- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Fitowa
Fitowa
Fitowa
Fit
Fitowa
Wahalar Isra’ilawa a Masar
Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isra’ila maza, waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub; kowanne da iyalinsa.
Ruben, Simeyon, Lawi da Yahuda;
Issakar, Zebulun da Benyamin;
Dan da Naftali;
Gad da Asher.
Zuriyar Yaƙub duka sun kai mutum saba’in. Yusuf ya riga ya kasance a Masar.
Yanzu Yusuf da dukan ’yan’uwansa da kuma dukan tsaran nan da suka tafi Masar, sun mutu, amma Isra’ilawa sun riɓaɓɓanya, suka kuma yi ta haihuwa sosai, suka yi yawan sosai, har ƙasar ta cika da su.
Sai wani sabon sarki wanda bai san Yusuf ba, ya hau sarautar Masar. Ya ce wa mutanensa, “Duba Isra’ilawa sun yi yawa, sun fi ƙarfinmu. Ku zo, mu yi dabara a kansu, in ba haka ba za su ƙaru fiye da haka, in kuwa yaƙi ya tashi tsakaninmu da abokan gāba, za su iya haɗa kai da abokan gāba, su yaƙe mu, su bar ƙasar.”
Saboda haka sai suka naɗa shugabannin gandu a kansu don su wahalshe su, su kuma bauta musu, suka sa su suka gina biranen Fitom da Rameses su zama biranen ajiya, domin Fir’auna. Amma duk da wannan ƙarin wulaƙancin da ake yi musu, su kuwa sai daɗa riɓaɓɓanya suke ta yi. Sai tsoron Isra’ilawa ya ƙaru a zuciyar Masarawa, ganin haka sai Masarawa suka ƙara musu wahala. Suka baƙanta wa Isra’ilawa rai da bauta mai wuya, ta wurin sa su yin tubali da yumɓu, da kuma kowace irin bauta a gonaki. A cikin dukan ayyukansu, Masarawa ba su ji tausayinsu ba ko kaɗan.
Sai Sarkin Masar ya gaya wa ungozomomin matan Ibraniyawa, wato, su Shofra da Fuwa ya ce, “Sa’ad da kuke taimakon matan Ibraniyawa lokacin haihuwa, in jaririn namiji ne ku kashe shi, amma in ta mace ce, ku bar ta da rai.” Amma ungozomomin nan masu tsoron Allah ne, ba su kuwa aikata abin da sarkin Masar ya gaya musu ba; suka bar jarirai maza su rayu. Sai sarkin Masar ya kira ungozomomin, ya tambaye su ya ce, “Don me kuka yi haka? Don me kuka bar jarirai maza su rayu?”
Ungozoman suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Ai, matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gwarzaye ne, sukan haihu kafin ungozomomin su kai wurinsu.”
Saboda haka Allah ya nuna alheri wa ungozomomin, Isra’ilawa kuwa suka yi yawa fiye da dā. Saboda ungozomomin suna tsoron Allah, sai Allah ya ba su iyalan kansu.
Sai Fir’auna ya ba da umarni wa mutanensa ya ce, “Duk yaron da yake namijin da haka haifa, dole ku jefa shi cikin kogi, amma ku bar yara mata su rayu.”
Haihuwar Musa
Ana nan, sai wani Balawe ya auri wata Balawiya, ta kuwa yi ciki, ta haifi ɗa. Sa’ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har watanni uku. Amma da ba tă iya ɓoye shi kuma ba, sai ta yi kwandon kyauro ta shafa masa kwalta. Bayan haka sai ta sa jaririn a cikin kwandon, ta je ta ajiye kwandon tare da jaririn a cikin kyauro, a bakin kogin. ’Yar’uwarsa ta tsaya da ɗan rata tana lura da abin da zai faru da shi.
Sai ’yar Fir’auna ta gangara zuwa kogi domin tă yi wanka, bayinta kuwa suna tafiya a bakin kogi. Sai ta ga kwandon a ciyawa, ta aiki ɗaya daga cikin masu hidimarta tă ɗauko mata. Da ta buɗe kwandon, sai ta ga yaro yana kuka, ta kuwa ji tausayinsa. Ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin jariran Ibraniyawa ne.”
Sai ’yar’uwarsa ta tambayi ’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?”
Sai ta amsa ta ce, “I, tafi.” Sai yarinyar ta tafi ta kawo mahaifiyar yaron. Diyar Fir’auna ta ce mata, “Ɗauki jaririn, ki yi mini renonsa, zan kuwa biya ki.” Saboda haka ta ɗauki yaron, ta yi renonsa. Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen ’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.”
Musa ya gudu zuwa Midiyan
Wata rana, bayan Musa ya yi girma, sai ya haura, ya tafi inda mutanensa suke, ya kuma ga yadda suke shan wahala da aiki. Ya ga wani mutumin Masar yana dūkan mutumin Ibraniyawa, ɗaya daga cikin mutanensa. Da ya leƙa nan da can bai kuwa ga kowa ba, sai ya kashe mutumin Masar, ya ɓoye shi a yashi. Kashegari ya fita, sai ya ga Ibraniyawa biyu suna faɗa. Ya tambayi mai laifin ya ce, “Don me kake bugun ɗan’uwanka, mutumin Ibraniyawa?”
Mutumin ya ce masa, “Wa ya mai da kai mai mulki da mai hukunci a kanmu? Kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan?” Sai Musa ya tsorata, ya yi tunani ya ce, “To, fa, abin nan da na yi, ya zama sananne.”
Da Fir’auna ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă kashe Musa, amma Musa ya gudu daga wajen Fir’auna, ya tafi ƙasar Midiyan inda ya zauna kusa da wata rijiya. To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da ’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu. Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu.
Da ’yan matan suka komo wurin Reyuwel mahaifinsu, sai ya tambaye su ya ce, “Yaya kuka dawo da wuri yau?”
Suka amsa suka ce, “Wani mutumin Masar ne ya taimake mu daga hannun waɗansu makiyaya. Har ma ya ɗebo ruwa ya shayar da dabbobin.”
Ya tambayi ’yan matansa, “To ina yake? Don me kuka bar shi a can? A gayyace shi, yă zo, yă ci wani abu.”
Musa ya yarda yă zauna da mutumin wanda ya ba da ’yarsa Ziffora aure da Musa. Ziffora ta haifi wa Musa ɗa, ya kuma raɗa masa suna Gershom cewa, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa.”
Ana nan dai, a kwana a tashi, sai sarkin Masar ya mutu. Isra’ilawa suka yi kuka mai zafi saboda bautarsu mai wuya, sai kukar neman taimakonsu saboda bauta, ya kai wurin Allah. Allah kuwa ya ji kukansu sai ya tuna da alkawarinsa da Ibrahim da Ishaku da Yaƙub. Sai Allah ya dubi Isra’ilawa, ya kuma damu da su.
Musa da ƙaramin itace mai cin wuta
Ana nan wata rana Musa yana kiwon tumakin Yetro surukinsa, firist na Midiyan, sai ya bi da tumaki zuwa gefe mai nisa a cikin hamada, har ya zo Horeb, dutsen Allah. A can mala’ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a ƙaramin itace. Musa ya lura cewa ko da yake wuta na ci ƙaramin itacen, amma bai ƙone ba. Sai Musa ya ce, “Wannan abin mamaki ne, don me wannan itace bai ƙone ba? Bari in matso kusa in gani.”
Da Ubangiji ya ga Musa ya matso don yă duba, sai Allah ya yi kira daga cikin ƙaramin itacen ya ce, “Musa! Musa!”
Sai Musa ya amsa ya ce, “Ga ni.”
Allah ya ce, “Kada ka zo kusa, tuɓe takalmanka, gama inda kake tsaye, wuri ne mai tsarki.” Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub.” Da jin wannan, sai Musa ya ɓoye fuskarsa, domin ya ji tsoro yă dubi Allah.
Ubangiji ya ce, “Tabbatacce na ga azabar mutanena a Masar. Na ji su suna kuka saboda matsin da shugabannin gandunsu suke musu, na kuma damu da wahalarsu. Saboda haka na sauko domin in cece su daga hannun Masarawa, in kuma fitar da su daga ƙasar Masar, in kai su ƙasa mai kyau mai fāɗi, ƙasa mai zub da madara da zuma, inda Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa suke. Yanzu kukan Isra’ilawa ya kai gare ni, na kuma ga yadda Masarawa suke wulaƙanta su To, fa, sai ka tafi. Ina aikan ka wurin Fir’auna don ka fitar da mutanena Isra’ilawa daga Masar.”
Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi wurin Fir’auna, in kuma fitar da Isra’ilawa daga Masar?”
Sai Allah ya ce, “Zan kasance da tare kai. Wannan kuwa za tă zama alama a gare ka cewa Ni na aike ka. Bayan ka fitar da mutanen daga Masar, za ku yi sujada ga Allah a kan dutsen nan.”
Musa ya ce wa Allah, “A ce ma na tafi wurin Isra’ilawa na ce musu, ‘Allah na kakanninku ya aiko ni wurinku,’ in suka tambaye ni, ‘Mene ne sunansa?’ Me zan ce?”
Allah ya ce wa Musa, “NI NE wanda NINE. Abin da za ka faɗa wa Isra’ilawa ke nan cewa, ‘NI NE, ya aiko ni wurinku.’ ”
Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan.
“Tafi ka tattara dattawan Isra’ila, ka ce musu, ‘Ubangiji, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, ya bayyana a gare ni ya ce, Na lura da ku, na kuma ga abubuwan da ake yi muku a Masar. Na kuma yi alkawari, zan fitar da ku daga azabarku a Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasa mai zub da madara da zuma.’
“Dattawan Isra’ila za su saurare ka. Sa’an nan da kai da dattawan Isra’ila, za ku tafi wurin sarkin Masar, ku ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya sadu da mu. Bari mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin hamada domin mu yi hadaya wa Ubangiji Allahnmu.’ Amma na san cewa sarkin Masar ba zai yarda ku tafi ba, sai hannu mai ƙarfi ya tilasta shi. Saboda haka zan miƙa hannuna in bugi Masarawa da duk al’ajaban da zan aikata a cikinsu. Bayan haka zai bar ku, ku tafi.
“Zan kuma sa mutanen su sami tagomashi daga wurin Masarawa, saboda sa’ad da za ku fita, ba za ku fita hannu wofi ba. Kowace mace ta tambayi maƙwabciyarta, da kuma duk wata macen da take cikin gidanta, kayayyakin azurfa da na zinariya da kuma na riguna, waɗanda za ku sa wa ’ya’yanku maza da mata. Ta haka nan za ku washe Masarawa.”
Mu’ujizai domin Musa
Musa ya amsa ya ce, “In ba su gaskata ni ba, suka kuma ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba fa’?”
Sai Ubangiji ya ce, “Mene ne wannan a hannunka?”
Musa ya amsa ya ce, “Sanda.”
Sai Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.”
Musa ya jefa shi ƙasa, sai sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya gudu daga gare shi. Sai Ubangiji ya ce masa, “Sa hannunka ka ɗauke shi ta wutsiya.” Sai Musa ya miƙa hannu, ya kama macijin, macijin kuwa ya dawo sanda a hannunsa. Ubangiji ya ce, “Wannan zai sa su ba da gaskiya cewa Ubangiji, Allah na kakanninsu, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da kuma Allah da Yaƙub, ya bayyana gare ka.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Sa hannunka cikin rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, sa’ad da ya fitar da shi, sai hannun ya a kuturce fari fat, kamar ƙanƙara.
Sai Ubangiji ya ce, “Yanzu, mayar da hannunka a rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, da ya fitar da shi, sai hannun ya koma kamar sauran jikinsa.
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “In ba su gaskata ba, ko kuma ba su kula da mu’ujiza ta fari ba, wataƙila su gaskata da ta biyun. Amma in ba su gaskata mu’ujizan nan biyu ba, ko kuwa ba su saurare ka ba, sai ka ɗibo ruwa daga Nilu, ka zuba a busasshiyar ƙasa. Ruwan da ka ɗebo daga kogin zai zama jini a ƙasar.”
Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ni ban mai iya magana ba ne, ban taɓa iya ba, ko a yanzu ma, bayan ka yi magana da ni, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”
Ubangiji ya ce masa, “Wa ya ba mutum bakinsa? Wa yake maishe shi kurma ko bebe? Wa yake ba shi gani ko yă makanta shi? Ashe ba Ni Ubangiji ba ne? Yanzu tafi, zan taimake ka ka yi magana, zan kuma koya maka abin da za ka faɗa.”
Amma Musa ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka nemi wani ka aika.”
Sai Ubangiji ya yi fushi da Musa ya ce, “Ɗan’uwanka Haruna Balawe, ba ya nan ne? Na san ya iya magana. Ya riga ya kama hanya don yă sadu da kai, zai kuma yi farin ciki sa’ad da ya gan ka. Za ka yi masa magana. Ka kuma sa masa maganata a baki; zan kuma taimake ku magana, in koya muku abin da za ku yi. Zai yi magana da mutane a madadinka, zai zama kamar bakinka, kai kuwa kamar Allah a gare shi. Amma ka ɗauki wannan sanda a hannunka domin yă aikata mu’ujizan.”
Musa ya koma Masar
Sai Musa ya koma wurin Yetro surukinsa, ya ce masa, “Bari in koma wurin mutanena a Masar, in ga ko da mai rai a cikinsu.”
Yetro ya ce, “Tafi, ka kuma sauka lafiya.”
Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa a Midiyan, “Koma Masar, domin dukan mutanen da suke neman su kashe ka sun mutu.” Sai Musa ya ɗauki matarsa da ’ya’yansa maza, ya sa su a kan jaki, suka kama hanya zuwa Masar. Ya kuma ɗauki sandan Allah a hannunsa.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Bayan ka koma Masar, ka tabbata ka aikata dukan mu’ujizan da na sa cikin ikonka a gaban Fir’auna. Amma zan taurare zuciyarsa domin kada yă bar mutanen su tafi. Sa’an nan ka gaya wa Fir’auna, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce; Isra’ila shi ne ɗan farina, na gaya maka, “Ka bar ɗana yă tafi domin yă yi mini sujada.” Amma ka ƙi ka bari yă tafi, saboda haka zan kashe ɗan farinka.’ ”
Ya zama kuwa sa’ad da Musa yake masauki a kan hanya sai Ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi. Amma Ziffora ta ɗauki dutsen ƙanƙara mai ci, ta yanke loɓar ɗanta ta taɓa ƙafafun Musa da shi. Ta ce, “Tabbatacce kai angon jini ne a gare ni.” Sai Ubangiji ya ƙyale shi. (A lokacin ta ce “angon jini,” tana nufin kaciya.)
Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi cikin hamada ka sadu da Musa.” Sai ya sadu da Musa a dutsen Allah, ya sumbace shi. Sai Musa ya gaya wa Haruna dukan abin da Ubangiji ya aike yă faɗa, da kuma dukan mu’ujizan da ya umarce shi yă aikata.
Musa da Haruna suka tattara dukan dattawan Isra’ilawa, sai Haruna ya gaya musu dukan abin da Ubangiji ya ce wa Musa. Ya kuma aikata mu’ujizan a gaban mutanen, sai suka gaskata. Sa’ad da suka ji cewa Ubangiji ya damu da su, ya kuma ga azabarsu, sai suka durƙusa suka yi sujada.
Yin tubalai ba tare da an ba da bunnu ba
Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’ ”
Fir’auna ya ce, “Wane ne Ubangiji da zan yi biyayya da shi, har in bar Isra’ila su tafi? Ban san Ubangiji ba, kuma ba zan bar Isra’ila su tafi ba.”
Sai suka ce, “Allah na Ibraniyawa ya sadu da mu. Yanzu bari mu ɗauki tafiyar kwana uku cikin hamada domin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu, don kada yă buga mu da annoba ko takobi.”
Amma sarkin Masar ya ce wa, “Musa da Haruna, don me kuke hana mutane yin aikinsu? Ku koma wurin aikinku!” Sa’an nan Fir’auna ya ce, “Ga shi mutane sun yi yawa a ƙasar Masar, ku kuma yanzu kuna so ku hana su yin aiki.”
A wannan rana Fir’auna ya ba da wannan umarni wa shugabannin masu gandu, “Kada ku ƙara ba wa mutanen ciyawar tattaka domin su yi tubula, bari su tafi su tattara tattaka da kansu. Ku kuma bukace su su yi tubula daidai yawan tubalin da suka saba yi, kada ku rage. Ragwaye ne, shi ya sa suke kuka cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya ga Allahnmu.’ Ku sa waɗannan mutane su yi aiki mai tsanani sosai, don kada su sami zarafin kasa kunne ga maganganun ƙarya.”
Sai shugabannin masu aikin gandu suka fita suka gaya wa mutanen Isra’ila, “Ga abin da Fir’auna ya ce, ‘Ba zan ƙara ba ku tattaka ba. Ku tafi ku nemo wa kanku tattaka duk inda za ku samu, amma ba za a rage aikinku ba ko kaɗan.’ ” Saboda haka mutane suka warwatsu ko’ina a Masar domin tattara bunnun da za su yi amfani da su, maimakon tattaka. Shugabannin gandu suka dinga matsa musu suna cewa, “Ku cika aikin da aka bukace ku na kowace rana kamar yadda kuke yi sa’ad da kuke da tattaka.” Manyan Isra’ilawa waɗanda shugabannin gandun Fir’auna suka naɗa, suka sha dūka, aka kuma yi musu tambayoyi ana cewa, “Don me ba ku cika yawan tubula na jiya da na yau kamar yadda kuka saba ba?”
Sai manyan Isra’ila masu bi da aikin gandu suka tafi wurin Fir’auna suka yi roƙo suna cewa, “Don me kake yi wa bayinka haka? Ba a ba wa bayinka tattaka, duk da haka ana ce mana, ‘Ku yi tubula!’ Ana wa bayinka dūka, amma fa laifin na mutanenka ne.”
Fir’auna ya ce, “Ku ragwaye ne! Shi ya sa kuke cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya wa Ubangiji.’ Ku ɓace yanzu daga nan, ku koma wurin aikinku. Ba za a ba ku tattaka ba, kuma dole ku fid da tubula kamar yadda kuka saba.”
Manyan Isra’ilawa da suke bi da aikin gandu suka gane cewa sun shiga uku, sa’ad da aka gaya musu, “Ba za ku rage yawan tubulan da aka bukace ku ku yi na kowace rana ba.” Da suka bar Fir’auna, sai suka sadu da Musa da Haruna suna jira su sadu da su, sai suka ce, “Bari Ubangiji yă duba, yă kuma hukunta ku! Kun maishe mu abin ƙyama ga Fir’auna da bayinsa, kuka kuma sa musu takobi a hannunsu don su kashe mu.”
Allah ya yi alkawarin ceto
Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, don me ka kawo wahala a kan mutanen nan? Abin da ya sa ka aiko ni ke nan? Gama tun da na tafi wurin Fir’auna, na yi masa magana da sunanka, sai ya fara gasa wa mutanen nan azaba, ba ka kuma ceci mutanenka.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”
Allah ya kuma ce wa Musa, “Ni ne Ubangiji. Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku da kuma ga Yaƙub a matsayin Allah Maɗaukaki, amma sunan nan nawa Ubangiji, ban bayyana kaina a gare su ba. Na kuma kafa alkawari da su don in ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci. Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina.
“Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan ’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku. Zan ɗauke ku tamƙar mutanena, in kuma zama Allahnku. Sa’an nan za ku sani Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga wahalar Masarawa. Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’ ”
Musa ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne a gare shi ba, don ɓacin rai saboda tsananin aikin bauta.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Koma ka ce wa Fir’auna sarkin Masar, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa.”
Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “In Isra’ilawa ba su ji ni ba, yaya Fir’auna zai ji ni, da yake ina magana da ƙyar?”
Asalin iyalin Musa da Haruna
Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna game da Isra’ilawa da Fir’auna sarkin Masar, ya umarce su su fitar da Isra’ilawa daga Masar.
Waɗannan su ne shugabannin iyalansu.6.14 Ibraniyanci yana da iyalai ne a nan, aya 25 kuma yana kwatanta babbar ƙungiya fiye da dangi ne.
’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila su ne,
Hanok da Fallu, Hezron da Karmi.
Waɗannan su ne dangin Ruben.
’Ya’yan Simeyon maza su ne,
Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana.
Waɗannan su ne dangin Simeyon.
Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta,
Gershon, Kohat da Merari.
Lawi ya yi shekara 137.
’Ya’yan Gershon maza, bisa ga dangi su ne,
Libni da Shimeyi.
’Ya’yan Kohat maza, su ne,
Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
Kohat ya yi shekara 133.
’Ya’yan Merari maza, su ne,
Mali da Mushi.
Waɗannan su ne dangin Lawi bisa ga abin da aka rubuta.
Amram ya auri ’yar’uwar mahaifinsa Yokebed, wadda ta haifa masa Haruna da Musa.
Amram ya yi shekara 137.
’Ya’yan Izhar maza, su ne,
Kora, Nefeg da Zikri.
’Ya’yan Uzziyel maza, su ne,
Mishayel, Elzafan da Sitri.
Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.
’Ya’yan Kora maza, su ne,
Assir, Elkana da Abiyasaf.
Waɗannan su ne dangin Kora.
Eleyazar ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin ’yan matan Futiyel, sai ta haifa masa Finehas.
Waɗannan su ne shugabannin iyalan Lawi, dangi, dangi.
Wannan Haruna da Musa ne, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana ya ce, “Ku fitar da Isra’ilawa daga Masar ɓangare-ɓangare.” Su ne suka yi magana da Fir’auna sarkin Masar game da fitar da Isra’ilawa daga Masar, wannan Musa da Haruna.
Haruna zai yi magana a madadin Musa
Ana nan, sa’ad da Ubangiji ya yi magana da Musa a Masar, ya ce masa, “Ni ne Ubangiji. Sai ka faɗa wa Fir’auna sarkin Masar kome da na faɗa maka.”
Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, ina magana da ƙyar, ƙaƙa Fir’auna zai kasa kunne gare ni?”
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, na maishe ka kamar Allah ga Fir’auna, ɗan’uwanka Haruna kuma zai zama annabinka. Za ka faɗi kome da na umarce ka, ɗan’uwanka Haruna kuwa zai faɗa wa Fir’auna, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa. Amma zan taurare zuciyar Fir’auna, kuma ko da na ninka mu’ujizai da kuma alamu a Masar, ba zai saurare ku ba. Don haka zan miƙa hannuna a kan Masar, in murƙushe ta da bala’i iri-iri, bayan haka zan fitar da taron mutanen Isra’ila daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu girma. Masarawa kuwa za su san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na miƙa hannuna a kan Masar, na kuma fitar da Isra’ilawa daga gare ta.”
Musa da Haruna suka aikata yadda Ubangiji ya umarce su. Musa yana da shekara tamanin da haihuwa, Haruna kuma yana da shekara tamanin da uku, sa’ad da suka yi magana da Fir’auna.
Sandan Haruna ya zama Maciji
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Sa’ad da Fir’auna ya ce muku, ‘Aikata wani al’ajabi,’ sai ka ce wa Haruna, ‘Ɗauki sandanka ka jefa shi a ƙasa, a gaban Fir’auna,’ zai kuwa zama maciji.”
Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa ƙasa, a gaban Fir’auna da bayinsa, sai sandan ya zama maciji. Fir’auna kuwa ya kira masu hikima da masu sihiri, sai bokayen Masarawa ma suka yi irin abubuwan nan da bokancinsu. Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, ya kuwa zama maciji. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu. Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurare su ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.
Annobar jini
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Zuciyar Fir’auna taurariya ce, ya ƙi yă bar mutanen su tafi. Ka je wurin Fir’auna da safe, yayinda za shi kogi. Ka jira a bakin Nilu don ka sadu da shi, ka ɗauki sandan nan da ya canja zuwa maciji a hannunka. Sa’an nan ka ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya aiko ni in faɗa maka, Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada a hamada. Amma har yanzu ba ka yi biyayya ba. Ga abin da Ubangiji ya ce, da wannan za ka san cewa ni ne Ubangiji. Da sandan da yake hannuna zan bugi ruwan Nilu, zai kuma zama jini. Kifi a ciki Nilu za su mutu, ruwan kuma zai yi ɗoyi; Masarawa ba za su iya shan ruwansa ba.’ ”
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka ɗauki sandanka, ka miƙa hannunka kan ruwan Masar, kan kogunansu da rafuffukansu da kududdufansu da kuma dukan tafkunansu, za su zama jini.’ Jini zai kasance ko’ina a Masar, har ma a cikin abubuwan ajiyar ruwansu7.19 Ko kuwa har ma a kan gumakansu da aka yi da itace da kuma dutse.”
Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarta. Ya ɗaga sandansa a gaban Fir’auna da bayinsa, ya bugi ruwan Nilu, dukan ruwan kuwa ya zama jini. Kifin da suke cikin Nilu suka mutu, kogin kuwa ya yi wari sosai yadda Masarawa ba su iya shan ruwan ba. Jini ya bazu ko’ina a Masar.
Amma bokayen Masar ma suka yi abubuwan nan da sihirinsu, sai zuciyar Fir’auna ta taurare; bai saurari Musa da Haruna ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa. A maimakon yă saurara, sai ya juya ya koma fadarsa, bai ma damu da abin da aka yi ba. Sai dukan Masarawa suka yi ta tonon gefen Nilu don su sami ruwan sha, domin ba su iya shan ruwan kogin ba.
Annobar kwaɗi
Kwana bakwai suka wuce bayan da Ubangiji ya bugi kogin.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada. In ka ƙi barinsu, zan hore ka da annoban kwaɗi a dukan ƙasarka. Nilu zai cika da kwaɗi. Za su haura zuwa cikin fadanka da kan gadonka, cikin gidajen bayinka da kan mutanenka, cikin kwanonin toye-toyenka da na cin abincinka. Kwaɗin nan za su yi ta tsalle a kanka, da kan mutanenka, da kuma kan dukan bayinka.’ ”
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka miƙa hannunka da sandanka bisa koguna da rafuffuka da kuma kududdufai, ka sa kwaɗi su fito su mamaye ƙasar Masar.’ ”
Sai Haruna ya miƙa hannunsa bisa ruwan Masar, kwaɗi kuwa suka fito, suka mamaye ƙasar Masar. Amma bokaye ma suka yi abubuwan nan ta wurin sihirinsu; suka sa kwaɗi suka fito suka mamaye ƙasar Masar.
Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Yi addu’a ga Ubangiji yă ɗauke kwaɗi daga gare ni da mutanena, zan kuwa bar mutanenku su tafi su yi hadaya ga Ubangiji.”
Musa ya ce wa Fir’auna, “Na ba ka dama ka ba da lokacin da zan yi addu’a dominka da kuma bayinka da mutanenka, gidajenku kuwa za su rabu da kwaɗi, amma ban da waɗanda suke cikin Nilu.”
Fir’auna ya ce, “Gobe.”
Musa ya amsa, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani kamar Ubangiji, Allahnmu. Kwaɗin za su bar ka da gidajenka, bayinka da mutanenka; za su kasance a Nilu ne kaɗai.”
Bayan Musa da Haruna sun bar Fir’auna, Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji saboda kwaɗin da ya kawo a bisa Fir’auna. Sai Ubangiji ya yi abin da Musa ya nema. Kwaɗin suka mutu a gidaje, da filaye, da kuma gonaki. Aka jibga su tsibi-tsibi, ƙasar ta yi ɗoyi saboda su. Amma da Fir’auna ya ga an sami sauƙi, sai ya taurare, ya ƙi yă saurari Musa da Haruna kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.
Annobar ƙwari masu cizo
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Miƙa hannunka ka bugi ƙurar ƙasa,’ dukan ƙurar ƙasar Masar kuwa za tă zama ƙwari masu cizo.” Suka yi haka, da Haruna ya miƙa hannunsa da sandan, ya bugi ƙurar ƙasa, sai ƙwari masu cizo suka fito a kan mutane da dabbobi. Dukan ƙurar, ko’ina a ƙasar Masar ta zama cinnaku. Sa’ad da bokayen Fir’auna suka yi ƙoƙari yin sihiri iri na rufe ido domin su fito da kwari, sai suka kāsa.
Ƙwari masu cizo kuwa suka rufe mutane da dabbobi. Sai bokaye suka ce wa Fir’auna, “Wannan fa da hannun Allah a ciki.” Amma zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurara ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.
Annobar ƙudaje
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tashi da sassafe ka sadu da Fir’auna a lokacin da za shi kogi, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, bari mutanena su tafi, don su yi mini sujada. In ba ka bar mutanena suka tafi ba, zan turo da tarin ƙuda a kanka da bayinka, a kan mutanenka da cikin gidajenka. Gidajen Masarawa za su cika da ƙudaje, har ma da ƙasa inda za su taka.
“ ‘Amma zan keɓe yankin Goshen, inda mutanena suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, domin ka sani cewa Ni, Ubangiji, ina cikin wannan ƙasa. Zan sa iyaka tsakanin jama’ata da jama’arka. Gobe ne wannan mu’ujiza za tă auku.’ ”
Ubangiji kuwa ya yi haka. Tarin ƙuda suka zubo a fadar Fir’auna da cikin gidajen bayinsa, da ko’ina a Masar, ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.
Sai Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tafi, ku miƙa hadaya ga Allahnku, a nan a cikin ƙasar.”
Amma Musa ya ce, “Wannan ba zai yiwu ba. Hadayun da mukan miƙa wa Ubangiji, Allahnmu haram ne ga Masarawa. In kuwa muka miƙa hadayun da suke haram a idanunsu, ba za su jajjefe mu ba? Dole mu yi tafiya kwana uku cikin hamada domin miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnmu, yadda ya umarce mu.”
Fir’auna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, don ku miƙa hadayu ga Ubangiji Allahnku, a cikin hamada, amma ba za ku tafi da nisa ba. Yanzu ku yi mini addu’a.”
Musa ya amsa, “Da zarar na bar ka, zan yi addu’a ga Ubangiji, gobe kuwa ƙudaje za su bar Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa. Sai dai a tabbata Fir’auna bai sāke yin ruɗi ta wurin ƙin barin mutane su tafi su miƙa hadayu ga Ubangiji ba.”
Sa’an nan Musa ya rabu da Fir’auna, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya yi abin da Musa ya roƙa. Ƙudaje suka rabu da Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa; ba ƙudan da ya rage. Amma a wannan lokaci ma, Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai kuma bar mutanen suka tafi ba.
Annoba a kan dabbobi
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, “Ka bar mutanena su tafi, domin su yi mini sujada.” In ka ƙi ka bar su su tafi, kana ta riƙonsu, hannun Ubangiji zai kawo muguwar annoba a kan dabbobinka a gona, a kan dawakanka, da jakuna da raƙuma, da kuma a kan shanunka da tumaki da awaki. Amma Ubangiji zai raba tsakanin dabbobin Isra’ila da na Masar, saboda kada wata dabbar Isra’ilawa ta mutu.’ ”
Sai Ubangiji ya sa lokaci ya ce, “Gobe Ubangiji zai yi wannan a ƙasar.” Kashegari Ubangiji ya yi haka. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, amma babu dabba guda ta Isra’ilawan da ta mutu. Fir’auna ya aiki mutane su bincika, sai suka tarar babu dabba guda ta Isra’ilawan da ta mutu. Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa bar mutanen su tafi ba.
Annobar marurai
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ɗibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa tokar sama a gaban Fir’auna. Za tă zama ƙura bisa dukan ƙasar Masar, sai marurai masu zafi su fiffito bisa mutane da dabbobi a dukan ƙasar.”
Sai suka ɗibi tokar matoya, suka tsaya a gaban Fir’auna, Musa ya watsa ta a iska, sai marurai masu zafi suka fiffito bisa mutane da dabbobi. Bokaye suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran da suke bisansu da a kan dukan Masarawa. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa saurare Musa da Haruna ba kamar yadda Ubangiji ya riga ya ce wa Musa.
Annobar ƙanƙara
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka sadu da Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, Ka bar mutanena su tafi don su yi mini sujada, ko kuwa a wannan lokaci zan aika da cikakkiyar annoba mai ƙarfi a kanka da a kan fadawanka da mutanenka, domin ka san cewa ba kama da ni a dukan duniya. Gama da ni kaina na miƙa hannuna na buge ka da jama’arka da annoba, ai, da an hallaka ku a duniya ƙaƙaf. Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana yă zama abin darajantawa a dukan duniya. Har yanzu kana gāba da mutanena, ba ka kuma bar su su tafi ba. Saboda haka, gobe war haka, zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske, irin wadda Masar ba tă taɓa gani ba tun kahuwarta, har yă zuwa yanzu. Yanzu, ka ba da umarni a dawo da shanunku da kuma kome da kuke da shi wanda yake a gona zuwa gida, gama ƙanƙarar za tă kashe kowane mutum ko dabba wadda take a gona wadda ba a kawo cikin gida ba, sa’ad da ta fāɗo.’ ”
Waɗansu daga cikin dattawan Fir’auna suka cika da tsoro saboda abin da Ubangiji ya faɗa, nan da nan suka shigo da dabbobinsu da bayinsu da sauri daga gona zuwa cikin gida. Amma waɗanda ba su kula da maganar Ubangiji ba, suka bar bayinsu da dabbobi a gona.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa dukan Masar, a bisa mutane da dabbobi, da bisa dukan abubuwan da suke girma a gonakin Masar.” Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar; ƙanƙara ta fāɗo, walƙiya kuma tana ta wulƙawa. Wannan ce ƙanƙara mafi munin da aka taɓa yi, a dukan ƙasar Masar, tun tarihin kahuwarta na zaman al’umma. Ko’ina a Masar ƙanƙara ta bugi duk abin da yake a gonaki, mutane da dabbobi, ta bugi duk ganyaye da suke a gonaki, ta kuma ragargaza kowane itace. Wuri guda kaɗai da ba a yi ruwan ƙanƙara ba, shi ne yankin Goshen, inda Isra’ilawa suke.
Sai Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “A wannan karo na yi zunubi. Ubangiji, shi ne da gaskiya, ni da mutane mu ke da kuskure. Ku roƙi Ubangiji, yă tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.”
Musa ya amsa, “To, da kyau, da zarar na fita daga birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, tsawar za tă tsaya, ƙanƙarar kuma za tă daina, don ku sani cewa duniya ta Ubangiji ce. Amma na san cewa kai da fadawanka, har wa yau ba ku ji tsoron Ubangiji Allah ba tukuna.”
(Rama da sha’ir suka lalace, gama sha’ir ya riga ya nuna, rama kuwa tana fid da kai. Alkama da gero kam, ba a hallaka su ba, gama lokacin nunansu bai yi ba tukuna.)
Sai Musa ya tashi daga gaban Fir’auna, ya fita daga birni. Da ya miƙa hannuwansa ta wajen Ubangiji, sai tsawa da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke. Da Fir’auna ya ga cewa ruwa da ƙanƙara da tsawa sun daina, sai ya sāke yin zunubi. Shi da fadawansa, suka taurare zukatansu. Ta haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa bar Isra’ilawa suka tafi ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa ta wurin Musa.
Annobar fāra
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu, don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”
Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada. In ka ƙi ka bari su tafi, gobe zan aiko da fāra a ƙasarka. Za su rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za su cinye ɗan sauran abin da ya rage muku daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a gonakinku. Za su cika gidajenka, da na fadawanka, da na dukan Masarawa, abin da iyayenka da kakanninka ba su taɓa gani ba, tun daga ranar da suka sami kansu a duniya, har yă zuwa yau.’ ” Sa’an nan Musa ya juya, ya rabu da Fir’auna.
Fadawan Fir’auna suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai zama mana tarko? Ka bar mutanen su tafi domin su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Har yanzu ba ka san cewa Masar ta lalace ba?”
Sa’an nan aka dawo da Musa da Haruna wurin Fir’auna. Sai ya ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?”
Musa ya amsa, “Za mu tafi tare da ƙanananmu, da tsofaffinmu, da ’ya’yanmu maza da mata, da kuma garkunanmu na shanu da tumaki, gama dole ne mu yi bikin ga Ubangiji.”
Fir’auna ya ce, “Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba! A fili yake kuna da niyyar mugunta. Sam! Wannan ba zai taɓa yiwu ba, sai ko maza kaɗai su tafi su yi wa Ubangiji sujada, gama abin da kuke so ke nan.” Sa’an nan aka kori Musa da Haruna daga gaban Fir’auna.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka a bisa Masar domin fāra su sauko bisa ƙasar, su ci duk abin da yake girma a gonaki, duk abin da ƙanƙara ta rage.”
Saboda haka Musa ya miƙa sandansa bisa Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a kan ƙasar dukan dare da kuma dukan yini. Da safe kuwa iskar ta kawo fāra; suka mamaye ƙasar duka, suka sauka a ko’ina a ƙasar. Ba a taɓa ganin annobar fāra haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin fāra kamar haka ba. Suka rufe ƙasar har ta zama baƙi. Suka cinye abin da ƙanƙara ta rage, kowane tsiron da yake girma a gonaki, da dukan ’ya’yan itatuwa. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.
Fir’auna ya kira Musa da Haruna da gaggawa ya ce, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku. Yanzu ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yă ɗauke wannan muguwar annoba daga gare ni.”
Sai Musa ya bar Fir’auna ya kuma yi addu’a ga Ubangiji. Sai Ubangiji ya canja iska zuwa iska mai ƙarfi ta yamma wadda ta ɗibi fārar zuwa Jan Teku. Babu fāran da suka rage a wani wuri a Masar. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa suka tafi ba.
Annobar duhu
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama domin a yi duhu a bisa Masar, duhun da za a iya taɓawa.” Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuma yi duhu baƙi ƙirin bisa dukan ƙasar Masar na kwana uku. Ba wanda ya iya gani wani ko yă bar wurinsa na kwana uku. Amma dukan Isra’ilawa sun kasance da haske a inda suke zama.
Sai Fir’auna ya aika aka kira Musa, ya kuma ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji sujada. Matanku da yaranku ma za su iya tafiya tare da ku; sai dai ku bar garkunanku na shanu da tumaki.”
Amma Musa ya ce, “Dole ka bari mu kasance da hadayu, da kuma hadayu na ƙonawa waɗanda za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu. Dole dabbobinmu ma su tafi tare da mu; ko kofato ma, ba za a bari a baya ba. A cikinsu ne za mu ɗibi abin da za mu yi wa Ubangiji Allahnmu sujada. Ba mu kuma san irin abin da za mu miƙa wa Ubangiji ba, sai mun kai can.”
Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, har bai yarda yă sake su ba. Fir’auna ya ce wa Musa, “Fita, ka ba ni wuri! Ka mai da hankali, kada ka ƙara bayyana a gabana, gama ran da ka sāke ganin fuskata, a ran nan za ka mutu.”
Musa ya amsa, “Madalla, kamar yadda ka faɗa, ba zan ƙara bayyana a gabanka ba.”
Annoba a kan ɗan fari
To, fa, sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan ƙara kawo annoba guda a kan Fir’auna da kan Masar. Bayan haka, zai bar ku, ku fita daga nan. Sa’ad da ya yi haka kuwa, zai kore ku gaba ɗaya. Ka faɗa wa mutane cewa dukan maza da mata, su roƙi maƙwabtansu kayan azurfa da na zinariya.” (Ubangiji ya sa mutane suka sami tagomashi a idon Masarawa, Musa kuwa ya sami girma sosai a cikin ƙasar Masar a gaban fadawan Fir’auna da kuma a gaban jama’ar.)
Saboda haka Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Wajen tsakar dare, zan ratsa dukan Masar. Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan ’yan farin shanu. Za a yi kuka mai zafi ko’ina a Masar, irin wadda ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a ƙara yi ba. Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila. Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir’auna zai ƙi kasa kunne gare ka, sai na ƙara aikata waɗansu mu’ujizai cikin Masar.” Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu’ujizai a gaban Fir’auna, amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa ba.
Bikin Ƙetarewa
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna a Masar, “Wannan wata za tă zama a gare ku wata na farko, wata na fari na shekararku. Ka faɗa wa dukan jama’ar Isra’ila cewa a rana ta goma ga wannan wata, kowane mutum zai ɗauki ɗan rago domin iyalinsa, ɗaya domin kowane gida. In akwai wani gidan da ba za su iya cinye rago guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki rago guda gwargwadon yawansu, bisa ga abin da mutum guda zai ci. Dabbobin da za ku zaɓa, dole su zama bana ɗaya, namiji marar tabo, za ku kuma kamo su daga cikin tumaki ko awaki. Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato, sa’ad da dukan taron jama’ar Isra’ila za su yanka ragunansu da yamma. Sa’an nan za su ɗauki jinin, su shafa a gefen da yake saman dogaran ƙofa na gidajen da suke cin naman dabbobin. A wannan dare, za su gasa naman, su ci da ganyaye masu ɗaci, da kuma burodi marar yisti. Kada ku ci nama ɗanye, ko kuma dafaffe, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kuma kayan cikin. Kada ku bar kome yă kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi. Ga yadda za ku ci shi, ku yi ɗamara, takalma kuwa a ƙafafunku, kuna riƙe da sandunan tafiya a hannunku. Ku ci shi da gaggawa; Bikin Ƙetarewa ne na Ubangiji.
“A wannan dare, zan ratsa Masar, in bugi kowane ɗan fari, na mutum da na dabba, zan kuma hukunta dukan gumakan Masar. Ni ne Ubangiji. Jinin zai zama alama a gare ku, a gidajen da kuke; sa’ad da kuwa na ga jinin, zan ƙetare ku. Ba wata annoba mai hallakarwa da za tă taɓa ku yayinda na bugi Masar.
“Wannan rana za tă zama muku abin tunawa dukan zamananku masu zuwa, za ku kiyaye ta kamar biki ga Ubangiji, dawwammamiyar farilla ce har abada. Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti. A rana ta fari, za ku fid da yisti daga gidajenku gama duk wanda ya ci abu mai yisti daga rana ta fari har zuwa rana ta bakwai, za a fid da shi daga Isra’ila. A rana ta fari, za ku yi taro mai tsarki, haka kuma za ku sāke yi a rana ta bakwai. Kada ku yi aiki a waɗannan ranaku, sai dai ku shirya abinci domin kowa, abin da za ku yi ke nan kawai.
“Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti domin a wannan rana ce na fitar da ku ɓangare-ɓangare daga Masar. Ku kiyaye wannan rana ta zama muku dawwammamiyar farilla wa tsara masu zuwa. A wata na fari, za ku ci burodi marar yisti daga yammancin ranar goma sha huɗu har zuwa yammancin ranar ashirin da ɗaya. Kada a sami yisti a gidajenku har kwana bakwai. Kuma duk wanda ya ci wani abu mai yisti, za a fid da shi daga taron jama’ar Isra’ila, ko baƙo ne, ko haifaffen ɗan ƙasa. Kada ku ci wani abincin da aka yi da yisti. Ko’ina kuka zauna, dole ku ci burodi marar yisti.”
Sa’an nan Musa ya kira dukan dattawan Isra’ila ya ce musu, “Ku je da sauri ku zaɓi dabbobin iyalanku, ku yanka ragon Bikin Ƙetarewa. Ku ɗauki ƙunshin itacen hizzob, ku tsoma cikin jinin da yake a kwano, ku yayyafa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada wani daga cikinku yă fita daga ƙofar gidansa sai da safe. Sa’ad da Ubangiji yake ratsa ƙasar don yă bugi Masarawa, zai ga jinin a bisa da kuma gefen madogaran ƙofa, zai ƙetare ƙofar, ba zai bar mai hallakawa yă shiga gidajenku, yă buge ku ba.
“Ku kiyaye waɗannan dokokin a matsayin dawwammamiyar farilla, da ku da ’ya’yanku har abada. Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku yadda ya alkawarta, ku kiyaye wannan biki. Sa’ad da kuma ’ya’yanku suka tambaye ku, ‘Mece ce manufar wannan biki?’ Sai ku faɗa musu, ‘Hadaya ce ta Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.’ ” Sai mutane suka rusuna, suka yi sujada. Isra’ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.
Da tsakar dare, sai Ubangiji ya karkashe dukan ’ya’yan fari a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato, magājinsa, har zuwa ɗan fari na ɗan sarƙa da yake kurkuku, har da ’ya’yan fari na dabbobi. Fir’auna da dukan fadawansa da kuma dukan Masarawa, suka tashi a cikin daren da kuka mai zafi, aka kuma ji kukan a ko’ina a cikin ƙasar Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.
Fitowa
A cikin daren, Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tashi, ku da jama’arku, ku fita daga cikin jama’ata. Ku tafi, ku bauta wa Ubangiji yadda kuka ce. Ku kwashi garkunanku na tumaki da na awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.”
Masarawa suka matsa wa Isra’ilawa su fita daga ƙasarsu da sauri. Gama mutanen Masar sun ce, “Ai, za mu mutu duka, in ba su tafi ba!” Sai mutanen suka ɗauki garin da sun kwaɓa ba yisti a ciki, tare da ƙwaryansu na aikin kwaɓan, suka nannaɗe su a mayafansu, suka rataye a kafaɗunsu. Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya umarce su, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi. Ubangiji kuwa ya sa Isra’ilawa suka yi farin jini a wurin Masarawa, Masarawa kuma suka saki hannu wa mutanen, suka ba su duk abin da suka roƙa; ta haka Isra’ilawa suka washe Masarawa.
Isra’ilawa suka kama tafiya daga Rameses zuwa Sukkot. Akwai maza dubu ɗari shida da suke tafiya da ƙafa, ban da mata da yara. Waɗansu mutane da yawa da ba Isra’ilawa ba, suka haura tare da su, da garkunan shanu, da na tumaki da awaki. Suka toya burodi marar yisti da garin da aka kwaɓa wanda suka kawo daga Masar. Garin da aka kwaɓan ba shi da yisti, domin an kore su daga Masar, ba su kuwa sami damar shirya wa kansu abinci ba.
Zaman da Isra’ilawa suka yi a Masar, ya kai shekara 430. A ranar da shekara 430 ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan ɓangare-ɓangare na mutanen Ubangiji suka bar Masar. Gama Ubangiji ya yi tsaro a wannan dare, domin yă fitar da su daga Masar, a wannan dare, dole dukan Isra’ilawa su yi tsaro, don su girmama Ubangiji, cikin dukan tsararraki masu zuwa.
Abubuwan da Bikin Ƙetarewa ya hana
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Waɗannan ne ƙa’idodin Bikin Ƙetarewa.
“Ba baƙon da zai ci shi. Duk bawan da kuka sayo, yana iya ci, in dai an yi masa kaciya, amma wanda ba ya zama tare da ku na ɗinɗinɗin, da kuma wanda aka ɗauki hayansa, ba zai ci ba.
“Dole a ci shi a cikin gida ɗaya; kada a kai naman waje. Kada a karya wani daga ƙasusuwansa. Dole dukan taron jama’ar Isra’ila su yi bikin.
“Baƙon da yake zama tare da ku da yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi wa dukan mazan da suke cikin gidansa kaciya; sa’an nan ne zai iya yin abubuwa kamar haifaffen ɗan ƙasa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta shafi ɗan ƙasa da kuma baƙon da yake zama a tsakaninku.”
Dukan Isra’ilawa suka yi na’am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna. A wannan rana, Ubangiji ya fito da Isra’ilawa ɓangare-ɓangare daga Masar.
Keɓewar ɗan fari
Ubangiji ya ce wa Musa, “Keɓe mini kowane ɗan fari. Ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa a cikin Isra’ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”
Sai Musa ya ce wa mutane, “Ku tuna da wannan rana, ranar da kuka fito daga Masar, daga ƙasar bauta, gama Ubangiji ya fito da ku da hannu mai iko. Kada ku ci wani abin da yake da yisti. A wannan rana kuka fita, wato, a watan Abib. Sa’ad da Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku, ƙasar da take zub da madara da zuma, za ku kiyaye wannan biki a wannan wata. Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, a kan rana ta bakwai kuma za ku yi biki ga Ubangiji. Ku ci burodi marar yisti cikin kwana bakwai; kada a sami wani abu mai yisti a cikinku, ko a sami yisti a ko’ina a wurinku. A ranan nan kowa zai faɗa wa ɗanka, ‘Ina yin haka saboda abin da Ubangiji ya yi mini, sa’ad da na fita daga Masar.’ Wannan abin tunawa zai zama muku alama a hannunku, da kuma a goshinku cewa dokar Ubangiji tana a bakinku. Gama Ubangiji ya fitar da ku daga Masar da hannu mai iko. Dole ku kiyaye wannan farilla kowace shekara a lokacinta.
“Bayan Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, ya kuma ba da ita yadda ya alkawarta muku da rantsuwa, ku da kakanninku, sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Duk ɗan farin dabbobinku na Ubangiji ne. Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. In kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Sai ku fanshe kowane ɗan farin daga cikin ’ya’yanku.
“A kwanaki masu zuwa, in ɗanka ya tambaye ka, ‘Mene ne manufar wannan?’ Ka faɗa masa cewa, ‘Da hannu mai iko Ubangiji ya fito da mu daga Masar, daga ƙasar bauta. Sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, sai Ubangiji ya kashe dukan ’ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba, gaba ɗaya. Domin haka nake yin hadaya ga Ubangiji da ’ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma nakan fanshi dukan ’ya’yan farina maza.’ Za tă kuma zama alama a hannunku da kuma shaida a goshinku cewa Ubangiji ya fito da mu daga Masar da hannunsa mai iko.”
Ƙetarewar teku
Sa’ad da Fir’auna ya bar mutane su tafi, Allah bai bi da su a hanyar da ta bi ta iyakar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ce ta fi kusa. Gama Allah ya ce, “In suka fuskanci yaƙi, wataƙila su canja ra’ayinsu su koma Masar.” Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi.
Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yusuf tare da shi, gama Yusuf ya sa Isra’ilawa su rantse masa. Ya ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, sai ku ɗibi ƙasusuwana tare da ku daga wannan wuri.”13.19 Dubi Far 50.25.
Bayan sun bar Sukkot sai suka kafa sansani a Etam a bakin hamada. Da rana Ubangiji yakan ja gabansu a cikin al’amudin girgije domin yă bishe su a kan hanyarsu, da dare kuma a cikin al’amudin wuta domin yă ba su haske, domin su iya tafiya dare da rana. Al’amudan nan biyu, na girgije da na wuta, ba su daina yi wa jama’a jagora ba.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, su juya su kafa sansani a Fi Hahirot, a tsakanin Migdol da teku. Za su kafa sansanin kai tsaye kusa da teku, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon. Fir’auna zai yi tsammani, ‘Aha, Isra’ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta yimƙe su.’ Zan kuma taurare zuciyar Fir’auna, zai kuwa bi su. Na shirya wannan domin in nuna ɗaukakata a bisa Fir’auna da ƙungiyar sojansa. Bayan wannan, mutanen Masar za su sani ni ne Ubangiji.” Sai Isra’ilawa suka yi haka.
Sa’ad da aka faɗa wa Fir’auna cewa Isra’ilawa sun gudu, sai Fir’auna da bayinsa suka canja ra’ayinsu game da su, suka ce, “Me muka yi? Mun bar Isra’ilawa suka tafi, mun kuwa rasa hidimarsu!” Sai shi da keken yaƙinsa suka shirya, ya kuma ɗauki sojojinsa tare da shi. Ya ɗauki kekunan yaƙi ɗari shida mafi kyau duka, tare da duk sauran keken yaƙin Masar, da shugabanni kuma a kan dukansu. Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna sarkin Masar, domin yă bi Isra’ilawa waɗanda suke tafiya ba tsoro. Masarawa, dukan dawakan Fir’auna da kekunan yaƙi da mahaya da sojoji, suka bi Isra’ilawa suka cin musu yayinda suke a sansani kusa da teku kurkusa da Fi Hahirot, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.
Da Fir’auna ya yi kusa, Isra’ilawa suka ɗaga idanu sai suka hange Masarawa daga nesa suna tā da ƙura suna zuwa. Sai suka tsorata ƙwarai, suka kuwa yi kuka ga Ubangiji. Suka ce wa Musa, “Don babu makabarta a Masar ne, ka kawo mu a hamada mu mutu? Me ka yi mana ke nan da ka fitar da mu daga Masar? Ba mu faɗa maka a Masar ba, cewa ‘Ka bar mu mu bauta wa Masarawa’? Ai, da ya fi mana mu bauta wa Masarawa, da a ce mu mutu a hamada!”
Musa ya amsa wa mutane ya ce, “Kada ku ji tsoro. Ku tsaya dai ku ga ceton da Ubangiji zai kawo muku yau. Masarawan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba. Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Don me kake mini kuka? Ka faɗa wa Isra’ilawa su ci gaba da tafiya. Ka ɗaga sandanka, ka miƙa shi bisa teku don ruwa yă rabu domin Isra’ilawa su wuce cikin teku a kan busasshiyar ƙasa. Zan taurare zukatan Masarawa su shiga don su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir’auna da rundunansa, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa. Masarawa za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na sami nasara bisa kan Fir’auna, da keken yaƙinsa, da mahayan dawakansa.”
Sai mala’ikan Allah wanda yake tafiya a gaban sojojin Isra’ila, ya janye, ya koma bayansu. Al’amudin girgije shi ma ya koma, ya tsaya a bayansu, ya dawo tsakanin sojojin Masar da na Isra’ila. Duk dare, girgijen ya jawo duhu ga gefe ɗaya, haske kuma ga ɗaya gefen; saboda haka ba wanda ya kusaci wani duk dare.
Da Musa ya miƙa hannunsa a bisa teku, sai Ubangiji ya tura teku baya da iskar gabas mai ƙarfi duk dare, ya maishe shi busasshiyar ƙasa. Ruwa ya rabu, sai Isra’ilawa suka wuce cikin teku a kan busasshiyar ƙasa, ruwan ya zama musu katanga dama da hagu.
Masarawa suka bi su da dukan dawakan Fir’auna, da kekunan yaƙi, da mahayan, suka bi su cikin teku. Da asubahin fāri, sai Ubangiji ya dubi ƙasa a kan sojojin Masarawa daga al’amudin wuta da kuma girgije, sai ya sa suka ruɗe. Ya sa ƙafafun keken yaƙinsu suka fita don su kāsa tuƙi. Sai Masarawa suka ce, “Bari mu gudu daga Isra’ilawa gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masar.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa teku don ruwa yă koma kan Masarawa, da keken yaƙinsu, da kuma mahayansu.” Musa ya miƙa hannunsa a bisa tekun, da wayewar gari kuwa teku ya koma wurinsa na dā. Masarawa suka yi ƙoƙari su gudu, sai Ubangiji ya tura su cikin teku. Ruwan ya komo ya rufe keken yaƙin da mahayan, dukan sojojin Fir’aunan da suka bi bayan Isra’ilawa cikin teku, ba ko ɗaya da ya tsira.
Amma Isra’ilawa suka wuce cikin teku a busasshiyar ƙasa, ruwa kuwa ya yi musu katanga dama da hagu. A rana nan Ubangiji ya cece Isra’ila daga hannuwan Masarawa, Isra’ilawa kuwa suka ga gawawwakin Masarawa a bakin teku. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga iko mai girma da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa, sai mutanen suka ji tsoron Ubangiji, suka amince da shi, da kuma bawansa Musa.
Waƙar Musa da Miriyam
Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,
“Zan rera waƙa ga Ubangiji
gama an ɗaukaka shi ƙwarai.
Doki da mahayinsa
ya jefa su cikin teku.
“Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,
ya zama cetona.
Shi Allahna ne, zan yabe shi.
Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.
Ubangiji mai yaƙi ne
Ubangiji ne sunansa.
Karusan Fir’auna da sojojinsa
ya jefa cikin teku.
Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.
Zurfafan ruwaye sun rufe su;
suka nutse cikin zurfi kamar dutse.
Hannun damanka, ya Ubangiji,
Mai kwarjini ne da iko,
hannun damanka, ya Ubangiji,
ya farfashe magabci.
“A cikin girman kwarjininka
ka kā da waɗanda sun yi gāba da kai.
Ka aiki fushinka mai zafi
ya cinye su kamar tattaka.
Da hucin numfashin hancinka
ruwaye suka tattaru.
Ruwaye masu kwararowa, suka tsaya kamar bango;
ruwaye na zurfafa suka daskare a tsakiyar teku.
Magabci ya yi fahariya, cewa
‘Zan fafare su, in ci musu.
Zan raba ganima;
abin da na so ya samu.
Zan ja takobina
hannuna kuwa zai hallaka su.’
Amma ka hura numfashinka
sai teku ya rufe su.
Suka nutse kamar darma
cikin manyan ruwaye.
Wane ne cikin alloli,
ya yi kamar ka, ya Ubangiji?
Wane ne kamar ka,
mai ɗaukaka cikin tsarki,
mai banrazana cikin ɗaukaka,
mai aikata al’ajabai?
“Ka miƙa hannunka na dama,
ƙasa ta haɗiye abokan gābanka.
A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe
mutanen da ka fansa.
A cikin ƙarfinka, za ka bishe su
zuwa mazauninka mai tsarki.
Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki
tsoro zai kama mutanen Filistiya.
Sarakunan Edom za su tsorata,
shugabannin Mowab za su yi rawar jiki,
mutanen Kan’ana za su narke.
Razana da tsoro za su fāɗo a kansu.
Da ikon hannunka
za su tsaya cik kamar dutse,
har sai mutanen da ka kawo sun wuce, ya Ubangiji.
Za ka kawo su, ka dasa su
a kan dutsen nan naka
inda, ya Ubangiji, ka shirya domin mazauninka,
wuri mai tsarkin da hannuwanka suka kafa, ya Ubangiji.
“Ubangiji zai yi mulki
har abada abadin.”
Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa. Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa. Miriyam ta yi musu waƙa.
“Ku rera ga Ubangiji
gama ya ci gawurtacciyar nasara.
Doki da mahayi,
ya jefa cikin teku.”
Ruwayen Mara da Elim
Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba. Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara). Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?”
Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi.
A can Ubangiji ya yi musu doka da farilla, a can kuma ya gwada su. Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”
Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.
Manna da makware
Dukan taron Isra’ila suka tashi daga Elim suka zo hamadar Sin, wadda take tsakanin Elim da Sinai, a rana ta goma sha biyar ga wata biyu, bayan sun fito daga Masar. A hamadan, dukan taro suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna. Isra’ilawa suka ce musu, “Da ma a hannun Ubangiji ne muka mutu a Masar, inda muka zauna kewaye da tukwanen nama, muna cin duk abincin da muke so, amma kun kawo mu cikin wannan hamada don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan zubo muku burodi kamar ruwa daga sama. Mutanen za su fita kowace rana su tattara abin da zai ishe su na ranan. Ta haka zan gwada su in ga ko za su bi umarnaina. A rana ta shida za su shirya abin da suka kwaso, wannan kuwa zai zama ninki biyu na abin da sukan tattara na sauran ranaku.”
Saboda haka Musa da Haruna suka ce wa dukan Isra’ila, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fitar da ku daga Masar. Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, saboda ya ji gunaguninku a kansa. Wane mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?” Musa ya kuma ce, “Za ku san cewa shi ne Ubangiji, sa’ad da ya ba ku nama ku ci da yamma, da kuma duk burodin da kuke so da safe, saboda ya ji gunagunin da kuka yi a kansa. Namu a wane? Ai, gunaguninku ba a kanmu ba, amma a kan Ubangiji ne.”
Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka faɗa wa dukan taron Isra’ila, ‘Ku zo gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninku.’ ”
Yayinda Haruna yake magana da dukan taron Isra’ila, sai suka duba wajen hamada, sai ga ɗaukakar Ubangiji tana bayyana a girgije.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, ‘A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”
Da yamman wannan rana, sai makware suka rufe dukan sansani, da safe kuma sai ga raɓa ta kewaye sansani. Lokacin da raɓar ta watse, sai ga wani abu kamar tsaki, falle-falle kuma da laushi, fari, kamar hazo, a ƙasa. Sa’ad da Isra’ilawa suka ga wannan, sai suka ce wa junansu, “Mene ne wannan?” Gama ba su san ko mene ne ba.
Musa ya ce musu, “Wannan shi ne burodin da Ubangiji ya ba ku ku ci. Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Kowane mutum zai tattara bisa ga bukatarsa. Ku tara rabin gallon don mutum guda da yake cikin tentinku.’ ”
Isra’ilawa suka yi kamar yadda aka faɗa musu, waɗansu suka tattara da yawa, waɗansu kuma kaɗan. Da suka gwada a mudu, wanda ya tattara da yawa bai sami mafi yawa ba, wanda kuma ya tattara kaɗan bai sami ƙanƙani ba. Kowane mutum ya tattara daidai bukatarsa.
Sa’an nan Musa ya ce musu, “Kada wani yă bar saura har safe.”
Duk da haka waɗansu ba su kula da umarnin Musa ba, suka bar saura har safe, kashegari kuwa ta yi tsutsotsi, ta ruɓe, sai Musa ya yi fushi da su.
Kowace safiya, kowanne mutum yakan tattara daidai bukatarsa, lokacin da rana ta yi zafi, sai ta narke. A rana ta shida, suka tattara ninki biyu, mudu biyu ga mutum guda, sai shugabannin taron suka zo suka kawo ƙara wurin Musa. Shi kuma ya ce musu, “Wannan shi ne umarnin Ubangiji, ‘Gobe za tă zama ranar hutu, Asabbaci mai tsarki ga Ubangiji. Domin haka sai ku toya abin da kuke so ku toya, ku kuma dafa abin da kuke so ku dafa. Abin da ya rage ku ajiye har safe.’ ”
Sai suka bar saura har safe, kamar yadda Musa ya umarta, bai kuwa yi wari ko yă yi tsutsa ba. Musa ya ce, “Ku ci shi yau, saboda yau Asabbaci ne na Ubangiji. Ba za ku same shi a ƙasa a yau ba. Kwana shida za ku tattara shi, amma a rana ta bakwai, Asabbaci, ba za a same shi ba.”
Duk da haka waɗansu mutane suka fita a ranar Asabbaci don su tattara, amma ba su sami kome ba. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe za ku ƙi bin dokokina da umarnaina? Ku lura fa, ai, Ubangiji ne ya ba ku Asabbaci; shi ya sa a kan ba ku burodi na kwana biyu, a rana ta shida. Kowa ya kamata yă kasance inda yake a rana ta bakwai; kada kowa yă fita.” Sai mutanen suka huta a rana ta bakwai.
Mutanen Isra’ila suka kira burodin Manna. Manna yana nan fari kamar farin riɗi, ɗanɗanonsa kuma yana kama da masa da aka yi da zuma. Musa ya ce, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Ku auna mudu guda na Manna, a adana ta dukan zamananku, domin kowane zamani yă ga irin abincin da na ba ku ku ci a hamada, yayinda na fitar da ku daga Masar.’ ”
Saboda haka Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki tulu, ka sa mudu guda na Manna a ciki. Sa’an nan ka sa shi a gaban Ubangiji, don a adana don tsararraki masu zuwa.”
Sai Haruna ya ajiye Mannar a gaban Akwatin Alkawari, don a adana ta kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa. Isra’ilawa suka yi shekaru arba’in suna cin Manna, har sai da suka shiga cikin ƙasar da take da mutane, suka ci Manna har zuwa kan iyakar ƙasar Kan’ana.
(Omer guda, daidai ne da kashi ɗaya bisa goma na Efa.)
Ruwa daga dutse
Dukan taron Isra’ilawa suka kama tafiya daga Hamadar Sin, suka yi ta tafiya suna sauka a wurare dabam-dabam bisa ga umarnin Ubangiji. A ƙarshe suka sauka a Refidim, suka zauna a can, amma ba ruwan da jama’a za su sha. Saboda haka suka yi wa Musa maganganun banza suka ce, “Ba mu ruwa mu sha.”
Musa ya amsa ya ce, “Don me kuke mini maganganun banza? Don me kuke gwada Ubangiji?”
Amma mutanen suka yi fama da ƙishirwa a can, suka yi gunaguni a kan Musa. Suka ce, “Don me ka fitar da mu daga Masar, ka sa mu da ’ya’yanmu da dabbobinmu, mu mutu da ƙishirwa?”
Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Me zan yi da wannan jama’a? Suna shiri su jajjefe ni da duwatsu.”
Ubangiji amsa wa Musa, “Ka ɗauki sandan da ka bugi ruwan Nilu da shi. Ka kira waɗansu shugabannin Isra’ila, ku wuce a gaban jama’ar. Zan tsaya a can a gabanka, kusa da dutsen Horeb. Ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito daga gare shi domin mutane su sha.” Sai Musa ya yi haka a idon dattawan Isra’ila. Sai suka ba wa wurin suna, Massa da Meriba, saboda Isra’ilawa sun yi jayayya, suka kuma gwada Ubangiji cewa, “Ubangiji yana tsakaninmu ko babu?”
An ci Amalekawa da yaƙi
Amalekawa suka zo, suka yaƙi Isra’ilawa a Refidim. Musa ya ce wa Yoshuwa, “Zaɓi waɗansu mazanmu, ka je ka yaƙi Amalekawa. Gobe zan tsaya a bisa tudu, da sandan Allah a hannuwana.”
Sai Yoshuwa ya yaƙi Amalekawa kamar yadda Musa ya umarta, Musa, Haruna da Hur kuwa suka tafi bisa tudu. Muddin hannun Musa yana a miƙe, sai Isra’ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara. Sa’ad da hannuwan Musa suka gaji, sai Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka sa ya zauna a kai. Sa’an nan su kuma suka tsaya gefe da gefe, suna riƙe da hannuwansa har fāɗuwar rana. Sai Yoshuwa kuwa ya ci nasara a kan Amalekawa da takobi.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta wannan a cikin littafi, yă zama abin tuni, ka kuma faɗa wa Yoshuwa zan hallaka Amalekawa ƙaƙaf daga duniya.”
Musa ya gina bagade, sai ya kira shi Ubangiji shi ne Tutata. Ya ce, “Gama an ɗaga hannuwa sama zuwa kursiyin Ubangiji, Ubangiji zai yaƙi Amalekawa daga tsara zuwa tsara.”
Yetro ya ziyarci Musa
Ana nan sai Yetro firist na Midiyan, kuma surukin Musa, ya ji duk abin da Allah ya yi wa Musa da mutanensa Isra’ila, da kuma yadda Ubangiji ya fitar da Isra’ila daga Masar.
Bayan da Musa ya tura matarsa Ziffora gida, sai surukinsa Yetro ya karɓe ta da ’ya’yanta biyu maza. Ana kira ɗaya Gershom, domin Musa ya ce, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa”; ɗayan kuma Eliyezer, domin ya ce, “Allah mahaifina ya taimake ni ya cece ni daga takobin Fir’auna.”
Yetro surukin Musa tare da ’ya’yan Musa da matarsa suka zo wurin Musa a hamada, inda suka kafa sansani kusa da dutsen Allah Yetro ya riga ya aika wa Musa cewa, “Ni surukinka Yetro, ina zuwa wurinka tare da matarka da ’ya’yanka maza biyu.”
Sai Musa ya tafi yă taryi surukinsa, ya sunkuya ya yi masa sumba. Suka gai da juna, sa’an nan suka shiga tenti. Musa kuwa ya faɗa wa surukinsa duk abubuwan da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da Masarawa domin Isra’ila, da batun wahalolin da suka sha a hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.
Yetro ya yi murna da jin duk abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi wa Isra’ila, wajen cetonsu daga hannun Masarawa. “Yabo ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da na Fir’auna, wanda kuma ya cece mutanensa daga hannun Masarawa. Yanzu na san cewa Ubangiji ya fi kowane allah, gama ya yi wannan ga masu girman kai da kuma waɗanda suka wulaƙanta Isra’ila.” Sa’an nan Yetro surukin Musa, ya kawo hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu wa Allah, Haruna ya zo tare da dukan dattawan Isra’ila, suka ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.
(Maimaitawar Shari’a 1.9-18)
Kashegari, Musa ya zauna domin yă yi wa mutane shari’a, sai suka tsaya kewaye da shi daga safe har yamma. Sa’ad da surukinsa ya lura da duk abin da Musa yake yi saboda mutane, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa mutane? Don me kai kaɗai kake zama kana yin shari’a wa mutane, yayinda mutanen nan suke tsaya kewaye da kai daga safe har yamma?”
Musa ya amsa ya ce, “Saboda mutanen suna zuwa wurina, don su nemi nufin Allah. Duk lokacin da suke da gardama, akan kawo su a wurina, ni kuma sai in raba tsakaninsu, in kuma koya musu dokokin Allah da farillansa.”
Surukin Musa ya amsa ya ce, “Abin da kake yi ba daidai ba ne. Kai da dukan mutanen da suke zuwa wurinka za ku gajiyar da kanku. Aikin ya fi ƙarfinka; ba za ka iya yinsa kai kaɗai ba. Ka kasa kunne gare ni yanzu, zan ba ka shawara, Allah kuma yă kasance tare da kai. Kai za ka zama wakilin mutane a gaban Allah, ka kuma kawo gardamansu gare shi. Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi. Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi. In ka yi haka, Allah ya umarta za ka iya jimre gajiyar, kuma dukan mutanen nan za su koma gida da murna.”
Musa ya kasa kunne ga surukinsa, ya kuma aikata duk abin da ya faɗa. Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. Suka yi hidimar alƙalanci na mutane a dukan lokaci. Gardandamin da suke da wuya, suka kawo wurin Musa, amma ƙananan batuttuwa, suka shari’anta a tsakaninsu.
Sa’an nan Musa ya sallame surukinsa Yetro, ya kuwa koma ƙasarsa.
A Dutsen Sinai
A rana ta farko a cikin watan uku bayan da Isra’ilawa suka bar Masar, a wannan rana, suka iso Hamadar Sinai. Bayan da suka tashi daga Refidim, suka shiga Hamadar Sinai, sai Isra’ilawa suka yi sansani a gaban dutsen.
Sai Musa ya hau kan dutsen don yă sadu da Allah, Ubangiji kuwa ya kira shi daga dutsen ya ce, “Wannan shi ne abin da za ka faɗa wa gidan Yaƙub, da kuma abin da za ka faɗa wa mutanen Isra’ila. ‘Ku da kanku kun ga abin da na yi wa Masar, da yadda na ɗauko ku a kan fikafikan gaggafa na kawo ku wurina. Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce, za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”
Sai Musa ya koma ya aika a kira dukan dattawan mutane, ya bayyana dukan kalmomin da Ubangiji ya umarta, ya faɗa. Dukan mutane suka amsa gaba ɗaya suka ce, “Za mu yi duk abin da Ubangiji ya faɗa.” Sai Musa ya mayar wa Ubangiji amsar da mutane suka bayar.
Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ina zuwa wurinka a cikin baƙin hadari, domin mutane su ji ni ina maganar da kai, domin su amince da kai koyaushe.” Sa’an nan Musa ya faɗa wa Ubangiji abin da mutane suka ce.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin mutanen, ka tsarkake su yau da gobe, ka sa su wanke tufafinsu. Su zama da shiri a rana ta uku, gama a ranar ce Ubangiji zai sauko a kan Dutsen Sinai a idon dukan mutane. Sai ka yi wa jama’a iyaka kewaye da dutsen, ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ku mai da hankali, kada ku hau dutsen ko ku taɓa gefensa. Duk wanda ya taɓa dutsen, lalle za a kashe shi. Za a jajjefe shi da duwatsu, ko a harbe shi da kibiyoyi, ba hannun da zai taɓa shi. Mutum ko dabbar da ya taɓa, ba za a bar shi da rai ba.’ Lokacin da aka ji muryar ƙaho ne kawai za su iya taru a gindin dutsen.”
Bayan da Musa ya gangara wurin mutane, ya tsarkake su, sai suka wanke tufafinsu. Sa’an nan ya ce wa mutane, “Ku shirya kanku domin rana ta uku. Ku ƙame kanku daga yin jima’i.”
A safiyar rana ta uku, aka yi tsawa, da walƙiyoyi, sai ga girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama’ar da suke cikin sansani suka yi rawar jiki. Sa’an nan Musa ya jagoranci mutane daga sansani domin su sadu da Allah, sai suka tsaya a gefen dutsen. Dutsen Sinai kuwa ya tunnuƙe duka da hayaƙi, gama Ubangiji ya sauko a bisan dutsen cikin wuta. Hayaƙin ya hau kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya, duk dutsen ya yi rawa da ƙarfi, sai karar ƙaho ya yi ta ƙaruwa. Sa’an nan Musa ya yi magana, murya Allah kuwa ta amsa masa.
Ubangiji ya sauko a kan ƙwanƙolin Dutsen Sinai, ya kira Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen. Musa kuwa ya haura sai Ubangiji ya ce masa, “Ka sauka ka faɗa wa jama’a, kada su kuskura su ƙetare layin iyakan nan, garin son zuwa don ganin Ubangiji, gama duk waɗanda suka yi haka za su mutu. Ko firistocin da za su kusato Ubangiji sai su tsarkake kansu, don kada in hallaka su.”
Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutanen ba za su hau Dutsen Sinai ba, gama kai da kanka ka gargaɗe mu, ‘Ku sa iyaka kewaye da dutsen ku kuma tsarkake shi.’ ”
Ubangiji ya amsa, “Sauka ka kawo Haruna tare da kai. Amma kada firistoci da mutane su zarce iyakan nan, a kan za su zo wurin Ubangiji, don kada in hallaka su.”
Saboda haka Musa ya sauka wurin mutane ya kuma faɗa musu.
Dokoki goma
(Maimaitawar Shari’a 5.1-21)
Sai Allah ya faɗi waɗannan kalmomi ya ce,
“Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.
“Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.
Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba. Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina, amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.
Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.
Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki. Kwana shida za ka yi dukan aikinka, amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.
Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
Ba za ka yi kisankai ba.
Ba za ka yi zina ba.
Ba za ka yi sata ba.
Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.
Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”
(Maimaitawar Shari’a 5.23-33)
Da mutane suka ga tsawa da walƙiya, suka ji karar ƙaho, suka kuma ga dutsen yana hayaƙi, sai suka yi rawar jiki don tsoro. Suka tsaya da nisa suka ce wa Musa, “Ka yi magana da mu da kanka, za mu kasa kunne. Amma kada Allah ya yi mana magana, don kada mu mutu.”
Musa ya ce wa mutane, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo don yă gwada ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”
Sa’ad da mutane suka tsattsaya da nesa, sai Musa ya matsa kusa da girgije mai duhu, inda Allah yake.
Gumaka da bagadai
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa wannan. ‘Kun gani da kanku cewa na yi magana da ku daga sama. Kada ku yi waɗansu alloli in ban da ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa ko na zinariya.
“ ‘Ku yi mini bagaden ƙasa, ku kuma miƙa mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, za ku hadayar da tumakinku da awakinku da shanu. Duk inda na sa a girmama sunana, zan zo wurinku, in sa muku albarka. In kuka yi mini bagade dutse, kada ku gina shi da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama inda guduma ta taɓa duwatsun, sun haramtu ke nan. Kada ku gina wa bagadena matakala, domin kada yayinda wani yana hawa, mutane su ga tsiraicinsa.’
(Maimaitawar Shari’a 15.12-18)
“Waɗannan su ne dokokin da za ka sa a gabansu.
Bayin Ibraniyawa
“In ka sayi mutumin Ibraniyawa a matsayin bawa, zai bauta maka shekara shida. Amma a shekara ta bakwai, za ka ’yantar da shi, yă tafi ’yantacce, ba tare da ya biya kome ba. In ya zo shi kaɗai, zai tafi ’yantacce shi kaɗai; amma in yana da mata a lokacin da ya zo, za tă tafi tare da shi. In maigidansa ya yi masa aure, ta kuwa haifa masa ’ya’ya maza ko mata, matan da ’ya’yan, za su zama na maigidan, sai mutumin kaɗai zai tafi ’yantacce.
“Amma in bawan ya furta ya ce, ‘Ina ƙaunar maigidana, da matata, da ’ya’yana, ba na so kuma in ’yantu,’ dole maigidansa yă kai shi gaban alƙalai. Zai kai shi ƙofa ko madogarar ƙofa, yă huda kunnensa da basilla, sa’an nan zai zama bawansa duk tsawon kwanakinsa a duniya.
“In mutum ya sayar da ’yarsa a matsayin baiwa, ba za a ’yantar da ita kamar bawa ba. In ba tă gamshi maigida wanda ya zaɓe ta domin kansa ba, dole yă bari a fanshe ta. Ba shi da dama yă sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba. In ya zaɓe ta domin ɗansa, dole yă ba ta duk damar da ’ya ta mace take da shi. In ya auri wata mace, ba zai hana wa baiwar abinci da sutura ba, ba kuma zai ƙi kwana da ita ba. In bai tanada mata waɗannan abubuwa uku ba, sai tă tafi ’yantacciya, babu biyan kome.
Jin rauni
“Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle a kashe shi. Amma in ba da nufin yă kashe shi ba, sai dai in Allah ne ya nufa haka, to, sai mutumin yă tsere zuwa inda zan nuna muku. Amma in mutumin ya yi dabara har ya kashe wani mutum da gangan, sai a ɗauke shi daga bagadena a kashe shi.
“Duk wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.
“Duk wanda ya saci mutum ya sayar da shi, ko kuwa aka iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.
“Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.
“Idan mutane suka yi faɗa, ɗayan ya jefa ɗayan da dutse, ko ya naushe shi amma bai mutu ba, sai dai ya yi ta jiyya, idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda ne, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓata masa, yă kuma lura da shi, har yă warke sarai.
“In mutum ya dūke bawansa ko baiwarsa da sanda, sai bawan ko baiwar ta mutu saboda dūkan, dole a hukunta shi, amma ba za a hukunta shi ba, in bawan ko baiwar ta tashi, bayan kwana ɗaya ko biyu, tun da bawan ko baiwar mallakarsa ne.
“Idan mutum biyu suna faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka za a biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara. Amma in akwai rauni mai tsanani, sai a ɗauki rai a maimakon rai, ido don ido, haƙori don haƙori, hannu don hannu, ƙafa don ƙafa, ƙuna don ƙuna, rauni don rauni, ƙujewa don ƙujewa.
“In mutum ya bugi bawa ko baiwa a ido, har idon ya lalace, dole yă ’yantar da shi ko ita, maimakon ido. In kuma ya fangare haƙorin bawa ko baiwa, dole yă ’yantar da bawan ko baiwar, a maimakon haƙorin.
“In bijimi ya kashe namiji ko ta mace, dole a jajjefe bijimin har yă mutu, ba za a kuma ci namansa ba. Amma mai bijimin ba shi da laifi. In, har an san bijimin da wannan hali, an kuma yi wa mai shi gargaɗi, amma bai ɗaura shi ba, har ya kashe namiji ko ta mace, za a jajjefe bijimin tare da mai shi, har su mutu. Amma fa, in an bukace shi yă biya, zai biya don yă fanshi ransa ta wurin biyan abin da aka aza masa. Wannan doka ta shafi batun bijimin da ya kashe ɗa ko ’ya. In bijimin ya kashe bawa ko baiwa, mai shi zai biya shekel talatin na azurfa wa maigidan bawan, a kuma a jajjefe bijimin.
“In mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai kuma rufe ba, sai saniya ko jaki ya fāɗi a ciki, Mai ramin zai biya rashin da aka yi wa mai shi, matacciyar saniyan ko jakin, zai zama na mai ramin.
“In bijimin mutum ya raunana bijimin wani, har ya mutu, sai mutanen biyu su sayar da mai ran, su raba kuɗin daidai, haka ma su yi da mai ran. Amma fa, in tun can, an san bijimin yana da wannan halin faɗa, duk da haka mai shi bai ɗaura shi ba, dole mai shi yă biya, dabba domin dabba, matacciyar dabbar kuwa tă zama nasa.
Tsarewar mallaka
“In mutum ya saci saniya ko tunkiya ya yanka, ko ya sayar, zai biya shanu biyar, a maimakon saniyar da ya sata, ko kuma tumaki huɗu, maimakon tunkiyar da ya sata.
“In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga yă yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa daga wurin kowa ba; amma in ya faru bayan wayewar gari, to, za a nemi alhakin jinin ɓarawon a hannun wanda ya bugi ɓarawon.
“Ɓarawon da aka kama da abin da ya sata, dole yă yi cikakkiyar ramuwa, amma in ba shi da kome, dole a sayar da shi a biya abin da ya sata. In an sami dabbar, ko saniya, ko jaki, ko tunkiya da ya sata da rai a hannunsa, dole ɓarawon yă biya taran da za a ci shi, sau biyu na kowane ɗaya.
“In mutum ya sa dabbobinsa su yi kiwo a fili ko a gonar inabi, ya kuma bar dabbobinsa suka yi ɓarna a cikin gonar wani, sai a sa mai dabbar yă biya tara daga amfanin gonarsa mafi kyau duka.
“In gobara ta tashi, ta kuma bazu cikin ƙayayyuwa, har ta cinye tarin hatsi, ko hatsin da ke tsaye, ko dukan gonar, dole wanda ya sa wutar, yă biya taran da aka yanka masa saboda ɓarnan da wutar ta yi.
“In mutum ya ba maƙwabcinsa azurfa, ko kaya ajiya, aka kuma sace su daga gidan maƙwabcin, in an kama ɓarawon, sai ɓarawon yă biya abin da ya sata har sau biyu. Amma in ba a sami ɓarawon ba, sai wanda aka yi ajiyar a gidansa, yă bayyana a gaban alƙalai a bincika ko yana da hannu a kan kayan maƙwabcinsa. A kowane rikicin cin amana da zai shiga tsakanin mutum biyu, ko a kan bijimi, ko jaki, ko tunkiya, ko riga, kai, ko a kan kowane irin abin da ya ɓata, da ma abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin a gaban alƙalai. Wanda alƙali ya ce shi ne mai laifi, sai yă biya ɗayan taran da za a yanka, har sau biyu.
“In mutum ya ba da jaki, ko saniya, ko tunkiya, ko kowace dabba wa maƙwabcinsa ajiya, sai abin ya mutu, ko ya ji rauni, ko an ɗauke shi, in ba shaida, rantsuwa ce za tă raba tsakaninsu a gaban Ubangiji cewa babu hannunsa a dukiyar maƙwabcinsa. Mai dukiyar kuwa zai yarda da rantsuwar, ba za a bukaci wanda aka bai wa amanar yă biya ba. Amma idan satan dabbar ce aka yi, dole wanda aka bai wa ajiyar yă biya mai dabbar taran da aka ci masa. In naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shaida, ba za a kuwa sa maƙwabcin yă biya abin da naman jeji ya kashe ba.
“In mutum ya yi aron dabba daga wurin maƙwabcinsa, sai dabbar ta ji rauni ko ta mutu, yayinda mai shi ba ya nan, dole wanda ya yi aron dabbar yă biya. Amma idan mai dabbar yana a wurin, wanda ya karɓa aron, ba zai biya kome ba. In an yi hayar dabbar ce, to, kuɗin da aka biya na hayar zai zama a madadin rashin.
Hakkin zamantakewa
“Idan mutum ya ruɗe budurwa, wadda ba wanda yake nemanta, ya kuma kwanta da ita, dole yă biya kuɗin aurenta, za tă kuma zama matarsa. In mahaifinta ya ƙi yă ba da ita ga mutumin, dole mutumin yă biya dukiya daidai da abin da akan biya domin budurwai.
“Kada ku bar maiya da rai.
“Duk mutumin da ya yi jima’i da dabba dole a kashe shi.
“Duk wanda ya yi hadaya ga wani allah ban da Ubangiji, dole a hallaka shi.
“Kada a wulaƙanta, ko a zalunci baƙo, domin dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.
“Kada ku ci zalin gwauruwa, ko maraya. In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu. Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu.
“In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa. In kun ɗauki mayafi maƙwabcinku a matsayin jingina, ku mayar masa kafin fāɗuwar rana, domin mayafin ne abin da yake da shi na rufe jikinsa. To, da me zai rufu yă yi barci? Sa’ad da ya yi mini kuka, zan ji, gama ni mai tausayi ne.
“Kada ku yi maganar saɓo ga Allah, ko ku la’anta mai mulkin mutanenku.
“Kada ku jinkirta fitar da zakarku daga rumbunanku, ko harajin kayan da kuka saya.
“Dole ku ba ni ’ya’yan farinku maza. Ku yi haka da shanunku da tumakinku. Bari su kasance da iyayensu mata, har kwana bakwai, amma ku ba ni su a rana ta takwas.
“Za ku kasance mutanena masu tsarki. Saboda kada ku ci naman da namun jeji suka kashe; ku jefa wa karnuka.
Dokokin adalci da jinƙai
“Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.
“Kada ku yi abin da ba daidai ba, don galibin mutane suna yin haka. Sa’ad da kuke ba da shaida a gaban shari’a, kada ku ba da shaidar ƙarya a kauce wa gaskiya don ku faranta wa taron jama’a rai. Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari’a.
“In ka ga saniyar abokin gābanka, ko jakinsa ya ɓace, ka yi ƙoƙari ka mai da shi wurinsa. In ka ga jakin wani maƙiyinka ya fāɗi a ƙarƙashin kayan da ya ɗauka, kada ka bar shi can, ka yi ƙoƙari ka taimake shi.
“Kada ku kāsa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a. Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi tare da mai adalci, gama ba zan bar mugun yă tafi haka kawai ba.
“Kada ka karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta waɗanda suke gani, yakan kuma karkatar da maganar masu adalci.
“Kada ka zalunci baƙo, ku kanku kun san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a Masar.
Dokokin Asabbaci
“Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar, amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.
“Kwana shida za ku yi aikinku, amma a rana ta bakwai, kada ku yi aiki, saboda saniyarku da jakinku su huta, haka kuma bawan da aka haifa a gidanku, da kuma baƙon da yake a cikinku yă wartsake.
“Ku mai da hankali, ku yi biyayya da duk abin da na faɗa muku. Kada ku kira sunaye waɗansu alloli; kada a ji su a bakinku.
Bukukkuwa uku na shekara
([Fitowa 34.18-26]; Maimaitawar Shari’a 16.1-17)
“Sau uku a shekara za ku yi mini biki.
“Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a lokacin da aka ayana a watan Abib, gama a watan ne kuka fito daga Masar.
“Kada wani yă zo a gabana hannu wofi.
“Ku yi Bikin Girbi da nunan fari na amfanin shuke-shuken gonarku.
“Ku yi Bikin Tattarawa a ƙarshen shekara, sa’ad da kuka tattara amfani daga gonarku.
“Sau uku a shekara, maza duka za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka.
“Kada ku miƙa mini hadayar jini tare da wani abu mai yisti.
“Ba za a bar kitsen bikin hadayata yă kwana ba.
“Dole ne ku kawo mafi kyau daga nunan fari na gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku.
“Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.
Mala’ikan Allah zai shirya hanya
“Ga shi, zan aika mala’ika a gabanku, yă tsare ku a tafiyarku, yă kuma kawo ku wurin da na shirya. Ku saurare shi, ku kuma kasa kunne ga abin da yake faɗa. Kada ku yi masa tawaye; ba zai gafarta tawayenku ba, gama shi wakilina ne. In kun kasa kunne sosai ga abin da yake faɗi, kuka kuma yi abin da na faɗa, zan zama magabci ga abokan gābanku, zan kuma yi hamayya da abokan hamayyanku. Mala’ikana zai sha gabanku, yă kawo ku cikin ƙasar Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan’aniyawa, da Hiwiyawa, da kuma Yebusiyawa, zan kuma kawar da su. Kada ku durƙusa wa allolinsu, ko ku yi musu sujada, ko kuma ku bi al’adunsu. Za ku hallaka dukan allolinsu, ku kuma farfasa keɓaɓɓun duwatsunsu. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku. A ƙasarku, mace ba za tă yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.
“Zan aiki razanata a gabanku, in kuma sa ruɗami a cikin kowace al’ummar da za ku sadu da ita. Zan sa duk abokan gābanku su juye da baya, su gudu. Zan aiki rina a gabanku, su kori Hiwiyawa, Kan’aniyawa da kuma Hittiyawa. Amma ba a shekara guda zan kore muku su ba, don kada ƙasar tă zama kufai har namun jeji su fi ƙarfinku. Da kaɗan da kaɗan zan kore muku su, har yawanku yă kai yadda za ku mallaki ƙasar.
“Zan kafa iyakokinku daga Jan Teku23.31 Da Ibraniyanci Yam Suf; wato, Tekun Iwa. zuwa Bahar Rum,23.31 Wato, Mediterraniyan daga hamada kuma zuwa Kogi.23.31 Wato, Yuferites Zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kuwa kore su daga gabanku. Kada ku ƙulla yarjejjeniya da su, ko da allolinsu. Kada ku bari su zauna a cikin ƙasarku, in har kuka bar su, za su ɓata ku da zunubinsu na bautar allolinsu, har zai yă zama muku tarko.”
An Tabbatar da alkawari
Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku hauro zuwa wurina, kai da Haruna, Nadab da Abihu, da kuma dattawa saba’in a cikin Isra’ila. Za ku yi sujada da ɗan nisa, sai Musa kaɗai zai kusaci Ubangiji. Amma sauran kada su zo kusa, kada kuma jama’a su hau tare da shi.”
Sa’ad da Musa ya tafi ya faɗa wa mutanen duk kalmomin Ubangiji da dokokinsa, sai suka amsa da murya ɗaya suna cewa, “Duk abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi.” Sai Musa ya rubuta duk abin da Ubangiji ya faɗa.
Ya tashi kashegari da sassafe ya gina bagade kusa da dutsen, ya aza al’amudai goma sha biyu bisa ga kabilu goma sha biyu na Isra’ila. Sai ya aiki samarin Isra’ilawa, suka miƙa hadaya ta ƙonawa, suka kuma miƙa ƙananan bijimai don hadaya ta salama ga Ubangiji. Musa ya ɗauki rabin jinin ya zuba a cikin kwanoni, rabin kuma ya yayyafa a kan bagaden. Sa’an nan ya ɗauki Littafin Alkawari ya karanta wa mutane. Suka amsa suka ce, “Za mu yi duk abin da Ubangiji ya faɗa; za mu yi biyayya.”
Musa ya kuma ɗauki jinin, ya yayyafa a kan mutanen ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, bisa ga dukan waɗannan kalmomi.”
Musa da Haruna, Nadab da Abihu, da dattawa saba’in, Allah na Isra’ila suka haura suka kuma ga Allah na Isra’ila. A ƙarƙashin ƙafafunsa akwai wani abu wanda aka yi da saffaya, mai haske kuma kamar sararin sama kansa. Amma Allah bai yi wa shugabannin Isra’ila wani abu ba; suka ga Allah, suka ci suka kuma sha.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Hauro wurina a kan dutse, ka tsaya a nan, zan ba ka allunan dutsen, da doka da umarnan da na rubuta don koyonsu.”
Sa’an nan Musa ya fita tare da Yoshuwa mataimakinsa, ya kuwa hau kan dutsen Allah. Ya ce wa dattawan, “Ku jira mu a nan, sai mun dawo wurinku. Haruna da Hur suna tare da ku, in wani yana da wata damuwa, sai yă je wurinsu.”
Da Musa ya hau dutsen, sai girgije ya rufe dutsen, sai ɗaukakar Ubangiji ta sauka a kan Dutsen Sinai, kwana shida girgije ya rufe dutsen, a rana ta bakwai, sai Ubangiji ya kira Musa daga cikin girgijen. Ga Isra’ilawa dai, ɗaukakar Ubangiji ta yi kamar wuta mai ci a kan dutse. Sa’an nan Musa ya shiga girgijen ya hau kan dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba’in da dare arba’in.
Hadayu don tabanakul
([Fitowa 35.4-9])
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar.
“Ga iri jerin kayan da za ka karɓo daga hannunsu,
“zinariya, da azurfa, tagulla,
shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin,
da gashin akuya,
fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau,
itacen akashiya,
mai domin fitila,
kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi,
da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
“Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu. Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka.
Akwatin alkawari
([Fitowa 37.1-9])
“Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya. Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe. Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya. Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa. Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba. Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin.
“Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin. Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya. Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin. Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki. Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.
Tebur
([Fitowa 37.10-16])
“Ka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. Ka dalaye shi da zinariya zalla ka kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya. Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya. Ka yi zoban zinariya huɗu domin teburin, ka daure su a kusurwoyi huɗu, inda ƙafafu huɗun suke. Zoban za su kasance kusa da dajiyar don riƙe sandunan da za a yi amfani don ɗaukar teburin. Ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya, da sandunan ne za ku riƙa ɗaukan teburin. Da zinariya zalla kuma za ka yi farantansa, da kwanoninsa na tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin zuban hadayu. Ka sa burodin Kasancewa a kan wannan tebur, yă kasance a gabana kullum.
Wurin ajiye fitila
([Fitowa 37.17-24])
“Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi. Wurin ajiye fitilar yă kasance da rassa shida, rassan nan za su miƙe daga kowane gefe na wurin ajiye fitilan, uku a gefe guda, uku kuma a ɗaya gefen. Kwafuna uku masu siffar furanni almon, da toho, da kuma furannin za su kasance a rashe guda, uku a kan rashe na biye, haka kuma a kan saura rassan shida da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan. A bisa wurin ajiye fitilan kuwa za a kasance da kwafuna huɗu masu siffar furannin almon, da toho, da furanni. Toho ɗaya zai kasance a ƙarƙashin rassa biyu na farkon da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku a ƙarƙashin rassa na uku, rassa shida ke nan duka. Tohon da kuma rassan za su kasance ɗaya da wurin ajiye fitilan da aka yi da ƙerarriyar zinariya.
“Sa’an nan ka yi fitilu bakwai, ka sa su a bisa wurin ajiye fitilan ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta. Za a yi lagwaninsa da manyan farantansa da ƙerarriyar zinariya. Da zinariya zalla na talenti ɗaya za ka yi wurin ajiye fitilan da waɗannan abubuwa duka. Sai ka lura ka yi su daidai bisa ga fasalin da aka nuna maka a kan dutse.
Tabanakul
([Fitowa 36.8-19])
“Ka yi tabanakul da labule goma na lilin mai laushi a naɗe shi biyu, a saƙa labulen da ulu mai ruwan shuɗi, da ulu mai ruwan shunayya, da kuma ulu mai ruwan ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani. Dukan labulen, girmansu zai zama kamu ashirin da takwas, fāɗinsu kuwa kamu huɗu. Labulen su zama daidai wa daida. Ka haɗa labule biyar tare, ka yi haka kuma da suran biyar ɗin. Ka sa wa labulen rammuka da ulu mai ruwan shuɗin a gefen ƙarshe na labule ɗaya, a kuma yi haka a ƙarshen gefe na ɗaya kuma. Ka yi wa labulen rammuka hamsin a ɗayan labule, ka kuma yi haka a ƙarshe ɗayan labulen, rammukan su fuskanci juna. Sa’an nan ka yi maɗauri hamsin na zinariya don amfanin ɗaura labulen a haɗe, domin tabanakul yă zama ɗaya.
“Ka yi labule goma sha ɗaya na gashin akuya da za ka rufe tabanakul. Tsawon kowanne yă zama kamu talatin, fāɗinsa kuma yă zama kamu huɗu. Labulen za su zama daidai wa daida. Ka haɗa labule biyar ka ɗinka. Haka kuma za ka yi da sauran shidan. Ka naɗe shida ɗin biyu, ka yi labulen ƙofar tentin da shi. Ka yi rammuka hamsin a ƙarshen gefen kashi ɗaya na labulen, haka kuma a ƙarshen kashi ɗayan. Sai ka kuma yi maɗauri hamsin da tagulla, ka ɗaura su a haɗe da tentin su zama ɗaya. Ragowar rabin labulen da yake a bisa tenti kuma sai a bar shi yana lilo a bayan tabanakul. Tsawon labulen tenti zai zama kamu ɗaya a kowane gefe, abin da ya rage kuma sai a bar shi ya yi ta lilo a kowane gefe don yă rufe tabanakul. Ka yi abin rufe tentin da fatun raguna da aka rina ja, a kansa kuma ka rufe shi da fatun shanun teku.
([Fitowa 36.20-34])
“Ka yi tabanakul da katakon itacen ƙiryar da aka kakkafa a tsaye. Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi, ka kafa katakan suna duban juna. Ka yi da dukan katakan tabanakul haka. Ka shirya katakai ashirin a gefen kudu na tabanakul, ka kuma yi rammuka arba’in da azurfar da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin rammukan. Game da ɗayan gefen, gefen arewa na tabanakul, za ka kafa katakai ashirin, da rammukan azurfa arba’in, biyu a ƙarƙashin kowane katako. Ka kafa katakai shida don can ƙarshen katakan, wato, a wajen yamma na ƙarshen tabanakul, ka kuma kafa katakai biyu a kusurwoyi can ƙarshe. Za a haɗa katakan nan a kusurwa daga ƙasa zuwa sama a daure su. Haka za a yi da katakan kusurwa na biyu. Ta haka za a sami katakai takwas da rammukansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da rammuka biyu.
“Ka kuma yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya na tabanakul, biyar domin katakai wancan gefe, biyar kuma domin na gefe wajen yamma, can ƙarshen tabanakul. Sandan da yake tsakiyar katakan, zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe. Ka dalaye dukan katakan da zinariya, ka kuma yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Ka kuma dalaye sandunan da zinariya.
“Ka yi tabanakul bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.
([Fitowa 36.35-38])
“Ka yi labule mai ruwan shuɗi, shunayya da jan zare da kuma lallausan lilin da aka tuƙa, da zānen kerubobin da mai fasaha ya yi. Ka rataye shi a bisa dogayen sanduna huɗun nan na itacen ƙirya, waɗanda aka dalaye da zinariya, waɗanda suke tsaya a rammuka huɗu na azurfa. Ka rataye labule daga maɗauri, ka sa akwatin alkawari a bayan labulen. Labulen zai raba Wurin Mai Tsarki da Wurin Mafi Tsarki. Ka sa murfin kafara a bisa akwatin alkawari a Wuri Mafi Tsarki. Ka sa tebur a gaba labulen, a gefen arewa na tabanakul, ka kuma sa wurin ajiye fitilan ɗaura da shi, a wajen kudu.
“Game da ƙofar shigar tenti kuwa, ka yi labule mai ruwan shuɗi, shunayya da jan zare na lallausan lilin da aka tuƙa, aikin gwani. Ka yi ƙugiyoyin zinariya domin wannan labule da katakai itacen ƙirya biyar, waɗanda aka dalaye da zinariya. Ka kuma yi zubi na tagulla biyar dominsu.
Bagaden hadaya ta ƙonawa
([Fitowa 38.1-7])
“Ka gina bagade da itacen ƙirya, mai tsawo kamu uku, zai zama murabba’i, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kuma kamu biyar. Ka yi masa ƙaho a kowace kusurwan nan huɗu, domin bagade da ƙahoni duk su zama ɗaya, ka dalaye bagade da tagulla. Ka yi duk kayan aikinsa da tagulla, tukwanensa na ɗiban toka, da manyan cokula, da kwanonin yayyafawa, da cokula masu yatsotsi don nama da kuma farantai domin wuta. Ka yi raga na tagulla dominsa, ka kuma yi zoben tagulla a kowace kusurwan nan huɗu na bagaden. Ka sa ragar a ƙarƙashin bagade domin tă kai tsakiyar bagade. Ka yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da tagulla. Za a zura sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefe biyu na bagade a lokacin da ake ɗaukarsa. Ka yi bagaden da katakai, sa’an nan ka robe cikinsa. Ka yi shi bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.
Filin tabanakul
([Fitowa 38.9-20])
“Ka yi fili domin tabanakul. Tsawon gefen kudu zai zama kamu ɗari da labulen da aka yi da zaren lili mai kyau, da katakai ashirin da rammukan tagulla ashirin da ƙugiyoyin azurfa da kuma rammuka a kan katakai. A wajen arewa shi ma, tsawon yă zama ƙafa ɗari. Ka kama labulen da ƙugiyoyin da aka yi da azurfa waɗanda aka manna a kan ƙarfen da aka dalaye da azurfa.
“Faɗin ƙarshen filin a yamma zai zama kamu hamsin. A kuma sa labule tare da rammuka goma da kuma katakai goma. A wajen gabas can ƙarshe, wajen fitowar rana, fāɗin filin zai zama kamu hamsin. Tsayin labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da katakai uku tare da rammukansu uku, haka kuma tsayin labule na wancan gefen, zai zama kamu goma sha biyar, da katakai uku tare da rammukansu uku.
“Domin ƙofar tentin, a saƙa labule mai tsayin kamu ashirin da lallausan zaren lilin mai ruwan shuɗi, da shunayya, da jan zare, mai aikin gwani, da katakai huɗu tare da rammukansu huɗu. Duk katakan da suke kewaye da filin, za a yi musu maɗaurai na azurfa da kuma ƙugiyoyi, da rammukan tagulla. Tsayin filin zai zama kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu hamsin, tsayin labulensa na lallausan zaren lilin zai zama kamu biyar, a kuma yi rammukansa da tagulla. Dukan sauran kayan da aka yi amfani da su a aikin wannan tabanakul, ko da wanda irin aiki ne za a yi da su, har da dukan dogayen turakunsa da na filin, za a yi su da tagulla ne.
Mai don wurin ajiye fitila
([Firistoci 24.1-4])
“Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai, tatacce daga zaitun domin fitilu, saboda fitilun su yi ta ci a koyaushe. A cikin Tentin Sujada, a waje da labulen da yake a gaban Akwatin Alkawari, Haruna da ’ya’yansa za su sa fitilu su yi ta ci a gaban Ubangiji, daga yamma har safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a cikin Isra’ila har tsararraki masu zuwa.
Rigunan firistoci
([Fitowa 39.1-7])
“Ka sa a kawo maka Haruna ɗan’uwanka, tare da ’ya’yansa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar daga cikin Isra’ilawa, domin su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka yi tufafi masu tsarki domin ɗan’uwanka Haruna, domin a girmama, a kuma ɗaukaka shi. Ka faɗa wa dukan gwanayen da na ba su hikima a irin abubuwan nan, cewa su yi tufafi saboda Haruna, don a tsarkakewarsa, domin yă yi mini hidima a matsayin firist. Waɗannan su ne tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da efod, da taguwa, da doguwar riga, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan’uwanka, Haruna da ’ya’yansa, waɗannan tsarkaka tufafi, don su zama firistoci masu yi mini hidima. Ka sa su yi amfani da zinariya, da zare mai ruwan shuɗi da shunayya da ja, da kuma lallausan lilin.
Efod
([Fitowa 39.2-7])
“Ka yi efod da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da kuma lallausan lilin, aikin gwani mai sana’a. Za a yi fele biyu, gaba da baya, sa’an nan a haɗa, a ɗinka a mahaɗinsu a kafaɗa. Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi efod da shi, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.
“Ka ɗauki duwatsu biyu masu daraja, ka rubuta sunayen ’ya’yan Isra’ila a kai bisa ga haihuwarsu, sunaye shida a kan dutse ɗaya, saura shida kuma a kan ɗaya dutsen. A rubuta sunayen ’ya’yan Isra’ila a kan duwatsu biyun, yadda mai yin aiki da dutse mai daraja yakan zāna hatimi. Sa’an nan a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya a ɗaura su a kan ƙyallen kafaɗa efod a matsayin duwatsun tuni ga ’ya’yan Isra’ila. Haruna ne zai ɗauki sunayen a kafaɗarsa don tuni a gaban Ubangiji. Ka yi tsaiko na zinariya da tuƙaƙƙun sarƙoƙi biyu kamar igiya, na zinariya zalla, ka kuma ɗaura wa tsaikunan nan biyu tuƙaƙƙun sarƙoƙi.
Ƙyallen maƙalawa a ƙirji
([Fitowa 39.8-21])
“Ka shirya ƙyallen da za a manna a ƙirji don neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa efod ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Zai zama murabba’i, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kuma kamu ɗaya, a naɗe shi biyu. Sa’an nan ka yi jeri huɗu na duwatsu masu daraja a kansa. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu. A jeri na biyu, a sa turkuwoyis, da saffaya, da emeral. A jeri na uku, a sa yakin, da idon mage da ametis. A jeri na huɗu, a sa kirisolit, da onis, da yasfa. Ka sa su a tsaiko na zinariya. A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zāna sunayen ’ya’yan Isra’ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zāna sunayen kamar hatimi.
“Ka yi wa ƙyallen maƙalawa a ƙirjin tuƙaƙƙun sarƙoƙin zinariya zalla. Ka yi zobe biyu na zinariya saboda ƙyallen maƙalawa a ƙirjin, ka kuma ɗaura su a kusurwoyin ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka ɗaura sarƙoƙin zinariyan nan biyu a zoban a kusurwan ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka kuma sa sauran bakunan sarƙoƙin nan biyu a kan tsaikon nan biyu, kana haɗa su da ƙyallen kafaɗa na efod a gaba. Ka yi zobai biyu na zinariya ka ɗaura su ga sauran kusurwoyi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a gefen ciki kusa da efod. Ka ƙara zobai biyu, ka kuma ɗaura su a bakin ƙyallen da ya sauka daga kafaɗa ta gaban efod, kusa da mahaɗin ƙyallaye biyu a bisa ɗamara na efod. Za a ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirji a zoban efod da shuɗiyar igiya, domin ƙyallen maƙalawa a ƙirji yă zauna a bisa abin ɗamarar efod, don kada yă kunce.
“Duk sa’ad da Haruna zai shiga Wuri Mai Tsarki, zai shiga riƙe da sunayen ’ya’yan Isra’ila a zuciyarsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji na neman nufin Allah, domin yă zama abin tunawa a gaban Ubangiji. Ka kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirji, don su kasance a zuciyar Haruna, a duk sa’ad da zai shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai koke-koken Isra’ilawa a gaban Ubangiji.
Sauran rigunan firistoci
([Fitowa 39.22-26],[30],[31])
“Ka yi taguwar efod da shuɗi duka, ka yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A kuma naɗe wuyan rigar yă yi kauri domin kada yă yage. Za a yi wa bakin rigar ado da fasalin ’ya’yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu. Za ka jera su bi da bi, wato, ’ya’yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya kewaye da bakin rigar. Dole Haruna yă sa shi sa’ad da yake hidima. Za a ji ƙarar ƙararrawar sa’ad da zai shiga Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji, da sa’ad da ya fita, don kada yă mutu.
“Ka yi allo na zinariya zalla, ka kuma yi rubutu a kansa kamar na hatimi, haka,
Mai tsarki ga Ubangiji.
Ka ɗaura shi da igiyar ruwa bula domin a haɗa shi da rawani; zai kasance a gaban rawanin. Zai kasance a goshin Haruna, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra’ilawa sun yi cikin miƙa baye-bayensu masu tsarki. Zai kasance a goshin Haruna kullayaumin, domin su zama abin karɓa ga Ubangiji.
“Ka saƙa doguwar riga da lallausan lilin ka kuma yi hula da lallausan zaren lilin, ka kuma saƙa abin ɗamara mai ado.
([Fitowa 39.27-29])
“Ka saƙa doguwar riga, abin ɗamara da kuma huluna domin ’ya’yan Haruna, don yă ba su girma da ɗaukaka. Bayan ka sa waɗannan riguna wa ɗan’uwanka Haruna da ’ya’yansa, ka shafe su da mai, ka kuma naɗa su. Ka keɓe su domin su yi mini hidima a matsayin firistoci.
“Ka yi ’yan wandunan ciki na lilin don su rufe tsiraicinsu, tsayinsu zai kama daga kwankwaso zuwa cinya. Dole Haruna da ’ya’yansa su sa su sa’ad da za su shiga Tentin Sujada, ko sa’ad da suka kusace bagade domin hidima a Wuri Mai Tsarki, don kada su yi laifi, su kuma mutu.
“Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa Haruna da zuriyarsa har abada.
Keɓewar firistoci
([Firistoci 8.1-36])
“Ga abin da za ka yi don ka keɓe su, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani. Daga garin alkama mai laushi marar yisti kuwa, ka yi burodi, da wainan da aka kwaɓa da mai, da ƙosai waɗanda an barbaɗa mai a kai. Ka sa waɗannan a cikin kwando. Sa’an nan ka miƙa su tare da ɗan bijimin da ragunan nan biyu. Bayan haka sai ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka yi musu wanka. Ka ɗauki rigar ka sa wa Haruna, ka sa masa doguwar rigar, da rigar efod, da efod kanta, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka ɗaura masa efod da ɗamarar da aka yi mata ado. Ka naɗa masa rawani a kai, ka kuma sa kambi mai tsarki a bisa rawanin. Ka ɗauki man shafewa ka shafe shi, ta wurin zuba man a kansa. Ka kawo ’ya’yansa, ka sa musu taguwoyi, ka kuma sa musu huluna a kansu. Sa’an nan ka ɗaura wa Haruna da ’ya’yansa abin ɗamara. Su kuwa da zuriyarsu, aikin firist kuwa zai zama nasu ta wurin dawwammamiyar farilla.
“Ta haka za ka keɓe Haruna da ’ya’yansa maza.
“Ka kuma kawo bijimin a gaban Tentin Sujada, sai Haruna da ’ya’yansa su ɗora hannuwansu a kansa. Ka yanka shi a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Ka ɗibi jinin bijimin ka zuba a kan ƙahoni na bagade da yatsanka, sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden. Sa’an nan ka ɗauki dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake manne da hanta, da ƙoda biyu da kuma kintsen da yake a kansu, ka ƙone su a kan bagade. Amma ka ƙone naman bijimin, da fatarsa, da kayan cikin, a bayan sansani. Hadaya ce ta zunubi.
“Ka ɗauki ɗaya daga cikin ragunan, Haruna kuwa da ’ya’yan maza za su ɗora hannuwansa a kansa. Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden. Ka yayyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikin, da ƙafafun, da kan, ka haɗa su da gunduwoyin. Sa’an nan ka ƙone ragon ɗungum a kan bagade. Hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
“Ka ɗauki ɗayan ragon, sai Haruna da ’ya’yansa maza su ɗora hannuwansu a kansa. Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka shafa a bisa leɓen kunnen Haruna na dama, da bisa leɓen kunnuwan ’ya’yansa maza na dama, da kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden. Ka ɗibi jinin da yake a kan bagade, da man shafewa, ka yafa a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan ’ya’yansa maza da rigunansu. Sa’an nan shi da ’ya’yansa maza da rigunansu za su tsarkake.
“Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.) Daga kwandon burodi marar yisti, wanda yake gaban Ubangiji, ka ɗauki dunƙule ɗaya, da waina da aka yi da mai, da kuma ƙosai. Ka sa dukan waɗannan a hannun Haruna da ’ya’yansa maza, su kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Sa’an nan ka karɓe su daga hannuwansu, ka ƙone su a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa, domin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Bayan haka, ka ɗauki ƙirjin ragon domin naɗin Haruna, ka kaɗa shi a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Wannan ƙirji zai zama rabonka.
“Ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa, waɗanda za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon naɗin, wanda yake na Haruna da kuma na ’ya’yansa maza. Wannan zai zama rabon Haruna da ’ya’yansa maza daga Isra’ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra’ilawa za su miƙa wa Ubangiji.
“Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na zuriyarsa bayan mutuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su. Ɗan da ya gāje shi a matsayin firist, shi ne zai sa su har kwana bakwai, lokacin da ya shiga Tentin Sujada, don yă yi aiki a Wuri Mai Tsarki.
“Ka ɗauki ragon naɗi, ka dafa naman a tsattsarkan wuri. A ƙofar Tentin Sujada, Haruna da ’ya’yansa maza za su ci wannan rago da burodin da yake cikin kwandon. Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne. In naman ragon naɗi ko wani burodin ya ragu har safiya, a ƙone shi, kada a ci gama tsarkake ne.
“Ka yi wa Haruna da ’ya’yansa maza duk abin da na umarce ka, ka ɗauki kwana bakwai don naɗinsu. Ka miƙa bijimi ɗaya kowace rana domin hadaya don zunubi ta yin kafara. Ka tsarkake bagade ta wuri yin kafara dominsa, ka shafe shi da mai don ka tsarkake shi. Kwana bakwai za ka yi kafara saboda bagaden, ka kuma tsarkake shi. Sa’an nan bagaden zai zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka.
([Firistoci 6.8-13]; [Ƙidaya 28.1-8])
“Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya. Ka miƙa ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma. Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha. Ka miƙa ɗaya ragon da yamma, tare da hadaya ta gari da hadaya ta sha kamar aka yi ta safe, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
“Wannan za tă zama hadaya ta ƙonawar da za a dinga yi kowace rana, daga tsara zuwa tsara. Za a yi ta miƙa hadayar a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. A can zan sadu da kai, in yi magana da kai; a can kuma zan sadu da Isra’ilawa, in kuma tsarkake wurin da ɗaukakata.
“Ta haka zan tsarkake Tentin Sujada da bagaden, in kuma tsarkake Haruna da ’ya’yansa maza su yi mini hidima a matsayin firistoci. Sa’an nan zan zauna a cikin Isra’ilawa, in kuma zama Allahnsu. Za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar saboda in zauna a cikinsu. Ni ne Ubangiji Allahnsu.
Bagaden turare
([Fitowa 37.25-28])
“Ka yi bagade da itacen ƙirya don ƙona turare. Zai zama murabba’i, tsawon zai zama kamu ɗaya, fāɗi kuma kamu ɗaya, amma tsayin yă zama kamu biyu, ƙahoninsa kuma su zama ɗaya da shi. Ka dalaye bisansa da kuma dukan gefe-gefensa da kuma ƙahoninsa da zinariya zalla, ka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi. Ka yi zobai biyu na zinariya domin bagade a ƙarƙashin zubin, biyu a gefe da gefe su fuskanci juna, don su riƙe sandunan da ake amfani da su don ɗaukarsa. Ka yi sandunan nan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya. Ka sa bagaden a gaban labulen da yake gaban akwatin alkawari, a gaba murfin kafara wanda yake bisa akwatin alkawari, inda zan sadu da kai.
“Haruna zai ƙone turare a bisa bagaden kowace safiya, sa’ad da yake shirya fitilu. Dole Haruna yă ƙone turare sa’ad da ya ƙuna fitilu da yamma, ta haka za a riƙa ƙona turare a gaban Ubangiji, daga tsara zuwa tsara. Ba za a ƙona wani irin turare dabam a bisa wannan bagade ba, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta hatsi, ko ta sha a bisansa ba. Sau ɗaya a shekara, Haruna zai yi kafara a bisa ƙahoninsa. Dole a yi wannan kafara ta shekara-shekara da jinin kafara ta hadaya don zunubi daga tsara zuwa tsara. Gama bagaden mafi tsarki ne ga Ubangiji.”
Kuɗin kafara
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su. Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji. Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji. Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku. Ku karɓi kuɗin kafara daga hannun Isra’ilawa, ku yi amfani da shi domin hidimar Tentin Sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar rayukansu.”
Kwano don wanki
([Fitowa 38.8])
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi daro na tagulla, ka yi masa ƙafafun da za a ajiye shi da tagulla don wanki. Ka ajiye shi tsakanin Tentin Sujada da bagade, ka zuba ruwa a ciki. Haruna da ’ya’yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu da ruwan da yake cikinsa. Duk lokacin da suka shiga Tentin Sujada, za su yi wanka, don kada su mutu. Duk lokacin da suka yi kusa da bagade don hidima ta miƙa hadayar da aka yi wa Ubangiji da wuta, za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu, don kada su mutu. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla domin Haruna da zuriyarsa daga tsara zuwa tsara.”
Man shafewa
([Fitowa 37.29])
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau, shekel 500 na ruwan mur, rabin turaren sinnamon mai daɗin ƙanshi shekel 250, shekel 250 na turaren wuta mai ƙanshi, shekel 500 na kashiya, duk bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, da moɗa na man zaitun. Da waɗannan za ka yi man shafewa mai tsarki, yadda mai yin turare yake yi. Zai zama man shafewa mai tsarki. Sa’an nan ka yi amfani da shi don shafa wa Tentin Sujada, da akwatin alkawari, da tebur da kuma dukan kayansa, da wurin ajiye fitila da dukan kayansa, da bagaden ƙona turare, bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, da daro da mazauninsa. Za ka tsarkake su don su zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa su, zai zama mai tsarki.
“Ka shafe Haruna da ’ya’yansa maza, ka kuma tsarkake su don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Wannan mai, zai zama mai tsarki ne a gare ni don shafewa, daga tsara zuwa tsara. Kada a zuba a jikunan mutane, kada kuma a yi wani mai irinsa. Wannan mai, mai tsarki ne, za ku kuma ɗauke shi a matsayi mai tsarki. Duk wanda ya yi irin wannan mai, duk wanda kuma ya shafa shi a kan wani wanda yake ba firist ba, za a ware shi daga mutanensa.’ ”
Turare
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki kayan yaji mai ƙanshi, resin na gum, da onika, da galbanum, da kuma zallan lubban, duk nauyinsu yă zama daidai. Ka yi turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yake yi. A sa masa gishiri, yă zama tsabtatacce, tsarkakakke. Ka ɗiba kaɗan daga ciki, ka niƙa, ka ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin Tentin Sujada, inda zan sadu da kai. Zai zama mafi tsarki a gare ku. Kada ku yi wani turare irinsa wa kanku; ku ɗauke shi a matsayi mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi irinsa don jin daɗin ƙanshinsa, dole a ware shi daga mutanensa.”
Bezalel da Oholiyab
(Fitowa 35.30–36.1)
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a, don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla, don yanka da shirya duwatsu, yin aikin katako, da kuma yin kowane irin aikin sana’ar hannu. Ban da haka, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, don yă taimake shi. Na kuma ba da fasaha ga dukan masu aikin sana’ar hannu, don yin duk abin da na umarce ka. Tentin Sujada, akwatin Alkawari tare da murfin kafara a bisansa, da dukan kayan aiki na tentin, tebur da kayansa, wurin ajiye fitila na zinariya zalla, da dukan kayansa, bagaden ƙona turare, bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, daro tare da mazauninsa, da kuma saƙaƙƙun riguna, tsarkakan riguna don Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci, da man shafewa, da turare mai ƙanshi don Wuri Mai Tsarki. Za a yi su kamar yadda na umarce ka.”
Asabbaci
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Dole ku kiyaye Asabbataina. Wannan zai zama alama tsakanina da ku daga tsara zuwa tsara, saboda ku sani ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.
“ ‘Ku kiyaye Asabbaci, domin yă zama mai tsarki a gare ku. Duk wanda ya ƙazantar da shi, za a kashe shi; duk wanda ya yi wani aiki a ranar, za a ware shi daga mutane. Kwana shida, za a yi aiki, amma a rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi wani aiki a Asabbaci, za a kashe shi. Isra’ilawa za su kiyaye Asabbaci, suna bikinsa daga tsara zuwa tsara a matsayin madawwamin alkawari. Zai zama alama tsakanina da Isra’ilawa har abada, gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya daina aiki, ya kuma huta.’ ”
Sa’ad da Ubangiji ya gama yin wa Musa magana a kan Dutsen Sinai, sai ya ba shi alluna biyu na Alkawari, allunan duwatsu rubutattu da yatsan Allah.
Ɗan maraƙin zinariya
(Maimaitawar Shari’a 9.6-29)
Sa’ad da mutane suka ga Musa ya daɗe bai sauko daga dutse ba, sai suka taru kewaye da Haruna suka ce, “Zo, ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora. Game da wannan Musa wanda ya fitar da mu daga Masar dai, ba mu san abin da ya faru da shi ba.”
Haruna ya amsa musu ya ce, “Ku tuttuɓe zoban zinariya waɗanda suke kunnuwan matanku, da na ’ya’yanku maza da mata, ku kawo mini.” Saboda haka dukan mutane suka tuttuɓe ’yan kunnensu suka kawo wa Haruna. Sai ya karɓi abubuwan da suka ba shi, ya yi gunki na siffar ɗan maraƙi, ya sassaƙa shi da kayan aiki. Sa’ad da mutane suka gani, sai suka tā da murya suka ce, “Waɗannan su ne allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga Masar.”
Da Haruna ya ga haka, sai ya gina bagade a gaban ɗan maraƙi, ya yi shela ya ce, “Gobe akwai biki ga Ubangiji.” Saboda haka kashegari, mutane suka tashi da sassafe suka miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Bayan haka suka zauna suka ci, suka sha, suka kuma tashi suka yi rawa.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama mutanenka, waɗanda ka fitar da su daga Masar sun ƙazantu. Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.”
Ubangiji ya ce wa Musa, “Na ga waɗannan mutane, mutane ne masu taurinkai.” Yanzu ka bar ni kurum fushina yă yi ƙuna a kansu, in hallaka su. Sa’an nan in maishe ka al’umma mai girma.
Amma Musa ya nemi tagomashin Ubangiji, Allahnsa ya ce, “Ya Ubangiji don me fushinka zai yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fisshe su daga Masar da ikon hannunka mai girma? Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, da mugun nufi ne ya fito da su don yă shafe su daga fuskar duniya’? Ka juya daga fushinka mai zafi, ka ji tausayi, kada ka kawo masifa a kan mutanenka. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ” Sai Ubangiji ya yi juyayi, bai kuwa kawo wa mutanensa bala’in da ya yi niyya ba.
Musa ya juya, ya sauka daga kan dutsen da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa. An yi rubutun a kowane gefe, gaba da baya. Allunan aikin Allah ne; rubutun kuma rubutun Allah ne, da ya zāna a kan alluna.
Sa’ad da Yoshuwa ya ji surutun mutane suna ihu, sai ya ce wa Musa, “Kamar akwai ƙarar yaƙi a sansani.”
Musa ya amsa ya ce,
“Ba ƙarar nasara ba ce,
ba ƙarar wanda yaƙi ya ci ba ne;
ƙarar waƙa ce nake ji.”
Da Musa ya kusato sansanin, sai ya ga ɗan maraƙin da kuma mutane suna rawa. Sai fushinsa ya yi ƙuna, ya kuwa jefar da allunan da suke hannuwansa, allunan kuwa suka farfashe a gindin dutsen. Sai ya ɗauki ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone a wuta; sa’an nan ya niƙa shi ya zama gari, ya barbaɗa garin a ruwa, ya sa Isra’ilawa suka sha.
Ya ce wa Haruna, “Mene ne waɗannan mutane suka yi maka da ka kai su ga wannan zunubi mai girma?”
Haruna ya amsa ya ce, “Kada ka yi fushi da ni ranka yă daɗe, ka san yadda mutanen nan suke da saurin yin mugunta. Sun ce mini, ‘Ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora, game da wannan Musa dai, wanda ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.’ Sai na gaya musu, ‘Duk wanda yana da kayan ado na zinariya, ya cire?’ Sa’an nan suka ba ni zinariya, sai na jefa cikin wuta, wannan ɗan maraƙi ya fito.”
Musa ya duba ya ga mutane sun kauce gaba ɗaya domin Haruna ya sa suka kauce, har suka zama abin dariya ga abokan gābansu. Saboda haka sai ya tsaya a ƙofar sansani ya ce, “Duk wanda yake na Ubangiji yă zo wurina.” Sai dukan Lawiyawa suka taru wurinsa.
Sa’an nan ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Kowane mutum yă rataya takobinsa, yă kai yă kawo daga wannan gefe zuwa wancan cikin sansani, kowa yă kashe ɗan’uwansa, da abokinsa, da kuma maƙwabcinsa.’ ” Lawiyawa suka yi yadda Musa ya umarta, a ranar, mutane wajen dubu uku suka mutu. Sa’an nan Musa ya ce, “An keɓe ku ga Ubangiji a yau, gama kun yi gāba da ’ya’yanku da ’yan’uwanku, ya kuma albarkace ku a wannan rana.”
Kashegari Musa ya ce wa mutane, “Kun yi zunubi mai girma. Amma yanzu zan hau wurin Ubangiji; wataƙila zan iya yin kafara domin zunubinku.”
Don haka Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Kaito, mutanen nan sun yi zunubi mai girma! Sun yi wa kansu allolin zinariya. Amma yanzu, ina roƙonka ka gafarta zunubinsu, in ba haka ba, to, ka shafe ni daga littafin da ka rubuta.”
Ubangiji ya amsa wa Musa, “Duk wanda ya yi mini zunubi, shi zan shafe daga littafina. Yanzu tafi, ka jagoranci mutanen zuwa inda na yi zance, mala’ikana kuma zai sha gabanku. Duk da haka sa’ad da lokaci ya yi da zan yi horo, zan hore su domin zunubinsu.”
Ubangiji kuwa ya bugi mutanen da annoba, saboda abin da suka yi da ɗan maraƙin da Haruna ya yi.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka bar wannan wuri, kai da mutanen da ka fito da su daga Masar, ka haura zuwa ƙasar da na alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub cewa, ‘Zan ba zuriyarka.’ Zan aika da mala’ika a gabanka in kuma kori Kan’aniyawa, Amoriyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa. Ka haura zuwa ƙasar da take zub da madara da zuma. Amma ba zan tafi tare da ku ba, saboda ku mutane ne masu taurinkai domin mai yiwuwa in hallaka ku a hanya.”
Da mutane suka ji wannan mugun magana, sai suka fara makoki. Ba kuma wanda ya sa kayan ado. Gama Ubangiji ya riga ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurinkai. In na yi tafiya da ku ko na ɗan lokaci, mai yiwuwa in hallaka ku. Yanzu sai ku tuɓe kayan adonku, zan kuwa yanke shawara a kan abin da zan yi da ku.’ ” Saboda haka Isra’ilawa suka tuttuɓe kayan adonsu a Dutsen Horeb.
Tentin sujada
Musa fa ya saba ɗaukan tenti yă kafa shi a bayan sansani da ɗan nisa, yana kiransa “Tentin Sujada.” Duk wanda yake neman wani abu daga wurin Ubangiji sai yă tafi Tentin Sujada a bayan sansani. A sa’ad da kuma Musa ya fita zuwa Tentin, dukan mutanen sukan tashi su tsaya a ƙofofin tentinsu, suna kallon Musa, sai ya shiga tentin. Yayinda Musa ya shiga cikin tentin, sai al’amudin girgije yă sauko, yă tsaya a ƙofar yayinda Ubangiji yana magana da Musa. Lokacin da mutane suka ga al’amudin girgije a tsaye a ƙofar tentin, sai duk su miƙe tsaye su yi sujada, kowa a ƙofar tentinsa. Ubangiji yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda mutum yake magana da abokinsa. Sa’an nan Musa yă koma sansani, amma saurayin nan Yoshuwa ɗan Nun mai taimakonsa ba ya barin tentin.
Musa da ɗaukakar Ubangiji
Musa ya ce wa Ubangiji, “Kana ta faɗa mini cewa, ‘Ka jagoranci mutane nan,’ amma ba ka faɗa mini wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi ka ƙara ce mini, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a wurina.’ In ka ji daɗina, ka koya mini hanyarka don in san ka, in kuma ci gaba da samun tagomashi daga gare ka. Ka tuna cewa wannan al’umma mutanenka ne.”
Ubangiji ya amsa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma rage maka nauyin kaya.”
Musa kuwa ya ce masa, “In ba za tă tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan. Yaya wani zai sani ko ka ji daɗina da kuma mutanenka, in ba ka tafi tare da mu ba? Mene ne kuma zai bambanta ni da mutanenka daga sauran jama’ar da suke a duniya?”
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka faɗa, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.”
Musa kuwa ya ce, “To, ka nuna mini ɗaukakarka.”
Sai Ubangiji ya ce, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka. Zan yi alheri ga duk wanda na so in yi masa alheri, zan nuna jinƙai ga duk wanda na so in yi masa jinƙai. Amma ya ce, ba za ka ga fuskata ba, don ba mutumin da zai gan ni yă rayu.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen. A sa’ad da ɗaukakata tana wucewa, zan sa ka a cikin tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har sai na wuce. Sa’an nan zan ɗauke hannuna, ka kuwa ga bayana; amma fuskata, ba za ka gani ba.”
Sababbin allunan dutse
(Maimaitawar Shari’a 10.1-5)
Ubangiji ya ce wa Musa “Sassaƙa alluna biyu kamar na farko, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa. Ka shirya da safe, ka hauro kan Dutsen Sinai. Ka gabatar da kanka a gare ni a can kan dutse. Ba wani da zai zo tare da kai, ko a gan shi ko’ina a kan dutsen, kada garkunan tumaki ko na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.”
Saboda haka Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na fari, sai ya hau Dutsen Sinai da sassafe, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, yana kuma ɗauke da alluna biyu na dutse a hannuwansa. Sa’an nan Ubangiji ya sauko a cikin girgije ya tsaya can tare da shi, ya kuma yi shelar sunansa. Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”
Musa ya yi sauri ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada. Ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a idanunka, bari Ubangiji yă tafi tare da mu. Ko da yake wannan mutane masu taurinkai ne, ka gafarta muguntanmu da zunubanmu, ka kuma sāke sa mu zama abin gādonka.”
([Fitowa 23.14-19]; Maimaitawar Shari’a 7.1-5; [16.1-17])
Sai Ubangiji ya ce, “Ga shi na yi alkawari da kai. A gaban dukan mutanenka zan yi abubuwan banmamakin da ba a taɓa yinsa a cikin wata al’umma a duniya ba. Mutanen da kuke zaune cikinsu za su ga aikin bantsoro, da Ni Ubangiji zan yi muku. Ku yi biyayya da umarnin da na ba ka yau. Zan kora muku Amoriyawa, Kan’aniyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa. Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da waɗanda suke zaune a ƙasar da za ku tafi, in ba haka ba, za su zama muku tarko. Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku sassare ginshiƙan Asheransu.34.13 Wato, alamun alliya Ashera Kada ku bauta wa wani allah, gama Ubangiji, wanda sunansa Kishi, Allah ne mai kishi.
“Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da mazaunan wannan ƙasa, don kada sa’ad da suke yi wa allolinsu sujada, suna miƙa musu hadaya, su gayyace ku, ku ci hadayar da suka miƙa wa allolinsu. Kada ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu, waɗanda suke yi wa alloli sujada, har su sa ’ya’yanku su bi allolinsu.
“Kada ku yi alloli na zubi.
“Sai ku yi Bikin Burodi Marar Yisti. Ku kuma ci burodi marar yisti har kwana bakwai, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a cikin watan ne kuka fita daga Masar.
“Ɗan fari na kowane mutum zai zama nawa, har da ɗan farin na dabbobi, ko na garken shanu ko na tumaki. Ku fanshi ɗan farin jaki da na tunkiya, amma in ba ku fanshe shi ba, ku karya wuyansa. Ku fanshi duk ’ya’yan farinku maza.
“Kada wani yă zo gabana hannu wofi.
“Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta.
“Ku kiyaye Bikin Makoni wato, bikin girbin nunan fari na alkama, da Bikin Gama Tattara amfanin gonaki, a ƙarshen shekara. Sau uku a shekara, dukan mazanku za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, Allah na Isra’ila. Zan kore al’umma daga gabanku, in fadada kan iyakarku, babu wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokutan nan uku na shekara da kuka haura don ku bayyana a gaban Ubangiji, Allahnku.
“Kada ku miƙa mini jinin hadaya tare da wani abin da yana da yisti, kada kuma ku bar kowace hadaya ta Bikin Ƙetarewa ta kwana.
“Ku kawo nunan farin amfanin gonarku mafi kyau a gidan Ubangiji, Allahnku.
“Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta waɗannan kalmomi, gama bisa ga kalmomin nan, na yi alkawari da kai da kuma Isra’ila.” Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.
Fuskar Musa mai haske
Sa’ad da Musa ya sauko daga kan Dutsen Sinai tare da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa, bai san cewa fuskarsa tana ƙyalli ba saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji. Da Haruna da dukan Isra’ila suka ga Musa, fuskarsa kuma tana ƙyalli, sai suka ji tsoron zuwa kusa da shi. Amma Musa ya kira su, sai Haruna da dukan shugabannin jama’ar suka zo wurinsa, ya kuwa yi musu magana. Daga baya sai dukan Isra’ilawa suka zo kusa da shi, ya kuma ba su dukan dokokin da Ubangiji ya ba shi a Dutsen Sinai.
Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa. Amma duk sa’ad da ya je gaban Ubangiji don yă yi magana da shi, sai yă tuɓe lulluɓin har sai ya fito. Kuma duk sa’ad da ya fito yă faɗa wa Isra’ilawa abin da aka umarce shi, sai su ga fuskarsa tana ƙyalli. Sa’an nan Musa yă sāke lulluɓe fuskarsa, har sai ya shiga don yă yi magana da Ubangiji.
Ƙa’idodin Asabbaci
Musa ya tara dukan jama’ar Isra’ilawa ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku, ku yi. Kwana shida za ku yi aiki, amma rana ta bakwai za tă zama rana mai tsarki, Asabbaci ne na hutu ga Ubangiji. Duk wanda ya yi aiki a wannan rana dole a kashe shi. Kada ku hura wuta a cikin duk mazauninku a ranar Asabbaci.”
Kayayyaki don tabanakul
([Fitowa 25.1-9]; [35.10-19])
Musa ya ce wa dukan jama’ar Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta. Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta,
“zinariya, azurfa da tagulla;
shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin,
da gashin akuya;
fatun rago da aka rina ja, da fatun shanun teku; da itacen ƙirya
da man zaitun don fitila; da kayan yaji don man shafewa, da kuma turare mai ƙanshi;
duwatsun onis, da sauran duwatsu masu daraja waɗanda za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
“Duk waɗanda suke da fasaha a cikinku, su zo su yi dukan abin da Ubangiji ya umarta,
“wato, aikin tabanakul da tentinsa tare da murfinsa, maɗauransa, katakansa, sandunansa da tussansa;
akwatin alkawari da sandunansa, murfin kafara da labulen da ya rufe shi;
tebur da sandunansa, da dukan kayansa da kuma burodin kasancewa;
wurin ajiye fitila da yake don fitilu da kayayyakinsa, fitilu da mai don fitila;
bagaden turare da sandunansa, man shafewa da turare mai ƙanshi; da labulen ƙofar shiga tabanakul;
bagaden hadaya ta ƙonawa da rigarsa ta tagulla da sandunansa da duk kayayyakinsa, daron tagulla da wurin ajiye shi.
Labulen filin tenti da sandunansa da tussansa, da kuma labulen ƙofar shiga fili;
turakun tenti don tabanakul da kuma don filin, da igiyoyinsu;
saƙaƙƙun riguna na sawa don hidima cikin wuri mai tsarki da tsarkakakkun riguna na Haruna firist, da riguna don ’ya’yansa maza lokacin da suke aiki a matsayin firistoci.”
Sai dukan jama’ar Isra’ilawa suka janye daga fuskar Musa, duk waɗanda suke da niyya, waɗanda kuma zukatansu suka motsa su, suka kawo kyautai wa Ubangiji, don aikin Tentin Sujada, don duk aikinsa, da don tsarkakakkun riguna. Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji. Kowane mutumin da yake da shuɗi, shunayya ko jan zare, ko lallausan lilin, ko gashin akuya, ko fatun rago da aka rina ja, ko fatun shanun teku, suka kawo. Masu miƙa kyautar azurfa, ko tagulla suka kawo su a matsayin kyautai ga Ubangiji, kuma kowane mutumin da yake da itacen ƙirya don kowane sashin aikin, ya kawo. Kowace mace mai fasaha ta kaɗa zare da hannuwanta, ta kuma kawo abin da ta kaɗa na shuɗi, shunayya, ko jan zare, ko lallausan lilin. Kuma dukan matan da suke da niyya, suke kuma da fasaha, suka kaɗa gashin akuya. Shugabannin suka kawo duwatsun Onis. Da duwatsu masu daraja don a jera a kan efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka kawo kayan yaji da man zaitun don fitila da don man shafewa da kuma don turare mai ƙanshi. Dukan mazan Isra’ilawa da matan da suke da niyya suka kawo wa Ubangiji kyautai na yardar rai, domin dukan aikin da Ubangiji ya umarce su ta bakin Musa.
Bezalel da Oholiyab
([Fitowa 31.1-11])
Sa’an nan ya ce wa Isra’ilawa, “Duba Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, daga kabilar Yahuda, ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu, don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla. Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta. Ya kuma ba Bezalel da Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan, iyawa don koya wa waɗansu. Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne.
Saboda haka Bezalel, Oholiyab da kowane mutumin da Ubangiji ya ba shi basira da iyawa, na sanin yadda za a yi duk aikin shirya wuri mai tsarki, za su yi aiki yadda Ubangiji ya umarta.”
Sa’an nan Musa ya kira Bezalel da Oholiyab da kowane mutumin da Ubangiji ya ba shi iyawa da kuma wanda ya yi niyya yă yi aiki. Suka karɓa daga wurin Musa dukan kyautai da Isra’ilawa suka kawo don su yi aikin shirya wuri mai tsarki. Mutane suka ci gaba da kawo kyautai yardar rai kowace safiya. Sai dukan masu fasaha waɗanda suke aikin wuri mai tsarki suka ɗan dakata suka ce wa Musa, “Mutane suna kawo fiye da abin da ake bukata domin aikin da Ubangiji ya umarta a yi.”
Sai Musa ya ba da umarni, suka aika ko’ina a cikin sansani cewa, “Kada namiji ko ta mace yă sāke kawo kyauta don wuri mai tsarki.” Ta haka mutane suka daina kawowa. Saboda abin da suke da shi ya fi abin da ake bukata domin aikin.
Tabanakul
([Fitowa 26.1-14])
Dukan maza masu fasaha a cikin sauran masu aikin suka yi tabanakul da labule goma na tuƙaƙƙun lallausan lilin na shuɗi, da shunayya, da jan zare, aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta. Tsawon kowane labule, kamu ashirin da takwas ne, fāɗinsa kuma kamu huɗu. Dukan labulen, girmansu ɗaya ne. Suka ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, suka kuma yi haka da sauran labule biyar ɗin. Suka yi rami a gefe-gefen labulen da zaren ruwan bula, haka kuma suka yi da ɗayan gefen na biyu ɗin. Suka kakkafa rammuka hamsin a daidai bakin labulen, haka kuma suka yi a kan labule na biyun. Haka aka ɗaɗɗaura rammukan nan da junansu yă zama kamar abu guda. Sa’an nan suka yi maɗaurai hamsin na zinariya, suka yi amfani da su don daurin kashi biyu na labulen saboda tabanakul yă zama ɗaya.
Suka yi labule da gashi akuya goma sha ɗaya don tenti a bisa tabanakul. Dukan labule goma sha ɗayan girmansu ɗaya ne, tsawonsa kamu talatin, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Suka harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, suka kuma harhaɗa shida wuri ɗaya. Sa’an nan suka yi rammuka hamsin a gefen labule na kashe na farko, haka kuma a gefen labule na ƙarshen na kashi biyar. Suka yi maɗaurin tagulla hamsin don su ɗaura tenti yă zama ɗaya. Sai suka yi wa tentin murfi da fatun rago da aka rina ja, a bisa wannan kuwa akwai murfin fatun shanun teku.
([Fitowa 26.15-30])
Suka yi katakan tabanakul da itacen ƙirya. Tsawon kowane katako kamu goma ne, kaurinsa kuma kamu ɗaya da rabi, tare da katakai a fiƙe ɗaura da juna. Haka suka yi da dukan katakan tabanakul. Suka yi katakai ashirin don gefen kudu na tabanakul suka kuma yi rammukan azurfa arba’in don katakan su shiga ƙarƙashinsu, rammuka biyu domin kowane katako, ɗaya ƙarƙashin kowanne da aka fiƙe. A ɗaya gefen, gefen arewa na tabanakul, suka yi katakai ashirin da rammuka arba’in na azurfa, biyu-biyu don kowane katako. Suka yi katako shida don iyaka ta ƙarshe, wato, gefen yamma na tabanakul, aka kuma yi katakai biyu domin kusurwoyi tabanakul a iyaka ta ƙarshe. A waɗannan kusurwoyi biyu, an ninka katakan sau biyu daga ƙasa har sama, aka kuma sa su cikin zobe guda; dukansu biyu an yi su daidai. Ta haka aka sami katakai takwas da rammukan azurfa goma sha shida, biyu-biyu a ƙarƙashin kowane katako.
Suka kuma yi sanduna na itace ƙirya, biyar domin katakan da suke a gefe guda na tabanakul, biyar domin waɗanda suke ɗayan gefen da kuma biyar domin katakan da suke gefen yamma na iyaka ta ƙarshen tabanakul. Suka sa sandan da yake a tsakiya yă wuce daga wannan gefe zuwa wancan. Sai suka dalaye katakan da zinariya, suka yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Suka kuma dalaye sandunan da zinariya.
([Fitowa 26.31-37])
Suka kuma yi labule da shuɗi, shunayya, jan zare, da kuma lallausan lilin, suka kuma yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta. Suka yi dogayen sanduna huɗu na itacen ƙirya dominsa, suka dalaye su da zinariya. Suka yi ƙugiya na zinariya dominsa, suka yi rammuka huɗu da azurfa. Suka yi wa ƙofar tenti labulen shuɗi, shunayya, jan zare, da kuma lallausan lilin, aikin gwaninta; suka kuma yi dogayen sanduna biyar da ƙugiya dominsu. Suka dalaye saman dogayen sandunan da abin daurinsu da zinariya, suka kuma yi rammukansu guda biyar da tagulla.
Akwatin alkawari
([Fitowa 25.10-22])
Bezalel ya yi akwatin alkawari da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi. Ya dalaye shi da zinariya zalla, ciki da waje, ya kuma yi zubin zinariya kewaye da shi. Ya yi masa zubi huɗu na zoban zinariya, ya kuma ɗaura su a ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a wannan gefe da kuma biyu a wancan. Sa’an nan ya yi sanduna na itacen ƙirya, ya dalaye shi da zinariya. Sai ya sa sandunan a cikin rammukan da suke gefen Akwatin don ɗaukarsa.
Ya yi murfin jinƙai da zinariya zalla, wato, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi. Sa’an nan ya yi kerubobi biyu da ƙeraren zinariya a ƙarshen murfin jinƙan. Ya yi kerub a iyakar gefe ɗaya, ya yi ɗayan kuma a wancan gefe; a iyakan nan biyu, ya yi su a haɗe da murfin. Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwatar da murfin da fikafikansu. Kerubobin suna fuskantar juna, suna kuma kallon murfin.
Tebur
([Fitowa 25.23-30])
Suka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa ƙafa ɗaya, tsayinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi. Sa’an nan suka dalaye shi da zinariya zalla, suka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi. Suka kuma yi masa baki mai fāɗin tafi hannu, suka yi zubin zinariya a bisa bakin. Suka yi zubin zobai huɗu na zinariya don tebur ɗin, sai suka ɗaura su a kusurwoyi huɗu inda ƙafafu huɗun suke. Sa’an nan aka sa zoban kurkusa da bakin don riƙe sandunan da ake amfani da su wurin ɗaukan teburin. An yi sandunan da ake ɗaukan tebur da itacen ƙirya, aka kuma dalaye su da zinariya. Suka kuma yi duk kayayyakin teburin da zinariya zalla, farantansa, kwanonin tuya, kwanoninsa, da kuma butoci domin hadaya ta sha.
Wurin ajiye fitila
([Fitowa 25.31-40])
Suka yi wurin ajiye fitila da zinariya zalla, suka yi gindinsa da kuma gorar jikinsa, da ƙerarriyar zinariya. Kwaf wurin ajiye fitila da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da wurin ajiye fitilan. Akwai rassa guda shida da suka miƙe daga gefe wurin ajiyar fitilar, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan. A reshe guda na wurin ajiye fitilan, akwai kwaf uku masu kama da tohon almon, akwai kuma uku a reshe na biye, haka kuma suke a dukan rassa shida da suke daga wurin ajiye fitilan. A bisa wurin ajiye fitilan kuma akwai kwaf huɗu da aka yi su kamar furannin almon da toho da kuma mahaɗai. Toho ɗaya yana a ƙarƙashin rassa biyu waɗanda suke daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu yana a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku kuma yana a ƙarƙashin rassa biyu na uku, duka-duka rassa shida ne. An ƙera mahaɗai da rassa wurin ajiye fitila a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi wurin ajiye fitilar da dukan komensa a haɗe.
Da zinariya zalla suka yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa. Daga talenti ɗaya na zinariya zalla suka yi wurin ajiye fitila da dukan kayayyakinsa.
Bagaden ƙona turare
([Fitowa 30.1-5])
Suka yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya. Shi bagaden, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu biyu, ƙahoninsa kuwa a haɗe suke da shi. Suka dalaye saman da dukan gefe-gefen da kuma ƙahonin da zinariya zalla, suka kuma yi zubin zinariya kewaye da shi. Suka yi zobai biyu na zinariya a ƙarƙashin zubin, biyu-biyu ɗaura da juna, don su riƙe sandunan da za a ɗauka shi. Suka yi sandunan da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da zinariya.
([Fitowa 30.22-38])
Suka kuma yi tsattsarkan mai na shafewa da kuma zalla turare mai ƙanshi, yadda mai yin turare yakan yi.
Bagaden hadaya ta ƙonawa
([Fitowa 27.1-8])
Suka gina bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba’i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku. Suka yi ƙahoni a kusurwansa huɗu, ƙahonin da bagade a haɗe suke, suka kuma dalaye bagaden da tagulla. Da tagulla kuma ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta. Suka yi wa bagaden raga, tagulla kuma don yă sa shi a tsakiya. Suka yi zubin zoban tagulla don riƙe sanduna a kusurwoyi huɗu na ragar tagullar. Suka yi sanduna da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da tagulla. Suka sa sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefen bagade don ɗaukarsa, suka yi rami cikinsa.
Kwano don wanki
([Fitowa 30.18-21])
Suka yi daro da gammonsa da tagulla daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar Tentin Sujada.
Filin tabanakul
([Fitowa 27.9-19])
Suka kuma yi filin Tentin Sujada. Suka yi labulanta na gefen kudu da lallausan lilin, tsawonsu kamu ɗari, da sanduna ashirin da rammukan sandunan tagulla ashirin, da kuma ƙugiyoyin azurfa da maɗauri a kan sandunan. Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne, yana kuma da sanduna guda ashirin da rammuka ashirin na tagulla, da ƙugiyoyin azurfa da maɗaurai a kan sandunan.
Labule na gefen yamma kamu hamsin, da sanduna guda goma, da rammuka guda goma, da ƙugiyoyin azurfa da maɗaurai a kan sandunan. A ƙarshen gefen gabas, wajen fitowar rana, shi ma fāɗinsa kamu hamsin ne. Labule na gefe ɗaya na ƙofar, kamu goma sha biyar ne, da sanduna guda uku da rammukansu, akwai labule mai kamu goma sha biyar a ɗayan gefen ƙofar shiga zuwa filin Tentin Sujada, da sanduna uku da rammuka uku. An yi dukan labulan da suke kewaye da filin Tentin Sujada da lallausan zaren lilin. An yi rammukan sandunan da tagulla. An dalaye ƙugiyoyi da maɗauran da suke kan sandunan da azurfa; saboda haka dukan sandunan filin Tentin Sujada suna da maɗaurai na azurfa.
Aka yi wa labulen ƙofar filin Tentin Sujada ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwaninta. Tsawonsa kamu ashirin, kuma kamar yadda labulen filin Tentin Sujada suke, tsayinsa kamu biyar ne, da sanduna guda huɗu da rammuka guda huɗu na tagulla. Ƙugiyoyinsu da maɗauransu na azurfa ne, aka kuma dalaye bisansu da azurfa. Aka yi dukan ƙarafan kafa tabanakul da kuma na kewayen filin Tentin Sujada da tagulla ne.
Kayayyakin da aka yi amfani da su
Waɗannan su ne kayayyakin da aka yi amfani da su domin aikin tabanakul, da tabanakul na Shaida, waɗanda aka rubuta bisa ga umarnin Musa ta wurin Lawiyawa, a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna, firist. (Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa; tare da shi akwai Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, shi gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin.) Jimillar zinariya daga hadaya ta kaɗawar da aka yi amfani da su domin aikin wuri mai tsarki ta kai talenti 29 da shekel 730, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama’a, talenti 100 ne, da shekel 1,775, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri. Duk mutumin da ya shiga ƙirge daga mai shekaru ashirin zuwa gaba, ya ba da rabin shekel. Mazan da suka shiga ƙirge sun kai mutum 603,550. An yi amfani da azurfa talenti 100 don yin rammuka na wuri mai tsarki, da kuma rammukan labule, rammuka 100 daga talenti 100, talenti ɗaya don rami ɗaya. Suka yi amfani da shekel 1,775 don yin ƙugiyoyi saboda sanduna, suka dalaye bisan sandunan da maɗauransu.
Tagullar da aka bayar daga hadaya ta kaɗawa ya kai talenti 70 da shekel 2,400. Suka yi amfani da shi don yin rammukan ƙofar Tentin Sujada, da bagaden tagulla tare da ragar tagulla da dukan kayayyakinsa, da rammukan sanduna don kewaye filin, da waɗanda suke ƙofarsa, da dukan ƙarafan kafa tenti don tabanakul, da kuma don kewaye filin.
Rigunan firistoci
([Fitowa 28.1-14])
Daga zare mai ruwan shuɗi, da shuɗayya da kuma jan zare suka yi tsarkaken rigunan domin hidima a wuri mai tsarki. Suka kuma yi tsarkaken riguna don Haruna, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Efod
Suka yi efod na zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da kuma lallausan lilin. Suka bubbuga zinariya ta zama falle, suka yayyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita, tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha. Suka yi wa efod kafaɗu, sa’an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama, don a iya ɗaurawa. Gwanin mai saƙa ya saƙa abin ɗamarar efod. Da irin kayan da aka saƙa efod ne aka saƙa abin ɗamarar, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da zaren lallausan lilin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Suka shimfiɗa duwatsun onis, suka jera su cikin tsaiko na zinariya, suka kuma zāna sunayen ’ya’yan Isra’ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi. Sa’an nan suka ɗaura su a ƙyallen kafaɗun efod a matsayin duwatsun tuni wa ’ya’yan Isra’ila, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Ƙyallen maƙalawa a ƙirji
([Fitowa 28.15-30])
Suka yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, aikin gwani. Suka yi shi kamar efod, na zinariya, da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da kuma na lallausan lilin. Ƙyallen maƙalawa a ƙirjin murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya-ɗaya ne. Sa’an nan suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na farko akwai yakutu, da tofaz, da zumurrudu; a jeri na biyu akwai turkuwoyis, da saffaya, da daimon; a jeri na uku akwai yakinta, da idon mage, da ametis; a jeri na huɗu akwai beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya. Aka zāna duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowane sunan ’ya’yan Isra’ila goma sha biyu, kamar yadda akan yi hatimi.
Sai suka yi tuƙaƙƙun sarƙoƙi na zinariya zalla a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka yi tsaiko biyu na zinariya da zoban zinariya biyu, suka kuma ɗaura zoban a kusurwoyi biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka ɗaura sarƙoƙi biyu na zinariya da kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa’an nan suka rataya su a kafaɗun efod daga gaba. Suka yi zobai biyu na zinariya suka haɗa, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da efod. Sa’an nan suka yi waɗansu ƙarin zobai biyu na zinariya, suka maƙale su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na efod kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar efod. Suka ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a zoban efod da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar efod don kada yă kunce daga efod, sun yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Sauran rigunan firistoci
([Fitowa 28.31-43])
Suka kuma saƙa taguwa ta efod da shuɗi duka, aikin gwani mai saƙa, an yi wa taguwar wuyan wundi a tsakiya kamar sulke, aka daje wuyan don kada yă kece. Suka yi fasalin ’ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da lallausan lilin kewaye da gefe-gefen taguwar. Suka yi ƙararrawa da zinariya zalla, suka sa su a tsakanin fasalin ’ya’yan rumman kewaye da gefe-gefen taguwa. Aka jera ƙararrawan da ’ya’yan rumman bi da bi. Haka aka jera su kewaye da gefe-gefen taguwar aiki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Suka saƙa doguwar riga da lallausan lilin don Haruna da ’ya’yansa, aikin gwani mai saƙa, suka yi rawanin da lallausan lilin, da hulan lilin da rigunan ciki na lallausan lilin. Suka yi abin ɗamara da lallausan lilin da shuɗi, shunayya da jan zare, aikin gwanin mai ɗinki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa, suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka,
Mai tsarki ga Ubangiji.
Sa’an nan suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Musa ya duba tabanakul
([Fitowa 35.10-19])
Ta haka aka gama dukan aikin tabanakul da Tentin Sujada. Isra’ilawa suka yi kome yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Sa’an nan suka kawo wa Musa tabanakul, tentin da dukan kayayyakinsa, ƙugiyoyinsa, katakansa, da sandunansa, da dogayen sandunansa da rammukansa;
murfi na fatun rago wanda aka rina ja, da murfi na fatun shanun teku; da kuma laɓulen
akwatin Alkawari da sandunansa da murfin kafara;
tebur da dukan kayayyakinsa, da burodin Kasancewa;
wurin ajiye fitilu na zinariya zalla, da jerin fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,
bagade na zinariya, da man shafewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar shiga tenti,
bagade na tagulla na raga, da sandunansa da kayan aikinsa; da daro da wurin ajiyarsa,
labulen filin, sandunansa da rammukansa, labulen ƙofar shiga filin; igiyoyi da ƙarafan kafa filin; dukan kayan aikin tabanakul da Tentin Sujada;
da kuma saƙaƙƙun rigunan da ake sawa don hidima a wuri mai tsarki, duk da tsarkakan riguna na Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci.
Isra’ilawa suka yi dukan aikin nan yadda Ubangiji ya umarci Musa. Musa ya duba aikin, sai ya ga cewa sun yi shi daidai yadda Ubangiji ya umarta. Sai Musa ya sa musu albarka.
Kafawa tabanakul
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari. Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule. Ka shigar da teburin ka shirya kayayyakin a kansa. Sa’an nan ka shigar da wurin ajiye fitilan ka kuma sa fitilunsa. Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul.
“Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada; ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa. Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin.
“Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake. Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki. Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.
“Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa. Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist. Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi. Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.” Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji ya umarce shi.
Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu. Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan. Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa. Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen. Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul. Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki, a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu. Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.
Ɗaukakar Ubangiji
Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul. Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul.
Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul. Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi. Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.