- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Hosiya
Hosiya
Hosiya
Hos
Hosiya
Maganar Ubangiji da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash1.1 Da Ibraniyanci Yowash, wani suna na Yehowash sarkin Isra’ila.
Matar Hosiya da ’ya’yanta
Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.” Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji.
Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila. A wannan rana zan karye ƙarfin Isra’ila a Kwarin Yezireyel.”
Gomer ta sāke ɗauki ciki ta kuma haifi ’ya mace. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba ta suna, Lo-Ruhama,1.6 Lo-Ruhama yana nufin ba tausayi. gama ba zan ƙara nuna wa gidan Isra’ila ƙauna ba, har da zan gafarta musu. Duk da haka zan nuna ƙauna ga gidan Yahuda; zan kuma cece su, ba da baka, takobi ko yaƙi ba, ko ta wurin dawakai, ko masu hawan dawakai ba, sai ko ta wurin Ubangiji Allahnsu.”
Bayan ta yaye Lo-Ruhama, sai Gomer ta sāke haifi wani ɗa namiji. Sai Ubangiji ya ce, “Ka ba shi suna Lo-Ammi,1.9 Lo-Ammi yana nufin ba mutanena ba. gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.
“Duk da haka Isra’ilawa za su zama kamar yashi a bakin teku, da ba za a iya aunawa ko a ƙirga ba. A inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ za a kira su ‘’ya’yan Allah mai rai.’ Mutanen Yahuda da mutanen Isra’ila za su sāke haɗu su zama ɗaya, za su kuma naɗa shugaba guda su kuma fita daga ƙasar, gama ranar za tă zama mai girma wa Yezireyel.
“Ka ce da ’yan’uwanka maza, ‘Mutanena,’ ka kuma ce da ’yan’uwanka mata, ‘Ƙaunatacciyata.’
An hukunta an kuma mayar da Isra’ila
“Ka tsawata wa mahaifiyarka, ka tsawata mata,
gama ita ba matata ba ce,
ni kuma ba mijinta ba ne.
Ku roƙe ta tă daina karuwancinta
da kuma rashin aminci a tsakanin nononta.
In ba haka ba zai tuɓe ta tsirara
in bar ta kamar yadda take a ranar da aka haife ta;
zan sa ta zama kamar hamada,
in mayar da ita busasshiyar ƙasar,
in kashe ta da ƙishirwa.
Ba zan nuna wa ’ya’yanta ƙaunata ba,
domin su ’ya’yan zina ne.
Mahaifiyarsu ta yi rashin aminci
ta kuma ɗauki cikinsu ta wurin yi abin kunya.
Ta ce, ‘Zan bi kwartayena,
waɗanda suke ba ni abinci da ruwa,
ulu nawa da lilina, mai nawa da kuma abin sha na.’
Saboda haka zai tare hanyarta da ƙaya;
zan yi mata katanga don kada tă sami hanya.
Za tă bi kwartayenta amma ba za tă kama su ba;
za tă neme su amma ba za tă same su ba.
Sa’an nan za tă ce,
‘Zan koma ga mijina na fari,
gama dā ya fi mini yadda nake a yanzu.’
Ba ta yarda cewa ni ne
wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba,
wanda ya jibge mata azurfa da zinariya,
waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba.
“Saboda haka zan ƙwace hatsina sa’ad da ya nuna,
da sabon ruwan inabina sa’ad da ya ƙosa.
Zan karɓe ulu nawa da lilina,
da take niyya ta rufe tsiraicinta.
Saboda haka yanzu zan buɗe tsiraicinta
a idanun kwartayenta;
ba wani da zai ƙwace ta daga hannuwana.
Zan tsayar da dukan bukukkuwarta,
bukukkuwarta na shekara-shekara, da kuma kiyaye bikin Sababbin Wata nata,
kwanakin Asabbacinta, dukan ƙayyadaddun bukukkuwarta.
Zan lalatar da inabinta da kuma itatuwan ɓaurenta,
waɗanda take cewa su ne abin da kwartayenta suka biya;
zan mayar da su kurmi,
namun jeji kuwa za su ci su.
Zan hukunta ta saboda kwanakin
da ta ƙone turare wa Ba’al;
ta yi wa kanta ado da zobai da duwatsu masu daraja,
ta bi kwartayenta,
amma ta manta da ni,”
in ji Ubangiji.
“Saboda haka yanzu zan rarrashe ta;
zan bishe ta zuwa hamada
in kuma yi mata magana a hankali.
A can zan mayar mata da gonakin inabinta,
zan kuma sa Kwarin Akor2.15 Akor yana nufin wahala. yă zama ƙofar bege.
A can za tă rera kamar a kwanakin ƙuruciyarta,
kamar a lokacin da ta fita daga Masar.
“A waccan rana,” in ji Ubangiji,
“za ki ce da ni ‘mijina’;
ba za ki ƙara ce ni ‘maigidana’2.16 miji, maigida. A Ibraniyanci kalman nan “maigida” daidai ne da sunan allahn nan Ba’al. Amma Ubangiji ya yi alkawari cewa mutanensa za su kasance da zurfin dangantaka da shi (kamar mace da mijin masu aminci) a maimako bin abin da doka ta kafa kawai (kamar mata da “maigidanta”) ba.
Zan cire sunayen Ba’al daga leɓunanta;
ba za a ƙara kira sunayensu ba.
A waccan rana zan yi alkawari dominsu
da namun jeji da kuma tsuntsayen sararin sama
da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa.
Baka da takobi da yaƙi
zan sa su ƙare a ƙasar,
domin duk su zauna lafiya.
Zan ɗaura aure da ke har abada;
zan ɗaura aure da yake cikin adalci da gaskiya,
cikin ƙauna da jinƙai.
Zan ɗaura aure da yake cikin aminci
za ki kuwa yarda cewa ni ne Ubangiji.
“A waccan rana zan amsa,” in ji Ubangiji,
“zan amsa wa sararin sama,
za su kuwa amsa wa ƙasa;
ƙasa kuma za tă amsa wa hatsi,
sabon ruwan inabi da kuma mai,
su kuma za su amsa wa Yezireyel.2.22 Yezireyel yana nufin shirye-shiryen Allah.
Zan dasa ta wa kaina a ƙasar;
zan shuka ƙaunata ga wanda na ce ‘Ba ƙaunatacciyata ba.’2.23 Ibraniyanci Lo-Ruhama
Zan faɗa wa waɗanda a ce ‘Ba mutanena ba,2.23 Ibraniyanci Lo-Ammi’ ‘Ku mutanena ne’;
za su kuwa ce, ‘Kai ne Allahna.’ ”
Sulhun Hosiya da matarsa
Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi, ka sāke nuna wa matarka ƙauna, ko da yake wani yana son ta, ita kuma mazinaciya ce. Ka ƙaunace ta yadda Ubangiji yake ƙaunar Isra’ilawa, ko da yake sun juya ga waɗansu alloli suna kuma ƙauna wainar zabibi mai tsarki.”
Ta haka na saye ta da shekel goma sha biyar na azurfa da kuma wajen buhu na sha’ir. Sai na faɗa mata, “Za ki zauna tare3.3 Ko kuwa jira da ni kwanaki masu yawa; kada ki yi karuwanci ko ki yi abuta da wani namiji, ni kuwa zan zauna tare3.3 Ko kuwa jira da ke.”
Gama Isra’ilawa za su yi kwanaki masu yawa ba tare da sarki ko shugaba ba, babu hadaya ko keɓaɓɓun duwatsu, babu efod ko gunki. Daga baya Isra’ilawa za su dawo su nemi Ubangiji Allahnsu da kuma Dawuda sarkinsu. Za su je da rawan jiki wajen Ubangiji da kuma ga albarkunsa a kwanakin ƙarshe.
Tuhuma a kan Isra’ila
Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa,
gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo
a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar.
“Babu aminci, babu ƙauna,
babu yarda da Allah a cikin ƙasar.
Akwai la’ana ce kawai,4.2 Wato, a yi la’ana a kai yin ƙarya da kisa,
yin sata da zina;
sun wuce gona da iri,
kisankai a kan kisankai.
Saboda wannan ƙasar tana makoki,4.3 Ko kuwa ta bushe
kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace;
namun jeji da tsuntsayen sararin sama
da kuma kifin teku suna mutuwa.
“Amma kada wani mutum yă kawo tuhuma,
kada wani mutum yă zargi wani,
gama mutanenka suna kama da waɗanda
suke kawo tuhume-tuhume a kan firist ne.
Kuna tuntuɓe dare da rana,
annabawa ma suna tuntuɓe tare da ku.
Saboda haka zan hallaka mahaifiyarku,
mutanena suna hallaka saboda jahilci.
“Domin kun ƙi neman sani,
ni ma na ƙi ku a matsayin firistocina;
domin kun ƙyale dokar Allahnku,
ni ma zan ƙyale ’ya’yanku.
Yawan ƙaruwar firistoci,
haka suke yawan zunubi a kaina;
sun yi musaya Ɗaukakarsu da wani abin kunya.
Suna ciyar da kansu a kan zunuban mutanena
suna kuma haɗamar muguntarsu.
Zai kuwa zama, kamar yadda mutane suke, haka firistoci suke.
Zan hukunta dukansu saboda al’amuransu
in kuma sāka musu saboda ayyukansu.
“Za su ci amma ba za su ƙoshi ba;
za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba,
gama sun rabu da Ubangiji
don su ba da kansu ga karuwanci,
ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi,
waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.
Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace
suka kuwa sami amsa daga sanda.
Halin karuwanci yakan ɓad da su;
sun yi rashin aminci ga Allahnsu.
Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu
suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai,
a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri,
inda inuwa take da daɗi.
Saboda haka ’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci
surukanku mata kuma suka shiga yin zina.
“Ba zan hukunta ’ya’yanku mata
sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba,
balle surukanku mata,
sa’ad da suka yi zina,
gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai
suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada,
mutane marasa ganewa za su lalace!
“Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila,
kada Yahuda ya yi laifi.
“Kada ku tafi Gilgal;
kada ku haura zuwa Bet-Awen.4.15 Bet-Awen yana nufin gidan mugunta (sunan Betel, wanda yake nufin gidan Allah).
Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’
Isra’ilawa masu taurinkai ne,
kamar karsana mai taurinkai.
Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu
kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa?
Efraim ya haɗa kai da gumaka;
ku ƙyale shi kurum!
Ko ma sa’ad da abin shansu ya ƙare,
sai suka ci gaba da karuwancinsu;
masu mulkinsu suna ƙaunar abin kunya.
Guguwa za tă share su,
hadayunsu kuma za su jawo musu abin kunya.
Hukunci a kan Isra’ila
“Ku ji wannan, ku firistoci!
Ku kasa kunne, ku Isra’ilawa!
Ku saurara, ya ku gidan sarauta!
Wannan hukunci yana a kanku,
kun zama tarko a Mizfa,
ragar da aka shimfiɗa a kan Tabor.
’Yan tawaye sun yi zurfi cikin kisan gilla.
Zan hore su duka.
Na san Efraim ƙaf;
Isra’ila ba a ɓoye take a gare ni ba.
Efraim, yanzu ka juya ka shiga karuwanci;
Isra’ila ta lalace.
“Ayyukansu ba su ba su dama
su koma ga Allahnsu ba.
Halin karuwanci yana cikin zuciyarsu;
ba su yarda da Ubangiji ba.
Girmankan Isra’ila yana ba da shaida a kansu;
Isra’ilawa, har ma Efraim, sun yi tuntuɓe a cikin zunubinsu;
Yahuda ma ya yi tuntuɓe tare da su.
Sa’ad da suka tafi tare da garkunan shanu, tumaki da awakinsu
don su nemi Ubangiji,
ba za su same shi ba;
ya janye kansa daga gare su.
Su marasa aminci ne ga Ubangiji;
suna haihuwar shegu.
Yanzu bukukkuwar Sabon Watansu
za su cinye su da gonakinsu.
“Amon kakaki a Gibeya,
ƙaho a Rama.
Ku yi kirarin yaƙi a Bet-Awen;
ku ja gaba, ya Benyamin.
Efraim za tă zama kango
a ranar hukunci.
A cikin kabilan Isra’ila
na yi shelar abin da yake tabbatacce.
Shugabannin Yahuda suna kamar waɗanda
suke matsar da duwatsun shaidar da aka sa a kan iyaka ne.
Zan zubo musu da fushina a kansu
kamar rigyawar ruwa.
An danne Efraim,
an murƙushe ta a shari’a
ta ƙudura ga bin gumaka.
Na zama kamar asu ga Efraim,
kamar ruɓa ga mutanen Yahuda.
“Sa’ad da Efraim ya ga ciwonsa,
Yahuda kuwa miyakunta,
sai Efraim ya juya ga Assuriya,
ya aika wurin babban sarki don neman taimako.
Amma bai iya warkar da kai ba,
bai iya warkar da miyakunka ba.
Gama zan zama kamar zaki ga Efraim,
kamar babban zaki ga Yahuda.
Zan yage su kucu-kucu in tafi;
zan kwashe su, ba wanda zai kuɓutar da su.
Sa’an nan zan koma wurina
sai sun yarda da laifinsu.
Za su kuma nemi fuskata;
cikin azabansu za su nace da nemana.”
Isra’ila marar tuba
“Ku zo, mu koma ga Ubangiji.
Ya yayyage mu kucu-kucu
amma zai warkar da mu;
ya ji mana ciwo
amma zai daure mana miyakunmu.
Bayan kwana biyu zai rayar da mu,
a rana ta uku zai tashe mu,
don mu rayu a gabansa.
Bari mu yarda da Ubangiji;
bari mu nace gaba don mu yarda da shi.
Muddin rana tana fitowa,
zai bayyana;
zai zo mana kamar ruwan bazara,
kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”
“Me zan yi da kai Efraim?
Me zan yi da kai Yahuda?
Ƙaunarku tana kamar hazon safiya,
kamar raɓar safiya da takan ɓace.
Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana,
na kashe ku da kalmomin bakina;
hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku.
Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,
ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.
Kamar Adamu, sun tā da alkawari,
sun yi mini rashin aminci a can.
Gileyad birni ce ta mugayen mutane,
da tabon alamun jini.
Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum,
haka ƙungiyoyin firistoci suke;
suna kisa a hanya zuwa Shekem,
suna aikata laifofi bankunya.
Na ga wani abu mai bantsoro
a gidan Isra’ila.
A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci
Isra’ila kuma ta ƙazantu.
“Ku kuma, ya mutanen Yahuda,
na shirya muku ranar girbi.
“A duk sa’ad da zan mayar da dukiya wa mutanena,
a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila,
zunuban Efraim za su tonu
za a kuma bayyana laifofin Samariya.
Suna ruɗu,
ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje,
’yan fashi sukan yi fashi a tituna;
amma ba su gane
cewa na tuna da dukan ayyukan muguntarsu ba.
Zunubansu sun kewaye su;
kullum suna a gabana.
“Suna faranta wa sarki zuciya da muguntarsu,
shugabanni kuma da ƙarairayinsu.
Dukansu mazinata ne
suna ƙuna kamar matoya
wadda mai gashin burodi ba ya bukata yă tura mata wuta
daga cuɗe kullu har kumburinsa.
A ranar bikin sarkinmu
shugabanni sukan bugu da ruwan inabi,
yă yi cuɗanya da masu ba’a.
Zukatansu suna kamar matoya;
sukan kusace shi da wayo.
Muguwar aniyarsu takan yi ta ci dukan dare;
da safe sai ta ƙuna kamar harshen wuta.
Dukansu suna da zafi kamar matoya;
suna kashe masu mulkinsu.
Dukan sarakunansu sukan fāɗi,
kuma babu waninsu da yake kira gare ni.
“Efraim yana cuɗanya da al’ummai;
Efraim waina ne mai fāɗi da ba a juye ba.
Baƙi sun tsotse ƙarfinsa,
amma bai gane ba.
Gashi kansa ya cika da furfura,
amma bai lura ba.
Girmankan Isra’ila ya ba da shaida a kansa,
amma duk da haka
bai dawo ga Ubangiji Allahnsa
ko yă neme shi ba.
“Efraim yana kama da kurciya,
marar wayo, marar hankali,
yanzu yana kira ga Masar,
yanzu yana juyewa ga Assuriya.
Sa’ad da suka tafi, zan jefa ragata a kansu;
zai janye su ƙasa kamar tsuntsayen sararin sama.
Sa’ad da na ji suna tafiya tare,
zan kama su.
Kaitonsu,
domin sun kauce daga gare ni!
Hallaka za tă aukar musu,
domin sun tayar mini!
Na ƙudura in cece su
amma suna faɗar ƙarya a kaina.
Ba sa yin mini kuka da zuciyarsu
amma suna ihu a kan gadajensu.
Sukan taru wurin ɗaya don hatsi da ruwan inabi
amma su juya mini baya.
Na horar da su na kuma ƙarfafa su,
amma sun ƙulla mini maƙarƙashiya.
Ba sa juya ga Mafi Ɗaukaka;
suna kama da tanƙwararren baka.
Za a kashe shugabanninsu da takobi
saboda banzan maganganunsu.
Saboda wannan za a wulaƙanta su
a ƙasar Masar.
Isra’ila za tă girbe guguwa
“Ka sa kakaki a leɓunanka!
Gaggafa tana a bisan gidan Ubangiji
domin mutane sun tā da alkawarina
suka kuma tayar wa dokata.
Isra’ila ta yi mini kuka,
‘Ya Allahnmu, mun yarda da kai!’
Amma Isra’ila sun ƙi abin da yake mai kyau;
abokin gāba zai fafare su.
Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba;
sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba.
Da azurfa da zinariya
sun ƙera gumaka wa kansu
wanda zai kai zuwa ga hallakarsu.
Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya!
Fushina yana ƙuna a kansu.
Sai yaushe za su rabu da gumaka?
Su daga Isra’ila ne!
Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi;
gunki ne ba Allah ba.
Za a farfashe shi kucu-kucu,
waccan maraƙin Samariya.
“Gama sun shuka iska
don haka za su girbe guguwa.
Hatsin da yake tsaye ba shi da kai,
ba zai yi tsaba ba.
Ko da ya yi tsaba ma,
baƙi ne za su ci.
An haɗiye Isra’ila;
yanzu tana cikin al’ummai
kamar abin da ba shi da amfani.
Gama sun haura zuwa Assuriya
kamar jakin jejin da yake yawo shi kaɗai.
Efraim ya sayar da kansa ga maza.
Ko da yake sun sayar da kansu a cikin al’ummai,
yanzu zan tattara su wuri ɗaya.
Za su fara lalacewa
a ƙarƙashi danniyar babban sarki.
“Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi,
waɗannan sun zama bagade don yin zunubi.
Na rubuta musu abubuwa masu yawa na dokata,
amma suka ɗauke su tamƙar wani baƙon abu ne.
Suna miƙa hadayun da aka ba ni
su kuma ci nama,
amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu.
Yanzu zai tuna da muguntarsu
yă kuma hukunta zunubansu.
Za su koma Masar.
Isra’ila ya manta da Mahaliccinsa
ya kuma gina fadodi;
Yahuda ya gina katanga a yawancin garuruwansa.
Amma zan aiko da wuta a bisa biranensu
da zai cinye kagaransu.”
Hukunci domin Isra’ila
Kada ku yi farin ciki, ya Isra’ila;
kada ku yi murna kamar waɗansu al’ummai.
Gama kun yi rashin aminci ga Allahnku;
kuna son hakkokin karuwa
a kowace masussuka.
Masussukai da wuraren matsin inabi ba za su ciyar da mutane ba;
sabon ruwan inabi zai kāsa musu.
Ba za su ci gaba da zama a ƙasar Ubangiji ba;
Efraim zai koma Masar
yă kuma ci abinci marar tsarki a Assuriya.
Ba za su zuba hadayun ruwan inabi ga Ubangiji ba,
ba kuwa hadayunsu za su gamshe shi ba.
Irin hadayun nan za su zama musu kamar burodin masu makoki;
duk wanda ya ci su zai ƙazantu.
Wannan abincin zai zama na kansu ne;
ba zai zo cikin haikalin Ubangiji ba.
Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar bukukkuwarku,
a ranakun bikin Ubangiji?
Ko da sun kuɓuta daga hallaka,
Masar za tă tattara su,
Memfis kuma za tă binne su.
Sarƙaƙƙiya za tă mamaye kayan azurfansu,
ƙayayyuwa su tsiro a cikin tentunansu.
Kwanakin hukunci suna zuwa,
kwanakin ba da lissafi suna a kusa.
Bari Isra’ila su san da wannan.
Saboda zunubanku sun yi yawa
ƙiyayyarku kuma ta yi yawa,
har ake ɗauka annabi wawa ne,
mutumin da aka iza kuwa mahaukaci.
Annabi, tare da Allahna,
su ne masu tsaro a bisa Efraim,9.8 Ko kuwa Annabi ne mai tsaro a bisa Efraim, mutanen Allahna
duk da haka tarko na jiransa a dukan hanyoyi,
da kuma ƙiyayya a cikin gidan Allahnsa.
Sun nutse da zurfi cikin lalaci,
kamar a kwanakin Gibeya.
Allah zai tuna da muguntarsu
yă kuma hukunta su saboda zunubansu.
“Sa’ad da na sami Isra’ila,
ya zama kamar samun inabi a hamada;
sa’ad da na ga kakanninku,
ya zama kamar ganin ’ya’yan itace na farko a itacen ɓaure.
Amma sa’ad da suka zo Ba’al-Feyor,
suka keɓe kansu wa gumaka bankunya
sai suka zama abubuwan banƙyama kamar abubuwan da suke ƙauna.
Darajar Efraim za tă yi firiya tă tafi kamar tsuntsu,
ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki.
Ko da sun yi renon ’ya’ya,
zan sa su yi baƙin cikin kowannensu.
Kaitonsu
sa’ad da na juya musu baya!
Na ga Efraim, kamar birnin Taya,
da aka kafa a wuri mai daɗi.
Amma Efraim zai fitar
da ’ya’yansu ga masu yanka.”
Ka ba su, ya Ubangiji
Me za ka ba su?
Ka ba su mahaifar da za su yi ɓarin ciki
da busassun nono.
“Saboda dukan muguntarsu a Gilgal,
na ƙi su a can.
Saboda ayyukansu na zunubi,
zan kore su daga gidana.
Ba zan ƙara ƙaunace su ba;
dukan shugabanninsu ’yan tawaye ne.
An ka da Efraim,
saiwarsu ta bushe,
ba sa ba da amfani.
Ko da sun haifi ’ya’ya
zan kashe waɗanda suka fi ƙauna.”
Allahna zai ƙi su
saboda ba su yi masa biyayya ba;
za su zama masu yawo a cikin al’ummai.
Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa;
ya fitar da ’ya’ya wa kansa.
Yayinda ’ya’yan suka ƙaru,
ya gina ƙarin bagadai;
da ƙasarsa ta wadata,
ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.
Zuciyarsu masu ruɗu ne,
yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu.
Ubangiji zai rushe bagadansu
yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.
Sa’an nan za su ce, “Ba mu da sarki
domin ba mu girmama Ubangiji ba.
Amma ko da ma muna da sarki,
me zai yi mana?”
Sun yi alkawura masu yawa,
suka yi rantsuwar ƙarya
da kuma yarjejjeniyoyi;
saboda haka ƙararraki suka taso
kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona.
Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro
saboda gunki maraƙin Bet-Awen.10.5 Bet-Awen yana nufin gidan mugunta (suna don Betel, wanda yake nufin gidan Allah).
Mutanensa za su yi makokinsa,
haka ma firistocinsa matsafa,
waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa,
don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.
Za a ɗauke shi a kai Assuriya
kamar gandu wa babban sarki.
Efraim zai sha kunya;
Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.
Samariya da sarkinta za su ɓace
kamar kumfa a bisa ruwaye.
Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta
zunubin Isra’ila ne.
Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma
su rufe bagadansu.
Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!”
Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!”
“Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila,
a can kuwa kuka ci gaba.10.9 Ko kuwa a can aka ɗauki matsayi
Yaƙi bai cimma
masu aikata mugunta a Gibeya ba?
Sa’ad da na ga dama, zan hukunta su;
al’ummai za su taru su yi gāba da su
don su daure su saboda zunubansu da suka riɓanya.
Efraim horarriyar karsana ce
mai son sussuka;
saboda haka zan sa karkiya
a kyakkyawan wuyanta.
Zan bi da Efraim,
Dole Yahuda yă yi noma,
dole kuma Yaƙub yă ja garman noma.
Ku shuka wa kanku adalci,
ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa,
ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba;
gama lokaci ne na neman Ubangiji,
sai ya zo
ya zubo adalci a kanku.
Amma kun shuka mugunta,
kuka girbe mugu
kuka ci ’ya’yan ruɗu.
Domin kun dogara da ƙarfinku
da kuma a jarumawanku masu yawa,
hayaniyar yaƙi za tă tashi gāba da mutanenku,
saboda a ragargaza kagaranku,
kamar yadda Shalman ya ragargaza Bet-Arbel a ranar yaƙi,
sa’ad da aka fyaɗa uwaye tare da ’ya’yansu da ƙasa.
Haka zai faru da kai, ya Betel,
domin muguntarka ta yi yawa.
Sa’ad da wannan rana ta zo,
za a hallaka sarkin Isra’ila ƙaƙaf.
Ƙaunar Allah domin Isra’ila
“Sa’ad da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi,
daga Masar kuma na kira ɗana.
Amma yawan kiran da na yi wa Isra’ila
haka nesa da ni da suke ta yi.
Suka miƙa hadaya ga Ba’al
suka kuma ƙona turare ga siffofi.
Ni ne na koya wa Efraim tafiya
ina kama su da hannu;
amma ba su gane
cewa ni ne na warkar da su ba.
Na bishe su da linzamin alheri da tausayi,
da ragamar ƙauna;
Na cire karkiya daga wuyansu
na kuma rusuna na ciyar da su.
“Ba za su koma Masar ba
Assuriya kuma ba za tă yi mulki a bisansu ba
saboda sun ƙi su tuba ba?
Takuba za su yi ta wulgawa a biranensu,
za su hallaka sandunan ƙarafan ƙofofinsu
su kuma kawo ƙarshen ƙulle-ƙullensu.
Mutanena sun ƙudura su juye daga gare ni.
Ko da ma suka yi kira ga Mafi Ɗaukaka,
ta ko ƙaƙa ba zai girmama su ba.
“Yaya zan ba da kai, Efraim?
Yaya zan miƙa ka, Isra’ila?
Yaya zan yi da kai kamar Adma?
Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim?
Zuciyata ta canja a cikina;
dukan tausayina ya huru.
Ba zan zartar da fushina mai zafi ba,
ba kuwa zan juya in ragargaza Efraim ba.
Gama ni Allah ne, ba mutum ba,
Mai Tsarki a cikinku.
Ba zan zo cikin fushi ba.
Za su bi Ubangiji;
zai yi ruri kamar zaki.
Sa’ad da ya yi ruri,
’ya’yansa za su zo da rawan jiki daga yamma.
Za su zo da rawan jiki
kamar tsuntsaye daga Masar,
kamar kurciyoyi daga Assuriya.
Zan zaunar da su a cikin gidajensu,”
in ji Ubangiji.
Zunubin Isra’ila
Mutanen Efraim sun kewaye ni da ƙarairayi,
gidan Isra’ila da ruɗu.
Mutanen Yahuda kuma suna yi wa Allah ƙin ji,
har ma a kan Mai Tsarkin nan mai aminci.
Efraim yana kiwo a kan iska;
yana fafarar iskar gabas dukan yini
yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici.
Ya yi yarjejjeniya da Assuriya
ya kuma aika wa Masar man zaitun.
Ubangiji yana da ƙarar da zai kawo a kan Yahuda;
zai hukunta Yaƙub bisa ga hanyoyinsa
zai sāka masa bisa ga ayyukansa.
A cikin mahaifa ya cafke ɗiɗɗigen ɗan’uwansa;
a matsayin mutum ya yi kokawa da Allah.
Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi;
ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi.
Ya same shi a Betel
ya kuma yi magana da shi a can,
Ubangiji Allah Maɗaukaki,
Ubangiji ne sunansa sananne!
Amma dole ku koma ga Allahnku;
ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya,
ku kuma saurari Allahnku kullum.
Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya;
yana jin daɗin cuta.
Efraim yana fariya yana cewa,
“Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta.
Da dukan wadatata ba za a sami
wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”
“Ni ne Ubangiji Allahnku,
wanda ya fitar da ku daga12.9 Ko kuwa Allah / tun kuna cikin Masar;
zan sa ku sāke zauna a tentuna,
kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku.
Na yi magana da annabawa,
na ba su wahayi da yawa
na kuma ba da misalai ta wurinsu.”
Gileyad mugu ne?
Mutanensa mutanen banza ne!
Suna miƙa bijimai a Gilgal?
Bagadansu za su zama tsibin duwatsu.
A gonar da aka nome.
Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram;12.12 Wato, Arewa maso yamma Mesofotamiya
Isra’ila ya yi bauta don yă sami mata,
domin kuma yă biya, sai da ya yi kiwon tumaki.
Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masar
ta wurin annabi ya lura da shi.
Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi;
shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansa
kuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa.
Fushin Ubangiji a kan Isra’ila
Sa’ad da Efraim ya yi magana, mutane sun yi rawan jiki;
an girmama shi a cikin Isra’ila.
Amma sai ya zama mai laifi na yin wa Ba’al sujada, ya kuwa mutu.
Yanzu sai yin zunubi a kai a kai suke;
suna yin gumaka wa kansu daga azurfansu,
da wayo suna sarrafa siffofi,
dukansu aikin masu aikin hannu ne.
Ana magana waɗannan mutane cewa,
“Suna miƙa hadayar mutum
su kuma sumbaci13.2 Ko kuwa “Mutanen da suke hadaya / sumbaci” gumakan maruƙa.”
Saboda haka za su zama kamar hazon safiya,
kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe,
kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka,
kamar hayaƙin da yake fita daga taga.
“Amma ni ne Ubangiji Allahnku,
wanda ya fitar da ku daga Masar.
Ba za ku yarda da wani Allah ba sai ni,
ba wani Mai Ceto in ban da ni.
Na lura da ku a hamada,
cikin ƙasar mai ƙunar zafi.
Sa’ad da na ciyar da su sun ƙoshi;
sa’ad da suka ƙoshi, sai suka fara taƙama;
sai suka manta da ni.
Saboda haka zan hau kansu kamar zaki,
zan ɓuya a bakin hanya kamar damisa.
Kamar beyar da aka ƙwace mata ’ya’yanta,
zan fāɗa musu in ɓarke su.
Kamar zaki zan cinye su;
kamar naman jeji zan yayyage su.
“An hallaka ku, ya Isra’ila,
domin kun tayar mini, kun tayar wa mai taimakonku.
Ina sarkinku, da zai cece ku?
Ina masu mulkinku cikin dukan garuruwanku,
waɗanda kuka ce,
‘Ba mu sarki da shugabanni’?
Saboda haka cikin fushina na ba ku sarki,
kuma cikin hasalata na ɗauke shi.
An yi ajiyar laifin Efraim,
aka lissafta zunubansa.
Naƙuda ta zo masa kamar a mace mai haihuwa,
amma shi yaro ne marar hikima;
sa’ad da lokaci ya kai,
ba ya zuwa inda mahaifa ta buɗe.
“Zan fanshe su daga ikon kabari;
zan cece su daga mutuwa.
Ina annobanki, ya mutuwa?
Ina hallakarka, ya kabari?
“Ba zan ji tausayi ba,
ko da ma ya ci gaba cikin ’yan’uwansa.
Iskar gabas daga Ubangiji za tă zo,
tana hurawa daga hamada;
maɓulɓularsa za tă kafe
rijiyarsa kuma ta bushe.
Za a kwashi kaya masu daraja
na ɗakin ajiyarsa ganima.
Dole mutanen Samariya su ɗauki laifinsu,
domin sun tayar wa Allahnsu.
Za a kashe su da takobi;
za a fyaɗa ƙananansu da ƙasa,
za a ɓarke matansu masu ciki.”
Tuba don kawo albarka
Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku.
Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku!
Ku ɗauki magana tare da ku
ku komo wurin Ubangiji.
Ku ce masa,
“Ka gafarta mana dukan zunubanmu
ka kuma karɓe mu da alheri,
don mu iya yabe ka da leɓunanmu.14.2 Ko kuwa miƙa leɓunanmu kamar hadayun bijimai
Assuriya ba za su iya cece mu ba;
ba za mu hau dawakan yaƙi ba.
Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’
wa abin da hannuwanmu suka yi ba,
gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.”
“Zan gyara ɓatancinsu
in kuma ƙaunace su a sake,
gama fushina ya juya daga gare su.
Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila
zai yi fure kamar lili.
Kamar al’ul na Lebanon
zai sa saiwarsa zuwa ƙasa;
tohonsa za su yi girma.
Darajarsa za tă zama kamar itacen zaitun,
ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon.
Mutane za su sāke zauna a inuwarsa.
Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi.
Zai yi fure kamar kuringa,
zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.
Efraim zai ce, me kuma zai haɗa ni da gumaka?
Zan amsa masa in kuma lura da shi.
Ni kamar koren itacen fir ne;
amincinka yana fitowa daga gare ni ne.”
Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa.
Hanyoyin Ubangiji daidai ne;
masu adalci sukan yi tafiya a kansu,
amma ’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.