- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Amos
Amos
Amos
Amos
Amos
Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila.
Ya ce,
“Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona
ya kuma yi tsawa daga Urushalima;
wuraren kiwo duk sun bushe,
dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”
Hukunci a kan maƙwabtan Isra’ila
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Damaskus,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Domin sun ci zalunci Gileyad
zalunci mai tsanani,
zan sa wuta a gidan Hazayel,
da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad.
Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus;
zan hallaka sarkin da yake cikin1.5 Ko kuwa mazaunan Kwarin Awen1.5 Awen yana nufin mugunta.
da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden.
Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,”
in ji Ubangiji.
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Gaza,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya
sun sayar wa Edom,
Zan aika da wuta a katangar Gaza
ta ƙone duk kagarunta.
Zan hallaka sarkin1.8 Ko kuwa mazaunan Ashdod
da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon.
Zan hukunta Ekron,
har sai dukan Filistiyawa sun mutu,”
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Taya,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom,
ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba,
zan aika da wuta a Taya,
da za tă ƙone kagarunta.”
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Edom,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.
Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi,
babu tausayi,
domin ya ci gaba da fusata
bai yarda yă huce daga fushinsa ba.
Zan aika wuta a Teman
da za tă ƙone kagarun Bozra.”
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Ammon,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.
Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu
don kawai yă ƙwace ƙasar.
Zan sa wuta a katangar Rabba
da za tă ƙone kagarunta
za a yi kururuwa a ranar yaƙi,
faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.
Sarkinta1.15 Ko kuwa Molek; Ibraniyawa malkam zai je bauta,
shi da ma’aikatansa,”
in ji Ubangiji.
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Mowab,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom
suka zama sai ka ce toka.
Zan sa wuta a Mowab
da za tă ƙone kagarun Keriyot2.2 Ko kuwa na biranenta
Mowab za tă gangara cikin hayaniya mai girma
cikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho.
Zan hallaka mai mulkinta
zan kuma kashe shugabanninta.”
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Yahuda,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji
ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba,
domin allolin ƙarya sun ruɗe su,
allolin da kakanninsu suka bauta.
Zan sa wuta a Yahuda
da za tă ƙone kagarun Urushalima.”
Hukunci a kan Isra’ila
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Isra’ila,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Don sun sayar da adalai waɗanda
suka kāsa biyan bashinsu.
Sun kuma sayar da matalauta
waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.
Sun tattake kawunan matalauta
kamar yadda suke taka laka
suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya.
Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda,
suna kuma ɓata sunana mai tsarki.
Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade
a kan tufafin da suka karɓe jingina.
A gidajen allolinsu
sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara.
“Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu,
ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul
kuma mai ƙarfi kamar itacen oak.
Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama,
da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.
Na fitar da ku daga ƙasar Masar,
na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada
don in ba ku ƙasar Amoriyawa.
“Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza
waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku.
Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?”
In ji Ubangiji.
“Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi
kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.
“Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku
kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi.
Masu gudu da sauri ba za su tsira ba,
masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba,
jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba.
’Yan baka ba za su iya dāgewa ba,
masu saurin gudu ba za su tsira ba
mahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba.
Ko jarumawa mafi jaruntaka
za su gudu tsirara a ranan nan,”
in ji Ubangiji.
An kira shaidu a kan Isra’ila
Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.
“Ku ne kaɗai na zaɓa
cikin dukan al’umman duniya;
saboda haka zan hukunta ku
saboda dukan zunubanku.”
Mutum biyu za su iya yin tafiya tare
in ba su yarda su yi haka ba?
Zaki yakan yi ruri a jeji
in bai sami kama nama ba?
Zai yi gurnani a cikin kogonsa
in bai kama kome ba?
Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasa
inda ba a sa tarko ba,
ko tarko yakan zargu daga ƙasa
in ba abin da ya taɓa shi?
Idan aka busa ƙaho a ciki birni
mutane ba sa yin rawar jiki?
Sa’ad da bala’i ya auko wa birni,
ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?
Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu
ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.
Zaki ya yi ruri,
wa ba zai tsorata ba?
Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana,
wa ba zai yi annabci ba?
Ku yi shela ga kagarun Ashdod
da kuma ga kagarun Masar.
“Ku tara kanku a tuddan Samariya;
ku ga rashin jituwar da take a cikinta,
da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”
“Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,”
in ji Ubangiji,
“sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”
Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,
“Abokin gāba zai ƙwace ƙasar,
zai saukar da mafakarku,
zai washe kagarunku.”
Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki
ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya,
haka za a ceci Isra’ilawa,
masu zama a Samariya
da kan gado kawai
da kuma a ɗan ƙyalle3.12 Ma’anar kalmar Ibraniyancin nan babu tabbas. a kan dogayen kujerunsu.3.12 Ko kuwa Za a ceci Isra’ilawa / waɗanda suke zama a Samariya / a gefen gadajensu / da kuma a Damaskus kan kujerunsu”
“Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki.
“A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta,
zan hallaka bagadan Betel;
za a yayyanka ƙahonin bagadan
za su fāɗa ƙasa
Zan rushe gidan rani
da na damina;
gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su
haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,”
in ji Ubangiji.
Isra’ila ba ta koma ga Allah ba
Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya,
ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta,
kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!”
Ubangiji Mai Iko Duka ya rantse da tsarkinsa.
“Tabbatacce lokaci yana zuwa
da za a jawo ku da ƙugiyoyi,
na ƙarshenku za a kama da ƙugiyar kifi.
Dukanku za ku wuce ta kai tsaye
ta inda katangar ta tsage,
za a jefar da ku a Harmon,”4.3 Rubuce-rubucen hannu na Masoretik; da ɓangare dabam na kalmar Ibraniyanci (dubi Seftuwajin) waje, ya dutsen danniya
in ji Ubangiji.
“Ku tafi Betel ku yi ta aikata zunubi;
ku je Gilgal ku ƙara yin zunubi.
Ku kawo hadayunku kowace safiya,
zakkarku kowace shekara uku.4.4 Ko kuwa zakka a rana ta uku
Ku ƙona burodinku mai yisti kamar hadaya ta godiya,
ku yi fariya game da hadayunku na yarda rai,
ku yi taƙama game da su, ya ku Isra’ilawa,
gama abin da kuke jin daɗin aikata ke nan,”
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“Na bar ku da yunwa4.6 Ibraniyanci ku da tsabtar haƙora a kowace birni,
da kuma rashin abinci a kowane gari,
duk da haka ba ku juyo gare ni ba,”
in ji Ubangiji.
“Na kuma hana muku ruwan sama
tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi.
Na sa aka yi ruwan sama a wani gari,
sai na hana a yi a wani gari.
Wata gona ta sami ruwan sama;
wata gona kuma ta bushe.
Mutane suna tangaɗi daga gari zuwa gari suna neman ruwa
amma ba su sami isashen ruwan sha ba,
duk da haka ba ku juyo gare ni ba,”
in ji Ubangiji.
“Sau da yawa na ɓata gonakinku
da fumfuna da kuma cuta.
Fāri suka cinye itatuwanku na inabi da na ɓaure, da na zaitun
duk da haka ba ku juyo gare ni ba,”
in ji Ubangiji.
“Na aiko muku annoba
yadda na yi a Masar.
Na karkashe samarinku da takobi,
tare da kamammun dawakanku.
Na cika hancinku da warin sansaninku,
duk da haka ba ku juyo gare ni ba”
in ji Ubangiji.
“Na hallaka waɗansunku
kamar4.11 Ibraniyanci Allah yadda na hallaka Sodom da Gomorra.
Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta,
duk da haka ba ku juyo gare ni ba,”
in ji Ubangiji.
“Saboda haka ga abin da zan yi da ku, ya Isra’ila,
don kuwa zan yi muku haka,
sai ku yi shirin gamuwa da Allahnku, ya Isra’ila.”
Shi wanda ya yi duwatsu,
ya halicci iska,
ya kuma bayyana wa mutum tunaninsa,
shi wanda ya juya safiya ta zama duhu
yana takawa a wurare masu tsawo na duniya,
Ubangiji Allah Maɗaukaki ne sunansa.
Makoki da kuma kira ga tuba
Ku ji wannan magana, ya gidan Isra’ila, ina makokin nan dominku.
“Budurwa Isra’ila ta fāɗi,
ba za tă ƙara tashi ba,
an yashe ta a ƙasarta,
ba wanda zai ɗaga ta.”
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,
“Birnin da ta fitar da masu ƙarfi dubbai don Isra’ila
guda ɗari kaɗai za su dawo;
garin da ya fitar da masu ƙarfi ɗari kuwa
goma kaɗai za su dawo.”
Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila.
“Ku neme ni ku rayu;
kada ku nemi Betel,
kada ku je Gilgal,
kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba.
Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta,
za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”5.5 Ko kuwa baƙin cikin; Ko kuwa mugunta; Da Ibraniyanci awen, kwatanci ga Bet Awen (wani sunan reni don Betel).
Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu,
ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta;
zai cinye
Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.
Ku ne masu mai da gaskiya ta koma ɗaci
ku kuma zubar da adalci.
(Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare,
wanda ya mai da duhu ya zama haske
ya kuma baƙanta rana ta zama dare,
yakan kwashe ruwan teku
ya zubar a ƙasa,
Ubangiji ne sunansa,
yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi
yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).
Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a
kuna ƙin mai faɗar gaskiya.
Kuna matsa wa matalauta
kuna sa su dole su ba ku hatsi.
Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu,
ba za ku zauna a cikinsu ba;
ko da yake kun nome gonaki masu kyau,
ba za ku sha ruwan inabinsu ba.
Gama na san yawan laifofinku
da kuma girman zunubanku.
Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci
kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.
Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka,
gama lokutan mugaye ne.
Ku yi nagarta, ba mugunta ba;
don ku rayu
sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku,
kamar yadda kuka ce zai yi.
Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta;
ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a.
Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin
raguwar Yusuf.
Saboda haka ga abin da Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa,
“Za a yi kururuwa a dukan tituna
a kuma yi kuka don azaba a dukan wuraren da jama’a sukan taru.
Za a yi kira ga manoma su yi kuka
masu makoki kuma su yi kuka.
Za a yi kuka a dukan gonakin inabi,
gama zan ratsa a cikinku,”
in ji Ubangiji.
Ranar Ubangiji
Kaitonku masu son
ganin ranar Ubangiji!
Don me kuke son ganin ranar Ubangiji?
Za a duhunta ranan nan, ba haske ba.
Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki
sai suka fāɗa a hannun beyar,
ko kuma kamar wanda ya shiga gida
ya dāfa hannu a bango
sai maciji ya sare shi.
Ashe, ranar Ubangiji ba duhu ba ce, a maimakon haske,
duhu wuluk, ba tare da ko ɗan haske ba.
“Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini;
ba na son ganin tarurrukanku.
Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi,
ba zan karɓa ba.
Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta,
ba zan ɗauke su a bakin kome ba.
Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku!
Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.
Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi,
adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!
“Kun kawo mini hadayu da sadakoki
shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila?
Kun ɗaga masujadar sarkinku,
siffofin gumakanku,
tauraron allahnku,5.26 Ko kuwa ɗaga Sakkut sarkinku da Kaiwan gumakanku, tauraron da suke allolinku; Seftuwajin ɗaga masujadar Molek da tauraro allahnku Refan, gumakansu
wanda kuka yi wa kanku.
Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,”
in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko.
Kaito ga zaman sakewa
Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona,
da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne,
ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya,
waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa!
Ku je Kalne ku dube ta;
ku wuce daga can zuwa Hamat-rabba,
sa’an nan ku gangara zuwa Gat a Filistiya.
Sun fi masarautunku biyu ne?
Ƙasarsu ta fi taku girma?
Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar rana
kuna kuma jawo mulkin tashin hankali kusa.
Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa
kuna mimmiƙe a kan kujerunku.
Kuna cin naman ƙibabbun raguna
da na ƙosassun ’yan maruƙa.
Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi
kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.
Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi
kuna kuma shafa mai mafi kyau,
amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.
Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta;
bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare.
Ubangiji yana ƙyamar girmankan Isra’ila
Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta,
“Ina ƙyamar girman kan Yaƙub,
ba na kuma son kagarunsa;
zan ba da birnin
da duk abin da yake cikinta.”
Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu. In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”
Gama Ubangiji ya ba da umarni,
zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu
ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi.
Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu?
Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma?
Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi
amfanin adalci kuma ya zama ɗaci,
ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar6.13 Lo Debar yana nufin wofi. da yaƙi
kuka kuma ce, “Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim6.13 Karnayim yana nufin ƙahoni; ƙaho a nan yana a matsayin ƙarfi. ba?”
Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce,
“Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila,
wadda za tă matsa muku tun
daga Lebo6.14 Ko kuwa daga mashigi zuwa Hamat zuwa kwarin Araba.”
Fāri, wuta, da igiyar gwaji
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa. Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa.
“Wannan ba zai faru ba,” in ji Ubangiji.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa. Sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”
Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa.
“Wannan ma ba zai faru ba,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa. Sai Ubangiji ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?”
Sai na amsa, “Igiyar gwada gini.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Duba, zan sa igiyan nan a cikin mutanena Isra’ila; ba zan ƙara barinsu ba.
“Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku
kuma tsarkakan wurare na Isra’ila za su zama kango;
da takobina zan tayar wa gidan Yerobowam.”
Amos da Amaziya
Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba. Gama ga abin da Amos yake cewa,
“ ‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi,
kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta,
nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can. Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.”
Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul. Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’ Yanzu fa, sai ka ji maganar Ubangiji. Ka ce,
“ ‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila,
kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’
“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce,
“ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni,
kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata.
Za a auna ƙasarka a kuma raba ta,
kai kuma za ka mutu a ƙasar arna.7.17 Da Ibraniyanci marasa tsabta
Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta,
nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
Kwandon nunannun ’ya’yan itace
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji ya nuna mini kwandon nunannun ’ya’yan itace. Ya yi tambaya ya ce, “Me ka gani Amos?”
Sai na amsa na ce, “Kwandon nunannun ’ya’yan itace.”
Sai Ubangiji ya ce mini, “Lokaci ya yi wa mutanena Isra’ila da ba zan ƙara barinsu ba.
“A ranan nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “Waƙoƙin a haikali za su koma makoki.8.3 Ko kuwa “mawaƙar haikali za su yi makoki” Za a ga gawawwaki a ko’ina! Shiru!”
Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata
kuka kori matalautan ƙasar.
Kuna cewa,
“Yaushe Sabon Wata zai wuce
don mu sayar da hatsi,
Asabbaci ta wuce,
don mu sayar da alkama?”
Mu yi awo da ma’aunin zalunci
mu ƙara kuɗin kaya
mu kuma cutar da mai saya,
mu sayi matalauta da azurfa
masu bukata kuma da takalmi,
mu sayar da alkamar haɗe da yayi.
Ubangiji ya rantse da Girman Yaƙub, “Ba zan taɓa mantawa da duk wani abin da suka yi ba.
“Shin, ƙasar ba za tă yi rawan jiki saboda wannan ba,
kuma duk masu zama a cikinta ba za su yi makoki ba?
Ƙasar duka za tă hau ta sauka kamar Nilu;
za a dama ta sa’an nan ta nutse
kamar kogin Masar.
“A wannan rana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka,
“Zan sa rana ta fāɗi da tsakar rana
in kuma duhunta duniya da rana tsaka.
Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki
kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka.
Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki
za ku kuma aske kawunanku.
Zan sa wannan lokaci yă zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi
kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci.
“Ranakun suna zuwa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka,
“sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar,
ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba,
sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji.
Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku
suna yawo daga arewa zuwa kudu,
suna neman maganar Ubangiji,
amma ba za su samu ba.
“A wannan rana
“kyawawan ’yan mata da kuma samari masu ji da ƙarfi
za su suma don ƙishirwa.
Waɗanda suka yi rantsuwa da abin kunya8.14 Ko kuwa da Ashima; ko da gunki na Samariya,
ko kuma su ce, ‘Muddin allahnku yana a raye, ya Dan,’
ko kuwa, ‘Muddin allahn8.14 Ko kuwa iko Beyersheba yana a raye,’
za su fāɗi,
ba kuwa za su ƙara tashi ba.”
Za a hallaka Isra’ila
Na ga Ubangiji yana tsaye a gaban bagade, ya kuma ce,
“Bugi kan ginshiƙan
don madogaran ƙofa su girgiza.
Saukar da su a kan dukan mutane;
waɗanda ba su mutu ba zan kashe su da takobi.
Ba mutum guda da zai tsere,
babu wani da zai tsira.
Ko da sun tona rami kamar zurfin kabari,
daga can hannuna zai fitar da su.
Ko da sun hau can sama
daga can zan sauko da su.
Ko da sun ɓuya a bisa Karmel,
a can zan farauce su in cafko.
Ko da sun ɓuya can ƙarƙashin teku,
a can zan umarci maciji yă sare su.
Ko da abokan gābansu sun kore su zuwa zaman bauta,
a can zan umarci takobi yă kashe su.
“Zan sa musu ido
don mugunta ba don alheri ba.”
Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki,
shi da yakan taɓa ƙasa sai ta narke,
kuma dukan mazauna cikinta suna makoki,
ƙasar gaba ɗaya takan hau ta kuma sauka kamar Nilu,
sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar,
shi da ya gina kyakkyawar fadarsa9.6 Ma’anar Ibraniyanci don wannan zance babu tabbas. a cikin sammai
ya kuma kafa harsashenta9.6 Ma’anar Ibraniyanci don wannan kalma babu tabbas. a duniya,
shi da yakan kira ruwan teku
yă kuma kwarara su a bisa duniya,
Ubangiji ne sunansa.
“Ku ba Isra’ilawa ba ne,
daidai gare ni kamar yadda Kushawa suke?”9.7 Wato, mutane daga yankin bisa na Nilu
In ji Ubangiji.
“Ban fito da Isra’ila daga Masar ba,
Filistiyawa kuma daga Kaftor9.7 Wato, Kirit
Arameyawa kuma daga Kir ba?
“Tabbatacce idanun Ubangiji Mai Iko Duka
suna a kan mulkin nan mai zunubi.
Zan hallaka shi
daga fuskar duniya,
duk da haka ba zan hallaka
gidan Yaƙub ƙaƙaf ba,”
in ji Ubangiji.
“Gama zan ba da umarni,
zan kuma tankaɗe gidan Isra’ila
a cikin dukan ƙasashe
kamar yadda ake tankaɗe hatsi a cikin matankaɗi
kuma ko ƙwaya ɗaya ba za tă fāɗi a ƙasa ba.
Dukan masu zunubi a cikin mutanena
za su mutu ta wurin takobi,
wato, su masu cewa,
‘Masifa ba za tă fāɗo ko ta same mu ba.’
Maidowar Isra’ila
“A wannan rana zan maido
da tentin Dawuda da ya fāɗi.
Zan gyaggyara wuraren da suka yayyage,
in kuma maido da kufansa
in gina shi kamar yadda yake a dā,
domin su mallaki raguwar Edom
da duk al’ummai da suke amsa sunana,”9.12 Da Ibraniyanci; Seftuwajin don raguwar mutane / da kuma dukan al’umman da ake kira da sunana za su nemi Ubangiji
in ji Ubangiji shi wanda zai yi waɗannan abubuwa.
“Ranaku suna zuwa, in ji Ubangiji,
“sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi
mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi.
Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu
yă kuma kwararo daga tuddai.
Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta9.14 Ko kuwa zan maido da nasarar mutanena Isra’ila.
“Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu.
Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu;
za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu.
Zan dasa Isra’ila a ƙasarsu,
ba kuwa za a ƙara tumɓuke su
daga ƙasar da na ba su ba,”
in ji Ubangiji Allahnku.