- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Daniyel Daniyel Daniyel Dan Daniyel Horarwar Daniyel a Babilon A Shekara ta uku ta mulki Yehohiyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zo Urushalima ya kuma yi mata ƙawanya. Sai Ubangiji ya bashe Yehohiyakim sarkin Yahuda a hannunsa, tare da waɗansu kayayyakin haikalin Allah. Ya ɗauki waɗannan kayan zuwa cikin haikalin allahnsa a Babilon1.2 Shinar na Ibraniyanci cikin ma’ajin gidan allahnsa. Sa’an nan sarkin ya umarci Ashfenaz, shugaban fadarsa yă kawo waɗansu daga cikin Isra’ilawan da suka fito daga gidan sarauta da kuma na fitattun mutane. Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu.1.4 Ko kuwa Kaldiyawa Sarki kuma ya sa a ba su abinci da ruwan inabi kowace rana daga cikin abincin sarki. Za a koyar da su har shekaru uku, bayan haka kuma su shiga yin wa sarki hidima. Daga cikin waɗannan da aka zaɓa akwai waɗansu daga Yahuda, Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya. Sai sarkin fada ya raɗa musu sababbin sunaye, ga Daniyel ya raɗa masa Belteshazar; ga Hananiya ya raɗa masa Shadrak; ga Mishayel ya raɗa masa Meshak; ga Azariya kuma ya raɗa masa Abednego. Amma Daniyel ya ƙudura a zuciyarsa ba zai ƙazantar da kansa da abinci da ruwan inabin sarki ba, sai ya tambayi sarkin fada don a ba shi izinin kada yă ƙazantar da kansa ta wannan hanya. Sai Allah ya sa sarkin fada ya nuna masa tagomashi ya kuma ƙaunaci Daniyel, amma sai sarkin fada ya ce wa Daniyel, “Ina jin tsoron ranka yă daɗe, sarkina wanda ya sa a ba ku abinci da ruwan inabi. Me zai sa yă ga kuna ramewa fiye da sauran samari, tsaranku? Sarki zai sa a fille mini kai saboda ku.” Sai Daniyel ya ce wa mai gadi wanda sarkin fada ya sa yă kula da Daniyel, Hananiya, Mishayel da Azariya, “Ina roƙonka ka gwada bayinka kwana goma. Kada ka ba mu kome sai kayan lambu mu ci da kuma baƙin ruwa mu sha. Sa’an nan sai ka dubi fuskokinmu da na sauran samarin da suke ci daga abincin sarki; sa’an nan ka yi da bayinka bisa ga abin da ka gani.” Sai ya amince da haka ya kuma gwada su har kwana goma. A ƙarshen kwana goma sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki. Sai mai gadinsu ya janye abinci da ruwan inabi irin na sarki, ya ci gaba da ba su kayan lambu. Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki. A ƙarshen lokacin da sarki ya sa da za a kawo su ciki, sai sarkin fada ya gabatar da su ga Nebukadnezzar. Sarki kuwa ya yi magana da su, sai ya gano cewa babu wani kamar Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya; don haka sai suka shiga yi wa sarki hidima. A dukan al’amuran hikima da na fahimta wanda sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa sau goma. Daniyel kuwa ya kasance a nan har shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus. Mafarkin Nebukadnezzar A shekara ta biyu ta mulkinsa, Nebukadnezzar ya yi mafarkai; hankalinsa ya tashi har ya kāsa barci. Sai sarki ya sa aka tattara masa masu sihiri da masu dabo da bokaye da masanan taurari2.2 ko na Kaldiyawa; da wanda har yanzu yake a aya ta 4, 5 da 10 domin su faɗi abin da ya yi mafarki a kai. Da suka shigo suka tsaya a gaban sarki, sai ya ce musu, “Na yi mafarkin da ya dame ni kuma ina so in san me yake nufi.”2.3 ko me wannan ya nuna Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki da Arameyanci2.4 daga ayoyin nan zuwa sura 7 da Arameyanci ne. “Ran sarki yă daɗe! Ka faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma sai mu fassara.” Sai sarki ya amsa wa masanan taurarin ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa-gunduwa, a mai da gidajenku juji. Amma in har kuka faɗa mini mafarkina kuka kuma bayyana fassararsa, za ku sami lada mai girma. Saboda haka ku faɗa mini mafarkin da kuma fassararsa.” Sai suka sāke amsa masa suka ce, “Ran sarki yă daɗe, faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma za mu fassara shi.” Sai sarki ya amsa ya ce, “Na gane cewa kuna ƙoƙari ku ɓata lokaci ne kawai domin ku ga na manta da abin. In ba ku faɗa mini mafarkin ba, akwai hukunci guda ɗaya kurum dominku. Kun haɗa baki domin ku faɗa mini munanan al’amura domin ku ruɗe ni har lokaci yă wuce. Sai ku faɗa mini mafarkin, ta haka kuwa zan sani za ku iya yi mini fassararsa.” Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki suka ce, “Babu wani mutum a duniyan nan da zai iya yin abin da sarki yake nema! Babu wani sarki mai daraja da girma wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya ga masu sihiri ko masu dabo ko masanan taurari. Abin da sarki yake nema yana da wuya matuƙa. Babu wani da zai iya bayyana wannan ga sarki sai dai alloli; kuma ba su zama tare da ’yan adam.” Wannan ya sa sarki ya fusata ƙwarai, ya ba da umarni a tafi da dukan masu hikima na Babilon a kashe su. Sai aka ba da dokar da za a kashe masu hikima, sa’an nan aka aika mutane su je su nemo Daniyel da abokansa domin a kashe su. Sa’ad da Ariyok, shugaban ƙungiyar matsaran sarki, ya fita domin yă kashe masu hikima na Babilon, sai Daniyel ya yi masa magana cikin hikima da dabara. Ya tambayi mai tsaro na sarki, “Me ya sa sarki ya fitar da wannan doka haka da fushi?” Sai Ariyok ya yi wa Daniyel bayanin batun. Da jin haka sai Daniyel ya tafi wurin sarki ya nemi ƙarin lokaci, domin yă bayyana wa sarki mafarkin da kuma fassararsa. Sa’an nan Daniyel ya komo gida ya kuma sanar wa abokansa Hananiya, Mishayel da Azariya, batun nan duka. Ya roƙe su su roƙi jinƙan Allah na sama domin wannan mafarki, saboda kada a kashe shi da abokansa tare da sauran masu hikima na Babilon. A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama. Ya ce, “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin; hikima da iko nasa ne. Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira. Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa; ya san abin da yake cikin dare, haske kuwa yana zaune tare da shi. Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina. Kai ka san hikima da iko, ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.” Daniyel ya fassara mafarkin Sai Daniyel ya tafi wurin Ariyok, wanda sarki ya sa yă kashe masu hikiman Babilon, ya kuma ce masa, “Kada ka kashe masu hikiman Babilon ka kai ni wurin sarki, ni kuma zan fassara masa mafarkinsa.” Sai Ariyok ya kai Daniyel wurin sarki nan take ya ce masa, “Na gano wani mutum daga cikin kamammun kabilar Yahuda wanda zai faɗa wa sarki abin da mafarkin yake nufi.” Sarki ya tambayi Daniyel (wanda ake kira Belteshazar), za ka iya faɗa mini mafarkin da na yi ka kuma fassara shi? Daniyel ya amsa, “Babu wani mai hikima, ko mai sihiri, ko mai dabo ko mai duban da zai iya warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi, amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne, “A sa’ad da kake kwance, ya sarki, tunaninka ya ga al’amuran da suke zuwa, kuma shi mai bayyana al’amuran ya bayyana maka asiran abubuwan da za su faru. Amma ba a bayyana mini wannan asiri saboda ina da wata hikima fiye da sauran mutane ba, sai dai domin a sanar wa sarki da fassarar, ka kuma san tunanin da ya shiga zuciyarka. “Ya sarki, ka ga wata babbar siffa, mai girma, siffa ce mai haske, abar bantsoro tana tsaye a gabanka. An yi kan wannan siffa da zinariya zalla, ƙirjinta da kuma hannuwanta an yi su da azurfa, cikinta da kuma cinyarta da tagulla ne. An yi ƙafafun da ƙarfe, tafin ƙafafunta kuma an yi rabi da ƙarfe rabi kuma da yumɓu. A lokacin da kake dubawa, sai aka yanko wani dutse, amma ba da hannun mutum ba. Ya fāɗa a kan ƙafafun siffar na ƙarfen da aka haɗa da yumɓu aka kuma ragargaje su. Sai ƙarfen da yambun da tagulla da azurfan da kuma zinariyan suka ragargaje a lokaci ɗaya ya zama kamar ƙaiƙayi a masussuka a lokacin kaka. Sai iska ta kwashe su ta tafi, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma dutsen da ya fāɗo a siffar ya girke ya zama tsauni ya kuma cika dukan duniya. “Wannan shi ne mafarkin, yanzu kuma za mu fassara ta wa sarki. Ya, sarki, kai ne sarkin sarakuna. Allah na sama ya ba ka iko da girma da suna; a cikin hannunka ya sanya ɗan adam, da namun jeji da tsuntsayen sama. A duk inda suke zaune, ya maishe ka ka yi mulki a bisansu kai ne kan zinariyan nan na siffar. “A bayanka, za a yi wani mulki, wanda bai kai naka ba. A gaba kuma, za a yi mulki na uku wanda yake na tagulla, zai yi mulkin dukan duniya. A ƙarshe, za a yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar ƙarfe, Da yake baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, haka nan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato, mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin ƙarfe da yake gauraye da yumɓu. Kamar yadda yatsotsin rabi na ƙarfe rabi kuma na yumɓu ne, haka wannan mulki zai zama rabi mai ƙarfi rabi kuma marar ƙarfi. Kamar dai yadda ka ga ƙarfen ya gauraye da yumɓu, haka mutanen za su zama a gauraye amma ba za su haɗu da juna ba, kamar yadda baƙin ƙarfe da yumɓu ba su haɗuwa. “A lokacin mulkin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai kafa mulki da ba zai taɓa rushewa ba, ba kuma za a ba ma waɗansu mutane ba. Zai ragargaje waɗannan mulkokin da kuma kawo su ga ƙarshe, amma shi wannan mulki zai dawwama har abada. Wannan shi ne ma’anar wannan wahayin da ka gani na dutsen da aka yanko daga jikin tsaunin, amma ba da hannun ɗan adam ba, dutsen da ya ragargaza ƙarfen, da tagullar, da yumɓun da azurfar da kuma zinariyar. “Allah mai girma ya nuna wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin gaskiya ne, fassararsa kuma abin dogara ne.” Sai sarki Nebukadnezzar ya fāɗi da fuskarsa har ƙasa a gaban Daniyel domin ya girmama shi ya kuma umarta a miƙa hadaya da kuma hadayar ƙonawa ta turare ga Daniyel. Sarki ya kuma ce wa Daniyel, “Tabbatacce Allahnka shi ne Allahn alloli da kuma Sarkin sarakuna da mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.” Sai sarki ya ɗora Daniyel a babban matsayi ya kuma sanya shi mai mulki a kan dukan yankin ƙasar Babilon; ya kuma ɗora shi yă zama mai kula da duk masu hikima. Bugu da ƙari, bisa ga bukatar Daniyel sai sarki yă naɗa Shadrak da Meshak da Abednego su zama masu kula da harkokin lardin Babilon, amma Daniyel kuma ya tsaya a fadar sarki. Siffar zinariya da tanderun wuta Sarki Nebukadnezzar ya yi gunkin zinariya, tsawonsa kamu tasa’in, fāɗinsa kuma kamu3.1 da Arameyanci yana nufin tsawonsa kamu sittin ne fāɗinsa kamu shida ne (wato, wajen taki 27, tsawonsa taki 2.7 fāɗinsa) tara ne, ya kafa shi a filin Dura a yankin Babilon. Sa’an nan ya aika a kira hakimai da wakilai da gwamnoni da mashawarta, da ma’aji, da alƙalai, da marubutan kotu, da dukan sauran ma’aikatan yankunan, suka hallara domin a rusuna wa wannan siffar da ya kafa. Saboda haka sai hakimai, da wakilai da gwamnoni, mashawarta da ma’aji da alƙalai, da marubutan alƙalai, da kuma dukan ma’aikatan yankunan suka tattaru domin kaddamar da siffar da Nebukadnezzar ya kafa, suka kuma tsaya a gabansa. Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare. Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.” Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa. A wannan lokaci sai waɗansu masanan taurari3.8 Ko kuwa Kaldiyawa suka zo gaba suka yi karar Yahudawa. Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ran sarki yă daɗe, Ya sarki, ka fitar da doka, cewa duk wanda ya ji karar ƙaho, da sarewa, da garayu da goge, da molo da algaita da kowane irin kayan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe sai yă rusuna yă yi sujada ga siffar zinariya, kuma cewa duk wanda bai rusuna ya yi sujadar ba za a jefa shi cikin tanderun wuta. Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.” Cikin fushi da hasala, Nebukadnezzar ya aika a kira Shadrak, Meshak da Abednego. Aka kawo waɗannan mutane a gaban sarki, sai Nebukadnezzar ya ce musu, “Gaskiya ne Shadrak, Meshak da Abednego, cewa kun ƙi ku bauta wa alloli kuka kuma ƙi yi sujada ga gunkin da na kafa? Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?” Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu. In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka. Amma ko da bai cece mu ba, muna so ka sani, ya sarki; cewa ba za mu bauta wa allolinka ba ko kuma mu yi sujada ga gunkin zinariyar da ka kafa ba.” Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā. Kuma ya umarci waɗansu ƙarfafan sojoji a cikin rundunarsa su daure Shadrak, Meshak da Abednego su jefa su cikin tanderun wutar. Waɗannan mutanen suna sanye da riguna, da wanduna, da rawani da waɗansu kayan sawa, aka daure su, aka jefa su cikin tanderun wuta. Sarki ya ba da umarnin da gaggawa kuma wutar ta yi zafi ƙwarai har harshen wutar ya kashe sojojin nan da suka ɗauki Shadrak, Meshak da Abednego, waɗannan mutane uku kuma a daure, suka fāɗa cikin tanderun wutar. Sai Sarki Nebukadnezzar ya miƙe tsaye, cike da mamaki ya tambayi mashawartansa, “Shin ba mutum uku ba ne muka daure muka jefa cikin wutar?” Suka amsa, “Tabbatacce haka yake ya sarki.” Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.” Sai Nebukadnezzar ya matsa kusa da ƙofar tanderun wutar ya yi kira da ƙarfi, “Shedrak, Meshak da Abednego, bayin Allah Mafi Ɗaukaka ku fito! Ku zo nan!” Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka fita daga cikin wutar, Sa’an nan hakimai, da wakilai, da gwamnoni da masu ba wa sarki shawara suka kewaya su. Suka ga wutar ba tă yi musu wani lahani a jikinsu ba, babu ko gashin kansu da ya ƙuna; ko warin wuta ma ba su yi ba. Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu. Domin haka ina ba da doka cewa duk mutane da kowace al’umma ko kowane yaren da ya ce wani abu mummuna a kan Allahn Shadrak, Meshak da Abednego za a yanka shi gunduwa-gunduwa kuma gidansu zai zama wurin zuba shara, domin babu wani allahn da zai iya ceto ta irin wannan hanya.” Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon. Nebukadnezzar ya yi mafarkin itace Daga sarki Nebukadnezzar. Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku! Ina murna in shaida muku game da alamu da al’ajabai waɗanda Allah Mafi Ɗaukaka ya yi ta wurina. Alamunsa da girma suke, ayyukansa da girma suke! Mulkinsa mulki ne na har abada; sarautarsa kuma za tă dawwama daga zamani zuwa zamani. Ni, Nebukadnezzar, ina zaune a gidana cikin fadata, ina jin daɗi ina bunkasa. Na yi mafarkin da ya ba ni tsoro. A sa’ad da nake kwance a gadona, siffofi da wahayoyi da suka bi ta cikin tunanina sun firgita ni. Don haka na ba da umarni a tattaro dukan masu hikima na Babilon su bayyana a gabana domin su fassara mini mafarkin. Sa’ad da masu sihiri, da masu dabo, da masanan taurari4.7 Ko kuwa Kaldiyawa da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya fassarta mini mafarkin ba. A ƙarshe, sai Daniyel ya zo gabana na kuma faɗa masa mafarkin. (Ana ce da shi Belteshazar, wanda aka ba shi sunan allahna kuma ruhun alloli masu tsarki suna a bisansa.) Na ce, “Belteshazar, shugaban masu sihiri, na san ruhun alloli suna a kanka, babu wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga dai mafarkin da na yi, sai ka fassara mini. Waɗannan su ne wahayin da na gani a lokacin da nake kwance a gadona, na duba, a gabana kuwa ga wani itace a kafe a tsakiyar duniya, yana da tsawo ƙwarai. Itacen ya yi girma ya kuma yi ƙarfi, har tsayinsa ya taɓa sarari sama; ana iya ganinsa a ko’ina a duniya. Ganyayensa suna da kyau, yana da ’ya’ya jingim, abinci kuma domin kowa da kowa. A ƙarƙashinsa namun jeji suke samun wurin hutawa, kuma tsuntsayen sama suna zaune a bisa rassansa; daga cikinsa kowace halitta take cin abinci. “A cikin wahayin da gani sa’ad da nake kwance a kan gadona, Na duba, a gabana kuwa ga wani ɗan saƙo,4.13 Ko kuwa mai tsaro; za a kuma iya samu a aya 17 da 23 mai tsarki, yana saukowa daga sama. Sai ya yi kira da babbar murya ya ce, ‘A sare itacen a kuma yayyanka rassansa; a karkaɗe ganyensa a kuma warwatsar da ’ya’yansa. Bari dabbobi su tashi daga ƙarƙashinsa da kuma tsuntsayen da suke a rassansa. Amma a bar kututturen da kuma saiwoyinsa, a daure shi da ƙarfe da kuma tagulla, a bar shi a cikin ƙasa, a cikin ciyayin filaye. “ ‘Bari yă jiƙu da raɓar, bari yă zauna cikin dabbobi tare da tsire-tsiren duniya. Bari a canja tunaninsa irin na mutane a ba shi tunani irin na dabbobi, har sau bakwai4.16 Ko kuwa shekaru bakwai; kamar yadda yake a aya 23, 25 da 32 su wuce a kansa. “ ‘An sanar da wannan matsayi ne ta bakin ’yan saƙo, masu tsarki ne kuwa suka sanar da hukuncin, domin masu rai su sani Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a bisa kowane mulkin mutane, yakan kuma ba wa duk wanda ya ga dama, yakan sanya talaka yă zama sarki.’ “Wannan shi ne mafarkin da ni, Nebukadnezzar, na yi. Yanzu Belteshazar, sai ka faɗa mini abin da yake nufi, domin babu wani a cikin masu hikima a mulkina da ya iya fassara mini shi. Amma za ka iya, domin ruhun alloli masu tsarki yana a bisanka.” Daniyel Ya Fassara Mafarkin Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan! Itacen da ka gani; wanda ya yi girma da ƙarfe, da tsayinsa ya taɓa sararin sama, wanda ana ganinsa ko’ina a duniya, wanda ganyayensa masu kyau ne yana da ’ya’yan itace da yawa, wanda yake ba da abinci ga duka, yana ba da wurin hutu ga namun jeji, kuma rassansa suna ɗauke da sheƙar tsuntsayen sama. Ya sarki kai ne itacen nan! Ka yi girma da ƙarfi; girmanka kuma ta kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko’ina a duniya. “Ya sarki ka ga ɗan saƙon mai tsarkin nan, yana saukowa daga sama yana cewa, ‘A sare itacen a hallaka shi, amma a bar kututturensa daure da ƙarfe da tagulla, a bar shi can a ɗanyar ciyawar filaye, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namun jeji har shekara bakwai.’ “Ga fassarar, ya sarki, wannan ita ce doka wadda Mafi Ɗaukaka ya bayar a kan ranka yă daɗe, sarkina. Za a kore ka daga cikin mutane, za ka kuma zauna cikin namun jeji; za ka ci ciyawa kamar shanu, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cif sa’an nan za ka sani cewa Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama. Umarni na barin kututturen itacen da saiwoyinsa yana nufin cewa za a maido maka da mulkinka a lokacin da ka gane cewa Mai sama ne yake mulki. Saboda haka, ya sarki, ina roƙonka ka karɓi shawarar da zan ba ka; ka furta zunubanka ta wurin yin abin da yake daidai. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.” Mafarkin Ya Cika Duk wannan kuwa ya faru da sarki Nebukadnezzar. Bayan wata goma sha biyu, a sa’ad da sarki yake takawa a bisan saman ɗakin fadar Babilon, sai ya ce, “Ba wannan ita ce Babilon babba da na gina domin wurin zaman sarautar Babilon, da ikona kuma domin ɗaukakar darajata ba?” Tun kalmomin suna cikin bakinsa sai ya ji murya daga sama tana cewa, “Wannan shi ne abin da aka zartar a kanka, Sarki Nebukadnezzar. An karɓe ikon mulkinka. Za a kore ka daga cikin mutane za ka kuma yi rayuwa tare da namun jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cif, sa’an nan za ka gane Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.” Nan da nan abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar tabbatarsa ya cika. Aka kore shi daga cikin mutane ya kuma shiga cin ciyawa kamar shanu. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar fikafikan gaggafa, kumbarsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu. A ƙarshen waɗannan kwanaki, ni, Nebukadnezzar, na ɗaga idanuna sama, sai hankalina ya komo mini. Na kuwa yabi Maɗaukaki, na girmama shi, na ɗaukaka shi wanda yake rayayye har abada. Mulkinsa dawwammamen mulki ne; sarautarsa ta dawwama daga zamani zuwa zamani. Dukan mutanen duniya ba a bakin kome suke ba. Yakan yi abin da ya gamshe shi da ikokin sama da kuma na mutanen duniya. Babu mai hana shi ko yă ce masa; “Me ka yi?” A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. ’Yan majalisata da fadawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā. Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin sama, ina waƙa ina kuma darjanta shi, saboda dukan abin da ya yi mini, mai kyau ne kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Kuma duk masu tafiya da girman kai zai ƙasƙantar da su. Rubutu a kan bango Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su. Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa5.2 Ko kakansa; ko wanda ya gāji sarauta daga gare shi; haka kuma a ayoyi 11, 13, da 18 ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su. Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse. Nan da nan sai ga yatsotsin hannun mutum sun bayyana, suna yin rubutu a kan shafen bangon, kusa da wurin da ake ajiye fitilar fadar sarki. Sarki kuwa yana ganin hannun yayinda yake rubutu. Sai fuskarsa ta ruɗe, ya kuma ji tsoro ƙwarai har gwiwoyinsa suka yi ta bugun juna, ƙafafunsa kuma suka rasa ƙarfi. Sai sarki ya kira masu dabo, masanan taurari5.7 Ko kuwa Kaldiyawa, haka ma a aya 11 da masu duba, a kawo su, ya kuma ce wa masu hikima na Babilon, “Duk wanda ya karanta wannan rubutu ya kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.” Sa’an nan sai dukan masu hikima suka zo ciki, amma ba su iya karanta rubutun ba ko su faɗa wa sarki abin da yake nufi. Saboda haka Sarki Belshazar ya firgita ƙwarai kuma fuskarsa ta ƙara ruɗewa. Hakimansa kuma suka rikice. Sai sarauniya,5.10 Ko kuwa mahaifiyar sarauniya da jin muryoyi na sarki da na hakimansa, ta shiga babban ɗakin liyafar. Ta ce, “Ya sarki, ranka yă daɗe! Kada ka firgita! Kada fuskarka ta ruɗe! Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba. Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.” Saboda haka aka kawo Daniyel a gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda mahaifina sarki ya kawo daga Yahuda? Na sami labari cewa kana da ruhun alloli a cikinka da kuma basira, da hazaka da kuma fitacciyar hikima. An kawo masu hikima da masu dabo a gabana domin su karanta wannan rubutu su kuma faɗa mini abin da yake nufi, amma ba su iya ba. Na sami labari cewa kana iya ba da fassara da kuma warware matsaloli masu wuya. In har ka iya karanta wannan rubutun ka kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.” Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi. “Ya sarki, Allah Mafi Ɗaukaka ya ba mahaifinka Nebukadnezzar sarauta, da girma, da ɗaukaka, da martaba. Saboda irin matsayin da ya ba shi, dukan mutane da al’ummai da kuma dukan harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani. Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa. Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama. “Amma kai ɗansa,5.22 Ko zuriya; ko magāji Ya Belshazar, ba ka ƙasƙantar da kanka ba, ko da yake ka san wannan duka. A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa. Saboda haka ya aiko da hannun da ya yi rubutun nan. “Wannan shi ne rubutun da aka yi, Mene, mene, tekel, farsin “Abin da kalmomin nan suke nufi shi ne, “Mene 5.26 Mene yana iya nufin ƙididdigewa Ko kuwa mina (ko kashi na kuɗi). , Allah ya ƙayyade yawan kwanakin mulkinka ya kuma kawo su ga ƙarshe. “Tekel 5.27 Tekel yana iya nufin awo Ko kuwa shekel. , An kuma auna ka a ma’auni aka tarar ka kāsa. “Feres 5.28 Feres (jumli ne na Farsin) yana iya nufin an raba Ko kuwa Farisa Ko kuwa rabin mina Ko kuwa rabin shekel. , An raba mulkinka aka ba wa Medes da Farisa.” Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar. A wannan dare aka kashe Belshazar, sarkin Babiloniyawa,5.30 Ko kuwa Kaldiyawa Dariyus mutumin Medes kuwa ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu. Daniyel a cikin ramin zakoki Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar, ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome. To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa. A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula. A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.” Saboda haka shugabannin nan suka haɗu da muƙaddasan nan suka tafi wurin sarki a ƙungiyance suka ce, “Ya Sarki Dariyus, ranka yă daɗe! Shugabannin masarauta, da masu mulki, da muƙaddasai, da mashawarta da gwamnoni duk sun amince cewa sarki yă kafa doka yă kuma yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu’a ga wani allah ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, jefa shi cikin kogon zakoki. Yanzu, ya sarki, sai ka yi umarni ka kuma yi shi a rubuce saboda kada a canja shi, bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” Sai Sarki Dariyus ya ba da umarnin a rubuce. To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi. Sai waɗannan mutane suka tafi a ƙungiyance suka kuma iske Daniyel yana addu’a yana roƙon Allah yă taimake shi. Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.” Da sarki ya ji haka, sai ya damu sosai, ya ƙudura yă ceci Daniyel, ya yi ta fama har fāɗuwar rana yadda zai yi yă kuɓutar da shi. Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.” Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!” Aka kawo dutsen aka rufe bakin ramin, sa’an nan sarki ya hatimce shi da zobensa da kuma zoban manyan mutanensa, don kada wani yă canja yanayin Daniyel. Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci. Gari yana wayewa, sai sarki ya tashi ya hanzarta zuwa ramin zakoki. Da ya yi kusa da ramin zakokin, sai ya kira Daniyel da muryar mai cike da damuwa ya ce, “Daniyel bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta wa kullum, ya iya cetonka daga zakoki?” Sai Daniyel ya amsa ya ce, “Ran sarki, yă daɗe! Allahna ya aiko da mala’ikansa, ya kuwa rufe bakunan zakoki. Ba su yi mini rauni ba, gama an same ni marar laifi ne a gabansa. Ban kuwa taɓa yin wani abu marar kyau a gabanka ba, ya sarki.” Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa. Sai sarki ya umarta, a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da ’ya’yansu, da matansu cikin ramin zakoki. Kafin ma su kai ƙurewar ramin, sai zakoki suka hallaka su suka yayyage su, suka yi kaca-kaca da su. Sa’an nan Sarki Dariyus ya rubuta wa dukan mutane, da al’ummai da kuma mutanen dukan harsunan a duk fāɗin ƙasar. “Bari yă yi nasara sosai! “Na fitar da doka cewa a cikin dukan iyakar ƙasar mulkina, dole mutane su ji tsoro su kuma girmama Allah na Daniyel. “Gama shi ne Allah mai rai kuma madawwami ne har abada; ba za a taɓa lalace masarautarsa ba, mulkinsa kuma ba za tă taɓa ƙarewa ba Yakan kuɓutar ya kuma ceci; yana yin alamu da al’ajabai a sama da kuma a duniya. Shi ya ceci Daniyel daga ikon zakoki.” Daniyel kuwa ya bunkasa a lokacin mulkin Dariyus da kuma mulkin Sairus6.28 Ko kuwa Dariyus, wato, mulkin Sairus na Farisa. Mafarkin Daniyel na dabbobi huɗu A shekara ta fari ta mulkin Belshazar sarkin Babilon, Daniyel ya yi mafarki, wahayoyi kuma suka ratsa tunaninsa a sa’ad da yake a kwance a gadonsa. Sai ya rubuta abin da mafarkin ya ƙunsa. Daniyel ya ce, “A cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga kusurwoyi huɗu na sama suna gurɓata babban teku. Sai ga dabbobi huɗu, kowannensu ya yi dabam da sauran, suna fitowa daga teku. “Na farkon ya yi kamar zaki kuma yana da fikafikai kamar gaggafa. Ina kallo, sai aka fizge fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum. “A gabana kuma ga dabba ta biyu, wadda ta yi kamar beyar. Aka ɗaga ta a gefenta guda, tana kuwa da haƙarƙarai uku a bakinta a tsakanin haƙoranta. Aka faɗa mata, ‘Tashi ki cika cikinki da ɗanyen nama!’ “Bayan haka, na duba, a gabana kuwa ga wata dabba wadda ta yi kamar Damisa, a bayanta kuma tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu. Wannan dabbar tana da kawuna huɗu, aka kuma ba ta iko tă yi mulki. “Bayan haka, a cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga dabba ta huɗu, wadda take da bantsoro da banrazana da kuma iko ƙwarai. Tana da manyan haƙoran ƙarfe; ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Ta bambanta da dukan sauran dabbobin da suka riga ta, tana kuma da ƙahoni goma. “Yayinda nake cikin tunani game da ƙahonin nan, a gabana kuwa ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙani, wanda ya fito daga cikinsu; kuma an tumɓuke uku daga cikin ƙahonin farko kafin wannan. Wannan ƙaho yana da idanu kamar na mutum da kuma bakin da yake maganganun fariya. “Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne. Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai. “Sa’an nan na ci gaba da kallo saboda kalmomin fariyar da wannan ƙaho yake furtawa. Na yi ta kallo har sai da aka yanke dabbar, aka kuma hallaka jikinta a cikin wuta. (An tuɓe sauran dabbobin daga mulkinsu, amma aka bar su su rayu na wani lokaci.) “A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum7.13 Kalmomin Arameyik nan bar enash suna nufin mutum. Kalmomin nan ɗan mutum an yi amfani da su a nan saboda a amfanin da aka yi da su a Sabon Alkawari a matsayi wakilin suna na Yesu, mai yiwuwa saboda dangane a kan wannan ayar. yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa. Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa. Fassarar mafarkin “Ni, Daniyel, ruhuna ya damu ƙwarai, kuma wahayin da ya ratsa tunanina ya dame ni. Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a can, na tambaye shi gaskiya ma’anar waɗannan al’amura. “Don haka sai ya faɗa mini, ya kuma ba ni fassarar waɗannan al’amura. ‘Waɗannan manyan dabbobi huɗu, Masarautai ne huɗu waɗanda za su taso a duniya. Amma tsarkaka na Mafi Ɗaukaka za su karɓi wannan sarauta, za su kuwa mallake ta har abada, I, har abada abadin.’ “Sa’an nan kuma sai na so in san ma’anar wannan dabba ta huɗu, wadda ta yi dabam da sauran dabbobin da suke da matuƙar bantsoro, da take da haƙoran ƙarfe da kuma farcen tagulla, dabbar ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Na kuma so in gane game da ƙahonin nan guda goma da suke a kanta da kuma game da ƙahon nan da ya fito, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa, ƙahon nan da yake da idanu da bakin da yake furta manyan maganganun fariya, wanda ya yi kamar ya fi sauran girma. Ina cikin dubawa, sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka yana kuma cin nasara a kansu, sai da Wannan wanda yake tun fil azal ya zo ya furta hukunci, aka kuma ba tsarkaka na Mafi Ɗaukaka gaskiya, lokaci kuwa ya cika sai suka karɓi mulki. “Sai ya ba ni wannan bayani, ‘Dabbar nan ta huɗu, ita ce mulki na huɗu da zai bayyana a duniya. Zai bambanta da dukan sauran mulkoki, zai kuma cinye dukan duniya, yă tattake ta, yă kuma ragargaje ta. Ƙahonin nan goma, sarakuna ne goma waɗanda za su taso daga wannan mulki. Bayansu kuma, wani sarki zai taso, wanda ya sha dabam da waɗanda suka riga shi. Zai rinjayi sarakunan nan uku. Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci.7.25 Ko kuwa na shekara biyu da rabi “ ‘Amma majalisa za tă yi zama, za a karɓe ikonsa, a kuma hallaka shi gaba ɗaya har abada. Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’ “Wannan shi ne ƙarshen batun. Ni, Daniyel na damu ƙwarai da irin tunanina, kuma fuskata ta rikice, amma na riƙe batun a zuciyata.” Wahayin Daniyel a kan rago da akuya A shekara ta uku ta mulkin sarki Belshazar, ni, Daniyel, na ga wahayi, bayan wancan da na riga gani. A cikin wahayin, na ga kaina a mafakar Shusha a yankin Elam; a wahayin na ga ina a bakin Kogin Ulai. Na ɗaga ido, a gabana kuwa sai ga rago mai ƙahoni biyu, yana tsaye a gefen mashigin kogin, ƙahonin kuma suna da tsawo. Ɗaya daga cikin ƙahonin ya fi ɗayan tsawo. Wanda ya fi tsawon shi ne ya tsiro daga baya. Na lura da ragon sa’ad da ya kai karo wajen yamma da arewa da kudu. Babu wata dabbar da ta iya ƙarawa da shi, babu kuma wanda ya iya kuɓuta daga ikonsa. Ya yi yadda ya ga dama, ya kuma zama mai girma. Yayinda nake tunani game da wannan, farat ɗaya sai ga bunsurun da yake da sanannen ƙaho tsakanin idanunsa ya ɓullo daga wajen yamma, yana ratsa dukan duniya ba ya ko taɓa ƙasa. Ya zo wajen rago mai ƙahoni biyu ɗin nan da na riga na gani tsaye a gefen mashigin kogin nan ya tasar masa da fushi mai zafi. Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, ya kai wa ragon hari. Ya kakkarya ƙahoninsa nan biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, bai iya kāre kansa daga bunsurun ba. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun. Bunsurun kuwa ya ƙasaita, amma a ƙwanƙolin ikonsa sai aka karye babban ƙahonsa, kuma a wurin da ƙahon nan ya kasance waɗansu sanannun ƙahoni huɗu suka tsiro suna fuskantar kusurwoyin nan huɗu. Daga cikin ɗayansu kuma wani ƙaramin ƙaho ya fito, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai zuwa kudu da kuma gabas da wajen Kyakkyawar Ƙasa. Ya yi girma sai da ya kai rundunar sammai, ya kuma fid da waɗansu rundunar taurari zuwa ƙasa ya kuma tattake su. Sai ya ɗora kansa ya zama mai girma kamar Sarkin runduna; sai aka ɗauke hadaya ta kullayaumi daga gare shi, aka kuma saukar da wurin masujadarsa ƙasa. Saboda tawaye, sai aka ba da rundunar tsarkaka8.12 ko tawayen, mayaƙan da kuma hadayar ƙonawa ta kowace rana ga ƙahon. Sai ya yi watsi da gaskiya, ya yi abin da ya ga dama, ya kuwa yi nasara. Sa’an nan na ji mai tsarkin nan yana magana, wani mai tsarki kuma ya ce da wancan, “Har yaushe wannan wahayi zai tabbata, wahayi game da hadaya ta kullayaumi, da tawayen da yake kawo lalacewa, da kuma miƙa wuri mai tsarki da kuma na rundunar da za a tattake a ƙarƙashin sawu?” Sai ya ce mini, “Zai ɗauki safiya da yamma 2,300; sa’an nan za a sāke tsarkake wuri mai tsarki.” Fassarar wahayin Yayinda ni, Daniyel, nake duban wahayi ina ƙoƙari in fahimce shi, sai ga wani a gabana wanda ya yi kama da mutum. Sai na ji muryar wani mutum daga Ulai tana cewa, “Jibra’ilu, faɗa wa wannan mutum ma’anar wahayin.” Da ya zo kusa da inda nake tsaye, na firgita na kuma fāɗi rubda ciki. Ya ce da ni “Ɗan mutum, ka gane da cewa wannan wahayi yana magana ne a kan kwanakin ƙarshe.” Yayinda yake magana da ni, barci mai nauyi ya kwashe ni, da nake kwance rubda ciki. Sai ya taɓa ni ya kuma tashe ni tsaye. Sai ya ce, “Zan faɗa maka abin da zai faru a lokacin fushi, saboda wahayin yana magana ne a kan lokacin da aka ƙayyade na ƙarshe.8.19 Ko kuwa domin ƙarshen zai zama a ƙayyadadden lokaci Rago mai ƙahoni biyu da ka gani, yana a madadin sarakunan Medes da Farisa ne. Bunsurun kuwa sarkin Girka ne, kuma babban ƙahon da yake tsakanin idanunsa, sarki na farko ne. Ƙahoni huɗu da suka maya wannan da ya karye yana a madadin masarautu huɗu da za su tashi daga cikin al’ummarsa amma ba za su sami irin ikonsa ba. “Can wajen ƙarshe mulkinsu, sa’ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai rashin hankali, uban makirci, zai fito. Zai yi ƙarfi ƙwarai da gaske, amma ba da ikonsa ba. Zai jawo mummunar hallakarwa kuma zai yi nasara a duk abin da ya sa gaba. Zai hallakar da majiya ƙarfi da kuma tsarkaka. Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba. “Wahayin nan na safiya da yamma da aka nuna maka gaskiya ne, amma ka ɓoye wahayin, gama ya shafi nan gaba mai tsawo ne.” Ni, Daniyel, na gaji matuƙa na kuma yi rashin lafiya na kwanaki masu yawa. Sa’an nan sai na tashi na ci gaba da hidimar sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ya fi ƙarfin fahimtata. Addu’ar Daniyel A shekara ta fari da mulkin Dariyus ɗan Zerzes9.1 Da Ibraniyanci Ahasuwerus (wanda yake Bamediye), wanda aka mai da shi sarki a masarautar Babiloniyawa9.1 Ko kuwa Kaldiyawa a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in. Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka. Na yi addu’a ga Ubangiji Allahna na furta laifina. “Ya Ubangiji, mai alfarma da kuma Allah mai banrazana, wanda yake cika alkawarinsa na ƙauna ga duk wanda ya ƙaunace shi ya kuma kiyaye dokokinsa, mun yi zunubi muka kuma yi ba daidai ba. Mu mugaye ne da kuma ’yan tawaye; mun juya wa umarninka da shari’unka baya. Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa. “Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka. Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi. Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye; ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ba, ba mu kuma kiyaye shari’unsa da ya ba mu ta wuri bayinsa annabawa ba. Dukan Isra’ila sun karya dokokinka suka kuma juya maka baya, sun ƙi yi maka biyayya. “Saboda haka la’anoni da rantsuwar hukunce-hukuncen da suke a rubuce a cikin Dokar Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi. Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba. Kamar yadda yake a rubuce cikin Dokar Musa, dukan wannan bala’i ya sauko a kanmu, duk da haka ba mu nemi tagomashin Ubangiji Allahnmu ta wurin barin aikatawa zunubanmu, mu kuma mai da hankali a kan gaskiyarka ba. Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba. “Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, wanda ya fito da mutanensa daga Masar ta hannu mai ƙarfi wanda kuma ya yi wa kansa sunan da ya dawwama har yă zuwa yau, mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba. Ya Ubangiji, ta wurin kiyaye dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hukuncinka da ka yi a kan Urushalima, birninka, tudunka mai tsarki. Zunubinmu da laifofin iyayenmu sun mai da Urushalima da kuma mutanenka abin ba’a ga dukan waɗanda suke kewaye da mu. “Yanzu, ya Allahnmu, ka ji addu’o’i da koke-koken bayinka. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka duba da rahama wurinka mai tsarki da ya zama kango. Ka kasa kunne, ya Allah, ka kuma ji; ka buɗe idanunka ka kuma ga yadda birninka ya zama kango, birnin da yake ɗauke da Sunanka. Ba cewa muna roƙonka saboda mu masu adalci ba ne, amma saboda girman jinƙanka. Ya Ubangiji, ka saurara! Ya Ubangiji ka gafarta! Ya Ubangiji, ka ji ka kuma yi wani abu! Saboda sunanka, ya Allahna, kada ka yi jinkiri, domin da sunanka ake kiran birninka da jama’arka.” Annabci a kan Mako Saba’in Yayinda da nake magana da addu’a, ina furta zunubina da zunubin mutanena Isra’ila ina miƙa koke-kokena ga Ubangiji Allahna saboda tudunsa mai tsarki, yayinda nake cikin addu’a, sai Jibra’ilu, mutumin nan da na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta yamma. Ya umarce ni ya kuma ce mini, “Daniyel, yanzu na zo domin in ba ka hikima da ganewa. Da zarar ka fara addu’a, an amsa, wadda na zo in faɗa maka, gama ana ƙaunar ka sosai. Saboda haka, ka yi lura da saƙon ka kuma fahimci wahayin. “An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali. “Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka9.25 Ko kuwa kalma don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan,9.25 Ko kuwa shafaffen nan; haka kuma a aya 26 mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka. Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome.9.26 Ko kuwa ba zai kasance da kome ba; Ko kuwa a kawar, amma ba don kansa ba Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara. Zai tabbatar da alkawari da mutane masu yawa har na shekara bakwai.9.27 Ko kuwa “mako” A tsakiyar bakwai ɗin nan ɗaya9.27 Ko kuwa “mako” zai kawo ƙarshen duk wata hadaya da baiko. Kuma a kusurwar haikali zai sa abin ƙyama mai kawo hallaka, har sai ƙarshen da aka ƙaddara ya auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”9.27 Ko kuwa shi (abin da ba mutum ba),9.27 Ko kuwa abin da zai kawo hallaka zai zo ne a kan ƙwanƙolin za tă zubo allahn birnin Wahayin Daniyel na mutum A shekara ta uku ta Sairus sarkin Farisa, sai aka ba wa Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) wahayi. Saƙon kuwa gaskiya ce wadda take tattare da babban yaƙi. Fahimtar saƙon ya zo masa a cikin wahayi. A wannan lokaci ni Daniyel na yi makoki har na sati uku. Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce. A rana ta ashirin da huɗu ga watan farko, a sa’ad da nake tsaye a bakin babban kogi, Tigris, na ɗaga kaina na duba sai ga wani mutum tsaye sanye da rigar lilin, ya yi ɗamara da zinariya zalla daga Ufaz kewaye da ƙugunsa. Jikinsa kamar lu’ulu’u yake, fuskarsa kuma kamar walƙiya, idanunsa kamar harshen wuta, hannuwansa da ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kuma kamar amon babban taron jama’a. Ni, Daniyel, kaɗai ne na ga wahayin; mutanen da suke tare da ni ba su gani ba, amma wata irin babbar razana ta auko musu har suka gudu suka ɓuya. Sai aka bar ni ni kaɗai, ina juyayi wannan babban wahayi, ba ni da sauran ƙarfi, fuskata ta yamutse kuma ba ni da sauran ƙarfi. Sai na ji yana magana, da ina sauraronsa, sai na shiga barci mai nauyi, na kuwa fāɗi rubda ciki. Sai hannu ya taɓa ni ya sa makyarkyata a hannuna da ƙafafuna. Sai ya ce, “Daniyel, kai ne wanda ake ƙauna sosai, ka yi lura da kyau game da kalmomin da zan yi maka magana a kansu, ka tashi yanzu, gama an aiko ni a gare ka.” Sa’ad da ya faɗa mini haka, sai na tashi a tsaye ina rawan jiki. Sai ya ci gaba da cewa, “Kada ka ji tsoro, Daniyel. Gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu’arka, amsar addu’arka ce ta kawo ni. Amma mai mulkin masarautar Farisa ya tsare ni har kwana ashirin da ɗaya. Sai da Mika’ilu, ɗaya daga cikin manya shugabanni, ya zo ya taimake ni, saboda an tsare ni a can tare da sarkin Farisa. Yanzu na zo domin in bayyana maka abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin ya shafi lokacin da bai riga ya zo ba ne.” Yayinda yake faɗin mini haka, sai na sunkuyar da kaina ƙasa shiru, ba magana. Sai wani wanda ya yi kama da mutum10.16 Yawancin rubuce-rubucen hannu na Nassin Masoretik; ɗaya daga cikin rubuce-rubucen Masoretik, Naɗaɗɗen littafin Mataccen Teku da kuma Seftuwajin Sa’an nan wani abu kamar hannun mutum ya taɓa leɓunana, na kuma buɗe bakina sai na fara magana. Na ce wa wannan da yake tsaye a gabana, “Na cika da azaba saboda wannan wahayi, ranka yă daɗe, ina kuma neman taimako. Yaya ni bawanka zan iya magana da kai, ranka yă daɗe? Ƙarfina ya ƙare kuma ina numfashi da ƙyar.” Har yanzu wannan wanda yana kama da mutum ya taɓa ni ya kuma ba ni ƙarfi. Ya kuma ce, “Kada ka ji tsoro, ya kai mutumin da ake fahariya, salama a gare ka! Ka ƙarfafa yanzu; ka yi ƙarfin hali.” Sa’ad da ya yi magana da ni, sai na samu ƙarfi na ce, “Ka yi magana ranka yă daɗe, tun da yake ka sa na sami ƙarfi.” Sai ya ce mini, “Ka san abin da ya kawo ni gare ka? Ba da jimawa ba zan koma in yi yaƙi da mai mulkin Farisa, kuma idan na tafi, mai mulkin Hellenawa zai taso; amma da farko zan faɗa maka abin da aka rubuta a cikin Littafin Gaskiya (Babu wanda ya taimake ni yaƙi da waɗannan sai dai Mika’ilu, sarkinku. A shekara ta fari ta Dariyus mutumin Mede, na ɗauki matsayina domin in goyi baya in kuma kāre shi.) Sarakunan kudu da arewa “Yanzu dai, zan faɗa maka gaskiya. Sarakuna uku za su taso a Farisa, sa’an nan kuma na huɗu, wanda zai fi dukansu dukiya. Sa’ad da zai sami iko saboda dukiyarsa, zai zuga dukan kowane mutum yă yi gāba da masarautar Girka. Sa’an nan wani babban sarki zai bayyana, wanda zai yi mulki da babban iko yă kuma yi abin da ya ga dama. Bayan da ya bayyana, daularsa za tă wargaje za a rarraba ta zuwa kusurwoyi huɗu na duniya, a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, ba kuwa za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki daularsa a kuma ba wa waɗansu. “Sai sarki Kudu zai yi ƙarfi ƙwarai, amma ɗaya daga cikin komandodinsa zai yi ƙarfi fiye da shi, zai kuma yi mulki masarautarsa da iko mai girma. Bayan ’yan shekaru, za su haɗa kai. Diyar sarkin Kudu za tă je wurin sarkin Arewa ta sada zumunci, amma ba za tă riƙe iko ba, shi kuwa da ikonsa11.6 Ko kuwa zuriyarsa ba za su daɗe ba. A waɗannan kwanaki za a bashe ta, da ita da masu rakiyarta da kuma mahaifinta11.6 Ko kuwa yaro (dubi Bulget da Siriyak) da kuma wanda ya goyi bayanta. “Wani daga cikin zuriyarta zai taso yă ɗauki matsayinta. Zai kai wa sojojin sarkin Arewa hari yă kuma shiga kagararsa; zai yi yaƙi da su yă kuma yi nasara. Zai ƙwace allolinsu, siffofinsu na ƙarfe da kuma kaya masu daraja na azurfa da na zinariya a kuma kai su Masar. Zai yi ’yan shekaru bai kai wa sarkin Arewa yaƙi ba. Sa’an nan sarkin Arewa zai kai wa sarkin Kudu hari, amma zai janye, yă koma ƙasarsa. ’Ya’yansa maza za su yi shirin yaƙi za su kuma tattara babbar rundunar sojoji, waɗanda za su yi ta mamayewa kamar rigyawar da ba iya tarewa, kuma za su kai yaƙin har kagararsa. “Sa’an nan sai sarkin Kudu zai kama hanya da fushi zuwa yaƙi da sarkin Arewa, wanda zai tattara babbar rundunar yaƙi, amma za a ci shi da yaƙi. Sa’ad da zai kawar da rundunar, sarkin Kudu zai cika da girman kai zai kuma kashe mutane dubbai, duk da haka ba zai kasance mai nasara ba. Sarki Arewa kuma zai ƙara tara babbar rundunar soja, wadda ta fi ta dā girma; bayan waɗansu shekaru kuma, zai tafi yaƙi da babbar rundunar mayaƙa cike da kayan yaƙi. “A waɗannan lokutan mutane da yawa za su tashi gāba da sarkin Kudu. Amma waɗansu ’yan kama-karya za su taso daga jama’arka da niyya su cika abin da wahayin ya ce, amma za a fatattake su. Sa’an nan sarkin arewa zai zo ya gina mahaurai a jikin katagar birni don yă ci birnin da yaƙi. Sojojin nan na Kudu kuwa ba za su iya tsayawa ba, ko zaɓaɓɓun jarumawansu ma, gama za su rasa ƙarfin tsayawa. Wanda ya kai harin zai yi yadda ya ga dama, ba wanda zai iya ja da shi. Zai kafa kansa a Kyakkyawar Ƙasa zai kuma sami ikon da zai hallaka ta. Zai yunƙura yă zo da ƙarfin dukan masarautarsa zai kuma nemi haɗinkan sarkin Kudu. Zai kuma ba shi diyarsa yă aura don yă lalatar da mulkin, amma shirinsa11.17 Ko kuwa amma ita ba zai yi nasara ba ko yă taimake shi ba. Sa’an nan zai mai da hankalinsa zuwa ƙasashe a bakin kogi, zai kuma kama da yawansu, amma wani komanda zai kawo ƙarshen faɗin ransa, zai kuma sa faɗin ransa yă koma masa. Bayan wannan, zai juya ga kagarar ƙasarsa, amma zai yi tuntuɓe yă fāɗi, ba kuwa za a ƙara ganinsa ba. “Magājinsa zai aiki mai karɓar haraji don darajar masarautarsa. Amma ba da daɗewa ba za a hallaka shi, duk da haka ba da fushi ko cikin yaƙi ba. “Magājin wannan sarki zai zama wani mutumin banza wanda ma bai fito daga gidan sarauta ba. Zai taso ba zato ba tsammani, yă ƙwace sarautar ta hanyar zamba. Sa’an nan zai shafe mayaƙa masu yawa a gabansa; zai hallaka har da waɗanda suke mulki na alkawari. Bayan ƙulla yarjejjeniya da shi, zai yi zamba cikin aminci, kuma zai sami damar hawan mulki da goyon baya mutane kaɗan. Sa’ad da yankuna mafi arziki suke ji kome lafiya yake, zai kai musu hari kuma Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba abin da aka kwaso daga yaƙi, da ganima, da dukiya ga dukan mabiyansa. Zai kuma yi shiri yă kai wa mafaka hari, amma na ɗan lokaci ne kawai. “Tare da babbar rundunar mayaƙa zai yi ƙarfin hali yă far wa sarkin Kudu da yaƙi. Sarkin kudu zai haɗa babbar rundunar soja mai ƙarfi don yaƙin, amma ba zai iya karo da shi ba, domin za a shirya masa maƙarƙashiya. Waɗanda suke ci daga tanadin sarki za su yi ƙoƙari su hallaka shi; za a share mayaƙansa, kuma za a kashe mutane masu yawa a yaƙin. Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna. “Sarkin Arewa zai koma ƙasarsa da dukiya mai girma, amma zuciyarsa za tă yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai ɗauki mataki a kan wannan abu sa’an nan yă koma ƙasarsa. “A ƙayyadadden lokaci zai sāke kai wa Kudu hari, amma a wannan karo abin da zai faru zai sha bamban daga abin da ya faru can baya. Jiragen ruwa yammancin bakin teku11.30 Da Ibraniyanci na Kittim za su yi gāba da shi, zuciyarsa kuwa za tă yi sanyi. Sa’an nan zai juya ya huce haushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai komo yă nuna jinƙai ga waɗanda suka juya wa tsattsarkan alkawari baya. “Mayaƙansa za su taso su ƙazantar da kagarar haikali za su kuma kawar da hadaya ta kullum. Sa’an nan za su kafa abin banƙyama da yake lalatarwa. Ta wurin daɗin baki zai gurɓata waɗannan da suka karya alkawari, amma mutanen da suka san Allahnsu za su yi tsayin daka su yi jayayya da shi. “Waɗanda suke da hikima za su wayar da kan mutane da yawa, duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta. Sa’ad da suka fāɗi, za su sami ɗan taimako, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci. Waɗansu masu hikima za su yi tuntuɓe, don a tsabtacce su, a tsarkake su, su yi tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi. Sarkin da ya ɗaukaka kansa “Sarkin zai yi abin da ya ga dama. Zai ɗaukaka yă kuma girmama kansa gaba da kowane allah zai kuma faɗa munanan abubuwa a kan Allahn alloli. Zai yi nasara har sai lokacin hukunci ya cika, gama abin da aka ƙaddara zai cika. Ba zai kula da alloli iyayensa ba ko wanda mata suke sha’awa, balle ma yă ga darajar wani allah, amma zai ɗaukaka kansa gaba da su duka. A maimakonsu, zai ɗaukaka allahn kagarai; allahn da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tsada. Zai kai wa kagarai mafi ƙarfi hari da taimakon baƙon allah zai kuma girmama waɗanda suka yarda da shi zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu.11.39 Ko kuwa ƙasar don lada “A lokaci ƙarshe sarkin Kudu zai tasar masa da yaƙi, sarkin Arewa kuwa zai tunzura, yă tasar masa da kekunan yaƙi da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, yă ci su da yaƙi, yă wuce. Zai kuma mamaye Kyakkyawa Ƙasa. Ƙasashe masu yawa za su fāɗi, amma Edom, Mowab da kuma shugabannin Ammon za su kuɓuta daga hannunsa. Zai fadada mulkinsa har zuwa ƙasashe masu yawa; Masar ma ba za tă tsira ba. Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tsada na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Kush da yaƙi. Amma labari daga gabas da arewa za su firgita shi, shi kuwa zai ci gaba da yin yaƙi da zafi, yă karkashe mutane da yawa, yă shafe su. Zai kafa tentin mulkinsa tsakanin tekunan da suke11.45 Ko kuwa teku da a kyakkyawan tsauni mai tsarki. Duk da haka zai zo ga ƙarshensa, kuma babu wanda zai taimake shi. Ƙarshe zamani “A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi. Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. Waɗanda suke da hikima12.3 Ko kuwa waɗanda suke ba da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin. Amma kai, Daniyel, ka rufe zancen nan ka kuma liƙe kalmomin littafin nan har sai ƙarshe. Mutane da yawa za su yi ta kai komo don neman sani.” Sa’an nan ni, Daniyel, na duba, a gabana kuwa ga waɗansu mutum biyu tsaye, ɗaya a wannan hayen kogi ɗaya kuma a ƙetaren kogin. Ɗayansu ya ce wa mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, “Har yaushe waɗannan abubuwan banmamakin za su cika?” Mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, ya ɗaga hannun damansa da kuma na hagunsa sama, sai na ji yana rantsuwa da wannan da yake raye har abada, yana cewa, “Zai kasance na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci.12.7 Ko kuwa shekara, shekara biyu da kuma rabi shekara Za a kammala waɗannan abubuwa, sa’ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.” Na kuma ji, amma ban fahimta ba. Don haka sai na yi tambaya, “Ranka yă daɗe, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?” Sai ya amsa ya ce, “Ka kama hanyarka, Daniyel, domin a rufe kalmomin aka kuma liƙe su har sai ƙarshen lokaci. Za a tsarkake mutane da yawa, za a maishe su marasa aibi a kuma tace su; amma mugaye za su ci gaba da mugunta. Babu wani mugun da zai fahimta, amma waɗanda za su zama masu hikima za su fahimta. “Daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kuma kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana 1,290. Mai albarka ne wanda ya jira har yă zuwa ƙarshen kwanakin nan 1,335. “Gare ka dai, ka yi tafiyarka har zuwa ƙarshe. Za ka huta, sa’an nan a ƙarshen kwanaki za ka tashi don karɓi sashen gadon da aka ba ka.”