- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Habakkuk
Habakkuk
Habakkuk
Hab
Habakkuk
Saƙon da annabi Habakkuk ya karɓa.
Habakkuk ya nuna damuwa
Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako,
amma ka ƙi ji?
Ina kuka a gare ka saboda zalunci
amma ba ka ce ufam ba.
Me ya sa ka bari ina ta kallon rashin gaskiya?
Me ya sa kake barin abin da ba daidai ba?
Hallaka da tashin hankali suna a gabana;
ga rashin jituwa da faɗa ko’ina.
Saboda haka ba a bin doka,
shari’a kuma ba ta aiki.
Mugaye sun kewaye masu adalci
don a hana gaskiya tă yi aiki.
Amsar Ubangiji
“Ka dubi al’ummai, ka gani,
ka sha mamaki.
Ga shi zan yi wani abu a kwanakinka,
wanda ko ma an faɗa maka
ba za ka gaskata ba.
Zan tā da Babiloniyawa,1.6 Ko kuwa Kaldiyawa
waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri,
waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya
don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.
Suna da bantsoro da firgitarwa;
dokoki da ƙa’idodinsu ne
kawai suka sani.
Dawakansu sun fi damisoshi sauri,
sun fi kyarketan yamma zafin rai.
Mahayansu suna zuwa a guje;
mahayansu daga nesa suka fito.
Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe;
duk sukan zo da nufin tā-da-na-zaune-tsaye.
Ana jin tsoronsu tun ma kafin su iso
suna tattara bayi kamar yashi.
Sukan yi wa sarakuna ba’a
su kuma rena masu mulki.
Sukan yi wa dukan birane masu mafaka dariya;
sukan tara ƙasa su hau, su cinye abokan gābansu da yaƙi.
Sa’an nan su wuce da sauri kamar iska,
mutane ne masu laifi, waɗanda ƙarfinsu shi ne allahnsu.”
Damuwa ta biyu ta Habakkuk
Ya Ubangiji, ba tun fil azal kake ba?
Ya Allahna, Mai Tsarkina, ba za mu mutu ba.
Ya Ubangiji ka sanya su su tabbatar da hukunci;
Ya Dutse, ka naɗa su don su yi hukunci.
Idanunka masu tsarki ne da suka fi gaban duban mugunta;
ba ka amince da abin da ke ba daidai ba.
To, don me ka ƙyale munafukai suna cin karensu ba babbaka?
Me ya sa kake shiru sa’ad da mugaye
suke haɗiye adalai da suka fi su adalci?
Ka mai da maza kamar kifin teku,
kamar halittun tekun da ba su da shugaba.
Mugu abokin gāba yakan kama su duka da ƙugiya,
yă jawo su waje da abin kamun kifinsa,
yă tattara su cikin ragarsa,
ta haka yakan yi murna da farin ciki.
Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa
yă kuma ƙona turare wa ragarsa,
domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi
yă kuma zaɓi irin abincin da yake so.
Zai ci gaba da juye abin kamun kifinsu ke nan,
suna hallaka al’ummai ba tausayi?
Zan tsaya wurin tsarona
in kuma zauna a kan katanga;
zan jira in ga abin da zai ce mini,
da kuma wace amsa zan bayar ga wannan kuka.
Amsar Ubangiji
Sa’an nan Ubangiji ya amsa ya ce,
“Ka rubuta wannan ru’uya
ka bayyana ta a fili a kan alluna
don mai shela2.2 Ko kuwa duk wanda ya karanta yă ruga da ita, yă kai.
Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci;
tana zancen ƙarshe
kuma ba za tă zama ƙarya ba.
Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta;
lalle za tă2.3 Ko kuwa ko da yake ya daɗe, ka jira shi zo, ba za tă makara ba.
“Duba, abokin gāba ya cika da ɗaga kai;
sha’awarsa ba daidai ba ce,
amma mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiyarsa2.4 Ko kuwa amintacce,
ba shakka, ruwan inabi ya yaudare shi;
yana fariya kuma ba ya hutu.
Domin shi mai haɗama ne kamar kabari2.5 Da Ibraniyanci Sheol
kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi;
yakan tattara dukan al’ummai wa kansa
yana kuma kama dukan mutane su zama kamammu.
“Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa,
“ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata
ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace!
Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’
Masu binka bashi2.7 Ko kuwa mai bin bashi ba za su taso maka nan da nan ba?
Ba za su farka su sa ka fargaba ba?
Ta haka ka zama ganima a gare su.
Domin ka washe al’ummai masu yawa,
mutanen da suka rage za su washe ka.
Domin ka zub da jinin mutane;
ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.
“Kaito ga wanda ya gina masarautarsa da ƙazamar riba
don yă kafa sheƙarsa can bisa,
don yă tsere wa zama kango!
Ka ƙulla lalacin mutane masu yawa,
ta haka ka kunyatar da gidanka ka kuma hallaka ranka.
Duwatsun katanga za su yi kuka,
ginshiƙan katako kuma za su amsa.
“Kaiton mutumin da ya gina birni da jinin da ya zubar
ya kuma kafa gari ta wurin mugun aiki!
Ba Ubangiji Maɗaukaki ne ya ƙudura
cewa wahalar mutane ta zama mai kawai don wuta ba,
cewa al’ummai su gajiyar da kansu a banza ba?
Gama duniya za tă cika da sanin ɗaukakar Ubangiji,
yadda ruwaye suka rufe teku.
“Kaito wanda ya ba wa maƙwabtansa abin sha,
yana ta zubawa daga salkan ruwan inabi har sai sun bugu,
don dai yă ga tsiraicinsu.
Za ka cika da kunya a maimakon ɗaukaka.
Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha, a kuma tone asirinka!2.16 Masoretik; Mataccen Teku, Akwila, Bulget da Siriyak (duba kuma Seftuwajin) da kuma tangaɗi
Gama kwaf na hannun daman Ubangiji yana zuwa kewaye da kai,
abin kunya kuma zai rufe darajarka.
Ɓarnar da ka yi wa Lebanon zai komo kanka,
kuma hallakar dabbobin da ka yi zai sa dabbobi su tsorata ka.
Gama ka zub da jinin mutum;
ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.
“Ina amfanin gunki da mutum ne ya sassaƙa?
Ko siffar da take koyar da ƙarya?
Gama wanda ya yi shi yana dogara ne ga halittarsa;
ya yi gumakan da ba sa magana.
Kaito wanda ya ce da katako, ‘Rayu!’
Ko kuwa dutse marar rai, ‘Farka!’
Zai iya bishewa ne?
An dalaye shi da zinariya da azurfa;
ba numfashi a cikinsa.”
Amma Ubangiji yana a cikin haikalinsa mai tsarki;
bari dukan duniya tă yi shiru a gabansa.
Addu’ar Habakkuk.
Addu’ar annabi Habakkuk. A kan shigiyont.3.1 Mai yiwuwa a zahiri, ko kuma kalma ce ta waƙa
Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi;
na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji.
Ka maimaita su a kwanakinmu,
ka sanar da su a lokacinmu;
ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi.
Allah ya zo daga Teman,
Mai Tsarkin nan daga Dutsen Faran. Sela3.3 kalma ce da babu tabbas; mai yiwuwa kalma ce ta waƙa; haka ma a ayoyin 9 da 13.
Ɗaukakarsa ta rufe sammai
yabonsa kuma ya cika duniya.
Darajarsa ta yi kamar fitowar rana;
ƙyalƙyali ya wulga daga hannunsa,
inda ikonsa yake a ɓoye.
Annoba ta sha gabansa;
cuta kuma tana bin bayansa.
Ya tsaya, ya kuwa girgiza duniya;
ya duba, sai ya sa al’ummai suka yi rawan jiki.
Tsofaffin duwatsu sun wargaje
daɗaɗɗun tuddai kuma suka rurrushe.
Hanyoyinsa dawwammamu ne.
Na ga tentin Kushan cikin azaba;
wuraren zaman Midiyan cikin damuwa.
Ka ji haushin koguna ne, ya Ubangiji?
Ko kuwa ka hasala da rafuffuka ne?
Ko ka yi fushi da teku ne
sa’ad da ka hau dawakanka
da kuma kekunan yaƙinka masu nasara?
Ka ja bakanka,
ka nemi a ba ka kibiyoyi masu yawa. Sela
Ka raba duniya da koguna;
duwatsu sun gan ka sai suka ƙame.
Ruwaye masu hauka sun yi ta fantsamawa;
zurfafa suka yi ruri
suka tā da raƙuman ruwansu sama.
Rana da wata suka tsaya cik a sammai
da ganin kibiyoyinka masu wucewa fyu,
da ganin hasken māshinka mai walƙiya.
Cikin hasala ka ratsa duniya
cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe.
Ka fito don ka fanshi mutanenka,
don ceci shafaffenka.
Ka ragargaza shugaban ƙasar mugaye,
ka tuɓe shi daga kai har ƙafa. Sela
Da māshinsa ka soki kansa
sa’ad da jarumawansa suka fito don su tarwatse mu,
suna farin ciki sai ka ce masu shirin cinye
matalautan da suke a ɓoye.
Ka tattake teku da dawakanka,
kana kaɗa manyan ruwaye.
Na ji sai zuciyata ta buga,
leɓunana sun yi rawa da jin murya;
ƙasusuwana suka ruɓe,
ƙafafuna kuma sun yi rawa.
Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i
ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.
Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba,
ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi,
ko da yake zaitun bai ba da amfani ba,
gonaki kuma ba su ba da abinci ba,
ko da yake babu tumaki a garke,
ba kuma shanu a turaku,
duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,
zan yi murna da Allah Mai Cetona.
Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina;
yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa,
yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi.
Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.