- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Ishaya
Ishaya
Ishaya
Ish
Ishaya
Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda.
Al’umma mai tayarwa
Ku kasa kunne, ya sammai! Ki saurara, ya duniya!
Gama Ubangiji ya yi magana,
“Na yi renon ’ya’ya, na kuma raya su,
amma sun tayar mini.
Saniya ta san maigidanta,
jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa,
amma Isra’ila ba su sani,
mutanena ba su gane ba.”
Kash, ya ke al’umma mai zunubi,
mutane cike da laifi,
tarin masu aikata mugunta,
’ya’yan da aka miƙa wa lalaci!
Sun yashe Ubangiji;
sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila
suka juya masa baya.
Me ya sa za a ƙara yin muku dūka?
Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa?
An yi wa dukan kanku rauni,
zuciyarku duk tana ciwo.
Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku
ba lafiya,
sai miyaku da ƙujewa
da manyan gyambuna,
ba a tsabtacce su ba ko a daure
ko shafa musu magani.
Ƙasarku ta zama kufai,
an ƙone biranenku da wuta;
baƙi suna ƙwace gonakinku
a idanunku,
ta zama kango kamar sa’ad da baƙi suka rushe ta.
An bar diyar Sihiyona
kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi,
kamar bukka a gonar kabewa,
kamar birnin da aka kewaye da yaƙi.
Da ba a ce Ubangiji Maɗaukaki
ya bar mana raguwar masu rai ba,
da mun zama kamar Sodom,
da mun zama kamar Gomorra.
Ku saurari maganar Ubangiji,
ku masu mulkin Sodom;
ku kasa kunne ga dokar Allahnmu,
ku mutanen Gomorra!
Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku,
mene ne suke a gare ni?”
Ina da isashen hadayun ƙonawa,
na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba;
ba na jin daɗin
jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.
Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana,
wa ya nemi wannan daga gare ku,
da kuke kai da kawowa a filayen gidana?
Ku daina kawo hadayu marasa amfani!
Turarenku abin ƙyama ne gare ni.
Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini,
ba zan iya jure wa mugun taronku ba.
Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku
na ƙi su.
Sun zama mini kaya;
na gaji da ɗaukansu.
Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a,
zan ɓoye fuskata daga gare ku;
ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa,
ba zan kasa kunne ba.
Hannuwanku sun cika da jini!
Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku.
Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana;
Ku daina aikata mugunta.
Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.
Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.1.17 Ko kuwa / ku tsawata wa masu zalunci
Ku ba wa marayu hakkinsu,
ku taimaki gwauruwa.
Ubangiji ya ce,
“Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare,
Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura,
za su zama fari kamar ƙanƙara;
ko da sun yi ja kamar mulufi,
za su zama kamar ulu.
In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya,
za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar;
amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa,
za a kashe ku da takobi.”
Ni Ubangiji na faɗa.
Dubi yadda amintacciyar birni
ta zama karuwa!
Dā ta cika da yin gaskiya;
dā masu adalci a can suke zama,
amma yanzu sai masu kisankai kaɗai!
Azurfarki ta zama jebu,
an gauraye ruwan inabinki mafi kyau da ruwa.
Masu mulkinki ’yan tawaye ne,
abokan ɓarayi;
dukansu suna ƙaunar cin hanci
suna bin kyautai.
Ba sa taɓa tsare marayu a ɗakin shari’a;
ba sa taimakon gwauruwa.
Saboda haka Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki,
Mai Iko nan na Isra’ila, ya furta,
“Kai, zan sami hutu daga maƙiyana
in kuma yi ramuwa a kan abokan gābana.
Zan juye hannuna a kanki;
zan wanke ke sarai
in fitar da dukan ƙazantarki.
Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can,
mashawartanki kamar yadda suke da fari.
Bayan haka za a ce da ke
Birnin Masu Adalci,
Amintacciyar Birni.”
Za a fanshi Sihiyona da adalci,
masu tubanta kuma da aikin gaskiya.
Amma za a karye ’yan tawaye da masu zunubi,
waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka.
“Za ku ji kunya saboda masujadan ƙarƙashin itatuwan oak
da kuka yi farin ciki;
za a kunyata ku saboda lambun
da kuka zaɓa.
Za ku zama kamar itacen oak mai busasshen ganyaye,
kamar lambu marar ruwa.
Mutum mai ƙarfi zai zama kamar rama,
aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta;
duka za su ƙone tare,
ba kuwa wanda zai kashe wutar.”
Dutsen Ubangiji
Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima.
A kwanaki masu zuwa
za a kafa dutsen haikalin Ubangiji
a matsayin babba cikin duwatsu;
za a daga shi bisa tuddai,
kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.
Mutane da yawa za su zo su ce,
“Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji,
zuwa gidan Allah na Yaƙub.
Zai koya mana hanyoyinsa,
domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.”
Dokar za tă fito daga Sihiyona,
maganar Ubangiji daga Urushalima.
Zai shari’anta tsakanin al’ummai
zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa.
Za su mai da takubansu su zama garemani
māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa.
Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba,
ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.
Ki zo, ya gidan Yaƙub,
bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.
Ranar Ubangiji
Ka rabu da mutanenka,
gidan Yaƙub.
Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas;
suna yin duba kamar Filistiyawa
suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.
Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya;
dukiyarsu kuma ba iyaka.
Ƙasarsu ta cika da dawakai;
kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka.
Ƙasarsu ta cika da gumaka;
sukan rusuna ga aikin hannuwansu,
ga abin da yatsotsinsu suka yi.
Saboda an jawo mutum ƙasa
aka kuma ƙasƙantar da ɗan adam,
kada ku gafarta musu.2.9 Ko kuwa kada a ɗaga su
Ku tafi cikin duwatsu,
ku ɓuya cikin ƙasa
daga razanar Ubangiji
da kuma darajar ɗaukakarsa!
Za a ƙasƙantar da mai girman kai
za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai;
Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana.
Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye
domin dukan masu girman kai da masu fariya
domin dukan waɗanda aka ɗaukaka
(zai kuwa ƙasƙantar da su),
domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya,
da kuma dukan itatuwan oak na Bashan,
domin dukan dogayen duwatsu
da kuma tuddai masu tsayi,
domin kowace doguwar hasumiya
da kowace katanga mai ƙarfi,
domin kowane jirgin ruwan kasuwanci2.16 Da Ibraniyanci kowane jirgin ruwan Tarshish
da kuma jirgi mafi girma mafi kyau.
Za a jawo mai girman kai ƙasa
a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai;
Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana,
za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf.
Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu
da kuma ramummuka a ƙasa
daga razanar Ubangiji
da kuma darajar ɗaukakarsa,
sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
A wannan rana mutane za su zubar wa
jaba da jamage
gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya
da suka yi don su bauta musu.
Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu
da kuma zuwa tsagaggun duwatsu
daga razanar Ubangiji
da kuma darajar ɗaukakarsa,
sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
Ku daina dogara ga mutum,
wanda numfashi ne kawai yake da shi a hancinsa.
Wace daraja gare shi?
Hukunci a kan Urushalima da Yahuda
Yanzu ka duba fa, Ubangiji,
Ubangiji Maɗaukaki,
yana shirin yă ɗauke kowane tanadi da taimako
daga Urushalima da Yahuda
dukan tanade-tanaden abinci da kuma dukan tanade-tanaden ruwa,
jarumi, da soja,
alƙali da annabi
masu duba da dattijo,
shugaban sojojin hamsin da mutum mai makami,
mai ba da shawara, gwanin sarrafa abubuwa da mai gwanintan dabo.
“Zan sa ’yan yara su zama shugabanninsu;
’yan yara kurum za su yi mulkinsu.”
Mutane za su zalunci juna
mutum da mutum, maƙwabci da maƙwabci.
Yara za su rena tsofaffi,
ƙasƙantacce zai rena mai daraja.
Mutum zai kama ɗaya daga cikin ’yan’uwansa
a gidan mahaifinsa ya ce,
“Kana da abin sawa, ka zama shugabanmu;
wannan kango kuma yă zama a ƙarƙashinka!”
Amma a ranan nan zai tā da murya ya ce,
“Ba ni ba dai.
Ba ni da abinci ko abin sawa a gidana;
kada ka mai da ni shugaban mutane.”
Urushalima tana tangaɗi,
Yahuda yana fāɗuwa;
maganganunsu da ayyukansu suna gāba da Ubangiji,
suna rena ɗaukakar kasancewarsa.
Fuskokinsu shaidu ne a kansu;
suna nuna zunubinsu a fili kamar yadda Sodom ya yi;
ba sa ma ɓoye shi.
Kaitonsu!
Sun jawo wa kansu masifa.
Ku faɗa wa masu adalci cewa kome zai zama musu da kyau,
gama za su ji daɗin aikin da hannuwansu suka yi.
Kaiton masu mugunta! Masifa tana a kansu!
Za a rama abin da hannuwansu suka yi.
Matasa suna zalunta mutanena,
mata suna mulki a bisansu.
Ya mutanena, jagorarinku suna ɓad da ku;
suna karkatar da ku daga hanya.
Ubangiji ya ɗauki mazauninsa a cikin ɗakin shari’a;
ya tashi don yă shari’anta mutane.
Ubangiji yana shari’a
da dattawa da kuma shugabannin mutanensa,
“Ku ne kuka lalace gonar inabina;
ganimar talakawa suna a gidajenku.
Ina dalilin da kuke marmatsa mutanena
kuna gurgurje fuskokin talakawa?”
Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
Ubangiji ya ce,
“Matan Sihiyona suna da girman kai,
suna tafiya da wuya a miƙe,
da idanu masu yaudara,
suna takawa ɗaya-ɗaya a hankali,
da mundaye a ƙafafunsu, suna cas-cas.
Saboda haka Ubangiji zai kawo gyambuna a kawunan matan Sihiyona;
Ubangiji zai sa a aske kawunansu, a bar su ƙwal.”
A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu, ’yan kunnensu, kwandagansu da lulluɓinsu, kitsonsu, sarƙar da suke sa wa damatsansu da ɗamararsu, kwalabai turare da layu, da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu, tufafi masu kyau, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakar kuɗinsu da madubi, da kuma tufafin lilin da adikai, da gyale.
A maimakon ƙanshi, wari ne za a ji;
a maimakon abin ɗamara, igiya ce za a samu;
a maimakon kyakkyawan gashi, sanƙo za su kasance da shi a kai;
a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki;
a maimakon kyau, za su zama munana.
Mazanku za su mutu ta wurin takobi,
jarumawanku za su mutu a yaƙi.
Ƙofofin Sihiyona za su yi makoki su kuma yi kuka;
za tă zama wofi, za tă zauna a ƙasa.
A wannan rana mata guda bakwai
za su cafke namiji guda
su ce, “Ma ciyar da kanmu
mu kuma yi wa kanmu sutura;
ka dai bari mu ce kai ne mijinmu.
Ka ɗauke mana kunyar da za mu sha.”
Reshen Ubangiji
A wannan rana Reshen Ubangiji zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila. Waɗanda suka rage a Sihiyona, waɗanda suka rage a Urushalima, za a ce da su masu tsarki, wato, dukan waɗanda aka rubuta a cikin masu rai a Urushalima. Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta. Sa’an nan Ubangiji zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa. Za tă zama rumfa da inuwar da za tă tare zafin rana, da kuma mafaka da wurin ɓuya daga hadari da ruwan sama.
Waƙar gonar inabi
Zan rera waƙa wa ƙaunataccena
waƙa game da gonar inabinsa.
Ƙaunataccena yana da gonar inabi
a gefen tudu mai dausayi.
Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun
ya shuka mata inabi mafi kyau.
Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta
ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi.
Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin,
amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya.
“Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda,
ku shari’anta tsakanina da gonar inabina.
Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina
fiye da abin da na yi mata?
Da na nemi inabi masu kyau,
me ya sa ta ba da munana ’ya’ya?
Yanzu zan faɗa muku
abin da zan yi da gonar inabina.
Zan cire katangar da ta kewaye ta,
za tă kuwa lalace;
zan rushe bangonta,
za a kuwa tattake ta.
Zan mai da ita kango,
ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba,
sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can
Zan umarci gizagizai
kada su yi ruwan sama a kanta.”
Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki
ita ce gidan Isra’ila,
mutanen Yahuda kuma
su ne lambun farin cikinsa.
Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini;
yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.
Kaito da hukunce-hukunce
Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidaje
kuke kuma haɗa gonaki da gonaki
har babu sauran filin da ya rage
ku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar.
Ubangiji Maɗaukaki ya furta a kunnuwana,
“Tabbatacce manyan gidajen za su zama kango,
za a bar kyawawan gidajen nan ba kowa.
Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai,
mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.”
Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe
don su nufi wurin shaye-shaye,
waɗanda suke raba dare
har sai sun bugu da ruwan inabi.
Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu,
ganguna da busa da ruwan inabi,
amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba,
ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta
domin rashin fahimi;
manyan mutanensu za su mutu da yunwa
talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.
Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa
ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka;
cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara
tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu.
Ta haka za a ƙasƙantar da mutum
kuma za a ƙasƙantar da ’yan adam,
za a ƙasƙanta da masu girman kai.
Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya,
kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa.
Sa’an nan tumaki za su yi kiwo kamar yadda suke yi a wurin kiwonsu;
raguna za su yi kiwo cikin abubuwa masu kyau da suka lalace.
Kaiton waɗanda suke jan zunubi da igiyar ruɗu,
da kuma mugunta da igiyoyin keken yaƙin,
waɗanda suke cewa, “Bari Allah yă gaggauta,
bari yă hanzarta aikinsa
don mu gani.
Bari yă iso,
bari shirin Mai Tsarkin nan na Isra’ila yă zo,
don mu sani.”
Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta
nagarta kuma mugunta,
waɗanda suke mai da duhu haske
haske kuma duhu,
waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi
zaƙi kuma ɗaci.
Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikima
da kuma wayo a idonsu.
Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi
da gwanaye a haɗin abubuwan sha,
waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci,
amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.
Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe kara
kuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta,
haka saiwarsu za su ruɓa
iska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura;
gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukaki
suka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan mutanensa;
ya ɗaga hannunsa ya kuma buge su.
Duwatsu sun jijjigu,
gawawwaki kuwa suka zama kamar juji a tituna.
Saboda wannan duka, fushinsa bai huce ba,
bai kuwa janye hannunsa ba.
Ya ɗaga tuta don al’ummai masu nisa,
ya yi feɗuwa wa waɗanda suke a iyakar duniya.
Ga shi sun iso,
da sauri da kuma gaggawa!
Babu ko ɗayansu da ya gaji ko ya yi tuntuɓe,
babu ko ɗaya da ya yi gyangyaɗi ko barci;
babu abin ɗamarar da ya kunce a gindi,
ba igiyar takalmin da ta tsinke.
Kibiyoyinsu masu tsini ne,
an ɗaura dukan bakkunansu;
kofatan dawakansu sun yi kamar dutsen ƙanƙara,
ƙafafun keken yaƙinsu kamar guguwa ne.
Rurinsu ya yi kamar na zaki,
suna ruri kamar ’yan zakoki;
suna yin gurnani yayinda suke kamun abin da suke farauta
su ɗauke shi ba mai ƙwace shi.
A wannan rana za su yi ta ruri a kansa
kamar rurin teku.
Kuma in wani ya dubi ƙasar,
zai ga duhu da damuwa;
haske ma zai zama duhu ta wurin gizagizai.
Aikin Ishaya
A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. Suna kiran juna,
“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;
duniya ta cika da ɗaukakarsa.”
Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.
Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”
Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade. Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”
Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?”
Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”
Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane,
“ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba;
Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’
Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe;
kunnuwansu su kurunce,
idanunsu kuma su makance.
In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,
su ji da kunnuwansu,
su fahimta da zuciyarsu,
su kuma juyo a kuma warkar da su.”
Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?”
Ya kuma amsa,
“Sai an lalatar da biranen
ba kowa a ciki,
sai an mai da gidaje kangwaye
ƙasa kuma ta zama kango ba amfani,
sai lokacin da Ubangiji ya kori kowa
aka kuma yashe ƙasar gaba ɗaya.
Ko da yake kashi ɗaya bisa goma zai ragu a ƙasar,
za tă sāke zama kango.
Amma kamar yadda katambiri da itacen oak
sukan bar kututturai sa’ad da aka yanke su,
haka iri mai tsarkin nan zai zama kututture a ƙasar mai tsarki.”
Alamar Immanuwel
Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.
Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa7.2 Ko kuwa ya kafa sansani a da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza.
Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub,7.3 Sheyar-Yashub yana nufin raguwa za tă komo. don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki. Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba. Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.” Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,
“ ‘Ba zai faru ba,
ba zai auku ba,
gama kan Aram shi ne Damaskus,
kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin.
Cikin shekaru sittin da biyar
za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba.
Kan Efraim shi ne Samariya,
kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya.
In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba,
ba za ku dawwama ba.’ ”
Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce, “Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.”
Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.”
Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure? Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel. In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa. Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango. Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.”
A wannan rana Ubangiji zai yi feɗuwa yă kira ƙudaje daga rafuffuka masu nisa na Masar da kuma ƙudan zuma daga ƙasar Assuriya. Za su zo su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, a kan dukan ƙayayyuwa da dukan rammukan ruwa.
A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi,7.20 Wato, Yuferites. sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku. A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai. Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma. A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can. Mutane za su je can da baka da kibiyoyi, gama ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne za su rufe ƙasar. Game da dukan tuddai da dā ake nome da garemani kuwa, ba za ku ƙara je wurin ba saboda tsoron ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya; za su zama wuraren da ake kai shanu a sake su su yi ta yawo da kansu, tumaki kuma su yi ta gudu.
Assuriya kayan aikin Ubangiji
Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz.8.1 Maher-Shalal-Hash-Baz yana nufin kwashe ganima nan da nan, washe kayan da aka ci a yaƙi da hanzari; haka ma a 3. Zan kuma kira Uriya firist da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama mini amintattun shaidu.”
Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz. Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”
Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce,
“Domin wannan jama’a ta ƙi
natsattsen ruwan rafin Shilowa
suka yi ta farin ciki a kan Rezin
ɗan Remaliya,
saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu
rigyawar ruwan Kogi,8.7 Wato, Yuferites.
wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa.
Zai cika dukan gaɓoɓinsa,
yă kuma malala har zuwa bakin kogi.
Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta,
yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa.
Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka,
Ya Immanuwel!”8.8 Immanuwel yana nufin Allah tare da mu.
Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro!
Ku saurara, dukanku manisantan ƙasashe.
Ku shirya don yaƙi, ku kuma ji tsoro!
Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba;
ku ƙulla shirye-shiryenku, amma ba za su yi amfani ba,
gama Allah yana tare da mu.8.10 Da Ibraniyanci Immanuwel
Ji tsoron Allah
Ubangiji ya yi mini magana da hannunsa mai ƙarfi a kaina, yana yi mini gargaɗi kada in bi hanyar waɗannan mutane. Ya ce,
“Kada ka kira wani abu makirci
game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci;8.12 Ko kuwa Kada ka ce a yi yarjejjeniya a kowane lokacin da mutanen nan suka ce a yi yarjejjeniya
kada ji tsoron abin da suke tsoro,
kada kuma ka firgita game da shi.
Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki,
shi ne wanda za ka ji tsoro,
shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa,
zai kuwa kasance a wuri mai tsarki;
amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama
dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe
dutse kuma da zai sa su fāɗi.
Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama
tarko da raga.
Yawancinsu za su yi tuntuɓe;
za su fāɗi a kuwa ragargaza su,
za a sa musu tarko a kuma kama su.”
Ɗaura shaidar nan ta gargadi
ka kuma yimƙe umarnin Allah a cikin almajiraina.
Zan saurari Ubangiji,
wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yaƙub.
Zan dogara gare shi.
Ga ni, da yaran da Ubangiji ya ba ni. Mu alamu ne da shaidu a cikin Isra’ila daga Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a Dutsen Sihiyona.
Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai? Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani. Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu. Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu.
A gare mu an haifi yaro
Duk da haka, babu sauran baƙin ciki ga waɗanda suke shan azaba. Dā ya ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zebulun da ƙasar Naftali, amma nan gaba zai girmama Galili na Al’ummai, ta hanyar teku wadda take ta Urdun.
Mutanen da suke tafiya cikin duhu
sun ga babban haske;
a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa9.2 Ko kuwa ƙasar duhu
haske ya haskaka.
Ka fadada al’umma
ka kuma ƙara farin cikinsu;
suna farin ciki a gabanka
yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi,
kamar yadda mutane sukan yi farin ciki
sa’ad da suke raba ganima.
Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi,
kuka ji tsoro
nauyin da ya nawaita musu,
sandar da yake a kafaɗunsu,
sandar masu zaluncinsu.
Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi
da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini
zai kasance an ƙone shi
zai kuma zama abin hura wuta.
Gama a gare mu an haifa mana yaro,
a gare mu an ba da ɗa,
gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa.
Za a ce da shi
Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki
Uban Madawwami, Sarkin Salama.
Game da girmar gwamnatinsa da salama
babu iyaka.
Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa,
zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,
tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.
Ubangiji Maɗaukaki ne
ya yi niyyar aikata wannan duka.
Fushin Ubangiji a kan Isra’ila
Ubangiji ya aika da saƙon gāba da Yaƙub;
zai auka wa Isra’ila.
Dukan mutane za su san shi,
Efraim da mazaunan Samariya,
waɗanda suke magana da fariya
suna kuma ɗaga kai,
“Tubalai sun zube a ƙasa,
amma za mu sāke gina su da dutse;
an sassare itatuwan ɓaure,
amma za mu maya su da al’ul.”
Amma Ubangiji ya ƙarfafa maƙiyan Rezin gāba da su
ya kuma ingiza abokan gāba.
Arameyawa daga gabas da Filistiyawa daga yamma
sun cinye Isra’ila da buɗaɗɗen baki.
Duk da haka, fushinsa bai huce ba,
hannunsa har yanzu yana a miƙe.
Amma mutanen ba su juyo wurin wanda ya buge su ba,
balle su nemi Ubangiji Maɗaukaki.
Saboda haka Ubangiji zai yanke Isra’ila kai da wutsiya,
da reshen dabino da iwa a rana guda;
dattawa da manyan mutane su ne kai,
annabawa waɗanda suke koyar da ƙarairayi su ne wutsiya.
Waɗanda suke jagorar wannan mutane suna ɓad da su,
su ne waɗanda ake jagora aka sa suka kauce.
Saboda haka Ubangiji ba zai ji daɗin matasa ba,
ba kuwa zai ji tausayin marayu da gwauraye ba,
gama kowa marar sanin Allah ne da kuma mugu,
kowane baki yana faɗin mugayen maganganu.
Duk da haka, fushinsa bai huce ba,
hannunsa har yanzu yana a miƙe.
Tabbatacce mugunta tana ƙuna kamar wuta;
tana cin ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya,
ta sa wuta a jeji mai itatuwa masu yawa,
don yă yi murtuke hayaƙi har zuwa sama.
Ta wurin fushin Ubangiji Maɗaukaki
ƙasar za tă ci wuta
mutane kuma za su zama abin hura wutar,
babu wanda zai ji tausayin ɗan’uwansa.
A dama za su ci,
amma su ci gaba da jin yunwa;
a hagu za su ci,
amma ba za su ƙoshi ba.
Kowa zai mai da naman ’ya’yansa abinci.
Manasse zai mai da Efraim abinci, Efraim kuma yă cinye Manasse;
tare za su yi gāba da Yahuda.
Duk da haka, fushinsa bai huce ba,
hannunsa har yanzu yana a miƙe.
Kaiton waɗanda suke kafa dokokin rashin gaskiya,
waɗanda suke ba da ƙa’idodin danniya,
don su hana matalauta hakkinsu
su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena,
suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu
suna kuma yi wa marayu ƙwace.
Me za ku yi a ranan nan ta hukunci,
sa’ad da masifa ta zo daga nesa?
Ga wa za ku tafi don neman taimako?
Ina za ku bar dukiyarku?
Babu abin da zai rage sai cizon haƙora a cikin kamammu
ko mutuwa cikin waɗanda aka kashe.
Duk da haka, fushinsa bai huce ba,
hannunsa har yanzu yana a miƙe.
Hukuncin Allah a kan Assuriya
“Kaiton Assuriya, sandar fushina,
a hannun da kulkin fushina yake!
Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah,
na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi,
don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima,
yă tattake su kamar laka a tituna.
Amma ba abin da ya yi niyya ke nan ba,
ba abin da yake da shi a zuciya ba;
manufarsa shi ne yă hallaka,
yă kuma kawo ƙarshen al’ummai da yawa.
Ya ce, ‘Dukan shugabannin yaƙina ba sarakuna ba ne?’
‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba?
Hamat bai zama kamar Arfad
Samariya kuma kamar Damaskus ba?
Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka,
mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,
ba zan yi da Urushalima da siffofinta
yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ”
Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa. Gama ya ce,
“ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan,
da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi.
Na kau da iyakokin ƙasashe,
na washe dukiyarsu;
a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.
Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu
haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai;
kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai,
haka na tattara dukan ƙasashe;
ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki,
ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ”
Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma,
ko zarto yă yi wa wanda yake amfani da shi taƙama?
Sanda za tă girgiza mutumin da yake riƙe da ita,
ko kuwa kulki yă jijjiga mutumin da yake riƙe da katako!
Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki,
zai aukar da cuta mai kisa a kan ƙosassu jarumawa;
a ƙarƙashin sansaninsa zai ƙuna wuta
kamar harshen wuta.
Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta,
Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta;
a rana guda zai ƙone yă kuma cinye
ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa.
Darajar jejinsa da gonakinsa masu dausayi
za a hallaka su ɗungum,
kamar yadda ciwo yakan kashe mutum.
Sauran itatuwan jejinsa kuma za su ragu
ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su.
Raguwar Isra’ila
A wannan rana raguwar Isra’ila,
waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub,
ba za su ƙara dogara ga
wanda ya kusa hallaka su ba
amma za su dogara ga Ubangiji,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Raguwa za tă komo,10.21 Da Ibraniyanci sheyar-yashub; haka ma a aya 22. raguwar Yaƙub
za su komo ga Maɗaukaki Allah.
Ko da yake mutanenka, ya Isra’ila, sun zama kamar yashin bakin teku,
raguwa ce kurum za tă komo.
A ƙaddara hallaka,
mai mamayewa da mai adalci.
Ubangiji Maɗaukaki, zai sa
hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasa ta faru.
Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce,
“Ya mutanena masu zama a Sihiyona,
kada ku ji tsoron Assuriyawa,
waɗanda suka dūke ku da sanda
suka kuma ɗaga kulki a kanku, kamar yadda Masar ta yi.
Ba da daɗewa ba fushina a kanku zai zo ga ƙarshe
hasalata kuma za tă koma ga hallakarsu.”
Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya,
kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb;
zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye,
yadda ya yi a Masar.
A wannan rana zai ɗauke nauyi daga kafaɗarku,
nauyinsu daga wuyanku;
za a karye karkiya
domin kun yi ƙiba ƙwarai.
Sun shiga Ayiyat;
sun bi ta Migron;
sun adana tanade-tanade a Mikmash.
Suka ƙetare ta hanya, suka kuma ce,
“Za mu kwana a Geba.”
Rama ta firgita;
Gibeya ta Shawulu ta gudu.
Ki yi ihu, ya Diyar Gallim!
Ki saurara, ya Layisha!
Kayya, Anatot abin tausayi!
Madmena tana gudu;
mutanen Gebim sun ɓuya.
A wannan rana za su dakata a Nob;
za su jijjiga ƙarfinsu
a dutsen Diyar Sihiyona,
a tudun Urushalima.
Duba, Ubangiji Maɗaukaki,
zai ragargaza rassa da iko mai girma.
Za a sassare itatuwa masu ganyaye,
za a yanke dogayen itatuwa har ƙasa.
Zai sassare itatuwan jeji da gatari har ƙasa;
Lebanon zai fāɗi a gaban Mai Iko.
Reshe daga Yesse
Toho zai fito daga kututturen Yesse;
daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.
Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa,
Ruhun hikima da na fahimta,
Ruhun shawara da na iko,
Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,
zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji.
Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba,
ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;
amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a,
da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya.
Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa;
da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.
Adalci ne zai zama abin ɗamararsa
aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.
Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago
damisa za tă kwanta tare da akuya,
ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare;
ɗan yaro ne zai lura da su.
Saniya da beyar za su yi kiwo tare,
ƙananansu za su kwanta tare,
zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.
Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa,
ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.
Ba za su yi lahani ko su hallaka
wani a dutsena mai tsarki ba,
gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji
kamar yadda ruwaye suka rufe teku.
A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja. A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa,11.11 Da Ibraniyanci daga Faturos daga Kush,11.11 Wato, yankin Nilu na Bisa daga Elam, daga Babiloniya,11.11 Da Ibraniyanci Shinar daga Hamat da kuma daga tsibiran teku.
Zai tā da tuta saboda al’ummai
yă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila;
zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatse
kusurwoyi huɗu na duniya.
Kishin Efraim zai ɓace,
za a kuma kau da abokan gāban Yahuda;
Efraim ba zai yi kishin Yahuda ba,
haka ma Yahuda ba zai yi gāba da Efraim ba.
Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma;
tare za su washe mutane wajen gabas.
Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab,
Ammonawa kuma za su yi musu biyayya.
Ubangiji zai busar da
bakin tekun Masar;
da iska mai zafi zai share hannunsa
a bisa Kogin Yuferites11.15 Da Ibraniyanci Kogi
Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai
saboda mutane su iya hayewa da ƙafa.
Za a yi babbar hanya saboda raguwa mutanensa
da ta rage daga Assuriya,
kamar yadda ta kasance wa Isra’ila
sa’ad da suka fito daga Masar.
Waƙoƙin yabo
A wannan rana za ku ce,
“Zan yabe ka, ya Ubangiji.
Ko da yake a dā ka yi fushi da ni,
amma yanzu ka daina fushi da ni
ka kuwa ta’azantar da ni.
Tabbatacce Allah shi ne mai cetona;
zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba.
Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata;
ya zama mai cetona.”
Da farin ciki zan ɗebo ruwa
daga rijiyoyin ceto.
A wannan rana za ku ce,
“Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;
a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai,
a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.
Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa;
bari a sanar da wannan ga dukan duniya.
Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona,
gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”
Annabci a kan Babilon
Abubuwan da Allah ya yi magana a kai game da Babilon da Ishaya ɗan Amoz ya gani.
A tā da tuta a kan tudun da yake mai fili,
ka tā da murya gare su;
ka ɗaga hannu ka ba su alama
don su shiga ƙofofi masu alfarma.
Na umarci tsarkakana;
na umarci jarumawan yaƙina su gamsar da fushina,
waɗanda suke farin ciki a nasarata.
Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu,
sai ka ce na babban taron jama’a!
Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki,
sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa!
Ubangiji Maɗaukaki yana shirya
mayaƙa don yaƙi.
Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa,
daga iyakokin duniya,
Ubangiji da kuma fushinsa,
zai hallaka dukan ƙasar.
Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa
za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki.13.6 Da Ibraniyanci Shaddai
Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni,
ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.
Tsoro zai kama su,
zafi da azaba za su ci ƙarfinsu;
za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda.
Za su dubi juna a tsorace,
fuskokinsu a ɓace.
Duba, ranar Ubangiji tana zuwa,
muguwar rana, mai hasala da zafin fushi,
don ta mai da ƙasar kango
ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.
Taurarin sama da ƙungiyoyinsu
ba za su ba da haskensu ba.
Rana za tă yi duhu
wata kuma ba zai ba da haskensa ba.
Zan hukunta duniya saboda muguntarta,
mugaye saboda zunubansu.
Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama
in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa,
fiye da zinariyar Ofir wuyan gani.
Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki;
duniya kuma za tă girgiza daga inda take
a fushin Ubangiji Maɗaukaki,
a ranar fushinsa mai ƙuna.
Kamar barewar da ake farautarta
kamar tumaki marasa makiyayi,
haka nan kowane mutum zai koma ga mutanensa,
kowane mutum zai gudu zuwa ƙasarsa.
Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu;
dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.
Za a fyaɗa ’ya’yansu a ƙasa su yi kucu-kucu a idanunsu;
za a washe gidajensu, a kuma kwana da matansu.
Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su,
su da ba su kula da azurfa ba
kuma ba sa damuwa da zinariya.
Bakkunansu za su kashe samari;
ba za su ji tausayin jarirai ba
ba za su kuwa nuna jinƙai ga ’yan yara ba.
Babilon, kayan daraja na mulkoki,
abin fariyar Babiloniyawa,13.19 Ko kuwa Kaldiyawa
Allah zai kaɓantar da ita
kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.
Ba za ƙara kasance da mazauna kuma ba
ko a yi zama a cikinta dukan zamanai;
Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can,
ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.
Amma halittun hamada za su kwanta a can,
diloli za su cika gidajenta;
a can mujiyoyi za su zauna,
a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.
Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta,
diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma.
Lokacinta ya yi kusa,
kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba.
Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai;
zai sāke zaɓi Isra’ila
yă kuma zaunar da su a ƙasarsu.
Baƙi ma za su zo su zauna tare da su
su haɗa kai da gidan Yaƙub.
Al’ummai za su ɗauke su
su kuma kawo wurin da yake nasu.
Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummai
a matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji.
Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammu
su kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su.
A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta, za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a.
Mai danniya ya zo ga ƙarshe!
Dubi yadda fushinsa ya ƙare!
Ubangiji ya karye sandar mugaye,
sandan mulkin masu mulki,
wanda cikin fushi ya kashe mutane
da bugu marar ƙarewa,
kuma cikin fushi ya mamaye al’ummai
da fushi ba ƙaƙƙautawa.
Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama;
sun ɓarke da waƙa.
Har itatuwan fir ma da kuma al’ul na Lebanon
suna murna a kanka suna cewa,
“Yanzu da aka ƙasƙantar da kai,
babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu.”
Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya
don yă sadu da kai a zuwanka;
yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka,
dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya;
ya sa suka tashi daga kujerun sarauta,
dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai.
Duk za su amsa,
za su ce maka,
“Ashe kai ma raunana ne, kamar mu;
ka zama kamar mu.”
An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari,
tare da surutan garayunka;
tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka
tsutsotsi kuma suka rufe ka.
Yaya aka yi ka fāɗo daga sama
Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba!
An fyaɗa ka da ƙasa,
kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!
Ka yi tunani a ranka ka ce,
“Zan hau zuwa sama;
zan ɗaga kursiyina
sama da taurarin Allah;
zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro,
a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.14.13 Ko kuwa arewa; Da Ibraniyanci Zafon
Zan haura can bisa gizagizai;
zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.”
Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari,
zuwa zurfafan rami.
Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido,
suna tunani abin da zai same ka.
“Wannan mutumin ne ya girgiza duniya
ya kuma sa mulkoki suka razana,
mutumin da ya mai da duniya ta zama hamada,
wanda ya tumɓuke biranenta
bai kuma bar kamammunsa suka tafi ba?”
Dukan sarakunan duniya suna kwance a mace,
kowa a kabarinsa.
Amma an jefar da kabarinka
kamar reshen da aka ƙi;
an rufe ka da waɗanda aka kashe,
tare da waɗanda aka soke da takobi,
waɗanda suka gangara zuwa duwatsun rami.
Kamar gawar da aka tattake da ƙafa,
ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba,
gama ka hallaka ƙasarka
ka kuma kashe mutanenka.
Ba za a ƙara ambaci
zuriyarka masu aikata mugunta ba.
A shirya wuri don a yayyanka ’ya’yansa maza
saboda zunuban kakanninsu;
kada a reno su su gāji ƙasar
su cika duniya da biranensu.
“Zan yi gāba da su,”
in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta,
’ya’yanta da zuriyarta,”
in ji Ubangiji.
“Zan mai da ita wuri domin mujiyoyi
da kuma fadama;
zan share ta da tsintsiyar hallaka,”
Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
Annabci a kan Assuriya
Ubangiji Maɗaukaki ya rantse,
“Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance,
kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama.
Zan ragargazar da Assuriya a cikin ƙasata;
a kan duwatsuna zan tattake shi.
Za a ɗauke nauyin da ya sa wa mutanena,
a kuma ɗauke nauyinsa daga kafaɗunsu.”
Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya;
wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.
Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi?
Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi?
Annabci a kan Filistiyawa
Wannan abin da Allah ya yi magana ya zo ne a shekarar da Sarki Ahaz ya mutu.
Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa,
cewa sandar da ta buge ku ta karye;
daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso,
’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama.
Mafi talauci na matalauta zai sami wurin kiwo,
mabukata kuma za su kwana lafiya.
Amma zan hallakar da saiwarka da matsananciyar yunwa;
za tă kashe naka da suka rage da rai.
Ki yi ihu, ya ke ƙofa! Yi kururuwa, ya ke birni!
Ku razana, dukanku Filistiyawa!
Ƙunshin hayaƙi yana tasowa daga arewa,
kuma babu matsorata a cikin sojojinsa.
Wace amsa ce za a bayar
wa jakadun wannan al’umma?
“Ubangiji ya kafa Sihiyona,
kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.”
Annabci a kan Mowab
Abin da Allah ya yi magana a kan Mowab shi ne,
An lalatar da Ar a Mowab,
an hallaka ta da dare!
An lalatar da Kir a Mowab,
an hallaka ta da dare!
Dibon ya haura zuwa haikalinta,
zuwa masujadan kan tudu don tă yi kuka;
Mowab ta yi ihu a kan Nebo da Medeba.
An aske kowane kai
an kuma yanke kowane gemu.
A tituna sun sa tsummoki a jikunansu;
a kan rufin ɗakuna da kuma dandalin taruwa
dukansu sai makoki suke yi,
sun kwanta suna kuka.
Heshbon da Eleyale sun yi kuka da ƙarfi,
aka ji muryoyinsu ko’ina har zuwa Yahaz.
Saboda haka mayaƙan Mowab suka yi kuka da ƙarfi,
har zuciyarsu ta karai.
Zuciyata ta yi kuka a kan Mowab;
mutanenta sun gudu har zuwa Zowar,
har zuwa Eglat Shelishiya.
Sun haura zuwa Luhit,
suna tafe suna kuka;
a kan hanyar zuwa Horonayim
suna makoki saboda hallakawarsu.
Ruwayen Nimrim sun ƙafe
ciyayin kuma sun bushe;
tsire-tsire duk sun ɓace
babu sauran ɗanyen abu.
Saboda haka dukiyar da suka tara suka kuma ajiye
sun ɗauka suka ƙetare Rafin Arabim da su.
Ƙugin kukansu ya kai ko’ina a iyakar Mowab;
kururuwarsu ta kai har zuwa Eglayim,
makokinsu ya kai har zuwa Beyer-Elim.
Ruwayen Dimon sun cika da jini,
amma zan yi ƙari a kan Dimon,
zan kawo zaki a kan masu gudu na Mowab
da kuma a kan waɗanda suka ragu a ƙasar.
Ku aiko da raguna a matsayin haraji
ga mai mulkin ƙasar,
daga Sela a hamada,
zuwa dutsen Diyar Sihiyona.
Kamar tsuntsaye masu firiya
da aka kora daga sheƙa,
haka matan Mowab suke
a kogunan Arnon.
“Ku ba mu shawara,
ku yanke shawara.
Ku mai da inuwarku kamar dare,
a tsakar rana.
Ku ɓoye masu gudun hijira,
kada ku bashe masu neman mafaka.
Ku bar Mowabawa masu gudun hijira su zauna tare da ku;
ku zama mafakarsu daga mai neman hallaka su.”
Mai danniya zai zo ga ƙarshe
hallaka kuma za tă daina;
masu lalatar da ƙasa za su kare
Da ƙauna za a kafa kursiyi;
da aminci mutum zai zauna a kansa,
wani daga gidan16.5 Da Ibraniyanci tenti Dawuda,
wani wanda ta shari’antawa yakan nuna gaskiya
ya hanzarta yin adalci.
Mun ji fariyar Mowab,
mun ji yawan fariyarta da girmankanta,
fariyarta da reninta,
amma taƙamarsu ta banza ce.
Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi,
za su yi kuka mai zafi tare saboda Mowab.
Ku yi makoki ku kuma yi baƙin ciki
saboda ƙosai da kuka riƙa ci a Kir Hareset.
Gonakin Heshbon sun bushe,
inabin Sibma ma haka.
Masu mulkin al’ummai
sun tattake inabi mafi kyau,
waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer
suka bazu ta wajen hamada.
Tohonsu sun buɗu
suka kai har teku.
Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka,
saboda inabin Sibma.
Ya Heshbon, ya Eleyale,
na cika ku da hawaye!
Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna
da kuma girbinku sun ɓace.
An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya;
babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi;
babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi,
gama na kawo ƙarshen yin sowa.
Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya,
na yi baƙin ciki saboda Kir Hareset.
Sa’ad Mowab ta bayyana a masujadar bisa tudu,
tana gajiyar da kanta ne kawai;
sa’ad da ta tafi wurin tsafinta don tă yi addu’a,
babu wani amfani.
Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya riga ya yi game da Mowab. Amma yanzu Ubangiji ya ce, “Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta, ’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”
Abin da Allah ya faɗa a kan Damaskus
Abin da Allah ya faɗa game da Damaskus.
“Duba, Damaskus ba za tă ƙara zama birni ba
amma za tă zama tsibin juji.
Za a watse a bar biranen Arower
a bar wa tumaki da shanu, waɗanda za su kwanta,
ba tare da wani wanda zai tsorata su ba.
Birni mai katanga za tă ɓace daga Efraim,
ikon sarauta kuma daga Damaskus;
raguwar Aram za tă zama
kamar darajar Isra’ila,”
in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“A wannan rana ɗaukakar Yaƙub za tă ƙare;
kitsen jikinsa zai lalace.
Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye
ya kuma girbe hatsin da hannunsa
kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi
a Kwarin Refayim.
Duk da haka waɗansu kala za su ragu,
sai ka ce sa’ad da an karkaɗe itace zaitun,
aka bar ’ya’yan zaitun biyu ko uku a can ƙwanƙolin rassan,
ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassa na gefe na itace mai ’ya’ya,”
in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.
A wannan rana mutane za su nemi Mahaliccinsu
su kuma juye idanunsu ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Ba za su dubi bagade ba,
waɗanda suke aikin hannuwansu,
ba za su kuma kula da ginshiƙan Ashera ba17.8 Wato, alamun alliya Ashera.
da kuma bagadan turaren da yatsotsinsu suka yi.
A wannan rana biranensu masu ƙarfi, waɗanda suka bari saboda Isra’ilawa, za su zama kamar wuraren da aka ƙyale suka zama kufai a jeji. Za su kuma zama kango.
Kun manta da Allah Mai Cetonku;
ba ku tuna da Dutse, kagararku ba.
Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau
kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje,
ko da yake a ranar kun shuka su, kuka sa su yi girma,
da safe kuma sa’ad da kuka shuka su, kuka sa suka yi toho suka yi fure,
duk da haka girbin ba zai zama kome ba
a ranar cuta da zafin da ba ta da magani.
Kash, ga hayaniyar al’ummai masu yawa
suna hayaniya kamar rurin teku!
Kash, ga fushin mutane
suna ruri kamar rugugi kamar manyan ruwaye!
Ko da yake mutane suna ruri kamar sukuwar raƙuman ruwa,
sa’ad da ya tsawata musu za su gudu can da nisa,
aka kore su kamar yayinda iska ya hura a kan tuddai,
kamar tattake kuma a cikin guguwa.
Da yamma, sai razana ba tsammani!
Kafin safiya, duk sun ɓace!
Wannan ne rabon waɗanda suka washe mu,
rabon waɗanda suka yi mana ƙwace.
Annabci a kan Kush
Kaiton ƙasar da ake jin ƙarar fikafikai18.1 Ko kuwa na fari
a bakin kogunan Kush,18.1 Wato, yankin Nilu na Bisa
wadda ta aiko da jakadu ta teku
cikin jiragen ruwan da aka yi da kyauro a bisa ruwa.
Ku tafi, ku ’yan saƙo masu sauri,
zuwa ga dogayen mutane masu sulɓin jiki,
zuwa ga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina,
al’umma mai ƙarfin iko tana jawabin da ba a saba ji ba,
mai ƙasar da koguna suka raba.
Ku dukan mutanen duniya,
ku da kuke zama a duniya,
sa’ad da aka ɗaga tutar a kan duwatsu,
za ku gan shi,
sa’ad da kuma aka busa ƙaho,
za ku ji shi.
Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini,
“Zan yi shiru in kuma duba a hankali daga mazaunina,
kamar ƙuna mai zafi a hasken rana,
kamar girgijen raba a lokacin girbi.”
Gama kafin girbi, sa’ad da furanni suka karkaɗe
furanni kuma suka zama ’ya’yan inabin da suka nuna,
zai faffalle rassan kuringar inabi da wuƙa,
ya yanke ya kuma kwashe rassan da suka bazu.
Duk za a bar su wa tsuntsayen dutse su ci
da kuma namun jeji;
tsuntsaye kuma za su ci rani a kansu,
namun jeji kuma za su yi damina a kansu.
A wannan lokaci za a kawo kyautai wa Ubangiji Maɗaukaki
daga dogayen mutane masu sulɓin jiki,
daga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina,
al’umma mai ƙarfin iko na jawabin da ba a saba ji ba,
mai ƙasar da koguna suka raba.
Za a kawo kyautai zuwa Dutsen Sihiyona, wurin da Sunan Ubangiji Maɗaukaki yake.
Annabci a kan Masar
Abin da Allah ya faɗa game da Masar,
Duba, Ubangiji yana a kan girgije a sukwane
yana kuwa zuwa Masar.
Gumakan Masar sun firgita a gabansa,
zukatan Masarawa sun karai.
“Zan tā da hargitsi tsakanin mutumin Masar da mutumin Masar,
ɗan’uwa zai yi gāba da ɗan’uwa
maƙwabci ya yi gāba da maƙwabci,
birni ya yi gāba da birni,
mulki ya yi gāba da mulki.
Masarawa za su karai,
zan kuma sa shirye-shiryensu su zama banza;
za su nemi shawarar gumaka da kuma ruhohin matattu,
za su nemi shawarar mabiya da na masu duba.
Zan ba da Masarawa
ga ikon azzalumi shugaba,
mugun sarki kuma zai yi mulki a kansu,”
in ji mai girma, Ubangiji Maɗaukaki.
Ruwayen kogi za su ƙafe,
bakin kogi zai shanye yă kuma bushe.
Wuriyoyi za su yi wari;
rafuffukan Masar za su yi ta raguwa har su ƙafe.
Iwa da jema za su bushe,
haka ma tsire-tsire kusa da Nilu,
a bakin kogi.
Kowane abin da aka shuka a gefen Nilu
zai bushe, iska ta kwashe su ƙaf.
Masu kamun kifi za su yi nishi su kuma yi makoki,
dukan waɗanda suke jefan ƙugiyoyi a Nilu;
waɗanda suke jefan abin kamun kifi a ruwa
abin kamun kifin za su zama marasa amfani.
Waɗanda suke aiki da kaɗin auduga za su karai,
masu yin lilin mai kyau za su fid da zuciya.
Masu aikin tufafi ransu zai ɓace,
kuma dukan masu samun albashi za su damu.
Shugabannin Zowan ba kome ba ne, wawaye ke kawai;
mashawarta masu hikima na Fir’auna suna ba da shawarwari marasa amfani.
Yaya za ka ce wa Fir’auna,
“Ni ɗaya ne cikin masu hikima,
almajirin sarakuna na dā can”?
Ina masu hikima suke yanzu?
Bari su nuna maka su kuma sanar
da abin da Ubangiji Maɗaukaki
ya shirya a kan Masar.
Shugabannin Zowan sun zama wawaye,
an ruɗe shugabannin Memfis19.13 Da Ibraniyanci Nof
dutsen kan kusurwa na mutanenta
su sa Masar ta kauce.
Ubangiji ya sa zuba musu
ruhun jiri;
suka sa Masar ta yi tangaɗi cikin kome da take yi,
kamar yadda mutumin da ya bugu yake tangaɗi cikin amansa.
Babu abin da Masar za tă yi,
kai ko wutsiya, reshen dabino ko iwa.
A wannan rana Masarawa za su zama kamar mata. Za su yi rawar jiki lokacin da Ubangiji Maɗaukaki ya ɗaga hannu a kansu. Ƙasar Yahuda kuma za kawo fargaba ga Masarawa; kowanne da Yahuda ya ambace zai firgita, saboda abin da Ubangiji Maɗaukaki yake shiri a kansu.
A wannan rana birane biyar a Masar za su yi yaren Kan’ana su kuma miƙa kai cikin yarjejjeniya ga Ubangiji Maɗaukaki. Za a ce da ɗayansu Birnin Hallaka.
A wannan rana za a kasance da bagade ga Ubangiji a tsakiyar Masar, da kuma ginshiƙin dutse Ubangiji a iyakarta. Zai zama alama da kuma shaida ga Ubangiji Maɗaukaki a ƙasar Masar. Sa’ad da suka yi kuka ga Ubangiji saboda masu zaluntarsu, zai aiko musu mai ceto da mai kāriya, zai kuma cece su. Saboda haka Ubangiji zai sanar da kansa ga Masarawa, kuma a wannan rana za su yarda da Ubangiji. Za su yi masa sujada da hadayu da hadayun hatsi; za su yi alkawura ga Ubangiji su kuma kiyaye su. Ubangiji zai bugi Masar da annoba; zai buge su ya kuma warkar da su. Za su juyo wurin Ubangiji, zai amsa roƙonsu ya kuma warkar da su.
A wannan rana za a kasance da babban hanya daga Masar zuwa Assuriya. Assuriyawa za su tafi Masar, Masarawa kuma za su tafi Assuriya. Masarawa da Assuriyawa za su yi sujada tare. A wannan rana Isra’ila za tă zama na uku, tare da Masar da Assuriya, abin albarka ga duniya. Ubangiji Maɗaukaki zai albarkace su, yana cewa, “Albarka ta tabbata ga Masar, mutanena, Assuriya aikin hannuna, da kuma Isra’ila gādona.”
Annabci a kan Masar da Kush
A shekarar da babban shugaban yaƙin da Sargon sarkin Assuriya ya aika, ya zo Ashdod ya kuma fāɗa mata ya kuma ci ta da yaƙi, a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,20.3 Wato, yankin Nilu na Bisa; haka ma a aya 5 haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar. Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya. A wannan rana mutanen da suke zama a bakin teku za su ce, ‘Dubi abin da ya faru da waɗanda muka dogara a kai, waɗanda muka gudu muka je don neman taimako da ceto daga sarkin Assuriya! Yaya za mu tsira?’ ”
Annabci a kan Babilon
Abin da Allah ya faɗa game da Hamada da take kusa da Teku.
Kamar guguwa mai share cikin ƙasar kudu,
mai hari ya zo daga hamada,
daga ƙasar mai banrazana.
An nuna mini mugun wahayi,
mai bashewa ya bashe, mai washewa ya washe.
Elam, ki yi yaƙi! Mediya, ki yi kwanto!
Zan kawo ƙarshen dukan nishe-nishen da ta jawo.
Game da wannan jikina yana ciwo,
zafi ya kama ni, kamar na mace mai naƙuda;
na razana game da abin da na ji,
na yi mamakin abin da na gani.
Gabana tana ta fāɗuwa,
tsoro ya sa ina rawan jiki;
hasken da nake marmari
ya zo da razana gare ni.
Sun shirya teburori,
sun shimfiɗa dardumai,
sun ci, sun sha!
Tashi, ku hafsoshi,
sa mai a garkuwoyi!
Ga abin da mai girma ya ce mini,
“Tafi, ka sa mai tsaro
ka kuma sa ya ba da rahoton abin da ya gani.
Sa’ad da ya ga kekunan yaƙi
tare da ƙungiyoyin dawakai,
mahaya a kan jakuna,
ko mahaya a kan raƙuma,
to, fa ya zauna a faɗake,
ya kintsa sosai.”
Mai tsaron kuma ya yi ihu,
“Kowace rana, ranka yă daɗe, nakan tsaya a hasumiyar tsaro;
kowane dare nakan tsaya a wurin aikina.
Duba, ga wani mutum tafe a keken yaƙin
tare da ƙungiyar dawakai.
Ya kuma mayar da amsa,
‘Babilon ta fāɗi, ta fāɗi!
Dukan siffofin allolinta
kwance a ragargaje a ƙasa!’ ”
Ya mutanena, an ragargaje ku a masussuka,
na faɗa muku abin da na ji
daga Ubangiji Maɗaukaki,
daga Allah na Isra’ila.
Annabci a kan Edom
Abin da Allah ya faɗa game da Duma,21.11 Duma yana nufin shiru Ko kuwa natsattse, wani sunan Edom.
Wani ya kira ni daga Seyir,
“Mai tsaro, me ya rage a daren?
Mai tsaro, me ya rage a daren?”
Mai tsaro ya amsa,
“Safiya ta gabato, haka kuma dare.
In za ka yi tambaya, to, yi tambaya;
sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”
Annabci a kan Arabiya
Abin da Allah ya faɗa game da Arabiya.
Ku ayarin Dedanawa,
ku da kuka sauka a jejin Arabiya,
ku kawo ruwa don ƙishirwa;
ku da kuke zama a Tema,
ku kawo abinci don masu gudun hijira.
Sun gudu daga takobi,
daga takobin da aka janye,
daga bakan da aka tanƙware
da kuma daga zafin yaƙi.
Ga abin da mai girma ya ce mini, “Cikin shekara ɗaya, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, dukan sojojin Kedar za su zo ga ƙarshe. Waɗanda suka yi rai na maharba, jarumawan Kedar, za su zama kaɗan.” Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa.
Annabci a kan Urushalima
Abin da Allah ya faɗa game da Kwarin Wahayi.
Mene ne ya dame ku a yanzu,
da dukanku kuka hau kan rufin gidaje.
Ya kai gari cike da hayaniya,
Ya ke birnin tashin hankali da alkarya mai murna?
Mutanenki ba su mutu ta wurin takobi ba,
ba kuwa za su mutu a yaƙi ba.
Dukan shugabanninki sun gudu gaba ɗaya;
an kama su ba tare da an yi amfani da baka ba.
Dukanku da aka kama an kwashe ku ɗaurarru gaba ɗaya,
kun gudu tun abokin gāba yana da nisa.
Saboda haka na ce, “Ƙyale ni kurum;
bari in yi kuka mai zafi.
Kada ka yi ƙoƙarin ta’azantar da ni
a kan hallakar mutanena.”
Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana da ranar
giggicewa da tattakewa da banrazana
a cikin Kwarin Wahayi,
ranar ragargazawar katanga
da ta yin kuka ga duwatsu.
Elam ya ɗauki kwari da baka,
tare da mahayan kekunan yaƙinta da dawakai;
Kir ta buɗe garkuwoyi.
Kwarurukanku mafi kyau sun cika da kekunan yaƙi,
an kuma tsai da mahayan dawakai a ƙofofin birni.
An rurrushe kāriyar Yahuda,
a ranan nan kuwa kun yi la’akari
da makamai a cikin Fadan Kurmi;
kuka ga cewa Birnin Dawuda
tana da wuraren kāriya masu yawa da suka tsattsage;
kuka tattara ruwa
a Tafkin Ƙasa.
Kuka ƙirga gine-gine a Urushalima
kuka kuma rurrushe gidaje don ku ƙarfafa katanga.
Kuka gina matarar ruwa tsakanin katanga biyu
saboda ruwan Tsohon Tafki,
amma ba ku yi la’akari da Wannan da ya yi su ba,
ko ku kula da Wannan da ya shirya shi tuntuni.
Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki
ya kira ku a wannan rana
don ku yi kuka ku yi ihu,
don ku aske gashinku ku kuma sa tsummoki.
Amma duba, sai ga shi kuna farin ciki kuna kuma murna,
kuna yankan shanu kuna kashe tumaki,
kuna cin nama kuna kuma shan ruwan inabi!
Kuna cewa, “Bari mu ci mu kuma sha,
gama gobe za mu mutu!”
Ubangiji Maɗaukaki ya bayyana wannan a kunnena cewa, “Har ranar mutuwarka ba za a yi kafarar wannan zunubi ba,” in ji mai girma Ubangiji Maɗaukaki.
Ga abin da Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa,
“Je, ka faɗa wa wannan mai hidima,
Shebna, sarkin fada.
Mene ne kake yi a nan kuma wa ya ba ka izini
ka haƙa kabari wa kanka a nan,
kana fafe kabarinka a bisa
kana sassaƙa wurin hutunka a dutse?
“Ka yi hankali, Ubangiji yana shirin ya kama ka da ƙarfi
ya kuma ɗauke ka, ya kai mai ƙarfi.
Zai dunƙule ka kamar ƙwallo
ya jefa ka a cikin ƙasa mai girma.
A can za ka mutu
a can kuma kekunan yaƙinka masu daraja za su kasance,
abin kunya kake ga gidan maigidanka!
Zan tumɓuke ka daga makaminka,
za a kuma kore ka daga matsayinka.
“A wannan rana zan kira bawana, Eliyakim ɗan Hilkiya. Zan rufe shi da rigarka in kuma yi masa ɗamara in miƙa masa ikonka. Zai zama mahaifi ga waɗanda suke zama a Urushalima da kuma gidan Yahuda. Zan sa mabuɗin gidan Dawuda a kafaɗarsa; abin da ya buɗe ba mai rufewa, kuma abin da ya rufe ba mai buɗewa. Zan kafa shi kamar turke a tsayayyen wuri; zai zama mazaunin22.23 Ko kuwa kursiyi daraja domin gidan mahaifinsa. Dukan ɗaukakar iyalinsa za tă rataya a kansa daga ’ya’yansa da zuriyarsa har zuwa dukan ƙananan kayan aikinsa, wato, daga kwanoni har zuwa tuluna.
“A ranan nan, in ji Ubangiji Maɗaukaki, turken da aka kafa a tsayayyen wuri zai sumɓule; za a sare shi ya fāɗi, za a kuma datse nauyin da yake rataya a kansa.” Ni Ubangiji na faɗa.
Annabci a kan Taya
Abin da Allah ya faɗa game da Taya.
Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish!
Gama an hallaka Taya
aka kuma bar su babu gida ko tasha.
Daga ƙasar Saifurus23.1 Da Ibraniyanci Kittim
magana ta zo musu.
Ku yi shiru, ku mutanen tsibiri
da ku ’yan kasuwan Sidon
waɗanda masu ciniki a teku suka azurta.
A manyan ruwaye
hatsin Shihor suka iso;
girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya
ta kuma zama kasuwar al’ummai.
Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku,
gama teku ya yi magana ya ce,
“Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi ’ya’ya;
ban taɓa goyon ’ya’ya maza ba balle in reno ’ya’ya mata.”
Sa’ad da magana ta kai Masar,
za su razana da jin labari daga Taya.
Ku haye zuwa Tarshish;
ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri.
Wannan ce birnin murnanku,
birnin nan na tun dā
wadda ƙafafunta suka kai ta
zama a ƙasashe masu nesa?
Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya
ita da take ba da rawanin sarauta,
wadda ’yan kasuwanta sarakuna ne,
wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya?
Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi,
don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta
ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya.
Ki nome ƙasarki har zuwa wajen Nilu,
Ya Diyar Tarshish,
gama ba ki da tashan jirgin ruwa kuma.
Ubangiji ya miƙa hannunsa a bisa teku
ya kuma sa mulkokinsa suka yi rawar jiki.
Ya ba da umarni game da Funisiya23.11 Da Ibraniyanci Kan’ana
cewa a hallaka kagararta.
Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba,
Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya!
“Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus;
a can ɗin ma ba za ki huta ba.”
Dubi ƙasar Babiloniyawa,23.13 Ko kuwa Kaldiyawa
wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani!
Assuriyawa sun mai da ita
wurin zaman halittun hamada;
sun gina hasumiyoyin kwanto,
suka ragargaza kagararta ƙaf
suka mai da ita kango.
Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish;
an rurrushe kagararku!
A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,
“Ɗauki garaya, ki ratsa birni,
Ya ke karuwar da aka manta da ita;
kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa,
saboda a tuna da ke.”
A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya. Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau.
Yin kaca-kaca da duniyar da Ubangiji zai yi
Duba, Ubangiji zai wofinta duniya
ya kuma yi kaca-kaca da ita;
zai ɓata fuskarta
ya watsar da mazaunanta,
zai zama abu ɗaya
ga firist kamar yadda yake ga mutane,
ga maigida kamar yadda yake ga bawa,
ga uwargijiya kamar yadda yake ga baiwa,
ga mai sayarwa kamar yadda yake ga mai saya,
ga mai karɓan rance kamar yadda yake ga mai ba da rance,
ga mai karɓan bashi kamar yadda yake ga mai ba da bashi.
Za a wofinta duniya ƙaƙaf
a kuma washe ta sarai.
Ubangiji ne ya faɗa haka.
Duniya ta bushe ta kuma yanƙwane,
duniya tana shan azaba ta kuma raunana,
masu daraja na duniya suna shan azaba.
Duniya ta ƙazantu ta wurin mutanenta
sun ƙi yin biyayya da dokoki,
sun keta farillai
suka kuma karya madawwamin alkawari.
Saboda haka la’ana za tă auko wa duniya;
dole mutanenta su ɗauki hakkin laifinsu.
Saboda haka aka ƙone mazaunan duniya,
kuma kaɗan ne kurum suka rage.
Sabon ruwan inabi ya bushe kuringar inabi kuma sun yanƙwane;
dukan masu farin ciki suna nishi.
Kaɗe-kaɗen garayu sun yi shiru,
surutun masu murna ya daina,
garayan farin ciki ya yi shiru.
Babu sauran shan ruwan inabi suna rera waƙa;
barasa ya zama da ɗaci ga masu shanta.
Birnin da aka birkice ta zama kango;
an kulle ƙofar shiga kowane gida.
A tituna suna kukan neman ruwan inabi;
dukan farin ciki ya dawo baƙin ciki,
an hana dukan kaɗe-kaɗe a duniya.
An bar birnin kango,
aka yi kaca-kaca da ƙofofinta.
Haka zai zama a duniya
da kuma a cikin al’ummai,
kamar sa’ad da akan karkaɗe itacen zaitun,
ko kuma kamar sa’ad da ake barin kala bayan an girbe inabi.
Sun daga muryoyinsu, sun yi sowa ta farin ciki;
daga yamma sun furta darajar Ubangiji.
Saboda haka a gabas sun ɗaukaka Ubangiji,
a ɗaukaka sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila,
a cikin tsibiran teku.
Daga iyakokin duniya mun ji waƙoƙi,
“Ɗaukaka ga Mai Adalcin nan.”
Amma na ce, “Na lalace, na lalace!
Kaitona!
Munafukai sun ci amana!
Da munafunci munafukai sun ci amana!”
Razana da rami da tarko suna jiranku,
Ya mutanen duniya.
Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga ƙarar razana
zai fāɗa cikin rami;
wanda kuma ya tsere daga rami
za a kama shi a tarko.
An buɗe ƙofofin ambaliyar ruwan sama,
harsashen ginin duniya suna rawa.
An tsage duniya,
duniya ta farfashe ta wage,
an girgiza duniya ƙwarai.
Duniya tana tangaɗi kamar mashayi,
tana lilo kamar rumfa a cikin iska;
laifin tayarwarta ya yi nauyi sosai
har ta fāɗi ba kuwa za tă ƙara tashi ba.
A wannan rana Ubangiji zai hukunta
ikokin da suke cikin sama
da kuma sarakunan da suke a duniya.
Za a tattara su tare
kamar ɗaurarru a kurkuku;
za a rufe su a kurkuku
a kuma hukunta su24.22 Ko kuwa a sāke su bayan kwanaki masu yawa.
Sa’an nan wata zai ruɗe, rana ta ji kunya;
gama Ubangiji Maɗaukaki zai yi mulki
a kan Dutsen Sihiyona da kuma a cikin Urushalima,
da kuma a gaban dattawanta, da ɗaukaka.
Yabo ga Ubangiji
Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,
gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,
abubuwan da aka shirya tun da.
Ka mai da birnin tsibin tarkace,
ka lalatar da gari mai katanga,
birnin baƙi mai ƙarfi, ta ɓace; ba za a ƙara gina ta ba.
Saboda haka mutane masu ƙarfi za su girmama ka;
biranen mugayen al’ummai za su ji tsoronka.
Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa,
wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana.
Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango
kuma kamar zafin hamada.
Ka kwantar da hayaniyar baƙi;
kamar yadda inuwar girgije kan rage zafin rana, haka ake kwantar da waƙar mugaye.
A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane,
liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau.
A wannan dutse zai kawar da
baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane,
ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;
zai haɗiye mutuwa har abada.
Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye
daga dukan fuskoki;
zai kawar da kunyar mutanensa
daga dukan duniya.
Ubangiji ne ya faɗa.
A wannan rana za su ce,
“Tabbatacce wannan shi ne Allah;
mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu.
Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi;
bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”
Hannun Ubangiji zai zauna a kan wannan dutse;
amma za a tattake Mowab a ƙarƙashinsa
kamar yadda ake tattaka kara a cikin taki.
Za su buɗe hannuwansa a cikinsa,
yadda mai iyo kan buɗe hannuwansa don yă yi iyo.
Allah ya ƙasƙantar da girmankansu
duk da wayon25.11 Ma’anar kalmar Ibraniyancin nan babu tabbas. hannuwansu.
Zai rurrushe manyan katangar kagaru
ya kuma ƙasƙantar da su;
zai rushe su har ƙasa,
su zama ƙura.
Waƙar yabo
A wannan rana za a rera wannan waƙa a ƙasar Yahuda.
Muna da birni mai ƙarfi;
Allah yake ceton
katanga da kuma kagarunta.
A buɗe ƙofofi
saboda al’umma mai adalci ta shiga,
al’ummar da mai aminci.
Za ka kiyaye shi da cikakken salama
shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,
domin ya dogara a gare ka.
Ku dogara ga Ubangiji,
gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.
Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa
ya kawar da birni mai alfarma ƙasa;
ya rusa ta har ƙasa
ya jefar da ita cikin ƙura.
Ƙafafu sukan tattake ta,
ƙafafu waɗanda aka zalunta,
wato, sawun matalauta.
Hanyar masu adalci sumul take;
Ya Mai Aikata Gaskiya, ka sa hanyar masu adalci ta yi sumul.
I, Ubangiji, cikin tafiya a hanyar dokokinka,26.8 Ko kuwa hukunce-hukunce
muna sa zuciya gare ka;
sunanka da tunani a kanka
su ne marmarin zukatanmu.
Raina yana marmarinka da dare;
da safe kuma raina yana son ganinka.
Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya,
mutanen duniya kan koyi adalci.
Ko da yake akan nuna wa mugaye alheri,
ba sa koyi adalci;
har ma a ƙasar masu aikata gaskiya sukan ci gaba da aikata mugunta
ba sa ganin girmar darajar Ubangiji.
Ya Ubangiji an ɗaga hannunka sama,
amma ba sa ganinsa.
Bari su ga himmarka don mutanenka su kuma sha kunya;
bari wutar da aka ajiye don abokan gābanka ta cinye su.
Ubangiji ka kafa salama dominmu;
duk abin da muka iya yi kai ne ka yi mana.
Ya Ubangiji, Allahnmu, waɗansu iyayengiji ban da kai sun yi mulki a kanmu,
amma sunanka kaɗai muka girmama.
Yanzu duk sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba;
waɗannan ruhohin da suka rasu ba za su tashi ba.
Ka hukunta su ka kuma kawo su ga hallaka;
ka sa ba za a ƙara tunawa da su ba.
Ka fadada al’umma, ya Ubangiji;
ka fadada al’umma.
Ka samo wa kanka ɗaukaka;
ka fadada dukan iyakokin ƙasar.
Ubangiji, sun zo gare ka a cikin damuwarsu;
sa’ad da ka hore su,
da ƙyar suna iya yin addu’a.26.16 Ma’anar wannan kalma a Ibraniyanci don wannan jumla babu tabbas.
Kamar mace mai ciki da take gab da haihuwa
takan yi ta murɗawa tana kuka saboda zafi,
haka muka kasance a gabanka, ya Ubangiji.
Muna da ciki, mun yi ta murɗewa saboda zafi,
amma mun haifi iska.
Ba mu kawo ceto ga duniya ba;
ba mu haifi mutanen duniya ba.
Amma matattunka za su rayu;
jikunansu za su tashi.
Ku da kuke zama a ƙura,
ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki.
Raɓarka kamar raɓar safiya ce;
duniya za tă haifi matattunta.
Ku tafi, mutanena, ku shiga ɗakunanku
ku kuma kulle ƙofofi;
ku ɓoye kanku na ɗan lokaci
sai ya huce fushinsa.
Duba, Ubangiji yana fitowa daga mazauninsa
don yă hukunta mutanen duniya saboda zunubansu.
Duniya za tă bayyana zub da jinin da aka yi a kanta;
ba za tă ƙara ɓoye waɗanda aka kashe a cikinta ba.
Ceton Isra’ila
A wannan rana,
Ubangiji zai yi hukunci da takobi,
takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna,
zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe,
dodon ruwa macijin nan mai murɗewa;
zai kashe dodon nan na teku.
A wannan rana,
“Ku rera game da gonar inabi mai ba da ’ya’ya ku ce
Ni, Ubangiji na lura da ita;
na yi ta yin mata banruwa.
Na yi tsaronta dare da rana
don kada wani yă yi mata ɓarna.
Ban yi fushi ba.
Da a ce ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suke kalubalanta na mana!
Zan fita in yi yaƙi da su;
da na sa musu wuta duka.
Ko kuma bari su zo wurina don mafaka;
bari su yi sulhu da ni,
I, bari su yi sulhu da ni.”
A kwanaki masu zuwa Yaƙub zai yi saiwa,
Isra’ila zai yi toho ya kuma yi fure
ya cika dukan duniya da ’ya’ya.
Ubangiji ya buge shi
kamar yadda ya bugi waɗanda suka buge shi?
An kashe shi
kamar yadda aka kashe waɗanda suka kashe shi?
Ta wurin yaƙi da zaman bauta ka hukunta shi,
da tsananin tsawa kuma ka kore shi,
kamar a ranar da iskar gabas ta hura.
A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub,
wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa.
Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade
suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu,
har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare
da za a bari a tsaye.
Birni mai katanga ya zama kufai,
yasasshen mazauni, an yashe shi kamar hamada;
a can ’yan maruƙa suke kiwo,
a can suke kwance;
sun kakkaɓe rassanta ƙaf.
Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su
mata kuma su zo su yi itacen wuta da su.
Gama mutane ne marar azanci;
saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba,
Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba.
A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites27.12 Da Ibraniyanci Kogi mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya. Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima.
Kaiton Efraim
Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim,
ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa,
da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,
ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!
Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi.
Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna,
kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa,
zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.
Za a tattaka wannan rawani,
girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.
Wannan fure mai yanƙwanewa, darajarar kyansa,
da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,
zai zama kamar ’ya’yan ɓaure, nunan fari,
da zarar wani ya gani ya kuma tsinka,
zai haɗiye shi.
A wannan rana Ubangiji Maɗaukaki
zai zama rawani mai daraja
kyakkyawan rawani
wa mutanensa da suka ragu.
Zai zama ruhun adalci
gare shi wanda yake zaune a kujerar shari’a,
wurin samun ƙarfi
ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofi.
Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi
suke jiri don sun sha barasa
Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa
sun kuma yi tatur da ruwan inabi;
suna jiri saboda sun sha barasa,
suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi,
suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.
Duk amai ya rufe teburori
kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.
“Wane ne yake so ya koyar?
Ga wa yake bayyana saƙonsa?
Ga yaran da aka yaye,
ga waɗanda ba a daɗe da yayewa ba ne?
Gama haka yake.
Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi,
mulki a kan mulki, mulki a kan mulki;28.10 Da Ibraniyanci / sab lasab sab lasab / kab lakab kab lakab (mai yiwuwa kalmomi marasa ma’ana ne; mai yiwuwa kwaikwayon maganar annabi ne); haka ma a aya 13.
nan kaɗan, can kaɗan.”
To da kyau, da leɓunan baƙi da ku harsunan da ba sani ba
Allah zai yi magana da wannan mutane,
waɗanda zai ce,
“Wannan shi ne wurin hutu, bari waɗanda suka gaji su huta”;
da kuma, “Wannan shi ne wurin wartsakewa”
amma sun ƙi su saurara.
Saboda haka fa, maganar Ubangiji gare su za tă zama,
Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi,
mulki akan mulki, mulki a kan mulki;
nan kaɗan, can kaɗan,
domin su tafi su kuma fāɗi da baya,
su ji rauni a kuma kama su da tarko, a kai su zaman bauta.
Saboda haka ku saurari maganar Ubangiji, ku masu ba’a
ku da kuke mulkin wannan mutane a Urushalima.
Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa,
mun kuma yi yarjejjeniya da kabari.
Sa’ad da zafi ya ratsa,
ba zai taɓa mu ba,
gama mun mai da ƙarya mafakarmu28.15 Ko kuwa allolin ƙarya
ruɗu kuma wurin ɓuyanmu.”
Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,
“Duba, na kafa dutse a Sihiyona,
dutsen da aka gwada,
dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe;
wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.
Zan mai da gaskiya igiyar gwaji
adalci kuma ɗan katakon gwajin ginin;
ƙanƙara za tă share mafakarku,
ƙarya, da ruwa kuma za su mamaye maɓuyanku.
Za a soke alkawarinku da mutuwa;
yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba.
Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa,
zai hallaka ku.
A duk sa’ad da ya zo;
ko da safiya, ko dare ko kuma da rana,
zai yi ta ratsawa yana kwasanku.”
Za ku zama kamar mutumin
da ya zama abin karin magana,
wanda ya yi ƙoƙari yă kwanta a gajeren gado,
yă kuma rufa da ɗan siririn bargo.
Ubangiji zai tashi kamar yadda ya yi a Dutsen Feratsim,
zai tā da kansa kamar a Kwarin Gibeyon
don yă aikata aikinsa, aikinsa da ba a saba gani ba,
yă kuma yi aikinsa, baƙon aikinsa.
Yanzu ku daina ba’arku,
in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi;
Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa mini
game da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar.
Ku saurara ku kuma ji muryata;
ku kasa kunne ku kuma ji abin da na faɗa.
Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne?
Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne?
Sa’ad da ya shirya wuri da kyau,
ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba?
Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsa28.25 Ba a tabbatar da ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba.
sha’ir a kunyoyinsa,28.25 Ba a tabbatar da ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba.
tamba kuma a filinsa ba?
Allahnsa ya umarce shi
ya kuma koya masa hanyar da take daidai.
Ba a bugan kanumfari da ƙaton sanda
ko a yi ta jujjuye ƙafar keke a kan ɗaɗɗoya;
akan buga kanumfari da siririn sanda
ɗaɗɗoya kuma da tsumagiya.
Dole a niƙa hatsi don a yi burodi;
saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba.
Ya san yadda zai sussuke alkamarsa,
ba tare da ya ɓata tsabarta ba.
Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne,
shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima.
Kaiton birnin Dawuda
Kaitonki, Ariyel,29.1 Ariyel. Wata ma’ana mai yiwuwa ta “ariyel” a Ibraniyanci za tă iya zama “Jarumi na Allah” ko kuwa “Zaki na Allah” ko kuma “Bagade na Allah.” Ariyel
birnin da Dawuda ya zauna!
Ƙara shekara ga shekara
a kuma bar shagulgulanki su yi ta kewayewa.
Duk da haka zan yi wa Ariyel kwanto
za tă kuma yi kuka da makoki,
za tă zama mini kamar bagaden jini.29.2 Ibraniyanci na bagaden jini ya yi kamar Ibraniyanci na Ariyel.
Zan kafa sansani kewaye da ke duka;
zan kewaye ki da hasumiyoyi
in tasar miki da ayyukan kwantona na yaƙi.
Za a ƙasƙantar da ke, za ki ƙi yin magana daga ƙasa;
maganarki za tă yi ƙasa-ƙasa daga ƙura.
Muryarki za tă zama kamar fatalwa daga ƙasa;
daga ƙura maganarki zai fito ƙasa-ƙasa.
Amma abokan gābanki masu yawa za su zama kamar ƙura mai laushi,
sojojinsu masu firgitarwa za su yi ta tashi kamar yayin da iska ta hura.
Farat ɗaya, cikin ɗan lokaci,
Ubangiji Maɗaukaki zai zo
da tsawa da rawar ƙasa da ƙara mai girma,
da hadarin iska da guguwa da harshe na wuta mai ci.
Sa’an nan sojojin dukan al’umman da suka yi yaƙi da Ariyel,
da suka fāɗa mata da kagararta suka kuma yi mata kwanto,
za su zama kamar yadda yake da mafarki,
wahayi da dare,
kamar sa’ad da mai yunwa yana mafarki cewa yana cin abinci,
amma sai ya farka, yunwan tana nan;
kamar sa’ad da mai ƙishirwa yana mafarki cewa yana shan ruwa,
amma sai ya farka yana suma, da ƙishinsa.
Haka zai zama da sojoji na dukan al’ummai
da suka yi yaƙi da Dutsen Sihiyona.
Ku firgita ku kuma yi mamaki,
ku makance kanku ku kuma zama a makance;
ku bugu, amma ba da ruwan inabi ba,
ku yi tangaɗi, amma ba daga barasa ba.
Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi,
Ya rufe idanunku (annabawa);
ya rufe kawunanku (masu duba).
Gare ku duk wannan wahayi ba kome ba ne sai dai maganganun da aka rufe a cikin littafi. In kuma kun ba da littafin ga wani wanda zai iya karanta, kuka kuma ce masa, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ba zan iya ba; an rufe shi.” Ko kuwa in kun ba da littafin ga wani wanda ba zai iya karantawa ba, kuka kuma ce, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ban iya karatu ba.”
Ubangiji ya ce,
“Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu
suka kuma girmama ni da leɓunansu,
amma zukatansu suna nesa daga gare ni.
Sujadar da suke mini
cike take da dokokin da mutane suka koyar.29.13 Da Ibraniyanci; Seftuwajin Suna mini sujada a banza; koyarwarsu ba kome ba ne illa dokokin da mutane suka koyar
Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya
da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki;
hikimar masu hikima za tă lalace,
azancin masu azanci zai ɓace.”
Kaiton waɗanda suke zuwa manyan zurfafa
don su ɓoye shirye-shiryensu daga Ubangiji,
waɗanda suke aikinsu cikin duhu su yi tunani,
“Wa yake ganinmu? Wa zai sani?”
Kuna birkitar abubuwa,
sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu!
Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi,
“Ba shi ne ya yi ni ba”?
Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane,
“Ba ka san kome ba”?
Cikin ɗan lokaci, za a mai da Lebanon gona mai taƙi
kuma gona mai taƙi za tă zama kamar kurmi?
A wannan rana kurame za su ji maganganun littafi,
daga duruduru da duhu kuma
idanun makafi za su gani.
Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji;
mabukata za su yi farin ciki cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
Masu zalunci za su ƙare,
masu ba’a za su ɓace,
kuma dukan waɗanda suke da ido don mugunta za su hallaka,
waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi,
waɗanda suke kafa tarko wa mai ba da kāriya a ɗakin shari’a
da shaidar ƙarya kuma su hana marar laifi samun shari’ar adalci.
Saboda haka ga abin da Ubangiji wanda ya fanshi Ibrahim, ya ce wa gidan Yaƙub,
“Ba za a ƙara kunyata Yaƙub ba;
fuskokinsu kuma ba za su ƙara yanƙwanewa ba.
Sa’ad da suka ga ’ya’yansu a tsakiyarsu,
aikin hannuwansu,
za su kiyaye sunana da tsarki;
za su san tsarkin Mai Tsarkin nan na Yaƙub,
za su kuma ji tsoron Allah na Isra’ila.
Su da suke marasa azanci a ruhu za su sami fahimtar;
waɗanda suke gunaguni za su yarda da koyarwa.”
Kaiton al’umma mai tayarwa
“Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,”
in ji Ubangiji,
“ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba,
suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba,
suna jibga zunubi a kan zunubi;
waɗanda suka gangara zuwa Masar
ba tare da sun nemi shawarata;
waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna,
don neman inuwar mafakar Masar.
Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya,
inuwar Masar za tă jawo muku kunya.
Ko da yake suna da shugabanni a Zowan
kuma jakadunsu sun iso Hanes,
kowa zai sha kunya
saboda mutanen da ba su da amfani gare su,
waɗanda ba sa taimako ko amfani,
sai dai jawo kunya da da-na-sani.”
Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa,
Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari
inda zakoki da zakanya,
inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke,
jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna,
dukiyarsu a kan raƙuma,
zuwa ƙasan nan marar riba,
zuwa Masar, wadda taimakonta marar amfani ne.
Saboda haka na yi mata laƙabi
Rahab Marar Yin Kome.
Tafi yanzu, ka rubuta musu a kan allo,
ka rubuta shi a kan littafi,
cewa kwanaki suna zuwa
zai zama madawwamin shaida.
Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu,
’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.
Sukan ce wa masu gani,
“Kada ku ƙara ganin wahayi!”
Ga annabawa kuwa sukan ce,
“Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai!
Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai,
ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu.
Ku bar wannan hanya,
ku tashi daga wannan hanya,
ku kuma daina kalubalantarmu
da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!”
Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa,
“Saboda haka kun ƙi wannan saƙo,
kuka dogara ga aikin kama-karya
kuka kuma dogara ga yin ruɗu,
wannan zunubi zai zama muku
kamar bango mai tsayi, tsagagge da yake kuma fāɗuwa,
da zai rushe nan da nan, ba tsammani.
Zai rushe kucu-kucu kamar tukunyar yumɓu,
ya ragargaje ƙaf
har cikin gutsattsarinsa ba za a sami ko ɗan katanga
don ɗiba garwashin wuta
ko a ɗiba ruwa daga tanki ba.”
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa,
“Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake,
cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku,
amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.
Kun ce, ‘A’a, za mu gudu a kan dawakai.’
Saboda haka za ku gudu!
Kun ce, ‘Za mu hau dawakai masu sauri mu gudu.’
Saboda haka masu fafararku za su fi ku gudu!
Dubu za su gudu
don barazanar mutum guda;
da jin barazanar mutane biyar
dukanku za ku yi ta gudu
sai an bar ku
kamar sandar tuta a kan dutse,
kamar tuta a kan tudu.”
Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;
ya tashi don yă nuna muku jinƙai.
Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.
Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!
Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku. Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su. Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.” Sa’an nan za ku ƙazantar da gumakanku da kuka dalaye da zinariya; za ku zubar da su kamar rigar al’adar mace ku kuma ce musu, “Ku ɓace mana da gani!”
Zai kuma aiko muku da ruwan sama don shuki a ƙasa, kuma abincin da zai fito daga gona zai zama mai albarka da kuma mai yawa. A wannan rana shanu za su yi kiwo a wadatacciyar makiyaya. Shanunku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau, wanda an sheƙe shi da babban cokali mai yatsu da kuma babban cokali. A ranar babban kisa, sa’ad da hasumiyoyi za su fāɗi, rafuffukan ruwa za su malalo a kan kowane dutse da kowane tudu mai tsawo. Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu.
Duba, Sunan Ubangiji yana zuwa daga nesa,
tare da fushi mai ƙuna da kuma baƙin hayaƙi;
leɓunansa sun cika da fushi,
harshensa kuma wuta ce mai cinyewa.
Numfashinsa kamar raƙuman ruwa masu gudu
yana tashi har zuwa wuya.
Yakan tankaɗe al’ummai cikin lariyar hallaka;
yakan sa a muƙamuƙan mutane
linzamin da zai jagorance su su kauce.
Za ku kuma rera
kamar a daren da kuke shagalin biki mai tsarki;
zukatanku za su yi farin ciki
kamar sa’ad da mutane sukan haura da busa
zuwa dutsen Ubangiji,
zuwa Dutse na Isra’ila.
Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja
ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa
tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa,
gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara.
Muryar Ubangiji za tă firgita Assuriya
da sandar mulkinsa zai kashe su.
Kowane bugun da Ubangiji zai yi musu
da bulalarsa na hukunci
zai zama kiɗi ga ganguna da garaya,
yayinda yake yaƙi da su da naushin hannunsa.
An riga an shirya wurin ƙonawa;
an shirya shi saboda sarki.
An haƙa ramin wutarsa da zurfi da kuma fāɗi,
da isashen wuta da itacen wuta;
numfashin Ubangiji,
yana kamar kibiritu mai ƙuna,
da aka sa masa wuta.
Kaiton waɗanda suke dogara ga Masar
Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako,
waɗanda suke dogara ga dawakai,
waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu
da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu,
amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila,
ko ya nemi taimako daga Ubangiji.
Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa;
ba ya janye kalmominsa.
Zai yi gāba da gidan mugu,
gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.
Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba;
dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba.
Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa,
shi da yake taimako zai yi tuntuɓe
shi da aka taimaka zai fāɗi;
dukansu biyu za su hallaka tare.
Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini,
“Kamar yadda zaki kan yi ruri
babban zaki a kan abin da ya yi farauta,
kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya
sun taru wuri ɗaya a kansa,
ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba
ko ya damu da kiraye-kirayensu,
ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko
don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.
Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama
haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima;
zai kāre ta ya kuma fanshe ta,
zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”
Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa. Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi.
“Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba;
takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye.
Za su gudu daga takobi
za a kuma sa samarinsu aikin dole.
Kagararsu za tă fāɗi saboda razana;
da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,”
in ji Ubangiji,
wanda wutarsa tana a Sihiyona,
wanda matoyarsa tana a Urushalima.
Mulkin adalci
Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci
masu mulki kuma su yi mulki da adalci.
Kowane mutum zai zama kamar wurin fakewa daga iska
mafaka kuma daga hadari,
kamar rafuffukan ruwa a hamada
da kuma inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.
Sa’an nan idanun waɗanda suka gani ba za su ƙara rufewa ba,
kunnuwan waɗanda suka ji kuma za su saurara.
Zuciya marasa haƙuri za su sani su kuma fahimta,
harshen masu ana’ana kuma zai sāke su yi magana sosai.
Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba
ko kuwa a ɗaukaka mazambaci.
Gama wawa maganar wauta yakan yi,
zuciyarsa ta cika da mugunta,
yana aikata abubuwan rashin sanin Allah
yana baza kurakurai game da Ubangiji;
yana barin mayunwata da yunwa
ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha.
Matakan mazambaci mugaye ne,
yana ƙulla mugayen shirye-shirye
don yă hallaka talakawa da ƙarairayi,
ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.
Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki,
kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki.
Matan Urushalima
Ku matan da kuke zaman jin daɗi,
ku tashi ku saurare ni;
ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya,
ku ji abin da zan faɗa!
Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda
ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki;
girbin ’ya’yan inabi zai kāsa,
girbin ’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.
Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi,
ku sha wahala, ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya!
Ku tuɓe rigunanku,
ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.
Ku bugi ƙirjinku don gonaki masu kyau
don ’ya’yan inabi
da kuma don ƙasar mutanena,
da ƙasar da ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suka yi girma,
I, ku yi kuka saboda dukan gidajen da dā ake biki
da kuma domin wannan birnin da dā ake murna a ciki.
Za a ƙyale kagarar,
a gudu a bar birnin da dā ake hayaniya;
mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada,
jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna,
sai an zubo Ruhu a kanmu daga sama,
hamada kuma ta zama ƙasar mai taƙi,
gona mai taƙi kuma ta zama kamar kurmi.
Aikin gaskiya zai zauna a hamada
adalci kuma zai zauna a ƙasa mai taƙi.
Aikin adalci zai zama salama;
tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.
Mutanena za su zauna lafiya a wuraren salama,
a gidaje masu kāriya,
a wuraren hutun da babu fitina.
Ko da yake ƙanƙara za tă fāɗo a jeji,
a kuma rurrushe birni gaba ɗaya,
zai zama muku da albarka,
ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi,
kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku.
Damuwa da taimako
Kaitonka, ya kai mai hallakarwa,
kai da ba a hallakar da kai ba!
Kaitonka, ya maciya amana,
kai da ba a ci amanarka ba!
Sa’ad da ka daina hallakarwa,
za a hallaka ka;
sa’ad da ka daina cin amana,
za a ci amanarka.
Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai;
muna marmarinka.
Ka zama ƙarfinmu kowace safiya,
cetonmu a lokacin damuwa.
Da tsawar muryarka, mutane za su gudu;
sa’ad da ka tashi, al’ummai za su watse.
Ganimarku, ya al’ummai ƙanana fāri sun girbe;
kamar tarin fārin da mutane sun fāɗa wa.
Ubangiji da girma yake, gama yana zaune a bisa;
zai cika Sihiyona cikin gaskiya da adalci.
Zai zama tabbataccen harsashi na koyaushe,
ma’ajin ceto da hikima da sani a yalwace;
tsoron Ubangiji shi ne mabuɗin wannan dukiya.33.6 Ko kuwa dukiya ce daga wurinsa
Duba, jarumawansu suna kuka da ƙarfi a tituna;
jakadun salama suna kuka mai zafi.
An gudu an bar manyan hanyoyi,
babu matafiye a kan hanyoyi.
Aka keta yarjejjeniya,
an rena shaidunsa
ba a kuwa ganin girman kowa.
Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta,
Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane;
Sharon ta zama kamar Araba,
Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu.
“Yanzu zan tashi,” in ji Ubangiji.
“Yanzu ne za a ɗaukaka ni;
yanzu za a ɗaga ni sama.
Kun yi cikin yayi,
kuka haifi kara;
numfashinku wuta ne da zai cinye ku.
Za a ƙone mutane kamar da ƙuna farar ƙasa;
kamar ƙayayyuwan da aka sare aka kuma sa musu wuta.”
Ku da kuke da nesa, ku ji abin da na yi;
ku da kuke kusa, ku san ikona!
Masu zunubi a Sihiyona sun firgita;
rawar jiki ya kama marasa sanin Allah suna cewa,
“Wane ne a cikinmu zai iya zama da wuta mai ci?
Wane ne a cikinmu zai iya zama da madawwamiyar ƙonewa?”
Shi da yake tafiya cikin adalci
yana kuma magana abin da yake daidai,
wanda yake ƙin riba daga cuta
yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci,
wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa
ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,
shi ne mutumin da zai zauna a bisa,
wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse.
Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba.
Idanunku za su ga sarki a cikin kyansa
ku kuma hangi ƙasar da take shimfiɗe can da nisa.
Cikin tunaninku za ku yi tunani firgitar da ta faru tun dā kuna cewa,
“Ina hafsan nan?
Ina wannan wanda yake karɓar haraji?
Ina hafsan da yake lura da hasumiyoyi?”
Ba za ku ƙara ganin waɗannan mutane masu girman kai kuma ba,
waɗannan mutane masu magana da harshen da ba ku fahimta ba.
Ku duba Sihiyona, birnin shagulgulanmu;
idanunku za su ga Urushalima,
mazauni mai lafiya, tentin da ba za a taɓa gusar ba;
wanda ba a taɓa tumɓuke turakunsa ba,
ko a tsinke igiyoyinta.
A can Ubangiji zai zama Mai Iko Duka namu.
Zai zama kamar inda manyan koguna da rafuffuka suke.
Matuƙan jirgin ruwa ba za su kai wurinsu ba,
manyan jiragen ruwa ba za su yi zirga-zirga a kansu ba.
Gama Ubangiji ne alƙalinmu,
Ubangiji ne mai ba mu dokoki,
Ubangiji ne sarkinmu;
shi ne wanda zai cece mu.
Maɗaurinku sun kunce
ƙarfafan itacen jirgin ba su da kāriya,
fikafikan jirgin ba su buɗu ba.
Ta haka za a raba yalwar ganima
har ma guragu za su kwashe ganimar.
Ba wani mazauna a Sihiyona da zai ce, “Ina ciwo”;
za a kuma gafarta zunuban waɗanda suke zama a can.
Hukunci a kan al’ummai
Ku zo kusa, ku al’ummai, ku kuwa saurara
ku kasa kunne, ku mutane!
Bari duniya ta ji, da kuma dukan abin da yake cikinta,
duniya, da dukan abin da yake fitowa daga gare ta!
Ubangiji yana fushi da dukan al’ummai;
hasalarsa tana a kan mayaƙansu.
Zai hallaka su tas,
zai ba da su a karkashe.
Za a jefar da waɗanda aka kashe
gawawwakinsu za su yi wari;
duwatsu za su jiƙu da jininsu.
Za a tumɓuke dukan taurarin sammai
za a kuma nannaɗe sararin sama kamar littafi;
dukan rundunar sama za su fāffāɗi
kamar ganyayen da suka yanƙwane daga kuringa,
kamar ’ya’yan ɓauren da suka bushe daga itacen ɓaure.
Takobina ya sha zararsa a cikin sammai;
duba, ya sauko cikin hukunci a kan Edom,
mutanen da zan hallaka tas.
Takobin Ubangiji ya jiƙu da jini,
ya rufu da kitse,
jinin raguna da na awaki,
kitse daga ƙodar raguna.
Gama Ubangiji ya yi hadayar Bozra
da kuma babban kisa a Edom.
Babban bijimin jeji zai fāɗi tare da su,
maruƙan bijimi da manyan bijimai.
Ƙasarsu za tă cika da jini,
ƙura kuma zai cika da kitse.
Gama Ubangiji yana da ranar ɗaukar fansa,
shekarar ramuwa, don biya wa Sihiyona bukata.
Za a mai da rafuffukan Edom rami,
ƙurarta za tă zama kibiritun farar wuta;
ƙasarta za tă zama rami mai ƙuna!
Ba za a kashe ta ba dare da rana;
hayaƙinta za tă yi ta tashi har abada.
Daga tsara zuwa tsara za tă zama kango;
babu wani da zai ƙara wucewa ta wurin.
Mujiyar hamada da mujiya mai kuka za su mallake ta;
babban mujiya da hankaka za su yi sheƙa a can.
Allah zai miƙe a kan Edom
magwajin bala’i
da ma’aunin kango.
Sarakunanta ba za su kasance da wani abin da ake kira masarauta ba,
dukan sarakunanta za su ɓace.
Ƙayayuwa za su mamaye fadodinta
ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za su cika kagaranta.
Za tă zama mazaunin diloli
da gida don mujiyoyi.
Halittun hamada za su sadu da kuraye,
awakin jeji za su yi ta kiran juna;
a can halittun dare su ma za su huta
su kuma nemi wurin hutu wa kansu.
Mujiya za tă yi sheƙa a can ta zuba ƙwai;
za tă ƙyanƙyashe su, ta kuma kula da ’ya’yanta a inuwar fikafikanta;
a can kuma shirwa za su taru,
kowa da abokinsa.
Duba a cikin littafin Ubangiji ka kuma karanta.
Babu wani a cikin waɗannan da ya ɓace,
babu ko ɗaya da ba ta da abokiya.
Gama bakinsa ne ya ba da umarni,
Ruhunsa kuma zai tara su wuri ɗaya.
Ya ba su rabonsu;
hannunsa ya rarraba musu ta wurin awo.
Za su mallake ta har abada
su kuma zauna a can daga tsara zuwa tsara.
Farin cikin waɗanda aka ceta
Hamada da ƙeƙasasshiyar ƙasa za su yi murna;
jeji zai yi farin ciki ya kuma hudo.
Kamar fure, zai buɗu ya hudo;
zai yi farin ciki mai girma ya kuma yi sowa don farin ciki.
Za a maido wa Lebanon da darajarta,
darajar Karmel da Sharon;
za su ga ɗaukakar Ubangiji,
darajar Allahnmu.
Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi,
ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji;
ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata,
“Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro;
Allahnku zai zo,
zai zo domin ya ɗau fansa;
da ramuwar Allah
zai zo don yă cece ku.”
Sa’an nan idanun makafi za su buɗe
kunnuwan kurame kuma su ji.
Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa,
bebaye kuma su yi sowa don farin ciki.
Ruwa zai kwararo daga jeji
rafuffuka kuma a cikin hamada.
Yashi mai ƙuna zai zama tafki,
ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka.
A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama,
ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma.
Kuma babbar hanya za tă kasance a can;
za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki.
Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba;
za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce;
mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba.
Zaki ba zai kasance a can ba,
balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta;
ba za a same su a can ba.
Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can,
kuma fansassu na Ubangiji za su komo.
Za su shiga Sihiyona da rerawa;
matuƙar farin ciki zai mamaye su.
Murna da farin ciki za su sha kansu,
baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.
Sennakerib ya yi wa Urushalima barazana
([2 Sarakuna 18.13-27]; [2 Tarihi 32.1-19])
A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin Sarki Hezekiya, Sennakerib sarkin Assuriya ya kai wa dukan birane masu kagaran Yahuda yaƙi ya kuma kame su. Sai sarkin Assuriya ya aiki sarkin yaƙinsa tare da mayaƙa masu yawa daga Lakish zuwa wurin Sarki Hezekiya a Urushalima. Sa’ad da sarkin yaƙi ya tsaya a wuriyar Tafkin Tudu, a hanya zuwa Filin Mai Wanki, Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka fita zuwa wurinsa.
Sai sarkin yaƙin ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya.
“ ‘Ga abin da babban sarki, sarkin Assuriya, ya faɗa. A kan me kake dangana wannan ƙarfin halinka? Ka ce kana da dabara da kuma ƙarfin mayaƙa, amma kana magana banza ce kawai. Ga wa ka dogara, da kake tayar mini? Yanzu duba, kana dogara ga Masar, wannan ɗan tsinken kyauron dogarawa, wanda zai soki hannun mutum yă kuma ji masa rauni in ya dangana a kansa! Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara da shi. Kuma in ka ce mini, “Mun dogara ga Ubangiji Allahnmu ne” ba shi ba ne Hezekiya ya rurrushe masujadan kan tudunsa da bagadansa, yana ce wa Yahuda da Urushalima, “Dole ku yi sujada wa gaban wannan bagade”?
“ ‘Yanzu fa, bari in yi ciniki da maigidana, sarki Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sa mahaya a kansu! Yaya za ka ƙi hafsan mafi ƙanƙanci na hafsoshin maigidana, ko da yake kana dogara ga Masar don kekunan yaƙi da mahayan dawakai? Ban da haka kuma, na zo ne in faɗa in kuma hallaka wannan ƙasa ba tare da Ubangiji ba? Ubangiji kansa ya faɗa mini in tasar wa wannan ƙasa in kuma hallaka ta.’ ”
Sai Eliyakim, Shebna da Yowa suka ce wa sarkin yaƙin, “Ka yi haƙuri ka yi wa bayinka magana da Arameyanci, da yake muna jinsa. Kada ka yi mana magana da Yahudanci a kunnen mutanen da suke kan katanga.”
Amma sarkin yaƙin ya amsa ya ce, “Kuna tsammani ga maigidanku da ku ne kawai maigidana ya aiko ni in yi waɗannan maganganu, ba ga mutanen da suke zama a kan katanga ba, waɗanda kamar ku, za su ci kashinsu su kuma sha fitsarinsu?”
Sa’an nan sarkin yaƙin ya tsaya ya kuma yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji kalmomin babban sarki, sarkin Assuriya! Ga abin da sarki ya ce kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku. Ba zai cece ku ba! Kada ku bar Hezekiya ya rarashe ku ku dogara ga Ubangiji sa’ad da ya ce, ‘Tabbatacce Ubangiji zai cece mu; ba za a ba da wannan birni a hannun sarkin Assuriya ba.’
“Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya faɗa. Ku nemi salama da ni ku kuma fito zuwa wurina. Ta haka kowa zai ci daga kuringarsa da kuma itacen ɓaurensa ya kuma sha ruwa daga tankinsa, sai na zo na kuma kwashe ku zuwa ƙasa kamar taku, ƙasar hatsi da kuma sabon ruwan inabi, ƙasar abinci da gonakin inabi.
“Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’ Allahn wata al’umma ya taɓa ceci ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya? Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim? Sun fanshi Samariya daga hannuna? Wanne cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa daga gare ni? Yaya kuwa Ubangiji zai iya ceci Urushalima daga hannuna?”
Amma mutanen suka yi shiru ba su kuwa ce kome ba, gama sarki ya yi umarni cewa, “Kada ku amsa masa.”
Sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da kuma Yowa ɗan Asaf marubuci suka tafi wurin Hezekiya, da rigunansu a kyakkece, suka kuwa faɗa masa abin da sarkin yaƙin ya yi ta farfaɗa.
An yi faɗin ceton Urushalima
([2 Sarakuna 19.1-13])
Sa’ad da Sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakkece rigunansa ya kuma sanya tsummoki ya tafi ya shiga haikalin Ubangiji. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz. Suka faɗa masa cewa, “Ga abin da Hezekiya ya ce wannan rana ce ta baƙin ciki da tsawatawa da shan kunya, sai ka ce sa’ad da ’ya’ya kan zo matakin haihuwa sa’an nan a rasa ƙarfin haihuwarsu. Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.”
Sa’ad da shugabannin Sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya, sai Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku cewa, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa. Kada ka ji tsoron abin da ka ji, maganganun nan da bayin sarkin Assuriya suka yi mini saɓo. Ka saurara! Zan sa ruhuna a cikinsa saboda sa’ad da ya ji wani labari, zai koma zuwa ƙasarsa, a can kuwa zan sa a kashe shi da takobi.’ ”
Sa’ad da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye ya kuma sami sarki yana yaƙi da Libna.
To, fa, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana fitowa don yă yi yaƙi da shi. Sa’ad da ya ji haka, sai ya aiki jakadu zuwa wurin Hezekiya da wannan magana. “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda cewa kada ka bar allahn da ka dogara a kai ya ruɗe ka sa’ad da ya ce, ‘Ba za a ba da Urushalima ga sarkin Assuriya ba.’ Tabbatacce ka ji abin da sarakunan Assuriya suka aikata ga dukan ƙasashe, suna hallaka su tas. Kai kuwa za ka tsira ne? Allolin al’umman da kakannina suka hallaka sun cece su ne, allolin Gozan, Haran, Rezef da kuma na mutanen Eden waɗanda suke zama a Tel Assar? Ina sarkin Hamat yake, sarkin Arfad fa, sarkin Sefarfayim, ko na Hena ko na Iffa?”
Addu’ar Hezekiya
([2 Sarakuna 19.14-19])
Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga jakadun ya karanta ta. Sa’an nan ya haura zuwa haikalin Ubangiji ya shimfiɗa ta a gaban Ubangiji. Sai Hezekiya ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya. Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai.
“Gaskiya ce, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriyawa sun mai da dukan waɗannan mutane da ƙasashensu kango. Sun jefar da gumakansu cikin wuta suka kuma hallaka su, gama su ba alloli ba ne itace ne kawai da dutse, da hannuwan mutane suka sarrafa. Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, saboda masarautai a duniya su san cewa kai kaɗai ne, ya Ubangiji, Allah.”
Fāɗuwar Sennakerib
([2 Sarakuna 19.20-34])
Sa’an nan Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wa Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa. Saboda ka yi addu’a gare ni game da Sennakerib sarkin Assuriya, ga abin da maganar Ubangiji ya faɗa a kansa,
“Budurwa Diyar Sihiyona
ta rena tana kuma maka ba’a.
Diyar Urushalima
tana kada kai yayinda kake gudu.
Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo?
A kan wa ka tā da muryarka
ka kuma daga idanu cikin fariya?
A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!
Ta wurin jakadunka
ka jibge zage-zage a kan Ubangiji.
Ka kuma ce,
‘Da kekunan yaƙina masu yawa
na hau ƙwanƙolin duwatsu,
ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon.
Na sassare al’ul mafi tsayi
fir mafi kyau.
Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.
Na haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa
na kuma sha ruwa a can.
Da tafin ƙafafuna
na busar da dukan rafuffukan Masar.’
“Ba ka ji ba cewa
tun dā can na shirya ya zama haka?
A kwanakin dā na kafa shi;
yanzu na sa ya faru,
cewa ka mai da birane masu mafaka
zuwa tsibin ɓuraguzai.
Mutanensu, suka rasa ƙarfi,
sun firgita suka kuma sha kunya.
Suka zama kamar tsire-tsire a gona,
kamar tsire-tsiren ta suka tohu,
kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi,
wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma.
“Amma na san inda kake zama
da sa’ad da kakan fita ka kuma koma
da yadda ka harzuƙa gāba da ni.
Saboda ka harzuƙa gāba da ni
kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana,
zan sa ƙugiya a hancinka
linzamina a bakinka,
zan kuma sa ka koma
ta hanyar da ka zo.
“Wannan zai zama alama gare ka, ya Hezekiya,
“Wannan shekara za ka ci abin da ya yi girma da kansa,
shekara ta biyu kuma abin da ya tsiro daga wancan.
Amma a shekara ta uku za ka yi shuki ka kuma girba,
za ka dasa gonakin inabi ka kuma ci ’ya’yansu.
Sauran da suka rage na gidan Yahuda kuwa
za su yi saiwa a ƙarƙashi su kuma ba da ’ya’ya a bisa.
Gama daga Urushalima raguwa za tă fito,
kuma daga Dutsen Sihiyona ƙungiyar waɗanda suka tsira.
Himmar Ubangiji Maɗaukaki
zai cika wannan.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarkin Assuriya,
“Ba zai shiga wannan birni ba
ya harbe kibiya a nan.
Ba zai zo gabansa da garkuwa ba
ko ya gina mahaurai kewaye a kansa ba.
Ta hanyar da ya zo da ita zai koma;
ba zai shiga wannan birni ba,”
in ji Ubangiji.
“Zan kāre wannan birni in kuma cece shi,
saboda girmana da kuma saboda sunan Dawuda bawana!”
([2 Sarakuna 19.35-37])
Sai mala’ikan Ubangiji ya fita ya kuma karkashe mutane dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar a sansanin Assuriya. Sa’ad da mutane suka farka kashegari, sai ga gawawwaki duk a kwance! Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya janye. Ya koma zuwa Ninebe ya zauna a can.
Wata rana, yayinda yake yin sujada a haikalin allahnsa Nisrok, ’ya’yansa maza Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka kuma gudu zuwa ƙasar Ararat. Esar-Haddon ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
Ciwon Hezekiya
([2 Sarakuna 20.1-11]; [2 Tarihi 32.24-26])
A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da ciwo ya kuma kusa ya mutu. Annabi Ishaya ɗan Amoz ya tafi wurinsa ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce ka shirya gidanka, domin za ka mutu; ba za ka warke ba.”
Hezekiya ya juye fuskarsa wajen bango ya kuma yi addu’a ga Ubangiji, “Ka tuna, ya Ubangiji, yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukan zuciya na kuma yi abin da yake nagari a idanunka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Ishaya cewa, “Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka. Zan kuwa cece ka da wannan birni daga hannun sarkin Assuriya. Zan kiyaye wannan birni.
“ ‘Ga alamar Ubangiji gare ka cewa Ubangiji zai aikata kamar yadda ya yi alkawari. Zan sa inuwar da rana ta yi a kan matakalar Ahaz ta koma baya da taki goma.’ ” Saboda haka inuwar ta koma da baya daga fuskar rana har taki goma.
Rubutun Hezekiya sarkin Yahuda bayan ciwonsa da kuma warkarwarsa.
Na ce, “Cikin tsakiyar rayuwata
dole in bi ta ƙofofin mutuwa
a kuma raba ni da sauran shekaruna?”
Na ce, “Ba zan ƙara ganin Ubangiji ba,
Ubangiji a ƙasa ta masu rai;
ba zan ƙara ga wani mutum,
ko in kasance tare da waɗanda suke zama a wannan duniya ba.
Kamar tentin makiyayi
an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni.
Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata,
ya kuma yanke ni daga sandar saƙa;
dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
Na yi jira da haƙuri har safiya,
amma kamar zaki ya kakkarya ƙasusuwana duka;
dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe,
na yi kuka kamar kurciya mai makoki.
Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai.
Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!”
Amma me zan ce?
Ya riga ya yi mini magana, shi kansa ne kuma ya aikata.
Zan yi tafiya da tawali’u dukan kwanakina
saboda wahalar raina.
Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa;
ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma.
Ka maido mini da lafiya
ka kuma sa na rayu.
Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne
cewa in sha irin wahalan nan.
Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni
daga ramin hallaka;
ka sa dukan zunubaina
a bayanka.
Gama kabari ba zai yabe ka ba,
matattu ba za su rera yabonka ba;
waɗanda suka gangara zuwa rami
ba za su sa zuciya ga amincinka ba.
Masu rai, masu rai, su suke yabonka,
kamar yadda nake yi a yau;
iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu
game da amincinka.
Ubangiji zai cece ni,
za mu kuma rera da kayan kiɗi masu tsirkiya
dukan kwanakinmu
a cikin haikalin Ubangiji.
Ishaya ya riga ya ce, “Ku shirya curin da aka yi da ’ya’yan ɓaure ku kuma shafa a marurun, zai kuwa warke.”
Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan haura zuwa haikalin Ubangiji?”
Jakadu daga Babilon
([2 Sarakuna 20.12-19])
A wannan lokaci Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu da kuma kyauta, domin ya ji rashin lafiyarsa da kuma warkarwarsa. Hezekiya ya marabci jakadun da murna ya kuma nuna musu abin da gidajen ajiyarsa sun ƙunsa, azurfa, zinariya, yaji, tatsatsen mai, dukan kayan yaƙinsa da kuma kome da yake a ma’ajinsa. Babu abin da yake a cikin fadansa ko cikin dukan masarautarsa da Hezekiya bai nuna musu ba.
Sai Ishaya annabi ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi ya ce, “Mene ne waɗannan mutane suka faɗa, kuma daga ina suka fito?”
Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Sun zo ne daga Babilon.”
Annabi ya yi tambaya ya ce, “Mene ne suka gani a fadanka?”
Hezekiya ya ce, “Sun ga kome da kome a fadana. Babu abin da ban nuna musu a cikin ma’ajina ba.”
Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji maganar Ubangiji Maɗaukaki. Tabbatacce lokaci yana zuwa sa’ad da kome da yake cikin fadanka, da kuma dukan abin da kakanninka suka ajiye har yă zuwa yau, za a kwashe zuwa Babilon babu abin da za a bari, in ji Ubangiji. Waɗansu cikin zuriyarka, nama da jininka waɗanda za a haifa maka, za a kwashe su a tafi, za su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”
Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka yi tana da kyau.” Gama ya yi tunani a ransa cewa, “Salama da kāriya za su kasance a zamanina.”
Ta’aziyya don mutanen Allah
Ta’aziyya, ku ta’azantu mutanena,
in ji Allahnku.
Yi magana mai kwantar da rai ga Urushalima,
ku kuma furta mata
cewa aiki mai zafinta ya isa,
cewa an fanshi zunubinta,
cewa ta karɓi daga hannun Ubangiji
ninki biyu saboda dukan zunubanta.
Muryar wani tana kira cewa,
“A cikin hamada ku shirya
hanya saboda Ubangiji;40.3 Ko kuwa Muryar wani mai kira a cikin hamada. “Ku shirya hanya domin Ubangiji”.
ku miƙe manyan hanyoyi domin Allahnmu
a cikin jeji.
Za a cike kowane kwari,
a baje kowane dutse da kowane tudu;
za a mayar da karkatattun wurare su zama sumul,
munanan wurare kuma su zama da kyau.
Za a kuma bayyana ɗaukakar Ubangiji,
dukan mutane kuwa za su gan ta.
Gama Ubangiji da kansa ne ya yi magana.”
Muryar tana cewa, “Ka yi shela.”
Na kuwa ce, “Me zan yi shelar?”
“Dukan mutane kamar ciyawa suke,
kuma dukan ɗaukakarsu kamar furannin jeji ne.
Ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi,
domin Ubangiji ya hura iska a kansu.
Tabbatacce mutane ciyawa ne.
Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi,
amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada.”
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona,
ka haura a bisa dutse.
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima,40.9 Ko kuwa Ya Sihiyona, mai kawo labari mai daɗi, haura bisa dutse. Ya Urushalima, mai kawo labari mai daɗi
ka tā da muryarka ka yi ihu,
ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro;
faɗa wa garuruwan Yahuda,
“Ga Allahnku!”
Duba, Ubangiji Mai Iko Duka yana zuwa da iko,
hannunsa kuma yana yin mulki dominsa.
Duba, ladarsa tana tare da shi,
sakamakonsa kuma na rakiyarsa.
Yakan lura da garkensa kamar makiyayi.
Yakan tattara tumaki wuri ɗaya
yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa;
a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.
Wane ne ya auna ruwaye a tafin hannunsa,
ko kuwa ya gwada tsawon sammai da fāɗin tafin hannunsa?
Wane ne ya riƙe ƙurar ƙasa a kwando,
ko kuwa ya auna nauyin duwatsu a magwaji,
tuddai kuma a ma’auni?
Wane ne ya fahimci zuciyar40.13 Ko kuwa Ruhun; Ko kuwa ruhu Ubangiji,
ko kuwa ya koya masa a matsayin mashawarcinsa?
Wane ne Ubangiji ya nemi shawararsa don yă ganar da shi,
wane ne kuma ya koya masa hanyar da ta dace?
Wane ne ya koya masa sani
ko ya nuna masa hanyar fahimta?
Tabbatacce al’ummai suna kama da ɗigon ruwa a cikin bokiti
an ɗauke su a matsayin ƙura a kan magwaji;
yakan auna tsibirai sai ka ce ƙura mai laushi.
Itatuwan Lebanon ba su isa a yi wutar bagade da su ba,
balle dabbobinsa su isa yin hadayun ƙonawa.
A gabansa dukan al’ummai ba kome ba ne;
ya ɗauke su ba a bakin kome ba
kuma banza ne kurum.
To, ga wane ne za ka kwatanta Allah?
Wace siffa za ka kwatanta shi da ita?
Gunki dai, maƙeri kan yi zubinsa,
maƙerin zinariya kuma yă ƙera shi da zinariya
yă kuma sarrafa masa sarƙoƙin azurfa.
Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba
kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba.
Yakan nemi gwanin sassaƙa
don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba.
Ba ku sani ba?
Ba ku taɓa ji ba?
Ba a faɗa muku daga farko ba?
Ba ku fahimta ba tun kafawar duniya?
Yana zaune a kursiyi a bisa iyakar duniya,
kuma mutanenta suna kama da fāra.
Ya miƙa sammai kamar rumfa,
ya kuma shimfiɗa su kamar tentin da za a zauna a ciki.
Yakan mai da sarakuna ba kome ba
yă mai da masu mulkin wannan duniya wofi.
Ba da jimawa ba bayan an shuka su,
ba da jimawa ba bayan an dasa su,
ba da jimawa ba bayan sun yi saiwa a ƙasa,
sai yă hura musu iska su yanƙwane,
guguwa kuma ta kwashe su kamar yayi.
“Ga wa za ku kwatanta ni?
Ko kuwa wa yake daidai da ni?” In ji Mai Tsarkin nan.
Ku ɗaga idanunku ku duba sammai.
Wane ne ya halicce dukan waɗannan?
Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya,
yana kiransu, kowanne da sunansa.
Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma,
babu ko ɗayansu da ya ɓace.
Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce
kana kuma gunaguni cewa,
“Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji;
Allah bai kula da abin da yake damuna ba”?
Ba ku sani ba?
Ba ku ji ba?
Ubangiji madawwamin Allah ne,
Mahaliccin iyakokin duniya.
Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,
kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Mai taimakon Isra’ila
“Ku yi shiru a gabana, ku tsibirai!
Bari al’ummai su sabunta ƙarfinsu!
Bari su zo gaba su yi magana;
bari mu sadu a wurin shari’a.
“Wa ya zuga wannan daga gabas,
yana kiransa cikin adalci ga yin hidima?41.2 Ko kuwa / wanda nasara ke samunsa a kowane mataki
Ya miƙa masa al’ummai
ya kuma yi nasara da sarakuna a gabansa.
Ya mai da su ƙura da takobinsa,
zuwa inda iska ke hurawa ta wurin bugun da ya yi musu.
Ya fafare su ya kuma yi tafiyarsa lafiya ƙalau,
a hanyar da ƙafafunsa ba su taɓa bi ba.
Wane ne ya taɓa yin haka ya kuma sa ya faru,
yana kira ga tsararraki daga farko?
Ni, Ubangiji ina can tun farkonsu
ni kuma ina can har ƙarshe, Ni ne shi.”
Tsibirai sun gan shi suka kuma ji tsoro;
iyakokin duniya sun yi rawar jiki.
Suka kusato suka kuma zo gaba;
kowa na taimakon wani
yana ce wa ɗan’uwansa, “Ka ƙarfafa!”
Masassaƙi yakan ƙarfafa maƙerin zinariya,
kuma shi mai gyara da guduma ya yi sumul
yakan ƙarfafa mai harhaɗawa.
Ya ce game da haɗin, “Ya yi kyau.”
Yakan buga ƙusoshi su riƙe gunkin don kada yă fāɗi.
“Amma kai, ya Isra’ila, bawana,
Yaƙub, wanda na zaɓa,
zuriyar Ibrahim abokina,
na ɗauke ka daga iyakar duniya,
daga kusurwoyi masu nesa na kira ka.
Na ce, ‘Kai bawana ne’;
na zaɓe ka ban kuwa ƙi ka ba.
Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
“Duk wanda ya yi fushi da kai
tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci;
waɗanda suka yi hamayya da kai
za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.
Ko ka nemi abokan gābanka,
ba za ka same su ba.
Waɗanda suke yaƙi da kai
za su zama kamar ba kome ba.
Gama ni ne Ubangiji Allahnka,
wanda ya riƙe ka da hannun damana
ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;
zan taimake ka.
Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi,
ya ƙaramin Isra’ila,
gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji,
Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
“Duba, zan sa ka cikin abin sussuka,
saboda kuma mai kaifi mai haƙora da yawa.
Za ka yi sussukar duwatsu ka ragargaza su,
ka kuma farfashe tuddai su zama kamar yayi.
Za ka tankaɗe su, iska kuma ta kwashe su,
guguwa kuma za tă warwatsa su.
Amma za ka yi farin ciki a cikin Ubangiji
ka kuma ɗaukaka a cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
“Matalauta da mabukata suna neman ruwa,
amma babu kome;
harsunansu sun bushe saboda ƙishi.
Amma Ni Ubangiji zan amsa musu;
Ni, Allah na Isra’ila, ba zan yashe su ba.
Zan sa koguna su malalo a ƙeƙasassun tuddai,
maɓulɓulan ruwa kuma a kwaruruka.
Zan mai da hamada tafkunan ruwa,
busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓulɓulan ruwa.
Zan sa a hamada ta tsiro da
al’ul da itacen ƙirya, da itacen ci-zaƙi, da zaitun.
Zan sa itace mai girma a ƙasashe masu sanyi ya tsiro a ƙeƙasasshiyar ƙasa,
tare da fir da kuma saifires,
don mutane su gani su kuma sani,
su lura su kuma fahimci,
cewa hannun Ubangiji ne ya aikata haka,
cewa Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya sa abin ya faru.
“Ka gabatar da damuwarka,” in ji Ubangiji.
“Ka kawo gardandaminka,” in ji Sarki na Yaƙub.
“Ka shigar da gumakanka don su faɗa mana
abin da zai faru.
Faɗa mana abubuwan da suka riga suka faru,
domin mu lura da su
mu kuma san abin da zai faru a ƙarshe.
Ko kuwa ku furta mana abubuwan da za su faru,
faɗa mana abin da nan gaba ta ƙunsa,
don mu san cewa ku alloli ne.
Ku yi wani abu, mai kyau ko mummuna,
don mu ji tsoro da fargaba.
Amma ku ba kome ba ne
kuma ayyukanku banza da wofi ne;
duk wanda ya zaɓe ku abin ƙyama ne.
“Na zuga wani daga arewa, ya kuwa zo,
wani daga inda rana ke fitowa wanda yake kira bisa sunana.
Yana takawa a kan masu mulki kamar da taɓarya,
sai ka ce maginin tukwane yana taka laka.
Wa ya faɗi wannan tun daga farko, don mu sani,
ko kafin ya faru, don mu ce, ‘Ya faɗi daidai’?
Ba wanda ya faɗa wannan,
ba wanda ya riga faɗe shi,
ba wanda ya ji wata magana daga gare ku.
Ni ne na farkon da ya ce wa Sihiyona, ‘Duba, ga su nan!’
Na ba wa Urushalima saƙon labari mai daɗi.
Na duba amma ba kowa
ba wani a cikinsu da zai ba da shawara,
ba wani da zai ba da amsa sa’ad da na tambaye su.
Duba, dukansu masu ƙarya ne!
Ayyukansu ba su da riba;
siffofinsu iska ne kawai da ruɗami.
Bawan Ubangiji
“Ga bawana, wanda na ɗaukaka,
zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi;
Zan sa Ruhuna a cikinsa
zai kuwa kawo adalci ga al’ummai.
Ba zai yi ihu ko ya tā da murya,
ko ya daga muryarsa a tituna ba.
Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba,
ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba.
Cikin aminci zai kawo adalci;
ba zai kāsa ko ya karai ba
sai ya kafa adalci a duniya.
Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”
Ga abin da Allah Ubangiji ya ce,
shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su,
wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta,
wanda ya ba wa mutanenta numfashi,
da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta.
“Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci;
zan riƙe hannunka.
Zan kiyaye ka in kuma sa ka
zama alkawari ga mutane
haske kuma ga Al’ummai,
don ka buɗe idanun makafi
ka ’yantar da kamammu daga kurkuku
kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.
“Ni ne Ubangiji; sunana ke nan!
Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka.
Duba, abubuwan da sun tabbata,
sababbin abubuwa kuwa nake furtawa;
kafin ma su soma faruwa
na sanar da su gare ku.”
Waƙar yabo ga Ubangiji
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
ku yi yabonsa daga iyakar duniya,
ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,
ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.
Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu;
bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki.
Bari mutanen Sela su rera don farin ciki;
bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.
Bari su ɗaukaka Ubangiji
su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.
Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi,
kamar jarumi zai yi himma;
da ihu zai tā da kirarin yaƙi
zai kuma yi nasara a kan abokan gābansa.
“Na daɗe ina shiru,
na yi shiru na kuma ƙame kaina.
Amma yanzu, kamar mace mai naƙuda,
na yi ƙara, ina nishi ina kuma haki.
Zan lalatar da duwatsu da tuddai
in busar da dukan itatuwansu;
zan mai da koguna su zama tsibirai
in kuma busar da tafkuna.
Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba,
a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su;
zan mai da duhu ya zama haske a gabansu
in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul.
Abubuwan da zan yi ke nan;
ba zan yashe su ba.
Amma waɗanda suka dogara ga gumaka,
waɗanda suke ce wa siffofi, ‘Ku ne allolinmu,’
za a mai da su baya da kunya.
Isra’ila makaho da kuma kurma
“Ka ji, kai kurma;
duba, kai makaho, ka kuma gani!
Wane ne makaho in ba bawana ba,
da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba?
Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni,
makaho kamar bawan Ubangiji?
Kun ga abubuwa masu yawa, amma ba ku kula ba;
kunnuwanku suna a buɗe, amma ba kwa jin wani abu.”
Yakan gamsar da Ubangiji
saboda adalcinsa
ya sa dokarsa ta zama mai girma da kuma mai ɗaukaka.
Amma ga mutanen da aka washe aka kuma kwashe ganima,
an yi wa dukansu tarko a cikin rammuka
ko kuma an ɓoye su cikin kurkuku.
Sun zama ganima,
babu wani da zai kuɓutar da su;
an mai da su ganima,
ba wanda zai ce, “Mayar da su.”
Wane ne a cikinku zai saurari wannan
ko ya kasa kunne sosai a cikin kwanaki masu zuwa?
Wa ya ba da Yaƙub don yă zama ganima
Isra’ila kuma ga masu kwasar ganima?
Ba Ubangiji ba ne,
wanda kuka yi wa zunubi?
Gama ba su bi hanyoyinsa ba;
ba su yi biyayya da dokarsa ba.
Saboda haka ya zuba musu zafin fushinsa,
yaƙi mai tsanani.
Ya rufe su cikin harsunan wuta, duk da haka ba su gane ba;
ya cinye su, amma ba su koyi kome ba.
Mai Ceto kaɗai na Isra’ila
To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,
shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,
“Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;
na kira ka da suna; kai nawa ne.
Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,
zan kasance tare da ku;
sa’ad da kuka bi ta koguna,
ba za su kwashe ku ba.
Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,
ba za tă ƙone ku ba;
harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;
na bayar da Masar don fansa,
Kush da Seba a maimakonku.
Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,
saboda kuma ina ƙaunarku,
zan ba da mutane a maimakonku,
al’umma kuma domin ranku.
Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku;
zan kawo yaranku daga gabas
in kuma tattara ku daga yamma.
Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’
Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’
Kawo ’ya’yana maza daga nesa
’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya,
kowa da ake kira da sunana,
wanda aka halitta saboda ɗaukakata,
wanda na siffanta na kuma yi.”
Jagoranci waɗanda suke da idanu amma suke makafi,
waɗanda suke da kunnuwa amma suke kurame.
Dukan al’ummai su taru
mutane kuma su tattaru.
Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan
ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru?
Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai,
don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.”
“Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji,
“bawana kuma wanda na zaɓa,
saboda ka sani ka kuma gaskata ni
ka kuma fahimci cewa ni ne shi.
Kafin ni babu allahn da aka siffanta,
ba kuwa za a yi wani a bayana ba.
Ni kaɗai, ni ne Ubangiji,
kuma in ban da ni babu wani mai ceto.
Na bayyana na ceci na kuma furta,
Ni ne, ba wani baƙon allah a cikinku.
Ku ne shaiduna,” in ji Ubangiji, “cewa ni ne Allah.
I, kuma tun fil azal ni ne shi.
Babu wani da zai amshi daga hannuna.
Sa’ad da na aikata, wa zai iya sauyawa?”
Jinƙan Allah da rashin amincin Isra’ila
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila,
“Saboda ku zan aika Babilon
in kawo dukan Babiloniyawa kamar masu gudun hijira,43.14 Ko kuwa Kaldiyawa
a cikin jiragen ruwa waɗanda suke taƙama da su.
Ni ne Ubangiji, Mai Tsarkin nan,
Mahaliccin Isra’ila, Sarkinku.”
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya yi hanya ta cikin teku,
hanya ta cikin manyan ruwaye,
wanda ya ja kekunan yaƙi da dawakai,
mayaƙa da kuma ƙarin mayaƙa tare
ya kwantar da su a can, ba kuwa za su ƙara tashi ba,
ya kashe hayaƙi daga lagwani,
“Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru;
kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce.
Duba, ina yi abu sabo!
Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba?
Ina yin hanya a cikin hamada
rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa.
Namun jeji suna girmama ni,
diloli da mujiyoyi ma haka,
domin na tanada musu ruwa a hamada
da rafuffuka a ƙeƙasasshiyar ƙasa,
don a ba da abin sha ga mutanena, zaɓaɓɓuna,
mutanen da na yi saboda kaina
don su furta yabona.
“Duk da haka ba ku kira bisa sunana ba, ya Yaƙub,
ba ku gajiyar da kanku saboda ni ba, ya Isra’ila.
Ba ku kawo mini tumaki don hadaya ta ƙonewa ba,
balle ku girmama ni da hadayunku.
Ban nawaita muku da hadaya ta gari ba
balle in gajiyar da ku da bukatar turare.
Ba ku saya wani turaren kalamus domina ba
ko ku gamshe ni da kitsen hadayunku.
Amma kun nawaita ni da zunubanku
kuka kuma gajiyar da ni da laifofinku.
“Ni kaɗai ne na shafe
laifofinku, saboda sunana,
ban kuma ƙara tunawa da zunubanku ba.
Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce,
bari mu yi muhawwara wannan batu tare;
ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku.
Mahaifinku na farko ya yi zunubi;
masu magana a madadinku suka yi mini tayarwa.
Saboda haka zan kunyata manyan baƙi na haikalinku,
zan tura Yaƙub ga hallaka
Isra’ila kuwa yă zama abin dariya.
Isra’ila zaɓaɓɓe
“Amma yanzu ka saurara, ya Yaƙub, bawana,
Isra’ila, wanda zaɓa.
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi wanda ya yi ka, wanda ya siffanta ka a cikin mahaifa,
wanda kuma zai taimake ka.
Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub, bawana,
Yeshurun, wanda na zaɓa.
Gama zan zuba ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa,
rafuffuka kuma a busasshiyar ƙasa;
zan ba da Ruhuna ga ’ya’yanka,
albarkata kuma ga zuriyarka.
Za su tsiro kamar ciyawa a wuriyar ruwa,
kamar kurmi kusa da rafuffuka masu gudu.
Wani zai ce, ‘Ni na Ubangiji ne’;
wani kuma zai kira kansa da sunan Yaƙub;
har yanzu wani zai rubuta a hannunsa, ‘Na Ubangiji,’
ya kuma ɗauki sunan Isra’ila.
Ubangiji, ba gumaka ba
“Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Sarki da kuma Mai Fansar Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki.
Ni ne farko ni ne kuma ƙarshe;
in ban da ni babu wani Allah.
Wane ne kuwa kama da ni? Ya faɗa a ji.
Bari yă yi shela ya kuma nuna shi a gabana
mene ne ya faru tun da na kafa mutanena na dā,
mene ne kuma bai riga ya faru ba,
I, bari yă faɗa abin da zai zo.
Kada ku firgita kada kuma ku ji tsoro.
Ban furta wannan na kuma yi faɗar haka tuntuni ba?
Ku ne shaiduna. Akwai wani Allah in ban da ni?
A’a, babu wani Dutse; ban san da wani ba.”
Duk masu yin gumaka ba kome ba ne,
da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne.
Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne;
jahilai ne, marasa kunya.
Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki,
waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba?
Shi da irinsa za su sha kunya;
masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum.
Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu;
za su firgita su kuma sha mummunan kunya.
Maƙeri yakan ɗauki kayan aiki
ya yi aiki da shi a cikin garwashi;
ya ƙera gunki da guduma,
ya gyara shi da hannuwansa masu ƙarfi.
Yakan ji yunwa ya kuma rasa ƙarfi;
yakan sha ruwa ya kuma ji gajiya.
Kafinta yakan gwada katako
yă kuma zāna siffar da alli;
yă goge shi da kayan aiki
yă kuma zāna shi da alƙalami.
Yă siffanta shi a kamannin mutum,
mutum cikin dukan darajarsa,
don yă ajiye shi a cikin masujada.
Yakan ka da itacen saifires, ko kuwa ya ɗauki saifires ko oak.
Yă bar shi yă yi girma a cikin itatuwan kurmi,
ko yă shuka itacen fir, ruwan sama kuma yă sa yă yi girma.
Abin hura wutar mutum ne;
yakan ɗebi waɗansu yă hura wuta don yă ji ɗumi,
ya hura wuta yă gasa burodi.
Amma yakan ƙera zinariya yă kuma yi masa sujada;
yakan yi gunki sa’an nan yă rusuna masa.
Rabin katakon yakan ƙone a wuta;
a kansa yakan dafa abincinsa,
yă gasa namansa yă kuma ci sai ya ƙoshi.
Yakan ji ɗumi yă kuma ce,
“Aha! Na ji ɗumi; na gan wutar.”
Da sauran itacen yakan yi allah, gunkinsa;
yă rusuna masa yă kuma yi sujada.
Yakan yi masa addu’a yă ce,
“Ka cece ni; kai ne allahna.”
Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba;
an rufe idanunsu don kada su gani,
tunaninsu kuma a rufe don kada su fahimta.
Ba wanda yakan dakata ya yi tunani,
ba wanda yake da sani ko fahimi ya ce,
“Da rabinsa na yi amfani da shi don hura wuta;
na ma gasa burodi a kan garwashinsa,
na gasa nama na kuma ci.
Ya kamata in yi abin ƙyama daga abin da ya rage?
Ya kamata in rusuna wa guntun katako?”
Yana cin toka, zuciyar da ta ruɗe tana ɓad da shi;
ba zai iya cece kansa ba, ko ya ce,
“Wannan abin da yake hannun dama na ba ƙarya ba ne?”
“Tuna da waɗannan abubuwa, ya Yaƙub,
gama kai bawana ne, ya Isra’ila.
Na yi ka, kai bawana ne;
Ya Isra’ila, ba zan manta da kai ba.
Na shafe laifofinka kamar girgije,
zunubanka kamar hazon safe.
Ka komo wurina,
gama na kuɓutar da kai.”
Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan;
ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi.
Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu,
ku jeji da dukan itatuwanku,
gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub,
ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.
Za a zauna a Urushalima
“Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa.
“Ni ne Ubangiji,
wanda ya yi dukan abubuwa,
wanda ya shimfiɗa sammai
ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,
wanda ya sassāke alamun annabawan ƙarya
ya masu duba suka zama wawaye,
wanda ya tumɓuke koyon masu hikima
ya mai da shi banza,
wanda ya tabbatar da maganganun bayinsa
ya kuma cika annabce-annabcen ’yan aikansa,
“wanda ya ce game da Urushalima, ‘Za a zauna a cikinta,’
game da garuruwan Yahuda, ‘Za a gina su,’
wanda ya ce wa zurfin ruwaye, ‘Ku bushe,
zan kuma busar da rafuffukanku,’
wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina
zan kuma cika dukan abin da na gan dama;
zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,”
game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’
“Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa,
ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi
don yă ci al’ummai a gabansa
ya kuma tuɓe makaman sarakuna,
don yă buɗe ƙofofi a gabansa
don kada a kulle ƙofofi.
Zan sha gabanka
in baje duwatsu;
zan farfashe ƙofofin tagulla
in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe.
Zan ba ka dukiyar duhu,
arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare,
saboda ka san cewa ni ne Ubangiji,
Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.
Saboda sunan Yaƙub bawana,
Isra’ila zaɓaɓɓena,
na kira ka da suna
na ba ka matsayin bangirma,
ko da yake ba ka san ni ba.
Ni ne Ubangiji, kuma babu wani;
in ban da ni babu wani Allah.
Zan ƙarfafa ka,
ko da yake ba ka san ni ba,
saboda daga fitowar rana
har zuwa fāɗuwarta
mutane za su san cewa babu wani in ban da ni.
Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu,
ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i;
ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.
“Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama;
bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci.
Bari ƙasa ta buɗe,
bari ceto ya tsiro,
bari adalci ya yi girma tare da shi;
ni, Ubangijine, na sa ya faru.
“Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka,
da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa.
Yumɓu ya iya ce wa magini,
‘Me kake yi?’
Aikinka na iya cewa,
‘Ba shi da hannuwa’?
Kaiton wanda yake cewa mahaifinsa,
‘Me ka manta?’
Ko kuwa ga mahaifiyarsa,
‘Me kin haifa?’
“Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa.
Game da abubuwan da ke zuwa,
kun tambaye ni game da ’ya’yana,
ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana?
Ai, ni ne wanda ya yi duniya
na kuma halicci mutum a kanta.
Hannuwana ne sun miƙe sammai;
na umarci rundunar sararin sama.
Zan tā da Sairus45.13 Da Ibraniyanci shi cikin adalcina.
Zan sa dukan hanyoyinsa su miƙe.
Zai sāke gina birnina
ya kuma ’yantar da mutanena masu bautar talala,
amma ba don wata haya ko lada ba,
in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Kayayyakin Masar da hajar Kush,45.14 Wato, yankin Nilu na Bisa
da waɗannan dogayen Sabenawa,
za su ƙetaro zuwa wurinku
za su kuma zama naku;
za su bi bayanku,
suna zuwa cikin sarƙoƙi.
Za su rusuna a gabanku
su roƙe ku, suna cewa,
‘Tabbas Allah yana tare da ku, babu kuma wani;
babu wani allah.’ ”
Tabbatacce kai ne Allah wanda ya ɓoye kanka,
Ya Allah da Mai Ceton Isra’ila.
Dukan masu yin gumaka za su sha kunya;
za su fita da kunya gaba ɗaya.
Amma Ubangiji zai ceci Isra’ila
da madawwamin ceto;
ba za ku sāke shan kunya ko ƙasƙanci ba,
har abada.
Gama ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya halicci sammai,
shi ne Allah;
shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya,
ya kafa ta;
bai halicce ta don ta zama ba kome ba,
amma ya yi ta don a zauna a ciki,
ya ce,
“Ni ne Ubangiji,
kuma babu wani.
Ban yi magana asirce ba,
daga wani wuri a ƙasar duhu ba;
ban faɗa wa zuriyar Yaƙub,
‘Ku neme ni a banza ba.’
Ni, Ubangiji maganar gaskiya nake yi;
na furta abin da yake daidai.
“Ku tattaru ku zo;
ku taru, ku masu gudun hijira daga al’ummai.
Masu jahilci ne waɗanda suke ɗaukan gumakan katakai suna yawo,
waɗanda suke addu’a ga allolin da ba za su cece su ba.
Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi,
bari su yi shawara tare.
Wa ya faɗa wannan tuntuni,
wa ya yi shelar sa a kwanakin dā?
Ba ni ba ne, Ubangiji?
Kuma babu Allah in ban da ni,
Allah mai adalci da kuma Mai Ceto;
babu wani sai ni.
“Ku juyo gare ni ku sami ceto,
dukanku iyakokin duniya;
gama ni ne Allah,
kuma babu wani.
Da kaina na rantse,
bakina ya furta cikin dukan mutunci
kalmar da ba za a janye ba.
A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa;
ta wurina kowane harshe zai rantse.
Za su yi zance game da ni su ce, ‘A cikin Ubangiji kaɗai
akwai adalci da kuma ƙarfafawa.’ ”
Duk wanda ya yi fushi da shi
zai zo wurinsa ya kuma sha kunya.
Amma a cikin Ubangiji dukan zuriyar Isra’ila
za su sami adalci za su kuwa yi yabo.
Allolin Babilon
Bel ya rusuna, Nebo ya durƙusa ƙasa;
ana ɗaukan gumakansu a kan dabbobi ne.46.1 Ko kuwa su dabbobi ne da shanu kurum
Siffofin da ake yawo da su nawaya ne,
kayan nauyi masu gajiyarwa.
Sun durƙusa suka kuma rusuna tare;
ba su iya kuɓutar da nauyin kaya
su kansu sukan tafi bauta.
“Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub,
dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila,
ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku,
na kuma riƙe ku tun haihuwarku.
Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura
ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.
Na yi ku zan kuma riƙe ku;
zan lura da ku
in kuma kuɓutar da ku.
“Da wa za ku kwatanta ni ko ku ɗauka daidai da ni?
Da wa nake kama da har da za ku kwatanta ni?
Waɗansu sukan zubar da zinariya daga jaka
su kuma auna azurfa a ma’auni;
sukan yi haya maƙerin zinariya don yă ƙera allah,
su kuma rusuna su yi masa sujada.
Sukan daga shi a kafaɗunsu su kuma ɗauke shi;
sukan kafa shi a tsaye a wurinsa, a can kuwa zai tsaya.
Daga wannan wuri ba zai iya gusawa ba.
Ko da wani ya nemi taimakonsa, ba ya amsawa;
ba zai iya cetonsa daga wahala ba.
“Ku tuna da wannan, ku sa shi a zuciya,
ku riƙe shi a zuciya, ku ’yan tawaye.
Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā;
ni ne Allah, kuma babu wani;
ni ne Allah kuma babu wani kamar ni.
Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko,
daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba.
Na ce nufina zai tabbata,
kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.
Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta;
daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina.
Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru;
abin da na shirya, shi zan aikata.
Ku kasa kunne, ku masu taurinkai,
ku da kuke nesa da adalci.
Ina kawo adalcina kusa,
ba shi da nisa;
kuma cetona ba zai jinkirta ba.
Zan yi wa Sihiyona ceto, darajata ga Isra’ila.
Fāɗuwar Babilon
“Ki gangara, ki zauna a ƙura,
Budurwa Diyar Babilon;
ki zauna a ƙasa ba tare da rawani ba,
Diyar Babiloniyawa.47.1 Ko kuwa Kaldiyawa; haka ma a aya 5.
Ba za a ƙara kira ke marar ƙarfi ’yar gata ba.
Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari;
ki kware lulluɓinki.
Ki ɗaga fatarinki ki bar ƙafafunki tsirara,
ki kuma yi ta ratsa cikin rafuffuka.
Tsirararki zai bayyana
za a kuma buɗe kunyarki.
Zan ɗauki fansa;
ba zan bar wani ba.”
Mai Fansarmu, Ubangiji Maɗaukaki shi ne sunansa,
shi ne Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
“Zauna shiru, tafi cikin duhu,
Diyar Babiloniya;
ba za a ƙara kira ke
sarauniyar masarautai.
Na yi fushi da mutanena
na ƙazantar da gādona;
na ba su ga hannunki,
ba ki kuwa nuna musu jinƙai ba.
Har ma da tsofaffi
kin jibga musu kaya masu nauyi sosai.
Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada,
madawwamiyar sarauniya!’
Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa
ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba.
“To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi,
mai zama da rai kwance
kina kuma ce wa kanki,
‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.
Ba zan taɓa zama gwauruwa
ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’
Duk waɗannan za su sha kanki
cikin farat ɗaya, a rana guda,
rashin ’ya’ya da gwauranci.
Za su zo a kanki da cikakken minzani,
duk da yawan masu dubanki
da kuma dukan sihirinki.
Kin dogara a muguntarki
kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’
Hikimarki da saninki sun ɓad da ke
sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’
Bala’i zai fāɗo a kanki,
kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba.
Masifa za tă fāɗo a kanki
da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba;
lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba
za tă auko miki nan da nan.
“Ki dai ci gaba, da sihirinki
da kuma makarunki masu yawa,
waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya.
Mai yiwuwa ki yi nasara,
mai yiwuwa ki jawo fargaba.
Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai!
Bari masananki na taurari su zo gaba,
waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata,
bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.
Tabbas suna kama da bunnu;
wuta za tă cinye su ƙaf.
Ba za su ma iya ceton kansu
daga ikon wutar ba.
Ba wutar da wani zai ji ɗumi;
ba wutar da za a zauna kusa da ita.
Abin da za su iya yi miki ke nan kawai,
waɗannan da kika yi ta fama da su
kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya.
Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa;
babu ko ɗayan da zai cece ki.
Isra’ila mai taurinkai
“Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub,
waɗanda ake kira da sunan Isra’ila
suka kuma fito daga zuriyar Yahuda,
ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji
kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila,
amma ba da gaskiya ko adalci ba,
ku da kuke kiran kanku ’yan ƙasar birni mai tsarki
kuna kuma dogara ga Allah na Isra’ila,
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,
na nanata abubuwan da suka riga suka faru tuntuni,
bakina ya yi shelar su na kuma sanar da su;
sai nan da nan na aikata, suka kuma faru.
Gama na san yadda kuke da taurinkai;
jijiyoyin wuyanku ƙarafa ne,
goshinku tagulla ne.
Saboda haka na faɗa waɗannan abubuwa tuntuni;
kafin su faru na yi shelarsu gare ku
saboda kada ku ce,
‘Gumakana ne suka yi su;
siffar itacena da allahn zinariyana ne ya ƙaddara su.’
Kun riga kun ji waɗannan abubuwa; kuka gan su duka.
Ba za ku yarda da su ba?
“Daga yanzu zuwa gaba zan faɗa muku sababbin abubuwa,
na ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba.
Yanzu an halicce su, ba da daɗewa ba;
ba ku riga kun ji game da su kafin yau ba.
Saboda haka ba za ku ce,
‘I, na san da su ba.’
Ba ku ji ko balle ku gane ba;
tun da kunnenku bai buɗu ba.
Tabbatacce na san yadda kun zama masu tayarwa;
an kira ku ’yan tawaye daga haihuwa.
Saboda girman sunana na jinkirta fushina;
saboda girman yabona na janye shi daga gare ku,
don dai kada a yanke ku.
Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba;
na gwada ku cikin wutar wahala.
Saboda girmana, saboda girmana, na yi haka.
Yaya zan ƙyale a ƙazantar da kaina?
Ba zan raba ɗaukakata da wani ba.
An ’yantar da Isra’ila
“Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub,
Isra’ila, wanda na kira cewa,
Ni ne shi;
ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe.
Hannuna ne ya kafa harsashen duniya,
hannuna na dama kuma ya shimfiɗa sammai;
sa’ad da na kira su,
duka suka miƙe tsaye gaba ɗaya.
“Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara,
Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa?
Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna
zai aikata nufinsa a kan Babilon;
hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa.48.14 Ko kuwa Kaldiyawa; haka ma a aya 20.
Ni kaina, na faɗa;
I, na kira shi.
Zan kawo shi,
zai kuma yi nasara a cikin aikinsa.
“Ku zo kusa da ni ku kuma saurari wannan.
“Daga farkon shela ban yi magana a ɓoye ba;
a lokacin da ya faru, ina nan a wurin.”
Yanzu kuwa Ubangiji Mai Iko Duka ya aiko ni,
da Ruhunsa.
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya ce,
“Ni ne Ubangiji Allahnku,
wanda ya koya muku abin da ya fi muku kyau,
wanda ya muku hanyar da za ku bi.
Da a ce kawai za ku mai da hankali ga umarnaina,
da salamarku ta zama kamar kogi,
adalcinku kamar raƙuman teku.
Da zuriyarku ta zama kamar yashi,
’ya’yanku kamar tsabar hatsin da ba a iya ƙidayawa;
da ba za a taɓa yanke sunansu
balle a hallaka su daga gabana ba.”
Ku bar Babilon,
ku gudu daga Babiloniyawa!
Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki
ku kuma furta shi.
Ku aika shi zuwa iyakokin duniya;
ku ce, “Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.”
Ba su ji ƙishi ba sa’ad da ya bishe su a cikin hamada;
ya sa ruwa ya malalo dominsu daga dutse;
ya tsage dutse
ruwa kuwa ya kwararo.
“Babu salama ga mugaye” in ji Ubangiji.
Bawan Ubangiji
Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai;
ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa.
Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni;
tun daga haihuwata ya ambaci sunana.
Ya yi bakina kamar takobi mai kaifi,
cikin inuwar hannunsa ya ɓoye ni;
ya sa na zama kamar kibiya mai tsini
ya kuma ɓoye ni cikin kwarinsa.
Ya ce mini, “Kai bawana ne,
Isra’ila, a cikinka zan bayyana darajata.”
Amma na ce, “Na yi aiki a banza;
na kashe duk ƙarfina a banza da wofi.
Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji,
ladana kuma tana a wurin Allahna.”
Yanzu fa Ubangiji ya ce
ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa
don in dawo da Yaƙub gare shi
in kuma tattara Isra’ila gare shi,
gama an girmama ni a gaban Ubangiji
Allahna kuma ne ƙarfina
ya ce,
“Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana
don ka maido da kabilar Yaƙub
ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye.
Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai,
don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila
gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki,
ga bawan masu mulki.
“Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye,
sarakuna za su gani su kuma rusuna,
saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”
Maidowar Isra’ila
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“A lokacin tagomashina zan amsa muku,
kuma a ranar ceto zan taimake ku;
zan kiyaye ku zan kuma sa
ku zama alkawari ga mutane,
don ku maido da ƙasa
ku kuma sāke raba gādon kufai,
don ku ce wa waɗanda suke cikin kurkuku, ‘Ku fito,’
ga waɗanda suke cikin duhu kuma, ‘Ku ’yantu!’
“Za su yi kiwo kusa da hanyoyi
su kuma sami wurin kiwo a kowane tudu.
Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba,
ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba.
Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su
ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa.
Zan mayar da dukan duwatsu su zama hanyoyi,
a kuma gyara manyan hanyoyina.
Duba, za su zo daga nesa
waɗansu daga arewa, waɗansu daga yamma,
waɗansu daga yankin Aswan.”49.12 Littattafan Bahar Rum; Rubuce-rubucen Masoretik suna da Sinim
Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai;
ki yi farin ciki, ya ke duniya;
ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu!
Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa
zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.
Amma Sihiyona ta ce, “Ubangiji ya yashe ni,
Ubangiji ya manta da ni.”
“Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta
ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?
Mai yiwuwa ta manta,
amma ba zan taɓa manta da ke ba!
Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;
katangarki kullum suna a gabana.
’Ya’yanki maza su komo da gaggawa,
waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su bar ki.
Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye;
dukan ’ya’yanki sun taru suka kuma dawo gare ki.
Muddin ina raye,” in ji Ubangiji,
“Za ki yafa su duka kamar kayan ado;
za ki yi ado da su, kamar amarya.
“Ko da yake an lalatar da ke aka kuma mai da ke kufai
ƙasarki kuma ta zama kango,
yanzu za ki kāsa sosai saboda yawan mutanenki,
kuma waɗanda suka cinye ki za su kasance can da nisa.
’Ya’yan da aka haifa a lokacin baƙin cikinki
za su ce a kunnenki,
‘Wannan wuri ya yi mana kaɗan ƙwarai;
ki ƙara mana wurin zama.’
Sa’an nan za ki ce a zuciyarki,
‘Wa ya haifa waɗannan?
Na yi baƙin ciki na kuma zama wadda ba ta haihuwa;
an yi mini daurin talala aka kuma ƙi ni.
Wane ne ya yi renon waɗannan?
An bar ni ni kaɗai,
amma waɗannan, ina suka fito?’ ”
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,
“Duba, zan yi alama wa Al’ummai,
zan ɗaga tutana wa mutane;
za su kawo ’ya’yanki maza a hannuwansu
su riƙe ’ya’yanki mata a kafaɗunsu.
Sarakuna za su zama kamar iyayen reno,
sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye.
Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa;
za su lashe ƙura a ƙafafunki.
Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji;
waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.”
Za a iya ƙwace ganima daga jarumawa,
ko a kuɓutar da kamammu daga hannun marasa tsoro?
Amma ga abin da Ubangiji yana cewa,
“I, za a ƙwace kamammu daga jarumawa,
a kuma karɓe ganima daga hannun marasa tsoro;
zan gwabza da waɗanda suke gwabzawa da ke,
zan kuwa ceci ’ya’yanki.
Zan sa masu zaluntarki su ci naman jikinsu;
za su bugu da jininsu, sai ka ce sun sha ruwan inabi.
Sa’an nan dukan mutane za su sani
cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki,
Mai Fansarki, Maɗaukakin nan na Yaƙub.”
Zunubin Isra’ila da kuma biyayyar bawa
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ina takardar shaida na saki mahaifiyarka daga aure
wadda na kora?
Ko kuwa ga wanda mutumin da nake bin bashi ne
na sayar da kai?
Saboda zunubanka aka sayar da kai;
saboda laifofinka ne ya sa aka kori mahaifiyarka.
Sa’ad da na zo, me ya sa babu kowa?
Sa’ad da na yi kira, me ya sa babu wani da ya amsa?
Hannuna ya kāsa ne sosai don fansarka?
Na rasa ƙarfin kuɓutar da kai ne?
Ta wurin tsawatawa kawai na busar da teku,
na mai da koguna hamada;
kifayensu duk sun ruɓe saboda rashin ruwa
suka kuma mutu saboda ƙishi.
Na suturar da sararin sama da duhu
na kuma mai da tsummoki abin rufuwarsa.”
Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni,
don in san maganar da za tă ƙarfafa gajiyayye.
Ya farkar da ni da safe,
ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa.
Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana,
kuma ban yi tayarwa ba;
ban ja da baya ba.
Na ba da bayana ga masu dūkana,
kumatuna ga masu jan gemuna;
ban ɓoye fuskata
daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba.
Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni,
ba zan sha kunya ba.
Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara,
na kuma sani ba zan sha kunya ba.
Gama shi da zai tabbatar da ni, marar laifi ne yana kusa.
Wane ne zai kawo ƙararraki game da ni?
Bari mu je ɗakin shari’a tare!
Wane ne mai zargina?
Bari yă kalubalance ni!
Ubangiji Mai Iko Duka ne zai taimake ni.
Wane ne zai iya tabbatar da ni mai laifi?
Duk za su koɗe kamar riga;
asu za su cinye su.
Wane ne a cikinku yake tsoron Ubangiji
yana kuma yin biyayya ga maganar bawansa?
Bari wanda yake tafiya cikin duhu,
wanda ba shi da haske,
ya dogara a sunan Ubangiji ya kuma dogara ga Allahnsa.
Amma yanzu fa, dukanku waɗanda kuke ƙuna wuta
kuna kuma tanada wa kanku fitilu masu ci,
ku je ku yi tafiya a cikin hasken wutarku
da na fitilun da kuka ƙuna.
Abin da za ku karɓa ke nan daga hannuna.
Za ku kwanta a cikin azaba.
Madawwamin ceto domin Sihiyona
“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuna neman adalci
kuke kuma neman Ubangiji.
Dubi dutse daga inda aka yanke ku
da kuma mahaƙar duwatsu inda aka fafe ku;
dubi Ibrahim, mahaifinku,
da Saratu, wadda ta haife ku.
Sa’ad da na kira shi kaɗai ne,
na kuma albarkace shi na kuma mai da shi da yawa.
Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona
zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta;
zai sa hamadanta ta zama kamar Eden,
ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji.
Za a sami farin ciki da murna a cikinta,
godiya da ƙarar rerawa.
“Ku kasa kunne gare ni, mutanena;
ku ji ni, al’ummata.
Doka za tă fito daga gare ni;
shari’ata za tă zama haske ga al’ummai.
Adalcina na zuwa da sauri,
cetona yana a kan hanya,
hannuna kuma zai kawo adalci ga al’ummai.
Tsibirai za su dube ni
su kuma jira da sa zuciya don hannuna.
Ku daga idanunku zuwa sammai
ku dubi duniya a ƙasa;
sammai za su ɓace kamar hayaƙi,
duniya za tă shuɗe kamar riga
mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje.
Amma cetona zai dawwama har abada,
adalcina ba zai taɓa kāsa ba.
“Ku ji ni, ku da kuka san abin da yake daidai,
ku mutanen da kuke da dokata a zukatanku.
Kada ku ji tsoron ba’ar da mutane suke yi
ko ku firgita saboda zargin da suke yi.
Gama asu za su cinye su kamar riga;
tsutsotsi za su cinye su kamar ulu.
Amma adalcina zai dawwama har abada,
cetona har dukan zamanai.”
Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi,
Ya hannun Ubangiji;
ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce,
kamar a zamanai na dā.
Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa,
wanda ya soki dodon ruwan nan?
Ba kai ba ne ka busar da teku,
ka busar da ruwan zurfafa masu girma,
wanda ya yi hanya a cikin zurfafan teku
saboda fansassu su ƙetare?
Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo.
Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi;
madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani.
Murna da farin ciki zai cika su,
baƙin ciki da nishi zai ɓace.
“Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku.
Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa,
’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,
har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku,
wanda ya shimfiɗa sammai
ya kuma kafa harsashen duniya,
har kuna zama da tsoro kowace rana
saboda fushin masu zalunci,
waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka?
Gama ina fushin mai zalunci?
Ba da daɗewa za a ’yantar da ’yan kurkuku;
ba za su mutu a kurkuku ba,
ba kuwa za su rasa abinci ba.
Gama ni ne Ubangiji Allahnku,
wanda ya dama teku domin raƙumansa su yi ruri,
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
Na sa maganata a bakinka
na kuma rufe ka da inuwar hannuna,
Na shimfiɗa sammai,
na kafa harsashen duniya,
na kuma ce wa Sihiyona, ‘Ku mutanena ne.’ ”
Kwaf na fushin Ubangiji
Ki farka, ki farka!
Ki tashi, ya Urushalima,
ke da kika sha daga hannun Ubangiji
kwaf na fushinsa,
ke da kika shanye har ƙasar kwaf
kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi.
Cikin dukan ’ya’yan da ta haifa;
cikin dukan ’ya’yan da ta yi reno
babu wani da zai kama hannunta.
Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki,
wa zai ta’azantar da ke?
Lalaci da hallaka, yunwa da takobi,
wa zai ƙarfafa ki?
’Ya’yanki sun sume;
sun kwanta kusurwar kowane titi,
kamar barewar da aka kama da tarko.
Sun cika da fushin Ubangiji
da kuma tsawatawar Allahnki.
Saboda haka ki ji wannan, ke mai wahala,
wadda ta bugu, amma ba da ruwan inabi.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
Allahnki, wanda ya kāre mutanensa,
“Duba, na ƙwace daga hannunki
kwaf da ya sa ki tangaɗi;
daga wannan kwaf, kwaf na fushina,
ba za ki ƙara sha ba.
Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba,
waɗanda suke ce miki,
‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’
Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa,
kamar titin da ake takawa a kai.”
Ki farka, ki farka, ya Sihiyona,
ki sanya wa kanki ƙarfi.
Ki sa rigarki na daraja,
Ya Urushalima, birni mai tsarki.
Marasa kaciya da maƙazanta
ba za su shi cikinki ba.
Ki kakkaɓe ƙurarki;
ki tashi, ki zauna a kursiyinki, ya Urushalima.
Ki ’yantar da kanki daga sarƙoƙi a wuyanki,
Ke kamammiyar Diyar Sihiyona.
Gama ga abin Ubangiji yana cewa,
“An sayar da ke ba da kuɗi ba,
kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.”
Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“Da farko mutanena suka gangara zuwa Masar don su zauna;
a baya-bayan nan, Assuriya sun zalunce su.
“Yanzu kuma me nake da shi a nan?”
In ji Ubangiji.
“Gama an kwashe mutanena ba a bakin kome ba
kuma waɗanda suka mallake su sun yi musu ba’a,
Kullum ana cin gaba da yin wa sunana saɓo.
Saboda haka mutanena za su san sunana;
saboda haka a wannan rana za su san
cewa ni ne wanda ya faɗa wannan.
I, ni ne.”
Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu
a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi
waɗanda suke shelar salama,
waɗanda suke kawo labari mai daɗi,
waɗanda suke shelar ceto,
waɗanda suke ce wa Sihiyona,
“Allahnki yana mulki!”
Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu;
tare sun yi sowa ta farin ciki.
Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona,
za su gan shi da idanunsu.
Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya,
kangonki na Urushalima,
gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa,
ya fanshi Urushalima.
Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a fili
a idanun dukan al’ummai,
da kuma dukan iyakokin duniya za su gani
ceton Allahnmu.
Ku fita, ku fita daga can!
Kada ku taɓa wani abu marar tsarki!
Ku fita daga cikinta ku zama da tsarki,
ku da kuke ɗaukan kayan aikin Ubangiji.
Amma ba za ku fita a gaggauce ba
ko ku tafi da gudu;
gama Ubangiji zai ja gabanku,
Allah na Isra’ila zai kasance mai tsaron bayanku.
Wahala da kuma ɗaukakar bawan
Duba, bawana zai aikata abubuwa da hikima;52.13 Ko kuwa zai yi nasara
za a tā da shi a kuma ɗaga shi da ɗaukaka ƙwarai.
Kamar dai yadda aka kasance da mutane masu yawa waɗanda suka giggice sa’ad da suka gan shi,
kamanninsa ya lalace ƙwarai fiye da na kowane mutum
siffarsa kuma ta yi muni fiye da yadda ta mutum take,
haka zai ba al’ummai masu yawa mamaki,
sarakuna kuma za su riƙe bakunansu don mamaki.
Gama abin da ba a faɗa musu ba, shi za su gani,
kuma abin da ba su ji ba, shi za su fahimta.
Wa ya gaskata saƙonmu
kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?
Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi,
kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa.
Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu,
babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa.
Mutane suka rena shi suka ƙi shi,
mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala.
Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi
aka rena shi aka yi banza da shi.
Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu
ya kuma daure da baƙin cikinmu
duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,
ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,
aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;
hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,
kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.
Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata,
kowannenmu ya kama hanyarsa;
Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa
hukuncin da ya wajaba a kanmu.
Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba,
duk da haka bai buɗe bakinsa ba;
aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka,
kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru,
haka bai buɗe bakinsa ba.
Da wulaƙanci53.8 Ko kuma Daga kamawa da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi.
Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa?
Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai;
saboda laifin mutanena aka kashe shi.53.8 Ko kuwa kawar. Duk da haka wane ne a zamaninsa ya kula cewa an yanke shi daga ƙasar masu rai saboda laifin mutanena, waɗanda ya kamata su sha bugun?
Aka yi jana’izarsa tare da mugaye,
aka binne shi tare da masu arziki,
ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba,
ko a sami ƙarya a bakinsa.
Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala,
kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi,
zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai,
nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa.
Bayan wahalar ransa,
zai ga hasken rai, ya kuma gamsu;
ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa,
zai kuma ɗauki laifofinsu.
Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya,
zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi,
domin ya ba da ransa har mutuwa,
aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi.
Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa,
ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.
Ɗaukakar nan gaba ta Sihiyona
“Ki rera, ya ke bakararriya,
ke da ba ki taɓa haihuwa ba;
ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki,
ke da ba ki taɓa naƙuda ba;
domin ’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,”
in ji Ubangiji.
“Ki fadada wurin tentinki,
ki miƙe labulen tentinki da fāɗi,
kada ki janye;
ƙara tsawon igiyoyinta,
ki kuma ƙara ƙarfin turakunta.
Gama za ki fadada zuwa dama da hagu;
zuriyarki za su kori al’ummai
su kuma zauna a kufan biranensu.
“Kada ki ji tsoro; ba za ki sha kunya ba.
Kada ki ji tsoron wulaƙanci, ba za a ƙasƙantar da ke ba.
Za ki manta da kunyar ƙuruciyarki
ba kuwa za ki tuna da zargin zaman gwauruwarki ba.
Gama Mahaliccinki shi ne mijinki,
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki;
ana ce da shi Allahn dukan duniya.
Ubangiji zai kira
sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta,
macen da ta yi aure a ƙuruciya,
sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki.
“Gama a ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke,
amma da ƙauna mai zurfi zan sāke dawo da ke.
Cikin fushi mai zafi
na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci,
amma da madawwamin alheri
zan ji tausayinki,”
in ji Ubangiji Mai Fansarki.
“A gare ni wannan ya yi kamar kwanakin Nuhu,
sa’ad da na rantse cewa ruwan Nuhu ba za su ƙara rufe duniya ba.
Yanzu fa na rantse ba zan yi fushi da ke ba,
ba zan ƙara tsawata miki kuma ba.
Ko da duwatsu za su girgiza
a kuma tumɓuke tuddai,
duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba
ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,”
in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.
“Ya ke birni mai shan azaba, wadda hadari ya bulale ki ba a kuma ta’azantar da ke ba,
zan gina ke da duwatsu turkuwoyis,54.11 Ma’anar kalmar Ibraniyancin nan ba ta da tabbas.
zan kafa harsashenki da duwatsun saffaya.54.11 Ko kuwa lafis lazuli
Zan gina hasumiyarki da jan yakutu,
ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske,
dukan katangarki kuma da duwatsu masu daraja.
Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza,
da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama.
Da adalci za a kafa ke.
Zalunci zai yi nesa da ke;
ba za ki kasance da wani abin da za ki ji tsoro ba.
Za a kawar da duk wani abin banrazana;
ba zai yi kusa da ke ba.
In wani ya far miki, ba daga wurina ba ne;
duk wanda ya far miki zai miƙa wuya gare ki.
“Duba, ni ne wanda na halicci maƙeri
wanda yake zuga garwashi ya zama harshen wuta
ya kuma ƙera makamin da ya dace da aikinsa.
Ni ne kuma na halicci mai hallakarwa ya yi ɓarna;
ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara,
za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki.
Wannan ne gādon bayin Ubangiji,
kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,”
in ji Ubangiji.
Gayyata ga masu jin ƙishi
“Ku zo, dukanku masu jin ƙishi,
ku zo wurin ruwaye;
ku kuma da ba ku da kuɗi,
ku zo, ku saya ku kuma ci!
Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara
ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba.
Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba,
ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba?
Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau,
ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau.
Ku kasa kunne ku kuma zo gare ni;
ku saurare ni, don ranku ya rayu.
Zan yi madawwamin alkawari da ku,
zan nuna muku ƙaunata marar ƙarewa da na yi wa Dawuda alkawari.
Duba, na mai da shi shaida ga mutane,
shugaba da kuma jagorar mutane.
Tabbatacce za ku kira al’umman da ba ku sani ba,
kuma al’umman da ba ku sani ba za su sheƙo a guje zuwa wurinku,
saboda Ubangiji Allahnku,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila,
gama ya darjanta ku.”
Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;
ku yi kira gare shi tun yana kusa.
Bari mugu ya bar irin halinsa
mugu kuma ya sāke irin tunaninsa.
Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa,
ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.
“Gama tunanina ba tunaninku ba ne,
yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,”
in ji Ubangiji.
“Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,
haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa
tunanina kuma dabam da naku.
Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke
saukowa daga sama,
ba sa komowa
ba tare da sun jiƙe duniya
sun kuma sa su yi ’ya’ya su kuma yi toho,
don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci,
haka maganata da take fitowa daga bakina.
Ba za tă koma gare ni wofi ba,
amma za tă cika abin da nake so
ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.
Za ku fita da farin ciki
a kuma bi da ku da salama;
duwatsu da tuddai
za su ɓarke da waƙa a gabanku,
dukan itatuwan jeji kuma
za su tafa hannuwansu.
A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro,
a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro.
Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi,
madawwamiyar alama ce,
wadda ba za a datse ba.”
Ceto domin waɗansu
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ku riƙe gaskiya
ku yi abin da yake daidai,
gama cetona yana kusa
za a kuma bayyana adalcina nan da nan.
Mai albarka ne mutumin da ya aikata wannan,
mutumin da ya riƙe kam
yana kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba,
yana kuma kiyaye kansa daga yin mugun abu.”
Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce,
“Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.”
Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa,
“Ni busasshen itace ne kawai.”
Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai,
waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni
suna kuma riƙe da alkawarina kankan,
a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa
zan ba da matuni da kuma suna
mafi kyau fiye da ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata;
zan ba su madawwamin sunan
da ba za a raba su da shi ba.
Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji
don su bauta masa,
su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji,
waɗanda kuma suke yin masa sujada,
duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba
suka kuma riƙe alkawarina kankan,
waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena
in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a.
Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu
za su zama abin karɓa a bagadena;
gama za a ce da gidana
gidan addu’a domin dukan al’ummai.”
Ubangiji Mai Iko Duka ya furta cewa,
zai tattara korarru na Isra’ila,
“Zan ƙara tattaro waɗansu
bayan waɗanda na riga na tattara.”
Zargin da Allah ya yi a kan mugaye
Ku zo, dukanku namun jeji,
ku zo ku ci, dukanku namun jeji!
Matsaran Isra’ila makafi ne,
dukansu jahilai ne;
dukansu bebayen karnuka ne
ba za su iya haushi ba;
suna kwance ne kawai suna mafarki,
suna son barci ba dama.
Su karnuka ne masu kwaɗayi;
ba su taɓa ƙoshi.
Su makiyaya ne marasa ganewa;
duk sun nufi inda suka ga dama,
kowa yana nemar wa kansa riba.
Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi!
Bari mu cika cikinmu da barasa!
Gobe ma zai zama kamar yau,
ko ma fiye da haka.”
Mai adalci yakan mutu,
ba kuwa wanda yakan yi tunani a zuciyarsa;
an kwashe mutanen kirki,
ba kuwa wanda ya fahimta
cewa an kwashe masu adalci
don a tsame su daga mugunta.
Waɗanda suke aikata abin da yake daidai
sukan shiga da salama;
sukan huta yayinda suka kwanta cikin kabari.
“Amma ku, ku matso nan, ku ’ya’ya maza na masu sihiri,
ku zuriyar mazinata da karuwai!
Wane ne kuke yi wa ba’a?
Ga wa kuke masa gwalo
kuna kuma fitar da harshe?
Ashe, ku ba tarin ’yan tawaye ba ne,
zuriyar maƙaryata?
Kuna cike da muguwar sha’awa mai ƙonawa a cikin itatuwan oak
da kuma a ƙarƙashin kowane itace mai inuwa;
kuna miƙa hadayar ’ya’yanku a rafuffuka
da kuma a ƙarƙashin tsagaggun duwatsu.
Gumakan da suke cikin duwatsu masu sulɓi su ne rabonku;
su ɗin, su ne rabonku.
I, gare su kuka kwarara hadayu na sha
kuka kuma miƙa hadayu na gari.
Saboda waɗannan abubuwa, zan yi haƙuri?
Kun yi gadonku a dogayen duwatsu masu tsayi da kuma a tudu mai tsawo;
a can kuka haura don ku miƙa hadayunku.
A bayan ƙofofi da madogaran ƙofofi
kuka kafa alamun gumakanku.
Kuka yashe ni, kuka kware gadonku,
kuka kwanta a kansa kuka fadada shi;
kuka kuma ƙulla yarjejjeniya da waɗanda kuke ƙaunar gadajensu,
kuka dubi tsiraicinsu.
Kuka tafi wurin Molek57.9 Ko kuwa zuwa wurin sarki da man zaitun
kuka kuma riɓaɓɓanya turarenku.
Kuka aika jakadunku57.9 Ko kuwa gumakan can da nisa;
kuka gangara zuwa cikin kabari kansa!
Kuka gaji cikin dukan al’amuranku,
amma ba ku iya cewa, ‘Aikin banza ne ba.’
Kuka sami sabuntar ƙarfinku,
ta haka ba ku suma ba.
“Wa ya sa ku fargaba, kuna jin tsoro
har kuka yi mini ƙarya,
ba ku kuma tuna da ni ba
balle ku yi tunanin wannan a zukatanku?
Ba don na daɗe ina shiru ba ne
ya sa ba kwa tsorona?
Zan bayyana adalcinku da kuma ayyukanku,
ba kuwa za su amfane ku ba.
Sa’ad da kuka nemi taimako,
bari tarin gumakanku su cece ku!
Iska za tă kwashe dukansu tă tafi,
ɗan numfashi kawai zai hura su.
Amma mutumin da ya mai da ni mafakarsa
zai gāji ƙasar
ya kuma mallaki dutsena mai tsarki.”
Ta’aziyya don mai tuba
Za a kuma ce,
“Ku gina, ku gina, ku gyara hanya!
Ku kawar da abubuwan sa tuntuɓe a hanyar mutanena.”
Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa
wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne,
“Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri,
amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu,
don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u
in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.
Ba zan tuhume su har abada ba,
ba kuwa kullum zai yi fushi ba,
gama a haka ruhun mutumin zan yi suma a gabana,
shi numfashin mutumin da na halitta.
Na yi fushi saboda kwaɗayin zunubinsa;
na yi masa horo, na kuma ɓoye fuskata saboda fushi,
duk da haka ya ci gaba da ayyukan zunubinsa.
Na ga al’amuransa, amma zan warkar da shi;
zan bi da shi in mayar da ta’aziyya a gare shi,
ina ƙirƙiro yabo a leɓunan masu makoki a Isra’ila.
Salama, salama, ga waɗanda suke nesa da kuma kusa,”
in ji Ubangiji. “Zan kuma warkar da su.”
Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku,
wanda ba ya natsuwa,
wanda raƙumansa sukan kawo gurɓacewa da tabo.
“Babu salama ga mugaye,” in ji Allahna.
Azumi na gaskiya
“Ku yi ihu da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa.
Ku tā da muryarku kamar busar ƙaho.
Ku furta wa mutanena tawayensu
da kuma ga gidan Yaƙub zunubansu.
Gama kowace rana suna nemana;
suna marmarin sanin hanyoyina,
sai ka ce al’ummar da take yin abin da yake daidai
ba ta kuma yashe umarnan Allahnta ba.
Sun nemi shawarwaran da suke daidai daga gare ni
suna kuma marmari Allah ya zo kusa da su.
Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi,
ba ka kuma gani ba?
Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu,
ba ka kuma lura da wannan ba?’
“Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama
kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata.
Azuminku yakan ƙare a faɗa da kuma hargitsi,
kuna ta naushin juna da mugayen naushe-naushe.
Ba za ku iya azumi kamar yadda kuke yi a yau
ku zaci za a ji muryarku can sama.
Irin azumin da na zaɓa ke nan,
rana guda kawai don mutum ya ƙasƙantar da kansa?
Sunkuyar da kanku kamar iwa kawai
kuna kuma kwance a tsummoki da toka?
Abin da kuke kira azumi ke nan
rana yardajje ga Ubangiji?
“Irin azumin da na zaɓa shi ne,
a kunce sarƙoƙin rashin adalci
a kuma kunce igiyoyin karkiya,
a ’yantar da waɗanda ake zalunta
a kuma kakkarye kowace karkiya?
Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata
ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli,
sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura,
kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?
Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir,
warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan;
sa’an nan adalcinku58.8 Ko kuwa Mai Adalcinka zai tafi a gabanku,
ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya.
Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa;
za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan.
“In kuka kawar da karkiyar zalunci,
kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,
in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata
kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani,
sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu
darenku kuma zai zama kamar tsakar rana.
Ubangiji zai bishe ku kullum;
zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana
ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku.
Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa,
kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa.
Mutanenku za su sāke gina kufai na da
su kuma daga tsofaffin harsashai;
za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe,
Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama.
“In kun kiyaye ƙafafunku daga take Asabbaci
da kuma daga aikata abin da kuka gan dama a ranata mai tsarki,
in kuka kira Asabbaci ranar murna
rana mai tsarki ta Ubangiji kuma mai bangirma,
in kuka girmama ta ta wurin ƙin yin abin da kuka gan dama
da kuma yin al’amuranku ko yin mugayen maganganu,
sa’an nan za ku yi farin ciki a cikin Ubangiji,
zan kuma sa ku a kan maɗaukaka ƙasashe
ku kuma yi biki a gādon mahaifinku Yaƙub.”
Ni Ubangiji ne na faɗa.
Zunubi, furci da kuma fansa
Tabbatacce hannun Ubangiji bai kāsa yin ceto ba,
kunnensa kuma bai kurmance da zai kāsa ji ba.
Amma laifofinku sun raba
ku da Allahnku;
zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku,
saboda kada yă ji.
Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini,
yatsotsinku kuma da alhaki.
Leɓunanku suna faɗin ƙarairayi,
harshenku kuma yana raɗar mugayen abubuwa.
Babu wani mai ce a yi adalci;
babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci.
Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi;
suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta.
Suna ƙyanƙyashe ƙwan kāsā
su kuma saƙa yanar gizo-gizo.
Duk wanda ya ci ƙwansu zai mutu,
kuma sa’ad da ƙwan ya fashe, zai ƙyanƙyashe kububuwa.
Yanar gizo-gizonsu ba amfani don tufa;
ba za su iya rufuwa da abin da suka yi ba.
Ayyukansu mugaye ne,
ayyukan tā da hargitsi kuma suna a hannuwansu.
Ƙafafunsu sukan gaggauta zuwa aikata zunubi;
suna da saurin zub da jini.
Tunaninsu mugaye ne;
lalaci da hallaka sun shata hanyoyinsu.
Ba su san hanyar salama ba;
babu adalci a hanyoyinsu.
Sun mai da su karkatattun hanyoyi;
babu wanda zai yi tafiya a kansu ya sami salama.
Saboda haka gaskiya ta yi nisa da mu,
adalci kuma ba ya kaiwa gare mu.
Muna neman haske,
sai ga duhu;
muna neman haske, sai muka yi ta tafiya cikin baƙin inuwa.
Kamar makafi, sai lallubar bango muke yi,
muna lallubawar hanyarmu kamar marasa idanu.
Da tsakar rana muna tuntuɓe sai ka ce wuri ya fara duhu;
cikin ƙarfafa, mun zama kamar matattu.
Muna gurnani kamar beyar;
muna ta ƙugi kamar kurciyoyi.
Muna ta neman adalci amma ina;
mun nemi fansa, amma yana can da nisa.
Gama laifofinmu suna da yawa a gabanka,
zunubanmu kuma suna ba da shaida gāba da mu.
Laifofinmu kullum suna a gabanmu,
muna kuma sane da laifofinmu,
tawaye da mūsun Ubangiji,
mun juye bayanmu ga Allahnmu,
zugawa a yi zalunci da tayarwa,
faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya.
Saboda haka aka kau da yin gaskiya
adalci kuma ya tsaya can da nesa;
gaskiya ta yi tuntuɓe a tituna,
sahihanci ba zai shiga ba.
Gaskiya ta ɓace gaba ɗaya,
kuma duk wanda ya guji mugunta zai zama ganima.
Ubangiji ya duba bai kuwa ji daɗi
cewa babu adalci ba.
Ya ga cewa babu wani,
ya yi mamaki cewa babu wanda zai shiga tsakani;
saboda haka hannunsa ya aikata masa ceto,
adalcinsa kuma ya raya shi.
Ya yafa sulke a matsayin rigar ƙirji,
da hulan kwanon ceto a kansa;
ya sa rigunan ɗaukar fansa
ya kuma nannaɗe kansa da kishi kamar a cikin alkyabba.
Bisa ga abin da suka yi,
haka za a sāka
fushi a kan abokan gābansa
ramuwa kuma a kan maƙiyansa;
zai sāka wa tsibirai abin da ya dace da su.
Daga yamma, mutane za su ji tsoron Ubangiji,
daga mafitar rana kuma, za su girmama ɗaukakarsa.
Gama zai zo kamar rigyawa mai tsananin gudu
cewa numfashin Ubangiji zai tafi tare da shi.59.19 Ko kuwa Sa’ad da abokin gāba ya shigo kamar rigyawa, Ruhun Ubangijizai kore shi.
“Mai fansa zai zo Sihiyona,
zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,”
in ji Ubangiji.
“Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji.
Ɗaukakar Sihiyona
“Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo,
ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.
Duba, duhu ya rufe duniya
duhu mai kauri kuma yana bisa mutane,
amma Ubangiji ya taso a kanki
ɗaukakarsa kuma ya bayyana a bisanki.
Al’ummai za su zo wurin haskenki,
sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.
“Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye da ke.
Duka sun tattaru suka kuma zo wurinki;
’ya’yanki maza daga nesa,
ana kuma ɗaukan ’ya’yanki mata a hannu.
Sa’an nan za ki duba ki kuma haskaka
zuciyarki zai motsa ya kuma cika da farin ciki;
za a kawo miki wadata daga tekuna,
za a kawo miki arzikin al’ummai.
Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar,
ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa.
Daga Sheba kuma duka za su zo,
suna ɗauke da zinariya da turare
suna shelar yabon Ubangiji.
Dukan garkunan Kedar za su taru a wurinki
ragunan Nebayiwot za su yi miki hidima;
za a karɓe su kamar hadayu a kan bagadenki,
zan kuma darjanta haikalina mai ɗaukaka.
“Su wane ne waɗannan da suke firiya kamar gizagizai,
kamar kurciyoyi suna zuwa sheƙarsu?
Babu shakka tsibirai suna dogara gare ni;
jiragen Tarshish kuma su ne a gaba,
suna kawo ’ya’yanki maza daga nesa,
tare da azurfa da zinariya,
domin su girmama Ubangiji Allahnki,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila,
gama ya cika ki da daraja.
“Baƙi za su sāke gina katangarki,
sarakunansu kuma za su yi miki hidima.
Ko da yake a cikin fushi na buge ki,
da tagomashi zan yi miki jinƙai.
Ƙofofinki kullum za su kasance a buɗe,
ba za a ƙara rufe su da rana ko da dare ba,
saboda mutane su kawo miki dukiyar al’ummai,
sarakunansu za su kasance a gaba a jerin gwanon nasara.
Gama al’umma ko masarautar da ba tă bauta miki ba, za tă hallaka;
za tă lalace sarai.
“Darajar Lebanon za tă zo wurinki,
itatuwan fir da dai ire-irensu da kuma itatuwan saifires duka
za su zo don su ƙayatar da wurina mai tsarki;
zan kuma ɗaukaka wurin ƙafafuna.
’Ya’ya maza masu zaluntarku za su zo suna rusunawa a gabanki;
dukan waɗanda suka rena ki za su rusuna a ƙafafunki
su kuma ce da ke Birnin Ubangiji,
Sihiyona na Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
“Ko da yake an yashe ki aka kuma ƙi ki,
har babu wani da ya ratsa a cikinki,
zan mai da ke madawwamiyar abar taƙama
da kuma farin cikin dukan zamanai.
Za ki sha madarar al’ummai
a kuma shayar da ke da nonon sarauta.
Sa’an nan za ki san cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki,
Mai Fansarki, Mai Ikon nan na Yaƙub.
A maimakon tagulla zan kawo zinariya,
azurfa kuma a maimakon baƙin ƙarfe.
A maimakon katako zan kawo tagulla,
baƙin ƙarfe kuma a maimakon duwatsu.
Zan sa salama ta zama gwamnarki
adalci kuma mai mulkinki.
Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali a ƙasarki ba,
balle lalacewa ko hallaka a cikin iyakokinki,
amma za ki kira katangarki Ceto
ƙofofinki kuma Yabo.
Rana ba za tă ƙara zama haskenki a yini ba,
balle hasken wata ya haskaka a kanki,
gama Ubangiji zai zama madawwamin haskenki,
Allahnki kuma zai zama ɗaukakarki.
Ranarki ba za tă ƙara fāɗuwa ba
watanki kuma ba zai ƙara shuɗewa ba;
Ubangiji zai zama madawwamin haskenki,
kwanakin baƙin cikinki za su ƙare.
Sa’an nan dukan mutanenki za su zama masu adalci
za su kuma mallaki ƙasar har abada.
Su ne reshen da na shuka,
aikin hannuwana,
don nuna darajata.
Mafi ƙanƙanta a cikinki za tă zama dubu,
ƙarami zai zama al’umma mai girma.
Ni ne Ubangiji,
cikin lokacinsa zan yi haka da sauri.”
Shekarar tagomashin Ubangiji
Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,
domin Ubangiji ya shafe ni
domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.
Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,
don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru
in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu
don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji
da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,
don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,
in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,
in maido musu rawani mai kyau
a maimako na toka,
man murna
a maimako na makoki,
da kuma rigar yabo
a maimako na ruhun fid da zuciya.
Za a ce da su itatuwan oak na adalci,
shukin Ubangiji
don bayyana darajarsa.
Za su sāke gina kufai na dā
su raya wurare da aka lalace tun da daɗewa;
za su sabunta biranen da aka rurrushe
da aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce.
Baƙi za su yi kiwon garkunanki;
baƙi za su yi miki noman gonaki da gonakin inabinki.
Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji,
za a kira ku masu hidimar Allahnmu.
Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai,
kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama.
A maimakon kunyarsu
mutanena za su sami rabi riɓi biyu,
a maimakon wulaƙanci
za su yi farin ciki cikin gādonsu;
ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu,
da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu.
“Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci;
na ƙi fashi da aikata laifi.
Cikin adalcina zan sāka musu
in kuma yi madawwamin alkawari da su.
Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai
’ya’yansu kuma a cikin mutane.
Dukan waɗanda suka gan su za su san
cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”
Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;
raina yana farin ciki a cikin Allahna.
Gama ya suturce ni da rigunan ceto
ya yi mini ado da rigar adalci,
yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist
kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu
lambu kuma ya sa iri ya yi girma,
haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo
su tsiro a gaban dukan al’ummai.
Sabon sunan Sihiyona
Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba,
saboda Urushalima ba zan huta ba,
sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya,
cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.
Al’ummai za su ga adalcinki,
sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki;
za a kira ki da sabon suna
sunan da bakin Ubangiji zai ambata.
Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji,
rawanin sarauta a hannun Allahnki.
Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba,
ko a kira ƙasarki Kango.
Amma za a ce da ke Hefziba62.4 Hefziba yana nufin farin cikina yana a cikinta.
ƙasarki kuma Bewula;62.4 Bewula yana nufin wadda ta yi aure.
gama Ubangiji zai ji daɗinki,
ƙasarki kuma za tă yi aure.
Kamar yadda saurayi kan auri yarinya,
haka ’ya’yanki maza62.5 Ko kuwa Mai gini za su aure ki;
kamar kuma yadda ango yakan yi farin ciki da amaryarsa,
haka Allahnki zai yi farin ciki da ke.
Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima;
ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana.
Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji,
kada ku ba kanku hutu,
kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima
ya kuma mai da ita yabon duniya.
Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama
ta hannunsa kuma mai iko cewa,
“Ba zan ƙara ba da hatsinki
ya zama abinci ga abokan gābanki ba,
baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin
wanda kika sha wahala samu ba;
amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi
su kuma yabi Ubangiji,
waɗanda kuma suka tattara ’ya’yan inabi za su sha shi
a filayen wurina mai tsarki.”
Ku wuce, ku wuce ƙofofi!
Ku shirya hanya saboda mutane.
Ku gina, ku gina babbar hanya!
Ku kawar da duwatsu.
Ku ɗaga tuta saboda al’ummai.
Ubangiji ya yi shela
ga iyakokin duniya cewa,
“Faɗa wa Diyar Sihiyona,
‘Ga Mai Cetonki yana zuwa!
Ga ladarsa tana tare da shi,
sakamakonsa yana raka shi.’ ”
Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane,
Fansassu na Ubangiji;
za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema
Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba.
Ranar ɗaukan fansa da kuma ceto na Allah
Wane ne wannan mai zuwa daga Edom,
daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa?
Wane ne wannan, sanye cikin daraja,
tafe cikin girmar ƙarfinsa?
“Ni ne, mai magana cikin adalci,
mai ikon ceto.”
Me ya sa rigunanka suka yi ja,
sai ka ce na wanda yake tattaka ’ya’yan inabi?
“Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai;
cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni.
Na tattake su cikin fushina
Na matse su cikin hasalata;
jininsu ya fantsamar wa rigunana,
na kuma ɓata dukan tufafina.
Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata,
kuma shekarar fansata ta zo.
Na duba, amma babu wanda zai taimaka,
na yi mamaki cewa ba wanda ya goyi baya;
saboda haka hannuna ya yi mini ceto,
fushina kuma ya rayar da ni.
Na tattake al’ummai cikin fushina;
cikin hasalata kuma na sa sun bugu
na kuma zub da jininsu a ƙasa.”
Yabo da addu’a
Zan ba da labarin alherin Ubangiji,
ayyukan da suka sa a yabe shi,
bisa ga dukan abubuwan da Ubangiji ya yi mana,
I, ayyuka masu kyan da ya yi
domin gidan Isra’ila,
bisa ga jinƙansa da yawan alheransa.
Ya ce, “Babu shakka su mutanena ne,
’ya’ya maza waɗanda ba za su ruɗe ni ba”;
ta haka ya zama Mai Cetonsu.
Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu,
mala’ikan da yake gabansa ya cece su.
Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su;
ya kuma ɗaga su ya riƙe su
dukan kwanakin dā
Duk da haka suka yi tawaye
suka ɓata wa Ruhu Mai Tsarki rai.
Saboda haka ya juya ya kuma zama abokin gābansu
shi kansa kuma ya yaƙe su.
Sa’an nan mutanensa suka tuna63.11 Ko kuwa Amma bari yă tuna kwanakin dā,
kwanakin Musa da mutanensa,
ina yake shi wanda ya fitar da su ta teku,
da makiyayan garkensa?
Ina shi yake wanda ya sa
Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu,
wanda ya aika hannu ɗaukakarsa mai iko
ya kasance a hannun dama na Musa,
wanda ya raba ruwaye a gabansu,
don yă sami wa kansa madawwamin suna,
wanda ya bishe su cikin zurfafa?
Kamar doki a fili,
ba su yi tuntuɓe ba;
kamar shanun da suke gangarawa zuwa kwari,
haka Ruhun Ubangiji ya ba su hutu.
Ga yadda ka bishe mutanenka
don ka ba wa kanka suna mai ɗaukaka.
Ka duba daga sama ka gani
daga kursiyinka da yake bisa, mai tsarki da kuma mai ɗaukaka.
Ina kishinka da kuma ikonka?
Ka janye juyayi da kuma tausayin da kake yi mana daga gare mu.
Amma kai Ubanmu ne,
ko Ibrahim bai san mu ba
Isra’ila kuma bai yarda da mu ba;
kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu,
Mai Fansarmu tun fil azal ne sunanka.
Don me, ya Ubangiji, ka sa muna barin hanyoyinka
muka kuma taurare zukatanmu don kada mu girmama ka?
Ka komo domin darajar bayinka,
kabilan da suke abin gādonka.
Gama a ɗan lokaci mutanenka suka mallaki wurinka mai tsarki,
amma yanzu abokan gābanmu sun tattake wurinka mai tsarki.
Mu naka tun fil azal;
ba ka taɓa yin mulki a kansu ba,
ba a taɓa kira su da sunanka ba.63.19 Ko kuwa Mun zama kamar waɗanda ba ka taɓa yin mulkinsu ba, kamar waɗanda ba a taɓa kira da sunanka ba
Da ma za ka tsage sammai ka sauko,
ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka!
Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa
ta sa ruwa ya tafasa,
ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka
ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka!
Gama sa’ad da ka aikata abubuwan bantsoron da ba mu sa tsammani ba,
ka sauko, duwatsu kuma suka yi rawar jiki a gabanka.
Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji,
babu kunnen da ya gane,
babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai,
wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi.
Kakan taimaki waɗanda suke murnan yin abin da yake daidai,
waɗanda sukan tuna da hanyoyinka.
Amma sa’ad da muka ci gaba da yin zunubi,
kakan yi fushi.
Ta yaya za mu sami ceto ke nan?
Dukanmu mun zama kamar wanda yake marar tsabta,
kuma dukan ayyukanmu masu adalci sun zama kamar ƙazaman tsummoki;
duk mun zama kamar busasshen ganye,
kamar iska haka zunubanmu sukan share mu.
Babu wanda yake kira bisa sunanka
ko ya yi ƙoƙarin riƙe ka;
gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu
ka kuma sa muka lalace saboda zunubanmu.
Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu.
Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane;
dukanmu aikin hannunka ne.
Kada ka yi fushi fiye da kima, ya Ubangiji;
kada ka tuna da zunubanmu har abada.
Da ma ka dube mu, muna roƙonka,
gama dukanmu mutanenka ne.
Biranenka masu tsarki sun zama hamada;
har Sihiyona ma ta zama hamada; Urushalima ta zama kango.
Haikalinmu mai tsarki da kuma mai daraja, inda kakanninmu suka yabe ka,
an ƙone da wuta,
kuma dukan abubuwan da muke ƙauna sun lalace.
Bayan dukan wannan, ya Ubangiji, ba za ka yi wani abu ba?
Za ka yi shiru ka hore mu fiye da kima?
Hukunci da kuma ceto
“Na bayyana kaina ga waɗanda ba su tambaye ni ba;
ina samuwa ga waɗanda ba su neme ni ba.
Ga al’ummar da ba tă kira bisa sunana ba,
Na ce, ‘Ga ni, ga ni.’
Dukan yini ina miƙa hannuwana
ga mutane masu tayarwa,
waɗanda suna tafiya a hanyoyin da ba su da kyau,
suna bin tunaninsu,
mutanen da suna cin gaba da tsokanata
a fuskata,
suna miƙa hadayu a gonaki
suna ƙone turare a bagadan tubali;
suna zama a kaburbura
su kwana suna yin asirtattun ayyuka;
suna cin naman aladu,
tukwanensu kuma sun cika da nama marar tsabta;
suna cewa, ‘Ku tsaya a can; kada ku yi kusa da ni,
gama na fi ku tsarki!’
Irin mutanen nan hayaƙi ne a hancina,
wuta kuma da take cin gaba da ci dukan yini.
“Ga shi, yana nan a rubuce a gabana cewa
ba zan ƙyale ba, zan yi cikakken ramuwa;
zan yi ramuwa a cinyoyinsu
saboda zunubanku da kuma zunuban kakanninku,”
in ji Ubangiji.
“Gama sun ƙone turare a kan duwatsu
suka kuma ƙazantar da ni a kan tuddai,
zan yi musu awo in zuba a cinyoyinsu
cikakken ramuwa saboda ayyukansu na dā.”
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Kamar sa’ad da ruwan ’ya’yan itace yana samuwa a cikin tarin ’ya’yan inabi
mutane kuma su ce, ‘Kada a lalace shi,
har yanzu akwai abu mai kyau a ciki,’
haka nan zan yi a madadin bayina;
ba zan hallaka su duka ba.
Zan fitar da zuriyar Yaƙub,
daga Yahuda kuma waɗanda za su mallaki duwatsuna;
zaɓaɓɓun mutanena za su gāje su,
a can kuma bayina za su zauna.
Sharon zai zama wurin kiwo don shanu,
Kwarin Akor kuma wurin hutun garkuna,
domin mutanena da suke nemana.
“Amma game da ku waɗanda kuka yashe Ubangiji
kuka manta da dutsena mai tsarki kuwa,
ku da kuka shimfiɗa tebur don sa’a
kuka kuma cika darunan ruwan inabin da aka dama don Ƙaddara,
zan ƙaddara ku ga kaifin takobi,
dukanku kuma za ku sunkuya wa mai yanka;
gama na yi kira amma ba ku amsa ba,
na yi magana amma ba ku saurara ba.
Kuka aikata mugunta a gabana
kuka kuma zaɓi abin da ba na jin daɗi.”
Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“Bayin za su ci,
amma ku za ku ji yunwa;
bayina za su sha,
amma ku za ku ji ƙishi;
bayina za su yi farin ciki
amma ku za ku sha kunya.
Bayina za su rera
da farin cikin zukatansu,
amma ku za ku yi kuka
daga wahalar zuciya
ku kuma yi kururuwa da karayar zuci.
Za ku bar sunanku
ga zaɓaɓɓuna yă zama abin la’antarwa;
Ubangiji Mai Iko Duka zai kashe ku,
amma ga bayina zai ba su wani suna.
Duk wanda zai roƙi albarka a cikin ƙasar
zai yi haka da gaskiyar Allah;
wanda zai yi rantsuwa a cikin ƙasar
zai rantse da gaskiyar Allah.
Gama za a manta da wahalolin baya
a kuma ɓoye su daga idanuna.
Sabuwar sama da kuma sabuwar duniya
“Ga shi, na halicci
sabuwar sama da kuma sabuwar duniya.
Abubuwa na dā za a manta da su,
ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.
Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada
a abin da na halitta,
gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna
mutanenta kuwa abin farin ciki.
Zan yi farin ciki a kan Urushalima
in kuma yi murna saboda mutanena;
a can ba za a ƙara jin
karar makoki da na kuka ba.
“A cikinta ba za a ƙara jin
jariri ya rayu na ’yan kwanaki kawai ba,
ko kuwa wani tsohon da bai cika kwanakinsa ba;
duk wanda ya mutu yana da shekaru ɗari
za a ce ya mutu a kurciya ne kawai;
duk wanda bai kai65.20 Ko kuwa / mai zunubin da ya kai ɗari ba
za a ɗauka la’antacce ne.
Za su gina gidaje su kuma zauna a cikinsu;
za su yi shuki a gonakin inabi su kuma ci ’ya’yansu.
Ba za su ƙara gina gidaje waɗansu kuma su zauna a cikinsu ba,
ko su yi shuki waɗansu kuma su ci ba.
Gama kamar yadda kwanakin itace suke,
haka kwanakin mutanena za su kasance;
zaɓaɓɓuna za su daɗe suna jin daɗin
ayyukan hannuwansu.
Ba za su yi wahala a banza ba
ko su haifi ’ya’yan da aka ƙaddara da rashin sa’a;
gama za su zama mutanen da Ubangiji ya yi wa albarka,
su da zuriyarsu tare da su.
Kafin su yi kira zan amsa;
yayinda suke cikin magana zan ji.
Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare,
zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi,
amma ƙura ce za tă zama abincin maciji.
Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna
a kan dukan dutsena mai tsarki ba,”
in ji Ubangiji.
Hukunci da kuma bege
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Sama kursiyina ce,
duniya kuma matashin sawuna.
Ina gidan da za ku gina mini?
Ina wurin hutuna zai kasance?
Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa,
ta haka suka kasance?”
In ji Ubangiji.
“Wannan mutum ne nake jin daɗi,
shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba,
yana kuma rawar jiki ga maganata.
Amma duk ya miƙa hadayar bijimi
yana kama da wanda ya kashe mutum,
kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago,
kamar wanda ya karye wuyan kare;
duk wanda ya miƙa hadaya ta gari
yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade,
kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni,
kamar wanda yake bauta gunki ne.
Sun zaɓi hanyoyinsu,
rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;
saboda haka ni ma zan aukar musu da masifa mai zafi
in kuma kawo musu abin da suke tsoro.
Gama sa’ad da na yi kira, ba wanda ya amsa,
sa’ad da na yi magana, ba wanda ya saurara,
Sun aikata mugunta a idona
suka kuma zaɓa abin da ba na jin daɗi.”
Ku ji maganar Ubangiji,
ku da kuke rawar jiki ga maganarsa,
“’Yan’uwanku da suke ƙinku,
suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce,
‘Bari a ɗaukaka Ubangiji,
don mu ga farin cikinku!’
Duk da haka za su sha kunya.
Ku ji wannan hayaniya daga birni,
ku ji surutu daga haikali!
Amon Ubangiji ne
yana sāka wa abokan gābansa abin da ya dace da su.
“Kafin naƙuda ya fara mata,
ta haihu;
kafin zafi ya zo mata,
ta haifi ɗa.
Wa ya taɓa jin irin wannan abu?
Wa ya taɓa gani irin abubuwan nan?
Za a iya ƙirƙiro ƙasa a rana ɗaya
ko a haifi al’umma farat ɗaya?
Duk da haka da zarar Sihiyona ta fara naƙuda
sai ta haifi ’ya’yanta.
Zan kai mace har haihuwa
in kuma sa ta kāsa haihu?” In ji Ubangiji.
“Zan rufe mahaihuwa
sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?” In ji Allahnku.
“Ku yi farin ciki tare da Urushalima ku kuma yi murna saboda ita,
dukanku waɗanda kuke ƙaunarta;
ku yi farin ciki matuƙa tare da ita,
dukanku waɗanda kuke makoki a kanta.
Gama za ku tsotsa ku kuma ƙoshi
da nonon ta’aziyyarta;
za ku sha sosai
ku kuma ji daɗin yalwarta.”
Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“Zan fadada salama gare ta kamar kogi,
wadatar al’ummai kuma kamar rafi mai gudu;
za ku tsotsa a kuma riƙe ku a hannunta
ku kuma yi wasa a gwiwoyinta.
Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta
haka zan ta’azantar da ku;
za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”
Sa’ad da kuka ga wannan, zuciyarku za tă yi farin ciki
za ku kuma haɓaka kamar ciyawa;
za a sanar da hannun Ubangiji ga bayinsa,
amma za a nuna wa maƙiyansa fushinsa.
Ga shi, Ubangiji yana zuwa da wuta,
kuma kekunan yaƙinsa suna kama da guguwa;
zai sauko da fushinsa da zafi,
tsawatawarsa kuma da harsunan wuta.
Gama da wuta da kuma takobi
Ubangiji zai yi hukunci a kan dukan mutane,
kuma yawanci za su kasance waɗanda Ubangiji zai kashe.
“Waɗanda suka tsarkake suka kuma tsabtacce kansu don su je lambu, suna bin wannan da yake tsakiya66.17 Ko kuwa lambu a bayan wannan na masujadanku, kuma waɗannan da suke cin naman aladu da ɓeraye da waɗansu abubuwan banƙyama, za su sadu da ƙarshensu tare,” in ji Ubangiji.
“Ni kuwa, saboda ayyukansu da kuma tunaninsu, ina dab da zuwa in tattara dukan al’ummai da harsuna, za su kuma zo su ga ɗaukakata.
“Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai. Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore. Zan kuwa zaɓa waɗansunsu kuma su zama firistoci da Lawiyawa,” in ji Ubangiji.
“Kamar yadda sabuwar duniya da sabuwar sama za su tabbata a gabana,” in ji Ubangiji, “haka sunanku da zuriyarku za su tabbata. Daga wannan sabon wata zuwa wancan, kuma daga wannan Asabbaci zuwa wancan, dukan mutane za su zo su rusuna a gabana,” in ji Ubangiji. “Za su kuma fita su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa; tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, balle wutar da take ƙona su ta mutu, za su kuma zama abin ƙyama ga dukan mutane.”