- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Esta
Esta
Esta
Esta
Esta
An tumɓuke sarauniya Bashti
Ga abin da ya faru a zamanin Zerzes.1.1 Da Ibraniyanci Ahasuwerus; a nan da kuma a dukan littafin Esta. Zerzes ya yi mulki bisan larduna 127 daga Indiya zuwa Kush. A lokacin nan, Sarki Zerzes ya yi mulki daga gadon sarauta, cikin mazaunin masarautar Shusha. A shekara ta uku ta mulkinsa, ya yi wa dukan hakimansa da ma’aikatansa liyafa. Shugabannin mayaƙan Farisa, da Mediya, da yerimai; da kuma hakimai na lardunan suka kasance.
Kwanaki 180 cif, ya nuna yawan dukiyar masarautarsa, da ɗaukakarta da kuma darajar girmansa. Sa’ad da waɗannan kwanaki suka wuce, sai sarki ya yi liyafa a cikin lambun da aka shinge na fadar sarki wadda ta ɗauki kwana bakwai wa dukan mutane daga ƙarami har zuwa babba, waɗanda suke zama a masarautar Shusha. Lambun yana da fararen labulen da aka rataye da shunayya na lallausan lilin, da aka ɗaura da igiyoyin fararen lilin, da yadin jan garura, haɗe da zoban azurfa a kan ginshiƙin farin ƙasa. A nan, akwai kujeru na zinariya da na azurfa a kan daɓe mai ado da aka yi da duwatsu masu daraja, da farin ƙasa, da fararen duwatsun wuya, da waɗansu duwatsu masu tsada. Aka rarraba ruwan inabi cikin kwaf na zinariya, kowanne kuwa dabam yake da ɗayan. Ruwan inabin kuwa yana da yawa, bisa ga wadatar sarki. Bisa ga umarnin sarki, aka bar kowane baƙo yă sha yadda ya ga dama, gama sarki ya umarci dukan bayin da suke rarraba ruwan inabin su ba wa kowa abin da yake so.
Sarauniya Bashti ita ma ta yi liyafa saboda mata a fadar Sarki Zerzes.
A rana ta bakwai, sa’ad da Sarki Zerzes, ya yi tilis da ruwan inabi, sai ya umarci bābānni bakwai waɗanda suke yin masa hidima, wato, Mehuman, Bizta, Harbona, Bigta, Abagta, Zetar da Karkas, su kawo Sarauniya Bashti a gabansa, sanye da rawanin sarautarta, don ta nuna kyanta wa mutane da kuma hakimai, gama ita kyakkyawa ce ƙwarai. Amma da masu hidima suka ba da umarnin sarki, sai Sarauniya Bashti ta ƙi zuwa. Wannan ya ɓata wa sarki rai, ya kuma yi fushi ƙwarai.
Da yake, al’ada ce sarki yă nemi shawara daga sanannu a batun doka da adalci, sai ya yi magana da masu hikima waɗanda suke fahimtar lokuta suke kuma mafi kusa da sarki. Waɗannan masu hikima kuwa su ne, Karshena, Shetar, Admata, Tarshish, Meres, Marsena da kuma Memukan. Su hakimai bakwai ne na Farisa da Mediya waɗanda suke da dama ta musamman ta kaiwa ga sarki, suke kuma da matsayi mafi girma a masarautar.
Ya ce, “Bisa ga doka, me za a yi wa Sarauniya Bashti? Gama ta ƙi yin biyayya da umarnin sarki Zerzes da bābānni suka kai mata?”
Sai Memukan ya amsa a gaban sarki da hakimai ya ce, “Sarauniya Bashti ta yi laifi, ba ga sarki kaɗai ba, amma ga dukan hakimai ma, da kuma mutanen dukan lardunan sarki Zerzes. Domin halin Sarauniya zai zama sananne ga dukan mata, ta haka kuwa za su ƙasƙantar da mazansu su kuma ce, ‘Sarki Zerzes ya umarta a kawo Sarauniya Bashti a gabansa, amma ta ƙi zuwa.’ Wannan rana matan hakiman Farisa da na Mediya waɗanda suka ji game da halin sarauniya, za su yi haka wa dukan hakiman sarki. Zai zama babu ƙarshen rashin bangirma da kuma reni.
“Saboda haka, in ya gamshi sarki, bari yă ba da hatimi na sarauta, bari kuma a rubuta shi cikin dokokin Farisa da Mediya, wanda ba za a iya sokewa ba, cewa Bashti ba za tă ƙara zuwa gaban sarkin Zerzes ba. Bari kuma sarki yă ba da matsayinta na sarauta ga wata, wadda ta fi ta. Ta haka, sa’ad da aka yi shelar dokar sarki ko’ina a fāɗin masarautarsa, dukan mata za su ba wa mazansu girma, daga ƙarami har zuwa babba.”
Sarki da hakimansa suka gamsu da wannan shawara. Saboda haka sarki ya yi kamar yadda Memukan ya faɗa. Ya aika da saƙo zuwa ga dukan ɓangarorin masarautar, zuwa ga kowane lardi a irin nasa rubutu, zuwa kuma ga kowane mutane a nasu harshe, ana shelar a kowane yare na mutane, cewa kowane mutum yă zama mai mulki bisa gidansa.
An mai da Esta sarauniya
Daga baya sa’ad da fushin Sarki Zerzes ya huce, sai ya tuna da Bashti da abin da ta yi, da kuma dokar da ya bayar game da ita. Sai masu hidimar sarki na musamman, suka kawo shawara cewa, “Bari a nemi, kyawawan budurwai saboda sarki. Bari sarki yă naɗa komishinoni a kowane yanki na masarautarsa, domin su kawo dukan waɗannan kyawawan ’yan mata cikin harabar mazaunin masarautar a Shusha. Bari a sa su a hannun Hegai, bābān sarki, wanda yake lura da mata, bari kuma a yi musu kulawa ta musamman. Sa’an nan bari yarinyar da ta gamshi sarki, tă zama sarauniya a maimakon Bashti.” Wannan shawara ta gamshi sarki, ya kuwa yi na’am da ita.
To, a cikin mazaunin masarauta a Shusha, akwai wani mutumin Yahuda, daga Kabilar Benyamin mai suna Mordekai, ɗan Yayir, ɗan Shimeyi, ɗan Kish, wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ɗauka tare ’yan zaman bauta cikin waɗanda ya ɗauko daga Urushalima, tare da Yekoniya, sarkin Yahuda. Mordekai yana da wata ’yar kawunsa mai suna Hadassa, wanda ya yi reno, ba ta da mahaifi ko mahaifiya. Ita ce yarinyar da aka santa da suna Esta. Kyakkyawa ce ƙwarai. Mordekai dai ya ɗauke ta tamƙar ’yarsa sa’ad da mahaifinta da mahaifiyarta suka mutu.
Da aka yi shelar umarni da dokar sarki, sai aka kawo ’yan mata masu yawa a mazaunin masarauta a Shusha, aka kuma sa su ƙarƙashin kulawar Hegai. Aka kawo Esta ma zuwa fadar sarki, aka danƙa ta wa Hegai, wanda yake lura da mata. Yarinyar ta gamshe shi, ta kuma sami tagomashinsa. Nan da nan ya tanada mata, ya ba ta man shafawa da abinci na musamman. Ya ba ta bayi mata bakwai da aka zaɓa daga fadar sarki. Ya kuma kai ta tare da bayinta zuwa wuri mafi kyau na gidan matan kulle.
Esta ba tă bayyana asalin al’ummarta da na iyalinta ba, domin Mordekai ya hana yin haka. Kowace rana Mordekai yana kai da komowa kusa da harabar filin gidan matan kulle, domin ya san yadda Esta take, da kuma abin da yake faruwa da ita.
Kafin a kai kowace yarinya wurin Sarki Zerzes, sai ta gama watanni goma sha biyu cif ana yin mata kwalliyar da aka tsara, akan ɗauki watanni shida ana shafa mata man mur, a ɗauki watanni shida kuma ana shafa mata man ƙanshi da kayan shafe-shafe. A kuma koya mata yadda za tă tafi wurin sarki. Aka ba ta duk abin da take so ta riƙe daga gidan matan kulle zuwa fadar sarki. Da yamma za tă tafi can, da safe kuma ta dawo wani ɓangaren gidan matan kullen da yake a ƙarƙashin kulawar Sha’ashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwarƙwarai. Ba ta dawowa wurin sarki sai in ta gamshe shi, sai ya kuma kira ta da suna.
Sa’ad da lokaci ya yi da Esta (yarinyar da Mordekai ya ɗauka tamƙar ’yarsa, ’yar kawunsa Abihayil) za tă shiga wurin sarki, ba tă nemi a ba ta kome ba in ban da abin da Hegai, bābān sarki mai lura da gidan matan kulle, ya ba da shawara. Esta kuwa ta sami tagomashin kowa da ya ganta. Aka kai Esta wurin Sarki Zerzes a mazaunin sarauta a wata na goma, watan Tebet, a shekara ta bakwai ta mulkinsa.
To, sarki ya so Esta fiye da duk sauran matan, ta kuma sami tagomashinsa da kuma yardarsa fiye da duk sauran budurwai. Saboda haka ya sa rawanin sarauta a kanta, ya kuma mai da ita sarauniya a maimakon Bashti. Sarki kuwa ya yi ƙasaitacciyar liyafa, liyafar Esta, wa dukan hakimansa da shugabannin masarautarsa. Ya yi shelar hutu ko’ina a larduna, ya kuma raba kyautai a yalwace irin na sarauta.
Mordekai ya gano maƙarƙashiya
Sa’ad da aka tara budurwai karo na biyu, Mordekai kuwa yana zama a bakin ƙofar sarki. Amma Esta ta ɓoye asalin iyalinta da na al’ummarta yadda Mordekai ya ce ta yi, gama ta ci gaba da bin umarnan Mordekai yadda take yi sa’ad da yake renonta.
Sa’ad da Mordekai yake zaune a bakin ƙofar sarki, sai Bigtana da Teresh, biyu daga cikin hafsoshin sarki masu gadin ƙofar shiga, suka yi fushi, suka kuma ƙulla su kashe sarki Zerzes. Mordekai kuwa ya sami labarin makircin, ya kuma faɗa wa Sarauniya Esta, wadda ta faɗa wa sarki, ta kuma nuna masa cewa Mordekai ne ya ji. Sa’ad da aka bincika labarin aka kuma iske gaskiya ne, sai aka rataye hafsoshin nan biyu a wurin rataye mai laifi. Aka rubuta dukan wannan a cikin littafin tarihi a gaban sarki.
Makircin Haman na neman yă hallaka Yahudawa
Bayan waɗannan al’amura, sai Sarki Zerzes ya girmama Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya ɗaukaka shi, ya kuma ba shi matsayi mafi girma fiye da na dukan sauran hakiman. Dukan masu hidimar da suke a ƙofar sarki suka riƙa durƙusa suna ba wa Haman girma, gama sarki ya ba da umarni a yi masa haka. Amma Mordekai bai durƙusa ya ba shi girma ba.
Sa’an nan masu hidimar da suke a ƙofar sarki suka tambaye Mordekai, “Me ya sa ba ka yin biyayya da umarnin sarki?” Kowace rana suna masa magana, amma ya ƙi yă yi. Saboda haka, suka faɗa wa Haman game da wannan don su ga ko za a jure da halin Mordekai, gama ya faɗa musu cewa shi mutumin Yahuda ne.
Sa’ad da Haman ya ga cewa Mordekai ba ya durƙusa ko yă girmama shi, sai ya fusata. Da yake an faɗa masa asalin Mordekai, sai ya ga a kashe Mordekai kaɗai ba zai biya masa bukata ba. A maimakon haka, Haman ya nemi hanya a hallaka dukan mutanen Mordekai, wato, Yahudawa, a ko’ina a dukan masarautar Zerzes.
A shekara ta goma sha biyu ta Sarki Zerzes, a wata na farko, watan Nisan, sai suka jefa fur (wato, ƙuri’a) a gaban Haman don a zaɓi rana da watan da zai dace da ƙulle-ƙullen. Sai ƙuri’a ta fāɗa a kan wata na goma sha biyu, wato, watan Adar.
Sai Haman ya ce wa Sarki Zerzes, “Akwai waɗansu mutanen da suke a warwatse, sun kuma bazu a cikin mutane cikin dukan lardunan masarautarka, waɗanda al’adunsu sun yi dabam da na dukan sauran mutane. Mutanen nan ba sa biyayya da dokokin sarki; ba zai yi wa sarki kyau a jure su ba. In ya gamshi sarki, bari a yi doka, don a hallaka su, zan kuma sa talenti dubu goma na azurfa a cikin ma’ajin fada saboda mutanen da suka aikata wannan sha’ani.”
Saboda haka sarki ya zare zoben hatimi daga yatsarsa, ya ba wa Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban Yahudawa. Sarki ya ce wa Haman, “Ka riƙe kuɗin, ka kuma yi da mutanen yadda ka ga dama.”
Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa. Aka aika ’yan-kada-tă-kwana da saƙoni zuwa dukan lardunan sarki da umarni a hallaka, a karkashe, a kuma kawar da dukan Yahudawa, manya da ƙanana, mata da yara, a kuma washe kayayyakinsu. Za a ba da kofin rubutun a matsayin doka a kowane lardi, a kuma sanar da mutanen kowace al’umma, domin su zauna da shiri don wannan rana.
Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan-kada-tă-kwana, suka tafi da sauri. Aka ba da umarni a mazaunin masarauta da yake a Shusha. Sai Sarki da Haman suka zauna don su sha, amma birnin Shusha ya ruɗe.
Mordekai ya lallashi Esta ta taimaka
Sa’ad da Mordekai ya sami labari game da dukan abin da aka yi, sai ya yayyage rigunansa, ya sanya tsummokin makoki, ya zuba toka a kā, ya kuma shiga ciki birni yana kuka mai zafi da ƙarfi. Amma ya kai bakin ƙofar sarki ne kawai, gama ba a yarda wani sanye da tsummokin makoki yă shiga cikin birni ba. Aka yi makoki sosai da azumi, da kuka mai zafi a cikin Yahudawa a kowane lardin da aka kai doka da kuma umarnin sarki. Mutane da yawa suka kwanta a cikin tsummokin makoki da kuma toka.
Sa’ad da bayi da bābānnin Esta suka zo suka faɗa mata game da Mordekai, sai ta damu ƙwarai. Ta aika masa da riguna domin yă sa a maimakon tsummokin makoki, amma ya ƙi. Sai Esta ta kira Hatak, ɗaya daga cikin bābānnin sarkin da aka ba shi aikin lura da ita, ta umarce shi yă yi tambaya me ke damun Mordekai da kuma me ya jawo haka.
Saboda haka Hatak ya tafi wurin Mordekai a dandalin birni, a gaban ƙofar sarki. Mordekai ya faɗa masa duk abin da ya faru da shi, haɗe da yawan kuɗin da Haman ya yi alkawari zai zuba a ma’ajin fada don a hallaka Yahudawa. Ya kuma ba shi kofi na rubutaccen doka na kakkaɓe su, wanda aka wallafa a Shusha don yă nuna wa Esta, yă bayyana mata. Mordekai ya faɗa wa Hatak yă iza ta tă tafi gaban sarki domin tă yi roƙo don jinƙai, tă kuma roƙe shi saboda mutanenta.
Hatak ya koma ya ba wa Esta rahoton abin da Mordekai ya faɗa. Sa’an nan Esta ta umarce Hatak yă ce wa Mordekai, “Dukan hafsoshin sarki da mutanen lardunan sarki sun san cewa duk wanda ya tafi wurin sarki a shirayi na ciki, mace ko namiji, ba tare da an kira shi ba, doka ɗaya ce take kan mutum, wato, kisa. Abu guda kawai da ya sha bamban shi ne sai wanda sarki ya miƙa wa sandan sarauta na zinariya don yă rayu. Kwana talatin ke nan ba a kira ni in tafi wurin sarki ba.”
Sa’ad da aka kai wa Mordekai rahoton maganan Esta, sai ya mayar da wannan amsa wa Esta cewa, “Kada ki yi tsammani cewa don kina a cikin gidan sarki, ke kaɗai cikin dukan Yahudawa za ki tsira. Gama in kin yi shiru a wannan lokaci, taimako da ceto zai zo daga wani wuri saboda Yahudawa, amma ke da gidanki za ku hallaka. Wa ya san ko saboda irin wannan lokaci ne kika sami wannan muƙami?”
Sai Esta ta aika da wannan amsa ga Mordekai cewa, “Ka tafi, ka tattara dukan Yahudawan da suke Shusha, ku yi azumi saboda ni. Kada ku ci ko ku sha, dare da rana har kwana uku. Ni kuwa da bayina za mu yi azumi yadda kuke yi. Idan aka yi haka, zan tafi wurin sarki, ko da yake wannan karya doka ce. Idan na hallaka, to, na hallaka.”
Saboda haka, Mordekai ya tafi, ya aikata dukan umarnan Esta.
Roƙon Esta ga sarki
A rana ta uku, Esta ta sanya rigunanta na sarauta, ta tafi ta tsaya a harabar fada, a gaban zaure sarki. Sarki yana zaune a kan gadon sarautarsa a zauren, yana fuskantar ƙofar shiga. Sa’ad da ya ga Sarauniya Esta tsaye a harabar, sai ya ji daɗin ganinta, ya miƙa mata sandan sarauta na zinariya da take hannunsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan.
Sai sarki ya ce mata, “Me kike so, Sarauniya Esta? Mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.”
Esta ta ce, “In ya gamshi sarki, bari sarki, tare da Haman su zo wurin liyafar da na shirya wa sarki yau.”
Sai sarki ya ce, “Maza a kawo Haman don mu yi abin da Esta ta roƙa.”
Saboda haka, sarki da Haman suka tafi liyafar da Esta ta shirya. Yayinda suke shan ruwan inabi, sarki ya sāke ce wa Esta, “Yanzu, mece ce bukatarki? Za a biya miki shi. Kuma mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.”
Esta ta amsa ta ce, “Bukatata da kuma roƙona shi ne, in na sami tagomashi a wurin sarki, in kuma sarki ya yarda yă biya mini bukatata, yă kuma ji roƙona, bari sarki da Haman su zo gobe wurin liyafar da zan shirya musu. Sa’an nan zan amsa tambayar sarki.”
Fushin Haman a kan Mordekai
Haman ya fita a ranan da murna, ya kuma ji daɗi. Amma sa’ad da ya ga Mordekai a bakin ƙofar sarki, ya kuma lura cewa bai tashi, ko yă nuna bangirma a gabansa ba, sai ya cika da fushi. Duk da haka, Haman ya cije, ya tafi gida.
Sai ya kira abokansa da kuma matarsa, Zeresh, ya yi ta taƙama game da ɗumbun wadatarsa, da yawan ’ya’yansa maza, da dukan yadda sarki ya girmama shi, ya kuma ɗaga shi bisan sauran hakimai da shugabanni. Haman ya ƙara da cewa, “Ba duka ke nan ba, kai, ni ne kaɗai mutumin da Sarauniya Esta ta gayyata yă tafi tare da sarki zuwa liyafar da ta shirya. Ta sāke gayyace ni tare da sarki gobe. Amma dukan wannan bai biya mini bukata ba, muddin ina ganin wannan mutumin Yahudan nan Mordekai, yana zama a bakin ƙofar sarki.”
Matarsa Zeresh, da dukan abokansa suka ce masa, “Ka sa a gina wurin rataye mai laifi, mai tsawo, ƙafa saba’in da biyar, da safe kuwa ka ce wa sarki a rataye Mordekai a kansa. Sa’an nan ka tafi cin abincin dare tare da sarki da murna.” Wannan shawarar ta faranta wa Haman rai, ya kuma sa aka gina wurin rataye mai laifi.
An girmama Mordekai
A daren nan, sarki bai iya barci ba, saboda haka ya ba da umarni a kawo, a kuma karanta masa littafin tarihi na shekara-shekara, da rubutaccen labarin mulkinsa. Aka tarar, a rubuce a ciki, cewa Mordekai ya tone ƙulle-ƙullen Bigtana da Teresh, biyu daga hafsoshin sarki, waɗanda suke tsaron mashigin ƙofa, waɗanda suka ƙulla su kashe Sarki Zerzes.
Sarki ya ce, “Wace girma da daraja ce aka ba wa Mordekai saboda wannan?”
Masu hidimarsa suka ce, “Ba a yi masa wani abu ba.”
Sarki ya ce, “Wa yake a haraba?” Daidai lokacin kuwa Haman ya shigo harabar waje na fada don yă yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a wurin rataye mai laifin da ya shirya.
Masu yi wa sarki hidima, suka amsa, “Haman yana tsaye a haraba.”
Sarki ya umarta, “A kawo shi ciki.”
Sa’an nan Haman ya shigo, sai sarki ya ce masa, “Me ya kamata a yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama?”
Haman dai ya yi tunani a ransa ya ce, “Wane ne sarki zai girmama in ba ni ba?” Sai ya amsa wa sarki cewa, “Saboda mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, bari a kawo rigar sarautar da sarki ya taɓa sawa, da kuma dokin da sarki ya taɓa hawa, wanda aka sa kambin sarauta a kai. Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’ ”
Sarki ya umarci Haman ya ce, “Tafi yanzu ka karɓi rigar da dokin, ka kuma yi yadda ka shawarta wa Mordekai, mutumin Yahudan nan, wanda yake zama a bakin ƙofar sarki. Kada ka kāsa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”
Saboda haka, Haman ya karɓo rigar da dokin. Ya sa wa Mordekai rigar, ya kuma bi da shi a kan doki ko’ina a titunan birnin, yana shela a gabansa yana cewa, “Wannan shi ne abin da ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!”
Daga baya, Mordekai ya dawo zuwa ƙofar sarki. Amma Haman ya ruga gida, kansa a rufe, saboda baƙin ciki. Ya je ya faɗa wa matarsa Zeresh, da dukan abokansa, me ya same shi.
Masu ba shi shawara, da matarsa Zeresh, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara fāɗuwa a gabansa, daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, tabbatacce za ka fāɗi a gabansa!” Suna cikin magana da shi ke nan, sai ga bābānnin sarki, suka iso suka kuma hanzarta da Haman zuwa liyafar da Esta ta shirya.
An rataye Haman
Saboda haka sarki da Haman suka tafi cin abinci wurin sarauniya Esta. Yayinda suke shan ruwan inabi a rana ta biyun nan, sai sarki ya sāke tambaya, “Sarauniya Esta, me kike so? Za a ba ki. Mene ne roƙonki? Ko da rabin masarautata ne, za a ba ki.”
Sai Sarauniya Esta ta amsa ta ce, “In na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, in kuma mai girma ya yarda, a bar ni da raina, wannan shi ne roƙona. Ka kuma sa kada a kashe mutanena, wannan ita ce bukata. Gama an sayar da ni da mutanena don a hallaka, a karkashe mu, a kuma ƙi mu. Da a ce an sayar da mu kamar bayi maza da mata ne, da na yi shiru, domin wannan zai zama abin da bai taka kara ya karye ba, har da za a dami sarki a kai.”7.4 Ko kuwa tabbatacce, gama ladar da abokin gābanmu zai bayar ba za a kwatanta da hasarar da sarki zai yi ba
Sarki Zerzes ya tambayi Sarauniya Esta ya ce, “Wane ne shi? Ina mutumin da ya yi ƙarfin halin yin wannan karambani?”
Esta ta ce, “Maƙiyi da abokin gāban, shi ne wannan mugun Haman.”
Sai Haman ya tsorota a gaban sarki da sarauniya. Sarki ya tashi cikin fushi, ya bar ruwan inabinsa, ya fita zuwa cikin lambun fada. Amma da Haman ya gane cewa sarki ya riga ya yanke shawara a kan ƙaddararsa, ya dakata domin yă roƙi sarauniya Esta saboda ransa.
Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune.
Sarki ya tā da murya da ƙarfi ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya yayinda take tare da ni a cikin gida?”
Sarki bai ma rufe baki ba, sai bayin sarki suka rufe fuskar Haman. Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar7.9 Da Ibraniyanci kamu hamsin (wajen mita 23). yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.”
Sai sarki ya ce, “Ku rataye shi a kansa!” Saboda haka suka rataye Haman a kan wurin rataye mai laifin da shi Haman ya shirya saboda Mordekai. Sa’an nan sarki ya huce.
Dokar sarki a madadin Yahudawa
A wannan rana, Sarki Zerzes ya ba wa Esta mallakar Haman, abokin gāban Yahudawa. Mordekai kuma ya zo gaban sarki, gama Esta ta faɗa yadda ta haɗa dangi da shi. Sarki ya cire zobensa na hatimi, wanda ya karɓo daga Haman ya ba Mordekai. Esta kuma ta naɗa shi a kan mallakar Haman.
Esta ta sāke roƙon sarki, ta fāɗi a ƙafafunsa tana kuka. Ta roƙe shi yă kawo ƙarshen mugun shirin nan na Haman, mutumin Agag; wanda ya shirya a kan Yahudawa. Sai sarki ya miƙa wa Esta sandan sarauta na zinariya, ta kuwa tashi ta tsaya a gabansa.
Ta ce, “In sarki ya yarda, in kuma na sami tagomashi daga gare shi, idan kuma ya gamshe shi yă yi abin da yake daidai, idan yana jin daɗina, bari a rubuta umarni a soke hukuncin saƙonin da Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya shirya ya kuma rubuta domin a hallaka Yahudawa a dukan lardunan sarki. Gama yaya zan jure da ganin masifa ta faɗa a kan mutanena? Yaya zan jure in ga an hallaka iyalina?”
Sarki Zerzes ya amsa wa Esta da Mordekai mutumin Yahuda, “Domin Haman ya kai wa Yahudawa hari, na ba da mallakarsa ga Esta, an kuma rataye shi a wurin rataye mai laifi. Yanzu ku rubuta wata doka, a sunan sarki, a madadin Yahudawa, yadda kuka ga ya fi kyau ku kuma hatimce ta da zoben hatimin sarki, gama babu takardar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce da zobensa da za a iya sokewa.”
Nan da nan aka kira magatakardun fada, a ranar ashirin da uku ga watan uku, wato, watan Siban. Suka rubuta dukan umarnan Mordekai ga Yahudawa, da kuma ga shugabanni, da gwamnoni, da hakiman larduna 127 tun daga Indiya har zuwa Kush. Aka rubuta waɗannan umarnan a rubutun kowane lardi, da kuma cikin harshen kowane mutane. Aka kuma rubuta ga Yahudawa a rubutunsu da harshensu. Mordekai ya yi rubutu da sunan Sarki Zerzes, ya hatimce saƙonin da zoben hatimin sarki, ya kuma aika da su ta hannun masu ’yan aika a kan dawakai, waɗanda sukan hau dawakai masu gudu sosai, da aka yi kiwonsu musamman saboda sarki.
Dokar sarki ta ba wa Yahudawa a kowace birni izini su taru, su kuma kāre kansu, domin su hallaka, su kashe, su kuma hallaka kowace ƙungiyar mayaƙa, na kowace ƙasa, ko lardi, da wataƙila za su kai musu, da matansu, da yaransu hari; su kuma washe mallakar abokan gābansu. Ranar da aka shirya domin Yahudawa su yi wannan a dukan lardunan Sarki Zerzes, ita ce ranar goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato, watan Adar. Za a ba da kofi na rubutacciyar dokar a matsayin ƙa’ida a kowane lardi, a kuma sanar wa mutanen kowace ƙasa, domin Yahudawa su zauna da shiri a ranar, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu.
’Yan aikan, a kan dawakan fada, suka fita a guje, umarnin sarki yana iza su. Aka kuma ba da dokar a mazaunin masarauta wadda take Shusha.
Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu ruwan shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai ruwan shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shusha. Ga Yahudawa kuwa, lokaci ne na murna da farin ciki, da jin daɗi da bangirma. A kowane lardi da kowace birni, ko’ina da dokar sarki ta kai, aka yi farin ciki a cikin Yahudawa, cike da bukukkuwa. Yawan mutane da waɗansu ƙasashe suka zama Yahudawa, don tsoron Yahudawa ya kama su.
Nasarar Yahudawa
A rana ta goma sha uku na watan goma sha biyu, wato, watan Adar ne za a aiwatar da dokar da sarki ya umarta. A wannan rana, abokan gāban Yahudawa suka sa zuciya za su sha ƙarfinsu, amma yanzu Zerzes ya canja, Yahudawa kuma suka yi galiba a bisa waɗanda suka ƙi jininsu. Yahudawa suka tattaru a cikin biranensu a dukan lardunan Sarki Zerzes don su kai wa waɗanda suka nemi a hallaka su hari. Babu wanda ya tasar musu domin mutanen dukan sauran al’ummai sun jin tsoronsu. Dukan sarakuna larduna, da hakimai, da gwamnoni da kuma ma’aikatan sarki suka taimaki Yahudawa, domin tsoron Mordekai ya kama su. Mordekai babban mutum ne a fada, sunansa ya kai ko’ina a lardunan, ikonsa ya yi ta ƙasaita gaba-gaba.
Yahudawa suka karkashe dukan abokan gābansu da takobi, suka karkashe waɗanda suka ƙi jininsu, suka kuma hallaka su yadda suka ga dama. A mazaunin masarautar a Shusha, Yahudawa suka karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar. Suka kuma kashe Farshandata, da Dalfon, da Asfata, da Forata, da Adaliya, da Aridata, da Farmashta, da Arisai, da Aridai da kuma Baizata, ’ya’ya maza goma na Haman ɗan Hammedata, abokin gāban Yahudawa. Amma ba su taɓa dukiyarsu ba.
A wannan rana, aka ba wa sarki rahoton yawan mutanen da aka kashe a mazaunin masarauta, a Shusha. Sarki ya ce wa Sarauniya Esta, “Yahudawa sun karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar, da kuma ’ya’ya maza goma na Haman a mazaunin masarauta a Shusha. Me suka yi a sauran lardunan sarki? Yanzu kuma mene ne roƙonki? Za a ba ki. Mece ce bukatarki? Za a biya miki.”
Esta ta ce, “In sarki ya yarda, yă ba wa Yahudawa da suke Shusha izini su aikata dokan nan gobe kuma, bari kuma a rataye ’ya’ya maza goma na Haman a kan gumagumai.”
Sai sarki ya ba da umarni a yi haka ɗin. Aka ba da doka a Shusha, aka kuma rataye ’ya’ya maza goma na Haman. Yahudawan da suke Shusha suka taru a ran goma sha huɗu na watan Adar suka kuma karkashe mutum ɗari uku a Shusha, amma ba su taɓa dukiyarsu ba.
Ana cikin haka, sai saura Yahudawa waɗanda suke lardunan sarki su ma suka taru domin su kāre kansu su kuma sami hutu daga abokan gābansu. Suka karkashe mutum dubu saba’in da biyar amma ba su taɓa dukiyarsu ba. Wannan ya faru a ran goma sha uku na watan Adar. A rana ta goma sha huɗu kuwa suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da kuma ta farin ciki.
An kafa bikin Furim
Amma Yahudawan da suke a Shusha suka taru a rana ta goma sha uku da ta sha huɗu, sa’an nan a rana ta goma sha biyar suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da ta farin ciki.
Shi ya sa Yahudawan ƙauyuka, waɗanda suke zama a karkara, suke kiyaye rana ta goma sha huɗu ta watan Adar a matsayin ranar farin ciki da ta biki, ranar ba da kyautai ga juna.
Sai Mordekai ya rubuta waɗannan abubuwa, ya kuma aika wasiƙu ga dukan Yahudawa ko’ina a lardunan Sarki Zerzes, na kusa da na nesa. Ya sa su yi bikin kowace shekara a ranaku goma sha huɗu da goma sha biyar na watan Adar a matsayin lokacin da Yahudawa suka sami huta daga abokan gābansu, da kuma a matsayin watan da aka mai da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama ranar biki. Ya rubuta musu su kiyaye ranakun a matsayin ranakun biki da na farin ciki. Su kuma ba da kyautai na abinci ga juna, da kuma kyautai ga matalauta.
Ta haka, Yahudawa suka yarda su ci gaba da bikin da suka fara, suna aikata abin da Mordekai ya rubuta musu. Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban dukan Yahudawa, ya ƙulla maƙarƙashiya game da Yahudawa, domin a hallaka su, ya kuma jefa fur (wato, ƙuri’a) don yă hallaka su. Amma sa’ad da sarki ya sami labarin maƙarƙashiyar,9.25 Ko kuwa sa’ad da Esta ta zo gaban sarki sai ya ba da umarnai a rubuce cewa mugun shirin da Haman ya ƙulla a kan Yahudawa yă komo kansa, kuma cewa a rataye shi da ’ya’yansa maza a kan gumagumai. (Saboda haka, aka kira ranakun nan Furim, daga kalma fur). Saboda dukan abin da aka rubuta cikin wannan wasiƙa da kuma abin da suka gani, da abin da ya same su. Yahudawa suka ɗauki nawayar kafa al’adar cewa su, da zuriyarsu, da dukan waɗanda suka haɗa hannun da su, za su kiyaye waɗannan kwanaki biyu, kowace shekara yadda aka tsara, a kuma lokacin da aka keɓe dominsu. Za a tuna, a kuma kiyaye waɗannan kwanaki a kowane zamani, cikin kowane iyali, da kuma cikin kowane lardi, da kowace birni. Kuma kada Yahudawa su fasa yin bikin waɗannan kwanakin Furim, ko su bar jikokinsu su manta da kiyaye waɗannan ranaku biyu.
Saboda haka Sarauniya Esta, ’yar Abihayil, tare da Mordekai mutumin Yahuda, suka rubuta da cikakken iko, suka tabbatar da wannan wasiƙa ta biyu game da Furim. Mordekai kuwa ya aika da wasiƙu zuwa ga dukan Yahudawa cikin larduna 127 na masarautar Zerzes. Saƙon fatan alheri da na tabbaci, don a kafa waɗannan ranakun Furim a keɓaɓɓen lokacinsu, kamar yadda Mordekai mutumin Yahuda da Sarauniya Esta suka dokace su. Yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu, game da lokutansu na azumi da makoki. Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan umarnai game da Furim, aka kuma rubuta ta cikin tarihi.
Girman Mordekai
Sarki Zerzes ya sa a biya haraji a ko’ina a cikin daular, har zuwa ƙasashe masu nesa na bakin teku. Dukan ayyukan Sarki Zerzes masu iko da masu girma tare da cikakken rahoton girmama Mordekai wanda sarki ya yi masa, ba a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Mediya da na Farisa ba? Mordekai mutumin Yahuda, shi ne na biyu a matsayi bayan Sarki Zerzes, mai farin ciki kuma a cikin Yahudawa, aka kuma ɗauke shi da martaba cikin ’yan’uwansa Yahudawa. Gama ya yi aiki don kyautatawar mutanensa, ya kuma yi magana don a kyautata rayuwar dukan Yahudawa.