- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Ezekiyel
Ezekiyel
Ezekiyel
Ezk
Ezekiyel
Halittu masu rai da kuma ɗaukakar Ubangiji
A1.1 Ko kuwa nawa shekara ta talatin, a wata na huɗu a rana biyar, yayinda nake cikin ’yan zaman bauta kusa da Kogin Kebar, sai sammai suka buɗe na kuwa ga wahayoyin Allah.
A rana biyar ga wata, a shekara ta biyar ne ta zaman bautan Sarki Yehohiyacin, maganar Ubangiji ta zo wa Ezekiyel firist, ɗan Buzi,1.3 Ko kuwa Ezekiyel ɗan Buzi firist kusa da Kogin Kebar a ƙasar Babiloniyawa.1.3 Ko kuwa Kaldiyawa A can hannun Ubangiji yana a kansa.
Na duba, sai na ga guguwa ta taso daga arewa babban hadari cike da walƙiya kewaye da haske mai haske sosai. Tsakiyar wutar ta yi kamar ƙarfe mai cin wuta balbal, a cikin wutar kuwa akwai abin da ya yi kamar halittu guda huɗu. A bayyane kamanninsu ya yi kamar siffar mutum, amma kowannensu yana da fuskoki huɗu da fikafikai guda huɗu. Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne; kuma ƙafafunsu sun yi kamar na maraƙi suna kuma walƙiya kamar tagullar da aka goge. A ƙarƙashin fikafikansu huɗu suna da hannuwan mutum a kowane gefe. Dukansu huɗu suna da fuskoki da fikafikai, kuma fikafikansu suna taɓan juna. Kowanne ya miƙe gaba; ba sa juyawa sa’ad da suke tafiya.
Fuskokinsu sun yi kamar haka. Kowanne a cikin huɗun yana da fuskar mutum, kuma a gefen dama kowanne yana da fuskar zaki, a hagu kuma fuskar maraƙi; kowanne yana kuma da fuskar gaggafa. Haka fuskokinsu suka kasance. Fikafikansu sun buɗu sama; kowanne yana da fikafikai biyu, ɗaya yana taɓa fikafikan ɗayan halittar a ɗayan gefe, fikafikai biyu kuma suna rufe jikinsa. Kowanne ya miƙe gaba sosai. Duk inda ruhu zai tafi, can za su, ba tare da juyawa ba yayinda suke tafiya. Kamannin halittun ya yi kamar garwashi mai cin wuta ko kuwa kamar fitilu. Wuta tana kai da kawowa a cikin halittun; ta yi haske ƙwarai, walƙiya kuma tana wulgawa daga cikinta. Halittun suna gaggauta kai da kawowa kamar walƙiya.
Yayinda nake kallon rayayyun halittun nan, sai na ga da’ira a ƙasa kusa da kowace halitta da fuskokinsa huɗu. Ga kamanni da fasalin da’irorin. Suna ƙyalƙyali kamar kirisolit, kuma dukan huɗun sun yi kama da juna. Kowacce ta yi kamar da’ira a cikin da’ira. Yayinda suke tafiya, sukan nufi duk wani gefe guda cikin gefe huɗun da halittun suka nufa; da’irorin ba za su juya ba sa’ad da halittun suke tafiya. Ƙarafansu da suka yi kamar zobe sun yi tsayi suna kuma da bantsoro, dukan ƙarafan nan huɗu kuwa da suka yi kamar zobe suna cike da idanu a kewaye.
Sa’ad da rayayyun halittun suke tafiya, da’irorin da suke kusa da su kan motsa; kuma sa’ad da rayayyun halittun sun tashi sama, da’irorin su ma sukan tashi sama. Duk inda ruhu za shi, su ma can za su, kuma da’irorin za su tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun nan yana a cikin da’irorin. Sa’ad da halittun sun motsa, sai su ma su motsa; sa’ad da halittun sun tsaya cik, su ma sai su tsaya cik, sa’ad da kuma halittun sukan tashi sama, da’irorin suka tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun nan yana a cikin da’irorin.
A bisa kawunan rayayyun halittun nan akwai abin da ya yi kamar ƙanƙara, mai bantsoro. A ƙarƙashin al’arshin fikafikansu sun miƙe kyam ɗaura da juna, kuma kowanne yana da fikafikai biyu da suka rufe jikinsa. Sa’ad da halittun suke tafiya, sai na ji ƙarar fikafikansu, kamar rurin ruwaye masu gudu, kamar muryar Maɗaukaki,1.24 Da Ibraniyanci Shaddai kamar hayaniyar rundunar mayaƙa. In sun tsaya cik, sukan sauko da fikafikansu.
Sai aka ji murya daga al’arshi a kan kawunansu yayinda suke tsaye da fikafikansu a sauke. A bisa al’arshin a kan kawunansu akwai abin da ya yi kamar saffaya,1.26 Ko kuwa lafis lazuli kuma a can bisa a kan kursiyin akwai siffa kamar na mutum. Na ga daga abin da ya yi kamar kwankwasonsa zuwa bisa ya yi kamar ƙarfe mai walƙiya, sai ka ce wuta, kuma daga kwankwasonsa zuwa ƙasa ya yi kamar wuta; haske kuma mai walƙiya sosai kewaye da shi. Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka hasken da ya kewaye shi.
Wannan shi ne kwatancin kamannin ɗaukakar Ubangiji. Sa’ad da na gani, sai na fāɗi rubda ciki, na kuma ji muryar wani tana magana.
Kiran Ezekiyel
Ya ce mini, “Ɗan mutum, tashi ka tsaya a ƙafafunka zan kuma yi maka magana.” Yayinda yake magana, sai Ruhu ya sauko mini ya kuma tā da ni a ƙafafuna, na kuma ji shi yana mini magana.
Ya ce, “Ɗan mutum, ina aikan ka zuwa ga Isra’ilawa, zuwa ga al’ummar ’yan tawayen nan da suka yi mini tayarwa; su da kakanninsu sun yi mini tawaye har yă zuwa yau. Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Kuma ko su ji ko kada su ji, gama su gida ne mai tawaye, za su san cewa akwai annabi a cikinsu. Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye. Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su ’yan tawaye ne. Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan ’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.”
Sai na duba, na kuma ga hannu ya miƙe zuwa wurina. A cikinsa akwai littafi, wanda ya nannaɗe a gabana. A kowane gefensa akwai rubutun kalmomin makoki da kuka da kuma kaito.
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci abin da yake a gabanka, ka ci wannan littafi; sa’an nan ka tafi ka yi magana wa gidan Isra’ila.” Saboda haka na buɗe bakina, ya kuma ba ni littafin in ci.
Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ci wannan littafin da nake ba ka, ka kuma cika cikinka da shi.” Sai na ci shi, ya kuma yi zaki kamar zuma a bakina.
Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka tafi gidan Isra’ila ka faɗa kalmomina gare su. Ba ina aikan ka wurin mutanen da suke da baƙon harshe da kuma yare mai wuya ba ne, amma zuwa ga gidan Isra’ila ne, ba ga mutane da yawa na baƙon harshe da yare mai wuya, waɗanda ba ka san kalmominsu ba. Tabbatacce da na aike ka wurin irinsu, da sun saurare ka. Amma gidan Isra’ila ba sa niyya su saurare ka domin ba sa niyya su saurare ni, gama dukan gidan Isra’ila sun taurare suna kuma kin ji. Amma zan sa ka zama mai taurinkai da taurin zuciya kamar su. Zan sa goshinka ya zama da tauri kamar dutse, da tauri fiye da dutsen ƙanƙara ƙarfi. Kada ka ji tsoronsu ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.”
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ji da kyau ka kuma lura da dukan kalmomin da nake maka magana. Ka tafi yanzu zuwa ga ’yan’uwanka waɗanda suke zaman bauta ka yi musu magana. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,’ ko ku ji, ko kada ku ji.”
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama, a bayana na ji wata karar babban motsi na cewa, Bari a yabi ɗaukakar Ubangiji a wurin zamansa! Karar fikafikan rayayyun halittun nan ne suke goge junansu da kuma karar da’irorin nan da suke kusa da su, ƙarar babban motsi. Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da ɓacin rai da kuma fushin ruhuna, tare da hannu mai ƙarfi na Ubangiji a bisa na. Na zo wurin masu zaman bautan da suke zama a Tel Abib kusa da Kogin Kebar, A can kuwa, inda suke zama, na zauna a cikinsu kwana bakwai, ina mamaki.
Kashedi ga Isra’ila
([Ezekiyel 33.1-9])
A ƙarshen kwana bakwai ɗin maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro don gidan Isra’ila; saboda haka ka ji maganar da zan yi ka kuma yi musu kashedin nan da ya fito daga gare ni. In na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ ba ka kuwa yi masa kashedi ko ka tsawata masa a kan mugayen hanyoyinsa don yă ceci ransa ba, wannan mugun zai mutu saboda3.18 Ko kuwa cikin; haka ma a ayoyi 19 da kuma 20 zunubinsa, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka. Amma in ka yi wa mugun kashedi bai kuwa juya daga mugayen hanyoyinsa ba, zai mutu saboda zunubinsa; amma kai kam za ka kuɓuta.
“Har yanzu, in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya aikata mugunta, na kuma sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Da yake ba ka yi masa kashedi ba, zai mutu saboda zunubinsa. Ba za a tuna da abin adalcin da ya yi ba, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka. Amma in ka yi wa mai adalcin kashedi kada yă yi zunubi bai kuwa yi zunubi ba, tabbatacce zai rayu saboda ya ji kashedin, kuma kai kam za ka kuɓuta.”
Hannun Ubangiji ya kasance a kaina a can, ya kuma ce mini, “Tashi ka fita zuwa fili, a can kuwa zan yi maka magana.” Saboda haka na tashi da tafi fili. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tsaya a can, kamar ɗaukakar da na gani kusa da Kogin Kebar, sai na fāɗi rubda ciki.
Sai Ruhu ya sauko a kaina ya kuma ɗaga ni na tsaya a ƙafafuna. Ya yi mini magana ya ce, “Ka fita, ka rufe kanka a cikin gida. Kuma kai, ɗan mutum, za su ɗaura ka da igiyoyi; za a daure ka yadda ba za ka iya fita a cikin mutane ba. Zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka yi shiru ka kuma kāsa tsawata musu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne. Amma sa’ad da na yi maka magana, zan buɗe bakinka za ka kuwa faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Duk mai ji ya ji, kuma duk wanda ya ƙi ji, ya ƙi ji; gama su gida ne na ’yan tawaye.
An nuna alamar kwanton ɓauna wa Urushalima
“Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki tubalin yumɓu, ka ajiye shi a gabanka ka kuma zāna birnin Urushalima a kansa. Sa’an nan ka yi mata ƙawanya. Ka kafa mata katangar ƙawanya, ka gina katangar da ɗan tudu ka kewaye ta da dundurusai. Sa’an nan ka ɗauki kwanon ƙarfe, ka shirya shi kamar katangar ƙarfe tsakaninka da birnin ka kuma zuba mata ido. Za tă kasance a ƙarƙashin ƙawanya, kai kuwa za ka yi mata ƙawanya. Wannan zai zama alama ga gidan Isra’ila.
“Sa’an nan ka kwanta a hagunka ka kuma sa zunubin gidan Isra’ila a kanka.4.4 Ko kuwa a gefenka Za ka ɗauki zunubinsu na waɗansu kwanakin da kake kwance a gefenka. Na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun zunubinsu. Saboda haka cikin kwana 390 za ka ɗauki zunubin gidan Isra’ila.
“Bayan ka gama haka, ka sāke kwantawa, a wannan lokaci a gefen damarka, ka kuma ɗauki zunubin gidan Yahuda. Na ɗora maka kwanaki 40, kwana guda a madadin shekara guda. Ka juya fuskarka wajen ƙawanyar Urushalima da hannunka a buɗe ka yi annabci a kanta. Zan ɗaura ka da igiyoyi don kada ka juya daga wannan gefe zuwa wani gefe sai ka gama kwanakin ƙawanyarka.
“Ka ɗauki alkama da sha’ir, wake da acca, gero da maiwa; ka sa su a tulun ajiya ka kuma yi amfani da su don yin burodi wa kanka. Za ka ci shi a kwanaki 390 da za ka kwanta a gefenka. Ka auna shekel ashirin na abinci don kowace rana ka kuma ci shi a ƙayyadadden lokaci. Haka ma ka auna kashi ɗaya bisa shida na garwan ruwa ka sha shi a ƙayyadadden lokaci. Ka ci abinci yadda za ka ci ƙosai sha’ir, ka gasa shi a gaban mutane, ka yi amfani da najasar mutane kamar itacen wuta.” Ubangiji ya ce, “Ta haka mutanen Isra’ila za su ci ƙazantaccen abinci a cikin al’ummai inda zan kore su in kai.”
Sai na ce, “Ba haka ba ne, Ubangiji Mai Iko Duka! Ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Daga ƙuruciyata har zuwa yanzu ban taɓa cin wani abin da aka samu ya mutu ko abin da namun jeji suka kashe ba. Ba nama marar tsabtan da ya taɓa shiga bakina.”
Sai ya ce, “To da kyau, zan bari ka gasa burodin a kan kashin shanu a maimakon najasar mutane.”
Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, zan yanke tanadin abinci a Urushalima. Mutane za su auna abincin da za su ci da tsoro su kuma auna ruwan da za su sha cikin fargaba, domin abinci da ruwa za su kāsa. Za su damu da ganin juna za su kuma lalace saboda zunubinsu.
“Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki takobi mai kaifi ka kuma yi amfani da shi kamar rezan mai aski don askin kanka da gemunka. Sa’an nan ka ɗauki ma’auni ka kuma raba gashin. Sa’ad da kwanakin ƙawanyarka sun ƙare, sai ka ƙone kashi ɗaya bisa uku na gashin da wuta a cikin birnin. Ka ɗauki kashi ɗaya bisa uku ka yayyanka shi da takobi kewaye da birnin. Ka kuma watsar da kashi ɗaya bisa uku a iska. Gama zan fafare su da takobin da aka zāre. Amma ka ɗibi gashi kaɗan ka daure a shafin rigarka. Har yanzu, ka ɗibi kaɗan na waɗannan ka zuba su cikin wuta su kuma ƙone. Wuta zai bazu daga nan zuwa dukan gidan Isra’ila.
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Urushalima ce wannan, wadda na kafa a tsakiyar al’ummai, da ƙasashe kewaye da ita a ko’ina. Duk da haka cikin muguntarta ta yi tayarwa a kan dokokina da ƙa’idodina fiye da al’ummai da ƙasashe kewaye da ita. Ta ƙi dokokina ba tă kuwa bi ƙa’idodina ba.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce kin yi ƙin ji fiye da al’umman da suke kewaye da ke ba ki kuma bi ƙa’idodina ko ki kiyaye dokokina ba. Ba ki ma dace da matsayin al’umman da suke kewaye da ke ba.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Ni kaina ina gāba da ke, Urushalima, kuma zan hukunta ki a gaban al’ummai. Saboda dukan gumakan banƙyamarki, zan yi abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan ƙara yinsa ba. Saboda haka a cikinki ubanni za su ci ’ya’yansu, ’ya’ya kuma za su ci ubanninsu. Zan hukunta ki zan kuma watsar da dukan waɗanda suke tsira da suke naki a iska. Saboda haka muddin ina a raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin kin ƙazantar da wuri mai tsarkina da dukan mugayen siffofinki da kuma ayyukanki masu banƙyama, ni kaina zan janye alherina; ba zan ji tausayinki ko in haƙura da ke ba. Kashi ɗaya bisa uku na mutanenki za su mutu da annoba ko su mutu da yunwa a cikinki; kashi ɗaya bisa uku takobi ne zai kashe su a waje da katangarki; kashi ɗaya bisa uku kuma zan watsar a iska in kuma fafare su da takobin da aka zāre.
“Sa’an nan ne fushina zai huce hasalata a kanki kuma ta lafa, in kuma wartsake. Kuma sa’ad da na zuba fushina a kansu, a sa’an nan ne za su san cewa Ni Ubangiji na yi magana a cikin fushin kishina a kansu.
“Zan mai da ki kufai da kuma abin dariya a cikin al’ummai kewaye da ke, a gaban dukan waɗanda suke wucewa. Za ki zama abin dariya da abin ba’a, kashedi da abin banrazana ga al’ummai kewaye da ke sa’ad da na hukunta ki cikin fushi da cikin hasala da kuma tsawatawa mai zafi. Ni Ubangiji na faɗa. Sa’ad da na harbe ki da mugayen kibiyoyina da kuma kibiyoyi masu hallakarwa na yunwa, zan yi harbi don in kashe ki. Zan kawo ƙarin yunwa a kanki in kuma yanke tanadin abincinki. Zan aika da yunwa da namun jeji a kanki, za su kuma bar ku ba ’ya’ya. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki, zan kuma kawo takobi a kanki. Ni Ubangiji na faɗa.”
Annabci a kan duwatsun Isra’ila
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka kafa idonka a kan duwatsun Isra’ila; ka yi annabci a kansu ka ce, ‘Ya ku duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa duwatsu da tuddai, ga rafuffuka da kuma kwaruruka. Ina shirin kawo takobi a kanku, kuma zan hallaka masujadanku. Za a ragargaza bagadanku a kuma farfasa bagadanku na ƙone turare; zan kuma kashe mutanenku a gaban gumakanku. Zan shimfiɗa gawawwakin Isra’ilawa a gaban gumakansu, in kuma watsar da ƙasusuwanku kewaye da bagadanku. Duk inda kuke zama, garuruwa za su zama kango, za a kuma ragargaza masujadai, saboda bagadanku su rurrushe su zama kango, a kuma farfasa gumakanku su lalace, za a rurrushe bagadan ƙone turarenku, a kuma shafe dukan abin da kuka yi. Za a kashe mutanenku a cikinku, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.
“ ‘Amma zan bar waɗansu, gama waɗansunku za su tsere wa takobi sa’ad da aka watsar da ku a cikin ƙasashe da al’ummai. Sa’an nan a cikin al’ummai inda aka kai ku zaman bauta, waɗanda suka a tsere za su tuna da ni, yadda raina ya ɓaci ta wurin zukatansu marasa imani, waɗanda suka rabu da ni, da kuma ta wurin idanunsu, waɗanda suka yi sha’awace-sha’awacen gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwan da suka aikata. Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji; ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ku tafa hannuwanku tare ku kuma taka ƙafafunku ku yi ihu ku ce, “Kaito!” Saboda dukan mugaye da kuma abubuwan banƙyama na gidan Isra’ila, gama za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba. Wanda yake da nisa zai mutu da annoba, shi da yake kusa kuma zai mutu ta takobi, wanda kuma ya tsira aka kuma bari zai mutu da yunwa. Ta haka zan aukar da fushina a kansu. Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da gawawwakin mutanensu suna kwance a kusa da gumakansu da kewaye da bagadansu, a kowane kan tudu mai tsawo da kuma a kan dukan kan duwatsu, a ƙarƙashin kowane inuwar itace da kuma kowane oak mai ganye, wuraren da suke ƙone turare masu ƙanshi wa dukan gumakansu. Zan kuma miƙa hannuna a kansu in mai da ƙasarsu kango daga hamadan Dibila, a duk inda suke zama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Ƙarshe ya zo
Maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa, “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa wa ƙasar Isra’ila,
“ ‘Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo
a kan kusurwoyi huɗu na ƙasar.
Ƙarshe yanzu yana a kanki.
Zan fashe fushina a kanki.
Zan shari’anta ki bisa ga halinki
in sāka miki kuma saboda dukan ayyukan banƙyamar da kika yi.
Ba zan dube ki da tausayi;
ko in ƙyale ki ba.
Tabbatacce zan sāka miki saboda halinki
da kuma ayyukanki masu banƙyama a cikinki.
Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji.’
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Masifa! Masifar da ba a taɓa gani ba
tana zuwa.7.5 Yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da na Siriyak suna da Masifa kan masifa ne a nan
Ƙarshe ya zo!
Ƙarshe ya zo!
Ya farka a kanki.
Ga shi, ya zo!
Ƙaddara ta auko miki,
ya ke wadda ke zama cikin ƙasar.
Lokaci ya yi, rana ta gabato;
akwai fargaba, ba farin ciki ba, a kan duwatsu.
Ina gab da fasa hasalata a kanki
in kuma aukar da fushina a kanki;
zan shari’anta ke bisa ga halinki
in kuma sāka miki saboda dukan ayyukanki masu banƙyama.
Ba zan dube ki da tausayi
ko in ƙyale ke ba;
zan sāka miki bisa ga halinki
da kuma ayyukan masu banƙyama a cikinki.
Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji wanda yake bugunki.
“ ‘Ga shi ranar ta zo!
Ta iso!
Ƙaddararki ta keto,
sandar ta yi toho,
girman kai ya yi fure!
Rikici ya yi girma ya zama
sandar da za a hukunta mugunta;
babu wani daga cikin mutanen da za a bari,
babu wani dukiyarsu da za a bari,
babu wani abin amfani.
Lokaci ya yi!
Ranar ta gabato!
Kada mai saya ya yi farin ciki
ko kuwa mai sayarwa ya yi baƙin ciki,
gama hasala tana a kan dukan jama’a.
Mai sayarwa ba zai mayar da ƙasar da ya sayar tuntuni ba
muddin dukansu suna da rai, gama ba za a sauya wahayin da ya shafi dukan jama’a ba.
Saboda zunubansu, babu ɗayansu da zai adana ransa.
“ ‘Ko da yake suna busa ƙaho suna kuma shirya kome,
ba wanda zai tafi yaƙi, gama hasalata tana a kan dukan jama’a.
A waje takobi ne,
a ciki annoba ne da yunwa;
waɗanda suke fili za su mutu ta wurin takobi,
waɗanda kuma suke cikin birni yunwa da annoba za su cinye su.
Duk waɗanda suka tsira suka tsere za su kasance a cikin duwatsu,
suna kuka kamar kurciyoyin kwaruruka,
kowanne saboda zunubansa.
Kowane hannu zai raunana,
kowace gwiwa kuma za tă zama marar ƙarfi kamar ruwa.
Za su sa tufafin makoki su kuma rufu da fargaba.
Fuskokinsu kuma za su rufu da kunya a kuma aske kawunansu.
“ ‘Za su zubar da azurfarsu a tituna,
zinariyarsu kuma za tă zama ƙazantacciyar aba.
Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu
a ranar hasalar Ubangiji ba.
Ba za su ƙosar da yunwansu ko su cika cikinsu da shi ba,
gama su ne sanadin tuntuɓensu cikin zunubi.
Sun yi fariya kyan kayan adonsu
suka kuma yi amfani da su don su yi gumakansu masu banƙyama,
da ƙazantattun abubuwa.
Zan ba da su duka kamar ganima ga baƙi
da kuma kamar abin da aka washe ga mugayen duniya,
za su kuma ƙazantar da su.
Zan juye fuskata daga gare su,
za su kuwa ƙazantar da wurina mai daraja;
’yan fashi za su shiga
su kuma ƙazantar da shi.
“ ‘Ka shirya sarƙoƙi,
domin ƙasar ta cika da alhakin jini,
birnin kuma ya cika da rikici.
Zan kawo al’ummai mafi mugunta su mallaki gidajenku;
zan kawo ƙarshen fariyar masu ƙarfi,
Wurare Masu Tsarkinsu za su ƙazantu.
Sa’ad da wahala ta zo,
za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.
Masifa a kan masifa za su zo,
jita-jita kuma a kan jita-jita.
Za su yi ƙoƙarin samun wahayi daga annabi;
koyarwar doka ta wurin firist
za tă ɓace,
kamar yadda shawarar dattawa za tă ɓace.
Sarki zai yi makoki, yerima zai fid da zuciya,
hannuwan mutanen ƙasar kuma za su yi rawa.
Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su bisa ga ma’auninsu.
Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Bautar gumaka a cikin haikali
A shekara ta shida, a wata shida a ranar ta biya, yayinda nake zaune a gidana dattawan Yahuda kuma suna zaune a gabana, hannun Ubangiji Mai Iko Duka ya zo a kaina a can. Na duba, sai na ga siffa kamar na mutum.8.2 Ko kuwa na ga siffa mai kamanni wuta Daga kwankwaso zuwa ƙasa ya yi kamar wuta, kuma daga kwankwaso zuwa sama kamanninsa ya yi haske yana ƙyalli kamar ƙarfe mai haske. Ya miƙa abin da ya yi kamar hannu ya kama a gashin kaina. Ruhu ya ɗaga ni tsakanin sama da ƙasa, a cikin wahayoyi kuma Allah ya ɗauke ni zuwa Urushalima, zuwa ƙofa zuwa gabas na cikin fili, inda gunki mai tsokanar kishi yake tsaye. A can gabana kuwa ga ɗaukakar Allah na Isra’ila, kamar a wahayin da na gani a fili.
Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, duba waje arewa.” Sai na duba, a mashigin arewa na ƙofar bagaden kuwa na ga wannan gunki na tsokanar kishi.
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwan banƙyamar da gidan Isra’ila ke yi a nan, abubuwan da za su kore ni daga wuri mai tsarkina? Amma za ka ga abubuwan da suka ma fi banƙyama.”
Sa’an nan ya kawo ni mashigin filin. Na duba, na kuma ga rami a bango. Ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka haƙa cikin bangon.” Da na haƙa cikin bangon sai na ga ƙofar shiga a can.
Sai ya ce mini, “Shiga ka ga mugaye da kuma abubuwa banƙyamar da suke yi a can.” Na kuwa shiga na duba, sai na ga zāne-zāne ko’ina a bangon na kowane irin abubuwa masu rarrafe da kuma dabbobi masu ƙazanta da dukan gumakan gidan Isra’ila. A gabansu ga dattawa saba’in na gidan Isra’ila tsaye a cikinsu, Ya’azaniya ɗan Shafan kuwa yana tsaye a cikinsu. Kowa yana da farantin ƙona turare a hannunsa, tulin hayaƙin turare mai ƙanshi ya tunnuƙe zuwa sama.
Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da dattawan gidan Isra’ila suke yi a cikin duhu, kowa yana a ɗakin tsafin gunkinsa? Suna cewa, ‘Ubangiji ba ya ganinmu; Ubangiji ya yashe ƙasar.’ ” Ya kuma ce, “Za ka gan su suna yin abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.”
Sa’an nan ya kawo ni mashigin arewa na ƙofar gidan Ubangiji, sai na ga mata zaune a can, suna makokin Tammuz. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan? Za ka ga abubuwan da suke masu banƙyama fiye da wannan.”
Sa’an nan ya kawo ni cikin fili na cikin gidan Ubangiji, a can kuwa a ƙofar haikali, tsakanin shirayi da bagade, akwai kamar mutum ashirin da biyar. Suka ba haikalin Ubangiji baya suna fuskanta wajen gabas, suna rusuna wa rana a gabas.
Ya ce mini, “Ka ga wannan, ɗan mutum? Ƙaramin abu ne gidan Yahuda su yi abubuwan banƙyamar da suke yi a nan? Dole ne su cika ƙasar da rikici su kuma ci gaba da tsokane ni in yi fushi? Dube su suna tsokanata! Saboda haka zan hukunta su cikin fushi; Ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba. Ko da yake suna ihu a kunnuwana, ba zan saurare su ba.”
An kashe masu bautar gumaka
Sai na ji ya yi kira da babbar murya yana cewa, “Kawo matsaran birni a nan, kowanne da makami a hannunsa.” Na kuma ga mutane shida suna zuwa daga kowane gefen ƙofar ta bisa, wadda take fuskantar arewa, kowanne da makamin kisa a hannunsa. Tare da su akwai mutum saye da lilin yana rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa. Suka shiga suka tsaya kusa da bagaden tagulla.
To, fa, ɗaukakar Allah na Isra’ila ta haura daga bisa kerubobi, inda ta kasance, ta tashi zuwa bakin madogarar ƙofar haikali. Sai Ubangiji ya kira mutumin da yake saye da lilin wanda ya rataye jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa ya ce masa, “Ka ratsa birnin Urushalima ka sa shaida a goshin waɗanda suke baƙin ciki da kuma makoki a kan dukan abubuwan banƙyamar da ake yi a cikinsa.”
Yayinda nake saurara, sai ya ce wa waɗansu, “Ku bi shi ta birnin ku kuma kashe, babu tausayi ko kuwa jinƙai. Ku kashe tsofaffi da samari da ’yan mata, mata da yara, amma kada ku taɓa wani wanda yake da shaida. Ku fara a wuri mai tsarkina.” Saboda haka suka fara da dattawan da suke gaban haikali.
Sa’an nan ya ce musu, “Ku ƙazantar da haikalin ku kuma cika filayen da kisassu. Ku tafi!” Saboda haka suka fita suka kuma fara kisa a duk birnin. Yayinda suke kisan sai aka bar ni kaɗai, na fāɗi rubda ciki, na yi kuka na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Za ka hallaka dukan raguwar Isra’ila a wannan zafin fushinka a Urushalima?”
Ya amsa mini ya ce, “Zunubin gidan Isra’ila da Yahuda ya yi girma ainun; ƙasar ta cika da rashin adalci. Suna cewa, ‘Ubangiji ya yashe ƙasar; Ubangiji ba ya gani.’ Saboda haka ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba, amma zan kawo wa kansu abin da suka yi.”
Sai mutumin da yana saye da lilin yake kuma rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa ya mayar da magana, yana cewa, “Na yi yadda ka umarci ni.”
Ɗaukaka ta rabu da haikali
Na duba, sai na ga kamannin kursiyin saffaya10.1 Ko kuwa lafis lazuli a kan sararin da yake a bisa kawunan kerubobi. Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da lilin, “Ka shiga cikin da’irorin da suke ƙarƙashin kerubobi. Ka cika hannuwanka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin ka kuma watsar da su a kan birnin.” Yayinda nake dubawa, sai ya shiga.
Kerubobin kuwa suna tsaye a gefen kudu na haikali sa’ad da mutumin ya shiga, sai girgije ya cika filin da yake can ciki. Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa kerubobi ya tafi zuwa madogarar ƙofar haikali. Girgijen ya cika haikali, filin kuwa ya cika da hasken ɗaukakar Ubangiji. Sai aka ji ƙarar fikafikan kerubobin har a filin waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki10.5 Da Ibraniyanci El-Shaddai sa’ad da ya yi magana.
Sa’ad da Ubangiji ya umarci mutumin da yake saye da lilin cewa, “Ka ɗibi wuta daga cikin tsakanin da’irorin, daga tsakanin kerubobin,” sai mutumin ya shiga ya tsaya kusa da da’irar. Sa’an nan ɗaya daga cikin kerubobin ya miƙa hannu zuwa wurin wutar da take tsakaninsu. Ya ɗebo wutar daga ciki ya zuba a hannuwan mutumin da yake saye da lilin, shi kuwa ya karɓa ya fita. (A ƙarƙashin fikafikan kerubobin ana iya ganin abin da ya yi kamar hannuwan mutum.)
Na duba, sai na ga kusa da kerubobin akwai da’irori huɗu, kowanne kusa da kerub guda; da’irorin suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja. Game da kamanninsu kuwa, huɗu a cikinsu sun yi kama da juna; kowanne ya yi kamar da da’ira a cikin da’ira. Yayinda suke tafiya, sukan tafi kowane gefe huɗun da kerubobin suka nufa; da’irorin ba sa juyawa yayinda kerubobin suke tafiya. Kerubobin suka tafi kowane gefen da kan ya nufa, ba tare da juyawa ba sa’ad da suke tafiya. Jikunansu gaba ɗaya, har da bayansu, hannuwansu da fikafikansu, sun cika gaba ɗaya da idanu, kamar yadda suke a da’irori huɗun. Na ji ana kiran da’irorin “da’irorin guguwa.” Kowane daga kerubobin yana da fuskoki huɗu. Fuska ɗaya na kerub ne, na biyun fuskar mutum ne, na ukun fuskar zaki ne, na huɗun kuwa fuskar gaggafa ce.
Sai kerubobin suka tashi sama. Waɗannan ne halittu masu ran da na gani kusa da Kogin Kebar. Sa’ad da kerubobin suka motsa, sai da’irorin da suke kusa da su su motsa; kuma sa’ad da kerubobin suka buɗe fikafikansu don su tashi daga ƙasa, da’irorin ba sa barin wurarensu. Sa’ad da kerubobin suka tsaya cik, su ma sukan tsaya cik; kuma sa’ad da kerubobin suka tashi, sai su ma su tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun yana a cikinsu.
Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa madogarar ƙofar haikali ya kuma tsaya a bisa kerubobi. Yayinda nake duba, kerubobin suka buɗe fikafikansu suka kuma tashi daga ƙasa, yayinda suka tafi kuwa, da’irorin suka tafi tare da su. Suka tsaya a mashigin ƙofar gabas na gidan Ubangiji, ɗaukakar Allah na Isra’ila kuwa yana a kansu.
Waɗannan ne rayayyun halittun da na gani a ƙarƙashin Allah na Isra’ila kusa da Kogin Kebar, na kuma gane cewa su kerubobi ne. Kowanne yana da fuskoki huɗu da fikafikai huɗu, a ƙarƙashin kuwa akwai wani abin da ya yi kamar hannuwan mutum. Fuskokinsu suna da kamanni ɗaya da waɗanda na gani kusa da Kogin Kebar. Kowanne ya tafi kai tsaye sosai.
Hukuncin shugabannin Isra’ila
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni ƙofar gidan Ubangiji wadda take fuskantar gabas. Can a mashigi zuwa ƙofar akwai mutum ashirin da biyar, na kuma ga a cikinsu akwai Ya’azaniya ɗan Azzur da Felatiya ɗan Benahiya, shugabannin jama’a. Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da suke ƙulla mugunta suna kuma ba da muguwa shawara a cikin wannan birni. Suna cewa, ‘Lokaci bai yi kusa da za a gina gidaje ba?11.3 Ko kuwa Wannan ba lokacin gina gidaje ba ne Wannan birni yana tukunyar dahuwa, mu ne kuwa naman.’ Saboda haka yi annabci a kansu; yi annabci, ɗan mutum.”
Sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya kuma faɗa mini in ce, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, haka kuke cewa, ya gidan Isra’ila, amma na san abin da yake a zuciyarku. Kun kashe mutane da yawa a wannan birni kuka kuma cika titunanta da gawawwaki.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa gawawwakin da kuka zubar a can su ne naman, wannan birni kuwa ita ce tukunya, amma zan kore ku daga cikinta. Kuna jin tsoron takobi, kuma takobi ne zan kawo muku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan kore ku daga birnin in miƙa ku a hannuwan baƙi in kuma azabtar da ku. Za ku mutu ta wurin takobi, zan kuma hukunta ku a iyakokin Isra’ila. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. Wannan birni ba za tă zama muku tukunya ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinta ba; zan hukunta ku a iyakokin Isra’ila. Za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji, gama ba ku bi ƙa’idodina ba balle ku kiyaye dokokina, amma kuka bi hanyoyin al’ummai kewaye da ku.”
Yanzu yayinda nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benahiya ya mutu. Sai na fāɗi rubda ciki na kuma yi kuka da babbar murya na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Za ka hallaka raguwar Isra’ila ƙaƙaf ne?”
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ’yan’uwanka, ’yan’uwanka waɗanda suke danginka na cikinka11.15 Ko kuwa suke zaman bauta tare da kai (dubi Seftuwajin da kuma Siriyak) da kuma dukan gidan Isra’ila su ne waɗanda mutanen Urushalima suka ce, ‘Su ne11.15 Ko kuwa waɗanda mutanen Urushalima suka ce, “Tsaya” da nisa daga Ubangiji; an ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu.’
Alkawarin komowar Isra’ila
“Saboda haka ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ko da yake na kore su zuwa cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama wuri mai tsarki a gare su a ƙasashen da suka tafi.’
“Saboda haka, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan tattaro ku daga al’ummai in kuma dawo da ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku, zan kuwa sāke mayar muku da ƙasar Isra’ila.’
“Za su dawo gare ta su kawar da dukan mugayen siffofi da gumaka masu banƙyama. Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama. Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu. Amma game da waɗanda zukatansu suka karkata ga bin mugayen siffofi da gumakan banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Sa’an nan kerubobi, tare da da’irori kusa da su, suka buɗe fikafikansu, ɗaukakar Allah kuwa tana a bisansu. Ɗaukakar Ubangiji ta haura daga cikin birnin ta sauka a bisa dutse gabas da shi. Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma kawo ni ga masu zaman bauta a ƙasar Babilon11.24 Ko kuwa Kaldiyawa cikin wahayin da Ruhun Allah ya bayar.
Sa’an nan wahayin da na gani ya rabu da ni, na kuwa faɗa wa masu zaman bautan dukan abin da Ubangiji ya nuna mini.
An yi alamar zaman bauta
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa ɗan mutum, kana zama a cikin mutane masu tawaye, Suna da idanun gani amma ba sa gani, suna da kunnuwan ji amma ba sa ji, gama ’yan tawaye ne.
“Saboda haka ɗan mutum, ka tattara kayanka don zuwa zaman bauta, ka tashi da rana suna gani ka ƙaura a inda kake zuwa wani wuri. Mai yiwuwa za su gane, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne. Da rana, yayinda suke kallo, ka fid da kayanka da ka tattara don zuwa zaman bauta. Sa’an nan da yamma, yayinda suke kallo, ka fita kamar yadda mutane masu tafiyar zaman bauta sukan yi. Yayinda suke kallo, ka huda katanga ka fitar da kayanka daga ciki. Ka sa su a kafaɗarka yayinda suke kallo ka kuma fitar da su da dare. Ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na mai da kai alama ga gidan Isra’ila.”
Sai na yi kamar yadda aka umarce ni. Da rana na fitar da kayana da na tattara don zuwa zaman bauta. Sa’an nan da yamma na huda katanga da hannuwana. Na kwashe kayana da dare, na ɗauke su a kafaɗuna yayinda suke kallo.
Da safe maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, gidan ’yan tawayen nan na Isra’ila ba su tambaye ka, ‘Me kake yi ba?’
“Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wannan abin da Allah ya yi magana a kai ya shafi sarki a Urushalima da kuma dukan gidan Isra’ila waɗanda suke a can.’ Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku.’
“Kamar yadda na yi, haka za a yi da su. Za a kai su zaman bauta kamar kamammu.
“Sarkin da yake a cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa da dare ya tafi, za a huda masa rami a katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada yă ga ƙasar. Zan shimfiɗa masa ragata, za a kuwa kama shi da tarkona; zan kawo shi Babiloniya, ƙasar Kaldiyawa, amma ba zai gan ta ba, a can kuwa zai mutu. Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi a dukan fuskokin iska, ma’aikatansa da dukan rundunoninsa, zan fafare su da takobin da aka zāre.
“Za su san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na watsar da su a cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe. Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, yunwa da annoba, saboda a cikin al’umman da suka tafi su furta dukan ayyukansu masu banƙyama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi rawar jiki yayinda kake cin abincinka, ka kuma yi makyarkyata don tsoro yayinda kake shan ruwanka. Ka faɗa wa mutanen ƙasar cewa, ‘Ga abin Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da waɗanda suke zama a Urushalima da kuma cikin ƙasar Isra’ila. Za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suna zama a can. Garuruwan da mutane suna ciki za su zama kufai ƙasar kuma za tă zama kango. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da kuke da shi a ƙasar Isra’ila mai cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba’? Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.’ Ka ce musu, ‘Kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi. Gama ba za a ƙara ganin wahayin ƙarya ko a yi duba na daɗin baki a cikin mutanen Isra’ila ba. Amma Ni Ubangiji zan yi magana abin da na nufa, za tă kuwa tabbata ba tare da jinkiri ba. Gama cikin kwanakinku, kai gidan ’yan tawaye, zan cika duk abin da na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, gidan Isra’ila suna cewa, ‘Wahayin da yake gani na shekaru masu yawa ne nan gaba, yana kuma annabce-annabce game da wani zamani ne can.’
“Saboda haka ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa ba wata maganata da za tă ƙara yin jinkiri; duk abin da na faɗa zai cika, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
An hukunta annabawan ƙarya
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, yi annabci a kan annabawan Isra’ila waɗanda suke annabci yanzu. Ka faɗa wa waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji! Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake faɗa, Kaiton wawaye annabawan da suke bin ruhunsu kuma ba su ga kome ba! Annabawanki, ya Isra’ila, suna kama da diloli a kufai. Ba ku haura don ku rushe katanga don ku gyara gidan Isra’ila saboda ya tsaya daram a yaƙi a ranar Ubangiji ba. Wahayoyinsu ƙarya ne suna yin dubansu na ƙarya ne. Sukan ce, Ubangiji ya furta, alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba; duk da haka sukan sa zuciya ga cikawar maganarsu. Ba ku ga wahayin ƙarya kuka kuma faɗa yin duban ƙarya sa’ad da kuka ce, “Ubangiji ya furta,” ko da yake bai yi magana ba?
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa saboda maganganunku na ƙarya da wahayinku na ƙarya, ina gāba da ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Hannuna zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya suna kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin gidan Isra’ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘Domin sun ɓad da mutanena, suna cewa, “Salama,” sa’ad da ba salama, kuma saboda, sa’ad da ana gina katanga marar ƙarfi, sukan shafe ta da farar ƙasa, saboda haka ka faɗa wa waɗanda suka shafe da farar ƙasa cewa za tă fāɗi. Ruwan sama zai sauko da rigyawa, zan kuma aika da ƙanƙara, kuma babbar iska za tă ɓarke. Sa’ad da katangar ta fāɗi, mutane ba za su tambaye ku ba cewa, “Ina shafen farar ƙasar da kuka yi mata?”
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a cikin hasalata zan saki babbar iska, kuma cikin fushina zan tura ƙanƙara kuma rigyawan ruwan sama zai sauko da fushin hallaka. Zan rushe katangar da kuka shafe da farar ƙasa zan baje ta har ƙasa saboda tushenta zai tsaya tsirara. Sa’ad da ta fāɗi, za a hallaka ku a cikinta; kuma za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka. Ta haka zan aukar wa katangar da hasalata da kuma a kan waɗanda suka yi shafenta da farar ƙasa. Zan ce muku, “Katangar ta fāɗi haka kuma mutanen da suka shafe ta da farar ƙasa, waɗannan annabawan Isra’ila waɗanda suka yi annabci wa Urushalima suka kuma ga mata wahayin salama sa’ad da ba salama, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” ’
“To, ɗan mutum, ka kafa idonka a kan ’yan matan mutanenka waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu. Yi annabci a kansu ka kuma ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton matan da suke ɗinka kambuna a hannuwansu suna kuma yin gyale masu tsawo dabam-dabam wa kawunansu don su farauci mutane. Za ku farauci rayukan mutanena ku bar naku? Kun jawo mini kunya a cikin mutanena don a tafa muku sha’ir da ɗan dunƙulen burodi. Ta wurin yin ƙarya wa mutanena, waɗanda suke jin ƙarairayi, kuka kashe waɗanda bai kamata su mutu ba kuka bar waɗanda ya kamata su mutu.
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kambunanku waɗanda kuke farautar mutane da su kamar tsuntsaye don haka zan kuma tsintsinke su daga hannuwanku; zan ’yantar da mutanen da kuka farauto kamar tsuntsaye. Zan kyakketa gyalenku in ceci mutanena daga hannuwanku, ba za su kuma ƙara zama ganima a hannunku ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji Domin kun karya zuciyar masu adalci da ƙarairayinku, sa’ad da na fitar da su babu damuwa, kuma domin kun ƙarfafa mugaye kada su juye daga mugayen hanyoyinsu su ceci rayukansu, saboda haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi duba. Zan ceci mutanena daga hannuwanku. A sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
An ƙi masu bautar gumaka
Waɗansu dattawan Isra’ila suka zo wurina suka zauna a ƙasa a gabana. Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, waɗannan mutane sun kafa gumaka a cikin zukatansu suka sa mugayen abubuwan sa tuntuɓe a gabansu. Zan bar su, su taɓa nemi ni? Saboda haka ka yi musu magana ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da wani mutumin Isra’ila ya kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuma sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina game da babban bautar gumakarsa. Zan yi haka don in sāke ƙame zukatan mutanen Isra’ila, waɗanda duk suka yashe ni don gumakansu.’
“Saboda haka ka faɗa wa gidan Isra’ila cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tuba! Ku juyo daga gumakanku ku kuma furta dukan ayyukanku masu banƙyama!
“ ‘Duk sa’ad da mutumin Isra’ila ko baƙo mai zama a Isra’ila ya rabu da ni ya kuma kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuna sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi don yă neme ni, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina. Zan yi gāba da mutumin in kuma sa ya zama misali da kuma abin karin magana. Zan ware shi daga mutanena. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘In kuma aka ruɗi annabin har ya yi annabci, Ni Ubangiji na rinjayi wannan annabi, zan kuma miƙa hannuna gāba da shi in hallaka shi daga cikin mutanena Isra’ila. Za su ɗauki hakkin laifinsu annabin zai zama mai laifi daidai da wanda ya zo neman shawararsa. Sa’an nan mutanen Isra’ila ba za su ƙara kauce daga gare ni ba, ba kuwa za su ƙara ƙazantar da kansu da dukan zunubansu ba. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Hukuncin Urushalima babu makawa
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, in wata ƙasa ta yi mini zunubi ta wurin rashin aminci na kuma miƙa hannuna gāba da ita don in toshe hanyar samun abincinta na kuma aika da yunwa a kanta na kashe mutanenta da dabbobinta, ko da waɗannan mutum uku Nuhu, Daniyel14.14 Ko kuwa Danel; yadda aka rubuta sunan da Ibraniyanci mai yiwuwa yana nuna wani ne dabam da annabi Daniyel, haka ma a aya 20 da kuma Ayuba suna a cikinta, za su iya ceton kansu ne kawai ta wurin adalcinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“Ko kuwa in na aika da namun jeji su ratsa cikin wannan ƙasa suka kuma bar ta babu yaro, ta kuma zama kufai har babu wanda zai ratsa cikinta saboda namun jeji, muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da ma waɗannan mutum uku suna a cikinta, ba za su iya ceton ’ya’yansu maza ko mata ba. Su kaɗai za a iya ceto, amma ƙasar za tă zama kufai.
“Ko kuma in na kawo takobi a kan wannan ƙasa na kuma ce, ‘Bari takobin ya ratsa cikin dukan ƙasar,’ na kuma kashe mutanenta da dabbobinsu, muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da waɗannan mutum uku suna cikinta, ba za su iya ceton ’ya’yansu maza ko mata ba. Su kaɗai za a iya ceto.
“Ko kuma in na aika da annoba a cikin wannan ƙasa na kuma yi fushi a kanta ta wurin kisa, ina kisan mutanenta da dabbobinsu, muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ko da Nuhu, Daniyel da Ayuba suna a cikinta, ba za su iya ceton ɗansu ko ’yarsu ba. Za su iya ceton kansu ne kaɗai ta wurin adalcinsu.
“Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa balle fa sa’ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi takobi da yunwa da namun jeji da annoba don su kashe mutanenta da dabbobinsu! Duk da haka za a sami mutanen da za su ragu ’ya’ya maza da matan da za a fitar daga cikinta. Za su zo wurinka, kuma sa’ad da ka gan halinsu da ayyukansu, za ka ta’azantu game da bala’in da na kawo a kan Urushalima kowane bala’in da na kawo a kanta. Za ka ta’azantu sa’ad da ka ga halinsu da kuma ayyukansu, gama za ka san cewa ban aikata wani abu a cikinta ba dalili ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Urushalima, kuringa marar amfani
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, da me itacen kuringa ya fi reshen waɗansu itatuwa kyau a cikin kurmi? An taɓa ɗaukan itacensa an yi wani abu mai amfani? Akan yi maratayi da ita da za a rataya wani abu a kai? Bayan kuma a jefa ta cikin wuta, wuta kuma ta cinye kowane gefe ta kuma babbaka tsakiyarta, tana da amfani don yin wani abu kuma? In ba ta da amfanin wani abu sa’ad da take cikakkiya, balle bayan da wuta ta babbake ta, za a iya yin amfani da ita?
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kamar yadda na ba da itacen kuringa a cikin itatuwan kurmi ya zama itacen wuta, haka zan sa mazaunan Urushalima su zama. Zan yi gāba da su. Ko da yake sun fito daga wuta, wuta za tă cinye su. Kuma sa’ad da na yi gāba da su, za ku san cewa ni ne Ubangiji. Zan mai da ƙasar kufai domin sun yi rashin aminci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Misalin rashin amincin Urushalima
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta masu banƙyama ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Urushalima, Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan’ana ne; mahaifinki mutumin Amoriyawa ne, mahaifiyarki kuma mutuniyar Hitti ce. A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki. Ba wanda ya dube ki da tausayi ko ya nuna miki isashen jinƙai don yă yi miki ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. A maimako, sai aka jefar da ke a fili, gama a ranar da aka haife ki an ji ƙyamarki.
“ ‘Sa’an nan na wuce na ga kina birgima cikin jininki, yayinda kike kwance can cikin jininki sai na ce miki, “Ki rayu!”16.6 Kaɗan cikin rubuce-rubucen Ibraniyanci, Seftuwajin, da kuma Siriyak; yawancin rubuce-rubucen Ibraniyanci na da “Ki rayu!” Kuma yayinda kike kwance cikin jininki na ce miki, “Ki rayu!” Na sa kin yi girma kamar tsiro a fili. Kin yi girma kika kuma yi tsayi kika zama mafiya kyau na kayan ado.16.7 Ko kuwa kika zama budurwa Nononki suka fito, gashinki kuwa suka yi girma, duk da haka tsirara kike tik.
“ ‘Daga baya na wuce, da na dube ki sai na ga cewa kin yi girma sosai har kin kai a ƙaunace ki, na yafa gefen tufafina a kanki na kuma rufe tsiraincinki. Na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘Na yi miki wanka na wanke miki jini daga gare ki na kuma shafa miki mai. Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada. Na yi miki ado da kayan ado masu daraja, na sa miki mundaye a hannuwanki da abin wuya a wuyanki, na kuma sa miki zobe a hancinki, abin kunne a kunnuwanki da rawani mai kyau a kanki. Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya. Sunanki ya yaɗu a cikin al’ummai saboda kyanki, domin darajar da na ba ki ya sa kyanki ya zama cikakke, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘Amma kika dogara ga kyanki kika kuma yi amfani da sunan da kika yi don ki zama karuwa. Kin yi ta jibga alherai a kan kowa da ya wuce, sai kyanki ya zama naki. Kin ɗauki waɗansu tufafinki don ki yi wa kanki masujadai masu ado, inda kike karuwancinki. Irin waɗannan abubuwa bai kamata su faru ba, bai kuma kamata su taɓa faruwa ba. Kika kuma ɗauki kayan ado masu kyau da na ba ki, kayan adon da aka yi da zinariya da azurfa, kika yi wa kanki gumakan maza kika kuma yi ta yin karuwanci da su. Kika ɗauki rigunanki masu ado don ki sa a kansu, kika kuma miƙa maina da turarena a gabansu. Haka ma abincin da na tanada miki, lallausan gari, man zaitun, da zuman da na ba ki ki ci, kin miƙa su kamar turare mai ƙanshi a gabansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘Kika kuma kwashe ’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne? Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su16.21 Ko kuwa kika kuma sa suka wuce ta cikin wuta ga gumaka. Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.
“ ‘Kaito! Kaitonki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Bugu da ƙari a kan dukan waɗansu muguntarki, kin gina wa kanki ɗakunan sama da gidajen tsafi a kowane dandali. A kowane titi kin gina ɗakin tsafi kika kuma wulaƙanta kyanki, kina miƙa jikinki da ƙarin fasikanci ga duk mai wucewa. Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi, kika tsokane ni har na yi fushi da ƙarin fasikancinki. Saboda haka na miƙa hannuna gāba da ke na kuma rage iyakarki; na ba da ke ga abokan gābanki masu haɗama, ’yan matan Filistiyawa, waɗanda suka sha mamaki saboda halinki na lalata. Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa, domin ba kya ƙoshi; kai ko bayan wannan, ba ki ƙoshi ba. Sai kika ƙara fasikancinki da ya haɗa da ƙasar cinikin Babilon,16.29 Ko kuwa Kaldiya amma duk da haka ba ki ƙoshi ba.
“ ‘Kina da rashin ƙarfi a zuci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da kika yi duk waɗannan abubuwa, kina yi kamar karuwar da aka watsa! Sa’ad da kika gina ɗakunan samanki a kowane gefen titi kika kuma gina ɗakunan tsafinki a kowane dandali, ba kamar karuwa kike ba, domin kin karɓi kuɗi.
“ ‘Ke mazinaciyar mace! Kin gwammace baƙi a maimakon mijinki! Kowace karuwa kan karɓi kuɗi, amma kina ba da kyautai ga dukan kwartayenki, kina ba su cin hanci don su zo wurinki daga ko’ina don alherai marasa ƙa’ida. Saboda haka cikin karuwancinki kin sha bamban da saura; babu wanda yake binki saboda alheranki. Ke dai dabam ce, gama kikan biya kuma ba mai biyanki.
“ ‘Saboda haka, ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji! Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kin zubar da dukiyarki16.36 Ko kuwa sha’awar kika bayyana tsiraicinki cikin fasikancinki da kwartayenki, kuma saboda dukan gumakan banƙyamarki, kuma saboda kin ba su jinin ’ya’yansu, saboda haka zan tattara dukan kwartayenki, waɗanda kike jin daɗinsu, waɗanda kike ƙauna da waɗanda kike ƙi. Zan tattara su gāba da ke daga dukan kewaye zan kuma tuɓe ki a gabansu, za su kuwa ga dukan tsiraicinki. Zan hukunta ki da hukuncin matan da suke zina da kuma waɗanda suke zub da jini; zan kawo hakkin jini na fushina da kuma fushin kishina. Sa’an nan zan miƙa ki ga kwartayenki, za su kuwa rurrushe ɗakunan samanki su kuma farfashe ɗakunan tsafinki. Za su tuɓe miki tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau su bar ki tsirara tik. Za su kawo taron jama’a a kanki, waɗanda za su jajjefe ki da dutse su sassare ki gunduwa-gunduwa da takubansu. Za su ƙone gidajenki su kuma hukunta ki a idon mata masu yawa. Zan kawo ƙarshen karuwancinki, ba za ki kuma ƙara biyan kwartayenki ba. Sa’an nan fushina a kanki zai huce fushin kishina kuma ya kwanta; zan huce ba kuwa zan ƙara yin fushi ba.
“ ‘Domin ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, tabbatacce zan sāka miki alhakin ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba kin ƙara lalata ga dukan waɗansu ayyuka masu banƙyamarki ba?
“ ‘Duk mai yin amfani da karin magana zai faɗi wannan karin magana a kanki cewa, “Kamar yadda mahaifiya take haka ’yar take.” Ke ’yar mahaifiyarki ce da gaske, wadda ta ƙi mijinta da ’ya’yanta; ke kuma ’yar’uwar ’yar’uwanki mata ce da gaske, waɗanda suka ƙi mazansu da ’ya’yansu. Mahaifiyarki mutuniyar Hitti ce, mahaifinki kuma mutumin Amoriyawa ne. Babbar ’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da ’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da ’ya’yanta mata. Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su. Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ’yar’uwarki Sodom da ’ya’yanta mata ba su yi abin da ’ya’yanki mata suka yi ba.
“ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba. Su masu girman kai ne kuma suka aikata abubuwa masu banƙyama a gabana. Saboda haka na kau da su kamar yadda ka gani. Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata. Ki sha kunyarki, gama kin yi rangwame wa ’yan’uwanki mata. Saboda zunubanki sun yi muni fiye da nasu, sai suka zama kamar sun fi ki adalci. Saboda haka, ki sha kunya ki kuma sha ƙasƙancinki, gama kin sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar su masu adalci ne.
“ ‘Amma fa, zan komo da nasarar Sodom da ’ya’yanta mata da ta Samariya da ’ya’yanta mata, nasararki kuma tare da su, domin ki sha ƙasƙancinki ki kuma sha kunyar dukan abin da kika aikata ta wurin ta’azantar da su. ’Yan’uwanki kuwa, Sodom da ’ya’yanta mata da Samariya tare da ’ya’yanta mata, za su koma kamar yadda suke a dā; ke kuma da ’ya’yanki mata za ku koma kamar yadda kike a dā. Ba za ki ma iya ambaci ’yar’uwarki Sodom a ranar fariyarki ba, kafin a tone muguntarki. Ko da ma haka, yanzu ’ya’yan Arameyawa mata da dukan maƙwabtanta da kuma ’ya’yan Filistiyawa mata suna miki dariyar, dukan waɗanda suke kewaye da ke da suka rena ki. Za ki ɗauki hakkin lalatarki da kuma ayyukanki masu banƙyama, in ji Ubangiji.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta kamar yadda ya dace da ke, domin kin ƙyale rantsuwana ta wurin karya alkawari. Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin ƙuruciyarki, zan kuma kafa madawwamin alkawari da ke. Sa’an nan za ki tuna da hanyoyinki ki kuma ji kunya sa’ad da kika karɓi ’yan’uwanki mata, waɗanda suka girme ki da kuma waɗanda kika girme su. Zan ba da su kamar ’ya’ya mata gare ki, amma ba bisa alkawarina da ke ba. Ta haka zan kafa alkawarina da ke, za ki kuma san cewa ni ne Ubangiji. Sa’an nan, sa’ad da na yi kafara saboda ke domin dukan abin da kika aikata, za ki tuna ki kuma ji kunya har ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Gaggafa biyu da kuringa guda
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka shirya kacici-kacici ka faɗa wa gidan Isra’ila misali. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa babbar gaggafa mai manyan fikafikai, dogayen gasusuwa da gasusuwa da yawa masu launi iri-iri ta zo Lebanon. Ta cire kan al’ul, ta karya kan tohonsa da yake can bisansa ta kai ƙasar ciniki, inda ta shuka shi a birnin ’yan kasuwa.
“ ‘Ta ɗebi waɗansu irin ƙasarku ta sa a ƙasa mai taƙi. Ta shuka shi kamar itacen wardi kusa da ruwa mai yawa, ya kuwa yi toho ya zama kuringa gajeruwa mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajen gaggafar, amma saiwoyinta suka zauna a ƙarƙashinta. Ta haka ta zama kuringa, ta yi rassa ta kuma fid da ganyaye.
“ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Kuringan nan ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajen wannan gaggafa daga inda aka shuka ta, ta kuma miƙe rassanta wajenta don gaggafar ta yi mata banruwa. An shuka ta a ƙasa mai kyau kusa da ruwa mai yawa don tă yi rassa masu yawa, ta ba da ’ya’ya ta kuma zama kuringa mai daraja.’
“Ka gaya musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wannan za tă ci gaba? Ba za a tumɓuke ta a kuma kakkaɓe ’ya’yanta don ta bushe ba? Dukan sababbin tohonta za su bushe. Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba. Ko da an sāke shuka ta, za tă yi amfani ne? Ba za tă bushe gaba ɗaya sa’ad da iskar gabas ta hura ba, tă bushe a ƙasar da ta yi girma?’ ”
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ka faɗa wa gidan ’yan tawayen nan, ‘Ba ka san abin da waɗannan abubuwa suke nufi ba?’ Ka faɗa musu cewa, ‘Sarkin Babilon ya tafi Urushalima ya tafi da sarkinta da kuma manyan garinta, ya dawo da su Babilon. Sa’an nan ya ɗauki wani daga iyalin sarauta ya yi yarjejjeniya da shi, ya sa shi ya yi rantsuwa. Ya kuma tafi da shugabannin ƙasar, don a raunana masarautar, kada tă ƙara tashi, amma ta tsaya dai kan cika yarjejjeniyarsa. Amma sarkin nan ya yi tawaye a kan sarkin Babilon ta wurin aika jakadunsa zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. Zai ci nasara? Shi da ya yi wannan abu zai tsira? Zai iya taka yarjejjeniya har ya tsere?
“ ‘Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zai mutu a Babilon, a ƙasar sarkin nan da ya naɗa shi, domin bai cika rantsuwa da alkawarin da ya yi ba. Fir’auna da yawan sojojinsa da kuma yawan jama’arsa ba zai zama da taimako gare shi a yaƙi ba, sa’ad da sarkin Babilon zai gina mahaurai ya kuma yi ƙawanya don yă hallaka rayuka masu yawa. Bai cika rantsuwa ba ta wurin take alkawari. Domin sarkin Isra’ila ya ƙulla alkawari ya kuma aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai tsira ba.
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce muddin ina raye, zan nemi hakkin rantsuwata da ya ƙi cikawa da kuma alkawarin da ya take. Zan kafa masa tarkona, zai kuma fāɗi a tarkona. Zan kawo shi a Babilon in kuma hukunta shi a can domin ya yi mini rashin aminci. Dukan sojojinsa zaɓaɓɓu za a kashe su da takobi, za a kuma watsar da waɗanda suka ragu ko’ina. Ta haka za ku san cewa Ni Ubangiji na faɗa.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan cire toho a kan itacen al’ul da yake can bisa in shuka; zan kuma karya ƙanƙanin reshe daga can bisan tohon in shuka a dutse mai tsayi. A ƙwanƙolin dutsen Isra’ila zan shuka shi; zai yi rassa yă ba da ’ya’ya yă kuma zama al’ul mai daraja. Tsuntsaye iri-iri za su yi sheƙa a cikinsa; za su sami mafaka a inuwar rassansa. Dukan itatuwan jeji za su san cewa Ni Ubangiji ne mai sa manyan itatuwa su zama ƙanana in kuma sa ƙananan itatuwa su zama manya. Nakan sa ɗanyen itace ya bushe, busasshen itace kuma ya zama ɗanye.
“ ‘Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.’ ”
Mutumin da ya yi zunubi zai mutu
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa,
“ ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami,
haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’?
“Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba. Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.
“A ce akwai mai adalci
wanda yake aikata abin da yake daidai da kuma gaskiya;
ba ya cin abinci a duwatsun tsafi
ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila.
Ba ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa
ko ya kwana da mace lokacin al’adarta ba.
Ba ya cin zalin wani,
amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa.
Ba ya yi fashi
amma yakan ba wa mayunwata abinci
ya kuma tanada wa marasa tufafi riga.
Ba ya ba da bashi da ruwa
ko ya karɓa ƙarin riba.18.8 Ko kuwa karɓi riba; yadda yake a ayoyi 13 da 17
Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta
yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum.
Yana bin ƙa’idodina
yana kuma kiyaye dokokina da aminci.
Wannan mutumin adali ne;
tabbatacce zai rayu,
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“A ce yana da ɗa wanda yana kisa ko yana yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa18.10 Ko kuwa abubuwa ga ɗan’uwa (ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba).
“Yakan ci abinci a duwatsun tsafi.
Yakan ƙazantar da matar maƙwabci.
Yakan ci zalin matalauta da mabukata.
Yakan yi fashi.
Ba ya mayar da abin da aka jinginar masa.
Ya dogara ga gumaka.
Yana aikata ayyukan banƙyama.
Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa.
Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa.
“Amma a ce wannan ɗa yana da ɗa wanda ya ga dukan zunuban da mahaifinsa yake aikata, kuma ko da yake ya gan su, bai yi ko ɗaya daga cikin irin abubuwan nan ba, wato,
“Bai ci abinci a duwatsun tsafi ba
ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila.
Bai ƙazantar da matar maƙwabcinsa ba.
Bai ci zalin wani
ko ya karɓi jingina ba.
Ba ya fashi
amma yakan ba da abincinsa ga mayunwata
ya tanada tufafi wa marasa tufafi.
Yakan janye hannunsa daga zunubi18.17 Seftuwajin (duba kuma aya 8); Ibraniyanci daga matalauta
ba ya kuma ba da bashi da ruwa ko karɓan riba da yawa.
Yakan kiyaye dokokina ya kuma bi ƙa’idodina.
Ba zai mutu saboda zunubin mahaifinsa ba; tabbatacce zai rayu. Amma mahaifinsa zai mutu saboda zunubinsa, domin ya yi ƙwace, ya yi wa ɗan’uwansa fashi ya kuma yi abin da ba daidai ba a cikin mutanensa.
“Duk da haka kukan yi tambaya, ‘Me ya sa ɗan ba zai sami rabo a laifin mahaifinsa ba?’ Da yake ɗan ya yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina, tabbatacce zai rayu. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.
“Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu. Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba?
“Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.
“Duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ka ji, ya gidan Isra’ila. Hanyata ba daidai ba ce? In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu. Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa. Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. Duk da haka mutanen Isra’ila sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Hanyoyina ba daidai ba ne, ya gidan Isra’ila? Ba hanyoyinku ne ba daidai ba?
“Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba. Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila? Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!
Makoki domin sarakunan Isra’ila
“Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila ka ce,
“ ‘Mahaifiyarki zakanya ce
cikin zakoki!
Takan kwanta cikin ’yan zakoki
ta kuma yi renon kwiyakwiyanta.
Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta,
ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi.
Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta
yakan kuma cinye mutane.
Al’ummai suka ji labarinsa,
aka kuma kama shi cikin raminsu.
Suka ja shi da ƙugiyoyi
zuwa ƙasar Masar.
“ ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba,
abin da take fata gani ya tafi,
sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta
ta mai da shi zaki mai ƙarfi.
Ya yi ta yawo a cikin zakoki,
gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi.
Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta
yakan kuma cinye mutane.
Ya rurrushe kagaransu
ya kuma ragargaza biranensu.
Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta
sun tsorata da jin rurinsa.
Sai al’ummai suka tayar masa,
waɗannan daga yankunan da suke kewaye.
Suka yafa raga dominsa
ya kuwa fāɗa cikin raminsu.
Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji
suka kawo shi wurin sarkin Babilon.
Suka sa shi cikin kurkuku,
saboda haka ba a ƙara jin rurinsa
a kan duwatsun Isra’ila ba.
“ ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi
da aka shuka kusa da ruwa;
ta ba da ’ya’ya da kuma cikakkun rassa
saboda yalwan ruwa.
Rassanta suka yi ƙarfi,
suka dace da sandar mai mulki.
Ta yi tsayi
zuwa sama
ana ganin ta saboda tsayinta
da kuma saboda yawan rassanta.
Amma aka tumɓuke ta cikin fushi
aka jefar da ita a ƙasa.
Iskar gabas ta sa ta yanƙwane,
aka kakkaɓe ’ya’yanta;
rassanta masu ƙarfi suka bushe
wuta kuma ta cinye su.
Yanzu an shuka ta a hamada,
a busasshiyar ƙasa marar ruwa.
Wuta ta fito daga jikin rassanta
ta cinye ’ya’yanta.
Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta
da ya dace da sandar mai mulki.’
Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”
Isra’ila ’yan tawaye
A shekara ta bakwai, a wata na biyar a rana ta goma, waɗansu dattawan Isra’ila suka zo don su nemi nufin Ubangiji, suka kuwa zauna a ƙasa a gabana.
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi magana da dattawan Isra’ila ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kun zo ne ku nemi shawarata? Muddin ina raye, ba zan bari ku nemi shawarata ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
“Za ka hukunta su? Za ka hukunta su, ɗan mutum? To, sai ka kalubalance su da ayyukan banƙyamar kakanninsu ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na zaɓi Isra’ila, na ɗaga hannuna, na rantse wa zuriyar gidan Yaƙub na kuma bayyana kaina gare su a Masar da hannun da na ɗaga na ce musu, “Ni ne Ubangiji Allahnku.” A ranar na yi musu rantsuwa cewa zan fitar da su daga Masar zuwa ƙasar da na samo musu, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe. Na kuma ce musu, “Kowannenku ya zubar da mugayen siffofin da kuka kafa idanunku a kai, kuma kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
“ ‘Amma sai suka yi tawaye a kaina ba su kuwa saurare ni ba; ba su zubar da mugayen siffofin da suka kafa idanunsu a kai ba, balle su ƙi gumakan Masar. Saboda haka zan zubo hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a Masar. Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da suka zauna a ciki da kuma a idanun al’ummai da na bayyana kaina ga Isra’ilawa ta wurin fitar da su daga Masar. Saboda haka na fisshe su daga Masar na kawo su cikin hamada. Na ba su ƙa’idodina na kuma sanar musu da dokokina, gama mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu. Na kuma ba su Asabbataina kamar alama tsakaninmu, domin su san cewa Ni Ubangiji ne yake tsarkake su.
“ ‘Duk da haka mutanen Isra’ila suka yi mini tawaye a cikin hamada. Ba su bi ƙa’idodina ba amma suka ki dokokina, ko da yake mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu, suka ɓata Asabbataina ƙwarai. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma hallaka su a hamada. Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su. Na kuma ɗaga hannu na rantse musu a hamada cewa ba zan kawo su ƙasar da na ba su ba, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe, domin sun ƙi dokokina ba su kuwa bi ƙa’idodina ba suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Gama zukatansu sun fi so su bauta wa gumakansu. Duk da haka na dube su ta tausayi ba zan hallaka su ko in kawo ƙarshensu a hamada ba. Na faɗa wa ’ya’yansu a hamada, “Kada ku bi farillai kakanninku ko ku kiyaye dokokinsu ko ku ƙazantar da kanku da gumakansu. Ni ne Ubangiji Allahnku; ku bi ƙa’idodina ku kuma kula ku kiyaye dokokina. Ku kiyaye Asabbataina da tsarki, don su zama alama tsakaninmu. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Allahnku.”
“ ‘Amma ’ya’yan suka yi mini tawaye. Ba su bi ƙa’idodina ba, ba su kula su kiyaye dokokina ba, ko da yake mutumin da ya kiyaye su zai rayu ta wurinsu, suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a hamada. Amma na janye hannuna, kuma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su. Na kuma ɗaga hannu na rantse musu cewa zan watsar da su cikin al’ummai in kuma warwatsa su cikin ƙasashe, domin ba su kiyaye dokokina ba amma suka ƙi ƙa’idodina suka kuma ƙazantar da Asabbataina, idanunsu suka yi sha’awar gumakan kakanninsu. Na kuma ba da su ga farillan da ba su da kyau da dokokin da ba za su rayu ta wurinsu ba; na bari suka ƙazantu ta wurin kyautai, hadayar kowane ɗan fari20.26 Ko kuwa sa kowane ɗan fari ya ratsa wuta don in cika su da abin tsoro domin su san cewa ni ne Ubangiji.’
“Saboda haka, ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra’ila ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a wannan kuma kakanninku suka saɓe ni ta wurin yashe ni. Sa’ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su suka kuma ga tudu mai tsawo ko itace mai ganye, a can suka miƙa hadayunsu, suka yi sadakokin da suka tsokane ni na yi fushi, suka miƙa turaren ƙanshinsu suka kuma zuba sadakokinsu na sha. Sai na ce musu, Wane ɗakin tsafi kuke tafiya?’ ” (Ana ce da shi Bama20.29 Bama yana nufin masujadar kan tudu. har wa yau.)
Hukunci da Maidowa
“Domin haka ka faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa za ku ƙazantar da kanku yadda kakanninku suka yi ne ku yi sha’awar mugayen siffofinsu? Sa’ad da kuka miƙa kyautai naku, hadayar ’ya’yanku maza a20.31 Ko kuwa kuna sa ’ya’yanku maza su ratsa ciki wuta, kuna cin gaba da ƙazantar da kanku da duka gumakanku har wa yau. Zan bari ku nemi shawarata, ya gidan Isra’ila? Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba zan bari ku nemi shawarata ba.
“ ‘Kukan ce, “Kuna so ku zama kamar sauran al’ummai, kamar sauran mutanen duniya, waɗanda suke bauta wa itace da dutse.” Amma abin da kuke tunani ba zai taɓa faruwa ba. Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan yi mulki a kanku da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi. Zan fitar da ku daga al’ummai in tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi. Zan kawo ku cikin hamadar al’ummai a can kuwa, fuska da fuska, zan hukunta ku. Yadda na hukunta kakanninku a hamadar ƙasar Masar, haka zan hukunta ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan lura da ku yayinda kuke wucewa ƙarƙashin sanda, zan kuma kawo ku cikin daurin alkawari. Zan fitar da waɗanda suke mini tayarwa da kuma ’yan tawaye. Ko da yake zan fitar da su daga ƙasar da suke zama, duk da haka ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘Game da ku, ya gidan Isra’ila, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tafi ku bauta wa gumakanku, kowannenku! Amma daga baya tabbatacce za ku saurare ni ba kuwa za ku ƙara ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku ba. Gama a kan dutsena mai tsarki, dutse mai tsayi na Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, a can a ƙasar gidan Isra’ila gaba ɗaya za su bauta mini, a can kuwa zan karɓe su. A can zan bukaci hadayunku da sadake sadakenku mafi kyau,20.40 Ko kuwa da kyautai ’ya’yan farinku tare da dukan tsarkakan hadayunku. Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa’ad da na fitar da ku daga al’ummai na kuma tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, zan kuma nuna kaina mai tsarki a cikinku a idon al’ummai. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na kawo ku cikin ƙasar Isra’ila, ƙasar da na ɗaga hannu na rantse zan ba wa kakanninku. A can za ku tuna da halinku da kuma dukan ayyukanku waɗanda kuka ɓata kanku da su, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwan da kuka aikata. Za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na yi muku haka saboda sunana ba bisa ga mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau ba, ya gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Annabci a kan kudu
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka kafa fuskarka wajen kudu; ka yi wa’azi a kan kudu ka kuma yi annabci a kan kurmin ƙasar kudu. Ka faɗa wa kurmin kudanci, ‘Ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da sa maka wuta, za tă kuwa cinye dukan itatuwanki sarai, da ɗanye da busasshe. Ba za a kashe wutar da take ci ba, kuma kowace fuska a kudu zuwa arewa za tă ƙone. Kowa zai san cewa Ni Ubangiji ne ya ƙuna ta; ba za a kashe ta ba.’ ”
Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Suna zance a kaina cewa, ‘Ba misalai kawai yake yi ba?’ ”
Babilon, takobin hukuncin Allah
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka kafa fuskarka gāba da Urushalima ka kuma yi wa’azi a kan wuri mai tsarki. Ka yi annabci gāba da ƙasar Isra’ila ka faɗa mata, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina gāba da ke. Zan ja takobina daga kubensa in karkashe adalai da mugaye daga cikinki. Domin zan karkashe adalai da kuma mugaye, ba zan rufe takobina a kan kowa daga kudu zuwa arewa ba. Sa’an nan duka mutane za su san cewa Ni Ubangiji na ja takobina daga kubensa; ba zai sāke koma kuma ba.’
“Saboda ka yi nishi, ɗan mutum! Yi nishi a gabansu da ajiyar zuciya da ɓacin rai. Kuma sa’ad da suka tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Domin labarun da suke fitowa. Kowace zuciya za tă narke kowane hannu kuma ya gurgunta; kowane ruhu zai sume kowane gwiwa kuma ta rasa ƙarfi kamar ruwa.’ Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“ ‘Takobi, takobi,
wasasshe da kuma gogagge,
wasasshe don kisa,
gogagge har yana walwal kamar walƙiya!
“ ‘Kada ku yi farin ciki, hukunci yana zuwa, domin kowa ya ƙi jin abin da na yi gargaɗi a kai.
“ ‘An ba da wannan takobi don a goge,
don a kama da hannu;
an washe shi aka kuma goge,
shiryayye don a yi kisa da shi.
Ka yi kuka ka yi makoki, ɗan mutum,
gama yana gāba da dukan sarakunan Isra’ila.
An jefa su ga takobi
tare da jama’ata.
Saboda haka ku buga ƙirjinku.
“ ‘Gwaji tabbatacce zai zo. Kuma a ce sandan Yahuda, wanda takobi ya ƙi, ya ci gaba? In ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
“Saboda haka fa, ɗan mutum ka yi annabci
ka kuma tafa hannuwanka.
Bari takobi ya yi sara sau biyu,
har sau uku ma.
Takobin kisa ne,
takobi ne don kisa mai girma,
zai kewaye su a kowane gefe.
Domin zukata su narke
da yawa kuma su fāɗi,
na tsai da takobin kisa
a dukan ƙofofinsu.
Kash! A sa ya haska kamar walƙiya,
ana riƙe da shi don kisa.
Ya takobi, yi sara zuwa dama
ka yi kuma zuwa hagu,
duk inda aka juya ka.
Zan tafa hannuwana,
fushina kuwa zai sauka.
Ni Ubangiji na faɗa.”
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka nuna hanyoyi biyu inda takobin sarkin Babilon zai bi, duka biyun su fara daga ƙasa guda. Ka kafa shaida inda hanyar za tă rabu zuwa cikin birni. Ka nuna hanya guda wadda takobi zai fāɗo wa Rabba ta Ammonawa ɗayan kuma da zai fāɗo a kan Yahuda da kuma Urushalima mai katanga. Gama sarkin Babilon zai tsaya a mararrabar hanya, a inda hanyar ta rabu biyu, don yă yi duba. Zai jefa ƙuri’a da kibiyoyinsa, zai nemi shawarar gumakansa, zai bincike hanta. A hannunsa na dama ƙuri’a don Urushalima za tă fito, inda zai kafa dundurusai, ya ba da umarni kisa, a yi kururuwar yaƙi, a kafa dundurusai a kan ƙofofi, a gina mahaurai a kuma yi ƙawanya. Zai zama kamar duban ƙarya ne ga waɗanda suka yi rantsuwar yin masa biyayya, amma zai tunashe su game da laifinsu ya kuma kama su.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku mutanen nan kun tuna da laifinku ta wurin tawaye, kun kuma bayyana zunubanku cikin dukan abin da kuke yi, domin kun yi haka, za a kama ku.
“ ‘Ya kai ƙazantaccen mugu, yerima Isra’ila, wanda kwanansa ta zo, wanda lokacin hukuncinsa ya cika fal, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka kunce rawanin, ka ɗauke rawanin nan. Ba zai zama kamar yadda yake ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da mai girma. Hallaka! Hallaka! Zan hallaka shi! Ba za a maido da shi ba sai ya ga ainihin mai shi; gare shi zan bayar da shi.’
“Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu.
“ ‘Takobi, takobi,
an ja don kisa,
an goge don cinyewa
yana haske kamar walƙiya!
Duk da wahayin ƙarya game da kai,
duban ƙarya game da kai,
za a sa shi a wuyan
mugaye waɗanda za a kashe,
waɗanda kwanansu ta zo,
waɗanda lokacin hukuncinsu ya cika fal.
“ ‘Ka mai da takobi a kubensa.
A inda aka halicce ka,
a ƙasar kakanninka,
zan hukunta ka.
Zan zub da hasalata a kanka
in hura maka wutar fushina;
Zan ba da kai a hannun mugayen mutanen
da suka gwanince a hallakarwa.
Za ka zama itacen wuta,
za a zub da jininka a ƙasarka,
ba za a ƙara tuna da kai ba;
gama Ni Ubangiji na faɗa.’ ”
Zunubin Urushalima
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
“Ɗan mutum, za ka shari’anta ta? Za ka shari’anta wannan birni mai kisankai? To, sai ka kalubalance ta da dukan ayyukanta na banƙyama ka kuma ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ya birnin da take kawo wa kansa hallaka ta wurin kisankai a cikinta kina kuma ƙazantar da kanki ta wurin yin gumaka, kin zama mai laifi saboda jinin da kika zubar kika kuma zama ƙazantacciya ta wurin gumakan da kika yi. Kin kawo kwanakinki ga ƙarshe, kuma ƙarshen shekarunki sun zo. Saboda haka zan mai da ke abar ba’a ga al’ummai da abin dariya ga dukan ƙasashe. Waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa za su yi miki ba’a, ya ke birni marar kunya, cike da rigima.
“ ‘Duba yadda kowane yerima Isra’ila waɗanda suke cikinki yake yin amfani da ikonsa yana kisankai. A cikinki sun rena mahaifi da mahaifiya; a cikinki sun zalunci baƙo suka wulaƙanta maraya da gwauruwa. Kin rena abubuwana masu tsarki kika kuma ƙazantar da Asabbataina. A cikinki akwai mutane waɗanda suka nace su yi kisankai; a cikinki akwai waɗanda suke ci a dutsen tsafi suna yin ayyukan lalata. A cikinki akwai waɗanda suke kwana da matan mahaifansu; a cikinki akwai waɗanda suke kwana da mata a lokacin da suke al’adarsu, sa’ad da suke da rashin tsarki. A cikinki mutum guda yakan yi laifi abin ƙyama da matar maƙwabcinsa, wani cikin rashin kunya ya ƙazantar da matar ɗansa, wani kuma ya kwana da ’yar’uwansa, ’yar mahaifinsa. A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki. Ƙarfin halinki zai jure ko kuwa hannuwanki za su yi ƙarfi a ranar da na gamu da ke? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata. Zan watsar da ke cikin al’ummai in warwatsa ke cikin ƙasashe; zan kuma kawo ƙarshen rashin tsarkinki. Sa’ad da ki ƙazantu22.16 Ko kuwa Sa’ad da na raba ki da gādonki a idanun al’umma, za ki san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, gidan Isra’ila ta zama ƙwan maƙera a gare ni; dukansu tagulla ne, kuza, ƙarfe da darma da suka rage a tanderu. Su ƙwan maƙerar azurfa ne kawai. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku duka kun zama ƙwan maƙera, zan tattara ku a Urushalima. Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, tagulla, ƙarfe, darma da kuza a cikin tanderu don su narkar da su da wuta, haka zan tattara ku cikin fushina da kuma hasalata in sa ku cikin birnin in narkar da ku. Zan tattara ku zan kuma hura muku wutar hasalata, za ku kuma narke a cikinta. Kamar yadda azurfa kan narke a tanderu, haka za ku narke a cikinta, kuma za ku san cewa Ni Ubangiji na zubo muku da zafin fushina.’ ”
Har yanzu maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa, “Ɗan mutum, ka faɗa wa ƙasar, ‘Ke ƙasa ce marar ruwan sama ko yayyafi a ranar hasala.’ Akwai haɗin bakin sarakunanki a cikinki kamar rurin zaki mai yayyage ganimarsa; suna cin mutane, suna kwashe dukiya da abubuwa masu daraja suna mai da yawanci gwauraye a cikinki. Firistocinki suna karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana; ba sa bambanta tsakanin tsarki da marar tsarki; suna koyarwa cewa babu bambanci tsakanin marar tsarki da mai tsarki; suna kuma rufe idanunsu ga kiyaye Asabbataina, da haka suke saɓon sunana. Shugabanninki a cikinki suna kama da kyarketai masu yayyage ganimarsu; suna kisa suna kuma kashe mutane don samun ƙazamar riba. Annabawanki sun yi wa waɗannan ayyuka shafe da farar ƙasa ta wurin wahayin ƙarya da duban ƙarya. Suna cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa’ alhali kuwa Ubangiji bai faɗa ba. Mutanen ƙasar na yin ƙwace suna yin fashi; suna cin zalin matalauta da mabukata suna wulaƙanta baƙo suna hana musu adalci.
“Na nemi mutum guda a cikinsu wanda zai gina katanga ya tsaya a gabana a tsakani a madadin ƙasar don kada in hallaka ta, amma ban sami ko ɗaya ba. Saboda haka zan zuba hasalata a kansu in cinye su da wutar fushina, ina ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
’Yan mata biyu mazinata
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, an yi mata biyu, ’yan matan mahaifiya guda. Suka zama karuwai a Masar, suka yi karuwanci tun daga ƙuruciyarsu. A wancan ƙasar an rungumi mamansu da ƙirjinsu na budurwanci. Sunan babbar Ohola, ƙanuwarta kuwa Oholiba. Sun zama nawa suka kuma haifi ’ya’ya maza da mata. Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.
“Ohola ta shiga karuwanci yayinda take zamana; ta kuwa yi ta kai da kawowa da kwartayenta, Assuriyawa, mayaƙa waɗanda suke saye da shunayya, gwamnoni da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha’awa, suna bisa kan dawakai. Ta ba da kanta ga duk waɗanda suke masu ilimin Assuriya ta kuma ƙazantar da kanta da dukan gumaka na kowa da take kai da kawowa a cikinsu. Ba ta bar karuwancin da ta fara a Masar ba, sa’ad da take budurwa maza sun kwana da ita, suka rungumi ƙirjinta suka kuma biya kwaɗayinsu a kanta.
“Saboda haka na bashe ta ga kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu. Suka tuɓe ta tsirara, suka kwashe ’ya’yanta maza da mata suka kuma kashe ta da takobi. Ta kuwa zama abin karin magana a cikin mata, aka kuma yi mata hukunci.
“Ƙanuwarta Oholiba kuwa ta ga wannan, duk da haka cikin kai da kawowarta da karuwancinta ta fi ’yar’uwar lalacewa. Ita ma ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, gwamnoni da manyan sojoji; mayaƙa masu saye da kayan yaƙi, suna bisa dawakai, dukansu samari ne masu bansha’awa. Na ga cewa ita ma ta ƙazantar da kanta; dukansu biyu sun bi hanya guda.
“Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a kan bango, siffofin sojojin Kaldiyawa23.14 Ko kuwa Babiloniyawa suna cikin jajjayen riguna, da ɗamara a gindinsu da rawuna a kansu suna kaɗawa falfal; dukansu sun yi kamar jarumawan kekunan yaƙin Babiloniyawa ’yan Kaldiya.23.15 Ko kuwa Babiloniya; haka ma a aya 16 Nan da nan da ta gan su, sai ta yi sha’awarsu ta aika da ’yan aika zuwa wurinsu a Kaldiya. Sai Babiloniyawan suka zo wurinta, zuwa gadon soyayya, cikin kai da kawowarsu suka ƙazantar da ita. Bayan sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su. Sa’ad da ta ci gaba da yin karuwancinta a fili ta kuma nuna tsiraicinta, sai na ji ƙyamarta, na rabu da ita, kamar dai yadda na rabu da ’yar’uwarta. Duk da haka sai ta yi ta ƙara fasikanci tana tuna da kwanakin budurcinta, sa’ad da take karuwa a Masar. A can ta yi ta kai da kawowa da kwartayenta, waɗanda al’auransu kamar na jakuna ne waɗanda maniyyinsu kuwa kamar na dawakai ne. Haka kika yi ta lalacin budurcinki, sa’ad da a Masar aka rungumi ƙirjinta aka tattaɓa nononta.23.21 Siriyak (dubi kuma 3); Ibraniyanci runguma saboda mamanki da suka fita sabo
“Saboda haka, Oholiba, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan zuga kwartayenki su yi gāba da ke, su waɗanda kika ji ƙyamarsu, zan kuma kawo su su yi gāba da ke daga kowane gefe, Babiloniyawa da dukan Kaldiyawa, mutanen Fekod da Showa da Kowa, da dukan Assuriyawa, samari masu bansha’awa, dukan gwamnoni da manyan sojoji, hafsoshin keken yaƙin da mutane masu manyan matsayi, dukansu a bisa dawakai. Za su yi gāba da ke da kayan yaƙi,23.24 Ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma babu tabbas. kekunan yaƙi da kekunan doki da mutane masu yawa; za su ja dāgā a kanki a kowane gefe da garkuwoyi manya da ƙanana da kuma hulunan kwano. Zan miƙa ke gare su don hukunci, za su kuma hukunta ki bisa ga shari’arsu. Zan nuna fushin kishina a kanki, za su kuwa wulaƙanta ki da fushi. Za su yanke hancinki da kunnuwanki, waɗanda suka rage miki kuma za a kashe su da takobi. Za su kama ’ya’yanki maza da mata, waɗanda suka rage miki kuwa za a ƙone su da wuta. Za su tuɓe tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau. Ta haka zan tsai da marmari da kuma karuwancin da kika fara a Masar. Ba za ki dubi waɗannan abubuwa da marmari ko ki ƙara tuna da Masar ba.
“Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina shirin miƙa ki ga waɗanda suke ƙinki, ga waɗanda kika ji ƙyamarsu kika rabu da su. Za su hukunta ki da ƙiyayya su kuma kwashe kome da kika yi wahalarsa. Za su bar ki tsirara tik, kunyan karuwancinki kuma zai tonu. Marmarinki da fasikancinki sun jawo miki wannan, domin ki yi ta kai da kawowa cikin ƙasashe kina ƙazantar da kanki da gumakansu. Kin bi hanyar ’yar’uwarki; saboda haka zan sa kwaf nata a hannunki.
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“Za ki sha kwaf na ’yar’uwarki,
kwaf wanda yake da girma da kuma zurfi;
zai jawo dariya da kuma reni
gama yana ɗauke da abubuwa da yawa.
Za ki cika da buguwa da baƙin ciki,
kwaf lalaci da kaɗaici,
kwaf na ’yar’uwarki Samariya.
Za ki sha shi ki kuma lashe shi ƙaf;
za ki buga shi da ƙasa ya yi rugu-rugu
ki tsattsage nononki.
Ni Ubangiji Mai Iko Duka na faɗa.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa da yake kin manta da ni kika tura ni bayanki, dole ki sha sakamakon marmarinki da karuwancinki.”
Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, za ka shari’anta Ohola da Oholiba? To, sai ka kalubalance su da ayyukansu masu banƙyama, gama sun yi zina kuma jinin yana a hannuwansu. Sun yi zina da gumakansu; har suka miƙa ’ya’yansu da suka haifa mini,23.37 Ko kuwa har sun mai da ’ya’yan da suka haifa mini su ratsa cikin wuta su zama musu abinci. Sun kuma yi mini wannan. A lokaci guda sun ƙazantar da wuri mai tsarkina suka ɓata Asabbataina. A ranar da suka miƙa ’ya’yansu ga gumakansu, sai suka shiga wuri mai tsarkina suka kuma ƙazantar da shi. Abin da suka yi a gidana ke nan.
“Sun ma aiki manzanni wa mutanen da suka zo daga nesa, kuma da suka iso kun yi wanka dominsu, kuka yi shafe-shafen idanunku, kuka kuma sa kayan adonku. Kuka zauna a gado mai daraja, da tebur a shirye a gabanku wanda kun ajiye turare da maina.
“Surutun taron mutane marasa kula suna kewaye da ita; aka kawo Sabenawa23.42 Ko kuwa bugaggu daga hamada tare da mutane daga mashaya, suka sa mundaye a hannuwan macen da kuma ’yar’uwarta suka kuma sa rawani masu kyau a kawunansu. Sai na yi magana a kan wadda ta ƙare ƙarfi ta wurin karuwanci na ce, ‘Yanzu bari su yi amfani da ita kamar karuwa, gama abin da take ke nan.’ Suka kuwa kwana da ita. Kamar yadda maza suke kwana ta karuwa, haka suka kwana da waɗannan lalatattun mata, Ohola da Oholiba. Amma masu adalci za su hukunta su irin da akan yi wa matan da suka yi zina suka kuma yi kisa, domin su mazinata ne kuma jini yana a hannuwansu.
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kawo taron mutane a kansu a kuma miƙa su don a firgitar da su a kuma washe su. Taron mutanen za su jajjefe su, su kuma sassare su da takuba; za su kashe ’ya’yansu maza da mata su kuma ƙone gidajensu.
“Ta haka zan kawo ƙarshe ga lalaci a ƙasar, don dukan mata su ji gargaɗi kada kuma su kwaikwaye ku Za ku sha hukuncin lalacinku ku kuma ɗauki hakkin zunuban bautar gumaka. Sa’an nan za ku san cewa Ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.”
Tukunyar dahuwa
A shekara ta tara, a wata na goma, a rana ta goma, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka rubuta wannan rana, wannan rana, domin sarkin Babilon ya yi ƙawanya wa Urushalima a wannan rana. Ka faɗa wa wannan gidan ’yan tawaye wani misali ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ka sa tukunyar dahuwa; ka sa ta a kan wuta
ka kuma zuba ruwa a cikinta.
Ka sa gunduwoyin nama a cikinta
dukan gunduwoyi masu kyau, cinya da kafaɗa.
Ka cika ta da waɗannan ƙasusuwa mafi kyau;
ka kama mafi kyau daga cikin garken.
Ka tara itace a ƙarƙashinta saboda ƙasusuwan;
ka sa ta tafasa
ka kuma dafa ƙasusuwan a cikinta.
“ ‘Gama wannan shi ne abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini,
ga tukunya wadda take da tsatsa,
wadda tsatsarta ba za tă fita ba!
Ka fitar da shi gunduwa-gunduwa
ba tare da jefa ƙuri’a a kansu ba.
“ ‘Gama zubar da jini yana a tsakiyarta,
ta zubar da shi a dutsen da yake a fili;
ba tă zubar da shi a ƙasa ba,
inda ƙura za tă rufe shi.
Don a zuga hasala a kuma yi sakayya
na sa jininta a dutsen da ba a rufe ba,
saboda kada a rufe.
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Kaito birnin nan mai zubar da jini!
Ni ma zan jibge itace da yawa.
Ka tula gumagumai
ka kuma ƙuna wuta.
Ka dafa naman da kyau,
kana haɗawa da yaji;
ka kuma bar ƙasusuwan su ƙone.
Sa’an nan ka sa tukunyan nan da babu kome a kan garwashi
sai ta yi zafi har darmarta ta yi ja wur
domin dattinta ya narke
tsatsarta kuma ta ƙone.
Ta gajiyar da dukan ƙoƙari;
ba a fid da tsatsarta nan mai yawa ba,
kai, ko a wuta ma.
“ ‘Yanzu ƙazantarki ita ce lalaci. Domin na yi ƙoƙari in tsabtacce ke amma ba ki tsabtattu daga ƙazantarki ba, ba za ki ƙara yin tsabta ba sai hasalata a kanki ya kwanta.
“ ‘Ni Ubangiji na faɗa. Lokaci ya zo da zan aikata. Ba zan janye ba; ba zan ji tausayi ba, ba kuwa zan bari ba. Za a hukunta ki bisa ga hali da ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Matar Ezekiyel ta rasu
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, da farat ɗaya ina gab da ɗauke abin da idanunka suke jin daɗin gani. Duk da haka kada ka yi makoki ko ka yi kuka ko ka zub da hawaye. Ka yi nishi shiru; kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka ka kuma sa takalmanka a ƙafa; kada ka rufe sashen fuskarka daga ƙasa ko ka ci abincin da masu kuka sukan ci.”
Da gari ya waye, sai na yi magana da mutane, da yamma kuwa matata ta rasu. Kashegari na yi yadda aka umarce ni.
Sai mutane suka tambaye ni suka ce, “Ba za ka faɗa mana abin da waɗannan abubuwa suke nufi a gare mu ba?”
Sai na ce musu, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da ƙazantar da wuri mai tsarkina, kagarar da kuke taƙama, abin da idanunku suke jin daɗin gani, abin faranta zuciyarku. ’Ya’yanku maza da mata waɗanda kun bari a baya za su mutu ta wurin takobi. Za ku kuma yi yadda na yi. Ba za ku rufe sashe ƙasa na fuskarku ko ku ci abinci da masu kuka sukan ci ba. Za ku naɗa rawunanku a kai ku sa takalmanku a ƙafafunku. Ba za ku yi kuka ko makoki ba amma za ku lalace saboda zunubanku ku kuma yi ta yin nishi. Ezekiyel zai zama alama gare ku; za ku yi daidai yadda ya yi. Sa’ad da wannan ya faru, za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’
“Kai kuma ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu kagararsu, farin cikinsu da darajarsu, abin da idanunsu ke jin daɗin gani, abin da yake faranta musu zuciya, da kuka ’ya’yansu maza da mata, a ranan nan wanda ya tsere zai zo don yă ba ka labari. A lokacin bakinka zai buɗe, za ka yi magana da shi ba kuwa za ka ƙara yin shiru ba. Ta haka za ka zama alama gare su, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.”
Annabci a kan Ammon
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa ka kuma yi annabci a kansu. Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun ce “Yauwa” a kan wuri mai tsarkina sa’ad da aka ƙazantar da shi da kuma a kan ƙasar Isra’ila sa’ad da aka mai da ita kufai da lokacin da aka kai mutanen Yahuda bautar talala, saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci ’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku. Zan mai da Rabba wurin kiwo don raƙuma, Ammon kuma wurin hutu don tumaki. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun tafa hannuwanku kuka kuma buga ƙafafunku, kuna farin ciki don nuna dukan ƙiyayyarku a kan ƙasar Isra’ila, saboda haka zan miƙa hannuna gāba da ku in kuma ba da ku ganima ga al’ummai. Zan datse ku daga al’ummai in kuma kore ku daga ƙasashe. Zan hallaka ku, za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Annabci a kan Mowab
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Mowab da Seyir sun ce, “Duba, gidan Yahuda ta zama sauran al’ummai,” saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab, farawa daga garuruwan da suke kan iyaka, Bet-Yeshimot, Ba’al-Meyon da Kiriyatayim, darajar ƙasar. Zan ba da Mowabawa tare da Ammonawa ga mutanen Gabas abin mallaka, don kada a ƙara tuna da Ammonawa a cikin al’ummai; zan hukunta Mowabawa. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Annabci a kan Edom
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Edom ya ɗauki wa kanta fansa a kan gida Yahuda, ta yi babban laifi ta wurin yin haka, saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan miƙa hannuna a kan Edom in kashe mutanenta da dabbobinsu. Zan sa ta zama kufai, kuma tun daga Teman har zuwa Dedan za a kashe su da takobi. Zan ɗau fansa a kan Edom ta hannun mutanena Isra’ila, za su kuwa hukunta Edom bisa ga fushina da hasalata; za su san sakayyata, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Annabci a kan Filistiya
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Filistiyawa sun yi sakayya, suka ɗauki fansa da mugunta a zukatansu, da kuma daɗaɗɗen ƙiyayya sun nemi su hallaka Yahuda, saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da miƙa hannuna a kan Filistiyawa, zan kuwa datse Keretawa in kuma hallaka waɗanda suka rage a bakin teku. Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani cikin hasalata. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na ɗauki fansa a kansu.’ ”
Annabci a kan Taya
A shekara ta goma sha ɗaya, a rana ta fari ga wata, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, domin Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Yauwa! Ƙofar zuwa al’ummai ta karye, an kuma buɗe mini ƙofofinta; yanzu da take kufai zan wadace,’ saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da ke, ya Taya, zan kuwa kawo al’ummai masu yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa. Za su hallaka katangar Taya su kuma rurrushe hasumiyoyinta; zan kankare tarkacenta, in maishe ta fā. Za tă zama wurin shanya abin kamun kifi a tsakiyar teku, gama na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Za tă zama ganima ga sauran al’ummai, za a kashe mazaunan filin ƙasar da takobi. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji.
“Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa daga arewa zan kawo wa Taya Nebukadnezzar26.7 Da Ibraniyanci Nebukadrezzar, wanda Nebukadnezzar wata hanyar ce na rubuta sunan; a nan da kuma sau da yawa Ezekiyel da Irmiya sun cika amfani da wannan hanyar rubuta sunan. sarkin Babilon, sarkin sarakuna, tare da dawakai da kekunan yaƙi, da mahayan dawakai da babbar rundunar soja. Zai kashe mazaunan filin ƙasar da takobi; zai yi miki ƙawanya, ya gina miki mahaurai, sa’an nan ya rufe ki da garkuwoyi. Zai rushe katangarki da dundurusai, ya rurrushe hasumiyoyinki da makamai. Dawakansa za su yi yawa har su rufe ke da ƙura. Katanga za su girgiza saboda motsin dawakan yaƙi, kekunan doki da keken yaƙin sa’ad da suka shiga birnin da aka rushe katangar. Kofatan dawakansa za su tattake dukan titunanki; zai kashe mutanenki da takobi, ginshiƙanki masu ƙarfi kuma za su fāɗi a ƙasa. Za su washe dukiyarki, kayan cinikinki kuma su zama ganima; za su rurrushe katangarki su ragargaza gidajenki masu kyau su kuma zubar da duwatsunki, katakanki da kuma tarkacenki a cikin teku. Zan kawo ƙarshen waƙoƙinki masu surutu, ba kuwa za a ƙara jin kaɗe-kaɗen garayunki ba. Zan maishe ki fā, za ki kuma zama wurin shanya abin kamun kifi. Ba za a sāke gina ki ba, gama Ni Ubangiji na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Taya. Ƙasashen da suke a bakin teku ba za su girgiza saboda ƙarar fāɗuwarki, sa’ad da nishin waɗanda aka yi wa rauni da kashe-kashen da aka yi a cikinki suka faru ba? Sa’an nan sarakunan bakin teku za su sauka daga gadajen sarautarsu, su tuɓe rigunansu, da rigunansu waɗanda aka yi wa ado. Za su zauna a ƙasa suna rawar jiki a kowane lokaci suna razana saboda abin da ya same ki. Sa’an nan za su yi makoki game da ke su ce,
“ ‘Yaya kika hallaka haka nan, ya birnin da ta yi suna,
cike da mutanen teku!
Ke da kika zama mai ƙarfi cikin tekuna,
ke da mazauna cikinki;
kin sa tsoronki
a kan dukan waɗanda suka zauna a can.
Yanzu tsibirai suna rawar jiki
a ranar fāɗuwarki;
tsibirai a cikin teku
sun tsorata a ɓacewarki.’
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na maishe ki kufai, kamar sauran biranen da ba a ƙara zama a ciki, sa’ad da kuma na kawo zurfafan teku a kanki da yawan ruwansa suka rufe ki, a sa’an nan zan sauko da ke ƙasa tare da waɗanda suke gangarawa zuwa rami, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna ƙarƙashin ƙasa, kamar a kufai na tun dā, tare da waɗanda suke gangarawa zuwa rami, ba kuwa za ki ƙara dawowa ba ko ki ɗauki matsayinki26.20 Seftuwajin; Da Ibraniyanci dawo, zan kuma ba da darajarki a ƙasar masu rai. Zan sa ki yi mummunan ƙarshe kuma ba za ki ƙara kasancewa ba. Za a neme ki, amma ba za a ƙara same ki ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Makoki domin Taya
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya. Ka ce wa Taya, wadda take zaune a hanyar shiga zuwa teku, kasuwar masu yawa mutane a bakin teku, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Kin ce, ya Taya,
“Ni kyakkyawa ce cikakkiya.”
Manyan tekuna ne wurin zamanki;
maginanki sun sa kyanki ya zama cikakke.
Sun yi dukan katakanki
daga itatuwan fir daga Senir;27.5 Wato, Hermon
sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon
don su yi miki jigon jirgin ruwa.
Da oak daga Bashan
suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa
da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus
suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.
Lilin mai kyau mai ado daga Masar ne filafilan jirgin ruwanki
suka kuma zama tutarki;
an yi tutarki da shuɗi da shunayya
daga bakin tekun Elisha.
Mutanen Sidon da Arfad su ne matuƙan jirgin ruwanki;
gwanayenki, ya Taya, suna ciki a matsayi matuƙan jiragen ruwa.
Masu hikima na Gebal27.9 Wato, Baibilos suna ciki
a matsayin masu tattoshe mahaɗan katakon jirginki.
Dukan jiragen ruwa da matuƙansu
sukan zo wurinki don kasuwanci.
“ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut
su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki.
Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki,
suna kawo miki daraja.
Mutanen Arfad da Helek
sun yi tsaron katangar a kowace gefe;
mutanen Gammad
su ne a hasumiyoyinki.
Sun rataye garkuwoyinsu kewaye da katangarki;
sun sa kyanki ya zama cikakke.
“ ‘Tarshish ta yi ciniki da ke saboda yawan wadatar kayayyakinki; sun sayi kayan cinikinki da azurfa, ƙarfe, kuza da dalma.
“ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla.
“ ‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai.
“ ‘Mutanen Dedan sun yi kasuwanci da ke, bakin teku masu yawa abokan cinikinki ne; sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya.
“ ‘Mutanen Aram27.16 Da yawa cikin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci; waɗansu rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da na Siriyak Edom sun yi ciniki da ke saboda yawan kayanki; suka sayi kayan cinikinki da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.
“ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa,27.17 Ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma babu tabbas. da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.
“ ‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar. Wedan da Yaban kusa da Uzal, suka sayi kayanki; wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.
“ ‘Mutanen Dedan sun sayi kayanki da sirdin zama a kan dawakai.
“ ‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da ’yan raguna, da raguna, da awaki.
“ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya.
“ ‘Haran, Kanne da Eden da kuma ’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke. A kasuwarki sun yi ciniki da ke suka sayar miki tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da dardumai masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tuƙa da kyau.
“ ‘Jiragen ruwan Tarshish sun zama
masu jigilar kayanki.
Kin cika da kaya masu nauyi
a tsakiyar teku.
Matuƙan jiragenki sun kai ki
can cikin manyan tekuna.
Amma iskar gabas za tă farfasa ki kucu-kucu
a tsakiyar teku.
Dukiyarki, cinikinki da kayan kasuwarki,
ma’aikatanki na jirgi, matuƙan jiragenki da masu tattoshe mahaɗan katakan jiragenki,
’yan kasuwarki da dukan sojojinki,
da kuma kowa da yake cikin jirgi
zai nutsa a tsakiyar teku
a ranar da jirginki zai nutse.
Ƙasashen bakin teku za su girgiza
sa’ad da matuƙan jirginki suka yi kuka.
Dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi
za su ƙyale jiragensu;
ma’aikatan jirage da dukan matuƙan jirage
za su tsaya a bakin teku.
Za su tā da muryarsu
su yi kuka mai zafi a kanki;
za su yayyafa ƙura a kawunansu,
su yi ta birgima a cikin toka.
Za su aske kawunansu saboda ke
za su kuma sa tufafin makoki.
Za su yi kuka dominki su yi ɓacin rai
da kuma kuka mai zafi.
Yayinda suke kuka a kanki kuwa,
za su yi makoki dominki suna cewa,
“Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya,
kewaye da teku?”
Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi,
kin gamsar da al’ummai masu yawa;
da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki
kin azurtar da sarakunan duniya.
Yanzu teku ta farfashe ki
cikin zurfafan ruwaye;
kayan cinikinki da dukan kamfaninki
sun nutse tare da ke.
Dukan mazaunan bakin teku
sun giggice saboda masifarki;
sarakunansu sun tsorata ƙwarai
fuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro.
’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki;
kin zo ga mummunar ƙarshe
ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”
Annabci a kan sarkin Taya
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka faɗa wa mai mulkin Taya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Cikin alfarmar zuciyarka
ka ce, “Ni allah ne;
ina zama a kan kursiyin allah
a tsakiyar tekuna.”
Amma kai mutum ne ba allah ba,
ko da yake ka ɗauka kana da hikima kamar allah.
Ka fi Daniyel hikima ne?28.3 Ko kuwa Danel; yadda aka rubuta Ibraniyanci na wannan suna zai yi kamar ana zance wani dabam ne da annabi Daniyel.
Ba asirin da yake ɓoye a gare ka?
Ta wurin hikimarka da ganewarka
ka sami dukiya wa kanka
ka kuma tara zinariya da azurfa
cikin wuraren ajiyarka.
Ta wurin dabararka mai girma cikin kasuwanci
ka ƙara dukiyarka,
kuma saboda dukiyarka
zuciyarka ta cika da alfarma.
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Domin ka ɗauka kai mai hikima ne,
mai hikima kamar allah,
zan kawo baƙi a kanka,
waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai;
za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka
su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya.
Za su jefar da kai cikin rami,
za ka kuwa yi muguwar mutuwa
a tsakiyar tekuna.
Za ka iya ce yanzu, “Ni allah ne,”
a gaban waɗanda suka kashe ka?
Za ka zama mutum kurum, ba allah ba,
a hannuwan waɗanda suka kashe ka.
Za ka yi mutuwar marar kaciya
a hannuwan baƙi.
Na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ka kasance hatimin cikakke,
cike da hikima da cikakke a kyau.
Ka kasance a Eden,
a lambun Allah;
aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja,
yakutu, tofaz, da zumurrudu,
kirisolit, onis da yasfa,
saffaya,28.13 Ko kuwa lafis lazuli turkuwoyis da beril.
Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne;
a ranar da aka halicce ka an shirya su.
An shafe ka kamar kerub mai tsaro,
gama haka na naɗa ka.
Kana a tsattsarkan dutsen Allah;
ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta.
Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka
daga ranar da aka halicce ka
sai da aka sami mugunta a cikinka.
Ta wurin yawan kasuwancinka
ka cika da rikici,
ka kuma yi zunubi.
Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah,
na kore ka, ya kerub mai tsaro,
daga cikin duwatsun wuta.
Zuciyarka ta cika da alfarma
saboda kyanka,
ka kuma lalace hikimarka
saboda darajarka.
Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa;
na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.
Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta
ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka.
Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka,
ta cinye ka,
na maishe ka toka a bisa ƙasa
a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.
Dukan al’umman da suka san ka
sun giggice saboda masifar da ta auko maka;
ka zo ga mummunar ƙarshe
ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’ ”
Annabci a kan Sidon
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon; ka yi annabci a kanta ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ina gāba da ke, ya Sidon,
zan sami ɗaukaka a cikinki.
Za su san cewa ni ne Ubangiji,
sa’ad da na zartar da hukunci a kanta
na kuma nuna kaina mai tsarki a cikinta.
Zan aika da annoba a kanta
in kuma sa jini ya zuba a titunanta.
Kisassu za su fāɗi a cikinta,
da takobi yana gāba da ita a kowane gefe.
Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘Mutanen Isra’ila ba za su ƙara kasance da mugayen maƙwabta waɗanda za su zama sarƙaƙƙiya masu zafi da ƙaya mai tsini ba. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga al’ummai inda suke a warwatse, zan nuna kaina mai tsarki a cikinsu a idon al’ummai. Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu, wadda na ba wa bawana Yaƙub. Za su zauna a can lafiya su kuma gina gidaje su nome gonakin inabi; za su zauna lafiya sa’ad da zan zartar da hukunci a kan dukan maƙwabtansu da suka wulaƙanta su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”
Annabci a kan Masar
A shekara ta goma, a wata na goma, a rana ta goma sha biyu, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir’auna sarkin Masar ka kuma yi annabci gāba da shi da dukan Masar. Yi masa magana ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ina gāba da kai, Fir’auna sarkin Masar,
kai babban mugun dodon ruwa kwance cikin rafuffukanka.
Ka ce, “Nilu nawa ne;
na yi shi wa kaina.”
Amma zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka
in sa kifin rafuffukanka su manne wa kamɓorinka.
Zan jawo ka daga cikin tsakiyar rafuffukanka,
da dukan kifayen rafuffukanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,
Zan bar ka a cikin hamada,
kai da dukan kifin rafuffukanka.
Za ka fāɗi a fili
ba kuwa za a tattara ka ko a kwashe ba.
Zan ba da kai kamar abinci
ga namun jeji na duniya da tsuntsayen sararin sama.
Ta haka dukan waɗanda suke zama a Masar za su san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘Ka zama sandan iwa domin gidan Isra’ila. Sa’ad da suka kama ka da hannuwansu, ka tsattsage, ka kuma buɗu a kafaɗunsu; sa’ad da suka jingina a kanka, sai ka karye, bayansu kuwa ya firgita.29.7 Siriyak (dubi kuma Seftuwajin da Bulget); Da Ibraniyanci ka kuma sa bayansu suka tsaya
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo takobi a kanka in kashe mutane da dabbobi. Masar za tă zama kufai. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘Domin ka ce, “Nilu nawa ne; ni na yi shi,” saboda haka ina gāba da kai da rafuffukanka, zan kuma maishe ƙasar Masar ta lalace ta kuma zama kango daga Migdol zuwa Aswan, har iyakar Kush.29.10 Wato, yankin bisa Nilu Ba ƙafar mutum ko ta dabbar da za tă ratsa ta; ba wanda zai zauna a can har shekaru arba’in. Zan mai da ƙasar Masar kufai a cikin ƙasashen da aka ragargaza, biranenta kuma za su zama kango har shekaru arba’in a cikin biranen da aka lalace. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe.
“ ‘Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ƙarshen shekaru arba’in ɗin zan tattara Masarawa daga al’ummai inda aka warwatsa su. Zan komo da su daga zaman bauta in mai da su zuwa Masar ta Bisa,29.14 Da Ibraniyanci zuwa Faturos ƙasarsu ta ainihi. A can za su zama masarauta marar ƙarfi. Za tă zama masarauta mafi rarrauna cikin masarautai, ba kuwa za tă ƙara ɗaga kanta a kan sauran al’ummai ba. Zan sa tă zama marar ƙarfi ƙwarai, har da ba za tă ƙara yin mulkin a kan al’ummai ba. Masar ba za tă ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra’ila ba amma za tă zama abin tunin zunubinsu na juyawa gare ta don taimako. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
A shekara ta ashirin da bakwai, a wata na fari a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya sa sojojinsa su matsa wa Taya; kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta goge. Duk da haka shi da sojojinsa ba su sami wani lada daga matsin da suka yi a kan Taya ba. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan ba da Masar ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai washe dukiyarta. Zai kwashe ya washe ƙasar ganima a matsayin abin biyan sojojinsa. Saboda haka na ba shi Masar a matsayin lada don ƙoƙarinsa domin shi da sojojinsa sun yi wannan domina ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“A wannan rana zan sa ƙaho29.21 Ƙaho a nan yana nuna alamar ƙarfi ne. ya tsiro wa gidan Isra’ila, zan kuma buɗe bakinka a cikinsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
Makoki domin Masar
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Yi kuka kana cewa,
“Kaito saboda wannan rana!”
Gama ranar ta yi kusa,
ranar Ubangiji ta gabato,
ranar gizagizai,
lokacin hallaka wa al’ummai.
Takobi zai zo a kan Masar,
azaba za tă zo a kan Kush.
Sa’ad da kisassu za su fāɗi a Masar,
za a kwashe dukiyarta a tafi
a rushe harsashinta.
Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya30.5 Da Ibraniyanci Kub da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar.
“ ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa,
“ ‘Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi
ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare.
Daga Migdol zuwa Aswan
za su mutu ta wurin takobi a cikinta,
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Za su zama kango
a cikin ƙasashen da suke kango,
biranensu kuwa za su zama kufai
a cikin biranen da suka lalace.
Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji,
sa’ad da suka ga na sa wuta wa Masar
aka kuma ragargaza masu taimakonta.
“ ‘A wannan rana manzanni za su fito daga wurina a jiragen ruwa don su tsorata Kush daga sake jikinta. Azaba za tă kama su a ranar hallakar Masar, gama tabbatacce za tă zo.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Zan kawo ƙarshen mutanen Masar
ta hannun Nebukadnezzar sarkin Babilon.
Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai,
za a kawo don su hallaka ƙasar.
Za su zāre takuba a kan Masar
su kuma cika ƙasar da kisassu.
Zan kafe rafuffukan Nilu
in sayar da ƙasar ga mugayen mutane;
ta hannun baƙi
zan sa ƙasar ta lalace da kome da yake cikinta.
Ni Ubangiji na faɗa.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Zan hallaka gumaka
in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis.30.13 Da Ibraniyanci Nof; haka ma a aya 16.
Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba,
zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar.
Zan lalace Masar ta Bisa30.14 Da Ibraniyanci lalace Faturos
in ƙuna wuta wa Zowan
in zartar da hukunci a kan Tebes.30.14 Da Ibraniyanci No; haka ma a ayoyi 15 da 16.
Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum,30.15 Da Ibraniyanci Sin; haka ma a ayar 16.
kagarar Masar,
in kuma datse mutanen Tebes.
Zan ƙuna wuta wa Masar;
Felusiyum za tă sha azaba mai zafi.
Za a tayar wa Tebes da hankali;
Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai.
Samarin Heliyofolis30.17 Da Ibraniyanci Awen (ko On). da Bubastis30.17 Da Ibraniyanci Fi Beset
za su mutu ta wurin takobi,
biranen kansu za su tafi bauta.
Duhu ne zai zama rana a Tafanes
sa’ad da na karye ikon Masar;
a can ƙarfin da take fariya zai ƙare.
Za a rufe ta da gizagizai
ƙauyukanta kuma za su tafi bauta.
Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar,
za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
An Ƙarye Hannuwan Fir’auna
A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari a rana ta goma sha bakwai, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, na karye hannun Fir’auna sarkin Masar. Ba a daure shi don warkarwa ba ko a sa tsinke saboda kada yă zama da ƙarfi har ya riƙe takobi. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon in kuma sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai kuwa yi nishi a gabansa kamar mutumin da aka yi wa raunin mutuwa. Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobi a hannun sarkin Babilon na kuma miƙa shi a kan Masar. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
Al’ul a Lebanon
A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na uku a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, faɗa wa Fir’auna sarkin Masar da jama’arsa cewa,
“ ‘Da wa za a kwatanta girmanka?
Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon
da rassa masu kyau suna inuwartar da kurmi;
ya yi tsayi ainun
kansa ya kai cikin gizagizai.
Ruwa ya sa ya yi girma,
zurfafan maɓulɓulai sun sa ya yi tsayi;
rafuffuka suna gudu
kewaye da tushensa
yana aika da rafuffukansa
zuwa dukan itatuwan kurmi.
Saboda haka ya yi tsayi
fiye da sauran itatuwan kurmi;
rassansa suka ƙaru
suka yi tsayi,
suka bazu saboda yalwar ruwaye.
Dukan tsuntsayen sararin sama
suka yi sheƙa a rassansa,
dukan namun jeji
suka haihu a ƙarƙashin rassansa;
dukan al’ummai
suka zauna a inuwarsa.
Yana da girma a kyau,
da dogayen rassansa da ya baza,
gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa
har cikin yalwar ruwaye.
Al’ul a cikin lambun Allah
ba su kai shi ba,
balle itatuwan kasharina
su kai rassansa,
ko itatuwan durumi
su kai rassansa,
ko itace a lambun Allah
ya kai kyansa.
Na sa ya yi kyau
da yalwar rassa,
abin ƙyashi na dukan itatuwan Eden
a lambun Allah.
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, kuma domin ya yi fariya saboda tsayinsa, na miƙa shi ga mai mulkin al’ummai, don yă sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na jefar da shi a gefe, kuma baƙi mafi mugunta na al’ummai suka sare shi suka bar shi. Rassansa sun fāɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka; rassansa kuma sun kakkarye, sun fāɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan al’umman duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka bar shi. Dukan tsuntsaye sararin sama suka zauna a itacen da ya fāɗi, dukan namun jeji kuma suna cikin rassansa. Saboda haka ba wani daga cikin itatuwan da suke kusa da ruwan da zai taɓa yin fariyar tsawonsa, har kawunansu su kai cikin gizagizai. Ba wani daga cikin itatuwan da ya sha ruwa sosai da zai taɓa yi wannan tsayi; duk an bashe su ga mutuwa, zuwa can ƙasa, a cikin matattu, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da aka yi ƙasa da shi zuwa kabari31.15 Da Ibraniyanci Sheol; haka ma yake a ayoyi 16 da 17. na rufe zurfafa maɓulɓulai da makoki dominsa; na janye rafuffukansa, aka kuma hana yalwan ruwansa. Saboda shi na rufe Lebanon da baƙin ciki, dukan itatuwan kurmi suka bushe. Na sa al’ummai suka yi rawar jiki da jin ƙarar fāɗuwarsa sa’ad da na yi ƙasa da shi zuwa kabari tare da waɗanda suka gangara rami. Sai dukan itatuwan Eden, zaɓaɓɓu da kuma mafi kyau na Lebanon, dukan itatuwan da aka yi musu banruwa, sun ta’azantu a ƙarƙashin ƙasa. Waɗanda suka zauna a inuwarsa, dukan masu tarayyarsa a cikin al’ummai, su ma sun gangara zuwa kabari tare da shi, sun haɗu da waɗanda aka kashe da takobi.
“ ‘Da wa cikin itatuwan Eden za a kwatanta da kai cikin girma da daraja? Duk da haka kai ma, za a yi ƙasa da kai tare da itatuwan Eden zuwa ƙarƙashin ƙasa; za ka kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.
“ ‘Fir’auna ke nan da dukan jama’arsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Makoki domin Fir’auna
A shekara ta goma sha biyu, a wata na goma sha biyu a rana ta fari, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir’auna sarkin Masar ka faɗa masa.
“ ‘Kai kamar zaki ne a cikin al’ummai;
kai kamar dodon ruwa a cikin tekuna
kana ɓullowa cikin rafuffukanka,
kana gurɓata ruwa da ƙafafunka kana kuma dama rafuffuka.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Da taron jama’a masu yawa zan jefa abin kamun kifi a kanka,
za su kuwa jawo ka da abin kamun kifi.
Zan jefar da kai a ƙasa zan jefa ka a fili.
Zan sa dukan tsuntsayen sararin sama su zauna a kanka
dukan namun jeji na duniya kuma za su ƙosar da kansu a kanka.
Zan baza namanka a kan duwatsu
in kuma cika kwaruruka da gawarka.
Zan jiƙa ƙasar da jininka mai gudu har zuwa duwatsu,
magudanan ruwa za su cika da namanka.
Sa’ad da na shafe ka, zan rufe sammai in duhunta taurarinsu;
zan rufe rana da girgije, wata kuwa ba zai ba da haskensa ba.
Dukan haskokin sammai za su zama duhu a kanka;
zan kawo duhu a kan ƙasarka,
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Zan dami zukatan mutane masu yawa
sa’ad da na kawo maka hallaka a cikin al’ummai, a cikin32.9 Da Ibraniyanci; Seftuwajin kai ka cikin zaman bauta a cikin al’ummai, zuwa ƙasashen da ba ka taɓa sani ba.
Zan sa mutane da yawa su giggice saboda abin da ya same ka,
sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa’ad da na kaɗa takobina a gabansu.
A ranar fāɗuwarka
kowannensu zai yi rawar jiki a kowane lokaci saboda ransa.
“ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Takobin sarkin Babilon
zai auko maka.
Zan sa jama’arka su mutu ta wurin takuban ƙarfafan mutane,
masu bantsoro na dukan al’ummai.
Za su lalatar da girman kan Masar,
su kuma tumɓuke dukan jama’arta.
Zan hallaka dukan dabbobinta
da suke kusa da ruwaye masu yawa
ƙafar mutum ba zai ƙara damunsa
ko kofaton dabba ya gurɓata shi.
Sa’an nan zan sa ruwanta su kwanta
in sa rafuffukanta su gudu kamar mai,
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Sa’ad da na mai da Masar kufai
na kuma raba ƙasar da abin da take cike da shi,
sa’ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta,
a sa’an nan ne za su san cewa ni ne Ubangiji.’
“Wannan ne makokin da za a yi mata. ’Yan matan al’ummai za su rera shi; gama Masar da dukan jama’arta za su rera shi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Masar ta Gangara zuwa Cikin Lahira
A shekara ta goma sha biyu, a rana ta goma sha biyar ga wata, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, yi kuka saboda jama’ar Masar ka kuma tura ta da ’yan matan manyan al’ummai zuwa ƙarƙashin ƙasa, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami. Ka ce, ‘Kin fi sauran tagomashi ne? Ki gangara, ki kwanta cikin marasa kaciya.’ Za su fāɗi cikin waɗanda aka kashe da takobi. Takobin da an zāre; bari a ja ta a tafi tare da dukan jama’arta. Daga cikin kabari32.21 Da Ibraniyanci Sheol; haka ma a aya 27. manyan shugabanni za su yi maganar Masar da abokanta su ce, ‘Sun gangara sun kuma kwanta da marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.’
“Assuriya tana can tare da dukan sojojinta; an kewaye ta da kaburburan dukan waɗanda aka kashe, dukan waɗanda suka mutu ta wurin takobi. Kaburburansu suna cikin zurfafan rami kuma sojojinta suna kwance kewaye da kabarinta. Dukan waɗanda suka haddasa tsoro a ƙasar masu rai sun mutu, an kashe su da takobi.
“Elam tana can, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu sun mutu, an kashe su da takobi. Dukan waɗanda suka haddasa tsoro a ƙasar masu rai sun gangara wurin marasa kaciya a duniyar da take ƙarƙashi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami. An yi mata gado a cikin matattu, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi. Domin tsoronsu ya bazu cikin ƙasar masu rai, suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami; an kwantar da su tare da waɗanda aka kashe.
“Meshek da Tubal suna can, tare da dukan jama’arsu kewaye da kaburburansu. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi domin sun haddasa tsoronsu a ƙasar masu rai. Ba sun kwanta tare da sauran jarumawa marasa kaciyan da aka kashe, waɗanda suka gangara kabari tare da makaman yaƙinsu, waɗanda aka yi musu matashin kai da takubansu ba? Hukuncin zunubansu yana a bisa ƙasusuwansu, ko da yake tsoron waɗannan jarumawa ya manne cikin ƙasar masu rai.
“Kai kuma, ya Fir’auna, za a kakkarye ka za ka kuma kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.
“Edom tana can, sarakunanta da dukan yerimanta; duk da ikonsu, sun kwanta tare da waɗanda aka kashe da takobi. Suna kwance tare da marasa kaciya, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
“Dukan yerima arewa da dukan Sidoniyawa suna can; sun gangara tare da waɗanda aka kashe cikin kunya duk da tsoron da suka haddasa ta wurin ikonsu. Sun kwanta tare da marasa kaciya tare da waɗanda aka kashe da takobi suna kuma shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
“Fir’auna, shi da dukan sojojinsa, za su gan su zai kuma ta’azantu domin dukan jama’arsa da aka kashe da takobi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ko da yake na sa ta haddasa tsoro a ƙasar masu rai, Fir’auna da dukan jama’arsa za su kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Ezekiyel mai tsaro
([Ezekiyel 3.16-21])
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, yi magana da mutanen ƙasarka ka faɗa musu cewa, ‘Sa’ad da na kawo takobi a kan ƙasar, mutanen ƙasar kuwa suka zaɓi ɗaya daga cikin mutanensu suka mai da shi mai tsaro, ya kuma ga takobi yana zuwa a kan ƙasar ya kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane, in wani ya ji busar amma bai kula ba, takobin zai zo ya ɗauki ransa, jininsa kuwa zai zauna a kansa. Da yake ya ji ƙarar busar amma bai kula ba, jininsa zai zauna a kansa. Da a ce ya kula, da ya ceci kansa. Amma a ce mai tsaron ya ga takobi yana zuwa bai kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane ba sai takobi ya zo ya ɗauki ran waninsu, za a kawar da wannan mutum saboda zunubinsa, amma zan nemi hakkin jinin mutumin a kan mai tsaron.’
“Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro bisa gidan Isra’ila; saboda haka ka ji abin da zan faɗa ka kuma gargaɗe su. Sa’ad da na ce wa mugu, ‘Ya mugun mutum, tabbatacce za ka mutu,’ kai kuma ba ka yi magana don ka juyar da shi daga hanyoyinsa ba, wannan mugun mutum zai mutu33.8 Ko kuwa ciki; haka ma a aya 9 domin zunubinsa, zan kuma nemi hakkin jininsa a kanka. Amma in ka faɗakar da mugun mutumin don yă juye daga hanyoyinsa bai kuwa yi haka ba, zai mutu saboda zunubinsa, amma kai za ka kuɓutar da kanka.
([Ezekiyel 18.21-30])
“Ɗan mutum, faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da kuke cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuma lalacewa saboda33.10 Ko kuwa lalacewa a ciki su. Ta ƙaƙa za mu rayu?” ’ Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’
“Saboda haka, ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen ƙasarka, ‘Adalcin adali ba zai cece shi sa’ad da ya ƙi yin biyayya ba, kuma muguntar mugu ba za tă sa ya fāɗi sa’ad da ya juya daga gare ta ba. Adali, in ya yi zunubi, ba za a bari yă rayu saboda adalcinsa na dā ba.’ In na faɗa wa adali cewa tabbatacce zai rayu, amma sai ya dogara ga adalcinsa ya kuma aikata mugunta, babu ayyukan adalcinsa da za a tuna; zai mutu saboda muguntar da ya aikata. Kuma in na ce wa mugu, ‘Tabbatacce za ka mutu,’ amma sai ya juye daga zunubinsa ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai, in ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya sata, ya kiyaye ƙa’idodin da suke ba da rai, ya daina yin mugunta, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. Babu wani zunubin da ya aikata da za a tuna da shi. Ya yi abin da yake gaskiya da kuma daidai; tabbatacce zai rayu.
“Duk da haka mutanen ƙasarka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Alhali kuwa tasu ce ba daidai ba. In adali ya juye daga adalcinsa ya yi mugunta, zai mutu saboda haka. Kuma in mugu ya juye daga muguntarsa ya aikata abin da yake gaskiya da kuma daidai, zai rayu ta yin haka. Duk da haka, ya gidan Isra’ila kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Amma zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.”
An yi bayyanin fāɗuwar Urushalima
A shekara ta goma sha biyu ta zaman bautanmu, a wata na goma a rana ta biyar, wani mutumin da ya gudu daga Urushalima ya zo wurina ya ce, “Birnin ya fāɗi!” To a yamman da ya wuce kafin mutumin ya iso, hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma buɗe bakina kafin mutumin ya iso wurina da safe. Sai bakina ya buɗu ban kuma yi shiru ba.
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, mutanen da suke zama a waɗannan kufai a ƙasar Isra’ila suna cewa, ‘Ibrahim mutum ɗaya ne kaɗai, duk da haka Ibrahim ya mallaki ƙasar. Amma mu da muke da yawa; lalle an ba mu ƙasar ta zama mallakarmu.’ Saboda haka ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa da yake kun ci nama da jini a cikinsa kuka kuma bauta wa gumakanku kuka zub da jini, kuna gani za ku mallaki ƙasar? Kun dogara ga takobinku, kuka aikata abubuwan banƙyama, kowannenku kuma ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa. Kuna gani za ku mallaki ƙasar?’
“Ka faɗa musu wannan, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa muddin ina raye, waɗanda aka rage a kufai za su fāɗi ga takobi, waɗanda suke bayan gari kuwa namun jeji za su cinye su, waɗanda suke a mafaka da kogwannin duwatsu annoba za tă kashe su. Zan mai da ƙasar kango, kuma fariyar ƙarfinta zai ƙare, duwatsun Isra’ila za su zama kufai don kada wani ya ratsa su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na mai da ƙasar kango saboda dukan abubuwan banƙyamar da suka yi.’
“Game da kai kuma, ɗan mutum, mutanen ƙasarka suna magana da juna game da kai a katanga da kuma ƙofofin gidaje, suna ce wa juna, ‘Ku zo mu tafi mu ji maganar da ta zo daga wurin Ubangiji.’ Mutanena sukan zo wurinka, yadda suka saba su zauna a gabanka don su saurari maganarka, amma ba sa aiki da abin da suka ji. Da bakunansu suna nuna ƙauna, amma zukatansu cike da haɗama suke don ƙazamar riba. Tabbatacce, gare su ba ka fi mai waƙar ƙauna da murya mai daɗi kana kuma yin kiɗa sosai ba, gama sukan ji maganarka amma ba sa amfani da ita.
“Sa’ad da dukan wannan ya cika kuma zai cika ɗin, sa’an nan za su sani akwai annabi a tsakiyarsu.”
Makiyaya da tumaki
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra’ila; ka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton makiyayan Isra’ila waɗanda suke kula da kansu ne kawai! Ashe, bai kamata makiyaya ne su lura da tumaki ba? Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba. Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ko ku warkar da marasa lafiya ko ku ɗaura waɗanda suka ji rauni. Ba ku dawo da waɗanda suka yi makuwa ko ku nemi waɗanda suka ɓace ba. Amma sai kuka mallake su ƙarfi da yaji. Saboda haka suka warwatse domin babu makiyayi, kuma da suka warwatsu sai suka zama abincin namun jeji. Tumakina suna ta yawo a kan dukan duwatsu da kuma kowane tudu. Sun watsu a dukan duniya, kuma ba wanda ya neme su.
“ ‘Saboda haka, ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji, Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin tumaki sun rasa makiyayi ta haka aka washe su suka kuma zama abincin dukan namun jeji, kuma domin makiyayana ba su nemi tumakina ba amma suka kula da kansu a maimakon tumakina, saboda haka, ya ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji, Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da makiyaya kuma zan nemi hakkin tumakina daga gare su. Zan hana su yin kiwon tumakin don kada makiyayan su ƙara yin kiwon kansu. Zan ƙwace tumakina daga bakunansu, ba kuwa za su ƙara zama abincinsu.
“ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan nemi tumakina. Kamar yadda makiyayi yakan lura da tumakinsa da suka watse sa’ad da yake tare da su, haka zan lura da tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu. Zan dawo da su daga al’ummai in kuma tattara su daga ƙasashe, zan kuma kawo su cikin ƙasarsu. Zan yi kiwonsu a kan duwatsun Isra’ila, a maɓulɓulai da kuma cikin wuraren zamansu a ƙasar. Zan kula da su a wurin kiwo mai kyau, kuma ƙwanƙolin duwatsun Isra’ila ne zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a wurin kiwo mai kyau, a can kuma za su yi kiwo a wurin kiwo mai kyau a kan duwatsun Isra’ila. Ni kaina zan lura da tumakina in kuma sa su kwanta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan nemi ɓatattuna in kuma dawo da waɗanda suka yi makuwa. Zan ɗaura raunin waɗanda suka ji ciwo in kuma ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafa da kuma masu ƙiba. Zan yi kiwo tumaki da adalci.
“ ‘Game da ku, tumakina, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin raguna da awaki. Bai isa ba a ce kun yi kiwo a wuri mai kyau? Sai kun tattake sauran wurin kiwonku da ƙafafunku tukuna? Bai isa ba a ce kun sha ruwa mai tsabta? Sai kun kuma gurɓata sauran da ƙafafunku? Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku?
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce musu, duba, ni kaina zan hukunta tsakanin turkakkun tumaki da ramammun tumaki. Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku sai da suka gudu, zan cece tumakina ba za su ƙara zama ganima ba. Zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya. Zan sa musu makiyaya guda, bawana Dawuda, zai kuwa lura da su; zai kula da su ya kuma zama makiyayinsu. Ni Ubangiji zan zama Allahnsu, bawana kuma Dawuda zai zama yerima a cikinsu. Ni Ubangiji na faɗa.
“ ‘Zan yi alkawarin salama da su in kuma kawar wa ƙasar da namun jeji domin su zauna a hamada su kuma kwana a kurmi lafiya lau. Zan albarkace su in kuma sa tuduna kewaye da su.34.26 Ko kuwa zan mai da su da kuma wurare kewaye da tuduna su zama sanadin samun albarka Zan zubo yayyafi a lokacinsa; za a kasance da yayyafin albarka. Itatuwan gona za su ba da ’ya’yansu, ƙasa kuma za tă ba da amfaninta; mutane za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su. Ba za su ƙara zama ganimar al’ummai ba, ba kuwa namun jeji za su cinye su ba. Za su zauna lafiya, kuma babu wani da zai sa su ji tsoro. Zan tanada musu ƙasar da aka sani don hatsinta, ba za su kuma ƙara zama abin da yunwa za tă fara musu a ƙasa ba ko su sha zargin sauran al’ummai. Sa’an nan za su san cewa ni, Ubangiji Allahnsu, ina tare da su kuma cewa su, gidan Isra’ila, mutanena ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tumakina, tumakin wurin kiwona, mutanena ne, ni kuwa Allahnku ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Annabci a kan Edom
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir; ka yi annabci a kansa ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, Dutsen Seyir, zan kuma miƙa hannuna gāba da kai in mai da kai kango. Zan mai da garuruwanka kufai za ka kuma zama kango. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘Domin ka riƙe ƙiyayya ta tun dā, ka kuma ba da mutanen Isra’ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, lokacin da adadin horonsu ya cika, saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sa a zub da jininka zan kuwa fafare ka. Da yake ba ka ƙi zub da jini ba, zub da jini zai fafare ka. Zan mai da Dutsen Seyir kango in kuma yanke dukan waɗanda suke shiga da fita a cikinka. Zan cika duwatsunka da matattu; waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi a kan tuddanka, da cikin kwarurukanka, da cikin dukan kwazazzabanka. Zan mai da kai kango har abada; ba za a zauna a cikin garuruwanka ba. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘Domin kun ce, “Waɗannan al’ummai biyu da ƙasashe za su zama namu za mu kuma mallake su,” ko da yake Ni Ubangiji ina a can, saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sāka maka gwargwadon fushi da kuma kishin da ka nuna a ƙiyayyarsu da ka yi zan kuma sanar da kaina a cikinsu sa’ad da na hukunta ka. Sa’an nan za ka san cewa Ni Ubangiji na ji duk abubuwan banzan da ka faɗa a kan duwatsun Isra’ila. Ka ce, “An mai da su kango an kuma ba mu su mu cinye.” Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa yayinda dukan duniya take farin ciki, zan mai da kai kango. Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Annabci wa duwatsun Isra’ila
“Ɗan mutum, ka yi annabci wa duwatsun Isra’ila ka ce, ‘Ya duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa abokin gāba yana magana game da ku cewa, “Yauwa! Tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu.” ’ Saboda haka ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin sun lalace ku suka kuma maishe ku kufai marar amfani a kowane gefe saboda ku zama mallakar sauran al’ummai da kuma abin magana da tsegumi ga mutane, saboda haka, ya duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana faɗa wa duwatsu da tuddai, wa kwazazzabai da kwaruruka, wa kufai da garuruwan da suka zama kango waɗanda aka washe aka wulaƙanta suka zama ganimar sauran al’ummai da suke kewaye da ku, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa cikin kishina mai ƙuna na yi magana gāba da sauran al’ummai, da kuma gāba da Edom, gama da farin ciki da reni a zukatansu suka mai da ƙasata mallakarsu don su washe wuraren kiwonta.’ Saboda haka ka yi annabci game da ƙasar Isra’ila ka kuma ce wa duwatsu da tuddai, wa kwazazzabai da kwaruruka, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al’ummai. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa na ɗaga hannuna sama na rantse cewa al’ummai da suke kewaye da ku za su sha ba’a.
“ ‘Amma ku, ya duwatsun Isra’ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanena Isra’ila, gama ba da daɗewa ba za su komo gida. Na damu da ku kuma zan dube ku da tausayi; za ku nome ku kuma shuka, zan kuma riɓaɓɓanya mutane a kanku, dukan gidan Isra’ila ke nan. Za a zauna a birane a kuma sāke gina rusassun wurare. Zan sa mutane da dabbobi su yi yawa a kanku, za su kuma ba da ’ya’ya su kuma yi yawa. Zan zaunar da mutane a kanku kamar dā zan kuma sa ku wadaita fiye da dā. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. Zan sa mutanena Isra’ila su yi tafiya a kanku. Za su mallake ku, za ku kuma zama gādonsu; ba za ku ƙara sa su rasa ’ya’yansu ba.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin mutane suna magana game da ku cewa, “Kun cinye mutane kuka kuma sa al’ummarku ta rasa ’ya’yanta,” saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ko ku sa al’ummarku ta rasa ’ya’ya ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba zan ƙara bari ku ji maganar banza ta al’ummai ba, ba kuwa za ku ƙara shan ba’ar mutane ko in sa al’ummarku ta fāɗi ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
An tabbatar da maidowar Isra’ila
Maganar Ubangiji ta sāke zuwa mini cewa, “Ɗan mutum, sa’ad da mutanen Isra’ila suke zama a ƙasarsu, sun ƙazantar da ita ta wurin halinsu da kuma ayyukansu. Halinsu ya yi kamar rashin tsarkin mace a lokacin al’adarta a gabana. Saboda haka na husata da su domin sun yi kisankai a ƙasar kuma domin sun ƙazantar da ita da gumakansu. Na warwatsa su cikin al’ummai, suka kuwa warwatsu cikin dukan ƙasashe; na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu. Kuma ko’ina da suka tafi a cikin al’ummai sun ɓata sunana mai tsarki, gama an yi magana a kansu cewa, ‘Waɗannan mutanen Ubangiji ne, duk da haka dole su bar ƙasarsa.’ Na damu saboda sunana mai tsarki, wanda gidan Isra’ila ya ɓata a cikin al’ummai inda suka tafi.
“Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba dominku ba ne, ya gidan Isra’ila da nake yin waɗannan abubuwa, amma saboda sunana ne mai tsarki, wanda kuka ɓata a cikin al’ummai inda kuka tafi. Zan nuna tsarkin girman sunana, wanda aka ɓata a cikin al’umma, sunana da kuka ɓata a cikinsu. Sa’an nan al’ummai za su san cewa ni ne Ubangiji, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinku a idanunsu.
“ ‘Gama zan fitar da ku daga al’ummai; zan tattara ku daga dukan ƙasashe in komo da ku zuwa ƙasarku. Zan yayyafa muku ruwa mai tsabta, zan kuwa tsarkake ku daga dukan ƙazantarku daga kuma dukan gumakanku. Zan ba ku sabuwa zuciya in kuma sa sabon ruhu a cikinku; zan fid da zuciyar dutse in kuma ba ku zuciyar nama. Zan kuma sa Ruhuna a cikinku in kuma motsa ku ku bi ƙa’idodina ku kuma kiyaye dokokina. Za ku zauna a ƙasar da na ba wa kakanninku; za ku zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku. Zan cece ku daga dukan rashin tsabtarku. Zan sa hatsi ya yi yalwa ba zan kawo yunwa a kanku ba. Zan ƙara ’ya’yan itatuwa da amfanin gona, saboda kada ku ƙara shan kunya a cikin al’ummai saboda yunwa. Sa’an nan za ku tuna mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda zunubanku da kuma ayyukanku na banƙyama. Ina so ku san cewa ba na yi wannan saboda ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku ji kunya ku kuma giggita saboda halinku, ya gidan Isra’ila!
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na tsarkake ku daga dukan zunubanku, zan sāke zaunar da ku a garuruwanku, a kuma sāke gina kufai. Ƙasar da take kango a dā za ku nome ta a maimakon zama kango a idon dukan masu ratsawa a cikinta. Za su ce, “Wannan ƙasar da take kango a dā ta zama kamar lambu Eden; biranen da dā suke kufai, kango da kuma aka lalata, yanzu suna da katanga ana kuma zama a ciki.” Sa’an nan al’ummai kewaye da ku da suka rage za su san cewa Ni Ubangiji na sāke gina abin da aka lalace na kuma sāke shuka abin da yake kango. Ni Ubangiji na faɗa, kuma zan aikata.’
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa har yanzu zan ji roƙon gidan Isra’ila in kuma yi musu wannan. Zan sa mutanensu su yi yawa kamar tumaki, yawansu ya yi kamar garken tumaki don hadaya a Urushalima a ƙayyadaddun lokuta bukukkuwarta. Haka biranen da suke kufai za su cika da ɗumbun mutane. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
Kwarin busassun ƙasusuwa
Hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma fitar da ni ta wurin Ruhun Ubangiji ya sa ni a tsakiyar kwarin; yana cike da ƙasusuwa. Ya sa na kai na komo a ciki, na kuma ga ƙasusuwa masu girma da yawa a ƙasar kwarin, ƙasusuwan da suka bushe ƙwarai. Sai ya tambaye ni cewa, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa za su iya rayu?”
Ni kuwa na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai kaɗai ka sani.”
Sai ya ce mini, “Ka yi wa waɗannan ƙasusuwa annabci ka ce musu, ‘Busassun ƙasusuwa, ku ji maganar Ubangiji! Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa waɗannan ƙasusuwa. Zan sa numfashi37.5 Ibraniyanci na wannan kalma zai iya zama iska ko ruhu (dubi ayoyi 6-14). ya shiga muku, za ku kuwa rayu. Zan harhaɗa muku jijiyoyi in sa muku tsoka in kuma rufe ku da fata; zan sa numfashi a cikinku, za ku kuwa rayu. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Saboda haka sai na yi annabci yadda aka umarce ni. Da nake annabcin, sai aka ji motsi, ƙarar girgiza, sai ƙasusuwan suka harhaɗu, ƙashi ya haɗu da ƙashi. Na duba, sai ga jijiyoyi da nama suka bayyana a kansu fata kuma ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.
Sa’an nan ya ce mini, “Ka yi annabci wa numfashi; ka yi annabci, ɗan mutum, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka fito daga kusurwoyi huɗu, ya numfashi, ka kuma numfasa cikin waɗannan matattu, don su rayu.’ ” Saboda haka na yi annabci yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga musu; suka rayu suka kuma miƙe tsaye a ƙafafunsu babbar runduna ce ƙwarai.
Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa su ne dukan gidan Isra’ila. Suna cewa, ‘Ƙasusuwanmu sun bushe, sa zuciyarmu duk ya tafi; an share mu ƙaf.’ Saboda haka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ya mutanena, zan buɗe kaburburanku in fitar da ku daga cikinsu; zan mai da ku ƙasar Isra’ila. Sa’an nan ku, mutanena, za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na buɗe kaburburanku na fitar da ku daga cikinsu. Zan sa Ruhuna a cikinku za ku kuwa rayu, zan kuma zaunar da ku a ƙasarku. Sa’an nan za ku san cewa Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata, in ji Ubangiji.’ ”
Al’umma ɗaya a ƙarƙashin sarki guda
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda ka rubuta a kansa, ‘Na Yahuda da Isra’ilawan da suke tare da shi.’ Sa’an nan ka ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Sandan Efraim, na Yusuf da dukan gidan Isra’ilan da suke tare da shi.’ Ka haɗa su su zama sanda guda saboda su kasance ɗaya a hannunka.
“In mutanen ƙasarka suka tambaye ka cewa, ‘Ba za ka faɗa mana abin da kake nufi da wannan ba?’ Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Zan ɗauki sandan Yusuf, wanda yake a hannun Efraim, da na kabilan Isra’ilawan da suke tare da shi, in haɗa shi da sandan Yahuda, in mai da su sanda guda, za su kuwa zama ɗaya a hannuna.’ Ka riƙe sandunan da ka yi rubutun a gabansu ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan fitar da Isra’ilawa daga al’ummai inda suka tafi. Zan tattara su daga dukan kewaye in komo da su ƙasarsu. Zan mai da su al’umma ɗaya a cikin ƙasar, a kan duwatsun Isra’ila. Za a kasance da sarki guda a kan dukansu ba za su ƙara zama al’ummai biyu ko su rabu su zama masarautai biyu ba. Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da mugayen siffofi ko kuma da wani daga laifofinsu ba, gama zan cece su daga dukan zunubinsu na ridda, zan kuma tsarkake su. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu.
“ ‘Bawana Dawuda zai zama sarki a kansu, dukansu kuwa za su kasance da makiyayi guda. Za su bi dokokina su kuma kiyaye ƙa’idodina. Za su zauna a ƙasar da na ba wa bawana Yaƙub, ƙasar da kakanninsu suka zauna. Su da ’ya’yansu da ’ya’ya ’ya’yansu za su zauna a can har abada, kuma Dawuda bawana zai zama sarkinsu har abada. Zan yi alkawarin salama da su; zai zama madawwamin alkawari. Zan kafa su in ƙara yawansu, zan kuma sa wuri mai tsarkina a cikinsu har abada. Mazaunina zai kasance da su; zan kuwa zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena. Sa’an nan al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji na mai da Isra’ila mai tsarki, sa’ad da wuri mai tsarkina yana a cikinsu har abada.’ ”
Annabci a kan Gog
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, ka fuskanci Gog, na ƙasar Magog, babban sarkin38.2 Ko kuwa sarkin Rosh, Meshek da Tubal; ka yi annabci a kansa ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin38.3 Ko kuwa sarkin Rosh, Meshek da Tubal. Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in fitar da kai tare da dukan sojojinka, dawakanka, mahayan dawakanka saye da makamai, da kuma jama’a mai girma masu riƙe da garkuwoyi manya da ƙanana, dukansu da takuba a zāre. Farisa, Kush38.5 Wato, yankin Nilu na Bisa da Fut za su kasance tare da su, duka riƙe da garkuwoyi da hulunan kwano, haka ma Gomer da dukan sojojinsa, da Bet Togarma daga can arewa tare da dukan sojojinsa, al’ummai masu yawa tare da kai.
“ ‘Ka shirya; ka kintsa, kai da dukan jama’arka da suka taru kewaye da kai, ka kuma zama mai ba su umarni. Bayan kwanaki masu yawa za a kira ka. A shekaru masu zuwa za ka kai hari a ƙasar da ta farfaɗo daga yaƙi, wadda aka tattara mutanenta daga al’ummai masu yawa zuwa duwatsun Isra’ila, dā kango ne sosai. An fitar da su daga al’ummai, yanzu kuwa dukansu suna zama lafiya. Kai da dukan sojojinka da kuma al’ummai masu yawa da suke tare da kai za ku haura, kuna cin gaba kamar hadari; za ku zama kamar girgijen da yake rufewa ƙasa.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, tunani zai shiga cikin zuciyarka za ka kuma ƙirƙiro muguwar dabara. Za ka ce, “Zan kai hari wa ƙasar da ƙauyukanta ba su da katanga; zan fāɗa wa mutanen da suke zamansu kurum cikin salama, dukansu suna zama babu katanga babu ƙofofi ko ƙyamare. Zan washe in kwashe ganima in kuma juye hannuna gāba da kufai da aka sāke zaunar da mutanen da aka tattara daga al’ummai, masu yawan shanu da kayayyaki, masu zama a tsakiyar ƙasa.” Sheba da Dedan da ’yan kasuwar Tarshish da dukan ƙauyukanta38.13 Ko kuwa zakokinta masu ƙarfi za su ce maka, “Ka zo ka kwashe ganima ne? Ka tattara jama’arka don ka yi waso, ka kuma kwashe azurfa da zinariya, ka kwashe shanu da kayayyaki ka kuma ƙwace ganima mai yawa?” ’
“Saboda haka ɗan mutum, ka yi annabci ka ce wa Gog, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, sa’ad da mutanena Isra’ila suna zaman lafiya, ba za ka sani ba? Za ka zo daga wurinka a can arewa, kai da al’ummai masu yawa tare da kai, dukansu suna hawan dawakai, jama’a mai yawa, babbar runduna. Za ka ci gaba a kan mutanena Isra’ila kamar yadda girgijen yakan rufe ƙasa. A kwanaki masu zuwa, ya Gog, zan kawo ka, ka yi yaƙi da ƙasata, domin al’ummai su san ni sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinka a gabansu.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba kai ba ne na yi magana da kai a kwanakin dā ta wurin bayina annabawan Isra’ila? A lokacin sun yi annabci shekaru masu yawa cewa zan kawo ka, ka yaƙe su. Ga abin da zai faru a ranar. Sa’ad da Gog ya fāɗa wa ƙasar Isra’ila, fushina mai zafi zai ƙuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Cikin kishina da hasalata mai zafi zan furta cewa a wannan lokaci za a yi babbar girgizar ƙasa a ƙasar Isra’ila. Kifin teku, tsuntsayen sarari, namun jeji, kowace halitta mai rarrafe da kuma dukan mutane a duniya za su yi rawar jiki a gabana. Za a tumɓuke duwatsu, a ragargaza tsaunuka, kuma kowane bango zai fāɗi ƙasa. Zan kira takobi a kan Gog a dukan duwatsuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Kowane takobin mutum zai yi gāba da ɗan’uwansa. Zan yi hukunci a kansa da annoba da kuma zub da jini; zan yi ruwa mai yawa da ƙanƙara da kibiritu mai cin wuta a kansa da a kan sojojinsa da kuma a kan al’ummai masu yawa da suke tare da shi. Ta haka zan nuna girmana da kuma tsarkina, zan sanar da kaina a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’
“Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin39.1 Ko kuwa Gog, sarkin Rosh, Meshek da Tubal. Zan juya ka in kuma ja ka. Zan kawo ka daga can arewa in aike ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra’ila. Sa’an nan zan karya bakan da take a hannun hagunka, in sa kibiyoyin da suke a hannun damanka su fāɗi. A kan duwatsun Isra’ila za ka fāɗi, kai da sojojinka da kuma al’ummai da suke tare da kai. Zan bayar da kai ka zama abinci ga tsuntsaye da namun jeji masu cin nama. Za ka mutu a fili, gama haka ni na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan aika da wuta a kan Magog da kuma a kan waɗanda suke zama lafiya a bakin teku, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.
“ ‘Zan sanar da sunana mai tsarki a cikin mutanena Isra’ila. Ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, kuma al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji Mai Tsarki ne a cikin Isra’ila. Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ranar da na yi magana ke nan.
“ ‘Sa’an nan waɗanda suke zama a garuruwan Isra’ila za su fita su tattara makamai su hura wuta da su su kuma ƙone su, manya da ƙanana garkuwoyi, bakkuna da kibiyoyi, kulake da māsu. Shekara bakwai za su yi amfani da su don hura wuta. Ba za su yi wahalar zuwa jeji don neman itacen hura wuta ba, domin za su yi amfani da makamai don hura wuta. Za su kuma washe waɗanda suka washe su ganima, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘A ranar zan yi wa Gog makabarta a cikin Isra’ila, a kwarin waɗanda suke tafiya wajen gabashin Teku. Za tă tare hanyar matafiya, domin za a binne Gog da dukan mutanensa a can. Ta haka za a kira wurin Kwarin Haman Gog.39.11 Haman Gog yana nufin mutanen Gog.
“ ‘Watanni bakwai gidan Isra’ila zai yi ta binne su don a tsarkake ƙasar. Dukan mutanen ƙasar za su binne su, kuma ranar da za a ɗaukaka ni za tă zama ranar tuni a gare su, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘Za a ɗauki mutane kullum don tsabtacce ƙasar. Waɗansu za su ratsa ƙasar, ƙari da waɗannan, waɗansu za su binne gawawwakin da suka ragu a ƙasar. A ƙarshen watanni bakwai ɗin za su fara bincikensu. Yayinda suke ratsa ƙasar, in waninsu ya ga ƙashin mutum, zai kafa shi kamar alama a gefe sai masu haƙa kabari sun binne shi a Kwarin Haman Gog. Akwai wani garin da ake kira Hamona39.16 Hamona yana nufin jama’a. zai kasance a can. Ta haka za su tsabtacce ƙasar.’
“Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan namun jeji, ‘Ku taru ku kuma zo wuri ɗaya daga ko’ina don hadayar da nake shirya muku, babbar hadaya a kan duwatsun Isra’ila. A can za ku ci nama ku kuma sha jini. Za ku ci naman manyan mutane ku kuma sha jinin sarakunan duniya sai ka ce an yanka raguna da ’yan tumaki, awaki da bijimai, dukansu turkakkun dabbobi daga Bashan. A hadayar da nake shirya muku, za ku ci kitse sai kun ƙoshi ku kuma sha jini sai kun bugu. A teburina za ku ci iya ƙoshiyarku da naman jama’a da kuma mahaya, manyan mutane da sojoji na kowane iri,’ in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“Zan nuna ɗaukakata a cikin al’ummai, kuma dukan al’ummai za su ga hukuncin da zan yi da kuma hannu mai nauyin da zan ɗora a kansu. Daga wannan rana zuwa gaba gidan Isra’ila zai san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu. Al’ummai kuma za su san cewa mutanen Isra’ila sun tafi zaman bauta saboda zunubinsu, domin sun yi rashin aminci gare ni. Saboda haka na kawar da fuskata daga gare su na miƙa su ga abokan gābansu, suka kuwa mutu ta takobi. Na yi da su gwargwadon rashin tsabtarsu da laifofinsu, na kuma kawar da fuskata daga gare su.
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan komo da Yaƙub daga zaman bauta39.25 Ko kuwa yanzu mai da nasarar Yaƙub zan kuma yi wa dukan Isra’ila jinƙai, zan kuma yi kishi saboda sunana mai tsarki. Za su manta da kunyar da suka sha da dukan rashin amincin da suka nuna mini sa’ad da suke zama lafiya a ƙasarsu inda ba wanda zai tsorata su. Sa’ad da na komo da su daga al’ummai na kuma tattara su daga ƙasashen abokan gābansu, zan nuna kaina mai tsarki ta wurinsu a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, gama ko da yake na tura su zaman bauta a cikin al’ummai, zan tattara su zuwa ƙasarsu, ba tare da barin wani a baya ba. Ba zan ƙara kawar da fuskata daga gare su, gama zan zuba Ruhuna a kan gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Wurin sabon haikali
A shekara ta ashirin da biyar ta zaman bauta, a farkon shekara, a rana ta goma ga wata, a shekara ta goma sha huɗu bayan fāɗuwar birnin Urushalima, a wannan rana ikon Ubangiji ya sauko a kaina ya kuma iza ni. Cikin wahayin, Allah ya kai ni ƙasar Isra’ila ya sa ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda a gefen kudunsa akwai gine-ginen da suka yi kamar birni. A cikin wahayin ya kai ni can, na kuma ga mutum wanda kamanninsa ya yi kamar tagulla; yana tsaye a hanyar shiga yana riƙe da igiyar lilin da kuma karan awo a hannunsa. Mutumin ya ce mini, “Ɗan mutum, duba da idanunka, ka ji da kunnuwanka ka kuma lura da kowane abin da zan nuna maka, gama abin da ya sa na kawo ka nan ke nan. Ka faɗa wa gidan Isra’ila duk abin da ka gani.”
Ƙofar shiga ta gabas zuwa filin waje
Na ga katanga da ya kewaye filin haikali gaba ɗaya. Tsawon karan awon da yake a hannun mutumin kamu shida ne, sai ya auna kaurin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida.
Sa’an nan ya tafi ƙofar da take fuskantar gabas. Ya hau matakanta ya auna madogarar ƙofa; zurfinta kamu shida ne. Tsawon kowane ɗakin matsara kamu shida ne, fāɗinsa kuma kamu shida, kaurin bangayen da suka raba ɗaki da ɗaki kamu biyar ne. Zurfin madogarar ƙofar da yake dab da shirayin da yake fuskantar haikalin kamu shida ne.
Sa’an nan ya auna shirayin hanyar shiga; zurfinsa kamu takwas ne, kaurin kowane madogarar ƙofarsa kuwa kamu biyu ne. Shirayi hanyar shiga yana fuskantar haikalin.
A cikin ƙofar gabas akwai ɗakuna uku a kowane gefe na hanyar shiga; dukan ukun girmansu ɗaya, bangayen da suke tsakani a kowane gefe girmansu ɗaya ne. Sa’an nan ya auna bakin hanyar shiga ya sami fāɗinsa kamu goma, tsawonsa kuma kamu goma sha uku. A gaban kowane ɗakin akwai bango mai tsayi kamu ɗaya, ɗakunan kuma kamu shida-shida ne a kowane gefe. Sa’an nan ya auna hanyar shiga daga saman bangon ɗaki a baya zuwa saman ɗakin da yake ɗaura da shi; nisansu kamu ashirin da biyar ne daga bango zuwa bango. Ya auna ɗakin bakin ƙofa na can ƙarshen hanyar shiga ya sami kamu sittin. Awon ya kai har zuwa shirayin40.14 Seftuwajin; Ibraniyanci bangon da yake fuskantar filin.40.14 Ma’anar Ibraniyanci na wannan aya dai babu tabbas. Nisan da take daga mashigin hanyar shiga zuwa can ƙarshen shirayin, kamu hamsin ne. Akwai ƙananan tagogi a ɗakunan da kuma a bangayen hanyar shiga, yadda suke a shirayin; tagogi a kewaye duka suna fuskantar ciki. An yi wa bangayen da suke waje ƙofar shiga ado da zāne-zāne siffofin itatuwan dabino.
Filin waje
Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar shiga zuwa filin waje, inda na ga ɗakuna talatin da aka gina kewaye a filin waje na filin. An gina waɗannan ɗakunan gefe a jikin bangon waje, a gabansu kuwa akwai daɓe kewaye da filin. Daɓen ya bi ta daidai gefen hanyoyin shiga, kuma faɗinsa ya yi daidai da tsawon ƙofofin shiga; wannan shi ne daɓen da yake ƙasa-ƙasa.
Sa’an nan ya auna nisan da take daga hanyar shiga da take ƙasa-ƙasa daga ciki zuwa waje na filin ciki; ya kai kamu ɗari a gefen gabas haka ma yake a gefen arewa.
Ƙofar arewa
Sa’an nan mutumin ya auna tsawo da fāɗin ƙofar da take fuskantar arewa, wadda take bi zuwa filin waje. Ƙofar shigar ma tana da ɗakuna uku-uku a kowane gefe. Girman bangayen da suka miƙe, da kuma shirayinta daidai suke da na ƙofa ta fari. Tsawonta kamu hamsin, fāɗinta kuwa kamu ashirin da biyar. Tagoginta, shirayinta da siffofin itatuwan dabinon da aka yi zāne-zānen adonta duk girmansu ɗaya ne da na ƙofar da take fuskantar gabas. Ɗakin shiga shi ma ya fuskanci filin yana kuma da matakai bakwai waɗanda suka bi zuwa ƙofar shiga, da shirayinta ɗaura da su. Akwai ƙofa zuwa filin ciki wadda take fuskantar ƙofar arewa, kamar dai yadda take a gabas. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofar da take ɗaura ta ita; ya sami kamu ɗari.
Ƙofar kudu
Sa’an nan ya kai ni gefen kudu, na kuma ga ƙofa tana fuskantar kudu. Ya auna madogaranta da shirayinta, dukansu girmansu ɗaya ne kamar sauran ƙofofi biyun. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye, kamar tagogin sauran. Tsawonta kamu hamsin ne fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne. Matakai bakwai sun haura zuwa ƙofar, da shirayi ɗaura da matakan; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a bangayen a kowane gefe. Filin cikin ma yana da ƙofar da ta fuskanci kudu, sai ya auna daga wannan ƙofa zuwa ƙofar waje a gefen kudu; ya sami kamu ɗari.
Ƙofofin zuwa filin ciki
Sai ya kawo ni cikin filin ciki ta ƙofar kudu, ya kuma auna ƙofar kudu; ita ma tana da girma ɗaya da sauran ƙofofin shiga. Ɗakunanta na matsara, bangayenta duk suna da girma ɗaya da sauran. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye. Tsawonta kamu hamsin ne, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar ne. (Fāɗin shirayun hanyoyin shiga kewaye da filin ciki kamu ashirin da biyar ne, fāɗinsu kuma kamu biyar.) Shirayin ƙofar yana fuskantar filin waje; an yi zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogarar bangayen hanyar shiga. Yana kuma da matakai takwas.
Sai ya kai ni filin da yake ciki a gefen gabas, ya kuma auna hanyar shiga; girmanta iri ɗaya ne kamar sauran. Ɗakunanta, bangayenta da shirayinta duk girmansu iri ɗaya ne kamar sauran. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye. Tsawon hanyar shiga kamu hamsin ne, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar. Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogararta. Tana kuma da matakai takwas.
Sa’an nan ya kawo ni ƙofar arewa ya kuma auna ta. Girmanta ɗaya ne da sauran, Haka ma ɗakunanta, bangayenta da shirayinta, ƙofar tana da tagogi duk a kewaye. Tsawonta kamu hamsin, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar. Shirayin ƙofar40.37 Seftuwajin (dubi kuma ayoyi 31 da 34); Ibraniyanci madogarar ta fuskanci filin waje; tana da zāne-zānen adon itatuwan dabino a madogaranta, matakai takwas kuwa sun haura zuwa wajenta.
Ɗakuna don shirya hadayu
Ɗakin da hanya ta ratsa ciki yana kusa da shirayin a kowane hanyoyin shiga na ciki, inda a kan wanke hadayun ƙonawa. A shirayin hanyar shiga akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yankan hadayun ƙonawa, hadayun zunubi da kuma hadayun laifi. Ta bangon waje na shirayin hanyar shiga, kusa da matakai a mashigin zuwa hanyar shiga da take arewa akwai tebur biyu, akwai kuma tebur biyu a gefe ɗaya na matakan. Duka dai akwai tebur huɗu a gefe ɗaya na hanyar shiga, huɗu kuma a ɗaya gefen, tebur takwas ke nan gaba ɗaya, inda a kan yanka hadayu a kai. Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu don hadayun ƙonawa, tsawon kowanne kuwa kamu ɗaya da rabi ne, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya. A kansu ne a kan ajiye kayan yanka hadayun ƙonawa da kuma sauran hadayu. Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye a bangon, tsawon kowanne ya yi fāɗin tafin hannu. An yi amfani da teburin don a riƙa ajiye naman hadayu.
Ɗakuna domin firistoci
Waje da ƙofar ciki, a cikin filin ciki, akwai ɗakuna biyu, ɗaya40.44 Seftuwajin; Ibraniyanci ɗakuna don mawaƙa, waɗanda suke a gefen ƙofar arewa yana kuma fuskantar kudu, wani kuma a gefen ƙofar kudu40.44 Seftuwajin; Ibraniyanci gabas yana fuskantar arewa. Sai mutumin ya ce mini, “Ɗakin da yake fuskantar kudu ne na firistocin da suke lura da haikali, ɗaya ɗakin kuma da yake fuskantar arewa ne na firistocin da suke lura da bagade. Waɗannan su ne ’ya’yan Zadok maza, waɗanda su ne kaɗai Lawiyawan da za su iya yin kusa da Ubangiji don su yi hidima a gabansa.”
Sa’an nan ya auna filin, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu ɗari. Bagaden kuwa yana a gaba a cikin haikalin.
Haikalin
Sai ya kawo ni shirayin haikalin ya kuma auna madogaran shirayin; fāɗinsu a kowane gefe kamu biyar-biyar ne. Fāɗin mashigin kamu goma sha huɗu ne, bangayenta40.48 Seftuwajin; Ibraniyanci bakin ƙofar take kuma kamu uku-uku ne a kowane gefe. Fāɗin shirayin kamu ashirin ne, kamu goma sha biyu40.49 Seftuwajin; Ibraniyanci goma sha ɗaya kuma daga gaba zuwa baya. A kan kai samansa ta wurin hawan matakai,40.49 Ibraniyanci; Seftuwajin Matakai goma suka haura zuwa wurinsa akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe na madogaran.
Sai mutumin ya kawo ni wuri mai tsarki da yake waje ya kuma auna madogaransa; fāɗin gefe-gefen kamu shida ne a kowane gefe. Faɗin ƙofar shiga kamu goma ne, fāɗin bangaye a kowane madogararta kamu biyar-biyar ne. Ya kuma auna wuri mai tsarkin da yake waje; tsawonsa kamu arba’in fāɗinsa kuma kamu ashirin.
Sa’an nan ya shiga wuri mai tsarki da yake can ciki ya auna madogarar ƙofar shigar; fāɗin kowanne kamu biyu ne. Faɗin ƙofar shigan kamu shida ne, fāɗin bangayen a kowane gefenta kamu bakwai-bakwai ne. Ya kuma auna tsawon wuri mai tsarki da yake can ciki; tsawon kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin daga ƙurewa wuri mai tsarki da yake waje. Ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.”
Sa’an nan ya auna bangon haikalin; kaurinsa kamu shida ne, kuma kowane ɗakin da yake a gefe kewaye da haikalin fāɗinsa kamu huɗu ne. Ɗakunan da suke gefe masu hawa uku ne, wani bisa wani, guda talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da bangayen haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon haikalin. Faɗin ɗakunan da suke gefe kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. Ginin da aka yi kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, don haka ɗakunan suka yi ta ƙara fāɗi yayinda suka ƙara bisa. Akwai mataki daga ɗaki na ƙasa zuwa ɗaki na bisa ta hanya hawa ɗaki na tsakiya.
Na ga cewa haikalin yana da ɗagaggen tushe kewaye da shi, wanda ya zama harsashin ɗakunan da suke gefe. Tsawonsa kara guda ne mai tsawon kamu shida. Kaurin bangon waje na ɗakunan da suke gefe kamu biyar ne. Faɗin filin da yake tsakanin ɗakunan da suke gefen haikalin da ɗakunan firistoci kamu ashirin ne kewaye da haikalin. Akwai ƙofofin shiga daga fili, ɗaya a arewa ɗaya kuma a kudu; fāɗin tushen da ya yi kusa da filin kamu biyar ne kewaye.
Faɗin ginin da yake fuskantar filin haikali a wajen yamma kamu saba’in ne. Kaurin bangon ginin kamu biyar ne kewaye, tsawonsa kuma kamu tasa’in ne.
Sa’an nan ya auna haikalin; tsawonsa kamu ɗari ne, tsawon filin haikalin da ginin tare da bangayensa su ma kamu ɗari ne. Faɗin filin haikalin a wajen gabas, haɗe da gaban haikalin, kamu ɗari ne.
Sa’an nan ya auna tsawon ginin da yake fuskantar filin a bayan haikalin, haɗe da rumfunansa a kowane gefe, kamu ɗari.
Wuri mai tsarki da yake waje, wuri mai tsarki da yake can ciki da shirayin da yake fuskantar filin, da madogaran ƙofa da matsattsun tagogi da rumfuna kewaye da su ukun, har da kome da yake gaba haɗe da madogarar ƙofa, an rufe su da katako. An rufe bangon haikalin daga ƙasa har zuwa tagogi, tagogin kuwa an rufe su. A filin da yake bisan ƙofar shiga na waje zuwa wuri mai tsarki na can ciki da kuma a bangayen da aka daidaita tsakani kewaye da wuri mai tsarki na can ciki da kuma na can waje an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino. Zānen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu, fuskar ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe, ɗaya fuskar kamar ta zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zāna su dukan a jikin bangon haikalin kewaye. Daga ƙasa zuwa daurin ƙofa, an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a waje na wuri mai tsarki.
Wuri mai tsarki da yake waje yana da madogarar ƙofa murabba’i, haka ma wadda take a gaban Wuri Mafi Tsarki. Akwai bagaden katako mai tsayi kamu uku, fāɗinsa kamu biyu da kuma tsawonsa kamu biyu; kusurwansa, tushensa da kuma gefe-gefensa duk katako ne. Sai mutumin ya ce mini, “Wannan shi ne tebur da yake a gaban Ubangiji.” A wuri mai tsarki da yake waje da kuma Wuri Mafi Tsarki suna da ƙofa biyu a haɗe. Kowace ƙofa tana da murfi biyu masu buɗewa ciki da waje. A ƙofofin wuri mai tsarki da yake waje an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangayen, akwai kuma rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin. A bangayen da suke gefen shirayin akwai matsattsun tagogi da aka zāna siffar itatuwan dabino a kowane gefe. Gefe-gefen ɗakunan haikalin ma suna da rumfuna.
Ɗakuna don firistoci
Sai mutumin ya kai ni wajen arewa zuwa cikin filin da yake waje ya kuma kawo ni ɗakunan da suke ɗaura da filin haikalin da yake a gefen arewa. Tsawon ginin da yake fuskantar arewa kamu ɗari ne fāɗinsa kuma kamu hamsin. A gaban kamu ashirin na filin da yake can ciki da kuma a gaban daɓen filin da yake waje, akwai rumfuna a jere waɗanda suke fuskantar juna hawa uku-uku. A gaban ɗakunan akwai hanya a can ciki mai fāɗin kamu goma, tsawonta kuma kamu ɗari. Ƙofofinsu suna wajen arewa. Ɗakunan da suke bisa ba su da fāɗi, gama mataki hawan benen ya cinye wuri fiye da a ɗakunan da suke a hawa na ƙasa da na tsakiya. Ɗakunan da suke a hawa na uku ba su da ginshiƙai, yadda filayen suka kasance da su, saboda haka suka matsu fiye da waɗanda suke a hawa na ƙasa da na tsakiya. Akwai katanga wadda take waje, wadda ta yi hannun riga da ɗakunan filin waje; ta miƙe a gaban ɗakunan, tsawonta kamu hamsin ne. Yayinda tsawon jerin ɗakunan da suke a gefe kusa da filin da yake waje kamu hamsin ne, tsawon jerin ɗakunan da suke a gefen da yake kurkusa da wuri mai tsarki kamu ɗari ne. Ɗakunan da suke can ƙasa suna da ƙofar shiga a wajen gabas in za a shiga cikinsu daga filin da yake waje.
A wajen kudu42.10 Seftuwajin; Ibraniyanci Wajen gabas a ta katangar filin da yake waje, kusa da filin haikali da yake ɗaura da katangar waje, akwai ɗakuna da hanya a gabansu. Waɗannan sun yi kama da ɗakunan da suke wajen arewa; tsawonsu da fāɗinsu duk iri ɗaya ne, da irin mafita ɗaya da kuma yadda aka shirya su. Sun yi kama da ƙofofin da suke wajen arewa haka ma ƙofofin ɗakunan a wajen kudu. Akwai ƙofa a farkon hanyar da ta yi hannun riga da ɗayan katangar da ta miƙe wajen gabas, inda za a iya shiga ɗakunan.
Sai ya ce mini, “Ɗakunan arewa da na kudu waɗanda suke fuskantar filin haikali ɗakunan firistoci ne, inda firistocin da suke kusaci Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A can za su ajiye hadayu mafi tsarki, hadayu na gari, hadayu na zunubi da hadayu na laifi, gama wuri mai tsarki ne. Da zarar firistoci suka shiga wuri mai tsarki, ba za su fita zuwa filin da yake waje ba sai sun tuɓe rigunan da suka yi hidima da su, gama waɗannan masu tsarki ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su kusaci wuraren da mutane suke.”
Da ya gama auna filin da yake cikin haikali, sai ya fitar da ni ta ƙofar gabas ya auna dukan filin kewaye. Ya auna gefen gabas da karan awo; ya samu kamu ɗari biyar.42.16 Dubi Seftuwajin na ayar 17; Ibraniyanci karan gwaji; haka ma a ayoyi 18 da 19.,42.16 Kamu ɗari biyar ya yi daidai kamar kamu 875 ko kuwa kamar mita 265; haka ma a ayoyi 17, 18 da 19. Ya auna gefen arewa da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar. Ya auna gefen kudu da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar. Sa’an nan ya juya zuwa gefen yamma ya auna shi da karan awon, ya samu kamu ɗari biya. Ta haka ya auna dukan kusurwoyi huɗu. Filin yana da katanga kewaye da shi, tsawon kamu ɗari biyar, fāɗin kuma kamu ɗari biyar don yă raba wuri mai tsarki daga wuri marar tsarki.
Ɗaukaka ta komo haikali
Sai mutumin ya kawo ni ƙofar da take fuskantar gabas, sai na ga ɗaukakar Allah na Isra’ila tana tahowa daga gabas. Muryarsa ta yi kamar rurin ruwaye masu gudu, ƙasa kuma ta haskaka da ɗaukakarsa. Wahayin da na gani ya yi kamar wahayin da na gani sa’ad da ya zo don yă hallaka birnin, kamar kuma wahayin da na gani kusa da Kogin Kebar, na kuwa fāɗi rubda ciki. Ɗaukakar Ubangiji ta shiga haikali ta ƙofar da take fuskantar gabas. Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni cikin fili na can ciki, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.
Yayinda mutumin yana tsaye kusa da ni, na ji wani yana magana da ni daga cikin haikalin. Ya ce, “Ɗan mutum, wannan shi ne kursiyina da wurin tafin ƙafafuna. A nan ne zan zauna a cikin Isra’ilawa har abada. Gidan Isra’ila ba zai ƙara ɓata sunana mai tsarki ba, ko su ko sarakunansu, ta wurin karuwanci43.7 Ko kuwa zinansu ta ruhaniya; haka ma a aya 9 da gumakan da ba su da rai,43.7 Ko kuwa gawawwaki; haka ma a aya 9 sarakunansu a masujadan kan tudu. Sa’ad da suka sa madogarar ƙofarsu kusa da madogarar ƙofata, da katanga kawai a tsakanina da su, sun ɓata sunana mai tsarki ta wurin ayyukansu masu banƙyama. Saboda haka na hallaka su cikin fushina. Yanzu bari su kawar da karuwancinsu da gumakansu waɗanda ba su da rai na sarakunansu daga gabana, zan kuwa zauna a cikinsu har abada.
“Ɗan mutum, ka bayyana haikalin ga mutanen Isra’ila, don su ji kunya saboda zunubansu. Bari su yi la’akari da fasalin, kuma in suka ji kunyar abubuwan da suka aikata, sai ka sanar musu fasalin haikalin da shirye-shiryensa, ƙofofinsa na shiga da fita, dukan fasalinsa da dukan ƙa’idodinsa da dokokinsa. Ka rubuta waɗannan a gabansu saboda su yi aminci da fasalinsa su kuma kiyaye dukan ƙa’idodinsa.
“Wannan ita ce dokar haikalin. Dukan filin da yake kewaye a kan dutsen, zai zama wuri mafi tsarki. Dokar haikalin ke nan.
Bagade
“Waɗannan su ne aune-aunen bagade a tsawon kamu, wannan kamu shi ne kamun tafin hannu. Zurfin magudanar ruwansa kamu ɗaya ne fāɗinsa kuma kamu ɗaya, tare da da’ira kamun tafi ɗaya kewaye da gefensa. Wannan kuma shi ne tsayin bagaden. Daga lambatun da yake a ƙasa har zuwa ƙaramin mahaɗin da yake ƙasa wanda ya kewaye bagade, tsayinsa kamu biyu ne, fāɗinsa kuma kamu guda. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗin wanda ya kewaye bagade, zai zama kamu huɗu, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya. Murhun bagaden kamu huɗu ne, akwai ƙahoni guda huɗu sun miƙe sama daga murhun. Murhun bagaden murabba’i ne, tsawonsa kamu goma sha biyu, fāɗinsa kuma kamu goma sha biyu. Gefen bisa ma murabba’i ne, tsawonsa kamu goma sha huɗu fāɗinsa kuma kamu goma huɗu, da da’ira da yake da fāɗin rabin kamu da magudanan ruwa kamu guda kewaye. Matakan bagaden suna fuskantar gabas.”
Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa waɗannan su ne za su zama ƙa’idodi don yin hadaya ta ƙonawa da yayyafawar jini a kan bagaden sa’ad da aka gina shi. Za ka ba da ɗan bijimi a matsayin hadaya ta ƙonawa ga firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, na iyalin Zadok, waɗanda suke zuwa kusa don hidima a gabana, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Za ka ɗibi jininsa ka zuba shi a ƙahoni huɗu na bagaden a gefen bisa da kuma kewaye da da’irar, ta haka za ka tsarkake bagaden ka kuma yi kafara dominsa. Za ka ɗauki bijimi na hadaya don zunubi ka ƙone shi a sashen da aka shirya na haikalin a wani wuri waje da wuri mai tsarki.
“A rana ta biyu za ka miƙa bunsuru marar lahani domin hadaya don zunubi, za a kuma tsarkake bagaden yadda aka yi da bijimin. Sa’ad da ka gama tsarkake shi, sai ka miƙa ɗan bijimi da kuma rago daga cikin garke, dukansu marasa lahani. Za ka miƙa su a gaban Ubangiji, firistoci kuma za su barbaɗe gishiri a kansu su kuma miƙa su kamar hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.
“Kwana bakwai za ka tanada bunsuru kullum domin hadaya don zunubi; za ka kuma tanada ɗan bijimi da rago daga garke, dukansu marasa lahani. Kwana bakwai za su yi kafara saboda bagaden su kuma tsarkake shi; ta haka za su keɓe shi. A ƙarshen waɗannan kwanaki, daga rana ta takwas zuwa gaba, firistoci za su miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kan bagade. Sa’an nan zan karɓe ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Sarki, Lawiyawa, Firistoci
Sai mutumin ya komo da ni zuwa ƙofar waje na wuri mai tsarki, wadda take fuskantar gabas, tana kuwa a rufe. Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofar za tă kasance a rufe. Ba za a buɗe ta ba; ba wanda zai shiga ta wurinta. Za tă kasance a rufe domin Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya shiga ta wurinta. Sarki kansa ne kaɗai zai zauna a hanyar shiga don yă ci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin hanyar shiga yă kuma fita a wannan hanya.”
Sa’an nan mutumin ya kawo ni ta hanyar ƙofar arewa zuwa gaban haikali. Na duba na kuma ga ɗaukakar Ubangiji tana cika haikalin Ubangiji, sai na fāɗi rubda ciki.
Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka saurara sosai ka kuma mai da hankali ga kome da na faɗa maka game da dukan ƙa’idodi game da haikalin Ubangiji. Ka lura sosai da ƙofar shigar haikali da kuma dukan ƙofofin wuri mai tsarki. Faɗa wa ’yan tawayen gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ayyukan banƙyamarku sun isa haka, ya gidan Isra’ila! Ban da dukan sauran ayyukanku na banƙyama, kun kawo baƙi marasa kaciya a zuciya da jiki a wurina mai tsarki, kun kuma ƙazantar da haikalina yayinda kuke miƙa mini abinci, kitse da kuma jini, kun kuma karya alkawarina. A maimakon yin ayyukanku bisa ga abubuwana masu tsarki, kun sa waɗansu su lura da wurina mai tsarki. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba baƙo marar kaciya a zuciya da jiki da zai shiga wurina mai tsarki, kai, har ma da baƙin da suke zama a cikin Isra’ila.
“ ‘Lawiyawan da suka yi nesa da ni sa’ad da Isra’ila suka kauce da kuma waɗanda suka karkata daga gare ni suka bi gumakansu, dole su ɗauki alhakin zunubinsu. Za su iya yin hidima a wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin haikali suna kuma hidima a cikinsu; za su iya yankan hadayun ƙonawa da sadaka don mutane su kuma tsaya a gaban mutane su yi musu hidima. Amma domin sun yi musu hidima a gaban gumakansu suka sa gidan Isra’ila ya yi zunubi, saboda haka na ɗaga hannu na rantse cewa dole su ɗauki alhakin zunubinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba za su yi kusa don su yi hidima kamar firistoci ko su zo kusa da abubuwana masu tsarki ko hadayuna mafi tsarki ba; dole su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama. Duk da haka zan sa su su lura da ayyukan haikali da kuma dukan ayyukan da za a yi a cikinsa.
“ ‘Amma firistoci, waɗanda suke Lawiyawa kuma zuriyar Zadok waɗanda suka yi aminci ta wurin yin ayyukansu a wurina mai tsarki sa’ad da Isra’ilawa suka kauce daga gare ni, su ne za su zo kusa don hidima a gabana; za su tsaya a gabana don miƙa hadayun kitse da jini, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Su ne kaɗai za su shiga wurina mai tsarki; su ne kaɗai za su zo kusa da teburina don yin hidima a gabana su kuma yi hidimata.
“ ‘Sa’ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, dole su sa tufafin lilin; kada su sa wani rigar da aka yi da ulu yayinda suke hidima a ƙofofin fili na can ciki da cikin haikali. Za su naɗa rawunan lilin a kawunansu, su kuma sa wandunan lilin. Kada su sa wani abin da zai sa su yi zuffa. Sa’ad da suka fita daga haikali zuwa fili na waje inda mutane suke, sai su tuɓe rigunan da suka yi hidima da su su bar su a tsarkakan ɗakuna, su sa waɗansu riguna, don kada su tsarkake mutane ta wurin rigunansu.
“ ‘Ba za su aske kawunansu ko su bar gashin kansu ya yi tsayi ba, amma sai su sausaye gashin kansu. Kada firist ya sha ruwan inabi sa’ad da zai shiga fili na can ciki. Kada su auri gwauruwa ko macen da aka sāke; za su auri budurwai ne kaɗai na Isra’ilawa ko gwaurayen firistoci. Za su koyar da mutanena bambanci tsakanin tsarki da rashin tsarki su kuma nuna musu yadda za su bambanta marar tsarki da mai tsarki.
“ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.
“ ‘Firist ba zai ƙazantar da kansa ta wurin zuwa kusa da gawa ba; amma, in gawar mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ko ɗansa ko ’yarsa, ko ɗan’uwansa ko ’yar’uwarsa ce, to, ba zai ƙazantar da kansa ba. Bayan ya tsarkaka, dole yă jira har kwana bakwai. A ranar da ya shiga fili na can ciki na wuri mai tsarki don hidima a wuri mai tsarki, zai miƙa hadaya don zunubi saboda kansa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘Ni ne kaɗai zan zama abin gādon da firistoci za su kasance da shi. Kada ka ba su wani mallaka a Isra’ila; zan zama mallakarsu. Za su ci hadaya ta gari, hadaya don zunubi da hadaya don laifi; da kuma kowane keɓaɓɓen abu a Isra’ila da za a ba wa Ubangiji zai zama nasu. Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku. Firistoci ba za su ci mushen tsuntsu ko na dabba ba, ba kuwa za su ci waɗanda namun jeji suka kashe ba.
Rabon ƙasa
“ ‘Sa’ad da kuka rarraba ƙasar gādo, ku miƙa wa Ubangiji rabon ƙasar ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa ya zama kamu 25,000 fāɗinsa kuma ya zama 20,000, dukan ƙasar za tă zama mai tsarki. Daga cikin wannan, sashe guda da yake murabba’i mai tsawo kamu 500 zai zama don wuri mai tsarki, kamu 50 kewaye da shi zai zama fili. A cikin yanki mai tsarki, ka auna tsawo kamu 25,000 da kuma fāɗi kamu 10,000. A cikinsa wuri mai tsarki zai kasance, Wuri Mafi Tsarki. Zai zama tsattsarkan rabo na ƙasa domin firistoci, waɗanda za su yi hidima a cikin wuri mai tsarki da kuma waɗanda za su zo kusa don su yi hidima a gaban Ubangiji. Zai zama wuri don gidajensu ya kuma zama tsattsarkan wuri saboda wuri mai tsarki. Wani sashi kuma mai tsawo kamu 25,000 da fāɗi 10,000 zai zama na Lawiyawa, waɗanda suke hidima a cikin haikali, zai zama mallakarsu don su zauna a ciki.
“ ‘Za ka ba wa birnin fāɗin mallakarsa kamu 5,000, tsawonsa kuma 25,000, haɗe da tsattsarkan rabo; zai kasance na gidan Isra’ila duka.
“ ‘Sarki zai kasance da fili da ya yi iyaka da kowane gefe na yankin wuri mai tsarki da kuma mallakar birnin. Zai miƙe ya yi wajen yamma daga gefen yamma ya kuma yi wajen gabas daga gefen gabas, yana miƙewa a tsawo daga wajen yamma zuwa wajen gabashin iyaka don yă yi hannun riga da rabon kabilan. Wannan fili zai zama mallakarsa a Isra’ila. Kuma sarakunana ba za su ƙara zaluntar mutanena ba amma za su bar gidan Isra’ila ya mallaki ƙasar bisa ga kabilansu.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko na ce ku sarakunan Isra’ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari’a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku yi amfani da garwan da yake daidai, efa45.10 Efa abin awo ne na busassun abubuwa. da yake daidai da kuma garwa45.10 Garwa abin awo ne na abubuwan da suke ruwa-ruwa. da yake daidai. Efa da garwan su kasance girmansu ɗaya, garwan ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga45.11 Ganga abin awo ne na busassun abubuwa. efa kuma ya zama kashi ɗaya bisa goma na ganga; ganga fitaccen ma’auni na duka biyu. Shekel zai kasance da gera ashirin. Shekel ashirin a haɗa da shekel ashirin da biyar a haɗa da shekel goma sha biyar zai zama mina guda.45.12 Wato, shekel 60; mina da aka saba amfani kan ci shekel 50.
Hadayu da ranaku masu tsarki
“ ‘Wannan ita ce bayarwa ta musamman da za ku miƙa, kashi ɗaya bisa shida na efa daga kowace gangan alkama da kashi ɗaya bisa shida na efa daga kowace gangan sha’ir. Sashe na man da aka ƙayyade, da aka auna da garwa, kashi ɗaya bisa goma ne na garwa daga ganga (wanda yakan ci garwa goma, gama garwa goma suna daidai da ganga guda). A kuma ba da tunkiya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu daga makiyaya da aka yi masa banruwa sosai na Isra’ila. Za a yi amfani da waɗannan don hadayun gari, hadayun ƙonawa da hadayun salama don yin kafara saboda mutane, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwa ta musamman saboda amfanin sarki a Isra’ila. Zai zama hakkin sarki ne ya tanada hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da hadayu na sha a bukukkuwa, Sabuwar Wata da Asabbatai, a duk ƙayyadaddun bukukkuwa na gidan Isra’ila. Zai tanada hadayu don zunubi, hadayu na gari, hadayu na ƙonawa da hadayu na salama don yin kafara saboda gidan Isra’ila.
([Fitowa 12.1-20]; [Firistoci 23.33-43])
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a farkon wata a rana ta fari za ku ba da ɗan bijimi marar lahani a kuma tsarkake wuri mai tsarki. Firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi ya shafa a madogaran ƙofar haikali, a kusurwoyi huɗu na gefen bisa na bagade da kuma a kan madogaran ƙofar shiga na fili na can ciki. Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan domin duk wanda ya yi zunubai ba da gangan ba ko ta wurin rashin sani; saboda haka sai ku yi kafara domin haikalin.
“ ‘A wata na fari a rana ta goma sha huɗu za ku kiyaye Bikin Ƙetarewa, bikin da yakan ɗauki kwana bakwai, a lokacin ne za ku riƙa cin burodi marar yisti. A wannan rana sarki zai tanada bijimi a matsayin hadaya don zunubi domin kansa da kuma domin dukan mutanen ƙasar. Kowace rana a kwanaki bakwai na Bikin zai tanada bijimai guda bakwai da raguna bakwai marar lahani a matsayi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da kuma bunsuru saboda hadaya don zunubi. Zai tanada efa na gari don kowane bijimi da kuma efa don kowane rago, tare da kwalabar mai don kowane efa guda.
“ ‘A lokacin kwana bakwai na Bikin, waɗanda za su fara a wata na bakwai a rana ta goma sha biyar, zai ba da abubuwan nan saboda hadayu don zunubi, hadayu na ƙonawa, hadayu na gari da kuma mai.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a rufe ƙofa ta fili na can cikin da take fuskantar gabas ranaku shida na aiki, amma a ranar Asabbaci da kuma a ranar ganin Sabuwar Wata a buɗe ta. Sarki zai shiga daga waje ta shirayin hanyar shiga yă tsaya a madogarar ƙofa. Firistoci za su miƙa hadayarsa ta ƙonawa da hadayunsa na salama. Zai yi sujada a madogarar ƙofar hanyar shiga sa’an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da yamma. A Asabbatai da kuma a Sabuwar Wata mutanen ƙasar za su yi sujada a gaban Ubangiji a mashigin wannan hanyar shiga. Hadaya ta ƙonawar da sarki ya kawo wa Ubangiji a ranar Asabbaci ’yan raguna shida ne da rago guda, dukansu marasa lahani. Hadayar garin da aka bayar tare da ragon efa guda ne, hadayar garin da ’yan ragunan yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa. A ranar Sabuwar Wata zai miƙa ɗan bijimi, ’yan raguna guda shida da kuma rago guda, dukansu marasa lahani. Zai tanada a matsayin hadaya ta gari, efa guda tare da bijimi, efa guda tare da ’yan raguna, da kuma ’yan raguna yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa. Sa’ad da sarki zai shiga, zai shiga ta shirayin hanyar shiga, zai kuma fita ta nan.
“ ‘Sa’ad da mutanen ƙasar suka zo gaban Ubangiji a ƙayyadaddun bukukkuwa, duk wanda ya shiga ta ƙofar arewa don yă yi sujada sai ya fita ta ƙofar kudu; kuma duk wanda ya shiga ta ƙofar kudu sai ya fita ta ƙofar arewa. Ba wanda zai koma ta ƙofar da ya shiga, amma kowa zai fita a ƙofar ɗaura da wadda ya shiga. Sarki zai kasance a cikinsu, zai shiga sa’ad da suke shiga ya kuma fita sa’ad da suka fita.
“ ‘A bukukkuwa da ƙayyadaddun bukukkuwa, hadaya ta gari zai zama efa tare da bijimi, efa da rago, da kuma ’yan raguna da ya ga dama, haɗe da kwalabar mai. Sa’ad da sarki ya ba da hadaya ta yardar rai ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa ce ko hadayun salama ne, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko hadayarsa ta salama yadda yakan yi a ranar Asabbaci. Sa’an nan ya fita, bayan kuma ya fita, sai a rufe ƙofar.
“ ‘Kullum za ku tanada ɗan rago bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji; kowace safiya za ku tanada shi. Tare da shi za ku tanada hadaya ta gari kowace safiya, da ya haɗa da kashi ɗaya bisa shida na efa tare da kashi ɗaya bisa uku na mai ga garin da aka cuɗa. Miƙawar wannan hadaya ta gari ga Ubangiji dawwammamiyar farilla ce. Saboda haka za a tanada ɗan rago da hadaya ta gari da kuma mai kowace safiya don hadaya ta ƙonawa ta kullum.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa in sarkin ya ba wa ɗaya daga cikin ’ya’yansa kyauta daga gādonsa, zai kuwa zama na zuriyar; zai kuwa zama mallakarsu ta wurin gādo. In kuma ya ba wa ɗaya daga cikin bayinsa kyauta daga gadonsa, bawan zai iya riƙe shi sai shekarar ’yantarwa; sa’an nan ya mayar wa sarkin. Gādon sarki na ’ya’yansa maza ne kaɗai; na su ne. Kada sarki ya ƙwace gādon mutane, yana korinsu daga mallakarsu. Zai ba wa ’ya’yansa maza gādonsu daga cikin mallakarsa, don kada a raba wani daga mutanena da mallakarsa.’ ”
Sa’an nan mutumin ya fitar da ni ta ƙofar shiga a gefen ƙofar zuwa tsarkakakkun ɗakuna waɗanda suke fuskantar arewa, waɗanda suke na firistoci, ya kuma nuna mini wani wuri daga can ƙurewar yamma. Ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya don laifi, da hadaya don zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gari, domin kada su kai su a filin da yake waje, su tsarkake mutane.”
Sa’an nan ya kawo ni filin da yake waje ya kuma bi da ni kewaye da kusurwoyi huɗunsa, na kuma ga kowace kusurwa na wani fili. A kusurwoyi huɗu na filin da yake waje akwai waɗansu filaye a haɗe, tsawonsu kamu arba’in fāɗinsu kuwa kamu talatin; kowane fili a kusurwoyi huɗun nan girmansu ɗaya ne. Kewaye da cikin kowane filin huɗun nan akwai ginin dutse, da murhu da aka gina a kewaye a ƙarƙashin ginin. Sai ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a haikali za su dafa hadayun da jama’a.”
Kogin da ya malalo daga haikali
Mutumin ya komo da ni zuwa mashigin haikalin, sai na kuwa ga ruwa yana malalowa daga ƙarƙashin madogarar ƙofar haikalin wajen gabas (gama haikalin yana fuskantar gabas). Ruwan yana malalowa daga ƙarƙashin gefen kudun haikalin, kudu da bagaden. Sai ya fitar da ni ta ƙofar arewa ya kewaye da ni ta waje zuwa ƙofar da take waje mai fuskantar gabas, ruwan kuwa yana malalowa daga wajen kudu.
Yayinda mutumin ya yi wajen gabas da karan awo a hannunsa, sai ya auna kamu dubu ya kuma bi da ni ta ruwan da zurfinsa ya kama ni a idon ƙafa. Ya auna wani kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa ya kai ni gwiwa. Ya sāke auna kamu dubu ya kuma bi da ni a ruwan da zurfinsa kama ni a gindi. Ya auna wani kamu dubu, amma a yanzu ruwan ya zama kogin da ban iya hayewa ba, domin ruwan ya taso ya kuma yi zurfin da ya isa a yi iyo a ciki, kogin da ba za a iya hayewa ba. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan?”
Sa’an nan ya komo da ni zuwa bakin kogin. Sa’ad da na iso can, sai na ga itatuwa masu yawa a kowane gefen kogin. Sai ya ce mini, “Wannan ruwa yana malalowa zuwa yankin gabas ya kuma gangaro zuwa cikin Araba,47.8 Ko kuwa Kwarin Urdun inda zai shiga Teku. Sa’ad da ya shiga cikin Tekun sai ruwan a can ya zama mai daɗi. Tarin halittu masu rai za su rayu a duk inda ruwan ya malalo. Za a kasance da kifi masu yawa, domin wannan ruwa yana malalowa a can yana kuma mai da ruwan gishiri yă zama ruwa mai daɗi; saboda haka duk inda ruwan ya malalo, kome zai rayu. Masunta za su tsaya a gaɓar; daga En Gedi zuwa En Eglayim, za a kasance da wuraren jefa abin kamun kifi. Za a sami kifayen iri-iri, kamar kifaye Bahar Rum.47.10 Wato, Mediterraniyan; haka ma a ayoyi 15, 19 da 20 Amma fadamun da tafkunan ba za su zama masu daɗi ba; za a bar su a gishirinsu. ’Ya’yan itatuwa na kowane iri za su yi girma a kowane gefen kogin. Ganyayensu ba su bushe ba, ba kuwa za su fasa yin ’ya’ya ba. Kowane wata za su ba da ’ya’ya domin ruwa daga wuri mai tsarki yana malalo musu. ’Ya’yansu za su zama abinci, ganyayensu kuma za su zama magani.”
Iyakokin ƙasar
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Waɗannan su ne iyakokin da za ku raba ƙasar gādo cikin kabilan Isra’ila goma sha biyu, da rabo biyu don Yusuf. Za ku raba ta daidai a cikinsu. Gama na ɗaga hannu na rantse zan ba da ita ga kakanninku, wannan ƙasa za tă zama gādonku.
“Wannan ce za tă zama iyakar ƙasa.
“A wajen arewa za tă fara daga Bahar Rum ta hanyar Hetlon ta wuce Lebo Hamat zuwa Zedad, Berota47.15,16 Dubi Seftuwajin da kuma Ezk 48.1; Ibraniyanci hanya zuwa cikin Zedad, 16 Hamat, Berota. da Sibrayim (wadda take a iyaka tsakanin Damaskus da Hamat), har zuwa Hazer-Hattikon, wadda take a iyakar Hauran. Iyakar za tă miƙe daga teku zuwa Hazar-Enon, ta iyakar Damaskus, da iyakar Hamat a arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa.
A wajen gabas iyakar za tă kama tsakanin Hauran da Damaskus, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra’ila, zuwa tekun gabas har zuwa Tamar.47.18 Seftuwajin da Siriyak; Ibraniyanci Isra’ila. Za ka auna zuwa tekun gabas. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.
A wajen kudu za tă fara daga Tamar har zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.
A wajen yamma, Bahar Rum ne zai zama iyakar zuwa wani wuri ɗaura da Lebo47.20 Ko kuwa ɗaura da ƙofar zuwa Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.
“Za ku rarraba wannan ƙasa a tsakaninku bisa ga kabilan Isra’ila. Za ku raba ta kamar gādo wa kanku da kuma wa baƙin da suka zauna a cikinku waɗanda suke da ’ya’ya. Za ku ɗauka su kamar ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa; za su yi gādo tare da ku a cikin kabilan Isra’ila. A duk kabilar da baƙon yake zama, a can za ku ba shi gādonsa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Rarraba ƙasar
“Ga kabilan, a jere bisa ga sunayensu.
“A iyaka ta arewa, Dan zai sami rabo; zai bi hanyar Hetlon zuwa Lebo48.1 Ko kuwa zuwa ƙofar Hamat. Hazar-Enan da iyakar arewancin Damaskus kusa da Hamat za tă zama sashen iyakarsa a wajen gabas zuwa wajen yamma.
Asher zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Dan daga gabas zuwa yamma.
Naftali zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Asher daga gabas zuwa yamma.
Manasse zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.
Efraim zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Manasse daga gabas zuwa yamma.
Ruben zai sami rabo; zai yi iyaka da Efraim daga gabas zuwa yamma.
Yahuda zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Ruben daga gabas zuwa yamma.
“Kusa da yankin Yahuda daga gabas zuwa yamma zai zama rabon da za ku bayar a matsayin kyauta ta musamman. Faɗinsa zai zama kamu 25,000, tsawonsa kuma zai zama daidai da tsawon yankunan kabilu daga gabas zuwa yamma; wuri mai tsarki zai kasance a tsakiyar wannan yanki.
“Tsawon rabo na musamman da za ku bayar ga Ubangiji zai zama kamu 25,000, fāɗinsa kuma kamu 10,000. Wannan ne zai zama tsattsarkan rabo domin firistoci. Tsawon zai zama kamu 25,000 a wajen arewa, fāɗin kuma kamu 10,000 wajen yamma, kamu 10,000 zai zama fāɗinsa a wajen gabas, tsawonsa a wajen kudu zai zama kamu 25,000. A tsakiyarsa ne wuri mai tsarki na Ubangiji zai kasance. Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci, zuriyar Zadok, waɗanda suka yi aminci cikin hidimata ba su kuwa karkata kamar yadda Lawiyawa suka yi sa’ad da Isra’ilawa suka karkace ba. Zai zama kyauta ta musamman a gare su daga tsattsarkan rabon ƙasar, kusa da yankin Lawiyawa.
“Dab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu 25,000, fāɗin kuma kamu 10,000. Tsawonsa gaba ɗaya zai zama kamu 25,000, fāɗinsa kuma kamu 10,000. Ba za su sayar da shi ko su musayar da wani sashensa ba. Wannan shi ne mafi kyau na ƙasar ba kuma za a jinginar da ita ga wani ba, gama mai tsarki ce ga Ubangiji.
“Sauran wurin da ya rage mai fāɗin kamu 5,000 da tsawon kamu 25,000 zai zama don amfanin kowa a birnin, don gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar wurin da ya ragen nan zai kuwa kasance da wannan awon, a wajen arewa kamu 45,000, wajen kudu kamu 45,000, wajen gabas kamu 45,000, wajen kudu kuma kamu 45,000. Wurin kiwo don birnin zai zama kamu 250 a wajen arewa, kamu 250 a wajen kudu, kamu 250 a wajen gabas da kuma kamu 250 a wajen yamma. Tsawon abin da ya rage a wurin, dab da tsattsarkan rabo, zai zama kamu 10,000 wajen gabas, kamu 10,000 kuma wajen yamma. Amfanin da zai bayar zai tanada abinci don ma’aikatan birnin. Masu aiki daga birnin waɗanda suka nome ta za su fito daga dukan kabilan Isra’ila. Dukan rabon zai zama murabba’i, kamu 25,000 kowane gefe. A matsayin kyauta ta musamman za ku keɓe tsattsarkan rabo, haka ma za ku yi da mallakar birnin.
“Abin da ya rage a kowane gefe na wurin zai zama tsattsarkan rabo kuma mallakar birnin za tă zama ta sarki. Zai miƙe wajen gabas daga kamu 25,000 na tsattsarkan rabo zuwa iyakar da take wajen gabashin iyaka, da kuma a wajen yamma kamu 25,000 zuwa iyakar da take a wajen yamma. Dukan wuraren nan da suke hannun riga da rabon kabilan zai zama na sarki, tsattsarkan rabon tare da wuri mai tsarkin za su kasance a tsakiyarsu. Ta haka mallakar Lawiyawa da mallakar birnin za su kasance a tsakiyar wurin da yake na sarki. Wurin da yake na sarki zai kasance tsakanin iyakar Yahuda da iyakar Benyamin.
“Game da sauran kabilun kuwa,
“Benyamin zai sami rabo; zai miƙe daga wajen gabas zuwa wajen yamma.
Simeyon zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Benyamin daga gabas zuwa yamma.
Issakar zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Simeyon daga gabas zuwa yamma.
Zebulun zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Issakar daga gabas zuwa yamma.
Gad zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Zebulun daga gabas zuwa yamma.
Iyakar kudu ta Gad za tă miƙe kudu daga Tamar zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum.48.28 Wato, Mediterraniyan
“Wannan ce ƙasar da za ku raba gādo ga kabilan Isra’ila, kuma wannan ne zai zama rabonsu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Ƙofofin sabon birni
“Waɗannan za su zama ƙofofin birnin.
“Farawa da gefen arewa, wanda yake da tsawon kamu 4,500 za a ba wa ƙofofin birnin sunaye kabilan Isra’ila. Ƙofofi uku a gefen arewa za su zama ƙofar Ruben, ƙofar Yahuda da ƙofar Lawi.
A gefen gabas, wanda yake da tsawon kamu 4,500 zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Yusuf, ƙofar Benyamin da ƙofar Dan.
A gefen kudu, wanda yake da tsawon kamu 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Simeyon, ƙofar Issakar da ƙofar Zebulun.
A gefen yamma, wanda yake da tsawon kamun 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Gad, ƙofar Asher da kuma ƙofar Naftali.
“Duk nisan wurare kewaye da birnin zai zama kamu 18,000 ne.
“Sunan birnin kuwa daga wannan lokaci zai zama, ‘Ubangiji yana a nan.’ ”