- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Mahukunta
Mahukunta
Mahukunta
Mah
Mahukunta
Isra’ila sun yaƙi sauran Kan’aniyawa
Bayan da Yoshuwa ya rasu, Isra’ilawa suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne zai fara tafiya don yă yaƙi Kan’aniyawa dominmu?”
Sai Ubangiji ya ce, “Yahuda zai tafi. Na riga na ba da ƙasar a hannunsu.”
Sa’an nan mutane Yahuda suka ce wa mutanen Simeyon “Ku zo tare da mu a yankin da aka ba mu rabon mu don mu yaƙi Kan’aniyawa. Mu ma mu bi ku wurin naku.” Saboda haka mutanen Simeyon suka tafi tare da su.
Sa’ad da Yahuda ya fāɗa musu, Ubangiji kuwa ya ba da Kan’aniyawa da Ferizziyawa a hannunsu, suka kuwa kashe mutum dubu goma a Bezek. A can suka iske Adoni-Bezek, suka yaƙe shi, suka fatattaki Kan’aniyawa da Ferizziyawa. Sai Adoni-Bezek ya gudu, amma suka bi shi suka kama shi, suka yayyanka manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa.
Sa’an nan Adoni-Bezek ya ce, “Sarakuna saba’in waɗanda aka yayyanka manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, sun yi kalan abinci a ƙarƙashin teburina. Ga shi yanzu Allah ya rama abin da na yi musu.” Suka zo da shi Urushalima, a can kuwa ya mutu.
Mutanen Yahuda suka yaƙi Urushalima ita ma suka ci ta. Suka karkashe mutanen birnin suka cinna mata wuta.
Bayan wannan, mutanen Yahuda suka gangara suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, Negeb, da gindin tuddai a yammanci. Suka ci gaba suka yaƙi Kan’aniyawan da suke zaune a Hebron (wadda dā ake kira Kiriyat Arba) suka kuma ci Sheshai, Ahiman da Talmai da yaƙi.
Daga nan kuma suka ci gaba suka yaƙi mutanen da suke zaune a Debir (da ake kira a dā Kiriyat Sefer).
Sai Kaleb ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat Sefer ya kuma ci ta da yaƙi, zan ba shi ’yata Aksa yă aura.” Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb ya ci birnin, saboda haka Kaleb ya ba shi ’yarsa Aksa ya aura.
Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ta zuga shi1.14 Da Ibraniyanci; Seftuwajin da Bulget Otniyel, ya zuga ta yă roƙi mahaifinta fili. Sa’ad da ta sauko daga jakinta, sai Kaleb ya ce mata, “Me zan yi miki?”
Sai ta ce, “Ka yi mini alheri na musamman. Da yake ka ba ni ƙasa a Negeb, to, sai ka ba ni maɓulɓulan ruwa kuma.” Sai Kaleb ya ba ta maɓulɓulan bisa da kuma na ƙasa.
Zuriyar surukin Musa, Keniyawa, suka haura daga Birnin dabino1.16 Wato, Yeriko tare da mutanen Yahuda don su zauna cikin mutanen Hamadan Yahuda a cikin Negeb kusa da Arad.
Sa’an nan mutanen Yahuda suka tafi tare da ’yan’uwansu mutanen Simeyon suka fāɗa wa Kan’aniyawan da suke zaune cikin Zefat, suka kuwa hallaka birnin gaba ɗaya. Saboda haka aka kira wurin Horma.1.17 Horma yana nufin hallaka. Mutanen Yahuda kuma suka ci1.18 Da Ibraniyanci; Seftuwajin Yahuda bai ci Gaza, Ashkelon, da Ekron, kowace birni tare da yankinsa.
Ubangiji kuwa yana tare da mutane Yahuda. Suka mallaki ƙasar tudu, amma ba su iya suka kori mutanen daga filaye ba, domin suna da keken yaƙin ƙarfe. Yadda Musa ya yi alkawari, sai aka ba Kaleb Hebron, wanda ya kori daga cikinta ’ya’ya maza uku na Anak. Ko da yake mutanen Benyamin sun kāsa su kori Yebusiyawa, waɗanda suke zaune a Urushalima; har yă zuwa yau, Yebusiyawa suna zaune a can tare da mutanen Benyamin.
To, gidan Yusuf suka auka wa Betel, Ubangiji kuwa yana tare da su. Sa’ad da suka aike mutane don su leƙi asirin Betel (da dā ake kira Luz), ’yan leƙen asirin suka ga wani ya fito daga birnin sai suka ce masa, “Ka nuna mana yadda za mu shiga birnin, mu kuwa za mu yi maka alheri.” Saboda haka ya nuna musu, suka kuwa hallaka birnin, suka bar mutumin da dukan iyalinsa da rai. Sa’an nan ya tafi ƙasar Hittiyawa, inda ya gina birni ya kuma kira shi Luz, haka ake kira birnin har wa yau.
Amma Manasse ba su kori mutane Bet-Sheyan ko Ta’anak ko Dor ko Ibileyam ko Megiddo tare da ƙauyukansu ba, gama Kan’aniyawa sun dāge su zauna a wannan ƙasa. Sa’ad da Isra’ila ta yi ƙarfi, sai suka tilasta Kan’aniyawa yin aikin gandu amma ba su kore su gaba ɗaya ba. Haka Efraim ma bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Gezer ba, amma Kan’aniyawa suka ci gaba da zama tare da su. Haka kuma Zebulun bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Kitron da Nahalol, waɗanda suka rage a cikinsu ba; sai dai sun sa su aikin gandu. Haka Asher ma bai kori waɗanda suke zama a Akko ko Sidon ko Ahlab ko Akzib ko Helba ko Afik ko kuma Rehob ba, kuma saboda wannan ne mutanen Asher suke zaune cikin mazaunan ƙasar Kan’aniyawa. Haka kuma Naftali bai kori waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh ko Bet-Anat; amma mutanen Naftali su ma suna zama a ciki Kan’aniyawa mazaunan ƙasar, waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh da Bet-Anat kuwa suka zama masu yi musu aikin gandu. Amoriyawa suka matsa wa mutanen Dan a ƙasar tudu, ba su yarda musu su gangaro zuwa filaye ba. Su Amoriyawa kuma suka dāge su zauna a Dutsen-Heres, Aiyalon, da Sha’albim. Amma yayinda mutanen Yusuf suka ƙara ƙarfi, sai suka su yin musu aikin gandu. Iyakar Amoriyawa kuwa daga Mashigin Kunama1.36 Da Ibraniyanci Akrabbim zuwa Sela da kuma zuwa gaba.
Mala’ikan Ubangiji a Bokim
Mala’ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim ya ce, “Na hauro da ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba wa kakanninku. Na ce, ‘Ba zan taɓa tā da yarjejjeniyata da ku ba, ku kuma kada ku shiga wata yarjejjeniya da mazaunan ƙasan nan, sai dai za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya mini ba. Me ya sa kuka yi haka? Saboda haka ina gaya muku cewa ba zan kore su a gabanku ba; za su zama muku ƙaya, gumakansu kuma za su zama muku tarko.”
Da mala’ikan Ubangiji ya faɗa wa dukan Isra’ilawa waɗannan abubuwa, sai mutane suka yi kuka mai zafi, sai suka sa wa wannan wuri suna, Bokim.2.5 Bokim yana nufin masu kuka. A nan suka miƙa hadaya a gaban Ubangiji.
Rashin biyayya da shan kayi
Bayan Yoshuwa ya sallami Isra’ilawa, sai suka tafi don su mallaki ƙasar, kowa da nasa gādon. Mutane suka bauta wa Ubangiji duk tsawon kwanakin Yoshuwa da na dattawan da suka rayu bayansa waɗanda suka ga manyan abubuwan da Ubangiji ya yi wa Isra’ila.
Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekara ɗari da goma. Aka binne shi a ƙasar gādonsa, a Timnat Heres2.9 An kuma santa kamar Timnat Sera (dubi Yosh 19.50 da Yosh 24.30). a ƙasar tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash.
Bayan tsaran nan duka suka rasu, sai wata tsara ta taso wadda ba tă san Ubangiji ko abin da ya yi wa Isra’ila ba. Sai Isra’ilawa suka yi mugaye abubuwa a gaban Ubangiji suka kuma bauta Ba’al. Suka yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar. Suka bi suka kuma bauta alloli dabam-dabam na mutanen da suke kewaye da su. Suka tsokani Ubangiji ya yi fushi domin sun bar shi suka bauta wa Ba’al da Ashtarot. Cikin fushinsa a kan Isra’ila Ubangiji ya ba da su ga hannun waɗanda suka kawo musu hari suka washe su. Ya sayar da su ga abokan gābansu da suke kewaye da su, waɗanda ba za su iya yin tsayayya da su ba. Duk sa’ad da Isra’ila suka fita yaƙi, Ubangiji yakan yi gāba da su don a ci su a yaƙi, kamar dai yadda ya rantse musu. Suka kuwa shiga wahala ƙwarai.
Sa’an nan Ubangiji ya naɗa mahukunta,2.16 Ko kuwa shugabanni; daidai kamar a ayoyi 17-19. waɗanda suka cece su daga hannun waɗannan musu hari. Duk da haka ba su saurari mahukuntansu ba amma sai suka shiga ha’inci da waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Ba kamar kakanninsu ba, nan da nan suka kauce daga hanyar da kakanninsu suka bi, hanyar biyayya ga umarnan Ubangiji. Duk sa’ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan kasance tare da mahukuncin, yă kuma cece su daga hannun abokan gāba, muddin mahukuncin yana a raye; gama Ubangiji yakan ji tausayinsu yayinda suke gunaguni ƙarƙashin waɗanda suka danne su suke kuma gasa musu azaba. Amma sa’ad da mahukuncin ya mutu, mutanen suka koma hanyar da ta fi ta kakanninsu muni, sukan bi waɗansu alloli suna bauta musu. Suka ƙi barin mugun ayyukansu da taurin zuciyarsu.
Saboda haka sai Ubangiji ya fusata da Isra’ila ya ce, “Domin wannan al’umma ta tā da yarjejjeniyar da na yi da kakanninsu ba su kuwa saurare ni ba, ba zan ƙara kori wata al’ummar da Yoshuwa ya bari sa’ad da ya rasu ba. Zan yi amfani da su in gwada Isra’ila in ga ko za su bi hanyar Ubangiji su kuma yi tafiya a cikinta kamar yadda kakanninsu suka yi.” Ubangiji ya bar waɗannan al’ummai su kasance; bai kore su nan take ta wurin ba da su a hannun Yoshuwa ba.
Waɗannan su ne al’umman da Ubangiji ya bari don yă gwada duk waɗannan Isra’ilawan da ba su san yaƙi a Kan’ana ba (ya yi haka ne domin yă koya wa zuriyar Isra’ilawa waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba), sarakuna biyar na Filistiyawa, dukan Kan’aniyawa, Sidoniyawa, da kuma Hiwiyawan da suke zaune a duwatsun Lebanon daga Dutsen Ba’al-Hermon zuwa Lebo3.3 Ko kuwa zuwa mashigi zuwa Hamat. An bar su domin su gwada Isra’ilawa a ga ko za su yi biyayya da umarnin Ubangiji, wanda ya ba wa kakanninsu ta wurin Musa.
Isra’ilawa suka zauna tare da Kan’aniyawa da Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa. Suka auri ’ya’yansu mata, su ma suka bar ’ya’yansu maza suka auri ’ya’yansu mata, suka kuma yi wa gumakansu sujada.
Otniyel
Isra’ilawa suka aikata mugunta a gaban Ubangiji; suka manta da Ubangiji Allahnsu suka kuma bauta wa Ba’al da Ashera. Fushin Ubangiji kuwa ya yi ƙuna a kan Isra’ila har ya sayar da su ga Kushan-Rishatayim sarkin Aram-Naharayim,3.8 Wato, Arewancin Mesofotamiya a wurinsa ne Isra’ilawa suka zama bayi shekara takwas. Amma da suka yi kuka ga Ubangiji, sai ya tad musu da mai ceto, Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb wanda ya cece su. Ruhun Ubangiji ya sauko masa, domin yă zama mahukuncin3.10 Ko kuwa shugaba Isra’ila yă kuma je yaƙi. Ubangiji ya bayar da Kushan-Rishatayim sarkin Aram a hannun Otniyel, ya kuwa sha ƙarfinsa. Saboda haka ƙasar ta zauna da lafiya shekara arba’in har sai da Otniyel ɗan Kenaz ya rasu.
Ehud
Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda sun aikata wannan mugunta sai Ubangiji ya ba wa Eglon sarkin Mowab ƙarfi a kan Isra’ila. Da ya sami Ammonawa da Amalekawa suka haɗa hannu tare, sai Eglon ya tafi ya auka wa Isra’ila, suka ƙwace Birnin Dabino.3.13 Wato, Yeriko Isra’ilawa suka zama bayin Eglon sarkin Mowab shekara goma sha takwas.
Isra’ilawa suka sāke yin kuka ga Ubangiji, ya kuwa ba su mai ceto, Ehud, wani bahago, ɗan Gera daga kabilar Benyamin. Isra’ilawa suka aike shi da haraji wurin Eglon sarkin Mowab. To, Ehud ya riga ya ƙera takobi mai kaifi biyu mai tsawo wajen kamu ɗaya da rabi, wanda ya yi ɗamara da shi a cinyarsa ta dama ƙarƙashin rigarsa. Ya kai wa Eglon sarkin Mowab harajin, wanda yake mai ƙiba ne. Bayan Ehud ya ba da harajin, sai ya sallame mutanen da suka ɗauko harajin. A wajen gumaka3.19 Ko kuwa wurin fashe duwatsu; haka ma a aya 26. kusa da Gilgal, shi kansa ya juya ya koma ya ce, “Ranka yă daɗe, ina da saƙo na asiri dominka.”
Sarkin ya ce, “Ku ba mu wuri!” Sai dukan fadawansa suka fita.
Sai Ehud ya matso yayinda shi kuwa yake zaune shi kaɗai a ɗakin sama mai sanyi a fadansa3.20 Ma’anar wannan magana a Ibraniyanci babu tabbas. ya ce, “Ina da saƙo daga wurin Allah dominka.” Sarki ya tashi daga kujerarsa, Ehud ya kai hannun hagunsa, ya zaro takobi daga cinyar ƙafar damansa ya soki sarki a ciki. Har ƙotar ma ta shige ciki, takobin kuma ya fito ta bayansa. Ehud bai zare takobin ba, kitse kuwa ya rufe shi. Sa’an nan Ehud ya fita daga shirayin;3.23 Ma’anar kalman nan a Ibraniyanci ba a tabbatar ba. ya rufe ƙofar ɗakin saman, ya kuma kulle su.
Bayan da ya tafi, bayin sarki suka zo suka tarar duk ƙofofin ɗakin sama suna kulle, suka ce, “Wataƙila yana bayan gari ne a ɗakin ciki.” Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ƙofar ba, sai suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe. Sai ga shugabansu a ƙasa matacce.
Yayinda suke fama jira, Ehud ya riga ya yi gaba. Ya bi ta wajen gumaka zuwa Seyira. Da ya iso can, sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuma suka gangaro tare da shi daga tuddai, shi kuwa yana jagorarsu.
Ya umarce su ya ce, “Ku bi ni, gama Ubangiji ya ba Mowab abokin gābanku a hannunku.” Haka suka gangaro tare da shi suna mallaki mashigin Urdun da ta shiga zuwa Mowab, ba su yarda wani ya haye ba. A lokacin sun kashe mutanen Mowab dubu goma, dukansu jarumawa da masu ji da ƙarfi; ba ko ɗaya da ya tsira. A wannan rana aka mai da Mowab bayin Isra’ila, ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya shekara takwas.
Shamgar
Bayan Ehud, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya karkashe Filistiyawa ɗari shida da sandar korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra’ila.
Debora
Bayan rasuwar Ehud, Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Saboda haka Ubangiji ya sayar da su ga Yabin sarkin Kan’ana wanda yake mulki a Hazor. Shugaban mayaƙansa shi ne Sisera, wanda yake zaune a Haroshet Haggoyim. Domin Yabin sarkin Kan’ana yana da kekunan yaƙin ƙarfe ɗari tara, ya ji wa Isra’ilawa ƙwarai har shekara ashirin, sai suka yi kuka ga Ubangiji, don taimako.
A lokacin Debora annabiya, matar Laffidot ce take bi4.4 A al’adance mahukunta da Isra’ila. Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a. Sai ta aika a kira mata Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali, ta ce masa, “Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce ka, ‘Je ka, ka ɗauki mutane Naftali da na Zebulun dubu goma tare da kai, ka yi jagoransu zuwa Dutse Tabor. Zan jawo Sisera, shugaban mayaƙan Yabin, da keken yaƙinsa da mayaƙansa zuwa Kogin Kishon in ba da su a hannunku.’ ”
Barak ya ce, “In kika tafi tare da ni, zan tafi; amma in ba ki zo tare da ni ba, ba zan tafi ba.”
Debora ta ce, “To, shi ke nan, zan tafi tare da kai. Amma saboda yadda ka ɗauki wannan batun, darajar ba za tă zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Saboda haka Debora ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh, a can Barak ya kira Zebulun da Naftali. Mutum dubu goma suka kuma bi shi, Debora kuma tana tare da shi.
To, Heber Bakene ya riga ya bar Keniyawa, zuriyar Hobab, ɗan’uwan4.11 Ko kuwa baban matar Musa, ya kafa tentinsa wajen babban itace a Za’anannim kusa da Kedesh.
Sa’ad da aka gaya wa Sisera cewa Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa dutsen Tabor, sai Sisera ya tattara keken yaƙinsa na ƙarfe ɗari tara wuri ɗaya da dukan mutanen da suke tare da shi daga Haroshet Haggoyim zuwa Kogin Kishon.
Sa’an nan Debora ta ce wa Barak, “Je ka! Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka. Ba Ubangiji ya riga ya sha gabanka?” Saboda haka Barak ya gangara zuwa Dutsen Tabor, da mutum dubu goma biye da shi. Da matsowar Barak, Ubangiji ya murƙushe Sisera da dukan sarakunansa da mayaƙansa da takobi, Sisera kuwa ya gudu da ƙafa ya bar keken yaƙinsa. Amma Barak ya bi keken yaƙin da mayaƙan har Haroshet Haggoyim. Aka karkashe dukan mayaƙan Sisera ba ko ɗayan da ya tsira.
Amma Sisera, ya tsere da ƙafa zuwa tentin Yayel, matar Heber Bakene, domin suna da abokantaka da Yabin sarkin Hazor da kuma kabilar Heber Bakene.
Yayel ta fito ta taryi Sisera ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka shigo, ka shigo ciki. Kada ka ji tsoro.” Saboda haka ya shiga cikin tentinta, sai ta rufe shi da bargo.
Sai ya ce, “Ina roƙonki, ki ba ni ruwa in sha, ina jin ƙishirwa.” Sai ta buɗe salkar madara, ta ba shi ya sha, sai ta kuma rufe shi.
Ya ce mata, “Ki tsaya a ƙofar tenti, in wani ya zo ya tambaye ki, ‘Akwai wani a nan?’ Ki ce masa ‘a’a.’ ”
Amma Yayel, matar Heber, ta ɗauki turken tenti da guduma ta tafi wurinsa da sauri sa’ad da yake barci saboda gajiya. Ta kafa masa turken a gindin kunnensa ta haɗa shi da ƙasa, har ya mutu.
Sai ga Barak mai bin sawun Sisera, Yayel kuwa ta fito don marabtarsa, ta ce, “Shigo, zan nuna maka mutumin da kake nema.” Saboda haka ya shiga ciki tare da ita, sai ga Sisera kwance da turken a gindin kunnensa, matacce.
A ranar Allah ya yi kaca-kaca da Yabin, sarkin Kan’ana a gaban Isra’ila. Isra’ilawa kuwa suka ƙara ƙarfi gāba da Yabin, sarkin Kan’aniyawa, har suka hallaka shi.
Waƙar Debora
A wannan rana ce Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa.
“Sa’ad da ’ya’yan sarki a Isra’ila suka yi jagora,
sa’ad da mutane suka niyya su ba da kansu,
suna yabon Ubangiji!
“Ya sarakuna, ku ji! Ku saurara, ku masu mulki!
Zan yi waƙa ga Ubangiji, zan yi waƙa;
zan yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.
“Ya Ubangiji, sa’ad da ka bar Seyir,
sa’ad da ka yi tafiya daga ƙasar Edom,
ƙasa ta girgiza, sammai suka zubo,
gizagizai sun zubo da ruwa.
Duwatsu suka girgizu a gaban Ubangiji, Wannan na Sinai,
a gaban Ubangiji, Allah na Isra’ila.
“A zamanin Shamgar ɗan Anat,
a zamanin Yayel, an yashe dukan hanyoyi;
matafiye suka bi hanyoyin da suka yi kona-kona.
Rayuwar ƙauye5.7 Ko kuwa Jarumawa a Isra’ila ta daina,
ta daina sai da ni, Debora, na taso,
na taso mahaifiya a Isra’ila.
Sa’ad da suka zaɓi sababbin alloli,
sai ga yaƙi a ƙofofin birnin,
ba a kuwa ga garkuwa ko māshi
a cikin mutum dubu arba’in a Isra’ila ba.
Zuciyata tana tare da ’ya’yan sarakunan Isra’ila,
tare da masu niyyar ba da kansu da yardan rai cikin mutane.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
“Ku da kuke hawan fararen jakuna,
kuna zama a sirdin barguna,
da ku da kuke tafiya a kan hanya,
ku kula da muryoyin mawaƙa a wuraren ruwaye.
Suna faɗi ayyukan adalcin Ubangiji,
ayyukan adalcin mayaƙansa a Isra’ila.
“Sa’an nan mutanen Ubangiji
suka gangara zuwa ƙofofin birni.
‘Ki farka, ki farka, Debora!
Ki farka, ki farka, ki tā da waƙa!
Ka farka, ya Barak!
Ka ta sa kamammunka gaba, ya ɗan Abinowam.’
“Sa’an nan waɗanda aka bari
suka sauko zuwa wajen shugabanni;
mutane na Ubangiji
suka zo wurina tare da masu ƙarfi.
Waɗansu suka zo daga Efraim, waɗanda ainihinsu daga Amalek ne;
Benyamin yana tare da mutanen da suka bi ka.
Daga Makir, shugabannin sojoji suka gangaro,
daga Zebulun waɗanda suke riƙe da sandan komanda suka fito.
’Ya’yan sarautar Issakar suna tare da Debora;
I, Issakar yana tare da Barak,
yana binsa a guje zuwa kwari.
A yankunan Ruben
aka kuma bincike zuciya sosai.
Don me kuka tsaya a wutar sansani
don ku ji makiyaya suna kiran garkuna?
A yankunan Ruben
aka yi bincike zuciya sosai.
Gileyad ya tsaya gaban Urdun.
Kai kuma Dan, don me ka ka yi ta zama a wajen jiragen ruwa?
Asher ya ci gaba da kasance a bakin teku
ya kasance a wuraren zamansa.
Mutanen Zebulun sun kasai da rayukansu;
haka ma Naftali a bakin dāgā.
“Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi;
sarakunan Kan’ana sun yi yaƙi
a Ta’anak a gefen ruwan Megiddo,
amma ba su ɗauki azurfa, ko ganima ba.
Daga sama taurari suka yi faɗa,
daga bakin tekuna suka yi yaƙi da Sisera.
Kogin Kishon ya kwashe su,
tsohon kogi, kogin Kishon.
Ci gaba raina; ka ƙarfafa!
Sa’an nan kofatan dawakai suka ƙwaƙula,
suna sukuwa, haka dawakansa masu ƙarfi suke tafiya.
Mala’ikan Ubangiji ya ce, ‘Ka la’anci Meroz.’
‘Ka la’anci mutanensa sosai,
domin ba su kawo wa Ubangiji taimako ba,
su kawo wa Ubangiji taimako a kan masu ƙarfi ba.’
“Mafi albarka a ciki mata ta zama Yayel
matar Heber Bakene,
mafi albarka na mata masu zama a alfarma.
Ya nemi ruwa, ta kuwa ta ba shi madara;
a ƙwaryar da ta dace da sarakuna ta kawo masa kindirmo.
Hannunta ya ɗauki turken tenti,
da hannunta na dama ta ɗauko guduma.
Ta bugi Sisera, ta ragargaza kansa,
ta ragargaza ta huda kunnensa.
A ƙafafunta ya fāɗi,
ya fāɗi; a can ya kwanta.
A ƙafafunta ya fāɗi, ya fāɗi;
a can ya fāɗi, matacce.
“Ta taga mahaifiyar Sisera ta leƙa;
a bayan madogarar ƙofa ta yi ta ihu,
‘Me ya sa keken yaƙinsa ta daɗe ba tă dawo ba?
Me ya sa dawakan keken yaƙinsa ba su dawo da wuri ba?’
Mafi hikima cikin ’yan matanta suka amsa mata,
tabbatacce, ta ci gaba ta ce wa kanta,
‘Ba nema suke su raba ganima ba,
yarinya guda ko biyu wa kowane mutum,
riguna masu launi a matsayin ganima don Sisera,
riguna masu ado,
riguna masu ado sosai don wuyata,
dukan wannan a matsayin ganima?’
“Ta haka bari dukan abokan gābanka su hallaka, ya Ubangiji!
Amma bari waɗanda suke ƙaunarka su zama kamar rana
sa’ad da ta fito da ƙarfinta.”
Sa’an nan ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba’in.
Gideyon
Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, sai ya ba da su ga Midiyawa shekara bakwai. Da Midiyawa suka matsa musu sosai, sai Isra’ilawa suka yi wa kansu mafakai a rammukan duwatsu, kogona da kuma mafaka. Duk lokacin da Isra’ilawa suka yi shuka sai Midiyawa da Amalekawa da waɗansu mutane daga gabashi sukan kai musu hari. Sukan yi sansani a ƙasar sun lalatar da hatsi har zuwa Gaza kuma ba sa barin wani abu mai rai wa Isra’ila, ko tumaki ko shanu ko jakuna. Sukan zo da dabbobinsu da tentinsu kamar tarin fāri. Yana da wuya a ƙidaya yawan mutanen da kuma raƙumansu; sukan mamaye ƙasar don su lalatar da ita. Midiyawa suka talauce Isra’ilawa ƙwarai, har ya sa suka yi kuka ga Ubangiji don taimako.
Sa’ad da Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji saboda Midiyawa, sai ya aika musu da annabi, wanda ya ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce na fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta. Na ƙwace ku daga ikon Masarawa da kuma daga dukan hannuwan masu danniya. Na kore su a gabanku na kuma ba ku ƙasarsu. Na ce muku, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku; kada ku bauta allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a ƙasarsu.’ Amma ba ku saurare ni ba.”
Sai mala’ikan Ubangiji ya zo ya zauna a ƙarƙashin itacen oak a Ofra na Yowash mutumin Abiyezer, inda ɗansa Gideyon yake sussukar alkama a wurin matsin inabi don yă ɓoye daga Midiyawa. Sa’ad da mala’ikan Ubangiji ya bayyana wa Gideyon, sai ya ce masa, “Ubangiji yana tare da kai, jarumi.”
Gideyon ya ce, “Ranka yă daɗe, in Ubangiji yana tare da mu, me ya sa waɗannan abubuwa suka faru da mu? Ina dukan abubuwan al’ajabinsa waɗanda kakanninmu suka gaya mana game su sa’ad da suka ce, ‘Ashe, ba Ubangiji ne ya fitar da mu daga Masar ba?’ Amma yanzu Ubangiji ya rabu da mu ya kuma sa mu hannun Midiyawa.”
Sai Ubangiji ya juya wajensa ya ce, “Ka je da ƙarfin da kake da shi ka ceci Isra’ila daga hannun Midiyawa. Ba Ni ne nake aikan ka ba?”
Gideyon ya ce, “Amma Ubangiji,6.15 Ko kuwa Ranka yă daɗe yaya zan iya ceci Isra’ila? Kabilata ce marar ƙarfi duka a Manasse, kuma ni ne ƙarami a iyalina.”
Ubangiji ya ce, “Zan kasance tare da kai, za ka kuwa fatattake dukan Midiyawa gaba ɗaya.”
Gideyon ya ce, “In lalle na sami tagomashi a gabanka, to, ka ba ni wata alamar da ta nuna lalle kai kake magana da ni. Ina roƙonka ka dakata har in komo in kawo maka hadayata in ajiye a gabanka.”
Sai Ubangiji ya ce, “Zan jira har ka dawo.”
Sai Gideyon ya shiga ciki, ya gyara ’yar akuya ya dafa, da garin efa ya yi burodi marar yisti. Da ya sa naman a kwando, romon kuma a tukunya, sai ya fito da su waje ya miƙa masa su a ƙarƙashin itacen oak.
Mala’ikan Allah ya ce masa, “Ka ɗauko naman da burodi marar yisti ka sa su a kan wannan dutse, ka zuba romon a kai.” Gideyon kuwa ya yi haka. Da kan sandan da yake a hannunsa, mala’ikan Ubangiji ya taɓa naman da burodi marar yistin. Sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da burodin. Mala’ikan kuwa ya ɓace. Sa’ad da Gideyon ya gane mala’ikan Ubangiji ne, sai ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka! Na ga mala’ikan Ubangiji ido da ido.”
Amma Ubangiji ya ce masa, “Salama! Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba.”
Saboda haka Gideyon ya gina wa Ubangiji bagade a can, ya kuma kira shi, Ubangiji Salama ne. Har wa yau bagaden yana a Ofra ta mutanen Abiyezer.
A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimi na biyu daga garken mahaifinka, wannan mai shekara bakwai.6.25 Ko kuwa Ka ɗauki balagaggen bijimi wanda ya yi girma daga garken mahaifinka Ka rushe bagaden mahaifinka na Ba’al ka sare ginshiƙin Ashera6.25 Wato, alamar alliya Ashera; a nan da kuma ko’ina a Mahukunta kusa da ita. Sa’an nan ka gina bagade irin6.26 Ko kuwa ka gina da jerin duwatsu da ya dace wa Ubangiji Allahnka a kan wannan tudu. Ka yi amfani da itacen katakon ginshiƙin Ashera da ka sare, ka miƙa bijiman nan biyu hadaya ta ƙonawa.”
Saboda haka Gideyon ya ɗebi bayinsa bakwai ya yi yadda Ubangiji ya ce masa. Amma saboda yana tsoron iyalinsa da mutanen gari, ya yi haka da dare a maimako da rana.
Da safe sa’ad da mutanen garin suka tashi, sai suka tarar an rushe bagaden Ba’al, tare da ginshiƙin Ashera da yake kusa da shi, duk an sare, bijimi na biyu kuma aka miƙa hadaya a kan sabon bagaden!
Sai suka tambayi junansu, “Wa ya yi wannan?”
Sa’ad da suka bincika a hankali, sai aka faɗa musu, “Gideyon ɗan Yowash ne ya yi haka.”
Mutanen garin suka ce wa Yowash, “Ka kawo mana ɗanka. Dole yă mutu, domin ya rushe bagaden Ba’al, ya sare ginshiƙin Asheran da yake tsaye kusa da shi.”
Amma Yowash ya ce wa taron da suka tayar masa, “Za ku yi hamayya domin Ba’al ne? Kuna ƙoƙari ku cece shi ne? Duk wanda ya yi faɗa saboda shi za a kashe shi kafin safe. In lalle Ba’al allah ne, zai kāre kansa sa’ad da wani ya rushe bagadensa.” Saboda haka a ranar suka kira Gideyon, “Yerub-Ba’al,”6.32 Yerub-Baal yana nufin bari Ba’al ya yi hamayya. suna cewa, “Bari Ba’al ya yi hamayya da shi,” domin ya rushe bagaden Ba’al.
To, dukan Midiyawa, Amalekawa da sauran mutanen gabashi suka haɗa ƙarfi suka ƙetare Urdun suka kafa sansani a Kwarin Yezireyel. Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko wa Gideyon, ya kuma busa ƙaho, ya kira mutanen Abiyezer su bi shi. Ya aika manzanni ko’ina a Manasse, yana kiransu su kintsa, haka ma Asher, Zebulun da Naftali, ta haka su ma suka haura su sadu da su.
Gideyon ya cewa Allah, “In za ka ceci Isra’ila ta hannuna yadda ka yi alkawari, to, zan shimfiɗa ulu a masussuka, inda safe akwai raɓa a kan ulun kaɗai, ƙasa kuwa a bushe, to, zan san cewa za ka ceci Isra’ila ta hannuna, yadda ka ce.” Abin da faru ke nan. Gideyon ya tashi da sassafe kashegari, ya matse ulun ya kakkaɓe raɓar, ruwan ya cika ƙwarya.
Sa’an nan Gideyon ya ce wa Allah, “Kada ka yi fushi da ni. Bari in ƙara yin wani gwaji kuma da ulun. A wannan lokaci ka sa ulun yă bushe, ƙasar kuma ta rufu da raɓa.” A wannan dare Allah ya yi haka. Ulun ne kaɗai yake a bushe, amma dukan ƙasar ta jiƙe da raɓa.
Gideyon ya ci Midiyawa da yaƙi
Kashegari da sassafe, Yerub-Ba’al (wato, Gideyon) da dukan mutanensa suka kafa sansani a maɓulɓulan Harod. Sansanin Midiyawa kuma yana arewa da su a kwari kusa da tudu na More. Sai Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Mutanen da kake da su sun yi mini yawa da zan ba da Midiyawa a hannunsu. Don kada Isra’ila tă yi mini fahariya cewa ƙarfinta ne ya cece su, ka yi shela ga mutane yanzu cewa, ‘Duk wanda ya yi rawan jiki don tsoro, sai yă juya yă bar Dutsen Gileyad.’ ” Saboda haka mutum dubu ashirin da biyu suka koma, sai mutum dubu goma suka rage.
Amma Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai cikin ruwa, in kuma tankaɗe maka su a can. In na ce, ‘Wannan zai tafi da kai,’ to, zai tafi; amma in na ce, ‘Wannan ba zai tafi da kai ba,’ to, ba zai tafi ba.”
Saboda haka Gideyon ya kai mutanen cikin ruwa. A can Ubangiji ya ce masa, “Ka ware waɗanda suka tanɗi ruwa kamar kare daga waɗanda suka durƙusa suka sha ruwan.” Mutum ɗari uku sun tanɗi ruwa, dukan sauran kuwa suka durƙusa suka sha ruwan.
Sai Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa, zan cece ka in kuma ba da Midiyawa a hannuwanku. Ka bar sauran mutane su tafi kowa zuwa wurinsa.” Saboda haka Gideyon ya mai da sauran Isra’ilawa zuwa tentinsu amma ya riƙe mutum ɗari uku waɗanda suka karɓi guzuri da ƙahonin sauran.
To, sansanin Midiyawa yana ƙasa da su a kwarin. A daren nan Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Tashi ka tafi sansaninsu domin zan ba da su a hannuwanka. In kana tsoron fāɗa musu, sai ka tafi da bawanka Fura ka kuma saurari abin da suke faɗi. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali ka auka musu.” Saboda haka sai ya tafi tare da Fura bawansa zuwa sansanin. Midiyawa, Amalekawa da dukan sauran mutane gabashi suka yi sansani a kwari, kamar fāra. Raƙumansu kuma kamar yashi a bakin teku don sun wuce ƙirge.
Gideyon ya iso daidai wani yana faɗa wa wani aboki mafarkinsa, yana cewa, “Na yi mafarki, na ga dunƙule burodin sha’ir ya fāɗo a tsakiyar sansanin Midiyawa. Ya bugi tentin da ƙarfin da ya sa tenti ta kife a ƙasa.”
Abokinsa ya ce, “Ai wannan ba wani abu ba ne fiye da takobin Gideyon ɗan Yowash, mutumin Isra’ila. Allah ya ba da Midiyawa da dukan sansani a hannuwansa.”
Da Gideyon ya ji mafarkin da fassararsa, sai ya yi wa Allah sujada. Ya koma sansanin Isra’ila ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku tashi! Ubangiji ya ba da sansanin Midiyawa a hannuwanku.” Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki.
Ya ce musu, “Ku dube ni, ku bi abin da na yi. Sa’ad da na kai sansanin, ku yi daidai abin da na yi. Sa’ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoninmu, to, ko’ina a kewayen sansanin sai ku busa naku ku kuma yi ihu, ku ce, ‘Don Ubangiji da kuma domin Gideyon.’ ”
Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu. Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka ɗauki acibalbal a hannuwansu na hagu da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama, sai suka yi ihu, “Takobi don Ubangiji da kuma don Gideyon!” Yayinda kowannensu ya tsaya a inda yake kewaye da sansanin, dukan Midiyawa suka fito da gudu, suna kuka yayinda suke gudu.
Sa’ad da aka busa ƙahonin nan ɗari uku sai Ubangiji ya sa Midiyawa suka yi ta saran juna. Mayaƙan suka gudu zuwa Bet-Shitta wajen Zerera har zuwa yankin Abel-Mehola kusa da Tabbat. Aka kira dukan Isra’ilawa daga Naftali, Asher da dukan Manasse, suka kuwa fatattaki Midiyawa. Gideyon ya aiki manzanni zuwa dukan ƙasar tudu ta Efraim cewa, “Ku gangaro ku yaƙi Midiyawa ku ƙwace ruwan Urdun gaba da su har zuwa Bet-Bara.”
Saboda haka aka kira dukan mutanen Efraim suka ƙwace ruwan Urdun har zuwa Bet-Bara. Suka kuma kama shugabannin biyu na Midiyawa, Oreb da Zeyib suka kashe Oreb a dutsen Oreb, Zeyib kuma a wurin matsin ruwa inabin Zeyib. Suka fatattaki Midiyawa suka kawo kawunan Oreb da Zeba wurin Gideyon, wanda yake kusa da Urdun.
Zeba da Zalmunna
To, mutanen Efraim suka ce wa Gideyon, “Me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ba ka kira mu lokacin da ka tafi yaƙi da Midiyawa ba?” Suka zarge shi sosai.
Amma ya ce musu, “Me na yi da za a iya kwatanta da abin da kuka yi? Ashe, kalar inabin da Efraim ta yi bai fi dukan girbin inabin da Abiyezer suka yi ba? Allah ya ba da Oreb da Zeyib, shugabannin Midiyawa a hannuwanku. Me na yi da ya fi naku? Da ya faɗi haka sai hankalinsu ya kwanta.”
Gideyon da mutanensa ɗari uku, sun gaji, duk da haka suka yi ta fafarar, suka zo Urdun suka haye shi. Ya ce wa mutanen Sukkot, “Ku ba wa mutanena burodi; sun gaji, har yanzu ina fafarar Zeba da Zalmunna, sarakunan Midiyawa.”
Amma shugabannin Sukkot suka ce, “Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Don me za mu ba wa mayaƙanka burodi?”
Sai Gideyon ya ce, “Haka ko? To, sa’ad da Ubangiji ya ba da Zeba da Zalmunna a hannuna, zan tsattsaga jikinku da ƙayayyuwan jeji.”
Daga nan ya wuce zuwa Fenuwel ya yi irin roƙon nan, amma suka amsa yadda mutanen Sukkot suka yi. Saboda haka sai ya ce wa mutanen Fenuwel, “Sa’ad da na dawo da nasara zan rushe wannan hasumiya.”
To, Zeba da Zalmunna suna a Karkor da mayaƙa wajen dubu goma sha biyar, abin da ya rage ke nan na mayaƙan gabashi; mayaƙa masu takobi dubu ɗari da ashirin ne suka mutu. Gideyon ya haura ta hanyar makiyaya, gabas da Noba, da kuma Yogbeha, ya fāɗa wa mayaƙan ta yadda ba su zata ba. Zeba da Zalmunna, sarakunan biyu na Midiyawa suka tsere, amma ya bi su ya kama, ya fatattaki dukan mayaƙansu.
Sa’an nan Gideyon ɗan Yowash ya komo daga yaƙi ta Hanyar Heres. Ya kama wani saurayin Sukkot ya tambaye shi, saurayin kuwa ya rubuta masa dukan sunayen shugabanni saba’in da bakwai na Sukkot, da dattawan garin. Sa’an nan Gideyon ya zo ya ce wa mutanen Sukkot, “To, ga Zeba da Zalmunna, waɗanda kuka yi mini ba’a kuna cewa, ‘Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Me zai sa mu ba mutanenka da suka gaji burodi?’ ” Ya kwashe dattawan garin ya koya wa mutanen Sukkot hankali ta wurin hukunta su da ƙayayyuwan hamada. Ya rushe hasumiyar Fenuwel ya kuma karkashe mutanen garin.
Sa’an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka karkashe a Tabor.”
Suka ce, “Mutane kamar ka ne kowane kamar ɗan sarki.”
Gideyon ya ce, “Waɗannan ’yan’uwana ne, ’ya’yan mahaifiyata. Muddin Ubangiji yana a raye, da a ce kun bar su da rai, da ba zan kashe ku ba.” Da ya juya wajen Yeter, ɗan farinsa, sai ya ce, “Ka kashe su!” Amma Yeter bai zāre takobinsa ba, domin shi yaro ne kawai kuma yana tsoro.
Zeba da Zalmunna suka ce masa, “Zo, ka yi da kanka. ‘Yadda mutum yake haka ƙarfinsa.’ ” Ta haka Gideyon ya matso gaba ya kashe su, ya ɗauki kayan ado daga wuyar raƙumansu.
Efod na Gideyon
Isra’ilawa suka ce wa Gideyon, “Ka yi mulkinmu, kai, ɗanka da jikanka, domin ka cece mu daga hannun Midiyawa.”
Amma Gideyon ya ce musu, “Ni, ko ɗana, ba za mu yi mulkinku ba. Ubangiji ne zai yi mulkinku.” Kuma ya ce, “Ina da roƙo guda ɗaya, cewa kowannenku ya ba ni ’yan kunne daga rabon ganima.” (Al’adar mutanen Ishmayel ce su sa ’yan kunnen zinariya.)
Suka ce, “Za mu yi farin cikin ba ka su.” Saboda haka suka shimfiɗa mayafi, kowanne ya sa ɗan kunne ɗaya daga ganimar. Nauyin ’yan kunnen zinariyar ya kai shekel ɗari goma sha bakwai, ban da kayan ado, abin wuya da tufafin shunayya waɗanda sarakuna Midiyawa suke sawa ko sarƙoƙin da suke wuyar raƙumansu. Gideyon ya efod da zinariyar, wanda ya ajiye a Ofra, garinsa. Dukan Isra’ila suka shiga yin karuwanci ta wurin yin sujada a can, ya kuwa zama wa Gideyon da dukan iyalinsa tarko.
Rasuwar Gideyon
Da haka Isra’ilawa suka mallaki Midiyawa ba su kuma sāke tā da kai ba. A zamanin Gideyon ƙasar ta sami zaman lafiya har shekara arba’in.
Yerub-Ba’al ɗan Yowash ya koma gida don yă zauna. Yana da ’ya’ya saba’in maza da ya haifa, gama yana da mata da yawa. Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take Shekem, ita ma ta haifa masa ɗa wanda ya ba shi suna Abimelek. Gideyon ɗan Yowash ya rasu da kyakkyawan tsufa aka kuma binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa a Ofra na mutanen Abiyezer.
Ba a daɗe da rasuwar Gideyon ba, sai Isra’ila ta sāke shiga karuwanci suna bauta wa Ba’al. Suka kafa Ba’al-Berit yă zama musu allahnsu ba kuma tuna da Ubangiji Allahnsu, wanda ya cece su daga hannuwan abokan gābansu a kowane gefe ba. Suka kāsa nuna alheri ga gidan Yerub-Ba’al (wato, Gideyon) saboda abubuwa masu alherin da ya yi musu.
Abimelek
Abimelek ɗan Yerub-Ba’al ya tafi Shekem wurin ’yan’uwan mahaifiyarsa, ya ce musu da kuma dukan dangin mahaifiyarsa, “Ku tambayi ’yan ƙasar Shekem, ‘Wanne ya fi muku, a sa dukan ’ya’yan Yerub-Ba’al saba’in maza su yi mulkinku, ko dai mutum guda kawai yă yi mulkinku?’ Ku tuna, ni jininku ne.”
Sa’ad da ’yan’uwan suka mayar wa ’yan ƙasar Shekem wannan, sai suka goyi bayan Abimelek, gama sun ce, “Shi ɗan’uwanmu ne.” Suka ba shi shekel saba’in na azurfa daga haikalin Ba’al-Berit, Abimelek kuwa ya yi amfani da shi ya yi hayar ’yan tauri waɗanda suka zama masu binsa. Sai ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra kuma a dutse guda ya kashe ’yan’uwansa, ’ya’yan Yerub-Ba’al. Amma Yotam, autan ɗan Yerub-Ba’al ya tsira ta wurin ɓuya. Sa’an nan duka ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo suka taru kusa da babban itacen wajen ginshiƙi a Shekem don a naɗa Abimelek sarki.
Sa’ad da aka gaya wa Yotam wannan, sai ya hau Dutsen Gerizim ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku saurare ni, ’yan ƙasar Shekem, don Allah yă saurare ku. Wata rana itatuwa suka fita don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Ka zama sarkinmu.’
“Amma itacen zaitun ya ce, ‘In bar mai nawa, wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in zo in yi ta fama da itatuwa?’
“Biye da wannan, sai itatuwan suka ce wa itacen ɓaure, ‘Zo ka zama sarkinmu.’
“Amma itacen ɓauren ya ce, ‘In bar kyawawan ’ya’yana da zaƙinsu, in zo in yi ta fama da itatuwa?’
“Sa’an nan itatuwan suka ce wa kuringar inabi, ‘Ki zo ki zama sarkinmu.’
“Amma kuringar ta ce, ‘In bar ruwan inabina, wanda yake faranta zuciyar alloli da mutane, in zo in yi fama da itatuwa?’
“A ƙarshe sai dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo ka zama sarkinmu.’
“Itacen ƙaya ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske ne kuke so ku naɗa ni sarkinku, ku zo ku sha inuwana; in ba haka ba, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al’ul na Lebanon!’
“To, da a ce kun yi abin bangirma da aniya mai kyau sa’ad da kuka naɗa Abimelek sarki, da kun nuna wa Yerub-Ba’al da iyalinsa ladabi, da kuma kun yi masa abin da ya cancanci shi, a yi tunani cewa mahaifina ya yi yaƙi saboda ku, ya yi kasai da ransa don yă cece ku daga hannun Midiyawa (amma ga shi yau kun tayar wa iyalin mahaifina, kuka kashe ’ya’yansa saba’in a dutse guda, kuka kuma naɗa Abimelek, ɗan baiwa, sarki a kan ’yan ƙasar Shekem domin shi ɗan’uwanku ne) in har kun aikata wannan cikin bangirma da kuma aminci wajen Yerub-Ba’al da iyalinsa a yau, bari Abimelek yă zama farin cikinku, ku kuma nasa! Amma in ba haka ba, bari wuta ta fito daga Abimelek ya cinye ku, ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo, bari wuta kuma daga wurinku ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo ta cinye Abimelek!”
Sa’an nan Yotam ya gudu, ya tsere zuwa Beyer ya zauna a can gama yana tsoron ɗan’uwansa Abimelek.
Bayan Abimelek ya yi shekara uku yana mulki a Isra’ila, sai Allah ya aiko da mugun ruhu tsakanin Abimelek da ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka ci amanar Abimelek. Allah ya yi haka saboda kisan ’ya’ya saba’in na Yerub-Ba’al, don a ɗauki fansar jininsu a kan Abimelek ɗan’uwansu da kuma ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka taimake shi kisan ’yan’uwansa. Cikin hamayya da shi waɗannan ’yan ƙasar Shekem suka sa mutane a kan tuddai don su yi kwanton ɓauna a kan su yi fashi ga duk wanda ya wuce a can, wannan fa ya kai kunnen Abimelek.
To, Ga’al ɗan Ebed ya tafi tare da ’yan’uwansa zuwa Shekem, ’yan ƙasarta kuwa suka dogara da shi. Bayan sun tafi gonaki suka tattara inabi suka matse su, sai suka yi biki a haikalin allahnsu. Yayinda suke ci da sha, sai suka la’anci Abimelek. Sa’an nan Ga’al ɗan Ebed ya ce, “Wane ne Abimelek, kuma wane ne Shekem, da za mu bauta masa? Shi ba ɗan Yerub-Ba’al ba ne, kuma ba Zebul ne mataimakinsa ba? Ku bauta wa mutanen Hamor, mahaifin Shekem! Me ya sa za mu bauta wa Abimelek? Da a ce waɗannan mutane suna a ƙarƙashina mana! Da zan hamɓarar da shi. In ce wa Abimelek, ‘Ka tara dukan mayaƙanka!’ ”
Sa’ad da Zebul gwamnar birnin ya ji abin da Ga’al ɗan Ebed ya ce, sai ya fusata. Asirce sai ya aiki manzanni wajen Abimelek, yana cewa, “Ga’al ɗan Ebed da ’yan’uwansa sun zo Shekem suna kuma zuga birnin sun tayar maka. To, in dare ya yi, sai ka zo da mutanenka ku yi kwanto a filaye. Kashegari da safe, sai ku tashi ku fāɗa wa birnin. Sa’ad da Ga’al da mutanensa suka faɗa maka, sai ka yi abin da ka iya yi da su.”
Saboda haka Abimelek da dukan mutanensa suka tashi da dare suka ɓuya kusa da Shekem a ƙungiyoyi huɗu. To, Ga’al ɗan Ebed ya riga ya fita waje yana tsaye a ƙofar birni daidai Abimelek da mayaƙansa suka fito daga inda suka ɓuya.
Sa’ad da Ga’al ya gan su, sai ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna gangarowa daga kan duwatsu!”
Zebul ya ce, “Kana ɗaukan inuwan duwatsu kana ce mutane.”
Amma Ga’al ya sāke magana ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa daga tsakiyar filaye, kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen masu duba.”
Sa’an nan Zebul ya ce masa, “Ina bakin da ka yi ɗin, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa.’ Ba mutanen ne ka yi musu ba’a ba? Fita, ka yaƙe su mana!”
Saboda haka Ga’al ya fito da ’yan ƙasar Shekem suka yaƙi Abimelek. Abimelek ya kore shi, mutane da yawa suka ji ciwo a yaƙin, har zuwa ƙofar birnin. Abimelek ya zauna a Aruma, Zebul kuwa ya kori Ga’al da ’yan’uwansa daga Shekem.
Kashegari mutanen Shekem suka tafi gonaki, aka kuwa gaya wa Abimelek. Saboda haka ya ɗauki mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, sa’an nan ya yi kwanto a gonakin. Sa’ad da ya ga mutanen suna fitowa daga birni, sai ya yi wuf ya fāɗa musu. Abimelek da ƙungiyoyin da suke tare da shi suka yi maza suka yi tsaya a ƙofar birnin. Sa’an nan ƙungiyoyi biyu suka ruga suka fāɗa wa waɗanda suke a gonaki suka karkashe su. Dukan yinin, Abimelek ya matsa yaƙi da birnin sai da ya cinye ta ya kuma kashe mutanenta. Sa’an nan ya hallaka birnin ya barbaza gishiri a kanta.
Da jin haka, sai ’yan ƙasa a hasumiyar Shekem suka shiga wurin mafaka a hankalin El-Berit. Da Abimelek ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru a can, sai Abimelek da dukan mutanensa suka haura zuwa Dutsen Zalmon. Sai ya ɗauki gatari ya sassare waɗansu rassa, waɗanda ya sa a kafaɗunsa. Ya umarci mutanen da suke tare da shi ya ce, “Sauri, ku yi abin da kuka ga na yi!” Saboda haka mutanen suka sassare rassan itatuwa suka bi Abimelek. Suka tattara su a jikin mafakar suka kuma cinna mata wuta a kan mutanen da suke a ciki. Ta haka dukan mutanen da suke cikin hasumiyar Shekem, wajen maza da mata dubu ɗaya suka mutu.
Biye da wannan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta ya kuma cinye ta da yaƙi. A cikin birnin, akwai wata hasumiya mai ƙarfi, inda dukan maza da mata, dukan mutanen birnin, suka ɓuya. Suka kulle kansu, suka kuma hau rufin hasumiyar. Abimelek ya je wajen hasumiya ya kuma auka mata. Amma da ya yi kusa da ƙofar hasumiyar don yă cinna mata wuta, sai wata mata ta saki ɗan dutsen niƙa a kan Abimelek ta fasa ƙoƙon kansa.
Da sauri ya kira mai riƙon masa makami ya ce, “Zaro takobinka ka kashe ni, don kada a ce ‘Mace ce ta kashe shi.’ ” Saboda haka bawansa ya soke shi, ya mutu. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga Abimelek ya mutu, sai suka tafi gida.
Ta haka Allah ya sāka muguntar da Abimelek da ya yi wa mahaifinsa ta wurin kisan ’yan’uwansa saba’in. Allah kuma ya sa muguntar mutanen Shekem suka koma kansu. La’anar Yotam ɗan Yerub-Ba’al kuma ta kama su.
Tola
Bayan zamanin Abimelek, sai Tola ɗan Fuwa ɗan Dodo daga Issakar ya tashi don yă ceci Isra’ila. Yana zama a Shamir a ƙasar tudu ta Efraim. Ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da uku sa’an nan ya mutu, aka kuma binne shi a Shamir.
Yayir
Bayansa kuma sai Yayir daga Gileyad, wanda ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da biyu. Yana ’ya’ya talatin, waɗanda suke hawan jakuna talatin. Sun shugabanci birane talatin a Gileyad, har wa yau ana ce da biranen Hawwot Yayir.10.4 Ko kuwa ana ce da su mazaunan Yayir Sa’ad da Yayir ya mutu, sai aka binne shi a Kamon.
Yefta
Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Suka shiga bautar Ba’al da Ashtarot, da kuma allolin Aram, allolin Sidon, allolin Mowab, Ammonawa da kuma allolin Filistiyawa. Kuma domin Isra’ilawa sun bar Ubangiji ba su ƙara bauta masa ba, sai ya fusata da su. Ya sayar da su ga hannun Filistiyawa da Ammonawa, waɗanda suka fatattake su a shekarar suka kuma ragargaza su. Shekara goma sha takwas suka yi ta danne dukan Isra’ilawan da suke gabashin Urdun a Gileyad, ƙasar Amoriyawa. Ammonawa su ma suka haye Urdun domin su yi yaƙi da Yahuda, Benyamin da kuma gidan Efraim; Isra’ila kuwa suka kasance cikin wahala ƙwarai da gaske. Sa’an nan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Mun yi maka zunubi, mun bar Allahnmu muka shiga bautar Ba’al.”
Ubangiji ya ce, “Sa’ad da Masarawa, Amoriyawa, Ammonawa, Filistiyawa, Sidoniyawa, Amalekawa da kuma mutanen Mawon suka wulaƙanta ku kuka kuwa yi mini kuka, ban cece ku daga hannunsu ba? Amma kuka bar ni kuka bauta wa waɗansu alloli, saboda haka ni ma ba zan ƙara cece ku ba. Ku tafi ku yi wa allolin da kuka zaɓa. Bari su cece ku sa’ad da kuke cikin wahala!”
Amma Isra’ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mu dai mun yi zunubi. Ka yi da mu abin da ka ga dama, amma muna roƙonka ka cece mu a yanzu.” Sa’an nan suka zubar da allolin nan daga cikinsu suka bauta wa Ubangiji. Ubangiji kuwa bai ƙara daure da azabar da Isra’ila suke sha ba.
Sa’ad da aka kira Ammonawa su yi ɗamarar yaƙi, sai su kuma kafa sansani a Gileyad, Isra’ilawa kuwa suka tattaru suka kafa sansani Mizfa. Shugabannin mutanen Gileyad suka cewa juna, “Duk wanda zai fara fāɗa wa Ammonawa shi zai zama shugaban duk waɗanda suke zama a Gileyad.”
Yefta mutumin Gileyad, jarumi ne ƙwarai. Mahaifinsa ne Gileyad; mahaifiyar kuwa karuwa ce. Matar Gileyad ta haifa masa ’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.” Saboda haka Yefta ya tsere daga ’yan’uwansa ya zauna a ƙasar Tob, inda waɗansu ’yan iska suka kewaye shi suka bi shi.
Ana nan, sa’ad da Ammonawa suka kai wa Isra’ilawa hari, dattawan Gileyad suka je suka nemo Yefta daga ƙasar Tob. Suka ce masa, “Ka zo ka zama mana shugaba, don mu yaƙi Ammonawa.”
Yefta ya ce musu, “Ba kun ƙi ni kuka kuma kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuke zuwa wurina yanzu sa’ad da kuke cikin wahala?”
Mutanen Gileyad suka ce masa, “Duk da haka, muna juyo wajenka yanzu, ka zo tare da mu mu yaƙi Ammonawa, za ka kuma zama shugaban duk wanda yake zama a Gileyad.”
Yefta ya ce, “A ce kun dawo da ni in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna, zan zama shugabanku?”
Dattawan Gileyad suka ce, “Ubangiji ne shaidanmu; za mu yi duk abin da ka ce.” Saboda haka Yefta ya tafi tare da dattawan Gileyad, mutanen kuwa suka naɗa shi shugabansu da kuma sarkinsu. Ya kuwa maimaita dukan maganarsa a gaban Ubangiji a Mizfa.
Sa’an nan Yefta ya aiki jakadu zuwa wurin sarkin Ammonawa su tambaya, “Me ya haɗa ka da ni, da ka kawo wa ƙasata yaƙi?”
Sarkin Ammonawa ya ce wa jakadu, “Sa’ad da Isra’ilawa suka fito daga Masar, sun ƙwace mini ƙasa tun daga Arnon zuwa Yabbok, har zuwa Urdun. Yanzu ka mayar mini ita cikin salama.”
Yefta ya sāke aikan jakadu wurin sarki, yana cewa,
“Ga abin da Yefta yake faɗi, Isra’ila ba tă ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba. Amma sa’ad da suka bar Masar, Isra’ila ta bi ta hamada zuwa Jan Teku11.16 Da Ibraniyanci Yam Suf; wato, Tekun Iwa. har suka zo Kadesh. Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.
“Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta.
“Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga Sihon sarkin Amoriyawa, wanda yake mulki a Heshbon, ta ce masa, ‘Ka bar mu mu ratsa ƙasarka mu wuce zuwa wurinmu.’ Sihon dai, bai amince da Isra’ila su ratsa ƙasarsa ba. Ya tattara dukan mutanensa suka yi sansani a Yahza suka kuwa yaƙi Isra’ila.
“Sa’an nan Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da Sihon da dukan mutanensa a hannun Isra’ila, suka kuwa ci nasara a kansu. Isra’ila ta ƙwace dukan ƙasar Amoriyawa da suke zaune a ƙasar, suka ƙwace dukan yankin Amoriyawa tun daga ƙasar Arnon zuwa Yabbok, daga hamada har zuwa Urdun.
“To, da yake Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya kori Amoriyawa a gaban mutanensa Isra’ila, wane ’yanci kake da shi da za ka karɓe ta? Ba za ka karɓi abin da allahnka Kemosh ya ba ka ba? Haka mu ma, duk abin da Ubangiji Allahnmu ya riga ya ba mu, za mu mallake shi. Ka fi Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab ne? Ka taɓa ji ya yi hamayya da Isra’ila ko yă yi yaƙi da su? Shekara ɗari uku Isra’ilawa suka yi zamansu a Heshbon, Arower da ƙauyukan kewayenta da dukan biranen da suke gefen Arnon. Me ya sa ba ka karɓe su a lokacin ba? Ban yi maka laifi ba, amma kana musguna mini ta wurin kawo mini hari. Bari Ubangiji yă zama Alƙali, yă yanke hukunci tsakani Isra’ilawa da Ammonawa.”
Duk da haka sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika ba.
Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko wa Yefta. Sai ya haye Gileyad da Manasse, ya ratsa ta Mizfa zuwa Gileyad, daga can kuma ya kai wa Ammonawa hari. Yefta kuwa ya yi wa’adi da Ubangiji ya ce, “In ka ba da Ammonawa a hannuwana, duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don yă tarye ni, sa’ad da na komo daga yaƙi da Ammonawa, zai zama na Ubangiji, zan miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”
Sa’an nan Yefta ya haye zuwa wajen Ammonawa don yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuwansa. Ya hallaka birane ashirin tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-Keramim. Haka Isra’ila ta cinye Ammonawa ƙaf.
Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi, ’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai ’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko ’ya. Da ya gan ta, sai ya yayyage tufafinsa ya yi kuka ya ce, “Kaito! ’Yata! Kin karya mini gwiwa, kuma na lalace, domin na yi wa’adi ga Ubangiji da ba zan iya in karya ba.”
Ta ce, “Mahaifina, idan ka riga ka yi wa Ubangiji magana, sai ka yi da ni yadda ka yi alkawari, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa.” Sai ta kuma ce, “Sai dai, ka biya mini wannan bukata guda. Ka ba ni wata biyu in yi ta yawo da ni da ƙawayena a kan duwatsu mu yi makoki, domin ba zan yi aure ba.”
Ya ce mata, “Ki tafi,” Ya bar ta tă tafi har wata biyu. Ita da ’yan matan suka tafi a kan duwatsu suka yi ta makoki domin ba za tă taɓa aure ba. Bayan watanni biyu ɗin sai ta komo wurin mahaifinta ya kuwa yi da ita yadda ya yi wa’adi. Ita kuwa ba tă taɓa san namiji ba.
Wannan ya zama al’ada a Isra’ila, cewa kowace shekara ’yan mata sukan fita kwana huɗu don yin bikin tunawa da ’yar Yefta mutumin Gileyad.
Yefta da Efraim
Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.”
Yefta ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya sosai da Ammonawa, ko da yake na kira ku, amma ba ku cece ni daga hannuwansu ba. Da na ga ba za ku taimake ni ba, sai na yi kasai da raina na kuwa haye don in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba ni nasara a kansu. To, don me kuka zo yau don ku yaƙe ni?”
Sa’an nan Yefta ya tara mutanen Gileyad wuri guda ya kuma yaƙi Efraim. Mutanen Gileyad suka fatattake su domin mutanen Efraim sun ce, “Ku Mutanen Gileyad masu neman mafaka ne cikin Efraim da Manasse.” Mutanen Gileyad suka ƙwace mashigan Urdun masu zuwa Efraim, duk sa’ad da wani daga Efraim da ya tsira ya ce, “Bari in haye,” sai mutane Gileyad su ce “Kai mutumin Efraim ne?” In ya ce, “A’a,” sai su ce, “To, ka ce, ‘Shibbolet.’ ” In ya ce, “Sibbolet,” saboda ba sa iya faɗin kalmar daidai, sai su kama shi su kashe a mashigan Urdun. Aka kashe mutanen Efraim dubu arba’in da biyu a ta haka.
Yefta ya shugabanci Isra’ila shekara shida. Sa’an nan Yefta mutumin Gileyad ya mutu, aka kuwa binne shi wani gari a Gileyad.
Ibzan, Elon da Abdon
Bayansa, Ibzan mutumin Betlehem, ya shugabanci Isra’ila. Yana ’ya’ya maza talatin da ’ya’ya mata talatin. Ya ba da auren ’ya’yansa mata ga waɗanda ba daga dangi ba, ga ’ya’yansa maza kuwa ya kawo ’yan mata talatin su zama matansu waje da danginsa. Ibzan ya shugabanci Isra’ila shekara bakwai. Sa’an nan Ibzan ya mutu, aka kuwa binne shi Betlehem.
Bayansa, Elon mutumin Zebulun, ya shugabanci Isra’ila shekara goma. Sa’an nan Elon ya mutu, aka kuwa binne shi a Aiyalon a ƙasar Zebulun.
Bayansa, Abdon ɗan Hillel, daga Firaton, ya shugabanci Isra’ila. Yana da ’ya’ya maza arba’in da ’yan taɓa kunne talatin, waɗanda suka hau jakuna saba’in. Ya shugabanci Isra’ila shekara takwas. Sa’an nan Abdon ɗan Hillel ya mutu, aka kuwa binne shi a Firaton a Efraim, a ƙasar tudu ta Amalekawa.
Haihuwar Samson
Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda haka ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba’in.
Akwai wani mutumin Zora, mai suna Manowa, daga kabilar Dan, matarsa kuwa bakararriya ce, ba ta haihuwa. Mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta ya ce, “Ga shi ke bakararriya ce ba kya haihuwa, amma za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa. To, sai ki lura kada ki sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye, kada kuma ki ci wani abu marar tsarki, gama za ki yi ciki, ki haifi ɗa. Aska ba za tă taɓa kansa ba, domin yaron zai zama Banazare, keɓaɓɓe ga Allah tun daga haihuwa, shi ne kuwa zai soma ceton Isra’ilawa daga hannuwan Filistiyawa.”
Sa’an nan matar ta tafi wajen mijinta ta faɗa masa cewa, “Wani mutumin Allah ya zo wurina. Ya yi kama da mala’ikan Allah, yana da bantsoro ƙwarai. Ban tambaye shi inda ya fito ba, kuma bai gaya mini sunansa ba. Sai dai ya ce mini, ‘Za ki yi ciki, ki kuma haifi ɗa. To, fa, kada ki sha ruwan inabi ko abu mai sa maye kada kuma ki ci abin da yake marar tsarki, gama ɗan zai zama Banazare na Allah tun daga haihuwa har ranar mutuwarsa.’ ”
Sai Manowa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, bari mutumin Allahn da ka aiko mana yă sāke zuwa don yă koya mana yadda za mu goyi yaron da za a haifa.”
Allah ya ji Manowa, sai mala’ikan Allah ya sāke zuwa wurin matar yayinda take gona; amma Manowa mijinta ba ya tare da ita. Sai matar ta ruga don ta faɗa wa mijinta, ta ce, “Ga shi ya zo! Mutumin da ya bayyana mini ran nan!”
Manowa ya tashi ya bi matarsa. Da ya zo wurin mutumin, sai ya ce, “Kai ne wanda ka yi magana da matata?”
Ya ce, “Ni ne.”
Saboda haka Manowa ya tambaye shi ya ce, “Sa’ad da maganarka ta cika, me za tă zama dokar rayuwar yaron da kuma aikinsa?”
Mala’ikan Ubangiji ya ce, “Dole matarka ta kiyaye duk abin da na riga na gaya mata. Kada tă ci kowane iri abin da ya fito daga inabi, ba kuwa za tă sha ruwan inabi, ko abu mai sa maye ko ta ci abu marar tsarki ba. Dole tă kiyaye duk abin da na umarce mata.”
Manowa ya ce wa mala’ikan Ubangiji, “Muna roƙonka ka jira mu yanka maka ɗan akuya.”
Mala’ikan Ubangiji ya ce, “Ko kun sa na tsaya, ba zan ci abincinku ba. Amma in kun shirya hadaya ta ƙonawa, ku miƙa wa Ubangiji.” (Manowa bai gane cewa mala’ikan Ubangiji ne ba.)
Sa’an nan Manowa ya sāke tambayi mala’ikan Ubangiji ya ce, “Mene ne sunanka, don mu girmama ka sa’ad da maganarka ta tabbata.”
Ya ce, “Me ya sa kake tambaya sunana? Ai, ya wuce fahimta.” Sa’an nan Manowa ya ɗauki ɗan akuya, tare da hadaya ta hatsi ya miƙa wa Ubangiji a kan dutse. Ubangiji kuwa ya yi abin mamaki yayinda Manowa da matarsa suke kallo. Yayinda harshen wuta ya yi sama daga bagaden, sai mala’ikan Ubangiji ya haura cikin harshen wutar. Da ganin wannan Manowa da matarsa suka fāɗi da fuskokinsu har ƙasa. Da mala’ikan Ubangiji bai ƙara bayyana kansa ga Manowa da matarsa ba, sai Manowa ya gane cewa mala’ikan Ubangiji ne.
Ya ce wa matar, “Ba shakka za mu mutu, gama mun ga Allah!”
Amma matar ta ce, “Da Ubangiji yana nufin kashe mu ne, da ba zai karɓi hadaya ta ƙonawa da hadaya ta hatsi daga hannunmu, ko yă nuna mana dukan waɗannan abubuwa ko abin da ya gaya mana ba.”
Matar kuwa ta haifi ɗa, aka sa masa suna Samson. Ya yi girma Ubangiji kuma ya albarkace shi, Ruhun Ubangiji kuwa ya fara iza shi yayinda yake a Mahane Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.
Auren Samson
Samson ya gangara zuwa Timna a can ya ga wata daga cikin ’yan mata Filistiyawa. Da ya komo, sai ya gaya wa mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, “Na ga wata mace a Timna; ku auro mini ita ta zama matata.”
Mahaifinsa da mahaifiyarsa suka ce, “Babu wata karɓaɓɓiyar yarinya a cikin zuriyarku ko cikin dukan mutanenmu ne? Dole ne ka tafi wajen Filistiyawa marasa kaciya ka nemi aure?”
Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “A auro mini ita dai. Ita ta dace da ni.” (Iyayensa ba su san cewa wannan daga wurin Ubangiji ne ba, wanda yake neman hanyar da za a kai wa Filistiyawa hari; gama a lokacin suna mulkin Isra’ila.)
Sai Samson ya gangara zuwa Timna tare da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Da suka yi kusa da gonar inabin Timna, nan da nan sai ga ɗan zaki ya taso ya nufe shi yana ruri. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa da ƙarfi, ya sa ya yaga zakin kashi biyu da hannu kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Sai dai bai gaya wa iyayensa abin da ya yi ba. Sa’an nan ya gangara ya yi magana da yarinyar, yana kuwa sonsa.
Daga baya, da ya koma don yă aure ta, sai ya ratse don yă ga gawar zakin. Sai ga taron ƙudan zuma da zuma a ciki, wanda ya sa hannu ya ɗebo yana tafiya yana sha. Sa’ad da ya iso wurin iyayensa, ya ba su zuman, su ma suka sha. Sai dai bai gaya musu cewa ya ɗebo zuman daga gawar zaki ba.
To, mahaifinsa ya gangara don yă ga yarinyar. Samson kuwa ya shirya wata liyafa a can, yadda yake bisa ga al’adar angwaye. Sa’ad da ya bayyana, sai aka haɗa shi abokai talatin.
Sai Samson ya ce, “Bari in yi muku kacici-kacici, in kun ba ni amsa cikin kwana bakwai na wannan biki, zan ba ku riguna lilin talatin da kuma tufafi talatin. In kuma ba ku iya ba ni amsar ba, dole ku ba ni rigunan lilin talatin da tufafi talatin.”
Suka ce, “Ka gaya mana kacici-kacicin.”
Sai ya ce,
“Daga mai ci, abinci ya fito;
daga mai ƙarfi, abu mai zaki ya fito.”
Har kwana uku ba su iya ba da amsa ba.
A rana ta huɗu14.15 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin da na Siriyak; da na Ibraniyanci suna da bakwai suka ce wa matar Samson “Ki rarrashi mijinki yă bayyana mana kacici-kacicin, ko kuwa mu ƙone ki da gidan mahaifinki duka da wuta. Kun kira mu domin ku yi mana fashi ne?”
Sa’an nan matar Samson ta kwanta masa a jiki tana kuka tana cewa, “Kai maƙiyina ne, lalle ba ka ƙaunata, ka yi wa mutanena kacici-kacici, amma ba ka gaya mini amsar ba.”
Ya amsa ya ce, “Ban ma bayyana wa mahaifina ko mahaifiyata ba, to, don me zan bayyana miki?” Ta yi ta kuka har kwana bakwai na bikin. Saboda haka a rana ta bakwai sai ya gaya mata, don ta dame shi. Ita kuwa ta bayyana kacici-kacicin wa mutanenta.
Kafin rana ta fāɗi a rana ta bakwai mutane garin suka ce masa,
“Me ya fi zuma zaki?
Me ya fi zaki ƙarfi?”
Samson ya ce musu,
“Da ba don kun haɗa baki da matata ba,
da ba za ku san amsar kacici-kacici ba.”
Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko masa da iko. Sai ya fita ya gangara zuwa Ashkelon, ya kashe mutanensu talatin, ya kwashe kayansu ya kuma ba da rigunarsu ga waɗanda suka bayyana kacici-kacicin. Cike da fushi, ya haura zuwa gidan mahaifinsa. Aka kuma ɗauki matar Samson aka ba wa ɗaya daga cikin waɗanda suka yi masa hidima a bikin.
Sakayyar Samson a kan Filistiyawa
Daga baya, a lokacin girbin alkama, Samson ya ɗauki ɗan akuya ya tafi yă ziyarci matarsa. Sai ya ce, “Zan in shiga ɗakin matata.” Amma mahaifinta ya hana shi shiga.
Ya ce wa, “Na tabbata ba ka sonta sam-sam, don haka na ba da ita ga abokinka. Ba ƙanuwarta ta fi kyau ba? Ka ɗauke ta a maimako.”
Samson kuwa ya ce musu, “A wannan lokaci ina da iko in rama a kan Filistiyawa; tabbatacce zan ji musu.” Saboda haka ya tafi ya kama yanyawa ɗari uku ya ɗaura wutsiyoyinsu wutsiya da wutsiya. Sa’an nan ya daure acibalbal a tsakanin ko waɗanne wutsiya biyu, sai ya sa wa acibalbal wuta, ya saki yanyawan suka shiga gonakin Filistiyawa. Suka ƙone dammunan hatsi da hatsin da yake tsaye, tare da gonakin inabi da na zaitun.
Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, “Wane ne ya yi wannan abu?” Sai aka ce musu, “Ai, Samson ne surukin mutumin Timna, domin an ba wa abokinsa matarsa.”
Saboda haka Filistiyawa suka haura suka je suka ƙone ta da mahaifinta ƙurmus da wuta. Samson ya ce musu, “Tun da kun aikata wannan, ba zan bari ba har sai na ɗau fansa a kanku.” Ya kuwa fāɗa musu ya kuma karkashe su da yawa. Sa’an nan ya gangara ya zauna a kogo a dutsen Etam.
Filistiyawa suka haura suka yi sansani a Yahuda, suka bazu kusa da Lehi. Mutanen Yahuda suka ce, “Me ya sa kuka zo mana da yaƙi?”
Sai suka ce, “Mun zo ne mu kama Samson, a matsayin fursunan yaƙi, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.”
Sa’an nan mutane dubu uku daga Yahuda suka gangara wajen Samson a kogo a dutsen Etam. Suka ce masa, “Ba ka san cewa Filistiyawa ne suke mulkinmu ba? Me ke nan ka yi mana?”
Ya ce musu, “Na ɗan yi musu abin da suka yi mini ne.”
Suka ce masa, “To, mun zo ne mu daure ka mu kai wa Filistiyawa.”
Samson ya ce, “Ku rantse mini ba za ku kashe ni da kanku ba.”
Suka ce, “Mun yarda, za mu dai daure ka mu ba da kai gare su. Ba za mu kashe ka ba.” Saboda haka suka daure shi da sababbin igiyoyi biyu, suka saukar da shi daga dutsen. Yayinda ya zo gab da Lehi, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje da ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko da iko a kansa. Igiyoyin da suke daure a hannuwansa kuwa suka zama kamar abin da wuta ta babbaka, suka tsintsinke suka zuba daga hannuwansa. Da ya samo muƙamuƙin jaki, ya ɗauka, sai ya karkashe mutane dubu ɗaya.
Sa’an nan Samson ya ce,
“Da muƙamuƙin jaki
na mai da su jakuna.15.16 Ko kuwa mai da su tsibi guda ko biyu; Ibraniyanci na kalman nan jaki ya yi kamar ta Ibraniyanci na tsibi.
Da muƙamuƙin jaki
na kashe mutum dubu.”
Da ya gama magana, sai ya jefar da muƙamuƙin; aka ba wa wannan wuri suna Ramat Lehi.15.17 Ramat Lehi yana nufin tudun muƙamuƙi.
Saboda ƙishirwa ta kama shi ƙwarai, sai ya ce wa Ubangiji, “Ka ba bawanka wannan babbar nasara. To, sai in mutu da ƙishirwa, har in shiga a hannun marasa kaciyan nan su kashe ni?” Sa’an nan Allah ya buɗe wani rami a Lehi, ruwa kuwa ya fito daga ciki. Da Samson ya sha, sai ƙarfinsa ya dawo, ya kuma wartsake. Aka sa wa wannan maɓulɓula suna En Hakkore,15.19 En Hakkore yana nufin maɓulɓular mai kira. yana nan a Lehi har wa yau.
Samson kuwa ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin a zamanin Filistiyawa.
Samson da Delila
Wata rana Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa. Ya shiga wurinta ya kwana. Aka gaya wa mutanen Gaza, “Ai, Samson yana a nan!” Saboda haka suka zo suka kewaye wurin suka yi kwanto dukan dare a bakin ƙofar birni. A daren nan ba su motsa nan da can ba, suna cewa, “Gari yana wayewa za mu kashe shi.”
Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakiyar dare. Sa’an nan ya tashi ya kama ƙofofin birnin, tare da madogarai biyunsu, ya tumɓuke, ya aza su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a fuskantar Hebron.
Bayan ɗan lokaci, sai ya shiga ƙaunar wata mace, mai suna Delila a Kwarin Sorek. Sai shugabannin Filistiyawa suka tafi wurinta suka ce, “Ki yi ƙoƙari ki ga ko za ki rarrashe shi yă nuna miki asirin ƙarfinsa da yadda za mu iya shan ƙarfinsa don mu ɗaura shi mu yi nasara a kansa. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu ɗari ɗaya na azurfa.”
Saboda haka Delila ta ce wa Samson, “Ka faɗa miki asirin ƙarfinka da yadda za a ɗaura ka a yi nasara a kanka.”
Samson ya ce mata, “In wani ya ɗaura ni da sababbin igiyoyin16.7 Ko kuwa igiyar baka; haka ma a ayoyi 8 da 9. da ba su bushe ba, zan zama marar ƙarfi kamar kowa.”
Sa’an nan shugabannin Filistiyawa suka kawo mata sababbin igiyoyi guda bakwai da ba su bushe ba, sai ta daure shi da su. Da mutane a ɓoye a cikin ɗaki tare da ita, sai ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Da jin haka sai ya tsintsinke igiyoyin kamar zaren da ya yi kusa da harshen wuta. Saboda haka asirin ƙarfinsa bai tonu ba.
Sa’an nan Delila ta ce wa Samson, “Ka mai da ni wawiya; ka ruɗe ni. Yanzu, ka gaya mini yadda za a daure ka.”
Ya ce, “In wani ya ɗaura ni sosai da sababbin igiyoyin da ba a taɓa amfani da su ba, zan zama marar ƙarfi kamar kowa.”
Saboda haka Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi ta ɗaura shi da su. Sa’an nan, tare da mutane a ɓoye a ɗakin, ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Amma sai ya tsintsinke su kamar zare.
Sa’an nan Delila ta ce, “Har yanzu, ka mai da shashasha, kana mai da ni wawiya kana kuma yin mini ƙarya. Ka gaya mini yadda za a daure ka mana.”
Ya ce mata, “In kin yi kitson gashin kaina guda bakwai kika ɗaura su da zare kika buga su da akwasha, zan rasa ƙarfi in zama kamar kowa.” Saboda haka yayinda yake barci, sai Delila ta yi kitson gashin kansa guda bakwai ta ɗinka su da zare, ta kuma16.13,14 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin; Ibraniyanci “Zan iya idan kin yi kitson gashin kaina guda bakwai su zama zare a daure.” 14 Saboda haka ta ɗaura su da akwasha.
Ta sāke yin ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka.” Ya tashi daga barcinsa ya tumɓuke akwashan tare da zaren da aka ɗaura gashin kansa da su.
Sa’an nan ta ce masa, “Yaya kake cewa kana sona alhali ba ka yarda da ni ba? Wannan shi ne sau na uku kana mai da ni wawiya kuma ba ka nuna mini asirin ƙarfinka ba.” Da irin wannan fitina ta tsokane shi kwana da kwanaki har sai da ya gaji kamar zai mutu.
Saboda haka sai ya faɗa mata kome ya ce, “Ba a taɓa sa reza a kaina ba, domin ni Naziri ne keɓaɓɓe ga Allah tun haihuwa. In kuwa an aske kaina, ƙarfina zai rabu da ni, sai in zama kamar kowa.”
Da Delila ta gane ya gaya mata kome yanzu, sai ta aika saƙo zuwa ga shugabannin Filistiyawa ta ce, “Ku ƙara zuwa sau ɗayan nan, ai, ya gaya mini kome.” Saboda haka shugabannin Filistiyawa suka dawo tare da azurfa a hannuwansu. Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi.
Sa’an nan ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!”
Sai ya farka daga barci yana tsammani cewa, “Zan fita kamar dā in miƙe jikina.” Amma bai san cewa Ubangiji ya rabu da shi ba.
Sa’an nan Filistiyawa suka fizge shi, suka ƙwaƙule idanunsa suka gangara da shi zuwa Gaza. Da suka daure shi da sarƙoƙin tagulla, sai aka sa shi yana niƙa a kurkuku. Amma gashi kansa ya fara tohuwa kuma bayan an aske shi.
To, sai Filistiyawa suka taru don su miƙa hadaya ga Dagon allahnsu su kuma yi biki cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu Samson a hannuwanmu.”
Sa’ad da mutane suka gan shi, sai suka yabi allahnsu, suna cewa,
“Allahnmu ya bashe abokin gābanmu
a hannunmu,
wanda ya lalace ƙasarmu
ya kuma raɓanya kisan mutanenmu.”
Yayinda suke cikin farin ciki, sai suka yi ihu, suka ce, “Fito mana da Samson yă yi mana wasa.” Saboda haka aka zo da Samson daga kurkuku, shi kuwa ya yi wasa a gabansu.
Sa’ad da suka tsai da shi a tsakanin ginshiƙai, sai Samson ya ce wa bawan da ya riƙe hannunsa, “Ka kai ni inda zan taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da wannan haikali, don in jingina a kai.” To, haikalin ya cika da mutane maza da mata; dukan shugabannin Filistiyawa kuwa suna a can, a bisan rufin kuwa akwai mutum wajen dubu uku maza da mata suna kallon Samson yana wasa. Sa’an nan Samson ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ya Allah ka tuna da ni, ka ƙarfafa ni sau ɗaya nan kaɗai, ka bar ni da bugu ɗaya kawai in ɗauki fansa a kan Filistiyawa domin idanuna.” Sa’an nan Samson ya kai hannuwansa ga ginshiƙan waɗanda haikalin yake a kai, ya jingina jikinsa, hannunsa dama yana a ɗaya, hannun hagu kuma na ɗayan, Samson ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Sa’an nan da dukan ƙarfinsa ya tura haikali ya fāɗa a kan shugabanni da dukan mutanen da suke ciki. Ta haka ya kashe mutane da yawa fiye da yayinda yake da rai.
Sa’an nan ’yan’uwansa da dukan dangin mahaifinsa suka gangaro don su ɗauke shi. Suka kawo shi suka binne tsakanin Zora da Eshtawol a kabarin Manowa mahaifinsa. Ya yi mulkin Isra’ila shekara ashirin.
Gumakan Mika
To, wani mutum mai suna Mika daga ƙasar tudu ta Efraim ya ce wa mahaifiyarsa, “Shekel dubu ɗaya da ɗari ɗaya na azurfa da aka ɗauka daga gare ki wanda kuma ji kin furta la’ana a kai, azurfan yana wurina; ni ne na ɗauka.”
Sa’an nan mahaifiyarsa ta ce, “Ubangiji yă albarkace ka ɗana!”
Sa’ad da ya mayar da azurfa dubu ɗaya da ɗari ɗaya na shekel wa mahaifiyarsa, sai ta ce, “Na ba da azurfata ga Ubangiji don ɗana yă sassaƙa sura yă kuma yi zubin gunki. Zan mayar maka.”
Saboda haka ya mayar da azurfan wa mahaifiyarsa, ita kuwa ta ɗauki azurfa ɗari biyu na shekel ta ba wa maƙeri, wanda ya mai da su sura da kuma gunki. Aka kuwa sa su a gidan Mika.
To, wannan mutum Mika yana da ɗakin gumaka, ya yi efod da waɗansu gumaka, ya kuma naɗa ɗaya daga cikin ’ya’yansa firist nasa. A kwanakin Isra’ila ba ta da sarki; kowa yana yin abin da ya ga dama.
Wani saurayi Balawe daga Betlehem a Yahuda, wanda yake zama cikin zuriyar Yahuda, ya bar garin ya tafi neman inda zai zauna. A hanyarsa17.8 Ko kuwa Don yin sana’arsa ya zo gidan Mika a ƙasar tudu ta Efraim.
Mika ya ce masa, “Daga ina kake?”
Ya ce, “Ni Balawe ne daga Betlehem a Yahuda, ina kuwa neman wurin zauna ne.”
Sa’an nan Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni ka zama mini mahaifi da firist, zan kuwa ba ka azurfa goma na shekel a shekara, tufafinka da kuma abincinka.” Sai Balawen ya tafi. Saboda haka Balawen ya yarda ya zauna tare da shi, ɗan saurayin kuwa ya zama kamar ɗaya daga cikin ’ya’yansa. Sa’an nan Mika ya naɗa Balawen, saurayin kuwa ya zama masa firist ya kuma zauna a gidansa. Mika ya ce, “Yanzu na san cewa Ubangiji zai yi mini alheri, da yake Balawen nan ya zama firist nawa.”
Mutanen Dan sun zauna a Layish
To, a kwanakin nan Isra’ila ba ta da sarki.
A kwanakin kuwa zuriyar Dan tana neman wurinsu na zama, gama ba su riga sun sami gādo tare da kabilan Isra’ila ba. Saboda haka mutanen Dan suka aika jarumawa guda biyar daga Zora da Eshtawol don su leƙi asirin ƙasar su kuma bincike ta. Waɗannan mutanen sun wakilci dukan kabilar. Suka ce musu, “Ku je, ku bincike ƙasar.”
Mutanen suka shiga ƙasar tudu ta Efraim suka zo gidan Mika, inda suka kwana. Sa’ad da suka yi kusa da gidan Mika, sai suka gane muryar saurayin nan Balawe; saboda haka suka shiga wurin suka tambaye shi, “Wa ya kawo ka nan? Me kake yi a nan? Me ya sa kake a nan?”
Ya gaya musu abin da Mika ya faɗa masa ya ce, “Ya ɗauke ni aiki ya kuma sa in zama masa firist.”
Sa’an nan suka ce masa, “Muna roƙonka ka nemi mana nufin Allah don mu sani ko tafiyarmu tana da nasara.”
Firist ya amsa ya ce, “Ku sauka lafiya, gama tafiyarku tana da yardan Ubangiji.”
Saboda haka mutum biyar ɗin suka tashi suka iso Layish, inda suka ga mutane suna zamansu a huce, kamar Sidoniyawa, ba sa zato ga tsaro. Kuma da yake ƙasarsu ba ta bukata kome, suna da wadata. Suna kuma nesa da Sidoniyawa, ba sa kuma hulɗa da kowa.
Da suka komo Zora da Eshtawol, ’yan’uwansu suka tambaye su, “Me kuka gano?”
Suka ce, “Ku zo mu yaƙe su! Mun ga ƙasar tana da kyau sosai. Ba za ku yi wani abu ba? Kada ku yi wata-wata, ku je kun mallaki ƙasar. Sa’ad da kun kai can, za ku iske mutanen suna zama a sake, ƙasar kuwa mai faɗi ce wadda Allah ya sa a hannuwanku, ƙasar da ba tă rasa kome ba.”
Sai mutane ɗari shida daga kabilar Dan suka yi ɗamarar yaƙi, suka tashi daga Zora da Eshtawol. A kan hanyarsu suka kafa sansani kusa da Kiriyat Yeyarim a Yahuda. Shi ya sa a ana kira wurin nan yamma da Kiriyat Yeyarim Mahane Dan18.12 Mahane Dan yana nufin Sansanin Dan. har wa yau. Daga can suka tafi ƙasar tudu ta Efraim suka zo gidan Mika.
Sa’an nan mutum biyar ɗin nan da suka leƙi asirin ƙasar Layish suka ce wa ’yan’uwansu, “Kun san cewa ɗaya daga cikin gidajen nan yana da efod, waɗansu allolin iyali, siffar da aka sassaƙa da kuma gunki na zubi? To, kun san abin da za ku yi.” Saboda haka suka juya a wurin suka shiga gidan saurayin nan Balawe a wajen Mika suka gaishe shi. Mutanen Dan ɗari shida da suka sha ɗamarar yaƙi suka tsaya a bakin ƙofa. Sai mutum biyar da suka leƙi asirin ƙasar suka shiga ciki suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi yayinda firist ɗin tare da mutane ɗari shida da suka yi ɗamarar yaƙi suna tsaye a bakin ƙofa.
Sa’ad da waɗannan mutane suka shiga gidan Mika suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi, sai firist ya ce musu, “Me kuke yi?”
Suka ce, “Ka yi shiru! Kada ka ce wani abu. Zo tare da mu, ka zama mahaifinmu da kuma firist. Bai fi maka ka yi wa kabila da kuma zuriya a Isra’ila aikin firist ba, da ka bauta wa iyali guda kawai?” Sai firist ya yi farin ciki. Ya ɗauki efod, sauran allolin gida da siffar da aka sassaƙa ya tafi tare da mutanen. Suka sa ’ya’yansu ƙanana a gaba, dabbobinsu da mallakansu a gabansu, suka juya suka tafi.
Sa’ad da suka yi ɗan nisa daga gidan Mika, sai aka kira mutanen da suke maƙwabtakar da Mika suka taru suka bi mutanen Dan suka cim musu. Da suna ihu suna binsu, sai mutanen Dan suka waiga suka cewa Mika, “Mece ce damuwarka da ka kira mutanenka su zo su fāɗa mana?”
Ya amsa ya ce, “Kun kwashe allolin da na yi, da kuma firist nawa, kuka tafi. Me kuma nake da shi? Yaya za ku ce, ‘Mece ce damuwata?’ ”
Mutanen Dan suka ce, “Kada ka kuskura ka ce kome, in ba haka ba mutanen nan za su harzuƙa, da kai da iyalinka duka ku rasa rayukanku.” Saboda haka mutanen Dan suka kama hanyarsu, Mika kuwa da ya ga an fi ƙarfinsa, sai ya juya ya koma gida.
Sa’an nan suka ɗauko abin da Mika ya yi, da firist nasa, suka tafi Layish, suka fāɗa wa mutanen da suke zaman lafiya, ransu kuma a kwance. Suka fāɗa musu suka kuma ƙone birninsu. Ba wanda zai cece su domin suna nesa da Bet-Sidon kuma ba sa hulɗa da kowa. Birnin yana a kwari kusa da Bet-Rekob.
Mutanen Dan suka sāke gina birnin suka zauna a can. Suka sa wa birnin suna Dan, wato, sunan kakansu Dan, wanda aka haifa wa Isra’ila, ko da yake a dā ana kira birnin Layish. A can mutanen Dan suka kafa wa kansu gumaka, Yonatan ɗan Gershom, ɗan Musa,18.30 Rubutun al’adu na dā na Ibraniyanci, da waɗansu rubuce-rubucen hannun Seftuwajin da na Bulget; da Nassin Masoretik Manasse da ’ya’yansa maza firistoci ne na kabilar Dan har lokacin da aka kwashe mutane zuwa bauta. Suka ci gaba da amfani da gumakan da Mika ya yi, a duk wannan lokacin gidan Allah yana a Shilo.
Balawe da ƙwarƙwararsa
A kwanakin nan Isra’ila ba su da sarki.
To, wani Balawe wanda yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Efraim ya ɗauko wa kansa ƙwarƙwara daga Betlehem cikin Yahuda. Amma ba tă yi aminci ba. Ta bar shi ta komo gidan mahaifiyarta a Betlehem, a Yahuda. Bayan ta zauna a can wajen wata huɗu, sai mijinta ya je wajenta biko don yă rarashe ta komo. Ya tafi tare bawansa da kuma jakuna biyu. Sai ta shigar da shi gidan mahaifinta, sa’ad da mahaifinta ya gan shi, ya marabce shi da murna. Surukinsa, mahaifin yarinyar, ya sha kansa, yă dakata; saboda haka ya dakata tare da shi har kwana uku, yana ci yana sha, yana kuma kwanciya a can.
A rana ta huɗu suka tashi da sassafe ya kuma yi shiri yă tafi, amma mahaifinta yarinyar ya ce wa surukinsa, “Ka ɗan ci wani abu don ka sami ƙarfi; sa’an nan ka tafi.” Saboda haka suka zauna su biyu suka ci suka sha tare. Bayan haka sai mahaifin yarinyar ya ce, “Don Allah ka kwana ka ji wa kanka daɗi.” Sa’ad da mutumin ya tashi zai tafi, sai surukinsa ya roƙe shi, saboda haka ya kwana a wannan dare. Da sassafen kashegari rana ta biyar, ya tashi zai tafi, sai mahaifin yarinyar ya ce, “Ka ɗan zauna ka shaƙata sai rana ta yi sanyi mana!” Saboda haka su biyu suka zauna suka ci abinci tare.
Sa’ad da mutumin da ƙwarƙwaransa da bawansa, suka tashi don su tafi, surukinsa, mahaifin yarinyar ya ce, “Duba, rana ta kusan fāɗuwa, yamma ta riga ta yi, ka kwana a nan. Ka sāke kwana ka ji wa ranka daɗi. Kashegari da sassafe za ka iya tashi ka kama hanyarka zuwa gida.” Amma bai so ya sāke kwana a can ba, mutumin ya tashi ya tafi ya bi ta Yebus (wato, Urushalima), tare da jakunansa biyu da aka yi musu shimfiɗa da kuma ƙwarƙwaransa.
Sa’ad da suka yi kusa da Yebus dare kuma ya riga ya yi, bawan ya ce wa maigidansa, “Mu dakata a birnin nan na Yebusiyawa mu kwana.”
Maigidansa ya ce, “A’a. Ba za mu shiga birnin baƙi waɗanda mutanensu ba Isra’ilawa ba. Za mu ci gaba zuwa Gibeya.” Ya kuma ce, “Zo, mu yi ƙoƙari mu kai Gibeya ko Rama mu kwana a ɗaya cikinsu.” Saboda haka suka ci gaba, rana tana fāɗuwa sa’ad da suka yi kusa da Gibeya a Benyamin. A can suka dakata don su kwana, suka tafi suka zauna a dandali birnin, amma wani ya shigar da su gidansa da daren.
A wannan yamma sai ga wani tsoho daga ƙasar tudu ta Efraim, wanda yake zama a Gibeya (mutane wurin kuwa mutanen Benyamin ne), ya shigo daga wurin aiki a gonaki. Sa’ad da ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, sai tsohon ya yi tambaya ya ce, “Ina za ku? Ina kuka fito?”
Balawen ya ce, “Muna fito daga Betlehem a Yahuda za mu wani lungu a ƙasar tudu ta Efraim inda nake da zama. Na tafi Betlehem a Yahuda, ga shi kuwa yanzu za ni gidan Ubangiji. Ba wanda ya shigar da ni gidansa. Muna da ƙara da abinci don jakunanmu, muna kuma da burodi da ruwan inabi dominmu da bayinka, ni, baiwarka da kuma saurayin nan tare da mu. Ba ma bukatar kome.”
Tsohon ya ce, “Na marabce ku a gidana. Bari ni ba ku duk abin da kuke bukata. Kada ku dai kwana a dandali.” Saboda haka sai kai shi zuwa gidansa ya ciyar da jakunansa. Bayan sun wanke ƙafafunsu, sai aka ba su abinci da abin sha.
Yayinda suke jin wa kansu daɗi, sai waɗansu ’yan iska daga birnin suka kewaye gidan. Suna bubbuga ƙofar, suna kira tsohon da yake da gidan suna cewa, “Ka fito mana da mutumin nan a gidanka domin mu yi jima’i da shi.”
Maigidan ya fita waje ya ce musu, “A’a, abokaina, kada ku yi abin kunyan nan. Da yake mutumin nan baƙona ne, kada ku yi rashin kunyan nan. Duba, ga ’yata da ba tă taɓa sanin namiji ba da kuma ƙwarƙwaransa. Zan fito muku da su a waje yanzu, za ku kuwa iya yin ko mene ne da kuke so da su. Amma wannan mutum, kada ku yi abin kunya.”
Amma mutanen ba su saurare shi ba. Saboda haka mutumin ya ba da ƙwarƙwaransa, suka yi mata fyaɗe suka yi lalata da ita dukan dare, gari yana wayewa sai suka bar ta. Da safe matar ta koma gidan da maigidanta yake, ta fāɗi a ƙofa ta kwanta a can har rana ta yi.
Sa’ad da maigidanta ya tashi da safe ya buɗe ƙofar gidan don yă fita ya ci gaba da tafiyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa, ta fāɗi a bakin ƙofar gidan da hannuwanta a madogarar ƙofar. Ya ce mata, “Tashi; mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya sa ta a kan jakinsa ya kama hanyar gida.
Da ya kai gida, sai ya ɗauki wuƙa ya yayyanka ƙwarƙwaransa gunduwa-gunduwa, kashi goma sha biyu ya aika da su a ko’ina a Isra’ila. Duk wanda ya gani, sai ya ce, “Ba a taɓa gani ko yin irin wannan abu ba, tun lokacin da Isra’ilawa suka fito daga Masar. Ku yi tunani wannan! Ku kuma yi la’akari! Ku gaya mana abin da za mu yi!”
Isra’ila sun yaƙi mutanen Benyamin
Sa’an nan dukan Isra’ilawa daga Dan zuwa Beyersheba kuma daga ƙasar Gileyad mutane kamar mutum guda suka fito suka taru a gaban Ubangiji a Mizfa. Shugabanni dukan kabilan mutane na kabilan Isra’ila suka zazzauna a wurarensu a taron jama’ar Allah, mayaƙa dubu ɗari huɗu masu ɗamara da takuba. (Mutanen Benyamin suka ji cewa Isra’ilawa sun haura zuwa Mizfa.) Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Gaya mana yadda wannan mugun abu ya faru.”
Sai Balawen, mijin matar da aka kashe ya ce, “Ni da ƙwarƙwarata mun zo Gibeya a Benyamin don mu kwana. Da dad dare mutanen Gibeya suka bi ni suka kewaye gidan da niyya su kashe ni. Suka yi wa ƙwarƙwarata fyaɗe, har ta mutu. Na ɗauki ƙwarƙwarata na yayyanka gunduwa-gunduwa na aika da shi ga kowane yankin gādon Isra’ila, domin sun aikata mugu abu da abin kunya a Isra’ila. To, dukanku Isra’ilawa, sai ku yi magana ku kuma yanke hukuncinku.”
Dukan mutane suka tashi kamar mutum ɗaya, suna cewa “Ba waninmu da zai tafi gida. Sam, babu ko ɗayanmu da zai koma gidansa. Amma yanzu ga abin da za mu yi wa Gibeya. Za mu haura mu fāɗa yadda ƙuri’a ta nunar. Za mu ɗauko mutum goma a kowane mutum ɗari daga dukan kabilan Isra’ila, da ɗari a dubu, da kuma dubu a dubu goma, domin a tanada wa mayaƙan. Sa’an nan, sa’ad da mayaƙan suka iso Geba a Benyamin, za su yi da su daidai bisa ga muguntar da suka yi a Isra’ila.” Saboda haka dukan mutane Isra’ilawa suka taru suka kuma haɗu kamar mutum guda don su fāɗa wa birnin da yaƙi.
Kabilan Isra’ila suka aika jakadu a ko’ina a cikin kabilar Benyamin cewa, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata? Yanzu fa sai ku fitar da waɗannan ’yan iskan da suka aikata wannan abu na Gibeya don mu kashe su mu kawar da mugunta daga Isra’ila!”
Amma mutanen Benyamin ba su saurari ’yan’uwansu Isra’ilawa ba. Daga biranensu suka tattaru a Gibeya don su yaƙi Isra’ilawa. Nan da nan mutanen Benyamin suka tattara mayaƙa dubu ashirin da shida masu takuba daga biranensu, ban da mayaƙa ɗari bakwai da aka zaɓa daga mazauna a Gibeya. Cikin dukan mayaƙan nan akwai zaɓaɓɓu mutane ɗari bakwai waɗanda su bahagwai ne, kowanne yana iya harbin gashin guda na kai da majajjawa ba kuskure.
Isra’ila kuwa, ban da Benyamin, sun tara mayaƙa masu takobi dubu ɗari huɗu, dukansu gwanayen yaƙi ne.
Sai Isra’ilawa suka haura zuwa Betel20.18 Ko kuwa zuwa gidan Allah; haka ma a aya 26. suka nemi nufin Allah, suka ce, “Wane ne a cikinmu zai fara fāɗa wa mutanen Benyamin?”
Ubangiji ya ce, “Yahuda ce za tă fara.”
Kashegari sai Isra’ilawa suka tashi suka kafa sansani kusa da Gibeya. Mutanen Isra’ila suka fita yaƙi da mutane Benyamin suka kuma ja dāgār yaƙi a Gibeya. Mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya suka kashe mutum dubu ashirin da biyu na Isra’ilawa a dāgār yaƙi a ranar. Amma mutanen Isra’ila suka ƙarfafa juna, suka sāke koma inda suka ja dāgā a rana ta farko. Isra’ilawa suka haura suka yi kuka a gaban Ubangiji, har yamma, suka nemi nufin Ubangiji. Suka ce, “Mu sāke koma yaƙi da mutanen Benyamin, ’yan’uwanmu?”
Ubangiji ya ce, “Ku haura ku fāɗa musu.”
Sai Isra’ilawa suka matsa kusa da Benyamin a rana ta biyu. A wannan lokaci, da mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya don su yaƙe su, sai suka sāke kashe Isra’ilawa dubu goma sha takwas, dukansu ɗauke da takuba.
Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji. Isra’ilawa suka nemi nufin Ubangiji (A kwanakin nan akwatin alkawarin Allah yana can, Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, kuwa yana hidima a gabansa.) Suka ce, “Mu sāke haura mu yi yaƙi da mutanen Benyamin ’yan’uwanmu, ko a’a?”
Ubangiji ya ce, “Ku je, gama gobe zan ba da su a hannuwanku.”
Sa’an nan Isra’ila ta yi kwanto kewaya da Gibeya. Suka haura su kara da mutanen Benyamin a rana ta uku suka ja dāgā a Gibeya kamar dā. Mutanen Benyamin suka fito su same su aka kuma jawo su nesa da birnin. Suka fara karkashe Isra’ilawa kamar dā, har aka kashe wajen mutum talatin a filaye da kuma a hanyoyi, wadda take zuwa Betel da kuma wadda take zuwa Gibeya. Yayinda mutanen Benyamin suna cewa, “Muna cin nasara a kansu kamar dā,” Isra’ilawa kuwa suna cewa, “Mu yi ta jan da baya mu janye su daga birni zuwa kan hanyoyi.”
Dukan mutanen Isra’ila suka taso daga wurarensu suka ja dāgā a Ba’al-Tamar, Isra’ilawan da suka yi kwanto a yammancin Geba kuwa suka fito. Sa’an nan jarumai Isra’ila dubu goma suka yi gaba suka kai wa Gibeya hari. Yaƙi kuwa ya yi zafi har mutane Benyamin ba su san masifa tana dab da su ba. Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Benyamin a gaban Isra’ila; a ranar kuwa Isra’ilawa sun kashe mutum 25,100 na mutanen Benyamin, dukansu ɗauke da takuba. Sa’an nan Benyamin suka ga an ci su.
To, mutanen Isra’ila sun yi ta ja da baya daga mutanen Benyamin domin suna dogara ga waɗanda sa su yi kwanto kusa da Gibeya ne. Mutanen da suke kwanto suka yi wuf suka ruga cikin Gibeya, suka bazu suka kuma karkashe dukan waɗanda suke a birnin. Mutanen Isra’ila sun riga sun shirya da ’yan kwanton cewa su murtuke hayaƙi daga birnin, a sa’an nan ne mutanen Isra’ila za su juya su fāɗa wa mutane Benyamin da yaƙi.
Mutanen Benyamin sun fara karkashe mutum talatin na Isra’ila, sai suka ce, “Muna cin nasara a kansu kamar dā.” Amma da alamar hayaƙi ya fara murtukewa daga birnin, sai mutanen Benyamin suka juya suka ga hayaƙi yana murtukewa ko’ina a cikin birnin zuwa sararin sama. Sa’an nan mutanen Isra’ila suka juyo musu, mutanen Benyamin kuwa suka tsorata domin sun gane masifa ta zo musu. Saboda haka suka tsere a gaban Isra’ila zuwa wajen hamada, amma ba su iya tsere wa yaƙin ba. Mutanen Isra’ila da suka fito daga cikin birnin suka karkashe su a can. Suka kewaye mutanen Benyamin, suka kore su, suka fatattake su a wajajen Gibeya a gabashi. Mutum dubu goma sha takwas na mutanen Benyamin suka mutu dukansu kuwa jarumai ne. Da suka juya suka juya suka tsere zuwa wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, Isra’ilawa suka kashe mutum dubu biyar a kan hanyoyi. Suka yi ta matsa wa mutanen Benyamin har zuwa Gidom suka kashe mutum dubu biyu kuma.
A ranar kuwa mutanen Benyamin dubu ashirin da biyar ne aka kashe, dukansu jarumai. Amma mutane ɗari shida suka juya suka tsere wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, inda suka zauna wata huɗu. Mutanen Isra’ila suka koma wurin mutanen Benyamin suka kashe dukan waɗanda suke a birnin, tare da dabbobi da kome da suka samu. Dukan garuruwan da suka samu sun ƙone su ƙaf.
Mata don mutanen Benyamin
Mutanen Isra’ila sun riga sun yi rantsuwa a Mizfa cewa, “Ba ɗayanmu da zai ba da ’yarsa aure ga mutumin Benyamin.”
Sai mutanen suka tafi Betel,21.2 Ko kuwa zuwa gidan Allah inda suka zauna a gaban Allah har yamma, suna tā da muryoyinsu suna kuka mai zafi. Suka ce, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, “Me ya sa wannan abu ya faru da Isra’ila? Don me kabila ɗaya daga Isra’ila za tă ɓace a yau?”
Kashegari da sassafe mutane suka gina bagade suka miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama.
Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji ba?” Gama an yi rantsuwa cewa duk wanda ya kāsa zuwa taro a gaban Ubangiji a Mizfa lalle a kashe shi.
To, Isra’ilawa suka yi juyayin ’yan’uwansu, mutanen Benyamin. “Yau an hallaka kabila daga cikin Isra’ila. Yaya za mu ba wa waɗanda suka rage mata, da yake mun riga mun yi rantsuwa a gaban Ubangiji, ba za mu ba su ɗaya daga ’ya’yanmu su aura ba?” Sa’an nan suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji a Mizfa ba?” Sai su gane cewa babu wani daga Yabesh Gileyad da ya zo sansani don taron. Gama da aka yi ƙidaya mutane, sai aka gane cewa babu wani daga mutanen Yabesh Gileyad da yake a can.
Saboda haka sai taron ya umarci jarumai dubu goma sha biyu su je Yabesh Gileyad su karkashe waɗanda suke zaune a can, duk da mata da yara. Suka ce musu, “Ga abin da za ku yi. Ku karkashe duk namiji da kowace macen da ta riga ta san namiji.” Suka samu a cikin mutanen da suke zaune a Yabesh Gileyad mata ɗari huɗu da ba su taɓa kwana da namiji ba, suka kwashe su zuwa sansani a Shilo a Kan’ana.
Sa’an nan dukan taro suka aika wa mutanen Benyamin da suke a Dutsen Rimmon cewa yaƙi ya ƙare, yanzu sai salama. Saboda haka mutanen Benyamin suka komo a lokacin aka kuma ba su matan Yabesh Gileyad nan da aka bari da rai. Amma matan ba su ishe su duka ba.
Mutanen kuwa suka yi juyayi saboda mutanen Benyamin, domin Ubangiji ya yi gibi a cikin kabilan Isra’ila. Shugabannin taron suka ce, “Da matan Benyamin da aka hallaka, yaya za mu yi da mazan da suka ragu da ba su sami mata ba?” Suka ce, “Dole mutanen Benyamin da suka ragu su sami gādo, domin kada wata kabila a Isra’ila ta ɓace. Ba za mu iya ba su ’yan matanmu su zama matansu ba, da yake mu Isra’ilawa mun riga mun yi wannan rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne wanda ya ba da ’yarsa aure ga mutum Benyamin.’ Sai suka tuna, akwai bikin Ubangiji da sukan yi shekara-shekara a Shilo ya yi kusa. Shilo yana arewancin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.”
Saboda haka suka cewa mutanen Benyamin, “Ku je ku ɓuya a gonakin inabi ku lura. Sa’ad da ’yan matan Shilo suka fito waje don su yi rawa, ku fito a guje daga gonakin inabi, kowannenku yă kama wa kansa mata daga cikin ’yan matan Shilo, ku tafi ƙasar Benyamin. Sa’ad da iyayensu maza ko ’yan’uwansu suka kawo mana ƙara, za mu ce musu, ‘Ku yi mana alheri ku bar su, domin ba mu samo musu mata ba lokacin yaƙi, ku kuma marasa laifi ne, tun da yake ba ku ba da ’ya’yan matanku gare su ba.’ ”
Haka mutanen Benyamin suka yi. Yayinda ’yan matan suke rawa, kowane mutum ya kama ɗaya ya yi gaba da ita ta zama matarsa. Sa’an nan suka komo ƙasar gādonsu suka sāke giggina garuruwan suka kuwa zauna a cikinsu.
A lokacin, Isra’ilawa sun bar wurin suka tafi gida zuwa ga kabilansu da zuriyoyinsu, kowane zuwa gādonsa.
A kwanakin Isra’ila ba ta da sarki; kowa ya yi abin da ya ga dama.