da takobi sai na kawo ƙarshensu. Zan sa kursiyina a Elam in kuma hallaka sarkinta da fadawanta,” in ji Ubangiji. “Duk da haka zan maido da wadatar Elam a kwanaki masu zuwa,” in ji Ubangiji. Saƙo game da Babilon Ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Irmiya annabi game da Babilon da kuma ƙasar Babiloniyawa. “Ka yi shela ka kuma furta a cikin al’ummai, ka tā da tuta ka kuma furta; kada ku ɓoye kome, amma ku ce, ‘Za a ci Babilon da yaƙi; za a kunyata Bel, Marduk ya cika da tsoro. Siffofinta za su sha kunya gumakanta za su cika da tsoro.’ Al’umma daga arewa za tă fāɗa mata su mai da ƙasar kango. Ba wanda zai zauna a cikinta; mutane da dabbobi za su gudu. “A kwanakin nan, a wannan lokaci,” in ji Ubangiji, “mutanen Isra’ila da mutanen Yahuda gaba ɗaya za su tafi cikin hawaye su nemi Ubangiji Allahnsu. Za su tambayi hanyar zuwa Sihiyona su kuma juya fuskokinsu wajenta. Za su zo su haɗa kansu ga Ubangiji a madawwamin alkawari da ba za a manta da shi ba. “Mutanena sun zama ɓatattun tumaki; makiyayansu sun bauɗar da su suka sa suna ta yawo a cikin duwatsu. Sun yi ta yawo a bisa dutse da tudu suka manta wurin hutunsu. Duk wanda ya same su ya cinye su; abokan gābansu suka ce, ‘Ba mu da laifi, gama sun yi zunubi wa Ubangiji, wurin kiwonsu na gaske, Ubangiji, abin sa zuciyar kakanninsu.’ “Ku gudu daga Babilon; ku bar ƙasar Babiloniyawa, ku zama kamar awakin da suke bi da garke. Gama zan kuta in kuma kawo a kan Babilon haɗinkan manyan al’ummai na arewa. Za su ja dāgār gāba da ita, kuma daga arewa za a ci ta da yaƙi. Kibiyoyinsu za su zama kamar na gwanayen jarumawa waɗanda ba sa dawowa hannu wofi. Saboda haka za a washe Babiloniyawa; dukan waɗanda suka washe ta za su ƙoshi,” in ji Ubangiji. “Saboda kuna farin ciki kuna kuma murna, ku da kuka washe gādona, domin kuna tsalle kamar karsana mai sussuka hatsi kuna kuma haniniya kamar ingarmu. Mahaifiyarku za tă sha babbar kunya; ita da ta haife ku za tă sha kunya. Za tă zama mafi ƙanƙanta na al’ummai, jeji, busasshiyar ƙasa, hamada. Saboda fushin Ubangiji ba za tă zauna a cikinta ba amma za tă zama kufai gaba ɗaya. Duk waɗanda suka wuce Babilon za su ji tsoro su kuma yi tsaki saboda dukan mikinta. “Ku ja dāgā kewaye da Babilon, dukanku waɗanda kuke jan baka. Ku harbe ta! Kada ku rage kibiyoyi, gama ta yi zunubi ga Ubangiji. Ku yi kuwwa a kanta a kowane gefe! Ta miƙa wuya, hasumiyarta ta fāɗi, katangarta sun rushe. Da yake wannan sakayya ce ta Ubangiji, ku ɗauki fansa a kanta; yi mata yadda ta yi wa waɗansu. Ku datse wa Babilon mai shuka, da mai girbi lauje a lokacin girbi. Saboda takobin mai zalunci bari kowa ya koma ga mutanensa, bari kowa ya gudu zuwa ga ƙasarsa. “Isra’ila garke ne da ya watse da zakoki suka kora. Na farkon da ya cinye shi sarkin Assuriya ne; na ƙarshen da ya ragargaza ƙasusuwansa Nebukadnezzar sarkin Babilon ne.” Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Zan hukunta sarkin Babilon da ƙasarsa yadda na hukunta sarkin Assuriya. Amma zan komo da Isra’ila zuwa wurin kiwonsa zai kuwa yi kiwo a Karmel da Bashan; zai ƙosar da marmarinsa a tuddan Efraim da Gileyad. A kwanakin nan, da kuma a lokacin nan,” in ji Ubangiji, “za a yi bincike don laifin Isra’ila, amma ba za a samu ba, kuma don zunubin Yahuda, amma ba za a sami wani abu ba, gama zan gafarta wa raguwar da na rage. “Ku fāɗa wa ƙasar Meratayim da waɗanda suke zama a Fekod. Ku fafara, ku kashe kuma hallaka su sarai,” in ji Ubangiji. “Ku aikata dukan abin da na umarce ku. Hargowar yaƙi tana a ƙasar, hargowar babbar hallaka! Dubi yadda aka karya aka kuma ragargaza gudumar dukan duniya! Dubi yadda Babilon ta zama kufai a cikin al’ummai! Na sa miki tarko, Babilon, kika kuwa kamu kafin ki sani; aka same ki aka kuma kama ki domin kin tayar wa Ubangiji. Ubangiji ya buɗe taskar makamansa ya fitar da makaman fushinsa, gama Maɗaukaki Ubangiji Mai Iko Duka yana da aikin da zai yi a ƙasar Babiloniyawa. Ku zo ku yi gāba da ita daga nesa. Ku buɗe rumbunanta; ku jibga ta kamar tsibin hatsi. Ku hallaka ta sarai kada ku bar mata raguwa. Ku kashe dukan ’yan bijimanta bari su gangara zuwa mayanka! Kaitonsu! Gama ranansu ta zo, lokaci ya yi da za a hukunta su. Ku saurari masu gudun hijira da masu neman mafaka daga Babilon suna furtawa a Sihiyona yadda Ubangiji Allahnmu ya ɗauki fansa, fansa domin haikalinsa. “Ku kira ’yan baka a kan Babilon, dukan waɗanda suke jan baka. Ku yi sansani kewaye da ita duka; kada ku bar wani ya tsira. Ku sāka mata don ayyukanta; ku yi mata yadda ta yi. Gama ta tayar wa Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila. Saboda haka, samarinta za su fāɗi a tituna; za a kawar da dukan sojojinta a wannan rana,” in ji Ubangiji. “Ga shi, ina gāba da ke, ya ke mai girman kai,” in ji Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, “gama ranarki ta zo, lokacin da za a hukunta ki. Mai ɗaga kai za tă yi tuntuɓe ta kuma fāɗi kuma ba wanda zai taimake ta tă tashi; zan hura wuta a garuruwanta da za tă cinye duk waɗanda suke kewaye da ita.” Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “An danne mutanen Isra’ila, haka ma mutanen Yahuda. Dukan waɗanda suka kama su suna riƙe su kankan, suna kin barinsu su tafi. Duk da haka Mai Fansarsu yana da ƙarfi; Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. Zai kāre muradunsu gabagadi don yă kawo hutu ga ƙasarsu, amma rashin hutu ga waɗanda suke zaune a Babilon. “Akwai takobi a kan Babiloniyawa!” In ji Ubangiji “a kan waɗanda suke zama a Babilon da kuma a kan fadawanta da masu hikimarta! Akwai takobi a kan annabawan ƙaryanta! Za su zama wawaye. Akwai takobi a kan jarumawanta! Za su cika da tsoro. Akwai takobi a kan dawakanta da kekunan yaƙinta da kuma dukan baƙin da suke cikin mayaƙanta! Za su zama mata. Akwai takobi a kan dukiyarta! Za a washe su. Fări a kan ruwanta! Za su bushe ƙaf. Gama ƙasa ce ta gumaka, gumakan da za su haukace da tsoro. “Saboda haka halittun hamada da kuraye za su zauna a can, a can kuma mujiya za tă zauna. Ba za a ƙara zauna ko a yi zama a cikinta ba daga tsara zuwa tsara. Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorra tare da maƙwabtan garuruwansu,” in ji Ubangiji “haka ma ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta. “Duba! Ga sojoji suna zuwa daga arewa; babbar al’umma da sarakuna masu yawa suna tahowa daga iyakokin duniya. Suna riƙe da baka da māshi; mugaye ne marasa tausayi. Amonsu ya yi kamar rurin teku yayinda suke hawan dawakansu; suna zuwa kamar mutane a dāgār yaƙi don su fāɗa miki, ya Diyar Babilon. Sarkin Babilon ya ji rahotanni game da su, hannunsa kuma ya yi laƙwas. Wahala ta kama shi, zafi kamar na mace mai naƙuda. Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai dausayi, zan fafare Babilon daga ƙasan nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa domin wannan? Wane ne kamar ni da zai kalubalance ni? Kuma wanda makiyayi zai iya tsaya gāba da ni?” Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Babilon, abin da ya nufa gāba da ƙasar Babiloniyawa. Za a kwashe ƙananan garkensu a tafi; zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su. Da jin an ci Babilon da yaƙi sai duniya ta girgiza; za a ji kukanta cikin al’ummai. Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan zuga ruhun mai hallakarwa a kan Babilon da mutanen Leb Kamai. Zan aika da baƙi zuwa Babilon su casa ta su kuma yi kaca-kaca da ƙasarta; za su yi hamayya da ita a kowane gefe a ranar masifarta. Kada ku bar maharbi yă ja bakansa, kada kuma ku bari yă sa kayan yaƙinsa. Kada ku rage samarinta, ku hallaka sojojinta ƙaf. Za su fāɗi matattu a ƙasar Babilon, da munanan raunuka a titunanta. Gama Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila da Yahuda bai yashe su ba, ko da yake ƙasarsu51.5 Ko kuwa / kuma ƙasar Babiloniyawa cike da take da laifi a gaban Mai Tsarki na Isra’ila. “Ku gudu daga cikin Babilon! Bari kowa yă ceci ransa! Kada a hallaka saboda zunubanta. Gama lokaci ne don ramuwar Ubangiji, zai sāka mata bisa ga alhakinta. Babilon ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashe sun sha ruwan inabinta, saboda haka yanzu sun haukace. Farat ɗaya Babilon za tă fāɗi ta farfashe. Ku yi kuka dominta! Ku samo mata magani saboda azabarta; wataƙila za a iya warkar da ita. “ ‘Da mun warkar da Babilon, amma ba za tă warke ba; mu ƙyale ta kowane yă koma garinsu, gama hukuncinta ya kai sammai, ya yi tsawo kamar gizagizai.’ “ ‘Ubangiji ya baratar da mu; zo mu tafi mu yi shelarsa a Sihiyona mu faɗa abin da Ubangiji Allahnmu ya yi.’ “Ku wasa kibiyoyi, ku ɗauko garkuwoyi! Ubangiji ya zuga sarakunan Medes, domin niyyarsa ce yă hallaka Babilon. Ubangiji zai yi ramuwa, zai yi ramuwa saboda haikalinsa. Ku tā da tuta gāba da katangan Babilon! Ku ƙara matsara, ku kafa masu tsaro, ku shirya kwanto! Ga shi, Ubangiji zai aikata abin da ya faɗa umarninsa a kan mutanen Babilon. Ke da kike zama kusa da ruwaye da kike kuma wadatar dukiya, ƙarshenki ya zo, lokaci ya yi da za a kau da ke. Ubangiji Maɗaukaki ya rantse da zatinsa, ya ce Tabbatacce zan cika ka da mutane kamar fāra, za su kuwa yi sowa don nasara a kanka. (Irmiya 10.12-16) “Ya halicci ƙasa ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa, ya kuma shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa. Sa’ad da ya yi tsawa ruwan da suke sammai sukan yi ruri; yakan sa gizagizai su tashi daga ƙarshen duniya. Yakan tura walƙiya tare da ruwan sama yakan kuma saki iska daga cikin taskokinsa. “Kowane mutum marar azanci ne kuma ba shi da sani; kowane maƙerin zinariya yakan sha kunya daga wurin gumakansa. Siffofinsa na ƙarya ne; babu numfashi a cikinsu. Su marasa amfani ne, abubuwan ba’a ne kawai; sa’ad da lokacin hukuncinsu ya kai, za su hallaka. Wanda yake na wajen Yaƙub ba kamar waɗannan ba ne, gama shi ne Mahalicci dukan abu, har da kabilar abin gādonsa, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa. “Kai ne kulkin yaƙina, kayan yaƙina, da kai ne na ragargaza ƙasashe, da kai ne na hallaka mulkoki, da kai ne na ragargaza doki da mahayi, da kai ne na ragargaza keken yaƙin da matuƙi, da kai ne na ragargaza miji da mata, da kai ne na ragargaza tsoho da saurayi, da kai ne na ragargaza saurayi da budurwa, da kai ne na ragargaza makiyayi da garke, da kai ne na ragargaza manoma da dawakan noma, da kai ne na ragargaza masu mulki da shugabanni. “Zan sāka wa Babilon da dukan mazaunan Babilon a idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona,” in ji Ubangiji. “Ga shi, ina gāba da kai, ya ke dutse mai hallakarwa, wadda ta hallaka duniya duka,” in ji Ubangiji. “Zan miƙa hannuna gāba da ke, zan mirgina ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, zan maishe ki ƙonannen dutse. Ba za a ɗauki dutsen yin kusurwa daga gare ki ba ko na kafa harsashen gini, gama za ki zama marar amfani har abada,” in ji Ubangiji. “Ku tā da tuta a ƙasa! Ku busa ƙahoni a cikin ƙasashe! Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita, ku kira waɗannan mulkokin gāba da ita. Ararat, Minni, da Ashkenaz. A naɗa shugaba gāba da ita; ku shirya dawakai kamar fāra. Ku shirya ƙasashe don yaƙi da ita, sarakunan Medes, gwamnoninsu da dukan masu shugabancinsu da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu. Ƙasa ta girgiza tana makyarkyata saboda nufin Ubangiji na gāba da Babilon ya tabbata, nufinsa na mai da ƙasar Babilon kufai don kada kowa yă zauna a can. Sojojin Babilon sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata. An sa wa wuraren zamanta wuta, an karya ƙyamaren ƙofofin garinta. Maguji yana biye da maguji a guje, jakada yana biye da jakada, don su faɗa wa sarkin Babilon, cewa an ci birninsa a kowane gefe. An ƙwace mashigai aka ƙone fadamu da wuta, sojoji kuma suka giggice.” Ni Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila na ce, “’Yar Babilon kamar daɓen masussuka a lokacin da ake sussuka, ba da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.” “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya cinye mu, ya sa muka rikice, ya maishe mu kamar tulun da babu kome a cikinsa. Ya cinye mu kamar yadda dodon ruwa yakan yi ya kuma cika cikinsa da kayan marmarinmu, sa’an nan kuma ya yi amanmu. Bari abin da aka yi wa jikinmu yă kasance a bisa Babilon,” in ji mazaunan Sihiyona. “Bari jininmu yă kasance a kan waɗanda suke zama a Babilon,” in ji Urushalima. Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “Duba, zan tsaya muku, zan ɗaukar muku fansa, zan sa tekunta kafe in kuma sa maɓulɓulanta su ƙafe. Babilon za tă zama tarin juji, wurin zaman diloli, abin ƙyama da abar ba’a, inda ba kowa. Mutanenta duk suna ruri kamar zakoki, suna gurnani kamar ’ya’yan zaki. Amma sa’ad da aka farkar da su, zan yi musu biki in sa su sha su bugu, domin yi sowa da dariya, sa’an nan su shiga barcin da ba za su farka ba,” in ji Ubangiji. “Zan sauko da su kamar tumaki zuwa mayanka, kamar raguna da bunsurai. “Yadda za a ci Sheshak, taƙamar duniya duka za tă daina! Babilon za tă zama abar ƙyama a cikin al’ummai! Teku zai malalo a kan Babilon, raƙumansa masu hauka za su rufe ta. Garuruwanta sun zama abin kufai, za tă zama hamada inda ba ruwa, ƙasar da ba mazauna, ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta. Zan hukunta Bel a Babilon, in sa ya yi aman abin da ya haɗiye. Ƙasashe ba za su ƙara bumbuntowa wurinsa ba. Katangan Babilon kuwa za tă rushe! “Ku fito daga cikinta, jama’ata! Ku tsere da ranku! Ku tsere daga zafin fushin Ubangiji. Kada zuciyarku tă yi suwu ko ku ji tsoro sa’ad da aka ji labarin a ƙasar, labari guda a wannan shekara, wani kuma a ta biye, labarin hargitsi a ƙasar mai mulki ya tasar wa mai mulki. Gama kwanaki tabbatacce suna zuwa, sa’ad da zan hukunta gumakan Babilon, zan kunyatar da dukan ƙasar kuma matattunta duk za su kwanta a cikinta. Sa’an nan sama da ƙasa da dukan abin da yake cikinsu, za su yi sowa ta murna a kan Babilon, gama daga arewa masu hallakarwa su auko mata,” in ji Ubangiji. “Babilon za tă fāɗi saboda kisassun mutanen Isra’ila, kamar dai yadda kisassu dukan duniya suka fāɗi saboda Babilon. Ku waɗanda kuka tsere wa takobi, ku gudu kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a ƙasa mai nesa, ku kuma yi ta tunani a kan Urushalima.” “Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana kunya ta rufe mu, domin baƙi sun shiga tsarkakan wurare na gidan Ubangiji.” “Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta gumakanta, da kuma a dukan ƙasarta waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi. Ko da Babilon za tă kai sararin sama ne, ta gina kagaranta mai ƙarfi, duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta,” in ji Ubangiji. “Ku ji muryar kuka daga Babilon, Da hargowar babbar hallakarwa daga ƙasar Babiloniyawa! Gama Ubangiji zai rushe Babilon, zai sa ta ƙame bakinta na alfarma. Sojoji za su yi ta kutsawa kamar raƙuman ruwa; suna tā da muryoyinsu. Gama mai hallakarwa ya auka wa Babilon, a kama sojojinta, a kuma kakkarya bakkunansu. Gama Ubangiji shi Allah ne mai sakayya; zai yi sakayya sosai. Zan sa mahukuntanta da masu hikimarta, gwamnoninta, shugabanninta da sojojinta su sha su bugu; za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” in ji Sarkin, mai suna Ubangiji Maɗaukaki. Ni Ubangiji Maɗaukaki, na ce, “Za a baje katangan nan na Babilon mai kauri za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta; mutane sun wahalar da kansu a banza, al’umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.” Jawabin da annabi Irmiya ya ba Serahiya, ɗan Neriya, wato, jikan Ma’asehiya, lokacin da ya tafi tare da Zedekiya, Sarkin Yahuda, zuwa Babilon a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Serahiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi. Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babilon, wato, dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babilon. Irmiya kuwa ya ce wa Serahiya, “Lokacin da ka kai Babilon, sai ka karanta dukan maganan nan. Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’ Sa’ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa’an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yuferites. Sa’an nan ka ce, ‘Haka Babilon za tă nutse, ba za tă ƙara tashi ba saboda masifar da zan kawo mata. Mutanenta kuwa za su fāɗi.’ ” Wannan shi ne ƙarshen kalmomin Irmiya. Fāɗuwar Urushalima (2 Sarakuna 24.18–25.30; 2 Tarihi 36.11-21) Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal, ’yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna. Sarki Zedekiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehohiyakim ya yi. Al’amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra’ila da Yahuda, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala. Zedekiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babilon. A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya, Sarkin Yahuda, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina katanga kewaye da ita. An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya. A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci. Sai aka huda katangan birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa’ad da Babiloniyawa suke kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba. Amma sojojin Babiloniyawa suka runtumi sarki Zedekiya, suka ci masa a filayen Yeriko. Dukan sojoji suka yashe shi. Da aka kama Zedekiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babilon a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babilon ya yanke masa shari’a. Sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuda a Ribla. Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babilon inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu. A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima. Sai ya ƙone haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gine-gine masu alfarman da suke Urushalima. Sojojin Babiloniyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan katangan Urushalima. Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon. Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki. Babiloniyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babilon. Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar haikali. Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe. Tagullar da sarki Solomon ya yi wa haikalin Ubangiji da ita, wato, ginshiƙai biyu, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna. Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki. A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman. Akwai siffofin rumman tasa’in da shida da ake gani a gefen. Dukan siffofin rumman da suke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne. Shugaban matsara kuma ya ɗauki Serahiya babban firist, da Zefaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar, ya tafi da su. Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai ’yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su. Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babilon a Ribla, Sarkin Babilon kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat. Haka aka tafi da mutanen Yahuda bautar talala, daga ƙasarta. Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta. A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa 3,023; a shekara ta goma sha takwas ta sarautar Nebukadnezzar, ya tafi da Yahudawa daga Urushalima 832; a shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa 745. Jimillarsu duka 4,600 ne. An saki Yehohiyacin (2 Sarakuna 25.27-30) A shekarar da Ewil-Merodak ya zama Sarkin Babilon, sai ya nuna wa Yehohiyacin Sarkin Yahuda alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yehohiyacin bauta. Ewil-Merodak ya nuna wa Yehohiyacin alheri, ya ba shi matsayi na daraja fiye da waɗansu sarakunan da aka kai su bautar talala a Babilon tare da shi. Yehohiyacin ya tuɓe tufafin kurkuku, ya riƙa cin abinci kullum a teburin sarki, har dukan sauran kwanakin ransa. Kowace rana akan ba shi kyauta bisa ga umarnin sarkin Babilon, saboda bukatarsa. Haka aka yi masa har rasuwarsa.