- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Farawa
Farawa
Farawa
Far
Farawa
Masomi
A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.
Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.
Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance. Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.
Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.
Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.
Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.
Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.
Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”
Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.
Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.
Miji da mace ya halicce su.
Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”
Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.
Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.
Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu.
Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
Adamu da Hawwa’u
Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su.
Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai, babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar, amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.
To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi. Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.
Akwai wani kogi mai ba da ruwa ga lambun wanda ya gangaro daga Eden, daga nan ya rarrabu, ya zama koguna huɗu. Sunan kogi na fari, Fishon. Shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya. (Zinariyar wannan ƙasa kuwa tana da kyau, akwai kuma kayan ƙanshi da duwatsun da ake kira onis a can ma.) Sunan kogi na biyu, Gihon. Shi ne ya malala kewaye da ƙasar Kush.2.13 Mai yiwuwa kudu maso gabas na Mesofotamiya ne Sunan kogi na uku Tigris. Wannan ne ya malala ya bi ta gefen gabashin Asshur. Kogi na huɗu kuwa shi ne Yuferites.
Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi. Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”
Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”
To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.
Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
Sai mutumin ya ce,
“Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana
nama kuma na namana.
Za a ce da ita ‘mace,’
gama an ciro ta daga namiji.”
Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.
Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.
Fāɗuwar mutum
To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”
Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”
Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”
Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci. Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.
Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu. Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”
Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”
Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”
Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka,
“Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji!
Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya
turɓaya kuma za ka ci
dukan kwanakin rayuwarka.
Zan kuma sa ƙiyayya
tsakaninka da macen,
tsakanin zuriyarka da zuriyarta.
Zai ragargaje kanka,
kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
Sa’an nan ya ce wa macen,
“Zan tsananta naƙudarki ainun,
da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya.
Za ki riƙa yin marmarin mijinki
zai kuwa yi mulki a kanki.”
Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’
“Za a la’anta ƙasa saboda kai.
Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya
za ka kuwa ci ganyayen gona.
Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa,
da yake daga cikinta aka yi ka.
Gama kai turɓaya ne,
kuma ga turɓaya za ka koma.”
Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka.
Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura. Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.” Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi. Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai.
Kayinu da Habila
Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.” Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila.
Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji. Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace.
Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace? Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.”
To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.”4.8 Rubuce-rubucen hannu na Fentatut na Samariyawa, Seftuwajin, Bulget da Siriyak; Rubuce-rubucen hannu na Masoretik ba su da “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.
Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?”
Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?”
Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa. Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka. In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.”
Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina. Ga shi, yau kana kori na daga ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”
Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi. Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod4.16 Nod yana nufin yawo (dubi ayoyi 12 da 14). a gabashin Eden.
Kayinu ya kwana da matarsa, ta kuwa yi ciki, ta haifi Enok. A lokacin Kayinu yana gina birni, sai ya sa wa birnin sunan ɗansa Enok. Aka haifa wa Enok Irad, Irad kuma ya haifi Mehujayel, Mehujayel kuma ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifin Lamek.
Lamek ya auri mata biyu, ana ce da ɗaya Ada, ɗayan kuma Zilla. Ada ta haifi Yabal, shi ne mahaifi waɗanda suke zama a tentuna, suna kuma kiwon dabbobi. Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa. Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama.
Wata rana, Lamek ya ce wa matansa, Ada da Zilla,
“Ku saurara, matan Lamek, ku ji maganata.
Na kashe4.23 Ko kuwa zan kashe wani saboda ya yi mini rauni,
na kashe wani saurayi saboda ya ji mini ciwo.
Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai,
lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.”
Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.” Set ma ya haifi ɗa, ya kuma kira shi Enosh.
A lokaci ne, mutane suka fara kira ga sunan Ubangiji.
Daga Adamu zuwa Nuhu
Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu.
Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah. Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”5.2 Da Ibraniyanci adam
Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set. Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu.
Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh. Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.
Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan. Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.
Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel. Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu.
Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared. Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu.
Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok. Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu.
Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela. Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365. Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek. Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu.
Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa. Ya ba shi suna Nuhu5.29 Nuhu ya yi kama da kalmar Ibraniyancin nan na ta’aziyya. ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.” Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da ’ya’ya maza da mata. Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu.
Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.
Mugunta a duniya
Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu ’ya’ya mata, sai ’ya’yan Allah maza suka ga cewa ’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.”
Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara.
Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci. Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai. Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.” Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
Ga tarihin Nuhu.
Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah. Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali. Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu. Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya. Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires6.14 Babu tabbas game da ma’anar kalman nan a Ibraniyanci., ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje. Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45. Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin.6.16 Ko kuwa Ka bar inda haske zai shiga ta wurin gamawa Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe. Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka. Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai. Za ka shigar da biyu na dukan halittu masu rai, namiji da ta mace a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai. Biyu na kowane irin tsuntsu, kowace irin dabba da kuma kowace irin halitta mai rarrafe a ƙasa, za su zo wurinka domin a bar su da rai. Za ka ɗauki kowane irin abinci wanda za a ci, ka adana don yă zama abincinka da nasu.”
Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. “Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani. Ka ɗauki bakwai na kowace iri tsabtaccen dabba tare da kai, namiji da ta mace, da kuma biyu na kowace dabba marar tsabta, namiji da ta mace, da kuma bakwai na kowane iri tsuntsu, namiji da ta mace, domin a bar kowane irinsu da rai a dukan duniya. Kwana bakwai daga yanzu zan aiko da ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in, zan kuma kawar da kowace halitta mai rai da na yi daga doron ƙasa.”
Nuhu ya aikata duk abin da Ubangiji ya umarce shi.
Nuhu yana da shekaru 106 ne sa’ad da aka yi ambaliya ruwa a duniya. Nuhu da matarsa da ’ya’yansa da matansu, suka shiga jirgi domin su tsira daga ruwa ambaliya. Biyu-biyu daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da tsuntsaye da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu. Bayan kwana bakwai kuwa ambaliya ruwa ta sauko a bisa duniya.
A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe. Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya, yini arba’in da dare arba’in.
A wannan rana Nuhu tare da matarsa da ’ya’yansa maza, Shem, Ham da Yafet da matansu uku suka shiga jirgi. Tare da su kuwa, akwai kowane naman jeji bisa ga irinsa, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinta, da kowane tsuntsun gida da na jeji bisa ga irinsa, da dukan abu mai fiffike. Biyu-biyu na dukan halittu masu numfashi suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi. Dabbobi da kowane abu mai rai da suka shiga ciki, namiji ne da ta mace, yadda Allah ya umarci Nuhu. Sa’an nan Ubangiji ya kulle jirgin daga baya.
Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya. Ruwa ya taso, ya ƙaru ƙwarai a duniya, jirgin kuma ya yi ta yawo a bisa ruwa. Ruwa ya ƙaru ƙwarai a duniya, ya kuma rufe dukan duwatsu masu tsawo a ƙarƙashin sammai. Ruwan ya taso ya rufe duwatsu, zurfin ruwa daga duwatsun zuwa inda jirgin yake ya fi ƙafa ashirin. Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane. Kome a busasshiyar ƙasa da yake numfashi a hancinsa ya mutu. Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi.
Ruwa ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.
Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye. Aka toshe maɓuɓɓugan zurfafa da ƙofofin ambaliyar sammai, ruwan sama kuma ya daina saukowa daga sarari. Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu. A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat. Ruwan ya ci gaba da janyewa har watan goma. A rana ta fari ga watan goma kuwa ƙwanƙolin duwatsun suka bayyana.
Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi, ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya. Sai ya saki kurciya don yă ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa. Amma kurciyar ba tă sami inda za tă sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar daga jirgi. Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya. Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar, amma a wannan ƙaro ba tă komo wurinsa ba.
A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe. A ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, ƙasa ta bushe ƙaƙaf.
Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu, “Fito daga jirgin, kai da matarka da ’ya’yanka maza da matansu. Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.”
Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa, da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu.
Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden. Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.
“Muddin duniya tana nan,
lokacin shuki da na girbi,
lokacin sanyi da na zafi,
lokacin damina da na rani,
dare da rana
ba za su daina ba.”
Alkawarin Allah da Nuhu
Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya. Dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifayen teku, za su riƙa jin tsoronku, suna fargaba. An sa su a cikin hannuwanku. Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome.
“Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, wato, nama wanda jininsa yake cikinsa tukuna. Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.
“Duk wanda ya zub da jinin mutum,
ta hannun mutum za a zub da jininsa;
gama a cikin siffar Allah ne,
Allah ya yi mutum.
Amma ku, ku yi ta haihuwa, ku ƙaru; ku yaɗu a duniya, ku yi yawa a bisanta.”
Sai Allah ya ce wa Nuhu da ’ya’yansa, “Yanzu na kafa alkawarina da ku da zuriyarku a bayanku, da kowace halitta mai rai wadda ta kasance tare da kai; wato, tsuntsaye da dabbobin gida da kuma dukan namun jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin; wato, kowane mai rai na duniya. Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba.”
Allah ya kuma ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na yi tsakanina da ku, da kowace halitta tare da ku; alkawari na dukan zamanai masu zuwa. Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya. Duk sa’ad da na kawo gizagizai a bisa duniya, bakan gizo kuma ya bayyana a ciki gizagizan, zan tuna da alkawari tsakanina da ku da kuma dukan halittu masu rai na kowane iri. Ruwa ba zai sāke yin ambaliyar da za tă hallaka dukan masu rai ba. Duk sa’ad da bakan gizo ya bayyana cikin gizagizan, zan gan shi in kuma tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da dukan halittu masu rai, na kowane iri a duniya.”
Saboda haka Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na kafa tsakanina da dukan masu rai a duniya.”
’Ya’yan Nuhu maza
’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.) Waɗannan su ne ’ya’yan Nuhu maza uku, daga gare su ne kuma duniya za tă cika da mutane.
Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi. Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa. Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje. Amma Shem da Yafet suka ɗauki mayafi, suka shimfiɗa a kafaɗarsu, sa’an nan suka shiga suna tafiya da baya har zuwa inda mahaifinsu yake kwance, suka rufe tsiraicinsa. Suka kau da fuskokinsu domin kada su ga tsiraicin mahaifinsu.
Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi, sai ya ce,
“Kan’ana la’ananne ne,
zai zama bawa mafi ƙanƙanta
ga ’yan’uwansa.”
Ya kuma ce,
“Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem!
Bari Kan’ana yă zama bawan Shem.
Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet;
bari Yafet yă zauna a tentunan Shem,
bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.”
Bayan ambaliyar, Nuhu ya yi shekaru 350. Gaba ɗaya dai, Nuhu ya yi shekara 950, sa’an nan ya mutu.
Tsarin Al’ummai
Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.
Mutanen Yafet
’Ya’yan10.2 ’Ya’ya maza na iya nufin zuriyoyi Ko kuwa magāda ko al’ummai; haka ma a ayoyi 3, 4, 6, 7, 20-23, 29 da 31. Yafet maza su ne,
Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.
’Ya’yan Gomer maza su ne,
Ashkenaz, Rifat, da Togarma.
’Ya’yan maza Yaban su ne,
Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)
Mutanen Ham
’Ya’yan Ham maza su ne,
Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.
’Ya’yan Kush maza su ne,
Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.
’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne,
Sheba da Dedan.
Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya. Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji. Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar. Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.
Mizrayim shi ne mahaifin
Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa, Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
Kan’ana shi ne mahaifin,
Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa, Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa, Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa.
Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
Mutanen Shem
Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.
’Ya’yan Shem maza su ne,
Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
’Ya’yan Aram maza su ne,
Uz, Hul, Geter da Mash.
Arfakshad ne mahaifin10.24 Da Ibraniyanci; Seftuwajin, mahaifin shi ne Kainan, Kainan kuwa shi ne mahaifin Shela.
Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu.
Aka ba wa ɗaya suna Feleg,10.25 Feleg yana nufin rarrabuwa. gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.
Yoktan shi ne mahaifin,
Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera, Hadoram, Uzal, Dikla, Obal, Abimayel, Sheba, Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.
Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.
Hasumiyar Babilon
To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce. Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.
Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka. Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”
Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini. Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba. Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”
Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin. Shi ya sa aka kira birnin Babel,11.9 Wato, Babilon; Babel ya yi kamar Ibraniyanci na rikitar. domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.
Daga Shem zuwa Abram
Wannan shi ne labarin Shem.
Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad. Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela. Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.11.12,13 Da Ibraniyanci; Seftuwajin (dubi kuma Luk 3.35,36 da kuma sharhi a Far 10.24) shekaru 35, ya haifi Kainan. 13 bayan kuma ya haifi Kaina, Arfakshad ya yi shekaru 430 ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata, sa’an nan ya mutu. Sa’ad da Kaina ya yi shekaru ɗari da talatin, ya haifi Shela. Bayan ya haifi Shela, Kaina ya yi shekaru 330 ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata
Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber. Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg. Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu. Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug. Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor. Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera. Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.
Wannan ita ce zuriyar Tera.
Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot. Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa. Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska. Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara.
Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.
Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.
Kiran Abram
Ubangiji ya ce wa Abram, “Tashi ka bar ƙasarka, da mutanenka, da iyalin mahaifinka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.
“Zan mai da kai al’umma mai girma,
zan kuma albarkace ka;
zan sa sunanka yă zama mai girma,
ka kuma zama sanadin albarka.
Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka,
in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka,
dukan mutanen duniya
za su sami albarka ta wurinka.”
Saboda haka Abram ya tashi yadda Ubangiji ya faɗa masa; Lot ma ya tafi tare da shi. Abram yana da shekaru 75, sa’ad da ya tashi daga Haran. Abram ya ɗauki matarsa Saira da Lot ɗan ɗan’uwansa, da dukan mallakar da suka tattara, da kuma mutanen da suka samu a Haran, suka kama hanya zuwa ƙasar Kan’ana.
Abram ya ratsa ƙasar har zuwa wurin babban itace na More a Shekem. A lokacin Kan’aniyawa suna a ƙasar. Ubangiji ya bayyana ga Abram ya ce, “Ga zuriyarka ne zan ba da wannan ƙasa.” Saboda haka Abram ya gina bagade a can ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.
Daga can, ya ci gaba zuwa wajen tuddai a gabashin Betel ya kafa tentinsa, Betel yana yamma, Ai, kuma a gabas. A can ya gina bagade ga Ubangiji ya kuma kira bisa sunan Ubangiji.
Sa’an nan Abram ya tashi ya ci gaba da tafiya zuwa wajen Negeb.
Abram a Masar
To, a lokacin, an yi yunwa a ƙasar, sai Abram ya gangara zuwa Masar don yă zauna a can na ɗan lokaci, domin yunwa ta yi tsanani. Yayinda yana gab da shiga Masar, sai ya ce wa matarsa Saira, “Na sani ke kyakkyawar mace ce. Sa’ad da Masarawa suka ganki, za su ce, ‘Wannan matarsa ce.’ Za su kuwa kashe ni, su bar ki da rai. Saboda haka ki ce ke ’yar’uwata ce, domin ta dalilinki a mutunta ni, a kuma bar ni da rai.”
Sa’ad da Abram ya isa Masar, Masarawa suka ga cewa Saira kyakkyawa mace ce ƙwarai. Sa’ad da fadawan Fir’auna suka gan ta kuwa, sai suka yabe ta wajen Fir’auna, aka kuwa kawo ta cikin fadarsa. Ya mutunta Abram sosai saboda ita, Abram kuwa ya mallaki tumaki da shanu, da jakuna maza da mata, da bayi maza da mata, da kuma raƙuma.
Amma Ubangiji ya wahalar da Fir’auna da gidansa da cututtuka masu zafi saboda Saira, matar Abram. Saboda haka Fir’auna ya kira Abram ya ce, “Me ke nan ka yi mini? Me ya sa ba ka faɗa mini cewa ita matarka ce ba? Don me ka ruɗe ni cewa, ‘Ita ’yar’uwata ce,’ har na ɗauke ta tă zama matata? To, ga matarka. Ɗauke ta ka tafi.” Sa’an nan Fir’auna ya yi wa mutanensa umarni a kan Abram, suka kuwa sallame shi tare da matarsa da kuma dukan abin da yake da shi.
Abram da Lot sun rabu
Saboda haka Abram ya haura daga Masar zuwa Negeb tare da matarsa, da dukan abin da yake da shi tare da Lot. Abram ya azurta ƙwarai da dabbobi, da azurfa, da kuma zinariya.
Daga Negeb, ya ci gaba da tafiyarsa a wurare dabam-dabam har ya kai tsakanin Betel da Ai, a inda dā ya kafa tentinsa na fari da kuma inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.
Lot wanda yake tafiya tare da Abram, shi ma yana da garken shanu da tumaki da kuma tentuna. Wannan ya sa har ƙasar ba tă ishe su yayinda suke zama tare ba, saboda mallakarsu ta yi yawa har ba za su iya zama tare ba. Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne.
Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu ’yan’uwa ne. Ba ga dukan ƙasar tana gabanka ba? Bari mu rabu. In ka yi hagu sai ni in yi dama. In ka yi dama, sai ni in yi hagu.”
Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.) Saboda haka sai Lot ya zaɓar wa kansa dukan kwarin Urdun, ya tashi ya nufi wajen gabas. Haka fa suka rabu da juna. Abram ya zauna a ƙasar Kan’ana, yayinda Lot ya zauna cikin biranen kwari, ya kafa tentunansa kusa da Sodom. Mutanen Sodom kuwa mugaye ne, sun aikata zunubi ƙwarai ga Ubangiji.
Bayan Lot ya rabu da Abram, sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ɗaga idanunka daga inda kake, ka dubi arewa da kudu, gabas da yamma. Dukan ƙasar da kake gani zan ba ka, kai da zuriyarka har abada. Zan sa zuriyarka tă yi yawa kamar ƙurar ƙasa, har in wani yana iya ƙidaya ƙurar, to, za a iya ƙidaya zuriyarka. Tafi, ka ratsa tsawo da fāɗin ƙasar, gama zan ba ka ita.”
Saboda haka Abram ya cire tentunansa, ya zo ya zauna kusa da manyan itatuwan Mamre a Hebron, inda ya gina bagade ga Ubangiji.
Abram ya kuɓutar da Lot
A zamanin Amrafel sarkin Shinar,14.1 Wato, Babilon; haka ma a aya 9 shi da Ariyok sarkin Ellasar, Kedorlayomer sarkin Elam, da kuma Tidal sarkin Goyim suka tafi don su yaƙi Bera sarkin Sodom, Birsha sarkin Gomorra, Shinab sarkin Adma, Shemeber sarkin Zeboyim, da kuma sarkin Bela (wato, Zowar). Dukan waɗannan sarakuna na bayan nan suka haɗa kai a Kwarin Siddim (Teku Gishiri). Shekara goma sha biyu suna bauta wa Kedorlayomer, amma a shekara ta sha uku sai suka yi tawaye.
A shekara ta goma sha huɗu, Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi suka tafi suka cinye Refahiyawa a Ashterot Karnayim, Zuziyawa a Ham, Emawa a Shabe Kiriyatayim, da Horiyawa a ƙasar tudun Seyir har zuwa El Faran kusa da hamada. Sa’an nan suka juya suka tafi En Mishfat (wato, Kadesh), suka cinye dukan ƙasar Amalekawa, da kuma Amoriyawa waɗanda suke zaune a Hazazon Tamar.
Sai sarkin Sodom, sarkin Gomorra, sarkin Adma, sarkin Zeboyim da sarkin Bela (wato, Zowar), suka fita suka ja dāgā a Kwarin Siddim gāba da Kedorlayomer sarkin Elam, Tidal sarkin Goyim, Amrafel sarkin Shinar da Ariyok sarkin Ellasar; sarakuna huɗu gāba da biyar. Kwarin Siddim kuwa ya cika da ramummukan kwalta, sa’ad da sarakunan Sodom da Gomorra suka gudu kuwa, waɗansu mutane suka fāɗa cikin ramummukan kwaltan, sauran kuwa suka gudu zuwa tuddai. Sarakunan nan huɗu suka washe dukan kayayyakin Sodom da Gomorra, da kuma dukan abincinsu, sa’an nan suka tafi. Suka kuma kama Lot ɗan ɗan’uwan Abram, wanda yake zaune a Sodom, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu.
Sai wani wanda ya tsira, ya zo ya faɗa wa Abram mutumin Ibraniyawa. Abram kuwa yana zama kusa da manyan itatuwan Mamre, Mamre mutumin Amoriyawa ne ɗan’uwan Eshkol da Aner, su kuwa abokan Abram ne. Da Abram ya ji cewa an kama danginsa, sai ya tara horarrun mutane 318, da aka haifa a gidansa, ya bi sawun sarakunan da suka tafi da Lot, har Dan. Da dad dare, Abram ya rarraba mutanensa don su fāɗa wa sarakunan nan, ya ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewa da Damaskus. Ya washe su da kuma dukan kayayyakinsu, ya kuma dawo da Lot danginsa da mallakarsa, tare da mata da sauran mutane.
Bayan Abram ya dawo daga cin Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi a yaƙi, sai sarkin Sodom ya fito don yă tarye Abram a Kwarin Shabe (wato, Kwarin Sarki).
Sai Melkizedek sarkin Salem14.18 Wato, Urushalima ya kawo burodi da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Mafi Ɗaukaka, ya albarkaci Abram yana cewa,
“Allah Mafi Ɗaukaka Mahaliccin sama da ƙasa
yă albarkace Abram.
Kuma albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka
wanda ya ba da maƙiyanka a hannunka.”
Sa’an nan Abram ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome.
Sarkin Sodom ya ce wa Abram, “Ka ba ni mutanena da ka ƙwace daga hannun sarakunan nan kawai, ka riƙe kayayyakin don kanka.”
Amma Abram ya ce, wa sarkin Sodom, “Na ɗaga hannu ga Ubangiji Allah Mafi Ɗaukaka, Mahaliccin sama da ƙasa, na riga na rantse cewa ba zan karɓi kome da yake naka ba, ko zare ko maɗaurin takalma, don kada ka ce, ‘Na azurta Abram.’ Ba zan karɓi kome ba, sai dai abin da mutanena suka ci da kuma rabon mutanen da suka tafi tare da ni, ga Aner, Eshkol, da Mamre. Bari su ɗauki rabonsu.”
Alkawarin Allah da Abram
Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa,
“Kada ka ji tsoro, Abram.
Ni ne garkuwarka,
kuma ladanka zai zama mai girma.”
Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?” Abram ya kuma ce, “Ga shi ba ka ba ni ɗa ba, don haka bawan da aka haifa a gidana ne zai zama magājina.”
Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Wannan mutum ba zai zama magājinka ba, ɗa da yake zuwa daga jikinka ne zai zama magājinka.” Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.”
Abram ya gaskata, Ubangiji kuma ya lasafta shi adalci ga Abram.
Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.”
Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, yaya zan san cewa zan mallake ta?”
Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.”
Abram ya kawo waɗannan duka a gaban Allah, ya raba kowannensu a tsakiya, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba. Sai tsuntsaye masu cin nama suka sauko a kan gawawwakin, amma Abram ya kore su.
Yayinda rana tana fāɗuwa, sai Abram ya yi barci mai zurfi, sai wani duhu mai kauri mai kuma bantsoro ya rufe shi.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani tabbatacce cewa shekaru ɗari huɗu, zuriyarka za tă zama baƙi a ƙasar da ba tasu ba, za a mai da su bayi, a kuma wulaƙanta su. Amma zan hukunta al’ummar da suka yi bauta kamar bayi, daga baya kuma za su fita da mallaka mai yawa. Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa. A tsara ta huɗu zuriyarka za tă komo nan, saboda zunubin Amoriyawa bai riga ya cika ba.”
Sa’ad da rana ta fāɗi, aka kuwa yi duhu, sai wata tukunya mai hayaƙi, mai harshen wuta mai ci, ta bayyana, ta kuma wuce tsakanin abubuwan nan da aka tsaga. A wannan rana, Ubangiji ya yi alkawari da Abram ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga kogin Masar zuwa babban kogi, Yuferites ke nan, ƙasar Keniyawa, Kenizziyawa, Kadmoniyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Refahiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Girgashiyawa da kuma Yebusiyawa.”
Hagar da Ishmayel
To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa ’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar, saboda haka sai ta ce wa Abram, “Ubangiji ya hana mini haihuwar ’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.”
Abram kuwa ya yarda da abin da Saira ta faɗa. Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa. Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki.
Sa’ad da Hagar ta gane tana da ciki, sai ta fara rena uwargijiyarta. Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.”
Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta.
Mala’ikan Ubangiji ya sami Hagar kusa da maɓulɓula a jeji, ita ce maɓulɓular da take gefen hanya zuwa Shur. Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?”
Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”
Sai mala’ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki Saira, ki yi mata biyayya.” Mala’ikan ya ƙara da cewa, “Zan ƙara zuriyarki har su yi yawan da ba wanda zai iya lasafta su.”
Mala’ikan Ubangiji ya kuma ce mata,
“Ga shi kina da ciki
za ki kuwa haifi ɗa.
Za ki ba shi suna Ishmayel,16.11 Ishmayel yana nufin Allah yana ji.
gama Ubangiji ya ga wahalarki.
Zai zama mutum mai halin jakin jeji.
Hannunsa zai yi gāba da kowa,
hannun kowa kuma zai yi gāba da shi.
Zai yi zama gāba
ga dukan ’yan’uwansa.”
Sai ta ba wa Ubangiji wanda ya yi magana da ita, wannan suna. “Kai Allah ne wanda yake ganina,” gama ta ce, “Yanzu na ga wanda yake ganina.” Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi16.14 Beyer-Lahai-Royi yana nufin rijiyar Mai Rai wanda yake ganina. tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered.
Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa. Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel.
Alkawarin kaciya
Sa’ad da Abram ya yi shekaru 99, sai Ubangiji ya bayyana a gare shi ya ce, ni “Ni ne Allah Maɗaukaki,17.1 Da Ibraniyanci El-Shaddai ka yi tafiya a gabana ka kuma zama marar abin zargi. Zan tabbatar da alkawarina tsakanina da kai, zan kuma ƙara zuriyarka ta yi yawa.”
Abram ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, Allah kuma ya ce masa, “Gare ni kam, wannan shi ne alkawarina da kai, za ka zama mahaifin al’ummai masu yawa. Ba za a ƙara kiranka Abram17.5 Abram yana nufin uban da aka ɗaukaka. ba; sunanka zai zama Ibrahim,17.5 Ibrahim yana nufin uban mutane da yawa. gama na mai da kai uban al’ummai masu yawa. Zan sa ka azurta sosai, zan yi al’ummai daga cikinka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka, zan kafa alkawarina kamar madawwamin alkawari tsakanina da kai da kuma zuriyarka bayanka har tsararraki masu zuwa, in zama Allahnka da kuma Allahn zuriyarka a bayanka. Dukan ƙasar Kan’ana inda kake baƙo a yanzu, zan ba da ita a matsayin madawwamiyar mallaka gare ka da kuma zuriyarka a bayanka, zan kuma zama Allahnsu.”
Sa’an nan Allah ya ce wa Ibrahim. “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, kai da zuriyarka bayanka, har tsararraki masu zuwa. Wannan shi ne alkawarina da kai da kuma zuriyarka a bayanka, alkawarin da za ka kiyaye ke nan. Kowane namiji a cikinku kuwa za a yi masa kaciya. Za ku yi kaciya, za tă kuma zama alamar alkawari tsakanina da kai. Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan zamananku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba. Ko haifaffe a gidanka ko an sayo da kuɗi, dole a yi musu kaciya. Alkawarina cikin jikinku zai kasance madawwamin alkawari. Kowane namijin da ba a yi masa kaciya a jiki ba, za a fid da shi daga cikin mutanensa; domin ya karya alkawarina.”
Allah ya kuma ce wa Ibrahim, “Game da Saira matarka kuwa, ba za ka ƙara kiranta Saira ba, sunanta zai zama Saratu. Zan sa mata albarka, ban da haka ma, zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za tă kuwa zama mahaifiyar al’ummai; sarakunan mutane za su fito daga gare ta.”
Ibrahim ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, ya yi dariya, ya ce wa kansa, “Za a haifi ɗa wa mutum mai shekaru ɗari? Saratu za tă haifi ɗa tana da shekaru tasa’in?” Ibrahim ya kuma ce wa Allah, “Me zai hana a dai bar Ishmayel kawai yă gāji alkawarin nan da ka yi mini.”
Sai Allah ya ce, “Duk da haka dai, matarka Saratu za tă haifi maka ɗa; za ka kuma kira shi Ishaku.17.19 Ishaku yana nufin ya yi dariya. A kansa zan tabbatar da madawwamin alkawarina, da kuma ga zuriyarsa da za su zo bayansa. Game da Ishmayel kuwa, na ji ka. Tabbatacce zan albarkace shi, zan sa yă azurta, zai kuma ƙaru ƙwarai. Zai zama mahaifin masu mulki goma sha biyu, zan kuma maishe shi babban al’umma! Amma dai zan kafa alkawarina da Ishaku wanda Saratu za tă haifa maka war haka shekara mai zuwa.” Da ya gama magana da Ibrahim, sai Allah ya tashi daga gare shi.
A wannan rana, Ibrahim ya ɗauki ɗansa Ishmayel da dukan waɗanda aka haifa cikin gidansa, da waɗanda aka sayo da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji a cikin gidansa kaciya kamar yadda Allah ya faɗa masa. Ibrahim yana da shekara tasa’in da tara sa’ad da aka yi masa kaciya, Ishmayel ɗansa kuma yana da shekara goma sha uku. Aka yi wa Ibrahim da ɗansa Ishmayel kaciya a rana ɗaya. Aka yi wa kowane namiji a gidan Ibrahim kaciya, da waɗanda aka haifa a gidansa, da waɗanda aka sayo da kuɗi daga baƙo.
Baƙi guda uku
Ubangiji ya bayyana ga Ibrahim kusa da manyan itatuwan Mamre yayinda yake zaune a mashigin tentinsa da tsakar rana. Da Ibrahim ya ɗaga ido, sai ya ga mutum uku suna tsaye kusa da shi. Sa’ad da ya gan su, sai ya tashi nan da nan daga mashigin tentinsa, ya tarye su, ya rusuna har ƙasa.
Ya ce, “Ranka yă daɗe, in na sami tagomashi daga gare ku kada ku wuce bawanku. Bari a kawo ruwa ku wanke ƙafafunku, ku huta a ƙarƙashin wannan itace. Bari in samo muku wani abu ku ci don ku wartsake, sa’an nan ku ci gaba da tafiyarku; da yake kun biyo wurin bawanku.”
Suka ce, “To, sai ka yi abin da ka ce.”
Saboda haka Ibrahim ya ruga zuwa wurin Saratu a cikin tenti ya ce, “Yi sauri, ki shirya mudu uku na gari mai laushi, ki cuɗa shi, ki yi burodi.”
Sa’an nan Ibrahim ya yi gudu zuwa garkensa, ya zaɓi ɗan maraƙi ya ba wa bawansa, bawansa kuma ya yi sauri ya gyara shi. Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.
Sai suka ce masa, “Ina Saratu matarka?”
Ibrahim ya ce, “Tana can cikin tenti.”
Sa’an nan ɗayansu ya ce, “Lalle zan komo wurinka war haka shekara mai zuwa. Saratu matarka kuwa za tă haifi ɗa.”
Saratu kuwa tana a bayansu tana ji daga mashigin tenti. Ibrahim da Saratu dai sun riga sun tsufa sosai. Saratu kuma ta wuce shekarun haihuwa. Saboda haka Saratu ta yi dariya da ta yi tunani a zuci tana cewa, “Bayan ƙarfina ya ƙare, maigidana18.12 Ko kuwa miji kuma ya tsufa, yanzu zan sami wannan jin daɗi?”
Sai Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya har da ta ce, ‘Har zan iya haifi ɗa duk ta tsufata yanzu?’ Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.”
Saratu ta ji tsoro, don haka sai ta yi ƙarya ta ce, “Ban yi dariya ba.”
Ya ce, “A’a, kin yi dariya.”
Ibrahim ya yi roƙo don Sodom
Sai mutanen suka tashi suka nufi Sodom, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya, ya yi bankwana da su. Sai Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin yi? Lalle Ibrahim zai zama al’umma mai girma da kuma mai iko, kuma ta wurinsa dukan al’umman duniya za su sami albarka. Saboda na zaɓe shi don yă umarci ’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai, zan gangara in ga ko abin da suka yi ya yi muni kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”
Sai mutanen suka juya suka nufi wajen Sodom amma Ibrahim ya ci gaba da kasance a gaban Ubangiji.18.22 Rubuce-rubucen Masoretik; rubutacciyar al’ada ta tsohon Ibraniyanci suna da amma Ubangiji ya ci gaba da kasance a gaban Ibrahim ne a nan. Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta? Me zai faru in akwai mutum hamshin masu adalci a cikin birnin? Ashe, za ka hallaka shi, ba za ka cece wurin saboda mutane hamsin nan masu adalcin da suke a cikinsa ba? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?”
Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.”
Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka, in yawan masu adalci sun kāsa hamshin da mutum biyar fa? Za ka hallaka dukan birnin saboda rashin mutum biyar ɗin?”
Ya ce, “In na sami mutum arba’in da biyar a wurin, ba zan hallaka shi ba.”
Ya sāke cewa, “In mutum arba’in kaɗai aka samu a can fa?”
Ya ce, “Saboda mutum arba’in ɗin, ba zan aikata ba.”
Sai ya ce, “Kada Ubangiji ya yi fushi, amma bari in ƙara magana. A ce mutum talatin kaɗai aka samu a can fa?”
Ya ce, “Ba zan aikata ba, in na sami mutum talatin a can.”
Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?”
Ya ce, “Saboda ashirin ɗin, ba zan hallaka shi ba.”
Sa’an nan Ibrahim ya ce, “Kada Ubangiji yă yi fushi, amma bari in ƙara magana sau ɗaya tak. In aka sami mutum goma kaɗai a can fa?”
Ubangiji ya ce, “Saboda goma nan, ba zan hallaka shi ba.”
Sa’ad da Ubangiji ya gama magana da Ibrahim, ya tafi, Ibrahim kuma ya koma gida.
An hallaka Sodom da Gomorra
Mala’ikun nan biyu suka iso Sodom da yamma. Lot kuwa yana zama a hanyar shiga birnin. Da ya gan su, sai ya tashi don yă tarye su, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa. Ya ce, “Ranku yă daɗe, ina roƙonku ku ratsa zuwa gidan bawanku. Ku wanke ƙafafunku, ku kwana, sa’an nan ku kama hanyarku da sassafe.”
Suka ce, “A’a, za mu kwana a dandali.”
Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka tafi tare da shi, suka kuma shiga gidansa. Ya shirya musu abinci, ya gasa burodi marasa yisti, suka ci. Kafin suka shiga barci, sai ga dukan mutane, ƙanana da manya daga kowane ɓangare na birnin Sodom, suka kewaye gidan. Suka kira Lot, suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka a daren nan? Fito mana da su waje domin mu kwana da su.”
Lot ya fita daga cikin gida, ya rufe ƙofar a bayansa. Ya je wurin mutanen ya ce musu, “A’a, abokaina kada ku yi wannan mummunan abu. Duba, ina da ’ya’ya mata biyu waɗanda ba su taɓa sanin namiji ba, bari in kawo muku su ku yi kome da kuke so da su. Amma kada ku taɓa waɗannan mutane, gama su baƙina ne kuma dole in tsare su.”
Sai mutanen birnin suka amsa, “Ba mu wuri! Wannan mutum ya zo nan kamar baƙo, ga shi yanzu yana so yă zama alƙali! Za mu wulaƙanta ka fiye da su.” Suka ci gaba da matsa wa Lot lamba, suka matsa kusa domin su fasa ƙofar.
Amma mutanen da suke ciki suka miƙa hannunsu, suka ja Lot zuwa cikin gida, suka rufe ƙofar. Sai suka bugi mutanen da suke a bakin ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu, suna lalluba inda ƙofar take.
Mutanen nan biyun suka ce wa Lot, “Kana da wani a nan, ko surukai, ko ’ya’ya maza ko mata, ko kuwa wani dai a cikin birni wanda yake naka? Ka fitar da su daga nan, gama za mu hallaka wannan wuri. Kukan da aka yi ga Ubangiji game da mutanen birnin nan ya yi yawa sosai, ya sa har ya aiko mu domin mu hallaka birnin.”
Saboda haka Lot ya tafi ya yi magana da surukansa waɗanda suka yi alkawari za su aure ’ya’yansa mata. Ya ce, “Ku yi sauri ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma surukansa suka ɗauka wasa yake yi.
Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.”
Da yana jan jiki, sai mutanen suka kama hannunsa da hannuwan matarsa da na ’ya’yansa biyu mata, suka kai su bayan birni, gama Ubangiji ya nuna musu jinƙai. Da suka fitar da su, sai ɗaya daga cikin mala’ikun ya ce, “Ku gudu domin ranku; kada ku duba baya, kada kuma ku tsaya ko’ina cikin kwarin! Ku gudu zuwa cikin duwatsu, don kada a hallaka ku!”
Amma Lot ya ce musu, “A’a, ranka yă daɗe, ka yi haƙuri! Bawanku ya riga ya sami tagomashi daga gare ku, kun kuma nuna mini alheri mai yawa. Ba zan iya in gudu zuwa duwatsu ba, wannan masifa za tă same ni, zan kuma mutu. Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.”
Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba. Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa can.” (Domin haka ne ake kira garin Zowar.)19.22 Zowar yana nufin ƙarami.
A lokacin da Lot ya isa Zowar, rana ta hau. Sai Ubangiji ya yi ta zuba kibiritu a bisa Sodom da Gomorra daga sama. Haka ya hallakar da waɗannan birane da kuma kwarinsu gaba ɗaya, haɗe da dukan waɗanda suke zama a biranen, da kuma dukan shuke-shuke da suke cikin ƙasar. Amma matar Lot ta waiwaya baya, ta kuma zama ginshiƙin gishiri.
Da sassafe kashegari, Ibrahim ya tashi ya koma wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji. Ya duba ta wajen Sodom da Gomorra, da wajen dukan filayen ƙasar, sai ya ga hayaƙi baƙin ƙirin yana tashi daga ƙasar kamar hayaƙi daga matoya.
Saboda haka sa’ad da Allah ya hallaka waɗannan biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya kuma fitar da Lot daga masifar da ta hallaka biranen da Lot ya zauna.
Asalin Mowabawa da Ammonawa
Lot da ’ya’yansa biyu mata suka bar Zowar suka kuma zauna a cikin duwatsu, gama ya ji tsoro yă zauna a Zowar. Shi da ’ya’yansa biyu mata suka zauna a ciki wani kogo. Wata rana ’yarsa babba ta ce wa ƙanuwarta, “Mahaifinmu ya tsufa, kuma babu wani mutum kusa a nan da zai yi mana ciki mu haifi ’ya’ya; yadda al’ada take a ko’ina a duniya. Bari mu sa mahaifinmu yă sha ruwan inabi, sa’an nan sai mu kwana da shi, don kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”
A wannan dare, suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi, ’yar farin ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba.
Kashegari, ’yar farin ta ce wa ƙanuwar, “Jiya da dare na kwana da mahaifina. Bari mu sa yă sha ruwan inabi kuma yau da dare, ke ma ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.” Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi, a wannan dare ma, ƙanuwar ta shiga ta kwana da shi. Bai kuwa san sa’ad da ta kwanta ko sa’ad da ta tashi ba.
Ta haka ’ya’yan Lot biyu mata duk suka yi ciki daga mahaifinsu. ’Yar farin ta haifi ɗa, ta kuma ba shi suna Mowab, shi ne mahaifin Mowabawa a yau. ’Yar ƙaramar ma ta haifi ɗa, ta kuwa ba shi suna Ben-Ammi,19.38 Ben-Ammi yana nufin ɗan mutanena. shi ne mahaifin Ammonawa a yau.
Ibrahim da Abimelek
Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi wajajen Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. Ya zauna a Gerar na ɗan lokaci, a can ne Ibrahim ya ce game da matarsa Saratu, “Ita ’yar’uwata ce.” Sai Abimelek sarkin Gerar ya aiko a kawo masa Saratu.
Amma wata rana da dad dare Allah ya zo wa Abimelek a cikin mafarki ya ce masa, “Kai da matacce ɗaya kuke, saboda matar da ka ɗauka. Ita matar aure ce.”
Abimelek dai bai riga ya kusace ta ba tukuna, saboda haka ya ce, “Ya Ubangiji za ka hallaka al’umma marar laifi? Ba shi ne ya ce mini, ‘Ita ’yar’uwata ba ce,’ ita ma ba tă ce, ‘Shi ɗan’uwana ba ne’? Na yi haka da kyakkyawan nufi da hannuwa masu tsabta.”
Sai Allah ya ce masa a cikin mafarki “I, na san ka yi wannan da kyakkyawan nufi, saboda haka ne na kiyaye ka daga yin mini zunubi. Shi ya sa ban bar ka ka taɓa ta ba. Yanzu ka komar da matar mutumin, gama shi annabi ne, zai kuma yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In ba ka komar da ita ba fa, ka sani tabbatacce kai da dukan abin da yake naka za ku mutu.”
Kashegari da sassafe, sai Abimelek ya tara dukan fadawansa, ya faɗa musu duk abin da ya faru, suka ji tsoro ƙwarai da gaske. Sa’an nan Abimelek ya kira Ibrahim ciki ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ta wace hanya ce na yi maka laifi har da ka kawo irin wannan babban laifi a kaina da kuma masarautata? Ka yi mini abubuwan da bai kamata a yi ba.” Abimelek ya kuma ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan?”
Ibrahim ya ce, “Na ce a raina, ‘Tabbatacce babu tsoron Allah a wannan wuri, za su kuwa kashe ni saboda matata.’ Ban da haka, tabbatacce ita ’yar’uwata ce, ’yar mahaifina, ko da yake ba daga uwata ba, ta kuma zama matata. Sa’ad da Allah ya sa na tashi daga gidan mahaifina na ce mata, ‘Wannan shi ne yadda za ki nuna mini ƙaunarki. Duk inda muka tafi, ki ce game da ni, “Shi ɗan’uwana ne.” ’ ”
Sai Abimelek ya kawo awaki da shanu da bayi maza da mata, ya ba wa Ibrahim, ya kuma komar da Saratu matarsa gare shi. Abimelek ya kuma ce, “Ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda kake so.”
Ga Saratu kuwa ya ce, “Ina ba wa ɗan’uwanki shekel dubu na azurfa, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa cewa ba ki da laifi.”
Sai Ibrahim ya yi addu’a ga Allah, Allah kuma ya warkar da Abimelek, da matarsa da bayinsa mata domin su haihu, gama Ubangiji ya rufe kowace mahaifa a gidan Abimelek saboda Saratu, matar Ibrahim.
Haihuwar Ishaku
Ana nan sai Ubangiji ya nuna wa Saratu alheri kamar yadda ya ce, Ubangiji kuma ya yi wa Saratu abin da ya yi alkawari. Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari. Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku. Sa’ad da ɗansa Ishaku ya kai kwana takwas da haihuwa, sai Ibrahim ya yi masa kaciya, kamar yadda Allah ya umarce shi. Ibrahim yana da shekara ɗari, sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.
Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, kuma duk wanda ya ji game da wannan, zai yi dariya tare da ni.” Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.”
An kori Hagar da Ishmayel
Yaron ya yi girma, aka kuma yaye shi, a ranar da aka yaye shi kuwa, Ibrahim ya yi babban biki. Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori, sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori baiwan nan tare da ɗanta, saboda ɗan baiwan nan ba zai taɓa raba gādo da ɗana Ishaku ba.”
Al’amarin ya ɓata wa Ibrahim rai sosai domin zancen ya shafi ɗansa. Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada hankalinka yă tashi game da yaron nan da kuma baiwarka. Ka saurari duk abin da Saratu ta faɗa maka, saboda ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka. Zan ba ɗan baiwan nan al’umma shi ma, domin shi zuriyarka ne.”
Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.
Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace. Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, “Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba.” Da ta zauna nesa da yaron, sai ta21.16 Da Ibraniyanci; Seftuwajin yaron. fara kuka.
Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can. Ki ɗaga yaron ki riƙe shi a hannu, gama zan mai da shi al’umma mai girma.”
Sa’an nan Allah ya buɗe idanunta ta ga wata rijiyar ruwa. Don haka sai ta tafi ta cika salkan da ruwa, ta kuma ba wa yaron ruwa ya sha.
Allah ya kasance da yaron, yayinda yake girma. Ya yi zama a jeji, ya kuma zama maharbi. Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar.
Yarjejjeniya a Beyersheba
A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi. Yanzu ka rantse mini a nan a gaban Allah cewa, ba za ka yaudare ni ko ’ya’yana ko kuma zuriyata ba. Ka nuna mini alheri, kai da ƙasar da kake zama baƙunci kamar yadda na nuna maka.”
Ibrahim ya ce, “Na rantse.”
Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace. Sai Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan ba. Ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba, sai yau.”
Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya. Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke, sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?”
Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.”
Saboda haka aka kira wurin Beyersheba, domin a nan ne su biyun suka yi rantsuwa.
Bayan da aka yi yarjejjeniya a Beyersheba, sai Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka koma ƙasar Filistiyawa. Sai Ibrahim ya shuka itacen tsamiya a Beyersheba, a can kuma ya kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami. Ibrahim kuwa ya zauna a ƙasar Filistiyawa na dogon lokaci.
An gwada Ibrahim
Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!”
Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”
Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.”
Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa. A rana ta uku Ibrahim ya ɗaga ido sai ya ga wurin daga nesa. Ibrahim ya ce wa bayinsa, “Ku tsaya a nan da jakin, ni da yaron kuwa mu haura can. Za mu yi sujada sa’an nan mu komo wurinku.”
Ibrahim ya ɗauki itace saboda hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuwa ya riƙe wuƙa da wutar. Yayinda su biyun suke tafiya, sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?”
Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!”
Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?”
Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya.
Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden. Sa’an nan Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauki wuƙar don yă yanka ɗansa. Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!”
Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”
Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.”
Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa. Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, Ubangiji Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen Ubangiji, za a tanada.”
Mala’ikan Ubangiji ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba, tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu, ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.”
Sa’an nan Ibrahim ya koma wurin bayinsa, suka kuma kama hanya tare zuwa Beyersheba. Ibrahim kuwa ya yi zamansa a Beyersheba.
’Ya’yan Nahor maza
Bayan wani ɗan lokaci, sai aka faɗa wa Ibrahim cewa, “Ga shi, Milka ita ma ta haifa wa Nahor ɗan’uwanka, ’ya’ya maza;
ɗan fari shi ne Uz, ɗan’uwansa kuma Buz,
Kemuwel (shi ne mahaifin Aram),
Kesed, Hazo, Fildash; Yidlaf, da kuma Betuwel.”
Betuwel ya haifi Rebeka.
Milka ta haifa wa Nahor ɗan’uwan Ibrahim waɗannan ’ya’ya maza takwas.
Ban da haka ma, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifa masa ’ya’ya maza,
Teba, Gaham, Tahash da kuma Ma’aka.
Mutuwar Saratu
Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya. Ta rasu a Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar Kan’ana, Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makokin Saratu, yana kuka saboda ita.
Sai Ibrahim ya tashi daga gefen matarsa da ta mutu, ya yi magana da Hittiyawa.23.3 Ko kuwa ’ya’yan Het maza; haka ma a ayoyi 5, 7, 10, 16, 18 da 20 Ya ce, “Ni baƙo ne, kuma baƙo a cikinku. Ku sayar mini da wani wuri yă zama wurin binnewa a nan, domin in binne mataccena.”
Hittiyawa suka ce wa Ibrahim, “Ranka yă daɗe, ka saurare mu. Kai babban yerima ne a cikinmu. Ka binne mataccenka a kabari mafi kyau na kaburburanmu. Babu waninmu da zai hana ka kabarinsa don binne mataccenka.”
Sai Ibrahim ya tashi ya rusuna a gaban mutanen ƙasar, wato, Hittiyawan. Ya ce musu, “In kuna so in binne mataccena, sai ku ji ni, ku roƙi Efron ɗan Zohar a madadina domin yă sayar mini da kogon Makfela, wanda yake nasa, wannan da yake a ƙarshen filinsa. Ku ce masa yă sayar mini a cikakken farashi, yă zama mallakata domin makabarta tsakaninku.”
Efron mutumin Hitti yana zaune a cikin mutanensa, sai ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birni. Ya ce, “A’a, ranka yă daɗe, ka ji ni, na ba ka filin, na kuma ba ka kogon da yake cikinsa. Na ba ka shi a gaban mutanena. Ka binne mataccenka.”
Ibrahim ya sāke rusuna a gaban mutanen ƙasar ya ce wa Efron a kunnuwansu, “Ka ji, in ka yarda. Zan biya farashin filin. Ka karɓa daga gare ni don in iya binne mataccena a can.”
Efron ya ce wa Ibrahim, “Ka saurare ni, ranka yă daɗe; darajan filin ya kai shekel ɗari huɗu na azurfa, amma mene ne wannan a tsakanina da kai? Ka binne mataccenka.”
Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin.
Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin. Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana. Da filin da kuma kogon da yake cikinsa, Hittiyawa suka tabbatar wa Ibrahim a matsayin makabarta.
Ishaku da Rebeka
Yanzu fa Ibrahim ya tsufa, yana da shekaru masu yawa, Ubangiji kuma ya albarkace shi a kowace hanya. Sai Ibrahim ya ce wa babban bawan gidansa, wanda yake lura da duk abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata. Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba. Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin ’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.”
Bawan ya ce masa, “Me zai faru in matar ba tă yarda tă zo tare da ni zuwa wannan ƙasa ba? In komar da ɗanka a ƙasar da ka fito ne ke nan?”
Ibrahim ya ce, “Ka tabbata ba ka komar da ɗana can ba.” Ubangiji Allah na sama, wanda ya fitar da ni daga gidan mahaifina, da kuma ƙasar asalina wanda kuma ya yi magana da ni, ya yi mini alkawari da rantsuwa cewa, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa, zai aika mala’ikansa yă sha gabanka domin ka samo wa ɗana mata daga can. In matar ba tă yarda tă zo tare da kai ba, za a kuɓutar da kai daga wannan rantsuwa. Sai dai kada ka kai ɗana a can.” Saboda haka bawan ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar maigidansa Ibrahim, ya kuma rantse masa game da wannan al’amari.
Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor. Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.
Sai ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ka ba ni nasara yau, ka kuma nuna alheri ga maigidana Ibrahim. Duba, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ’ya’ya matan mutanen gari kuma suna fitowa domin ɗiban ruwa. Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.”
Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim. Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro.
Bawan ya yi sauri ya same ta ya ce, “Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.”
Ta ce, “Ka sha, ranka yă daɗe,” ta yi sauri ta saukar da tulun a hannuwanta, ta kuma ba shi, ya sha.
Bayan ta ba shi ya sha, sai ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka ruwa su ma, har sai sun gama sha.” Sai ta yi sauri ta juye ruwan da yake tulunta cikin kwami, ta koma zuwa rijiyar da gudu don ta ƙara ɗebo ruwa, ta kuma ɗebo isashe saboda dukan raƙumansa. Mutumin bai ce uffam ba, ya dai kalle ta sosai don yă san ko Ubangiji ya ba shi nasara a tafiyarsa ko babu.
Sa’ad da raƙuman suka gama shan ruwa, mutumin ya fitar da zoben hanci na zinariya mai nauyin giram biyar da woroworo biyu na zinariya masu nauyin shekel goma, ya ba ta. Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Ke ’yar wace ce? Ina roƙonki ki faɗa mini, akwai wuri a gidan mahaifinki da za mu kwana?”
Sai ta ce masa, “Ni ’yar Betuwel ce ɗan da Milka ta haifa wa Nahor.” Ta ƙara da cewa, “Muna da isashen ciyawa da abincin dabbobi, da kuma wuri domin ku kwana.”
Sa’an nan mutumin ya rusuna ya yi wa Ubangiji sujada, yana cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna alheri da amincinsa ga maigidana ba. Ni kam, Ubangiji ya bishe ni a tafiyata zuwa gidan ’yan’uwan maigidana.”
Yariyan ta gudu ta faɗa wa mutanen gidan mahaifiyarta game da abubuwan nan. Rebeka fa tana da wani ɗan’uwa mai suna Laban, sai ya yi hanzari ya fita zuwa wurin mutumin a rijiyar. Nan da nan da ya ga zoben hancin da woroworo a hannuwan ’yar’uwansa, ya kuma ji Rebeka ta faɗa abin da mutumin ya ce mata, sai ya fita zuwa wurin mutumin, ya same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar. Sai ya ce, “Zo, ya kai mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”
Don haka mutumin ya tafi gidan, aka kuma saukar da kaya kan raƙuman. Aka kawo wa raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma kawo ruwa dominsa da mutanensa su wanke ƙafafunsu. Sa’an nan aka ajiye abinci a gabansa, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.”
Sai Laban ya ce, “Faɗa mana.”
Saboda haka ya ce, “Ni bawan Ibrahim ne. Ubangiji ya albarkaci maigidana sosai, ya kuma zama mai arziki. Ya ba shi tumaki, shanu, azurfa, zinariya, bayi maza da mata, raƙuma, da kuma jakuna. Saratu matar maigidana ta haifa masa ɗa a tsufanta, ya kuma ba shi duk mallakarsa. Maigidana ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, ‘Kada ka ɗauko wa ɗana mata daga ’ya’ya matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama a ƙasarsu, amma ka tafi wajen gidan mahaifina da kuma dangina, ka ɗauko wa ɗana mata.’
“Sai na ce wa maigidana, ‘A ce matar ba tă yarda tă zo tare da ni ba fa?’
“Maigidana ya ce, ‘Ubangiji wanda yake tare da ni zai aiki mala’ikansa tare da kai, yă kuma sa tafiyarka tă yi nasara, don ka samo wa ɗana mata daga dangina, daga kuma gidan mahaifina. Ta haka za ka kuɓuta daga rantsuwata sa’ad da ka tafi wurin dangina, ko ma sun ƙi su ba ka ita, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’
“Sa’ad da na zo rijiya a yau, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ina roƙonka ka ba ni nasara a tafiyar da na yi. Duba, ina tsaye kusa da wannan rijiya; in wata yarinya ta fito domin tă ɗiba ruwa, wadda in na ce mata, “Ina roƙonki bari in ɗan sha ruwa daga tulunki,” in ta ce, “Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma,” bari tă zama wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’
“Kafin in gama addu’ar, a zuciyata, sai ga Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗarta. Ta gangara zuwa rijiyar ta ɗebo ruwa, na kuma ce mata, ‘Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.’
“Ta yi sauri ta saukar da tulun daga kafaɗarta ta ce, ‘Sha, zan kuma ba wa raƙumanka su ma.’ Sai na sha, ta kuma shayar da raƙumana su ma.
“Na tambaye ta, ‘Ke ’yar wane ne?’
“Ta ce, ‘’Yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’
“Sai na sa mata zobe a hancinta, woroworo kuma a hannuwata, na kuma sunkuya na yi wa Ubangiji sujada. Na yabi Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim wanda ya bi da ni a hanyar da take daidai, don in samo wa ɗan maigidana jikanyar ɗan’uwansa. Yanzu fa in za ku nuna wa maigidana alheri da aminci, ku faɗa mini, in kuma ba haka ba, ku faɗa mini, don in san hanyar da zan juya.”
Laban da Betuwel suka ce, “Wannan daga wurin Ubangiji ne, ba abin da za mu ce I, ko a’a ba. Ga Rebeka, ɗauke ta ku tafi, bari tă zama matar ɗan maigidanka, yadda Ubangiji ya umarta.”
Sa’ad da bawan Ibrahim ya ji abin da suka ce, sai ya rusuna har ƙasa a gaban Ubangiji. Sa’an nan bawan ya fito da kayan ado na zinariya da azurfa da kayayyaki na tufafi ya ba wa Rebeka; ya kuma ba wa ɗan’uwanta da mahaifiyarta kyautai masu tsada. Sa’an nan shi da mutanen da suke tare da shi suka ci, suka sha, suka kuma kwana a can.
Kashegari da safe da suka tashi sai ya ce, “A sallame ni in koma wurin maigidana.”
Amma ɗan’uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Bari yarinyar ta ɗan zauna tare da mu kwana goma ko fiye, sa’an nan ka24.55 Ko kuwa ta ta fi.”
Amma ya ce musu, “Kada ku tsai da ni, tun da Ubangiji ya ba ni nasara a tafiyata. Ku sallame ni domin in tafi wurin maigidana.”
Sa’an nan suka ce, “Bari mu kira yarinyar mu tambaye ta game da zancen.” Saboda haka suka kira Rebeka suka ce mata, “Za ki tafi tare da mutumin nan?”
Sai ta ce, “Zan tafi.”
Saboda haka suka sallame Rebeka, ’yar’uwarsu, duk da uwar goyonta da bawan Ibrahim da mutanensa. Suka kuma albarkaci Rebeka suka ce mata,
“’Yar’uwarmu, bari ki zama mahaifiyar
dubu dubbai,
bari zuriyarki su mallaki
ƙofofin abokan gābansu.”
Sa’an nan Rebeka da bayinta mata suka shirya suka hau raƙumansu suka koma tare da mutumin. Da haka bawan ya ɗauki Rebeka ya tafi.
Ishaku kuwa ya zo daga Beyer-Lahai-Royi, gama yana zama a Negeb. Wata rana da yamma ya fita zuwa fili domin yă yi tunani24.63 Ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba a tabbatar ba., sa’ad da ya ɗaga ido, sai ya ga raƙuma suna zuwa. Rebeka ma ta ɗaga ido sai ta ga Ishaku. Ta sauka daga raƙuminta da sauri, ta ce wa bawan, “Wane ne mutumin can a fili, da yake zuwa yă tarye mu?”
Bawan ya ce, “Maigidana ne.” Saboda haka ta ɗauki mayafinta to rufe kanta.
Sai bawan ya faɗa wa Ishaku duk abin da ya yi. Ishaku ya kawo ta cikin tentin mahaifiyarsa Saratu, ya kuma auri Rebeka. Ta haka ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta; Ishaku kuma ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.
Mutuwar Ibrahim
Ibrahim ya auro wata mace, mai suna Ketura. Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. Yokshan shi ne mahaifin Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Ashur, da mutanen Letush, da kuma mutanen Lewummin. ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce.
Ibrahim ya bar wa Ishaku kome da ya mallaka. Amma yayinda Ibrahim yake da rai, ya ba wa ’ya’yan ƙwarƙwaransa maza kyautai, ya kuma sallame su daga ɗansa Ishaku zuwa ƙasashen gabas.
Duka-duka, Ibrahim ya yi shekara ɗari da saba’in da biyar. Sa’an nan Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu da kyakkyawar tsufa, tsoho da kuma shekaru masu yawa; aka kuma tara shi ga mutanensa. ’Ya’yansa maza kuwa Ishaku da Ishmayel suka binne shi cikin kogon Makfela, kusa da Mamre, a cikin filin Efron ɗan Zohar mutumin Hitti, filin da Ibrahim ya saya daga Hittiyawa. A nan aka binne Ibrahim tare da matarsa Saratu. Bayan rasuwar Ibrahim, Allah ya albarkaci ɗansa Ishaku wanda a lokacin yana zama kusa da Beyer-Lahai-Royi.
’Ya’yan Ishmayel maza
([1 Tarihi 1.28-31])
Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.
Ga jerin sunayen ’ya’yan Ishmayel maza bisa ga haihuwarsu,
Nebayiwot ɗan farin Ishmayel,
Kedar, Adbeyel, Mibsam,
Mishma, Duma, Massa,
Hadad, Tema, Yetur,
Nafish da Kedema.
Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza, waɗanda kuma suke sunayen kabilu goma sha biyu masu mulki bisa ga wuraren zamansu da sansaninsu.
Duka-duka Ishmayel ya yi shekara ɗari da talatin da bakwai; sai ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa. Zuriyarsa sun zauna tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake kusa da gabashin iyakar Masar wajen Asshur. Sun yi zaman rikici da dukan sauran ’yan’uwansu.
Haihuwar Yaƙub da Isuwa
Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim.
Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku yana da shekara arba’in sa’ad da ya auri Rebeka ’yar Betuwel, mutumin Aram, daga Faddan Aram, ’yar’uwar Laban mutumin Aram.
Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki. Jariran suka kama kokawa da juna a cikinta, sai ta ce, “Me ya sa wannan yake faruwa da ni?” Saboda haka ta tafi don ta nemi nufin Ubangiji.
Ubangiji ya ce mata,
“Al’ummai biyu suna a cikin mahaifarki
mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna,
ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi,
babban kuma zai bauta wa ƙaramin.”
Da lokaci ya yi da za tă haihu, sai ga ’yan biyu maza a mahaifarta. Wanda ya fara fita ja ne, dukan jikinsa kuwa kamar riga mai gashi. Don haka aka sa masa suna Isuwa. Bayan wannan, ɗan’uwansa ya fito, da hannunsa yana riƙe da ɗiɗɗigen Isuwa; don haka aka sa masa suna Yaƙub. Ishaku yana da shekara sittin, lokacin da Rebeka ta haife su.
Yaran suka yi girma, Isuwa kuwa ya zama riƙaƙƙen maharbi, mutumin jeji, yayinda Yaƙub, shiru-shiru ne mai son zama a tentuna. Ishaku, mai son ci naman jeji, ya ƙaunaci Isuwa, amma Rebeka ta ƙaunaci Yaƙub.
Wata rana sa’ad da Yaƙub yana dafa fate. Isuwa ya shigo daga jeji, da yunwa sosai. Ya ce wa Yaƙub, “Ina roƙonka, ka ɗan ɗiba mini faten nan! Ina fama da yunwa!” (Shi ya sa aka kira shi Edom.)25.30 Edom yana nufin ja.
Yaƙub ya amsa ya ce, “Ka fara sayar mini da matsayinka na ɗan fari tukuna.”
Isuwa ya ce, “Duba, ina gab da mutuwa, me matsayina na ɗan fari zai yi mini?”
Amma Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini tukuna.” Don haka ya rantse masa, ya sayar da matsayinsa na ɗan fari ga Yaƙub.
Sa’an nan Yaƙub ya ba wa Isuwa burodi da ɗan miyan lansir. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya tashi ya tafi.
Ta haka Isuwa ya yi banza da matsayinsa na ɗan fari.
Ishaku da Abimelek
Aka yi yunwa a ƙasar; ban da yunwar da aka yi da fari a zamanin Ibrahim, sai Ishaku ya tafi wurin Abimelek sarkin Filistiyawa a Gerar. Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ishaku ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar; ka yi zauna a ƙasar da zan faɗa maka. Ka zauna a wannan ƙasa na ɗan lokaci, zan kuwa kasance tare da kai, zan kuma albarkace ka. Gama zan ba da waɗannan ƙasashe gare ka da kuma zuriyarka. Zan kuma cika rantsuwar da na yi wa mahaifinka Ibrahim. Zan sa zuriyarka ta yi yawa kamar taurari a sararin sama zan kuwa ba su dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin ’ya’yanka kuma za a albarkaci dukan al’umman duniya, domin Ibrahim ya yi mini biyayya ya kuma kiyaye umarnaina, ƙa’idodina da kuma dokokina.” Sai Ishaku ya zauna a Gerar.
Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, “’Yar’uwata ce,” gama yana tsoro yă ce, “Ita matata ce.” Ya yi tunani, “Mutane wannan wuri za su kashe ni ta dalili Rebeka, domin kyakkyawa ce.”
Sa’ad da Ishaku ya daɗe a can, sai Abimelek sarkin Filistiyawa ya duba daga taga ya ga Ishaku yana rungumar matarsa Rebeka. Saboda haka Abimelek ya aika Ishaku yă je, sa’an nan ya ce, “Tabbatacce ita matarka ce! Me ya sa ka ce, ‘Ita ’yar’uwata ce?’ ”
Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”
Sa’an nan Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Da a ce wani daga mazanmu ya kwana da matarka, ai, da ka jawo laifi a kanmu.”
Saboda haka Abimelek ya yi umarni ga dukan mutane. “Duk wanda ya fitine wannan mutum ko matarsa, tabbatacce za a kashe shi.”
Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi. Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa. Saboda haka dukan rijiyoyin da bayin mahaifinsa suka haƙa a kwanakin da mahaifinsa Ibrahim yake da rai, Filistiyawa sun toshe su, suka kuma ciccike su da ƙasa.
Sai Abimelek ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu; ka fi ƙarfinmu.”
Saboda haka Ishaku ya fita daga can, ya yi sansani a Kwarin Gerar, ya kuma zauna a can. Ishaku ya sāke tona rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa suka tattoshe bayan mutuwar Ibrahim, ya kuma sa musu sunayen da mahaifinsa ya ba su.
Barorin Ishaku suka haƙa cikin kwarin suka kuwa sami rijiya mai ruwa mai kyau a can. Amma makiyayan Gerar suka yi faɗa da na Ishaku suka ce, “Ruwan namu ne!” Saboda haka Ishaku ya ba wa rijiyar suna Esek,26.20 Esek yana nufin rikici. domin sun yi faɗa da shi. Sai suka haƙa wata rijiya, amma suka yi faɗa a kanta ita ma, saboda haka ya ce da ita Sitna.26.21 Sitna yana nufin adawa. Sai Ishaku ya matsa daga can ya sāke haƙa wata rijiyar, babu wani kuma da yi faɗa a kanta. Sai ya ba ta suna Rehobot,26.22 Rehobot yana nufin ɗaki. yana cewa, “Yanzu Ubangiji ya ba mu wuri, za mu kuwa yi ta haihuwa a ƙasar.”
Daga can ya haura zuwa Beyersheba. A wannan dare Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka Ibrahim. Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan albarkace ka, zan kuma ƙara yawan zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”
Sai Ishaku ya gina bagade a can, ya kuma kira bisa sunan Ubangiji. A can ya kafa tentinsa, a can kuma bayinsa suka haƙa wata rijiya.
Ana cikin haka, sai Abimelek ya zo wurinsa daga Gerar, tare da Ahuzzat mai ba shi shawara da Fikol shugaban mayaƙansa. Ishaku ya tambaye su, “Me ya kawo ku gare ni, da yake kun yi gāba da ni, kuka kuma kore ni?”
Suka amsa, “Mun ga a zahiri cewa Ubangiji yana tare da kai; saboda haka muka ce, ‘Dole rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai.’ Bari mu yi yarjejjeniya da kai cewa ba za ka cuce mu ba, kamar yadda ba mu fitine ka ba, amma muka yi maka kirki, muka kuma sallame ka cikin salama. Yanzu kuwa kai albarkatacce ne na Ubangiji.”
Sai Ishaku ya shirya musu liyafa, suka ci suka kuma sha. Kashegari da sassafe sai mutanen suka yi wa juna rantsuwa. Sa’an nan Ishaku ya sallame su, suka kuwa tafi cikin salama.
A wannan rana bayin Ishaku suka zo suka faɗa masa game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, “Mun sami ruwa!” Sai ya kira ta Shiba,26.33 Shiba yana iya nufin rantsuwa ko kuma bakwai. don haka har wa yau ana kira garin Beyersheba.26.33 Beyersheba yana iya nufin rijiyar rantsuwa ko kuwa rijiyar bakwai.
Sa’ad da Yaƙub ya kai shekaru arba’in da haihuwa, sai ya auri Yudit ’yar Beyeri mutumin Hitti, da kuma Basemat ’yar Elon mutumin Hitti. Su ne suka zama sanadin baƙin ciki ga Ishaku da Rebeka.
Yaƙub ya sami albarkar Ishaku
Sa’ad da Ishaku ya tsufa idanunsa suka raunana har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa ya ce masa, “Ɗana.”
Isuwa kuwa ya amsa, ya ce “Ga ni.”
Ishaku ya ce, “Yanzu na tsufa kuma ban san ranar mutuwata ba. Saboda haka yanzu, ka ɗauki makamanka, kwari da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama. Ka shirya mini irin abinci mai daɗin da nake so, ka kawo mini in ci, domin in sa maka albarka kafin in mutu.”
Ashe, Rebeka tana ji sa’ad da Ishaku ya yi wa ɗansa Isuwa magana. Da Isuwa ya tafi jeji don yă farauto nama yă kawo, sai Rebeka ta ce wa ɗanta Yaƙub, “Ka ji nan, na ji mahaifinka ya ce wa ɗan’uwanka Isuwa, ‘Kawo mini nama ka shirya mini abinci mai daɗi don in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in mutu.’ Saboda haka ɗana, ka saurara da kyau ka kuma yi abin da na faɗa maka. Je garke ka kawo mini awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi wa mahaifinka, kamar yadda dai yake so. Sa’an nan ka kai wa mahaifinka yă ci, domin yă sa maka albarka kafin yă mutu.”
Yaƙub ya ce wa mahaifiyarsa Rebeka, “Amma ɗan’uwana Isuwa mutum ne mai gashi a jiki, ni kuma jikina sumul yake. A ce baba ya tattaɓa ni fa? Zai zama kamar ina ruɗunsa ne, wannan fa zai jawo mini la’ana a maimakon albarka.”
Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, bari la’anar tă fāɗo a kaina. Kai dai yi abin da na faɗa, jeka ka kawo mini su.”
Sai ya tafi ya kamo su, ya kawo wa mahaifiyarsa, ta kuwa shirya abinci mai daɗi, yadda mahaifinsa yake so. Sa’an nan Rebeka ta ɗauki riguna mafi kyau na Isuwa babban ɗanta, waɗanda take da su a gida ta sa wa ƙaramin ɗanta Yaƙub. Sai ta mamanne gashin awakin nan biyu a hannuwansa da bayan wuyarsa wanda ba gashi. Sa’an nan ta ba wa ɗanta Yaƙub abinci mai daɗi da kuma burodin da ta yi.
Shi kuwa ya tafi wurin mahaifinsa ya ce, “Babana.”
Shi kuma ya amsa “I, ɗana, wane ne?”
Yaƙub ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini. Ina roƙonka tashi ka zauna ka ci naman, domin ka sa mini albarkarka.”
Ishaku ya tambayi ɗansa, “Yaya aka yi ka samo shi da sauri haka, ɗana?”
Yaƙub ya amsa ya ce, “Ubangiji Allahnka ne ya ba ni nasara.”
Sai Ishaku ya ce wa Yaƙub, “Zo kusa don in taɓa ka, ɗana, domin in sani ko tabbatacce kai ne ɗana Isuwa ko babu.”
Yaƙub kuwa ya matsa kusa da mahaifinsa Ishaku, wanda ya tattaɓa shi, sa’an nan ya ce, “Muryan nan dai, muryar Yaƙub ce, amma hannuwan, hannuwan Isuwa ne.” Bai gane shi ba, gama hannuwansa suna da gashi kamar na ɗan’uwansa Isuwa, saboda haka ya albarkace shi. Ya tambaya, “Tabbatacce kai ne ɗana Isuwa?”
Ya amsa ya ce “Ni ne.”
Sa’an nan ya ce, “Ɗana, kawo mini naman da ka farauto in ci, domin in sa maka albarka.”
Yaƙub ya kawo masa ya kuwa ci; ya kuma kawo masa ruwan inabi ya kuma sha. Sa’an nan mahaifinsa Ishaku ya ce masa, “Zo nan, ɗana ka sumbace ni.”
Saboda haka ya je gunsa ya sumbace shi. Sa’ad da Ishaku ya ji ƙanshin rigunansa, sai ya sa masa albarka ya ce,
“Aha, ƙanshin ɗana
yana kama da ƙanshin jejin
da Ubangiji ya sa wa albarka ne.
Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa,
yalwar hatsi da sabon ruwan inabi.
Bari al’ummai su bauta maka mutane kuma su rusuna maka.
Ka zama shugaba a kan ’yan’uwanka
bari kuma ’ya’yan mahaifiyarka su rusuna maka.
Bari waɗanda suka la’anta ka, su la’antu;
waɗanda kuma suka sa maka albarka, su sami albarka.”
Bayan Ishaku ya gama sa masa albarka, Yaƙub yana fita daga mahaifinsa ke nan, sai ga ɗan’uwansa Isuwa ya dawo daga farauta. Shi ma ya shirya abinci mai daɗi ya kawo wa mahaifinsa. Sa’an nan ya ce masa, “Babana, tashi ka zauna ka ci daga abin da na farauto, domin ka sa mini albarka.”
Mahaifinsa Ishaku ya tambaye shi, “Wane ne kai?”
Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.”
Ishaku ya yi makyarkyata ƙwarai ya ce, “To, wane ne wannan da ya farauto nama ya kawo mini kafin ka zo, har na ci na kuma sa masa albarka? Tabbatacce zai zama mai albarka!”
Sa’ad da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya fashe da kuka mai zafi kuma da ƙarfi, ya ce wa mahaifinsa, “Ka albarkace ni, ni ma, baba!”
Amma ya ce, “Ɗan’uwanka ya zo da makirci ya karɓi albarkarka.”
Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yaƙub27.36 Yaƙub yana nufin ya kama ɗiɗɗigi, a habaici ya yi ruɗu. ba? Ya yi mini ƙwace sau biyu ke nan; ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi yanzu kuma ya karɓi albarkata.” Sa’an nan ya yi tambaya, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”
Ishaku ya amsa wa Isuwa, “Na mai da shi shugaba a kanka, na sa dukan dangoginsa su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Saboda haka me kuma zan yi maka ɗana?”
Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Ka albarkace ni ni ma, baba!” Sai Isuwa ya ɗaga murya ya yi kuka.
Mahaifinsa Ishaku ya amsa masa ya ce,
“Ga shi, ni’imar ƙasar za tă
nisanci mazauninka.
Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za
tă nisance ka.
Za ka rayu ta wurin takobi
za ka kuwa bauta wa ɗan’uwanka.
Amma sa’ad da ka ɓalle,
za ka kakkarye karkiyarsa
daga wuyanka.”
Yaƙub ya gudu zuwa wurin Laban
Isuwa ya riƙe Yaƙub a zuciya saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Ya ce wa kansa, “Kwanakin mutuwar mahaifina sun yi kusa; sa’an nan zan kashe ɗan’uwana Yaƙub.”
Sa’ad da aka faɗa wa Rebeka abin da babban ɗanta Isuwa ya faɗa, sai ta kira ɗanta Yaƙub ta ce masa, “Ɗan’uwanka Isuwa yana ta’azantar da kansa da tunanin kashe ka. To, fa, ɗana, yi abin da na ce; gudu nan take zuwa wurin ɗan’uwana Laban a Haran. Zauna tare da shi na ɗan lokaci sai ɗan’uwanka ya huce. Sa’ad da ɗan’uwanka ya daina fushi da kai, ya kuma manta da abin da ka yi masa, zan aika don ka dawo daga can. Don me zan rasa ku biyu a rana guda?”
Sa’an nan Rebeka ta ce wa Ishaku, “Ni fa na gaji da matan Hittiyawan nan. In Yaƙub ya auri mata daga cikin matan ƙasan nan, wato, daga matan Hittiyawa irin waɗannan, rayuwata ba za tă daɗa mini kome ba.”
Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace28.1 Ko kuwa gaishe shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana. Tashi nan da nan ka tafi Faddan Aram,28.2 Wato, arewa maso gabashin Mesofotamiya, haka ma a ayoyi 5, 6 da 7 zuwa gidan mahaifin mahaifiyarka Betuwel. Ka ɗauko wa kanka mata a can daga cikin ’ya’ya matan Laban ɗan’uwan mahaifiyarka. Bari Allah Maɗaukaki28.3 Da Ibraniyanci El-Shaddai. yă albarkace ka, yă kuma sa ka yi ta haihuwa ka riɓaɓɓanya har ka zama ƙungiyar jama’o’i. Bari Allah yă ba ka da kuma zuriyarka albarkar da ya ba wa Ibrahim, don ka amshi ƙasar da kake baƙunci, ƙasar da Allah ya ba wa Ibrahim.” Sa’an nan Ishaku ya sallami Yaƙub, ya kuwa tafi Faddan Aram, zuwa wurin Laban ɗan Betuwel mutumin Aram. Laban ne ɗan’uwan Rebeka, wadda take mahaifiyar Yaƙub da Isuwa.
Yanzu Isuwa ya san cewa Ishaku ya albarkaci Yaƙub ya kuma aike shi zuwa Faddan Aram don yă auri mata daga can, ya kuma san cewa sa’ad da ya albarkace shi, ya umarce shi cewa, “Kada ka auro wata mace daga cikin Kan’aniyawa,” ya kuma san cewa Yaƙub ya yi biyayya da mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa, ya kuwa tafi Faddan Aram. Sai Isuwa ya gane cewa matan Kan’aniyawa ba su gamshi mahaifinsa Ishaku ba; saboda haka sai ya tafi wurin Ishmayel ya auri Mahalat, ’yar’uwar Nebayiwot da kuma ’yar Ishmayel ɗan Ibrahim, ban da matan da yake da su.
Mafarkin Yaƙub a Betel
Yaƙub ya bar Beyersheba ya kama hanyar Haran. Sa’ad da ya kai wani wuri, sai ya dakata domin yă kwana, gama rana ta riga ta fāɗi. Ya ɗauki dutse daga cikin duwatsun wurin, ya sa shi ya zama matashin kansa, sa’an nan ya kwanta don yă yi barci. Ya yi mafarki inda ya ga wata matakalar hawa,28.12 Ko tsani. tsaye a ƙasa, kanta ta kai sama, mala’ikun Allah kuwa suna hawa, suna sauka a kanta. A can bisanta28.13 Ko kuwa can kusa da shi Ubangiji ya tsaya, ya kuma ce, “Ni ne Ubangiji Allah na mahaifinka Ibrahim da kuma Allah na Ishaku. Zan ba ka, kai da kuma zuriyarka, ƙasar da kake kwance a kai. Zuriyarka za tă zama kamar ƙurar ƙasa, za ka kuma bazu zuwa yamma da kuma gabas, zuwa arewa da kuma kudu. Dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka da kuma ta wurin ’ya’yanka. Ina tare da kai, zan lura da kai duk inda ka tafi, zan kuma dawo da kai zuwa wannan ƙasa. Ba zan rabu da kai ba sai na cika abin da na yi maka alkawari.”
Sa’ad da Yaƙub ya farka daga barci, sai ya yi tunani ya ce, “Tabbatacce Ubangiji yana a wannan wuri, ban kuwa sani ba.” Ya ji tsoro, ya kuma ce, “Wane irin wuri ne mai banrazana haka! Lalle wannan gidan Allah ne, kuma nan ne ƙofar sama.”
Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa. Ya kira wannan wuri Betel28.19 Betel yana nufin gidan Allah. ko da yake dā ana kiran birnin Luz ne.
Sa’an nan Yaƙub ya yi alkawari cewa, “In Allah zai kasance tare da ni yă kuma lura da ni a wannan tafiya, yă kuma ba ni abinci in ci da tufafi in sa, har in dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubangiji28.20,21 Ko kuwa Da yake Allah… gidan mahaifina, Ubangiji zai zama Allahna kuma28.21,22 Ko kuwa gida, Ubangiji, kuwa zai zama Allahna, sa’an nan. 22 Kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.”
Yaƙub ya isa Faddan Aram
Sa’an nan Yaƙub ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai ƙasar mutanen gabashi. A can ya ga rijiya a jeji da garkuna uku na tumaki kwance kusa da ita, gama a wannan rijiya ce ake shayar da garkuna. Dutsen da ake rufe bakin rijiyar mai girma ne. Sa’ad da dukan garkuna suka taru a can, sai makiyayan su gungurar da dutsen daga bakin rijiyar su shayar da tumaki. Sa’an nan su mai da dutsen a wurinsa a bakin rijiya.
Yaƙub ya tambayi makiyayan ya ce, “’Yan’uwa, ina kuka fito?”
Suka amsa, “Mu daga Haran ne.”
Sai ya ce musu, “Kun san Laban, jikan Nahor?”
Suka amsa, “I, mun san shi.”
Sa’an nan Yaƙub ya tambaye su, “Yana nan lafiya?”
Suka ce, “I, yana lafiya, ga ma ’yarsa Rahila tafe da tumaki.”
Ya ce, “Duba har yanzu da sauran rana da yawa, lokaci bai kai na tara garkuna ba. Ku shayar da tumaki ku mai da su wurin kiwo.”
Suka amsa suka ce, “Ba za mu iya ba, sai dukan garkunan sun taru, aka kuma gungurar da dutsen daga bakin rijiyar. Sa’an nan za mu shayar da tumakin.”
Tun yana cikin magana da su, sai ga Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, gama ita makiyayyiya ce. Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa. Sa’an nan Yaƙub ya sumbaci Rahila, ya kuma ɗaga murya ya yi kuka. Ya riga ya faɗa wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne kuma ɗan Rebeka. Saboda haka ta ruga da gudu ta faɗa wa mahaifinta.
Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan ’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa. Sa’an nan Laban ya ce masa, “Kai nama da jinina ne.”
Yaƙub ya auri Liyatu da Rahila
Bayan Yaƙub ya zauna da shi na wata guda cif, sai Laban ya ce masa, “Don kawai kai dangina ne na kusa, sai kawai ka yi mini aiki a banza? Faɗa mini abin da albashinka zai zama.”
Laban dai yana da ’ya’ya mata biyu; sunan babbar Liyatu, sunan ƙaramar kuwa Rahila. Liyatu tana da raunannun29.17 Ko kuwa mai laulayi idanu, amma Rahila dai tsarinta yana da kyau kuma kyakkyawa ce. Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar ’yarka Rahila.”
Laban ya ce, “Ya fi kyau in ba ka ita, da in ba wani mutum dabam. Zauna tare da ni.” Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar ’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata.
Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.”
Saboda haka Laban ya tara dukan mutanen wurin, ya yi biki. Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki ’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita. Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa ’yarsa tă zama mai hidimarta.
Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?”
Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da ’ya ƙarama aure kafin ’yar fari. Ka gama makon amaryanci na ’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.”
Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa. Laban ya ba da baranyarsa Bilha wa ’yarsa Rahila ta zama mai hidimarta. Yaƙub ya kwana da Rahila ita ma, ya kuwa ƙaunaci Rahila fiye da Liyatu. Ya kuma yi wa Laban aiki na ƙarin waɗansu shekaru bakwai.
’Ya’yan Yaƙub
Sa’ad da Ubangiji ya ga ba a ƙaunar Liyatu, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ta zama bakararriya. Sai Liyatu ta yi ciki ta haifi ɗa. Ta sa masa suna Ruben,29.32 Ruben ya yi kamar Ibraniyanci na, ya ga wahalata; sunan yana nufin duba, ɗa. gama ta ce, “Domin Ubangiji ya ga wahalata. Tabbatacce mijina zai ƙaunace ni yanzu.”
Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon.29.33 Simeyon mai yiwuwa yana nufin wanda yake ji.
Har yanzu ta yi ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Yanzu, a ƙarshe mijina zai manne mini, gama na haifa masa ’ya’ya maza uku.” Saboda haka ta ba shi suna Lawi.29.34 Lawi ya yi kamar, kuma za a iya ɗauka daga Ibraniyanci a matsayin manne.
Ta sāke yin ciki, sa’ad da ta haifi ɗa sai ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta ba shi suna Yahuda.29.35 Yahuda ya yi kamar, kuma za a iya ɗauka daga Ibraniyanci a matsayin Yabo. Sa’an nan ta daina haihuwa.
Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!”
Yaƙub ya fusata da ita ya ce, “Ina a matsayin Allah ne wanda ya hana ke samun ’ya’ya?”
Sa’an nan ta ce, “Ga Bilha, mai baiwata, ka kwana da ita don tă haifa mini ’ya’ya, ta gare ta kuwa ni ma in gina iyali.”
Saboda haka ta ba shi baranyarta Bilha tă zama matarsa. Yaƙub kuwa ya kwana da ita, ta kuwa yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Sa’an nan Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni; ya saurari roƙona ya kuma ba ni ɗa.” Saboda wannan ta ba shi suna Dan.30.6 Dan a nan yana nufin an baratar.
Baranyar Rahila ta sāke yin ciki ta kuma haifi wa Yaƙub ɗa na biyu. Sai Rahila ta ce, “Na yi kokawa sosai da ’yar’uwata, na kuwa yi nasara.” Saboda haka ta kira shi Naftali.30.8 Naftali yana nufin famata.
Sa’ad da Liyatu ta ga cewa ta daina haihuwa, sai ta ɗauki mai hidimarta Zilfa ta ba da ita ga Yaƙub tă zama matarsa. Baranyar Liyatu, Zilfa ta haifa wa Yaƙub ɗa. Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad.30.11 Gad zai iya nufin, sa’a ko kuwa ƙungiya.
Zilfa baranyar Liyatu ta haifa wa Yaƙub ɗa na biyu. Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher.30.13 Asher yana nufin farin ciki.
A lokacin girbin alkama, sai Ruben ya je jeji ya ɗebo manta-uwa ya kawo wa mahaifiyarsa Liyatu. Sai Rahila ta ce wa Liyatu, “Ina roƙonki ki ɗan sam mini manta-uwa ɗanki.”
Amma ta ce mata, “Bai ishe ki ba ne da kika ƙwace mijina? Yanzu kuma kina so ki ƙwace manta-uwa na yarona?”
Sai Rahila ta ce “Shi ke nan, mijina zai iya kwana da ke yau saboda manta-uwa na ɗanki.”
Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare.
Allah ya saurari Liyatu, ta kuwa yi ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na biyar. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya sāka mini saboda na ba da mai hidimata ga mijina.” Saboda haka ta ba shi suna Issakar.30.18 Issakar ya yi kamar Ibraniyanci na lada.
Liyatu ta sāke yin ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na shida. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya ba ni kyauta mai daraja. A wannan lokaci mijina zai darajarta ni, domin na haifa masa ’ya’ya maza shida.” Saboda haka ta ba shi suna Zebulun.30.20 Zebulun mai yiwuwa yana nufin daraja.
Daga baya ta haifi ’ya ta kuwa ba ta suna Dina.
Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta. Sai ta yi ciki ta kuma haifi ɗa ta ce, “Allah ya ɗauke mini kunyata.” Ta ba shi suna Yusuf,30.24 Yusuf mai yiwuwa yana nufin ya ƙara. ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.”
Garkunan Yaƙub sun ƙaru
Bayan Rahila ta haifi Yusuf, sai Yaƙub ya ce wa Laban, “Ka sallame ni don in koma ƙasata. Ba ni matana da ’ya’yana, waɗanda na bauta maka dominsu, zan kuwa tafi. Ka dai san yadda na bauta maka.”
Amma Laban ya ce masa, “In na sami tagomashi daga gare ka, ina roƙonka ka zauna. Na gane ta wurin duba cewa30.27 Ko kuwa mai yiwuwa ya arzuta da kuma Ubangiji ya albarkace ni saboda kai.” Ya ƙara da cewa, “Faɗa albashinka, zan kuwa biya shi.”
Yaƙub ya ce masa, “Ka dai san yadda na yi maka aiki da kuma yadda dabbobinka suka yi yawa a hannuna. Kaɗan da kake da shi kafin zuwata ya ƙaru sosai, kuma Ubangiji ya albarkace ka a duk inda na tafi. Amma yanzu, yaushe zan yi wani abu domin gidana ni ma?”
Sai Laban ya yi tambaya, “Me zan ba ka?”
Yaƙub ya amsa ya ce, “Kada ka ba ni wani abu. Amma in za ka yi mini abu guda ɗaya, zan ci gaba da kiwon garkunanka, ina kuma lura da su. Bari in ratsa cikin dukan garkunanka yau in fid da masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki daga ciki, waɗannan ne za su zama ladana. Gaskiyata kuwa za tă zama mini shaida nan gaba, duk sa’ad da ka bincika a kan albashin da ka biya ni. Duk akuyar da take tawa da ba dabbare-dabbare ko babare-babare, ko ɗan ragon da ba baƙi ba, zai kasance sata na yi.”
Sai Laban ya ce, “Na yarda. Bari yă zama yadda ka faɗa.” A wannan rana ya ware dukan bunsurai da suke dabbare-dabbare da masu zāne-zāne, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare (duka da suke da fari-fari a jikinsu), da dukan baƙaƙen tumaki, ya sa su a hannun ’ya’yansa maza. Sa’an nan ya sa nisan tafiya kwana uku tsakaninsa da Yaƙub, yayinda Yaƙub ya ci gaba da lura da sauran garkunan Laban Yaƙub.
Yaƙub ya samo ɗanyen reshen itatuwan aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bar fararen cikin katakon rassan. Sa’an nan ya zuba ɓararre rassan cikin dukan kwamame na banruwa saboda su kasance a gaban garkunan sa’ad da suka zo shan ruwa. A sa’ad da garkunan suke barbara suka kuma zo shan ruwa, sai su yi barbara a gaban rassan. Sai kuwa su haifi ƙanana masu zāne dabbare-dabbare, ko babare-babare ko masu zāne-zāne. Sai Yaƙub yă ware ƙananan garken dabam, amma sai yă sa sauran su fuskanci dabbobin da suke dabbare-dabbare da kuma baƙaƙe da suke na Laban. Ta haka ya ware garkuna dabam domin kansa bai kuwa haɗa su da dabbobin Laban ba. A duk sa’ad da ƙarfafa dabbobi mata suke barbara, Yaƙub yakan zuba rassan a kwamame a gaban dabbobin saboda su yi barbara kusa da rassan, amma in dabbobin raunana ne, ba ya sa su a can. Saboda haka raunanan dabbobi suka zama na Laban, ƙarfafan kuma suka zama na Yaƙub. Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙe mai arziki, ya kasance mai manya-manyan garkuna, da bayi mata da maza, da raƙuma da kuma jakuna.
Yaƙub ya gudu daga wurin Laban
Yaƙub ya ji cewa ’ya’ya Laban mazan suna cewa, “Yaƙub ya kwashe dukan abin da mahaifinmu yake da shi, ya kuma sami dukan wannan arziki daga abin da yake na mahaifinmu.” Yaƙub kuma ya lura cewa halin Laban gare shi ya canja ba kamar yadda yake a dā ba.
Sai Ubangiji ya ce wa Yaƙub, “Koma ƙasar kakanninka da kuma danginka, zan kuwa kasance tare da kai.”
Saboda haka Yaƙub ya aika a ce wa Rahila da Liyatu su zo jeji inda garkunan suke. Sai ya ce musu, “Na ga cewa halin mahaifinku gare ni ba kamar yadda dā yake ba, amma Allah na mahaifina yana tare da ni. Kun san cewa na yi aiki wa mahaifinku da dukan ƙarfina, duk da haka mahaifinku ya cuce ni ta wurin sauya albashina sau goma. Amma dai, Allah bai yardar masa yă yi mini lahani ba. In ya ce, ‘Dabbare-dabbare ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce, ‘Masu zāne-zāne ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi ƙananan masu zāne-zāne. Ta haka Allah ya kwashe dabbobin mahaifinku ya ba ni.
“A lokacin ɗaukar cikin garken, na taɓa yin mafarki inda na ga bunsuran da suke barbara da garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne. Sai mala’ikan Allah ya ce mini a mafarkin, ‘Yaƙub.’ Sai na amsa na ce, ‘Ga ni.’ Ya ce, ‘Ɗaga idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne, gama na ga dukan abin da Laban yake yin maka. Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa al’amudi mai, da kuma inda ka yi mini alkawari. Yanzu ka bar wannan ƙasa nan take, ka koma ƙasarka ta ainihi.’ ”
Sai Rahila da Liyatu suka amsa suka ce, “Muna da wani rabo a gādon kayan mahaifinmu ne? Ba kamar baƙi ne yake ɗaukarmu ba? Ba sayar da mu kaɗai ya yi ba, har ma ya yi amfani da abin da aka biya saboda mu. Tabbatacce dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga mahaifinmu ya zama namu da ’ya’yanmu. Saboda haka ka yi duk abin da Allah ya faɗa maka.”
Sa’an nan Yaƙub ya sa ’ya’yansa da matansa a kan raƙuma, ya kuma kora dukan dabbobinsa, suka ja gabansa, tare da dukan abubuwan da ya samu a Faddan Aram,31.18 Wato, arewa maso gabashin Mesofotamiya don su tafi wurin mahaifinsa Ishaku a ƙasar Kan’ana.
Sa’ad da Laban ya tafi don askin tumakinsa, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta. Yaƙub kuwa ya ruɗe Laban mutumin Aram da bai sanar da shi zai gudu ba. Saboda haka ya gudu da dukan abin da ya mallaka, ya ƙetare Kogi,31.21 Wato, Yuferites ya nufi yankin tuddan Gileyad.
Laban ya bi bayan Yaƙub
A rana ta uku, sai aka faɗa wa Laban cewa Yaƙub ya gudu. Sai Laban ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi bayan Yaƙub har kwana bakwai, ya kuma same shi a yankin tuddan Gileyad. Sai Allah ya bayyana ga Laban mutumin Aram a mafarki da dare, ya ce masa, “Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu, ko mai kyau ko marar kyau.”
Yaƙub ya riga ya kafa tentinsa a yankin tuddan Gileyad sa’ad da Laban ya same shi. Laban da danginsa suka kafa sansani a can su ma. Sai Laban ya ce wa Yaƙub, “Me ke nan ka yi? Ka ruɗe ni, ka kuma ɗauki ’ya’yana mata kamar kamammun yaƙi. Me ya sa ka gudu a ɓoye ka kuma ruɗe ni? Me ya sa ba ka faɗa mini don in sallame ka da farin ciki da waƙoƙi haɗe da kiɗin ganguna da garayu ba? Ba ka ma bari in sumbaci jikokina da ’ya’yana mata in yi musu bankwana ba. Ka yi wauta. Ina da iko in cuce ka; amma jiya da dare Allahn mahaifinka ya faɗa mini, ‘Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu ko mai kyau ko marar kyau.’ Yanzu ka gudu domin kana marmari komawa gidan mahaifinka. Amma don me ka sace mini gumakana?”
Yaƙub ya amsa wa Laban, “Na ji tsoro ne, domin na yi tsammani za ka ƙwace ’ya’yanka mata daga gare ni ƙarfi da yaji. Amma in ka sami wani wanda yake da gumakanka, ba zai rayu ba. Kai da kanka ka duba a gaban danginmu, ko akwai wani abin da yake naka a nan tare da ni; in ka gani, ka ɗauka.” Yaƙub dai bai san cewa Rahila ta sace gumakan ba.
Saboda haka Laban ya shiga tentin Yaƙub, ya shiga tentin Liyatu da kuma tentuna matan nan biyu bayi, amma bai sami kome ba. Bayan ya fita daga tentin Liyatu, sai ya shiga tentin Rahila. Rahila fa ta kwashe gumakan gidan ta sa su cikin sirdin raƙumi, ta kuma zauna a kansu. Laban ya bincika cikin kowane abu a tentin amma bai sami kome ba.
Sai Rahila ta ce wa mahaifinta, “Kada ka yi fushi, ranka yă daɗe da ban tashi tsaye a gabanka ba; gama ina al’adar mata ne.” Saboda haka ya bincika amma bai sami gumakan gidan ba.
Yaƙub ya fusata, ya kuma yi wa Laban faɗa. Ya tambayi Laban, “Mene ne laifina? Wanda zunubi na yi da kake farautata? Yanzu da ka bincika dukan kayayyakina, me ka samu da yake na gidanka? Kawo shi nan a gaban danginka da kuma dangina, bari su zama alƙali tsakaninmu biyu.
“Na kasance tare da kai shekaru ashirin. Tumakinka da awakinka ba su yi ɓarin ciki ba, ban kuwa ci raguna daga garkunanka ba. Ban kawo dabbobinka da namun jeji suka yayyaga; na kuma ɗauki hasarar ba? Ka nemi in biya dukan abin da aka sace da rana ko da dare. Yanayin da na kasance ke nan, da rana na sha zafin rana da dare kuma na sha sanyi, ga rashin barci. Haka ya kasance shekaru ashirin da na yi a gidanka. Na yi maka aiki shekaru goma sha huɗu domin ’ya’yanka mata biyu, na kuma yi shekaru shida domin garkunanka, ka kuma canja albashina sau goma. Da ba don Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim da kuma Tsoron Ishaku ya kasance tare da ni ba, tabbatacce da ka sallame ni hannu wofi. Amma Allah ya ga wahalata da famar hannuwana, ya kuwa tsawata maka da dare jiya.”
Laban ya amsa wa Yaƙub, “Matan, ’ya’yana ne, ’ya’yansu, ’ya’yana ne, garkunan kuma garkunana ne. Dukan abin da kake gani, nawa ne. Duk da haka me zan yi a rana ta yau ga waɗannan ’ya’yana mata, ko kuma ga ’ya’yan da suka haifa? Zo, bari mu ƙulla yarjejjeniya, da kai da ni, bari kuma ta kasance shaida a tsakaninmu.”
Saboda haka Yaƙub ya ɗauki dutse ya kafa yă zama al’amudi. Ya ce wa danginsa. “Ku tattara waɗansu duwatsu.” Sai suka kwashe duwatsu suka tsiba, suka kuwa ci abinci a can kusa da tsibin. Laban ya sa masa suna Yegar Sahaduta,31.47 Kalman nan ta Yegar Sahaduta a Arameyanci yana nufin tsibi. Yaƙub kuwa ya kira shi Galeyed.31.47 Kalman nan da Ibraniyanci tana nufin tsibi.
Laban ya ce, “Wannan tsibi, shi ne shaida tsakaninka da ni a yau.” Shi ya sa aka kira shi Galeyed. Aka kuma kira shi Mizfa,31.49 Mizfa yana nufin hasumiyar tsaro. domin ya ce, “Ubangiji yă sa ido tsakanin ni da kai sa’ad da muka rabu da juna. Laban ya ce in ka wulaƙanta ’ya’yana mata, ko ka auri waɗansu mata ban da ’ya’yana mata, ko da yake babu wani da yake tare da mu, ka tuna cewa Allah shi ne shaida tsakaninka da ni.”
Laban ya kuma ce wa Yaƙub, “Ga wannan tsibi, ga kuma wannan al’amudin da na kafa tsakaninka da ni. Wannan tsibin shi ne shaida, wannan al’amudi kuma shaida ne, cewa ba zan tsallake wannan tsibi zuwa gefenka don in cuce ka ba, kai kuma ba za ka tsallake wannan tsibi da al’amudi zuwa gefena don ka cuce ni ba. Bari Allah na Ibrahim da Allah na Nahor, Allah na iyayensu, yă zama alƙali tsakaninmu.”
Saboda haka Yaƙub ya yi rantsuwa da sunan Tsoron mahaifinsa Ishaku. Ya miƙa hadaya a can a ƙasar tudu, ya kuma gayyaci danginsa zuwa wurin cin abinci. Bayan suka ci, sai suka kwana a can.
Da sassafe kashegari sai Laban ya sumbaci jikokinsa da ’ya’yansa mata, ya sa musu albarka. Sa’an nan ya yi bankwana da su, ya koma gida.
Yaƙub ya shirya yă sadu da Isuwa
Yaƙub shi ma ya kama hanyarsa, sai mala’ikun Allah suka sadu da shi. Sa’ad da Yaƙub ya gan su sai ya ce, “Wannan sansanin Allah ne!” Saboda haka ya kira wannan wuri Mahanayim.32.2 Mahanayim yana nufin sansanoni biyu.
Sai Yaƙub ya aiki manzanni su sha gabansa zuwa wurin ɗan’uwansa Isuwa a ƙasar Seyir, a ƙauyen Edom. Ya umarce su, “Ga abin da za ku faɗa wa maigidana Isuwa, ‘Bawanka Yaƙub ya ce, na yi zama tare da Laban na kuwa kasance a can sai yanzu. Ina da shanu da jakuna, tumaki da awaki, bayi maza da mata. Yanzu ina aika da wannan saƙo zuwa ga ranka yă daɗe, don in sami tagomashi a idanunka.’ ”
Sa’ad da manzannin suka komo wurin Yaƙub, suka ce, “Mun tafi wurin ɗan’uwanka Isuwa, yanzu kuwa yana zuwa ya sadu da kai, da kuma mutum ɗari huɗu tare da shi.”
Da tsoro mai yawa da kuma damuwa, Yaƙub ya rarraba mutanen da suke tare da shi ƙungiyoyi32.7 Ko kuwa sansanoni; haka ma a aya 10 biyu, haka ma garkunan tumaki da awaki, da garkunan shanu da raƙuma. Ya yi tunani, “In Isuwa ya zo ya fāɗa wa ƙungiya ɗaya,32.8 Ko kuwa sansani sai ƙungiya ɗayan da ta ragu ta tsira.”
Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya Ubangiji kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’ Ban cancanci dukan alheri da amincin da ka nuna wa bawanka ba. Da sanda kaɗai nake sa’ad da na ƙetare wannan Urdun, amma ga shi yanzu na zama ƙungiyoyi biyu. Ka cece ni, ina roƙonka daga hannun ɗan’uwana Isuwa, gama ina tsoro zai zo yă fāɗa mini, yă karkashe mu duka, ’ya’ya da iyaye. Amma ka riga ka faɗa, ‘Tabbatacce zan sa ka yi albarka. Zan kuma sa zuriyarka su zama kamar yashin teku da ba a iya ƙirgawa.’ ”
Ya kwana a can, daga cikin abin da yake tare da shi kuwa, ya zaɓi kyauta domin ɗan’uwansa Isuwa, awaki ɗari biyu da bunsurai ashirin, tumaki ɗari biyu da raguna ashirin, raƙuma mata talatin tare da ƙananansu, shanu arba’in da bijimai goma, jakuna mata ashirin da kuma jakuna maza goma. Ya sa su a ƙarƙashin kulawar bayinsa, kowane kashin garke ya kasance a ware. Ya ce wa bayinsa, “Ku sha gabana, ku kuma ba da rata tsakanin garke da garke.”
Ya umarci wanda yake jagorar ya ce, “Sa’ad da ɗan’uwana Isuwa ya sadu da ku ya kuma yi tambaya, ‘Ku na wane ne, ina za ku, kuma wane ne mai dukan dabbobin nan da suke gabanku?’ Sai ku ce, ‘Na bawanka Yaƙub ne. Kyauta ce wa maigidana Isuwa, yana kuma tafe a bayanmu.’ ”
Yaƙub ya kuma umarci na biyu da na uku da kuma dukan waɗansu da suka bi garkunan, “Sai ku faɗa irin abu guda ga Isuwa sa’ad da kuka sadu da shi. Ku kuma tabbata kun ce, ‘Bawanka Yaƙub yana tafe a bayanmu.’ ” Gama Yaƙub ya yi tunani cewa, “Zan kwantar da ran Isuwa da waɗannan kyautai, kafin mu sadu fuska da fuska, wataƙila yă karɓe shi.” Saboda haka kyautai Yaƙub suka sha gabansa, amma shi kansa ya kwana a sansani.
Yaƙub ya yi kokawa da Allah
A wannan dare Yaƙub ya tashi ya ɗauki matansa biyu, da matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansa goma sha ɗaya ya haye rafin Yabbok. Bayan ya sa suka haye rafin, haka ma ya tura dukan mallakarsa zuwa hayen. Saboda haka sai aka bar Yaƙub shi kaɗai. Sai ga wani mutum ya zo ya yi kokawa da shi har wayewar gari. Da mutumin ya ga cewa bai fi ƙarfin Yaƙub ba, sai ya bugi kwarin ƙashin cinyar Yaƙub, sai gaɓar ƙashin cinyarsa ya goce, a sa’ad da yake kokawa da mutumin. Sa’an nan mutumin ya ce, “Bar ni in tafi, gama gari ya waye.”
Amma Yaƙub ya amsa ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”
Mutumin ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?”
Yaƙub ya amsa ya ce, “Yaƙub.”
Sai mutumin ya ce, “Sunanka ba zai ƙara zama Yaƙub ba, amma Isra’ila,32.28 Isra’ila yana nufin ya yi kokawa da Allah. gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”
Yaƙub ya ce, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.”
Amma mutumin ya amsa ya ce, “Me ya sa kake tambayata sunana?” Sa’an nan ya albarkace shi.
Saboda haka Yaƙub ya kira wurin Feniyel,32.30 Feniyel yana nufin fuskar Allah. yana cewa, “Domin na ga Allah fuska da fuska, duk da haka aka bar ni da rai.”
Rana ta yi sama a sa’ad da ya wuce Fenuwel yana kuma ɗingishi saboda ƙashin cinyarsa. Wannan ya sa har wa yau Isra’ilawa ba sa cin jijiyar ƙashin cinya wadda take a kwarin ƙashin cinya, domin an taɓa kwarin ƙashin cinyar Yaƙub kusa da jijiyar.
Yaƙub ya sadu da Isuwa
Yaƙub ya ɗaga ido ke nan, sai ga Isuwa yana zuwa tare da mutanensa ɗari huɗu; saboda haka sai ya rarraba ’ya’yan wa Liyatu, Rahila da kuma matan nan biyu masu hidima. Ya sa matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansu a gaba, Liyatu da ’ya’yanta biye, sa’an nan Rahila da Yusuf a baya. Shi kansa ya sha gabansu, ya rusuna har ƙasa sau bakwai, kafin ya kai kusa da inda ɗan’uwansa Isuwa yake.
Amma Isuwa ya ruga a guje ya sadu da Yaƙub ya rungume shi; ya faɗa a wuyansa ya sumbace shi. Suka kuma yi kuka. Sa’an nan Isuwa ya ɗaga ido ya ga mata da ’ya’ya. Ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan tare da kai?”
Yaƙub ya amsa, “Su ne ’ya’yan da Allah cikin alheri ya ba bawanka.”
Sai matan nan biyu masu hidima da ’ya’yansu suka matso kusa suka durƙusa. Biye da su, Liyatu da ’ya’yanta suka zo suka rusuna. A ƙarshe duka, sai Yusuf da Rahila suka zo, su ma suka rusuna.
Isuwa ya yi tambaya, “Me kake nufi da dukan abubuwan nan da na sadu da su ana korarsu?”
Sai Yaƙub ya ce, “Don in sami tagomashi a idanunka ne, ranka yă daɗe.”
Amma Isuwa ya ce, “Na riga na sami abin da ya ishe ni, ɗan’uwana. Riƙe abin da kake da shi don kanka.”
Sai Yaƙub ya ce, “A’a, ina roƙonka, in na sami tagomashi a idanunka, sai ka karɓi wannan kyautai daga gare ni. Gama ganin fuskarka kamar ganin fuskar Allah ne, yanzu da ka karɓe ni da farin ciki. Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa.
Sa’an nan Isuwa ya ce, “Bari mu tafi, zan yi maka rakiya.”
Amma Yaƙub ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ka san cewa ’ya’yan ƙanana ne, dole in lura da tumaki da shanun da suke shayar da jariransu. In aka kore su da gaggawa a rana guda kaɗai, dukan dabbobin za su mutu. Saboda haka bari ranka yă daɗe yă sha gaban bawansa, ni kuma in tafi a hankali bisa ga saurin abin da ake kora a gabana da kuma saurin ’ya’yan, sai na iso wurinka ranka yă daɗe, a Seyir.”
Sai Isuwa ya ce, “To, bari in bar waɗansu mutanena tare da kai.”
Yaƙub ya ce, “Amma me ya sa za ka yi haka? Bari dai in sami tagomashi a idanunka ranka yă daɗe.”
Saboda haka a wannan rana Isuwa ya kama hanyar komawa zuwa Seyir. Yaƙub kuwa, ya tafi Sukkot, inda ya gina wuri domin kansa, ya kuma yi bukkoki domin dabbobinsa. Shi ya sa aka kira wurin Sukkot.33.17 Sukkot yana nufin bukkoki.
Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram,33.18 Wato, arewa maso yammancin Mesofotamiya ya iso lafiya a birnin33.18 Ko kuwa isa a Salem, wani Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni. Ya sayi fili daga ’ya’yan Hamor maza, mahaifin Shekem inda ya kafa tentinsa, a bakin azurfa33.19 Da Ibraniyanci Kesita ɗari; Kesita shi ne ma’aunin kuɗi na nauyi da kuma darajar abin da ba a sani ba. ɗari. A can ya kafa bagade ya kuma kira shi El Elohe Isra’ila.33.20 El Elohe Isra’ila yana nufin Allah, Allahn Isra’ila ko kuwa Maɗaukaki ne Allah na Isra’ila.
Dina da mutanen Shekem
To, Dina, ’yar da Liyatu ta haifa wa Yaƙub, ta je ta ziyarci matan ƙasar. Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta. Zuciyarsa kuwa ta damu da son Dina ’yar Yaƙub, ya kuwa ƙaunaci yarinyar, ya yi mata magana a hankali. Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka auro mini wannan yarinya ta zama matata.”
Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa an ɓata ’yarsa Dina, sai ya yi shiru game da batun sai ’ya’yansa maza sun dawo gida, gama ’ya’yansa suna a jeji tare da dabbobinsa suna kiwo.
Sai Hamor mahaifin Shekem ya je don yă yi magana da Yaƙub. Da ’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da ’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba.
Amma Hamor ya ce musu, “Ɗana Shekem ya sa zuciyarsa a kan ’yarku. Ina roƙonku ku ba shi ita yă aura. Ku yi auratayya da mu; ku aurar mana da ’ya’yanku mata, ku kuma ku auro ’ya’yanmu mata wa kanku. Za ku iya zauna a cikinmu, ƙasar tana nan a buɗe dominku. Ku yi zama a cikinta, ku yi sana’a,34.10 Ko kuwa ku yi ma’amala a sauƙaƙe; haka ma a aya 21 ku kuma sami dukiya.”
Sai Shekem ya ce wa mahaifin Dina da kuma ’yan’uwanta. “Bari in sami tagomashi a idanunku, zan kuwa ba ku duk abin da kuka tambaya. Ku faɗa mini nawa ne dukiyar aure da kuma sadakin da zan kawo bisa ga yadda kuke so, zan kuwa biya duk abin da kuka ce. Ku dai bar ni in aure yarinyar ta zama matata.”
Domin an ɓata ’yar’uwansu Dina, sai ’ya’yan Yaƙub maza suka amsa a ha’ince yayinda suke wa Shekem da mahaifinsa Hamor magana. Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, ba za mu iya ba da ’yar’uwarmu ga mutumin da ba shi da kaciya ba. Wannan zai zama abin kunya ne a gare mu. Za mu yarda da wannan kaɗai ta wannan sharaɗi, cewa za ku zama kamar mu ta wurin yin wa dukan ’ya’yanku maza kaciya. Sa’an nan za mu ba da ’ya’yanmu mata aure gare ku, mu kuma mu aure ’ya’yanku mata wa kanmu. Za mu zauna a cikinku mu kuma zama mutane ɗaya da ku. Amma in ba za ku yarda a yi muku kaciya ba, za mu ɗauki ’yar’uwanmu34.17 Da Ibraniyanci ’ya. mu tafi.”
Sharuɗansu sun gamshi Hamor da ɗansa, Shekem. Saurayin wanda aka fi girmamawa a cikin dukan gidan mahaifinsa, bai ɓata lokaci a yin abin da suka ce ba, domin ya ji daɗin ’yar Yaƙub. Saboda haka Hamor da ɗansa Shekem suka tafi ƙofar birninsu don su yi magana da mutanen garinsu. Suka ce, “Waɗannan mutane ba su da damuwa, bari su zauna a cikin ƙasarmu, su kuma yi sana’a a ciki; ƙasar tana da isashen fili dominsu. Za mu iya auro ’ya’yansu mata, su kuma su auri namu. Amma mutanen za su yarda su zauna tare da mu kamar mutane ɗaya kawai bisa wannan sharaɗi, cewa a yi wa mazanmu kaciya, kamar yadda su kansu suke. Ashe, shanunsu, dukiyarsu da dukan sauran dabbobinsu, ba za su zama namu ba? Saboda haka mu yarda, za su kuwa zauna a cikinmu.”
Dukan mazan da suka fito ƙofar birnin suka yarda da Hamor da kuma ɗansa Shekem, aka kuwa yi wa kowane namiji a birnin kaciya.
Bayan kwana uku, yayinda dukansu suna cikin zafi mikin kaciya, sai biyu daga cikin ’ya’yan Yaƙub maza, Simeyon da Lawi, ’yan’uwan Dina, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka kashe kowane namiji. Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dina daga gidan Shekem suka tafi. Sa’an nan ’ya’yan Yaƙub maza suka bi kan gawawwakin, suka washe arzikin birni34.27 Ko kuwa domin saboda an ɓata ’yar’uwarsu. Suka kwashe garkunansu na shanu da jakuna, da kuma kome na mutanen a birnin da kuma cikin gonaki. Suka kwashe dukan dukiyarsu da dukan matansu da ’ya’yansu, suka kwashe kome da yake cikin gidaje.
Sai Yaƙub ya ce wa Simeyon da Lawi, “Kun jawo mini wahala ta wurin sa in zama abin ƙi ga Kan’aniyawa da Ferizziyawa, mazaunan wannan ƙasa. Mu kima ne, in kuwa suka haɗa kai gāba da ni, suka fāɗa mini, za su hallaka ni da gidana.”
Amma ’ya’yansa suka amsa, “To34.31 Ko kuwa wato, ya dace ke nan da ya yi da ’yar’uwarmu kamar karuwa?”
Yaƙub ya koma zuwa Betel
Sa’an nan Allah ya ce wa Yaƙub, “Haura zuwa Betel ka yi zama a can, ka kuma gina bagade a can wa Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake gudu daga ɗan’uwanka Isuwa.”
Saboda haka Yaƙub ya ce wa gidansa da kuma dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku zubar da baƙin allolin da kuke da su, ku tsarkake kanku, ku kuma canja tufafinku. Sa’an nan ku zo, mu haura zuwa Betel, inda zan gina bagade wa Allah wanda ya amsa mini a ranar wahalata, wanda kuma ya kasance tare da ni a dukan inda na tafi.” Saboda haka suka ba Yaƙub dukan baƙin allolin da suke da su, da zoban da suke kunnuwansu, sai Yaƙub ya binne su a ƙarƙashin itacen oak a Shekem. Sa’an nan suka kama hanya, tsoron Allah kuwa ya kama dukan garuruwan da suke kewayensu har babu wanda ya iya bin su.
Yaƙub da dukan mutanen da suke tare da shi suka zo Luz (wato, Betel) a ƙasar Kan’ana. A can ya gina bagade, ya kuma kira wurin El Betel,35.7 El Betel yana nufin Allah na Betel. gama a can ne Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake gudu daga ɗan’uwansa.
To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut.35.8 Allon yana nufin itacen oak na kuka.
Bayan Yaƙub ya komo daga Faddan Aram,35.9 Wato, arewa maso yammancin Mesofotamiya, haka ma a aya 26 sai Allah ya bayyana gare shi, ya kuma albarkace shi. Allah ya ce masa, “Sunanka Yaƙub35.10 Yaƙub yana nufin ya kama ɗiɗɗige, a habaici dai, ya ruɗi. ne, amma ba za a ƙara kira ka Yaƙub ba; sunanka zai zama Isra’ila.”35.10 Isra’ila yana nufin kokawa da Allah. Saboda haka ya ba shi suna Isra’ila.
Sai Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki35.11 Da Ibraniyanci El-Shaddai, ka yi ta haihuwa, ka kuma riɓaɓɓanya. Al’umma da tarin al’ummai za su fito daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga jikinka. Ƙasar da na ba wa Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba ka, zan kuma ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka.” Sa’an nan Allah ya tashi sama daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi.
Yaƙub kuwa ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi magana da shi, ya zuba hadaya ta sha a kansa; ya kuma zuba mai a kansa. Yaƙub ya kira inda Allah ya yi magana da shi, Betel.35.15 Betel yana nufin gidan Allah.
Mutuwar Rahila da Ishaku
Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai. Sa’ad da take cikin zafin haihuwa, sai macen da ta karɓi haihuwar ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.” Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni.35.18 Ben-Oni yana nufin ɗa na wahalata. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin.35.18 Benyamin yana nufin ɗa na hannun damana.
Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem). Yaƙub ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.
Isra’ila ya yi gaba, ya kafa tentinsa gaba da Migdal Eder. Yayinda Isra’ila yana zama a wancan yanki, Ruben ya shiga ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya ji labari.
Yaƙub ya haifi ’ya’ya maza goma sha biyu.
’Ya’yan Liyatu maza,
Ruben shi ne ɗan fari na Yaƙub.
Sauran su ne, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar da Zebulun.
’Ya’yan Rahila maza su ne,
Yusuf da Benyamin.
’Ya’yan Bilha maza, mai hidimar Rahila su ne,
Dan da Naftali.
’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne,
Gad da Asher.
Waɗannan su ne ’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram.
Yaƙub ya dawo gida wurin mahaifinsa Ishaku a Mamre, kusa da Kiriyat Arba (wato, Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna. Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin, sa’an nan ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuwa mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa da kyakkyawan tsufa da kuma cikakken shekaru. ’Ya’yansa maza, Isuwa da Yaƙub suka binne shi.
Zuriyar Isuwa
Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).
Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye ya kuma auri Basemat ’yar Ishmayel wadda take ’yar’uwar Nebayiwot.
Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel. Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.
Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub. Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu. Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.
Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.
Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isuwa maza,
Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.
’Ya’yan Elifaz maza su ne,
Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz. Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.
’Ya’yan Reyuwel maza su ne,
Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
’Ya’yan Oholibama maza ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne,
Yewush, Yalam da Kora.
Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa,
’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa,
Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz, Kora,36.16 Masoretik, Fentatut na Samariya (dubi kuma Far 36.11 da 2Tar 1.3-6) ba su da Kora. Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.
’Ya’yan Reyuwel maza,
Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa,
Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama ’yar Ana matar Isuwa.
Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.
Waɗannan su ne ’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin,
Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
’Ya’yan Lotan maza su ne,
Hori da Homam.36.22 Da Ibraniyanci Hemam, wani suna na Homam (dubi 1Tar 1.39) Timna ’yar’uwar Lotan ce.
’Ya’yan Shobal maza su ne,
Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
’Ya’yan Zibeyon maza su ne,
Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan36.24 Bulget, Siriyak sami ruwa; ma’anar Ibraniyanci don wannan kalma ba tabbatacce ba ne. ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.
’Ya’yan Ana su ne,
Dishon da Oholibama ’yar Ana.
’Ya’yan Dishon maza36.26 Da Ibraniyanci Dishan, wani suna na Dishon su ne,
Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
’Ya’yan Ezer maza su ne,
Bilhan, Za’aban da Akan.
’Ya’yan Dishan maza su ne,
Uz da Aran.
Waɗannan su ne manyan Horiyawa,
Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan.
Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.
Masu mulkin Edom
Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,36.31 Ko kuwa kafin wani sarkin Isra’ilawa ya yi mulki a kansu
Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.
Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.
Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.
Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.
Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.
Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi36.37 Mai yiwuwa Yuferites ya gāje shi.
Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.
Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad36.39 Yawancin rubuce-rubucen hannu na Masoretik, Fentatut na Samariya da Siriyak (dubi kuma 1Tar 1.50); yawancin rubuce-rubucen hannu na Masoretik suna da Hadar ne. ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.
Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne,
Timna, Alwa, Yetet.
Oholibama, Ela, Finon.
Kenaz, Teman, Mibzar.
Magdiyel da Iram.
Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna.
Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.
Mafarkan Yusuf
Yaƙub ya zauna a ƙasar da mahaifinsa ya zauna, wato, ƙasar Kan’ana.
Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub.
Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa.
Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran ’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau.37.3 Ma’anar Ibraniyanci na mai ado ba tabbatacce ba ne; haka ma a ayoyi 23 da 32. Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi. Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”
Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.
Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da ’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?” ’Yan’uwansa suka yi kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe batun nan a zuciya.
’Yan’uwan Yusuf maza sun sayar da shi
To, ’yan’uwansa suka tafi kiwon garkunan mahaifinsu kusa da Shekem. Sai Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Kamar yadda ka sani, ’yan’uwanka suna kiwon garkuna kusa da Shekem. Zo, in aike ka gare su.”
Ya ce, “To.”
Saboda haka Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Jeka ka ga ko kome lafiya yake da ’yan’uwanka da kuma garkunan, ka kawo mini labari.” Sa’an nan ya sallame shi daga Kwarin Hebron.
Sa’ad da Yusuf ya kai Shekem, sai wani mutum ya same shi yana yawo a cikin jeji, sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”
Yusuf ya amsa ya ce, “Ina neman ’yan’uwana ne. Za ka iya faɗa mini inda suke kiwon garkunansu?”
Mutumin ya amsa, “Sun yi gaba daga nan. Na ji su suna cewa, ‘Bari mu je Dotan.’ ”
Saboda haka Yusuf ya bi bayan ’yan’uwansa, ya kuwa same su kusa da Dotan. Amma da suka gan shi daga nesa, kafin yă kai wurinsu, sai suka ƙulla su kashe shi.
Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can zuwa! Ku zo mu kashe shi mu kuma jefa shi a ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, mu ce mugun naman jeji ya cinye shi. Mu ga yadda mafarkinsa zai cika.”
Sa’ad da Ruben ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă cece shi daga hannuwansu. Ya ce, “Kada mu ɗauki ransa. Kada mu zub da wani jini. Mu dai jefa shi cikin wannan rijiya a nan cikin hamada, amma kada mu sa hannu a kansa.” Ruben ya faɗa wannan ne don yă cece shi daga gare su, yă kuma mai da shi ga mahaifinsa.
Saboda haka sa’ad da Yusuf ya zo wurin ’yan’uwansa, sai suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai gwanin kyau da ya sa, suka kuma ɗauke shi suka jefa a cikin rijiya. To, rijiyar wofi ce, babu ruwa a ciki.
Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.
Yahuda ya ce wa ’yan’uwansa, “Me zai amfane mu in muka kashe ɗan’uwanmu muka ɓoye jininsa? Ku zo, mu sayar da shi wa mutanen Ishmayelawan nan, kada mu sa hannuwanmu a kansa; ban da haka ma, shi ɗan’uwanmu ne, jiki da jininmu.” Sai ’yan’uwansa suka yarda.
Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel37.28 Wato, kamar ons 8 (kamar kilo 0.2) ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.
Sa’ad da Ruben ya dawo wurin rijiyar, sai ya tarar cewa Yusuf ba ya can, sai ya kyakkece tufafinsa. Ya koma wurin ’yan’uwansa ya ce, “Yaron ba ya can! Ina zan bi yanzu?”
Sai suka ɗauki rigar Yusuf, suka yanka akuya suka tsoma rigar a cikin jinin. Suka ɗauki rigan nan mai gwanin kyau, suka kawo wa mahaifinsu suka ce, “Mun sami wannan. Ka bincika shi ka gani ko rigar ɗanka ne.”
Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.”
Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa. Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari37.35 Da Ibraniyanci Sheol. wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi.
Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna.
Yahuda da Tamar
A wannan lokaci, Yahuda ya bar ’yan’uwansa ya gangara don yă zauna da mutumin Adullam, mai suna Hira. A can Yahuda ya sadu da ’yar wani Bakan’ane, mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya kuma kwana da ita; ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa, wanda aka kira Er. Ta sāke yin ciki, ta haifi wani ɗa, ta kira shi Onan. Ta kuma haifi wani ɗa har yanzu, aka kuwa ba shi suna Shela. A Kezib ne ta haife shi.
Sai Yahuda ya auro wa Er mata, ɗansa na fari, sunanta Tamar. Amma Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a fuskar Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.
Sa’an nan Yahuda ya ce wa Onan, “Ka kwana da matar ɗan’uwanka ka cika wajibinka gare ta a matsayin ɗan’uwan miji, don ka samar wa ɗan’uwanka ’ya’ya.” Amma Onan ya san cewa ’ya’yan ba za su zama nasa ba; saboda haka a duk sa’ad da ya kwana da matar ɗan’uwansa, sai yă zub da maniyyinsa a ƙasa don kada yă samar wa ɗan’uwansa ’ya’ya. Abin nan da ya yi mugunta ce a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi, shi ma.
Sai Yahuda ya ce wa surukarsa Tamar, “Ki yi zama kamar gwauruwa a gidan mahaifinki sai ɗana Shela ya yi girma.” Gama ya yi tunani, “Shi ma zai mutu, kamar ’yan’uwansa.” Saboda haka Tamar ta je ta zauna a gidan mahaifinta.
Bayan an daɗe sai matar Yahuda, ’yar Shuwa ta rasu. Sa’ad da Yahuda ya gama makoki, sai ya haura zuwa Timna, zuwa wurin mutanen da suke askin tumakinsa, abokinsa Hira mutumin Adullam kuwa ya tafi tare da shi.
Sa’ad da aka faɗa wa Tamar cewa, “Surukinki yana kan hanyarsa zuwa Timna don askin tumakinsa,” sai ta tuɓe rigunan gwaurancinta ta rufe kanta da lulluɓi don ta ɓad da kamanninta, sa’an nan ta je ta zauna a ƙofar shigar Enayim, wadda take a hanyar zuwa Timna. Gama ta lura cewa ko da yake Shela yanzu ya yi girma, ba a ba da ita gare shi ta zama matarsa ba.
Sa’ad da Yahuda ya gan ta, ya yi tsammani karuwa ce, gama ta lulluɓe fuskarta. Bai san cewa ita surukarsa ce ba, sai ya ratse zuwa wurinta a gefen hanya ya ce, “Zo mana, in kwana da ke.”
Sai ta ce, “Me za ka ba ni in na kwana da kai?”
Ya ce, “Zan aika miki da ɗan akuya daga garkena.”
Sai ta ce, “Za ka ba ni wani abu jingina, kafin ka aika da shi?”
Ya ce, “Wace jingina zan ba ki?”
Sai ta amsa, “Hatiminka da ka rataye a wuya da kuma sandan da yake a hannunka.” Ya ba da su gare ta, ya kuma kwana da ita, sai ta yi ciki. Bayan ta tafi, sai ta tuɓe lulluɓin, ta sāke sa tufafin gwaurancinta.
Ana cikin haka sai Yahuda ya aika da ɗan akuya ta hannun abokinsa mutumin Adullam don yă karɓo masa jinginar daga wurin macen, amma bai same ta a can ba. Ya tambayi mutanen da suke zama a can ya ce, “Ina karuwar haikalin da take a bakin hanya a Enayim?”
Sai suka ce, “Ba a taɓa kasance da karuwar haikali a nan ba.”
Saboda haka sai ya koma zuwa wurin Yahuda ya ce, “Ban same ta ba. Ban da haka ma, mutanen da suke zama a can, sun ce, ‘Ba a taɓa kasance da wata karuwar haikali a nan ba.’ ”
Sa’an nan Yahuda ya ce, “Bari tă riƙe kayan kiɗa garin nema mu zama abin dariya. Ni kam, na aika da tunkiyar amma ba a same ta ba.”
Bayan misalin wata uku sai aka faɗa wa Yahuda cewa, “Tamar, surukarka ta yi laifin karuwanci, a sakamakon haka yanzu ta yi ciki.”
Yahuda ya ce, “A fid da ita, a ƙone!”
Yayinda ake fitar da ita, sai ta aika saƙo zuwa wurin surukinta, ta ce, “Mutumin da yake da waɗannan kayan ne ya yi mini ciki.” Ta kuma ƙara da cewa, “Duba ko za ka gane da hatimin nan, da abin ɗamaran nan, da kuma sandan nan, ko na wane ne?”
Yahuda ya gane su, sai ya ce, “Ai, ta fi ni gaskiya, da yake ban ba da ita ga ɗana Shela ba.” Bai kuwa ƙara kwana da ita ba.
Sa’ad da lokaci ya yi da za tă haihu, ashe, tagwaye ’yan maza ne suke cikinta. Yayinda take haihuwa, ɗaya daga cikinsu ya fid da hannunsa; sai ungonzomar ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, ta ce, “Wannan ne ya fito da farko.” Amma sa’ad da ya janye hannunsa, sai ɗan’uwansa ya fito, sai ta ce, “Wato, haka ne ka keta ka fito!” Sai aka ba shi suna Ferez.38.29 Ferez yana nufin ƙetawa waje. Sa’an nan ɗan’uwansa wanda yake da jan zare a hannunsa ya fito, aka kuma ba shi suna Zera.38.30 Zera na iya nufin ja ko mai haske.
Yusuf da matar Fotifar
To, aka kai Yusuf Masar, Fotifar wani mutumin Masar wanda yake ɗaya daga cikin hafsoshin Fir’auna, shugaban masu tsaro, ya saye shi daga mutanen Ishmayel waɗanda suka kai shi can.
Ubangiji kuwa yana tare da Yusuf, Yusuf kuwa yi nasara, ya zauna a gidan mutumin Masar maigidansa. Sa’ad da maigidansa ya ga cewa Ubangiji yana tare da Yusuf, kuma cewa Ubangiji ya ba shi nasara a kome da ya yi, sai Yusuf ya sami tagomashi a idanunsa, ya kuma zama mai hidimarsa. Fotifar ya sa shi yă zama shugaba a gidansa, ya kuma danƙa masa kome da yake da shi. Daga lokacin da ya sa shi shugaban gidansa da kuma a kan dukan abin da yake da shi, sai Ubangiji ya albarkaci gidan mutumin Masar saboda Yusuf. Albarkar Ubangiji tana a kan kome da Fotifar yake da shi a gida da kuma a jeji. Saboda haka sai ya bar kome a ƙarƙashin kulawar Yusuf, bai dame kansa a wani abu ba sai dai abincin da yake ci.
To, fa, Yusuf ƙaƙƙarfa ne, kyakkyawa kuma, bayan an ɗan jima sai matar maigidansa ta fara sha’awar Yusuf, sai ta ce, “Zo ka kwana da ni!”
Amma ya ƙi. Ya ce mata, “Ga shi kome yana a ƙarƙashina, don haka ne ma maigidana bai dami kansa da wani abu a cikin gidan nan ba; kome da ya mallaka, ya danƙa ga kulawata. Babu wani da ya fi ni a wannan gida. Maigidana bai hana ni kome ba sai ke, saboda ke matarsa ce. Yaya fa, zan yi irin wannan mugun abu, in yi zunubi wa Allah?” Ko da yake ta yi ta yin wa Yusuf maganar kowace rana, amma ya ƙi yă kwana da ita, ko ma yă zauna da ita.
Wata rana, ya shiga cikin gida don yă yi ayyukansa, ba wani daga cikin bayin gidan da yake ciki. Sai ta cafke shi a riga, ta ce, “Zo ka kwana da ni!” Amma ya bar rigarsa a hannunta, ya gudu ya fita daga gidan.
Sa’ad da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita daga gidan, sai ta kira bayin gidan ta ce musu, “Duba, an kawo mana wannan mutumin Ibraniyawa don yă ci mutuncinmu! Ya zo nan don yă kwana da ni, amma na yi ihu. Sa’ad da ya ji na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.”
Ta ajiye rigar kusa da ita sai da maigidansa ya dawo gida. Sa’an nan ta faɗa masa wannan labari, “Mutumin Ibraniyawan, bawan da ka kawo mana, ya zo wurina don yă ci mutuncina. Amma da zarar na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.”
Sa’ad da maigidansa ya ji labarin da matarsa ta faɗa masa cewa, “Ga yadda bawanka ya yi da ni,” sai ya husata. Maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya sa a kurkuku, wurin da ake tsare ’yan kurkukun sarki.
Amma yayinda Yusuf yake can a cikin kurkuku, Ubangiji ya kasance tare da shi; ya nuna masa alheri, ya kuma sa ya sami tagomashi a idanun mai gadin kurkukun. Saboda haka mai gadin ya sa Yusuf ya zama shugaban dukan waɗanda aka tsare a kurkukun, Yusuf ne kuma yake lura da dukan abin da ake yi a can. Mai gadin ba ya sa kansa game da kome da yake ƙarƙashin kulawar Yusuf, gama Ubangiji yana tare da Yusuf, ya kuma ba shi nasara a cikin dukan abin da ya yi.
Mai riƙon kwaf da mai tuya
Bayan ɗan lokaci, sai mai riƙon kwaf da mai tuyan sarkin Masar suka yi wa maigidansu, sarkin Masar laifi. Fir’auna ya yi fushi da hafsoshin nan nasa guda biyu, shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya, ya kuma sa su a kurkuku a cikin gidan shugaban masu tsaro, a wannan kurkukun da aka sa Yusuf. Sai shugaban masu tsaro ya danƙa su a hannun Yusuf, ya kuwa yi musu hidima.
Bayan sun jima cikin kurkuku, sai kowanne a cikin mutum biyun nan, mai riƙon kwaf da mai tuya na sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, suka yi mafarki a dare ɗaya, kuma kowane mafarki ya kasance da fassara irin tasa.
Sa’ad da Yusuf ya zo wurinsu kashegari, sai ya ga duk sun damu. Saboda haka ya tambayi hafsoshin Fir’auna, waɗanda suke a kurkuku tare da shi, a gidan maigidansa ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a ɓace haka?”
Sai suka amsa, “Mu biyu, mun yi mafarki, amma babu wani da zai fassara mana su.”
Sa’an nan Yusuf ya ce musu, “Fassara ba daga Allah take zuwa ba? Ku faɗa mini mafarkanku.”
Sai shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusuf mafarkinsa. Ya ce masa, “A cikin mafarkina, na ga kuringa a gabana, kuma a kuringar, akwai rassa uku. Nan da nan kuringar ta yi toho, ta huda, ta kuma yi nonna har suka nuna, suka zama inabi. Kwaf Fir’auna kuwa yana a hannuna, na kuma ɗiba inabin na matse su cikin kwaf Fir’auna, na kuma sa kwaf ɗin a hannunsa.”
Yusuf ya ce masa, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Rassan nan uku, kwana uku ne. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa. Amma fa, sa’ad da kome ya zama maka da kyau, ka tuna da ni, ka kuma yi mini alheri, ka ambace ni wa Fir’auna, ka fid da ni daga wannan kurkuku. Gama da ƙarfi ne aka ɗauke ni daga ƙasar Ibraniyawa, ko a nan ma ban yi wani abin da ya cancanci a sa ni cikin kurkuku ba.’ ”
Sa’ad da shugaban masu tuya ya ga cewa Yusuf ya ba da fassara mai gamsarwa, sai ya ce, wa Yusuf, “Ni ma na yi mafarki. A kaina, akwai kwanduna uku na burodi40.16 Ko kuwa kwanduna uku marasa ƙarfi. A kwandon na bisa, akwai kayan iri-iri da aka toya, masu kyau domin Fir’auna, amma tsuntsaye suka ci su a kwandon da yake kaina.”
Yusuf ya ce, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Kwanduna uku, kwanaki uku ne. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace.40.19 Ko kuwa ya cira ka a itace Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’ ”
To, a rana ta uku ne, ranar tunawa da haihuwar Fir’auna, ya kuwa yi biki wa dukan hafsoshinsa. Ya fid da shugaban masu shayarwa da kuma shugaban masu tuya a gaban hafsoshinsa. Ya mai da shugaban masu shayarwa a matsayinsa, saboda haka shugaban masu shayarwa ya sāke sa kwaf a hannun Fir’auna, amma ya rataye40.22 Ko kuwa cira shugaban masu tuya, kamar dai yadda Yusuf ya faɗa musu a fassarar mafarkan da suka yi.
Shugaban masu shayarwa fa, bai tuna da Yusuf ba; ya mance da shi.
Mafarkan Fir’auna
Bayan shekaru biyu cif, Fir’auna ya yi mafarki. A mafarkin, ya ga yana tsaye kusa da Nilu, sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul, suka fito daga kogin, suna kiwo a cikin kyauro. Bayansu, sai ga waɗansu shanu bakwai, munana, ramammu, suka fito daga Nilu, suka tsaya kusa da waɗancan masu ƙiban, a bakin kogin. Shanun nan da suke munana ramammu, suka cinye shanu bakwai nan masu ƙiba mulmul. Sai Fir’auna ya farka.
Ya sāke yin barci, sai ya yi mafarki na biyu; ya ga kawuna bakwai na dawa, ƙosassu masu kyau, suka yi girma a kara guda. Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai na dawa, suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta sa suka yanƙwane. Siraran dawan suka haɗiye kawuna bakwai nan ƙosassu masu kyau. Sai Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne.
Da safe sai hankalinsa ya tashi, saboda haka sai ya aika a kawo dukan masu duba da masu hikima na Masar. Fir’auna ya faɗa musu mafarkansa, amma babu wanda ya iya ba shi fassararsu.
Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir’auna, “Yau an tuna mini da kāsawata. Sai ya ci gaba ya ce, Fir’auna ya taɓa husata da bayinsa, ya kuma jefa ni da shugaban masu tuya a cikin kurkuku a gidan shugaban masu tsaro. Kowannenmu ya yi mafarki a wani dare, kowane mafarki kuma ya kasance da ma’anarsa. To, wani saurayi, mutumin Ibraniyawa ya kasance a can tare da mu, bawan shugaban masu tsaro. Sai muka faɗa masa mafarkanmu, ya kuwa fassara mana su, yana ba wa kowane mutum fassarar mafarkinsa. Abubuwan kuwa suka kasance daidai yadda ya fassara su gare mu; aka mai da ni a matsayina, ɗaya mutumin kuwa aka rataye shi.”
Sai Fir’auna ya aika a kawo Yusuf, aka kuwa kawo shi da sauri daga kurkuku. Sa’ad da ya yi aski, ya kuma canja tufafinsa, sai ya zo gaban Fir’auna.
Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Na yi mafarki, kuma babu wanda ya iya fassara shi. Amma na ji an ce sa’ad da ka ji mafarki, kana iya fassara shi.”
Yusuf ya amsa wa Fir’auna ya ce, “Ba ni ne da iyawar ba, Allah zai iya ba wa Fir’auna amsar da yake nema.”
Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “A cikin mafarkina, na ga ina tsaye a bakin Nilu, sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul, suka fito daga kogin, suna kiwo a cikin kyauro. Bayansu kuma, sai ga waɗansu shanu bakwai suka fito ƙanjamammu, munana, ramammu. Ban taɓa ganin irin munanan shanu haka a cikin dukan ƙasar Masar ba. Ramammun shanun nan munana, suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba da suka fito da fari. Amma ko bayan da suka cinye su, babu wanda zai iya faɗa cewa sun yi haka; suna nan dai munana kamar yadda suke a dā. Sai na farka.
“Har yanzu kuma, a cikin mafarkina na ga kawuna bakwai na dawa ƙosassu masu kyau, suna girma a kara guda. Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai suka fito, yanƙwananne sirara waɗanda iskar gabas ta yanƙwane. Siraran kawunan dawan nan suka haɗiye kawuna bakwai nan masu kyau. Na faɗa wannan wa masu duba, amma ba wanda ya iya fassara mini shi.”
Sai Yusuf ya ce wa Fir’auna, “Mafarkan Fir’auna, ɗaya ne. Allah ya bayyana wa Fir’auna abin da yake shirin yi. Shanu masu kyau nan, shekaru bakwai ne, kawunan dawa bakwai ƙosassun nan kuwa shekaru bakwai ne; mafarkan iri ɗaya ne. Shanun nan ramammu, munana, da suka zo daga baya, shekaru bakwai ne, haka ma kawuna dawan nan shanyayyu da iskar gabas ta yanƙwane. Shekaru ne bakwai na yunwa.
“Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir’auna cewa Allah ya nuna wa Fir’auna abin da yake shirin yi. Shekaru bakwai na yalwar abinci suna zuwa a dukan ƙasar Masar, amma shekaru bakwai na yunwa za su biyo bayansu. Tsananin yunwar za tă sa a manta da dukan isashen abincin da aka samu a ƙasar Masar, yunwa kuwa za tă rufe dukan ƙasar. Ba za a tuna da isashen abincin da aka samu a ƙasar ba, domin yunwar da za tă biyo baya za tă zama da tsanani ƙwarai. Dalilin da aka ba wa Fir’auna mafarkan nan kashi biyu kuwa shi ne cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin. Allah zai aikata shi, ba da daɗewa ba.
“Yanzu fa, bari Fir’auna yă nemi mutum mai basira da kuma hikima, yă sa shi yă shugabanci ƙasar Masar. Bari Fir’auna yă naɗa komishinoni a kan ƙasar don su karɓi kashi ɗaya bisa biyar na girbin Masar a lokacin shekaru bakwai na yalwar abinci. Ya kamata su tara dukan abincin waɗannan shekaru masu kyau da suke zuwa, su yi ajiyar hatsin a ƙarƙashin ikon Fir’auna, don a ajiye a birane don abinci. Ya kamata a adana abincin nan don ƙasar, kāriya shekaru bakwai na yunwa, domin a yi amfani da shi a lokacin shekarun yunwan da za su zo wa Masar, saboda kada ƙasar ta lalace da yunwa.”
Shirin ya yi wa Fir’auna da kuma dukan hafsoshinsa kyau. Saboda haka Fir’auna ya tambaye su, “Za mu iya samun wani kamar wannan mutum, wannan wanda Ruhun Allah yake cikinsa?”41.38 Ko kuwa na alloli
Sai Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Da yake Allah ya ba ka sanin dukan waɗannan, babu wani mai basira da kuma hikima kamar ka. Za ka shugabanci fadata, kuma dukan mutanena za su zama a ƙarƙashinka. Da sarauta kaɗai zan fi ka girma.”
Yusuf shugaban Masar
Saboda haka Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ga shi na sa ka zama shugaban dukan ƙasar Masar.” Sa’an nan Fir’auna ya zare zoben sarauta daga yatsarsa, ya sa shi a yatsan Yusuf. Ya sanya masa rigar lallausan lilin, ya kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa. Ya sa shi ya hau keken yaƙi a matsayi mai binsa na biyu,41.43 Ko kuwa a cikin keken yaƙi ta muƙaddashinsa; ko kuwa cikin keken yaƙinsa ta biyu mutane kuwa suka yi shela a gabansa suna cewa, “A ba da hanya!”41.43 Ko kuwa Rusuna Ta haka ya sa shi shugaba a kan dukan ƙasar Masar.
Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ni ne Fir’auna, amma in ba tare da umarninka ba, ba wanda zai ɗaga hannu ko ƙafa a cikin dukan Masar.” Fir’auna ya ba wa Yusuf suna Zafenat-Faneya, ya kuma ba shi Asenat ’yar Fotifera firist na On,41.45 Wato, Heliyofolis; haka ma a aya 50 ta zama matarsa. Yusuf kuwa ya zaga dukan ƙasar Masar.
Yusuf yana zuwa shekara talatin sa’ad da ya shiga hidimar Fir’auna sarkin Masar. Yusuf kuwa ya fita daga gaban Fir’auna, ya zaga ko’ina a Masar. A shekaru bakwai na yalwa, ƙasar ta ba da amfani mai yawa. Yusuf ya tattara dukan abincin da aka samu a waɗannan shekaru bakwai na yalwa a Masar, ya kuma yi ajiyarsu a cikin birane. A kowane birni, ya sa abincin da aka nome a kewayensa. Sai Yusuf ya tara hatsi da yawan gaske, kamar yashi a bakin teku, har sai da ya kāsa iya auna shi, gama ba a iya aunawa.
Kafin shekarun yunwa su zo, Asenat ’yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusuf ’ya’ya maza biyu. Yusuf ya ba wa ɗansa na fari suna Manasse41.51 Manasse ya yi kamar, kuma za a iya ɗauko daga kalmar Ibraniyanci mai ma’ana manta. ya ce, “Gama Allah ya sa na mance dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.” Ya ba wa ɗansa na biyu suna Efraim41.52 Efraim ya yi kamar kalmar Ibraniyanci na wadata sau biyu. ya ce, “Gama Allah ya wadata ni cikin wahalata.”
Shekaru bakwai na yalwa a Masar suka zo ga ƙarshe, sai shekaru bakwai na yunwa suka soma shigowa, kamar yadda Yusuf ya faɗa. Aka yi yunwa ko’ina amma ban da ƙasar Masar. Don akwai abinci. Sa’ad da dukan Masar ta fara jin yunwa, sai mutane suka yi wa Fir’auna kuka don abinci. Sai Fir’auna ya ce wa dukan Masarawa, “Ku tafi wurin Yusuf, ku kuma yi abin da ya faɗa muku.”
Sa’ad da yunwa ta bazu a dukan ƙasar, sai Yusuf ya buɗe gidajen ajiya, ya kuma sayar da hatsi ga Masarawa, gama yunwa ta yi tsanani a dukan Masar. Dukan ƙasashe kuwa suka zo Masar don saya hatsi daga Yusuf, gama yunwa ta yi tsanani a dukan duniya.
’Yan’uwan Yusuf maza sun tafi Masar
Sa’ad da Yaƙub ya sami labari cewa akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa ’ya’yansa maza, “Don me kuke duban juna kawai?” Ya ci gaba, “Na ji cewa akwai hatsi a Masar. Ku gangara can ku sayo mana, domin mu rayu kada mu mutu.”
Sai goma daga cikin ’yan’uwan Yusuf suka gangara don su saya hatsi daga Masar. Amma Yaƙub bai aiki Benyamin, ɗan’uwan Yusuf tare da sauran ba, gama yana tsoro kada wani abu yă faru da shi. Sai ’ya’yan Yaƙub suka isa Masar tare da sauran mutanen don sayen abinci, gama yunwar ta kai yankin Kan’ana ma.
To, Yusuf ne gwamnar ƙasar wanda yake sayar da hatsi ga dukan mutanenta. Saboda haka sa’ad da ’yan’uwan Yusuf suka isa, sai suka rusuna masa har ƙasa da fuskokinsu. Nan da nan da Yusuf ya ga ’yan’uwansa, sai ya gane su, amma ya yi kamar baƙo, ya kuma yi musu magana da tsawa. Ya tambaya, “Daga ina kuka fito?”
Suka amsa, “Daga ƙasar Kan’ana, don mu saya abinci.”
Ko da yake Yusuf ya gane ’yan’uwansa, su ba su gane shi ba. Sa’an nan ya tuna da mafarkansa game da su, ya kuma ce musu, “Ku ’yan leƙen asiri ne! Kun zo don ku leƙi asirin ƙasar ku ga inda ba ta da tsaro.”
Suka amsa suka ce, “A’a, ranka yă daɗe, bayinka sun zo don saya abinci ne. Mu duka ’ya’yan mutum ɗaya maza ne. Bayinka mutane ne masu gaskiya, ba ’yan leƙen asiri ba ne.”
Ya ce musu “Sam! Kun zo ne ku ga inda ƙasarmu babu tsaro.”
Amma suka amsa suka ce, “Bayinka dā su goma sha biyu ne, ’yan’uwa, ’ya’yan mutum guda maza, wanda yake zama a ƙasar Kan’ana. Ƙaraminmu yanzu yana tare da mahaifinmu, ɗayan kuma ya rasu.”
Yusuf ya ce musu, “Daidai ne yadda na faɗa muku. Ku ’yan leƙen asiri ne! Ga kuwa yadda za a gwada ku. Muddin Fir’auna yana a raye, ba za ku bar wannan wuri ba sai ƙaramin ɗan’uwanku ya zo nan. Ku aiki ɗaya daga cikinku yă kawo ɗan’uwanku; za a sa sauranku a kurkuku, saboda a gwada maganarku a ga ko gaskiya ce kuke faɗi. In ba haka ba, to, da ran Fir’auna, ku ’yan leƙen asiri ne!” Ya kuwa sa su duka a kurkuku na kwana uku.
A rana ta uku, Yusuf ya ce musu, “Ku yi wannan za ku kuwa rayu, gama ina tsoron Allah. In ku mutane masu gaskiya ne, ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku yă zauna a kurkuku, yayinda sauranku su tafi, su kai hatsi don gidajenku da suke yunwa. Amma dole ku kawo ƙaramin ɗan’uwanku gare ni, saboda a tabbatar da maganarku har ba za ku mutu ba.” Suka kuwa yi haka.
Sai suka ce wa juna, “Tabbatacce ana hukunta mu ne saboda ɗan’uwanmu. Mun ga yadda ya yi wahala sa’ad da ya roƙe mu saboda ransa, amma ba mu saurare shi ba, shi ya sa wannan wahala ta zo mana.”
Ruben ya amsa, “Ban faɗa muku cewa kada ku ɗauki alhakin yaron nan ba, sai kuka ƙi ji, to, yau ga alhakin jininsa muke biya.” Ba su san cewa Yusuf yana jin su ba, da yake yana amfani da mai fassara ne.
Sai ya juya daga gare su ya yi kuka, sa’an nan ya dawo ya yi musu magana kuma. Ya sa aka ɗauke Simeyon daga gare su, aka daure shi a idanunsu.
Yusuf ya yi umarni a cika buhunansu da hatsi, a kuma sa azurfan kowane mutum a cikin buhunsa, a kuma ba su kalaci don tafiyarsu. Bayan aka yi musu wannan, suka jibga hatsinsu a kan jakuna, sai suka kama hanya.
A wurin da suka tsaya don su kwana, ɗaya daga cikinsu ya buɗe buhunsa don yă ciyar da jakinsa, sai ya ga azurfansa a bakin buhunsa. Sai ya ce wa ’yan’uwansa, “An mayar mini da azurfata. Ga shi a cikin buhuna.”
Zuciyarsu ta karai, suka dubi juna suna rawan jiki, suka ce, “Mene ne wannan da Allah ya yi mana?”
Sa’ad da suka zo wurin mahaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana, suka faɗa masa dukan abin da ya faru da su. Suka ce, “Mutumin da yake shugaba a ƙasar ya yi mana matsananciyar magana, ya kuma ɗauke mu tamƙar ’yan leƙen asirin ƙasa. Amma muka ce masa, ‘Mu masu gaskiya ne; mu ba ’yan leƙen asiri ba ne. Dā mu ’yan’uwa ne goma sha biyu, ’ya’yan mahaifi guda maza. Ɗayanmu ya rasu, kuma ƙaramin yanzu yana tare da mahaifinmu a Kan’ana.’
“Sai mutumin wanda yake shugaba a kan ƙasar ya ce mana, ‘Ga yadda zan san ko ku mutane masu gaskiya ne. Ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku a nan tare da ni, ku ɗauki abinci domin gidajenku masu yunwa, ku tafi. Amma ku kawo mini ƙaramin ɗan’uwanku domin in san cewa ku ba ’yan leƙen asiri ba ne, amma mutane ne masu gaskiya. Sa’an nan zan mayar muku da ɗan’uwanku, ku kuma iya yin sana’a42.34 Ko kuwa ma’amala a sake a ƙasar.’ ”
Yayinda suke juyewa hatsi daga buhunansu, sai ga ƙunshin azurfan kowane mutum a buhunsa! Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshe-ƙunshen kuɗi, suka firgita. Yaƙub mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashin ’ya’yana. Yusuf ya rasu, Simeyon kuma ba ya nan, yanzu kuma kuna so ku ɗauki Benyamin. Kome yana gāba da ni!”
Sai Ruben ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe dukan ’ya’yana maza, in ban dawo da shi gare ka ba. Ka sa shi ga kulawata, zan kuwa dawo da shi.”
Amma Yaƙub ya ce, “Ɗana ba zai gangara zuwa can tare da ku ba, ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kaɗai ya rage. In wani abu ya faru da shi a tafiyar da za ku yi, za ku sa furfurata ta gangara zuwa kabari42.38 Da Ibraniyanci Sheol. cikin baƙin ciki.”
Tafiya ta biyu zuwa Masar
A yanzu, yunwa ta yi tsanani a ƙasar. Saboda haka sa’ad da suka cinye dukan hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ƙarin abinci.”
Amma Yahuda ya ce masa, “Mutumin ya gargaɗe mu sosai cewa, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai in ɗan’uwanku yana tare da ku.’ In za ka aika da ɗan’uwanmu tare da mu, za mu gangara mu sayo maka abinci. Amma in ba za ka aika da shi ba, ba za mu gangara ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai ko in ɗan’uwanku yana tare da ku.’ ”
Isra’ila ya yi tambaya, “Me ya sa kuka kawo wannan damuwa a kaina ta wurin faɗa wa mutumin cewa kuna da wani ɗan’uwa?”
Suka amsa, “Mutumin ya yi mana tambaya sosai game da kanmu da iyalinmu. Ya tambaye mu, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna da wani ɗan’uwa?’ Mu dai mun amsa tambayoyinsa ne. Ta yaya za mu sani zai ce, ‘Ku kawo ɗan’uwanku a nan’?”
Sa’an nan Yahuda ya ce wa Isra’ila mahaifinsa, “Ka aika saurayin tare da ni za mu kuwa tafi nan da nan, saboda mu da ’ya’yanmu mu rayu, kada mu mutu. Ni kaina zan tabbatar da lafiyarsa; na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. In ban dawo da shi gare ka, in sa shi nan a gabanka ba, zan ɗauki laifin a gabanka dukan kwanakina. Ai, da ba mun jinkirta ba, da mun komo har sau biyu.”
Sa’an nan mahaifinsu Isra’ila ya ce musu, “In dole ne a yi haka, to, sai ku yi. Ku sa waɗansu amfani mafi kyau na ƙasar a buhunanku, ku ɗauka zuwa wurin mutumin a matsayin kyauta, da ɗan man ƙanshi na shafawa, da kuma ’yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta da kuma almon. Ku ɗauki ninki biyu na yawan azurfa tare da ku, gama dole ku mayar da azurfan da aka sa a cikin bakunan buhunanku. Mai yiwuwa an yi haka a kuskure ne. Ku ɗauki ɗan’uwanku kuma ku koma wurin mutumin nan da nan. Bari Allah Maɗaukaki43.14 Da Ibraniyanci an rubuta El-Shaddai ne. yă nuna muku alheri a gaban mutumin saboda yă bar ɗan’uwanku da Benyamin su dawo tare da ku. Ni kuwa, in na yi rashi, na yi rashi.”
Saboda haka mutanen suka ɗauki kyautar, da kuma kuɗin da ya ninka na farko. Suka kuma ɗauki Benyamin, suka gaggauta suka gangara zuwa Masar suka kuma gabatar da kansu ga Yusuf. Sa’ad da Yusuf ya ga Benyamin tare da su, sai ya ce wa mai hidimar gidansa, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.”
Mutumin ya yi kamar yadda Yusuf ya faɗa masa, ya kuwa ɗauki mutanen zuwa gidan Yusuf. Mutanen dai suka firgita sa’ad da aka ɗauke su zuwa gidansa. Suka yi tunani, “An kawo mu nan ne saboda azurfan da aka sa a cikin buhunanmu da farko. Yana so yă fāɗa mana, yă kuma sha ƙarfinmu, yă ƙwace mu kamar bayi, yă kuma kwashe jakunanmu.”
Saboda haka suka je wurin mai yin wa Yusuf hidima, suka yi masa magana a bakin ƙofar gida. Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun zo nan ƙaro na farko don mu saya abinci, amma a inda muka tsaya don mu kwana, da muka buɗe buhunanmu sai kowannenmu ya sami azurfansa daidai a bakin buhunsa. Saboda haka ga kuɗin a hannunmu, mun sāke komowa da su. Mun kuma kawo ƙarin azurfa tare da mu don mu saya abinci. Ba mu san wa ya sa azurfanmu a cikin buhunanmu ba.”
Sai mai hidimar ya ce, “Ba kome, kada ku ji tsoro. Allahnku, Allahn mahaifinku ne ya ba ku dukiyar a cikin buhunanku; ni dai, na karɓi azurfanku.” Sa’an nan ya fitar musu da Simeyon.
Mai yin hidimar ya ɗauki mutane zuwa gidan Yusuf ya ba su ruwa su wanke ƙafafunsu, ya kuma tanada wa jakunansu abinci. Suka shirya kyautansu domin isowar Yusuf da rana, gama sun ji cewa zai ci abinci a nan.
Sa’ad da Yusuf ya zo gida, sai suka ba shi kyautai da suka kawo, suka rusuna a gabansa har ƙasa. Ya tambaye su, yaya suke, sa’an nan ya ce, “Yaya tsohon nan mahaifinku da kuka faɗa mini? Yana da rai har yanzu?”
Suka amsa, “Bawanka mahaifinmu yana da rai har yanzu da kuma ƙoshin lafiya.” Suka kuma rusuna suka yi mubaya’a.
Da ya ɗaga idanu, sai ya ga ɗan’uwansa Benyamin, ɗan mahaifiyarsa, sai ya yi tambaya, “Wannan ne ƙaramin ɗan’uwanku, wanda kuka faɗa mini a kai?” Ya kuma ce, “Allah yă yi maka albarka, ɗana.” Saboda motsi mai zurfi da zuciyarsa ta yi da ganin ɗan’uwansa, sai Yusuf ya gaggauta ya fita, ya nemi wuri yă yi kuka. Ya shiga ɗakinsa ya yi kuka a can.
Bayan ya wanke fuskarsa, sai ya fito ya daure, ya umarta, “A kawo abinci.”
Sai aka raba musu abinci, nasa shi kaɗai su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sa cin abinci tare da Ibraniyawa, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa. Aka zaunar da ’yan’uwan Yusuf a gabansa bisa ga shekarunsu, daga ɗan fari zuwa auta. ’Yan’uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki. Daga teburin da yake a gaban Yusuf aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Benyamin ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.
Kwaf Azurfa a cikin buhu
Yusuf kuwa ya ba wa mai yin masa hidima a gida, waɗannan umarnai cewa, “Cika buhunan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin buhunsa. Sa’an nan ka sa kwaf nawa, wannan na azurfa a bakin buhun autan, tare da kuɗinsa na hatsi.” Sai mai hidimar ya yi kamar yadda Yusuf ya umarta.
Da gari ya waye, sai aka sallami mutanen tare da jakunansu. Ba su yi nisa da birnin ba sa’ad da Yusuf ya ce wa mai yin masa hidima, “Tashi, ka bi waɗannan mutane nan da nan, in ka same su, ka ce musu, ‘Me ya sa kuka sāka alheri da mugunta? Ba da wannan kwaf ne maigidana yake sha daga ciki yana kuma yin amfani da shi don duba? Wannan mugun abu ne da kuka yi.’ ”
Sa’ad da ya same su, sai ya maimaita waɗannan kalmomi gare su. Amma suka ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake faɗin irin waɗannan abubuwa? Allah yă sawwaƙe bayinka su yi irin wannan abu! Mun ma dawo maka da kuɗin da muka samu a cikin bakunan buhunanmu daga ƙasar Kan’ana. Saboda haka me zai sa mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka? In aka sami wani daga cikin bayinka da shi, zai mutu; sai sauran su zama bayin mai girma.”
Sai ya ce, “To, shi ke nan, bari yă zama yadda kuka faɗa. Duk wanda aka same shi da kwaf na azurfan zai zama bawana, sauran kuwa za su ’yantu daga zargin.”
Da sauri kowannensu ya sauko da buhunsa ƙasa, ya buɗe. Sa’an nan mai hidimar ya fara bincike, farawa daga babba, ya ƙare a ƙaramin. Aka kuwa sami kwaf ɗin a buhun Benyamin. Ganin wannan sai suka kyakkece rigunansu. Sa’an nan suka jibga wa jakunansu kaya, suka koma birni.
Yusuf yana nan har yanzu a gida sa’ad da Yahuda da ’yan’uwansa suka shiga, suka fāɗi rub da ciki a ƙasa a gabansa. Yusuf ya ce musu, “Mene ne wannan da kuka yi? Ba ku san cewa mutum kamar ni yana iya gane abubuwa ta wurin duba ba?”
Yahuda ya amsa ya ce, “Me za mu ce wa ranka yă daɗe? Yaya kuma za mu wanke kanmu daga wannan zargi? Allah ya tona laifin bayinka. Ga mu, za mu zama bayinka, da mu da wanda aka sami kwaf ɗin a hannunsa.”
Amma Yusuf ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka! Mutumin da aka sami kwaf ɗin a hannunsa ne kaɗai zai zama bawana. Sauranku, ku koma ga mahaifinku da salama.”
Sai Yahuda ya haura zuwa wurinsa ya ce, “Ranka yă daɗe, roƙo nake, bari bawanka yă yi magana da ranka yă daɗe. Kada ka yi fushi da bawanka, ko da yake daidai kake da Fir’auna kansa. Ranka yă daɗe ya tambayi bayinka ya ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan’uwa?’ Muka kuwa amsa, ‘Muna da mahaifi tsoho, akwai kuma ɗa matashi, wanda aka haifa masa cikin tsufarsa. Ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kuwa ɗa kaɗai na mahaifiyarsa da ya rage, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’
“Sai ka ce wa bayinka, ‘Ku kawo mini shi don in gan shi da kaina.’ Muka kuwa ce wa ranka yă daɗe, ‘Saurayin ba zai iya barin mahaifinsa ba, gama in ya bar shi, mahaifinsa zai mutu.’ Amma ka faɗa wa bayinka, ‘Sai kun kawo ƙaramin ɗan’uwanku tare da ku, in ba haka ba, ba za ku sāke ganin fuskata ba.’ Sa’ad da muka koma wurin bawanka mahaifinmu, sai muka faɗa masa abin da ranka yă daɗe ya ce.
“Sai mahaifinmu ya ce, ‘Ku koma ku sayo ƙarin abinci.’ Amma muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, sai in ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare da mu. Ba za mu iya ganin fuskar mutumin ba, sai ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare mu.’
“Bawanka mahaifinmu ya ce mana, ‘Kun san cewa matata ta haifa mini ’ya’ya biyu maza. Ɗayansu ya tafi daga gare ni, na kuwa ce, “Tabbatacce an yayyage shi kaca-kaca.” Ban kuwa gan shi ba tuntuni. In kun ɗauki wannan daga wurina shi ma wani abu ya same shi, za ku kawo furfura kaina zuwa kabari44.29 Da Ibraniyanci Sheol; haka kuma a aya 31. cikin baƙin ciki.’
“Saboda haka yanzu, in saurayin ba ya nan tare da mu sa’ad da na koma ga bawanka mahaifina, in kuma mahaifina, wanda ransa yana daure kurkusa da ran saurayin, ya ga cewa saurayin ba ya nan, zai mutu. Bayinka za su sa bawanka, mahaifinmu, yă mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa. Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin a wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa yă zauna a kaina a gaban mahaifina, dukan raina!’
“To, yanzu, ina roƙonka bari bawanka yă zauna a nan a matsayin bawanka, ranka yă daɗe a maimakon saurayin, a kuma bar saurayin yă koma da ’yan’uwansa. Yaya zan koma ga mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? A’a! Kada ka bari in ga baƙin cikin da zai auko wa mahaifina.”
Yusuf ya sanar da kansa
Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, “Kowa yă tashi daga gabana!” Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga ’yan’uwansa. Sai ya yi kuka da ƙarfi har Masarawa suka ji, har labarin ya kai gidan Fir’auna.
Yusuf kuwa ya ce wa ’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma ’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa.
Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar! Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka. Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba. Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto45.7 Ko kuwa cece ka kamar ƙungiya mai girma da suka tsira mai girma.
“Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar. Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta. Za ka yi zama a yankin Goshen, ka kasance kusa da ni. Kai, ’ya’yanka da kuma jikokinka, garkunanka da shanunka, da kuma dukan abin da kake da shi. Zan tanada maka a nan, domin akwai saura shekaru biyar na yunwa masu zuwa. In ba haka ba, kai da gidanka da dukan mallakarka za ku zama gajiyayyu.’
“Ku kanku kun gani, haka ma ɗan’uwana Benyamin, cewa tabbatacce ni ne nake magana da ku. Faɗa wa mahaifina game da dukan girman da aka ba ni a Masar, da kuma game da kome da kuka gani. Ku kuma kawo mahaifina a nan da sauri.”
Sa’an nan ya rungume ɗan’uwansa Benyamin ya yi kuka, sai Benyamin ya rungume shi yana kuka. Ya sumbaci dukan ’yan’uwansa, ya kuma yi kuka a kansu. Bayan haka sai ’yan’uwansa suka yi masa magana.
Sa’ad da labarin ya kai fadan Fir’auna cewa ’yan’uwan Yusuf sun zo, sai Fir’auna da dukan hafsoshin suka ji daɗi. Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Faɗa wa ’yan’uwanka, ‘Yi wannan; ku jibge dabbobinku ku koma zuwa ƙasar Kan’ana, Ku kawo mahaifinku da iyalanku zuwa wurina. Zan ba ku mafi kyau na ƙasar Masar, za ku kuwa ci moriyar ƙasar.’
“An kuma umarce ka, ka faɗa musu, ‘Ku yi wannan, ku ɗauki wagonu daga Masar domin ’ya’yanku da matanku, ku ɗauki mahaifinku ku zo. Kada ku damu da mallakarku, gama mafi kyau na Masar za su zama naku.’ ”
Sai ’ya’yan Isra’ila maza suka yi haka. Yusuf ya ba su wagonu kamar yadda Fir’auna ya umarta, ya kuma ba su guzuri don tafiyarsu. Ya ba da sababbin riguna ga kowannensu amma ga Benyamin ya ba shi shekel45.22 Wato, kamar fam bakwai da rabi (kamar kilo 3.5) ɗari uku na azurfa da riguna kashi biyar. Ga kuma abin da ya aika wa mahaifinsa, jakuna goma da aka jibge da abubuwa mafi kyau na Masar, da jakuna mata guda goma ɗauke da hatsi da burodi da waɗansu tanade-tanade don tafiyarsa. Sa’an nan ya sallami ’yan’uwansa, yayinda suke barin wurin ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya!”
Saboda haka suka haura, suka fita daga Masar, suka zo wurin maihaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana. Suka faɗa masa, “Yusuf yana da rai! Gaskiya, shi ne mai mulkin dukan Masar.” Gaban Yaƙub ya fāɗi, domin bai gaskata su ba. Amma sa’ad da suka faɗa masa kome da Yusuf ya faɗa musu, da kuma sa’ad da ya ga wagonun da Yusuf ya aika don a ɗauke shi a kai da shi can, sai ya farfaɗo, ya dawo cikin hankalinsa. Sai Yaƙub ya ce, “Na yarda! Ɗana Yusuf yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”
Yaƙub ya tafi Masar
Saboda haka Isra’ila ya kama hanya da dukan abin da yake nasa, sa’ad da ya kai Beyersheba, sai ya miƙa hadayu ga Allah na Ishaku, mahaifinsa.
Allah kuwa ya yi magana ga Isra’ila a wahayi da dare ya ce, “Yaƙub! Yaƙub!”
Yaƙub kuwa ya amsa ya ce, “Ga ni.”
Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama zan mai da kai al’umma mai girma a can. Zan gangara zuwa Masar tare da kai, tabbatacce zan sāke dawo da kai. Kuma hannun Yusuf zai rufe idanunka.”
Sa’an nan Yaƙub ya bar Beyersheba, ’ya’yan Isra’ila maza, suka ɗauki mahaifinsu Yaƙub da ’ya’yansu da matansu a cikin wagonun da Fir’auna ya aika don a kawo shi. Suka kuma ɗauki dabbobinsu da mallakarsu, da suka samu a Kan’ana, Yaƙub kuwa da dukan zuriyarsa suka tafi Masar. Ya ɗauki ’ya’yansa maza da jikokinsa da ’ya’yansa mata da jikokinsa mata, dukan zuriyarsa zuwa Masar.
Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza (Yaƙub da zuriyarsa) waɗanda suka tafi Masar,
Ruben ɗan farin Yaƙub.
’Ya’yan Ruben maza su ne,
Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
’Ya’yan Simeyon maza su ne,
Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana.
’Ya’yan Lawi maza su ne,
Gershon, Kohat da Merari.
’Ya’yan Yahuda maza su ne,
Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana).
’Ya’yan Ferez maza su ne,
Hezron da Hamul.
’Ya’yan Issakar maza su ne,
Tola, Fuwa,46.13 Fentatut na Samariya da na Assuriya (dubi kuma 1Tar 7.1); Rubuce-rubucen Masoretik na da Fuwa ne. Yoshub46.13 Fentatut na Samariya da waɗansu Seftuwajin (dubi Ƙid 26.24 da 1Tar 7.1); rubuce-rubucen Masoretik. da Shimron.
’Ya’yan Zebulun maza su ne,
Sered, Elon da Yaleyel.
Waɗannan su ne ’ya’yan Liyatu maza da ta haifa wa Yaƙub a Faddan Aram,46.15 Wato, arewa maso yamman Mesofotamiya ban da ’yarsa Dina. ’Ya’yansa maza da mata duka, mutum talatin da uku ne.
’Ya’yan Gad maza su ne,
Zafon,46.16 Fentatut Samariya da Seftuwajin (dubi kuma Ƙid 26.15); rubuce-rubucen Masoretik Zifiyon. Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi da Areli.
’Ya’yan Asher maza su ne,
Imna, Ishba, Ishbi da Beriya. ’Yar’uwarsu ita ce Sera.
’Ya’yan Beriya maza su ne,
Heber da Malkiyel.
Waɗannan su ne ’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Liyatu. ’Ya’yan duka, su sha shida ne.
’Ya’yan Yaƙub maza waɗanda Rahila ta haifa su ne,
Yusuf da Benyamin.
A Masar, Asenat ’yar Fotifera, firist na On46.20 Wato, Heliyofolis ta haifi Manasse da Efraim wa Yusuf.
’Ya’yan Benyamin maza su ne,
Bela, Beker, Ashbel, Gera, Na’aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim da Ard.
Waɗannan su ne ’ya’yan Rahila maza waɗanda ta haifa wa Yaƙub, dukansu mutum goma sha huɗu ne.
Yaron Dan shi ne,
Hushim.
’Ya’yan Naftali maza su ne,
Yazeyel, Guni, Yezer da Shillem.
Waɗannan su ne ’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa ’yarsa Rahila. ’Ya’yan suka su bakwai ne.
Dukan waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub, waɗanda suke zuriyarsa kai tsaye ban da matan ’ya’yansa maza, su mutum sittin da shida ne. In aka haɗa da ’ya’yan nan maza46.27 Da Ibraniyanci; Seftuwajin, yara tara guda biyu waɗanda aka haifa wa Yusuf a Masar, membobin iyalin Yaƙub, waɗanda suka tafi Masar, duka su saba’in46.27 Da Ibraniyanci (dubi kuma Fit 1.5 da kuma fassara ƙasar shafi); Seftuwajin (dubi kuma Ayy M 7.14) saba’in da biyar. ne.
To, Yaƙub ya aiki Yahuda yă yi gaba yă sadu da Yusuf, don yă nuna musu hanyar da za su bi zuwa yankin Goshen. Da suka isa yankin Goshen, sai Yusuf ya kintsa keken yaƙinsa ya haura zuwa Goshen don yă taryi mahaifinsa, Isra’ila. Nan da nan da isowar Yusuf a wurin mahaifinsa, sai ya rungumi mahaifinsa46.29 Da Ibraniyanci kewaye da shi., ya yi kuka na dogon lokaci.
Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Yanzu ina a shirye in mutu, da yake na gani da kaina cewa har yanzu kana da rai.”
Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa da gidan mahaifinsa, “Zan haura in yi magana da Fir’auna, zan kuwa ce masa, ‘’Yan’uwana da gidan mahaifina, waɗanda suke zaune a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina. Mutanen fa, makiyaya ne; suna kiwon dabbobi, sun kuma zo tare da garkunansu da shanunsa da kuma kome da suka mallaka.’ Sa’ad da Fir’auna ya kira ku ciki, ya yi tambaya, ‘Mece ce sana’arku?’ Ku amsa, ‘Bayinka suna kiwon dabbobi ne, tun muna samari har zuwa yanzu, kamar yadda kakanninmu suka yi.’ Ta haka za a bar ku ku zauna a yankin Goshen, gama Masarawa suna ƙyamar makiyaya.”
Yusuf ya tafi yă faɗa wa Fir’auna, “Mahaifina da ’yan’uwana, tare da garkunansu da shanunsu da kome da suke da shi, sun zo daga ƙasar Kan’ana, suna kuwa a Goshen yanzu.”
Sai ya zaɓi mutum biyar daga cikin ’yan’uwansa, ya gabatar da su a gaban Fir’auna.
Fir’auna ya tambayi ’yan’uwan, “Mece ce sana’arku?”
Suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Bayinka makiyaya ne, kamar yadda kakanninmu suke.” Suka kuma ce masa, “Mun zo, mu zauna a nan na ɗan lokaci, gama yunwa ta yi tsanani a Kan’ana, dabbobin bayinka kuma ba su da wurin kiwo. Saboda haka yanzu, muna roƙonka, bari bayinka su zauna a Goshen.”
Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Mahaifinka da ’yan’uwanka sun zo maka, ƙasar Masar kuma tana gabanka, ka zaunar da mahaifinka da ’yan’uwanka a sashe mafi kyau na ƙasar, bari su zauna a Goshen. Idan kuma ka ga waɗansu a cikinsu da suka fi dacewa, sai ka sa su lura mini da shanuna.”
Sa’an nan Yusuf ya shigar da Yaƙub mahaifinsa, ya gabatar da shi a gaban Fir’auna. Bayan Yaƙub ya albarkaci47.7 Ko kuwa gai da Fir’auna, sai Fir’auna ya tambaye shi, “Shekarunka nawa da haihuwa?”
Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.” Sai Yaƙub ya albarkaci47.10 Ko kuwa ya yi bankwana da Fir’auna, ya yi masa bankwana, sa’an nan ya fita.
Ta haka Yusuf ya zaunar da mahaifinsa da ’yan’uwansa a Masar, ya ba su mallaka a sashe mafi kyau na ƙasar, a yankin nan na Rameses, kamar yadda Fir’auna ya umarta. Yusuf ya kuma tanada wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa da dukan gidan mahaifinsa, abinci bisa ga yawan ’ya’yansu.
Hidimar Yusuf a lokacin yunwa
A yanzu, a cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwa ta yi tsanani ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka shiga matsananciyar wahala! Yusuf ya tattara dukan kuɗaɗen da suke a Masar da Kan’ana don biyan hatsin da suke saya, ya kuwa kawo su a fadan Fir’auna. Sa’ad da kuɗin mutanen Masar da Kan’ana suka ƙare, dukan Masar ta zo wurin Yusuf ta ce, “Ka ba mu abinci. Me zai sa mu mutu a idanunka? Kuɗinmu duk sun ƙare.”
Yusuf ya ce, “To, ku kawo dabbobinku, zan sayar muku da abinci a madadin dabbobinku, tun da kuɗinku ya ƙare.” Saboda haka suka kawo dabbobinsu wa Yusuf, ya kuma ba su abinci a madadin dawakai, tumaki da awaki, shanu da jakunansu. Ya kuwa ba su abinci a madadin dabbobinsu, a wannan shekara.
Sa’ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biye suka ce, “Ba za mu ɓoye maka ba ranka yă daɗe, kuɗinmu sun ƙare, dabbobinmu kuma sun zama naka. Ranka yă daɗe, in ban da jikunanmu da gonakinmu, ba abin da ya rage mana. Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakinmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna. Ka ba mu iri don mu rayu, kada mu mutu, don kuma kada gonakin ƙasarmu su zama kango.”
Ta haka Yusuf ya saya wa Fir’auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da gonakinsu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama mallakar Fir’auna. Yusuf kuwa ya mai da mutanen bayi47.21 Fentatut da Seftuwajin (dubi kuma Bulget); Masoretik ya kai mutane zuwa birane., daga wannan iyakar Masar zuwa wancan. Amma bai sayi gonakin firistoci ba, gama suna karɓa rabo daga Fir’auna ne, suna kuma da isashen abinci daga rabon da Fir’auna yake ba su. Dalilin ke nan da ba su sayar da gonakinsu ba.
Yusuf ya ce wa mutane, “Yanzu da na saye ku da kuma gonakinku a yau wa Fir’auna, ga iri don ku shuka a gonaki. Amma sa’ad da hatsi suka nuna, za ku ba da kashi ɗaya bisa biyar ga Fir’auna. Sauran kashi huɗu bisa biyar kuma ku riƙe a matsayin iri don gonaki da kuma abinci wa kanku da gidajenku da kuma ’ya’yanku.”
Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ya gamshe ka, ranka yă daɗe, za mu zama bayin Fir’auna.”
Ta haka Yusuf ya kafa wannan ya zama doka game da ƙasa a Masar, har yă zuwa yau cewa kashi ɗaya bisa biyar na amfani gona ya zama na Fir’auna. Gonakin firistoci ne kaɗai ba su zama na Fir’auna ba.
To, Isra’ilawa suka zauna a Masar a yankin Goshen. Suka mallaki filaye a can, suka riɓaɓɓanya suka ƙaru ƙwarai.
Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai. Sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, sai ya kira ɗansa Yusuf, ya ce masa, “Ka yi mini wannan alheri, ka sa hannunka ƙarƙashin cinyar ƙafata, ka yi mini alkawari saboda ina roƙonka kaɗa ka bizne ni a Masar, amma sa’ad da na huta da kakannina, ka ɗauke ni, ka fid da ni daga Masar, ka binne ni a inda aka binne su.”
Yusuf ya ce, “Zan yi yadda ka faɗa.”
Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini.” Sai Yusuf ya rantse masa, Isra’ila kuwa ya yi godiya ga Allah yayinda ya jingina a kan sandansa.47.31 Ko kuwa Isra’ila ya rusuna a kan gadonsa
Manasse da Efraim
Bayan wani lokaci aka faɗa wa Yusuf, “Mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki ’ya’yansa maza biyu, Manasse da Efraim suka tafi tare da shi. Sa’ad da aka faɗa wa Yaƙub, “Ɗanka Yusuf ya zo gare ka,” sai Isra’ila ya ƙoƙarta ya tashi ya zauna a kan gado.
Yaƙub ya ce wa Yusuf, “Allah Maɗaukaki48.3 Da Ibraniyanci El-Shaddai ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana, a can ya albarkace ni ya kuma ce mini, ‘Zan sa ka yi ta haihuwa ka kuma riɓaɓɓanya, za ka ƙaru a yawa. Zan mai da kai al’ummar mutane, zan kuma ba ka wannan ƙasa tă zama madawwamiyar mallaka ga zuriyarka a bayanka.’
“To, yanzu, ’ya’ya mazanka biyu da aka haifa maka a Masar kafin in zo a nan za su zama nawa; Efraim da Manasse za su zama nawa, kamar yadda Ruben da Simeyon suke nawa. Duk waɗansu ’ya’yan da aka haifa maka bayansu za su zama naka; a yankin da suka gāda za a lissafa a ƙarƙashin sunayen ’yan’uwansu. Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram,48.7 Wato, arewa maso yamman Mesofotamiya cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem).
Sa’ad da Isra’ila ya ga ’ya’yan Yusuf maza, sai ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan?”
Yusuf ya ce wa mahaifinsa, “Su ne ’ya’yan da Allah ya ba ni a nan.”
Sa’an nan Isra’ila ya ce, “Kawo mini su saboda in albarkace su.”
Yanzu fa idanun Isra’ila sun fara rasa ƙarfi saboda tsufa, har ba ya iya gani sosai. Saboda haka Yusuf ya kawo ’ya’yansa maza kusa da shi, sai mahaifinsa ya sumbace su ya rungume su.
Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ban yi tsammani zan ga fuskarka kuma ba, yanzu kuwa Allah ya bar ni in ga ’ya’yanka su ma.”
Sa’an nan Yusuf ya ɗauke su daga gwiwoyin Isra’ila ya rusuna da fuskarsa har ƙasa. Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi. Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.
Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce,
“Bari Allah a gaban wanda kakannina
Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya,
Allahn da ya zama makiyayina
dukan raina zuwa wannan rana,
Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta
bari yă albarkaci samarin nan.
Bari a kira su da sunana
da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku
bari kuma su ƙaru ƙwarai
a bisa duniya.”
Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse. Yusuf ya ce masa, “A’a, mahaifina, wannan shi ne ɗan farin; ka sa hannunka na dama a kansa.”
Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.” Ya albarkace su a wannan rana ya ce,
“A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka
‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ”
Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.
Sa’an nan Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ina gab da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku Kuma gare ka, a matsayi wanda yake kan ’yan’uwanka, na ba da gonar da na karɓe daga Amoriyawa da takobi da kuma bakana.”
Yaƙub ya albarkaci ’ya’yansa maza
Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.
“Ku tattaru, ku saurara, ’ya’yan Yaƙub maza;
ku saurari mahaifinku, Isra’ila.
“Ruben, kai ne ɗan farina,
ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina,
mafi matsayi, kuma mafi iko.
Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba,
gama ka hau gadon mahaifinka
ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.
“Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne,
takubansu makamai ne na tā da hankali.
Ba zan shiga shawararsu ba,
ba zan shiga taronsu ba,
gama sun kashe maza cikin fushinsu
cikin ganin dama suka kashe bijimai.
La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai,
hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai!
Zan warwatsa su cikin Yaƙub
in kuma daidaita su cikin Isra’ila.
“Yahuda,49.8 Yahuda ya yi kamar ya fito daga Ibraniyanci na yabo ne. ’yan’uwanka za su yabe ka;
hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka,
’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.
Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda,
ka dawo daga farauta, ɗana.
Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe,
kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?
Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba,
ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba,
sai ya zo ga wanda yake mai shi49.10 Ko kuwa sai Shilo ya zo; ko kuwa sai ya zo ga girma ya dace..
Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.
Zai daure jakinsa a kuringa,
aholakinsa a rassa mafi kyau;
zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi
rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.
Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi,
haƙorarsa farare kamar madara.49.12 Ko kuwa zai zama marar walƙiya daga ruwan inabi, haƙorarsa farare daga madara
“Zebulun zai zauna a bakin teku,
yă zama tasar jiragen ruwa;
iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.
“Issakar doki49.14 Ko kuwa mai ƙarfi mai ƙarfi,
kwance tsakanin buhunan sirdi.49.14 Ko kuwa sansanin wuta
Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau
da kuma daɗin da ƙasarsa take,
zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyi
yă miƙa kai ga aikin dole.
“Dan49.16 Dan a nan yana nufin yakan tanada adalci. zai tanada adalci wa mutanensa
kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.
Dan zai zama maciji a gefen hanya,
kububuwa a bakin hanya,
da take saran ɗiɗɗigen doki
domin mahayinsa yă fāɗi da baya.
“Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.
“Masu fashi za su fāɗa wa Gad,49.19 Gad na iya nufin fāɗawa da kuma ƙungiyar mahara.
amma zai runtume su.
“Abincin Asher zai zama a wadace,
zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki.
“Naftali sakakkiyar barewa ce
da take haihuwar kyawawan ’ya’ya.49.21 Ko kuwa yakan faɗa kyawawan kalmomi
“Yusuf kuringa ce mai ba da amfani.
Kuringa mai ba da amfani kusa da rafi
wadda rassanta na hawan bango.49.22 Ko kuwa Yusuf aholakin jeji ne, aholakin jeji kusa da rafi, jakin jeji a tudun mai kunyoyi
Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa;
suka harbe shi babu tausayi.
Amma bakansa yana nan daram
hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa49.23,24 Ko kuwa mahara za su fāɗa, za su harba, za su rage, za su tsaya
saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub,
saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,
saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka,
saboda Maɗaukaki,49.25 Da Ibraniyanci Shaddai wanda yake albarkace ka
da albarkar sama da take bisa
albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa
albarkun mama da kuma mahaifa.
Albarkun mahaifi suna da girma fiye
da albarkun daɗaɗɗun duwatsu
fiye49.26 Ko kuwa kakana, mai girma kamar da yalwar madawwaman tuddai.
Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf,
a goshin ɗan sarki a cikin49.26 Ko kuwa wanda aka raba da ’yan’uwansa.
“Benyamin kyarkeci ne mai kisa;
da safe yakan cinye abin da ya farauto
da yamma yakan raba ganima.”
Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.
Mutuwar Yaƙub
Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti, kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu. Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.”49.32 Ko kuwa ’ya’ya mazan Het
Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga ’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.
Yusuf kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya kuma sumbace shi. Sa’an nan Yusuf ya umarci masu maganin da suke yin masa hidima, su shafe mahaifinsa Isra’ila da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe shi da maganin hana ruɓa. Suka ɗauki kwana arba’in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi makoki dominsa kwana saba’in.
Sa’ad da kwanakin makoki suka wuce, sai Yusuf ya ce wa iyalin gidan Fir’auna, “In na sami tagomashi a idanunku, ku yi magana da Fir’auna domina. Ku faɗa masa, ‘Mahaifina ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, “Ina gab da mutuwa, ka binne ni a kabarin da na haƙa wa kaina a ƙasar Kan’ana.” Yanzu fa bari in haura in binne mahaifina, sa’an nan in dawo.’ ”
Fir’auna ya ce, “Haura ka binne mahaifinka, kamar yadda ya sa ka rantse za ka yi.”
Saboda haka Yusuf ya haura don yă binne mahaifinsa. Dukan hafsoshin Fir’auna suka yi masa rakiya tare da manyan mutanen gidan Fir’auna, da kuma dukan manyan mutanen Masar da kuma dukan membobin gidan Yusuf, da ’yan’uwansa da kuma waɗanda suke na gidan mahaifinsa. Yara kaɗai da garkunansu da kuma shanunsu ne aka bari a Goshen. Kekunan yaƙi da mahayan dawakai50.9 Ko kuwa mahayan kekunan yaƙi su ma suka haura tare da shi. Babbar ƙungiya jama’a ce ƙwarai.
Sa’ad da suka kai masussukar Atad, kusa da Urdun, sai suka yi kuka da ƙarfi da kuma mai zafi, a can Yusuf ya yi makoki kwana bakwai saboda mahaifinsa. Sa’ad da Kan’aniyawa waɗanda suke zama a can suka ga makokin a masussukan Atad, sai suka ce, “Masarawa suna bikin makoki na musamman.” Shi ya sa ake kira wannan wurin da yake kusa da Urdun, Abel-Mizrayim.50.11 Abel-Mizrayim yana nufin makokin Masarawa.
Haka fa ’ya’yan Yaƙub maza suka yi yadda ya umarce su. Suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan’ana suka kuma binne shi a kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, ya zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. Bayan ya binne mahaifinsa, sai Yusuf ya koma Masar, tare da ’yan’uwansa da kuma dukan waɗanda suka tafi tare da shi don binne mahaifinsa.
Yusuf ya sāke ba wa ’yan’uwansa tabbaci
Sa’ad da ’yan’uwan Yusuf suka ga cewa mahaifinsu ya mutu, sai suka ce, “Mai yiwuwa Yusuf yana riƙe da mu a zuciya, wataƙila zai rama dukan abubuwa marasa kyau da muka yi masa?” Saboda haka suka aika wa Yusuf suna cewa, “Mahaifinka ya bar waɗannan umarnai kafin yă rasu. Ga abin da za ku ce wa Yusuf, ‘Na roƙe ka, ka gafarta wa ’yan’uwanka zunubai da laifofin da suka aikata na abubuwa marasa kyau da suka yi maka.’ Yanzu muna roƙonka ka gafarta zunuban bayin Allah na mahaifinka.” Sa’ad da saƙonsu ya zo masa, sai Yusuf ya yi kuka.
’Yan’uwansa kuwa suka zo suka fāɗi a gabansa suka ce, “Mu bayinka ne.”
Amma Yusuf ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Ni Allah ne? Kun yi niyya ku yi mini lahani, amma Allah ya nufe wannan ya zama alheri don yă cika abin da yanzu yake faruwa, ceton rayuka masu yawa. Saboda haka, kada ku ji tsoro. Zan tanada muku da kuma ’ya’yanku.” Ya sāke tabbatar musu, ya kuma yi musu magana ta alheri.
Mutuwar Yusuf
Yusuf ya zauna a Masar tare da dukan iyalin mahaifinsa. Ya rayu shekara ɗari da goma. Ya kuma ga tsara ta uku ta ’ya’yan Efraim. Haka ma ’ya’yan Makir ɗan Manasse, an haife su aka sa a gwiwoyin Yusuf.50.23 Wato aka ɗauka su kamar nasa.
Sai Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ina gab da mutuwa. Amma tabbatacce Allah zai taimake ku, yă fid da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.” Yusuf kuwa ya sa ’ya’yan Isra’ila maza suka yi rantsuwa, ya kuma ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, ku kuma dole ku ɗauki ƙasusuwana, ku haura da su daga wannan wuri.”
Yusuf kuwa ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Bayan an shafe shi da maganin hana ruɓa, sai aka sa shi a akwatin gawa a Masar.