- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Galatiyawa
Galatiyawa
Galatiyawa
Gal
Galatiyawa
Bulus manzo, aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da kuma Allah Uba, wanda ya tā da Yesu daga matattu. Dukan ’yan’uwan kuma da suke tare da ni a nan,
Suna gai da ikkilisiyoyi a Galatiya.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.
Babu wata bishara
Ina mamaki yadda kuka yi saurin yashe wanda ya kira ku ta wurin alherin Kiristi, kuna juyewa ga wata bishara dabam wadda a gaskiya ba bishara ba ce ko kaɗan. Tabbatacce waɗansu mutane suna birkitar da ku, suna kuma ƙoƙari su karkatar da bisharar Kiristi. Amma ko mu, ko mala’ika daga sama ya yi wa’azin wata bishara dabam da wadda muka yi muku, bari yă zama la’ananne har abada! Kamar yadda muka riga muka faɗa, haka yanzu ma ina ƙara cewa in wani yana muku wa’azin wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, bari yă zama la’ananne har abada!
Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba.
Bulus kirayaye na Allah
Ina so ku sani ’yan’uwa, cewa bisharar da nake wa’azi, ba mutum ne ya ƙago ta ba. Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne.
Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta. Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin al’adun kakannina. Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa1.15 Ko kuwa daga cikin mahaifiyata ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba. Ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na hanzarta na tafi ƙasar Arabiya, daga baya sai na koma Damaskus.
Bayan shekara uku, sai na haura zuwa Urushalima domin in sadu da Bitrus1.18 Girik Kefas, na kuwa zauna tare da shi kwana goma sha biyar. Ban ga wani a ciki sauran manzanni ba, sai dai Yaƙub ɗan’uwan Ubangiji. Ina tabbatar muku a gaban Allah cewa abin da nake rubuta muku ba ƙarya ba ne.
Daga baya sai na tafi Suriya da Silisiya. Ikkilisiyoyin da suke cikin Kiristi da suke a Yahudiya ba su san ni ba tukuna. Sun dai sami labari ne kawai cewa, “Mutumin da dā yake tsananta mana yanzu yana wa’azin bangaskiyar da dā ya yi ƙoƙari yă hallaka.” Sai suka yabi Allah saboda ni.
Manzanni sun karɓi Bulus
Bayan shekara goma sha huɗu sai na sāke haurawa zuwa Urushalima, a wannan lokaci na tafi tare da Barnabas. Na kuma ɗauki Titus muka tafi tare. Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Da na kai can, sai na bayyana musu bisharar da nake wa’azi a cikin Al’ummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yă zama a banza. Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi mutumin Al’ummai ne. Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu ’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi. Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku.
Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba. A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai,2.7 Girik marasa kaciya kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa.2.7 Girik masu kaciya; haka ma a ayoyi 8 da kuma 9 Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai. Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa. Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.
Bulus ya tsawata wa Bitrus
Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake. Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Al’ummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Al’ummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya. Sauran Yahudawa suka haɗa kai da shi a munafuncinsa har Barnabas ma ya bauɗe.
Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa?
“Mu da muke Yahudawa ta wurin haihuwa ba Al’ummai masu zunubi ba, mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka.
“In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Kiristi, sa’an nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Kiristi yana ƙarfafa zunubi ke nan? A’a, ko kusa! In na sāke gina abin da na rushe, na zama mai karyar Doka ke nan.
“Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah. An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina. Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!”
Bangaskiya ko kiyaye doka
Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari. Zan so in san abu guda tak daga gare ku. Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji? Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Bayan kun fara da Ruhu, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa? Ashe, wahaloli dabam-dabam da kuka sha sun zama a banza ke nan? Haka zai yiwu kuwa? Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne? Ku dubi Ibrahim mana, “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.”3.6 Far 15.6
Ku sani fa, waɗannan waɗanda suka gaskata, ’ya’yan Ibrahim ne. Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Al’ummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yă yi cewa, “Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinka.”3.8 Far 12.3; Far 18.18; Far 22.18 Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya.
Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”3.10 M Sh 27.26 A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”3.11 Hab 2.4 Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”3.12 Fir 18.5 Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.”3.13 M Sh 21.23 Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.
Doka da kuma alkawari
’Yan’uwa, bari in yi muku misali da rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar dai yadda ba mai kawarwa ko yă ƙara wani abu cikin alkawarin da mutane suka kafa, haka yake a wannan batu. Alkawaran nan fa ga Ibrahim ne aka faɗa da kuma wani zuriyarsa. Nassi bai ce, “da zuriyoyi ba” wanda ya nuna kamar mutane da yawa, amma “ga zuriyarka,”3.16 Far 12.7; Far 13.15; Far 24.7 wanda yake nufin mutum ɗaya, wanda shi ne Kiristi. Abin da nake nufi shi ne, Dokar da aka shigar ita bayan shekaru 430, ba tă kawar da alkawarin da Allah ya yi tun dā ba. Gama da a ce gādon yă dangana a kan doka ne, ai, da ba zai dangana a kan alkawari ba; amma Allah cikin alherinsa ya ba wa Ibrahim gādon ta wurin alkawari.
To, don me aka kawo Doka? An yi ƙari da Doka ne don fitowa da laifi fili har kafin na zuriyan nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an ba da doka ta wurin mala’iku ne, aka kuma danƙa ta a hannun matsakanci. Kuma akan bukaci wani a tsakani ne idan da mutum biyu ake zance, Allah kuwa ɗaya ne.
To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, tabbatacce, da sai a sami adalci ta wurin Doka. Amma Nassi ya kulle kome a ƙarƙashin ikon zunubi, domin abin da aka yi alkawarin nan, da ake bayar ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata.
’Ya’yan Allah
Kafin bangaskiyan nan tă zo, mun kasance a daure a kurkuku a ƙarƙashin Doka, a kulle sai da bangaskiyar da za tă zo ta bayyana. Ta haka aka sa Dokar ta zama jagorarmu zuwa ga Kiristi don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya. Yanzu da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a ƙarƙashin Doka.
Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan. Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu. In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.
Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome. Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa. Haka yake, sa’ad da muke ’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya. Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya. Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba,4.6 Arameyik na Mahaifi Uba.” Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.
Damuwar Bulus domin Galatiyawa
Dā da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda a ainihi ba alloli ba ne. Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne? Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokuta da shekaru na musamman! Kai, kun ba ni tsoro, don ya zama kamar duk wahalar da na yi a kanku banza ne!
Ina roƙonku ’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba. Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko. Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa. Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni. Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?
Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su. Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba. Ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku. Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku!
Saratu da Hagar
Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba ne? Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ’ya’ya biyu maza, ɗaya ta wurin mace ’yar aikin gidansa, ɗaya kuma ta wurin ainihin matarsa. Ɗansa na wajen mace ’yar aikin gidansa ya zo bisa ga ƙa’idar jiki ne; amma ɗansa na wajen ainihin matarsa ya zo a sakamakon alkawarin ne.
Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan. Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ’ya’yanta. Amma Urushalimar da take sama ’yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu. Gama a rubuce yake cewa,
“Ki yi farin ciki, ya ke bakararriya,
wadda ba ta haihuwa
ki ɓarke da murna, ki kuma tā da murya,
ke da ba kya naƙuda;
domin da yawa ne ’ya’yan macen da aka yashe,
fiye da na mai miji.”4.27 Ish 54.1
To, ku ’yan’uwa, ku ’ya’yan alkawari ne kamar Ishaku. A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu. Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan ’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace ’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.”4.30 Far 21.10 Saboda haka, ’yan’uwa, mu ba ’ya’yan mace ’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.
’Yanci cikin Kiristi
Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta.
Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kuka yarda aka yi muku kaciya, wannan ya nuna Kiristi ba shi da amfani a gare ku ba ko kaɗan. Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yă kiyaye dukan Doka. Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi ke nan; kuka kuma fāɗi daga alheri. Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu. Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.
Kun yi tsere mai kyau a dā. Wa ya shige gabanku ya hana ku bin gaskiya? Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne. “Ɗan yisti kaɗan ne yake gama dukan curin burodi.” Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne. ’Yan’uwa, da a ce har yanzu ina wa’azin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan. Da ma a ce masu tā da hankalinku ɗin nan su yanke gabansu gaba ɗaya mana!
Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka5.13 Ko kuwa na jiki; haka ma a ayoyi 16, 17, 19 da 24 a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna. Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”5.14 Fir 19.18 In kun ci gaba da cizo, kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna.
Rayuwa ta wurin Ruhu
Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba. Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so. Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku a ƙarƙashin Doka ke nan.
Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.
Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa. Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa. Da yake muna rayuwa ta Ruhu ne, bari mu ci gaba da al’amuranmu ta wurin Ruhu. Kada mu zama masu girman kai, muna tsokana muna kuma jin kishin juna.
Yin alheri ga kowa
’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba. Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi. In wani yana tsammani shi wani abu ne alhali kuwa shi ba kome ba, ruɗin kansa yake yi. Kowa yă auna ayyukansa. A sa’an nan ne zai iya yin taƙama da kansa, ba tare da kwatanta kansa da wani ba, gama kowa zai ɗauki kayansa. Duk haka, wanda aka koya wa maganar Kiristi, bari yă raba abubuwan nan na alheri tare da wanda ya koyar da shi.
Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami. Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba. Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.
Ba kaciya ba, sai dai sabuwar halitta
Ku dubi irin manya-manyan harufan da na yi amfani da su yayinda nake rubuta muku da hannuna!
Waɗanda suke son nuna bajinta a fili suna ƙoƙari su tilasta muku ku yi kaciya ne. Dalilin kaɗai da suke yin haka shi ne don gudu kada a tsananta musu saboda gicciyen Kiristi ne. Kai, su masu kaciya ma ba su kiyaye Doka ba, duk da haka suna so a yi muku kaciya don su yi taƙama kan an yi muku kaciya. Kada in taɓa yin taƙama ga kome sai dai a cikin gicciyen Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa aka gicciye duniya a gare ni, aka kuma gicciye ni ga duniya. Kaciya ko rashin kaciya ba wani abu ba ne; abin da yake da amfani shi ne sabuwar halitta. Salama da jinƙai su tabbata ga dukan waɗanda suke bin wannan ƙa’ida, har ma ga Isra’ila na Allah.
A ƙarshe, kada kowa yă ƙara damuna, gama ina ɗauke da raunuka masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu ne.
’Yan’uwa! Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ruhunku. Amin.