- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ 1 Sarakuna 1 Sarakuna 1 Sarakuna 1Sar 1 Sarakuna Adoniya ya naɗa kansa Sarki Sa’ad da Sarki Dawuda ya tsufa ya kuma ƙara shekaru, ba ya iya jin ɗumi ko an rufe shi da abin rufuwa. Saboda haka bayinsa suka ce masa, “Bari mu nemi wata budurwa wadda za tă yi wa ranka yă daɗe, sarki hidima, tă kuma kula da shi. Za tă dinga kwanta kusa da ranka yă daɗe, yă ji ɗumi.” Suka nemi kyakkyawar yarinya cikin fāɗin Isra’ila, sai suka sami Abishag, mutuniyar Shunam, suka kawo ta wa sarki. Yarinyar kuwa kyakkyawa ce ƙwarai; ta kuwa lura da sarki, ta kuma yi masa hidima, amma sarki bai yi jima’i da ita ba. Adoniya,1.5 Adoniya shi ne ɗa na huɗu na Dawuda (2Sam 3.4) kuma yana da shekara 35 da haihuwa. Amnon, Absalom, da Kileyab (da ya mutu yana yaro) duk sun mutu. wanda mahaifiyarsa ce Haggit, ya fito ya ce, “Zan zama sarki.” Saboda haka ya nemi kekunan yaƙi, ya kuma shirya dawakai, tare da mutane hamsin da za su sha gabansa. (A duk rayuwarsa mahaifinsa bai taɓa tsawata masa yă ce, “Me ya sa kake yin haka ba?” Shi kuwa mai kyan gani ne ƙwarai, shi ne aka haifa bayan Absalom.) Adoniya ya haɗa baƙi da Yowab ɗan Zeruhiya1.7 Zeruhiya ’yar’uwar Dawuda ce da kuma Abiyatar firist, suka kuma ba shi goyon baya. Amma Zadok firist, Benahiya ɗan Yehohiyada, annabi Natan, Shimeyi, Reyi1.8 Ko kuwa da abokansa da kuma matsara na musamman na Dawuda ba su bi Adoniya ba. Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda, amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benahiya, ko wani daga matsara na musamman, ko kuwa ɗan’uwansa Solomon ba. Sai Natan ya ce wa Batsheba, mahaifiyar Solomon, “Ki san cewa Adoniya, ɗan Haggit, ya zama sarki ba tare da sanin ranka yă daɗe, sarkinmu Dawuda ba? Yanzu bari in ba ki shawara yadda za ki cece ranki da kuma ran ɗanki Solomon. Ki shiga wurin Sarki Dawuda ki ce masa, ‘Ranka yă daɗe sarki, ba ka rantse mini ni baiwarka cewa, “Tabbatacce Solomon ɗanka ne zai zama sarki bayana, yă kuma zauna a kujerar sarautar ba”? To, me ya sa Adoniya ya zama sarki?’ Yayinda kike can kina magana da sarki, zan shiga in kuma tabbatar da abin da kika faɗa.” Saboda haka Batsheba ta je don tă ga sarki. A yanzu dai sarki ya tsufa, yana nan kuma a cikin ɗakinsa, inda Abishag mutuniya Shunam take masa hidima. Batsheba ta rusuna ta kuma durƙusa a gaban sarki. Sai sarki ya tambaye ta ya ce, “Me kike so?” Ta ce masa, “Ranka yă daɗe, kai kanka ka rantse mini ni baiwarka da sunan Ubangiji Allahnka cewa, ‘Solomon ɗanka zai zama sarki bayana, zai kuma zauna a kujerar sarautata.’ Amma yanzu Adoniya ya zama sarki, kai kuwa ranka yă daɗe sarki, ba ka san wani abu game da shi ba. Ya miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa, ya kuma gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da Abiyatar firist, da Yowab shugaban mayaƙa, amma bai gayyaci Solomon bawanka ba. Ranka yă daɗe sarki, idanun dukan Isra’ila suna a kanka, domin su san wa zai zauna a kujerar ranka yă daɗe sarkina, a bayanka. In ba haka, bayan an binne ranka yă daɗe sarki, tare da kakanninsa, za a wulaƙance ni da Solomon ɗana, kamar masu laifi.” Yayinda take cikin magana tare da sarki, sai annabi Natan ya iso. Sai aka faɗa wa sarki, “Ga annabi Natan.” Da Natan ya je gaban sarki, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa. Natan ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki, ko ka furta cewa Adoniya ne zai zama sarki a bayanka, yă kuma zauna a kujerar sarautarka? Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’ Amma bai gayyace ni bawanka, da Zadok firist, da Benahiya ɗan Yehohiyada, da kuma bawanka Solomon ba. Ranka yă daɗe, sarki, ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fadawanka, cewa ga wanda zai gāje Ranka yă daɗe, sarki ba?” Dawuda ya naɗa Solomon Sarki Sai Dawuda ya ce, “Kira Batsheba tă shiga.” Sai ta zo gaban sarki ta kuma tsaya a gabansa. Sai sarki ya yi rantsuwa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya cece ni daga kowace damuwa, tabbatacce a yau zan aikata abin da na yi miki rantsuwa da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila; Solomon ɗanki zai zama sarki bayana, kuma shi zai zauna a kan kujerar sarautata a maimakona.” Sai Batsheba ta rusuna da fuskarta har ƙasa, ta kuma durƙusa a gaban sarki ta ce, “Bari ran Sarkina Dawuda yă daɗe, har abada!” Sarki Dawuda ya ce, “Ku kira mini Zadok firist, annabi Natan, da Benahiya ɗan Yehohiyada.” Da suka zo gaban sarki, sai ya ce musu, “Ku ɗauki bayin sarki tare da ku, ku kuma sa ɗana Solomon a kan dokina, ku gangara da shi zuwa Gihon. A can ku sa Zadok firist, da annabi Natan su shafe shi sarki a bisa Isra’ila. Ku busa ƙaho, ku kuma yi ihu, kuna cewa, ‘Ran Sarki Solomon yă daɗe!’ Sa’an nan ku haura tare da shi, zai kuwa zo yă zauna a kujera sarautata, yă yi mulki a maimakona. Na naɗa shi mai mulki a bisa Isra’ila da Yahuda.” Benahiya ɗan Yehohiyada ya amsa wa sarki, ya ce, “Amin! Bari Ubangiji Allah na ranka yă daɗe sarkina, yă tabbatar da haka. Kamar yadda Ubangiji ya kasance da ranka yă daɗe, sarki, haka ma bari yă kasance da Solomon, yă kuma mai da kujerar sarautarsa tă fi kujerar sarautar ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, girma!” Sai Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa suka gangara, suka sa Solomon a kan dokin Sarki Dawuda, suka raka shi zuwa Gihon. Zadok firist ya ɗauki ƙahon mai daga tenti mai tsarki, ya shafe Solomon. Sa’an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka yi ihu, suna cewa “Ran Sarki Solomon yă daɗe!” Dukan mutane kuwa suka haura suka bi shi, suna busan sarewa, suna farin ciki sosai, har ƙasa ta girgiza saboda sowa. Adoniya tare da dukan baƙin da suke tare da shi kuwa suka ji wannan sa’ad da suke gama bikinsu. Da jin busan ƙaho, sai Yowab ya yi tambaya, ya ce, “Me ya jawo surutu haka a birni?” Tun yana cikin magana, sai Yonatan ɗan Abiyatar ya iso. Adoniya ya ce, “Shigo! Ai, mutumin kirki irinka, lalle ka kawo labari mai daɗi ne.” Yonatan ya ce wa Adoniya, “A ina! Ranka yă daɗe, Sarkinmu Dawuda ya naɗa Solomon sarki. Sarki ya aika shi tare da Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa, suka sa shi a kan dokin sarki, Zadok firist kuwa da annabi Natan sun shafe shi sarki a Gihon. Daga can suka haura suna kirari, birni kuwa ta ɓarke da sowa. Surutun da kake ji ke nan. Ban da haka ma, Solomon ne sarki yanzu. Yanzu haka, fadawa sun zo suna wa ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, sam barka, suna cewa, ‘Bari Allahnka yă sa sunan Solomon yă zama sananne fiye da naka, bari kuma sarautarsa tă fi taka girma!’ Sarki kuwa ya rusuna, ya yi sujada a kan gadonsa ya ce, ‘Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bar idanuna suka ga magāji a kan kujerar sarautata a yau.’ ” A nan fa, dukan baƙin Adoniya suka taso da rawar jiki suka watse. Amma Adoniya, don tsoron Solomon, ya je ya kama ƙahon bagade ya riƙe. Sa’ad da aka faɗa wa Solomon cewa, “Adoniya yana tsoron Sarki Solomon, kuma ya manne wa ƙahonin bagade. Yana cewa, ‘Bari Sarki Solomon yă rantse mini a yau cewa ba zai kashe bawansa da takobi ba.’ ” Solomon ya amsa ya ce, “In ya nuna kansa mai biyayya, ba gashin kansa da zai fāɗi ƙasa; amma in aka same mugunta a cikinsa, zai mutu.” Sai Sarki Solomon ya aiki mutane, suka kuma sauko da shi daga bagade. Adoniya kuwa ya zo, ya rusuna wa Sarki Solomon, sai Solomon ya ce, “Tafi gidanka.” Dawuda ya gargaɗe Solomon Da lokacin mutuwar Dawuda ya yi kusa, sai ya gargaɗe Solomon ɗansa, ya ce, “Ina gab da bin hanyar da kowa a duniya zai bi. Saboda haka ka yi ƙarfin hali, ka nuna kanka namiji, ka kiyaye abin da Ubangiji Allahnka yake bukata. Yi tafiya a hanyoyinsa, ka kiyaye ƙa’idodi, da umarnai, da dokoki, da kuma farillansa, kamar yadda suke a rubuce a Dokar Musa, don ka yi nasara a cikin kome da za ka yi, da kuma inda za ka tafi. Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, ‘In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.’ “Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa. Ka yi da shi gwargwadon hikimarka, amma kada ka bari yă gangara kabari da furfura2.6 Da Ibraniyanci Sheol; haka ma a aya 9. cikin salama. “Amma ka yi alheri ga ’ya’yan Barzillai mutumin Gileyad, ka sa su kasance a cikin waɗanda suke ci a teburinka. Sun goyi bayana sa’ad da nake gudu daga ɗan’uwanka Absalom. “Ka tuna, akwai kuma Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim, wanda ya yi ta yin mini muguwar la’ana a ranar da na tafi Mahanayim. Sa’ad da ya gangara ya same ni a Urdun, na rantse masa da sunan Ubangiji na ce, ‘Ba zan kashe ka da takobi ba.’ Amma yanzu, kada ka ɗauke shi marar laifi. Kai mutum ne mai hikima; za ka san abin da za ka yi da shi. Ka kawo furfuransa zuwa kabari da jini.” Sa’an nan Dawuda ya huta tare da kakanninsa. Sai aka binne shi a Birnin Dawuda. Ya yi sarauta shekaru arba’in a bisa Isra’ila. Wato, shekaru bakwai a Hebron da kuma talatin da uku a Urushalima. Solomon kuwa ya zauna a kan kujerar sarautar mahaifinsa Dawuda, mulkinsa kuwa ya kahu sosai. Sarautar Solomon ta kahu To, sai Adoniya, ɗan Haggit ya tafi wurin Batsheba mahaifiyar Solomon. Ita kuwa ta tambaye shi ta ce, “Lafiya?” Ya amsa ya ce, “I, lafiya.” Sa’an nan ya ƙara da cewa, “Ina da ɗan wani abin da zan faɗa miki.” Ta ce, “Faɗa.” Sai ya ce, “Kamar yadda kika sani, mulkin nan nawa ne. Dukan Isra’ila suna ɗaukana a matsayin sarki. Amma abubuwa suka canja, sai mulkin ya koma ga ɗan’uwana; gama ya zo masa daga Ubangiji ne. Yanzu ina da roƙo guda da zan yi gare ki. Kada ki hana mini.” Ta ce, “Sai ka faɗa.” Sai ya ci gaba, “In kin yarda, ki yi magana da Sarki Solomon, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce yă ba ni yarinyan nan, Abishag, mutuniyar Shunam, tă zama matata.” Batsheba ta ce, “Da kyau, zan yi magana da sarki dominka.” Sai Batsheba ta tafi wurin Sarki Solomon don tă yi masa magana a kan Adoniya. Sarki ya miƙe tsaye don yă sadu da ita, ya rusuna mata, ya kuma zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo wa mahaifiyar sarki kujerar sarauta, ta kuwa zauna a gefen damansa. Ta ce, “Ina da ɗan roƙon da zan nema ka yi mini. Ina fata ba za ka hana ni ba.” Sai sarki ya amsa ya ce, “Mahaifiyata, sai ki faɗa in ji, ba zan hana miki ba.” Saboda haka sai ta ce, “Ka sa a ba wa ɗan’uwanka Adoniya, Abishag mutuniyar Shunam tă zama matarsa.” Sarki Solomon ya amsa wa mahaifiyarsa ya ce, “Me ya sa kika roƙar wa Adoniya Abishag mutuniyar Shunam kawai? Ki ma sa a ba shi mulkin mana. Ai, shi yayana ne. I, ki roƙa dominsa, da domin Abiyatar firist, da kuma domin Yowab ɗan Zeruhiya mana!” Sai Sarki Solomon ya rantse da sunan Ubangiji ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani, idan ban sa Adoniya ya biya wannan roƙo da ransa ba! Yanzu kuwa, muddin Ubangiji yana a raye, shi wanda ya kafa ni sosai a kan kujerar sarautar mahaifina Dawuda, ya kuma kafa mini mulki kamar yadda ya yi alkawari; za a kashe Adoniya yau!” Saboda haka Sarki Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada yă kashe Adoniya; ya kuwa kashe shi. Ga Abiyatar firist kuwa sarki ya ce, “Tafi gonarka a Anatot. Ka cancanci ka mutu, amma ba zan kashe ka yanzu ba, domin ka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji Mai Iko Duka a gaban mahaifina Dawuda, ka kuma sha wahala tare mahaifina.” Saboda haka Solomon ya cire Abiyatar daga aikin firist na Ubangiji, ya cika maganar da Ubangiji ya yi a Shilo game da gidan Eli. Sa’ad da labarin ya kai wurin Yowab, wanda ya haɗa kai da Adoniya, ko da yake bai haɗa kai da Absalom ba, sai ya gudu zuwa tentin Ubangiji, ya kama ƙahonin bagade ya riƙe. Aka faɗa wa Sarki Solomon cewa Yowab ya gudu zuwa tentin Ubangiji, yana kuma kusa da bagade. Sai Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada ya ce, “Je ka kashe shi!” Sai Benahiya ya shiga tentin Ubangiji ya ce wa Yowab, “Sarki ya ce, ‘Ka fita!’ ” Amma Yowab ya amsa ya ce, “A’a, a nan zan mutu.” Sai Benahiya ya ce wa sarki, “Ga yadda Yowab ya amsa mini.” Sai sarki ya umarci Benahiya ya ce, “Yi kamar yadda ya faɗa. Ka kashe shi, ka kuma binne shi, ka wanke ni da gidan mahaifina daga laifin jini marasa laifin da Yowab ya zubar. Ubangiji zai sāka masa saboda jinin da ya zubar, domin ba da sanin mahaifina Dawuda ne ya fāɗa wa mutum biyun nan da takobi ba. Dukansu biyu, Abner ɗan Ner, shugaban mayaƙan Isra’ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban mayaƙan Yahuda, mutane ne mafi kyau da kuma mafi adalci fiye da shi. Bari alhakin jininsu yă koma a kan Yowab da kuma zuriyarsa har abada. Amma bari salamar Ubangiji tă kasance a kan Dawuda da zuriyarsa, da gidansa, da kuma mulkinsa, har abada.” Sai Benahiya ɗan Yehohiyada ya haura ya bugi Yowab, ya kashe shi, ya kuwa binne shi a gidansa2.34 Ko kuwa binne shi a kabarinsa a ƙauye. Sai sarki ya sa Benahiya ɗan Yehohiyada ya zama shugaba a bisa mayaƙa a matsayin Yowab, ya kuma sa Zadok firist a wurin Abiyatar. Sa’an nan sarki ya aika aka kawo Shimeyi, ya kuma ce masa, “Ka gina wa kanka gida a nan a Urushalima, ka zauna a ciki, kada ka kuskura ka tafi wani wuri. Gama ran da ka fita, ka haye Kwarin Kidron, ka tabbata za ka mutu, alhakin jininka kuwa zai koma kanka.” Shimeyi ya amsa wa sarki ya ce, “Abin da ka faɗa yana da kyau. Bawanka zai yi kamar yadda ranka yă daɗe sarki, ya faɗa.” Shimeyi kuwa ya yi zama a Urushalima na dogon lokaci. Amma bayan shekaru uku, biyu daga cikin bayin Shimeyi suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma’aka, sarkin Gat. Aka faɗa wa Shimeyi cewa, “Bayinka suna a Gat.” Da jin haka, sai ya tashi ya shimfiɗa wa jakinsa abin zama, ya hau, ya tafi Gat wurin Akish domin neman bayinsa. Shimeyi kuwa ya dawo da su gida daga Gat. Da aka faɗa wa Solomon cewa Shimeyi ya bar Urushalima zuwa Gat, har ya dawo. Sai sarki ya aika a kawo Shimeyi, ya ce masa, “Ban sa ka rantse da sunan Ubangiji, na kuma ja maka kunne cewa, ‘A ranar da ka kuskura ka bar nan ka tafi wani wuri, ka tabbata za ka mutu ba’? A lokacin ka ce mini, ‘Abin da ka faɗa yana da kyau. Zan kuwa kiyaye.’ To, me ya sa ba ka kiyaye rantsuwar da ka yi ga Ubangiji, ka kuma yi biyayya da umarnin da na ba ka ba?” Sarki ya ce wa Shimeyi, “Ka sani a zuciyarka dukan muguntar da ka yi wa mahaifina Dawuda. Yanzu Ubangiji zai sāka maka saboda muguntarka. Amma za a yi wa Sarki Solomon albarka, sarautar Dawuda kuma za tă kasance a tsare a gaban Ubangiji har abada.” Sai sarki ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada, yă fita, yă bugi Shimeyi, yă kashe shi. Ya kuwa kashe shi. Mulki kuwa ya kahu sosai a hannun Solomon. Solomon ya nemi hikima (2 Tarihi 1.1-13) Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima. A lokacin dai mutane suna miƙa hadaya a wurare a bisa tuddai, domin ba a riga an gina haikali saboda Sunan Ubangiji ba. Solomon ya ƙaunaci Ubangiji ta wurin yin tafiya bisa ga farillan mahaifinsa Dawuda, sai dai ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a wuraren nan na bisa tuddai. Sai sarki Solomon ya tafi Gibeyon don yă miƙa hadayu, gama a can ne wuri mafi muhimmanci na sujada. Solomon kuwa ya miƙa hadayun ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade. A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.” Solomon ya amsa ya ce, “Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana. “Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?” Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba. Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna. In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.” Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne. Ya koma Urushalima, ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama. Sa’an nan ya shirya wa fadawansa biki. Shari’a mai hikima To, ana nan sai waɗansu karuwai biyu suka zo wurin sarki, suka tsaya a gabansa. Sai ɗaya ta ce, “Ranka yă daɗe, wannan mata da ni muna zama a gida ɗaya. Na haifi jariri yayinda take can tare da ni. Kwana uku bayan haihuwar jaririna, wannan mata ma ta haifi jariri. Mu dai kaɗai ne; babu wani a gidan sai mu biyu. “Da dare ɗan wannan matan ya mutu domin ta kwanta a kansa. Saboda haka ta tashi da tsakar dare ta ɗauki ɗana daga gefena yayinda baiwarka take barci. Sai ta sa shi kusa da ƙirjinta, ta kuma sa mataccen ɗanta kusa da ƙirjina. Kashegari, da na farka don in shayar da ɗana, sai na tarar ya mutu! Amma sa’ad da na dube shi da kyau da safe, sai na ga ashe ba ɗan da na haifa ba ne.” Amma ɗaya matar ta ce, “A’a! Mai rai ɗin ne ɗana; mataccen naki ne.” Amma ta farin ta nace, “A’a! Mataccen ne naki; mai ran ne nawa.” A haka suka yi ta gardama a gaban sarki. Sarki ya ce, “Wannan ta ce, ‘Ɗana ne a raye, naki ne matacce,’ yayinda ɗayan tana cewa, ‘A’a! Ɗanki ne mataccen, nawa ne a raye.’ ” Sai sarki ya ce, “Kawo mini takobi.” Sai aka kawo takobi wa sarki. Ya ba da umarni ya ce, “Yanka yaron nan mai rai, gida biyu, kowacce ta ɗauki rabi.” Ainihin mamar ɗan da yake a raye ta cika da tausayi saboda ɗanta, sai ta ce wa sarki, “Ina roƙonka, ranka yă daɗe, kada ka kashe yaron! Ka ba ta kawai!” Amma ɗayan matar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu ɗan da rai, a ci gaba a raba shi!” Sai sarki ya zartar da hukuncinsa ya ce, “A ba da jariri mai ran ga mata ta fari. Kada a kashe shi; ita ce ainihin mahaifiyarsa.” Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci. Shugabanni da gwamnonin Solomon Sai Sarki Solomon ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila. Waɗannan su ne manyan shugabanninsa. Azariya ɗan Zadok shi ne firist; Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne mai lura da takardu. Benahiya ɗan Yehohiyada, shi ne shugaban mayaƙa. Zadok da Abiyatar, su ne firistoci. Azariya ɗan Natan, shi ne mai lura da shugabannin yanki. Zabud ɗan Natan, shi ne firist da kuma mai wa sarki shawara. Ahishar, shi ne sarkin fada. Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura da aikin gandu. Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara. Ga sunayensu, Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim; Ben-Deker, shi ne a Makaz, Sha’albim, Bet-Shemesh da Elon Bet-Hanan; Ben-Hesed, shi ne a Arubbot (Soko da dukan ƙasar Hefer); Ben-Abinadab, shi ne a Nafot Dor (ya auri Tafat ’yar Solomon); Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam; Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla); Ahinadab ɗan Iddo, shi ne a Mahanayim; Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon); Ba’ana ɗan Hushai, shi ne a Asher da Bayelot; Yehoshafat ɗan Faruwa, shi ne a Issakar; Shimeyi ɗan Ela, shi ne a Benyamin; Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin. Tanajin Solomon na kowace rana Mutanen Yahuda da na Isra’ila sun yi yawa sai ka ce yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka kuma yi farin ciki. Solomon kuwa ya yi mulki a bisa dukan masarautai daga Kogi4.21 Wato, Yuferites; haka ma a aya 24. zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Waɗannan ƙasashe sun yi ta kawo haraji, suka kuma zama bayin Solomon dukan kwanakin ransa. Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci, shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba. Gama ya yi mulki a bisa dukan masarautai yamma da Kogi, daga Tifsa zuwa Gaza, aka kuwa sami zaman lafiya a kowane gefe. A kwanakin da Solomon yake raye, Yahuda da Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba, sun zauna lafiya, kowane mutum ya zauna a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaurensa. Solomon yana da rumfunan dawakai masu jan kekunan yaƙi, dubu huɗu,4.26 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin (dubi kuma 2Tar 9.25); Ibraniyanci na da arba’in da kuma dawakai dubu goma sha biyu4.26 Ko kuwa masu hawa Shugabannin yankuna, kowanne a watansa yakan yi tanajin abinci domin Sarki Solomon da kuma duk wanda ya zo teburin sarki. Sun tabbatar ba a rasa kome ba. Kowa a cikinsu, bisa ga lokacin da aka ba shi, yakan kai hatsin sha’ir da ciyawa domin dawakan-kekunan yaƙi, da sauran dawakai a inda aka ajiye su. Hikimar Solomon Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku. Hikimar Solomon ta fi hikimar mutanen Gabas, ta kuma fi dukan hikimar Masar girma. Ya fi kowane mutum hikima, har da Etan dangin Ezra ma. Yana da hikima fiye da Heman, Kalkol da Darda, ’ya’yan Mahol maza. Sunansa ya bazu ko’ina a ƙasashen da suke kewaye. Ya yi karin magana dubu uku. Waƙoƙinsa kuwa sun kai dubu ɗaya da biyar. Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi. Mutane suka yi ta zuwa daga ƙasashe dabam-dabam don su ji hikimar Solomon. Sarakuna daga ko’ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi. Shirye-shirye don ginin haikali (2 Tarihi 2.1-16) Sa’ad da Hiram sarkin Taya ya ji an shafe Solomon sarki yă gāji mahaifinsa Dawuda, sai ya aika da jakadunsa zuwa wurin Solomon, gama shi da Dawuda abokai ne sosai dukan kwanakinsa. Solomon ya mayar da wannan saƙo ga Hiram ya ce, “Ka san cewa saboda yaƙe-yaƙen da abokan gāba suka yi da mahaifina a kowane gefe, ya sa bai iya gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahnsa ba, sai da Ubangiji ya sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa. Amma yanzu Ubangiji Allahna ya ba ni hutu a kowane gefe, babu kuma gāba ko masifa. Ina niyya in gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, yadda Ubangiji ya faɗa wa mahaifina Dawuda, sa’ad da ya ce, ‘Ɗanka wanda zai gāje ka, shi zai gina haikali domin Sunana.’ “Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.” Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.” Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan, “Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir. Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.” A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata. Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara. Ubangiji ya ba wa Solomon hikima, kamar yadda ya yi masa alkawari. Dangantakar zaman lafiya ta kasance tsakanin Hiram da Solomon, su biyun suka yi yarjejjeniya. Sarki Solomon ya ɗebi ma’aikata daga dukan Isra’ila, su dubu talatin. Ya riƙa aika su dubu goma-goma zuwa Lebanon kowane wata, saboda su yi wata ɗaya a Lebanon, watanni biyu kuma a gida. Adoniram ne ya lura da aikin gandun. Solomon ya kasance da ’yan ɗauko guda dubu saba’in da masu yankan duwatsu guda dubu tamanin a cikin tuddai, ya kuma kasance da shugabanni dubu uku da ɗari uku waɗanda suke lura da aikin, su ne kuma suke bi da ma’aikatan. Bisa ga umarnin sarki sai suka cire manyan duwatsu masu kyau don a tanada tushen duwatsun da aka gyara domin haikalin daga wurin haƙar duwatsun. Gwanayen Solomon da na Hiram da kuma mutanen Gebal5.18 Wato, Baibilos., su suka yanka, suka kuma shirya katako da dutse don ginin haikali. Solomon ya gina haikali A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji. Haikalin da Sarki Solomon ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu talatin ne. Shirayin da yake a gaban ainihin zauren haikalin, ya ƙara faɗin haikalin da kamu ashirin, ya kuma nausa daga gaban haikalin kamu goma. Ya yi tagogin da suka fi fāɗi daga ciki fiye da waje a haikalin. A jikin bangayen babban zaure da kuma cikin wuri mai tsarki, ya gina ɗakuna kewaye da ginin, inda akwai ɗakuna a gefe. Fāɗin ɗakunan ƙasa, kamu biyar ne, fāɗin ɗakunan tsakiya, kamu shida ne, fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa, kamu bakwai ne. Ya yi bangaye kewaye a waje da haikalin don kada a sa wani abu a bangayen haikali. A yin ginin haikalin, duwatsun da aka fafe ne kaɗai daga wurin fafe duwatsu aka yi amfani da su, ba a ji karar guduma ko gizago, ko wani abin da aka yi da ƙarfe a wurin ginin haikali yayinda ake gina shi ba. Ƙofar zuwa ɗakunan ƙasa tana gefen kudu na haikalin; akwai matakai da suka bi zuwa hawa na tsakiya, daga can kuma matakan sun wuce zuwa hawa na uku. A haka ya gina haikalin ya kuma gama shi, ya jinƙe shi da manyan katakai da kuma katakan al’ul. Ya kuma gina ɗakunan gefe duka a gefen haikalin. Tsayin kowanne, kamu biyar ne, aka haɗa su da haikalin da manyan katakan al’ul. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Solomon ta ce, “Game da wannan haikalin da kake ginawa, in ka bi ƙa’idodina, ka cika farillaina, ka kiyaye dukan umarnaina, ka kuma yi biyayya da su, zan cika alkawarin da na yi wa mahaifinka Dawuda ta wurinka. Zan kuma zauna a cikin Isra’ilawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.” Saboda haka Solomon ya gina haikalin ya kuma gama shi. (2 Tarihi 3.8-14) Ya rufe bangon ciki da katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama, ya kuma rufe daɓen da katakan itacen fir. Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi a can ƙuryar haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama. Tsawon babban zaure a gaban wannan ɗaki, kamu arba’in ne. An yi wa katakan itacen al’ul na cikin haikalin zāne mai fasalin gora da na buɗaɗɗun furanni. An rufe bangon ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin. Ya shirya wuri mai tsarki na ciki can cikin haikali don yă sa akwatin alkawarin Ubangiji a can. Tsawon wuri mai tsarki na ciki kamu ashirin, fāɗin kamu ashirin, tsayin kuma kamu ashirin. Ya dalaye cikin da zinariya zalla, ya kuma dalaye bagade al’ul ɗin. Solomon ya rufe cikin haikalin da zinariya zalla, ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban wuri mai tsarki na ciki, wanda aka dalaye da zinariya. Haka ya dalaye dukan cikin da zinariya. Ya kuma dalaye bagade na cikin wuri mai tsarki da zinariya. A wuri mai tsarki na can ciki, ya yi kerubobi biyu na itacen zaitun, kowanne mai tsayi kamu goma. Fiffike ɗaya na kerub na fari tsawonsa kamu biyar ne, ɗayan fiffike kuma kamu biyar, kamu goma daga ƙarshen fiffike zuwa ƙarshen fiffike. Kerub na biyun shi ma kamu goma ne, gama kerubobi biyun sun yi kama da juna a girma da kuma siffa. Tsayin kowane kerub kamu goma ne. Ya ajiye kerubobin a ɗaki na can cikin haikalin, da fikafikansu a buɗe. Fiffiken kerub ɗaya ya taɓa bango guda, yayinda fiffiken ɗayan ya taɓa ɗayan bangon, kuma fikafikansu sun taɓa juna a tsakiyar ɗakin. Ya dalaye kerubobin da zinariya. A bangaye kewaye da haikali, a ɗakuna ciki da waje, ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da furanni buɗaɗɗu. Ya kuma rufe ƙasan ɗakuna ciki da wajen haikali da zinariya. Don ƙofar shiga wuri mai tsarki na ciki kuwa, ya yi ƙofofin katakon zaitun da madogarai masu gefe biyar. A kan ƙofofin katakan zaitun kuwa ya zāzzāna kerubobi, itatuwa dabino, da furanni buɗaɗɗu, ya kuma dalaye kerubobin, da kuma itatuwan dabinon da zinariya. Haka ma ya yi madogarai masu gefe huɗu na katakon zaitun don ƙofar shiga zuwa babban zaure. Ya yi ƙofofi biyu na itacen fir, kowanne yana da shafi biyu da suke juyewa a maɗaurai. Ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da kuma furanni buɗaɗɗu a kansu, ya kuma dalaye su da zinariyar da aka buga daidai a kan sassaƙa. Ya kuma gina filin ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu, jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul. An kafa tushen haikalin Ubangiji a shekara ta huɗu, a watan Zif. A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin. Solomon ya gina fadarsa Ya ɗauki Solomon shekaru goma sha uku kafin yă gama gina fadarsa. Ya gina fadarsa mai suna Kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, fāɗinsa kamu hamsin, tsayinsa kuma kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al’ul, aka shimfiɗa katakan itacen al’ul a bisa ginshiƙan. Aka yi rufin da al’ul bisa ginshiƙan da suke bisa ginshiƙai arba’in da biyar, goma sha biya a kowane jeri. Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana ɗaura da ’yar’uwarta, har jeri uku. Dukan ƙofofin da madogaransu murabba’i ne, taga kuma tana ɗaura da ’yar’uwarta har jeri uku. Ya yi babban zaure mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, fāɗinsa kuwa kamu talatin. A gabansa kuwa akwai shirayi, kuma a gaban wannan shirayi akwai ginshiƙai da kuma rufin da yake a shimfiɗe. Ya kuma gina shirayi ta sarauta, da ya kira Zauren Adalci, inda zai riƙa yin shari’a, ya kuma rufe dukan daɓensa da itacen al’ul daga ƙasa har sama. A fadar da zai zauna kuwa, wadda aka gina a can baya, ya yi ta da irin fasali guda. Solomon ya kuma yi wata fada kamar wannan zaure domin ’yar Fir’auna, wadda ya auro. Dukan waɗannan gine-gine, daga waje zuwa babban fili, da kuma daga tushen zuwa rufin, an yi su da duwatsun da aka yanka, aka kuma gyara da zarto a fuskokinsu na ciki da waje. Aka kafa tushen da manyan duwatsu masu kyau, tsayin waɗansunsu ya kai kamu goma, waɗansu kuma kamu takwas. A can bisa akwai duwatsu masu tsada da aka yayyanka bisa ga ma’auni, da kuma ginshiƙan al’ul. An kewaye babban filin da katanga da jerin uku-uku na duwatsun da aka gyara, da kuma jeri guda na gyararren al’ul, kamar yadda aka yi na filin cikin haikalin Ubangiji da shirayinsa. Kayan haikali (2 Tarihi 3.15-17; 4.1-10) Sarki Solomon ya aika zuwa Taya aka kuma kawo Huram, wanda mahaifiyarsa gwauruwa ce daga kabilar Naftali, wanda kuma mahaifinsa mutumin Taya ne, shi Huram, gwani ne a aikin tagulla. Huram gwani ne sosai kuma ya saba da yin kowane irin aikin tagulla. Sai ya zo wurin Sarki Solomon ya kuma yi dukan aikin da aka sa shi. Ya yi ginshiƙan tagulla, kowanne tsayinsa kamu goma sha takwas, ya kuma yi guru mai kamu goma sha biyu, kewaye da shi. Ya yi dajiyoyi biyu na zubin tagulla don yă sa a bisa ginshiƙai; kowace dajiya tsayinta kamu biyar ne. Aka yi yanar tuƙaƙƙun sarƙoƙi aka ɗaura dajiyoyin a bisa ginshiƙai guda bakwai don kowace dajiya. Ya yi rumman jeri biyu kewaye da kowace yanar don yă yi adon dajiyoyin a bisa ginshiƙan. Haka kuma ya yi wa ɗaya dajiyar. Dajiyoyin da suke a bisa ginshiƙan a shirayi suna da fasalin furen bi-rana, tsayinsu kamu huɗu-huɗu ne. A inda kan ginshiƙin ya buɗu kamar kwano, sama da zāne-zānen sarƙar, an yi zāne-zānen rumman wajen ɗari biyu, layi-layi kewaye da kawunan ginshiƙan nan. Ya ta da ginshiƙai a shirayin haikali. Ya ba wa ginshiƙi na wajen kudu sunan Yakin,7.21 Yakin mai yiwuwa yana nufin ya kafa. na wajen arewa kuma ya kira Bowaz.7.21 Bowaz mai yiwuwa yana nufin a cikinsa akwai ƙarfi. Dajiyoyin da suke a bisa suna da fasalin bi-rana ne. Ta haka aka gama aiki a kan ginshiƙan. Sai Huram ya yi wani ƙaton kwano na ƙarfen tagulla, da ya kira Teku. Zurfin kwanon nan kamu bakwai da rabi, fāɗinsa kamu goma sha biyar, da’irarsa kuma kamu talatin ne. A kewayen bakin ƙaton kwanon akwai layi biyu na siffofin goran ƙarfen tagulla, akwai gora shida cikin kowane ƙafa. An yi zubinsu haɗe da kwanon nan da kira Teku. Kwanon ya tsaya a kan siffofin bijimai goma sha biyu, uku suna fuskantar arewa, uku suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, sa’an nan uku suna fuskantar gabas. Kwanon da ya kira Teku ya zauna a kansu, gindin siffofin bijimai goma sha biyun nan suna wajen tsakiya. Kaurin kwanon ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kamar da’iran kwaf, kamar bi-ranar da ta buɗe. Wannan kwanon da aka kira Teku yakan ci garwa dubu biyu. Ya kuma yi dakalai guda goma na tagulla da ake iya matsar da su; kowane tsawonsa kamu huɗu ne, fāɗinsa kamu huɗu, tsayinsa kuma kamu uku. Ga yadda aka yi dakalan, dakalan suna da ɓangarori haɗe da mahaɗai. A bisa sassan tsakanin mahaɗan, akwai siffofin zakoki, bijimai da kuma kerubobi, suna a kan mahaɗan su ma. A sama da kuma ƙasan siffofin zakokin da na bijiman kuwa akwai hotunan furanni. Kowane dakali yana da ƙafa huɗu na tagulla kamar na keken yaƙi, da sandunan tagulla don sa kwanon nan da aka kira Teku. A kusurwoyin akwai abubuwan zubi don riƙe kwanon. An zāna furanni a kowane gefensu. A dakalin daga ciki, akwai bakin da yake da’ira, mai zurfi kamun guda. Bakin da’irar ne, yana da zāne-zānensa da ya kai kamu ɗaya da rabi. Kusa da bakin akwai zāne-zāne. Sassan dakalin murabba’i ne, ba da’ira ba ne. Ƙafafu huɗun suna a ƙarƙashin ɓangarorin, aka kuma haɗa gindin ƙafafun keken da dakalin. Tsayin kowace ƙafa kamu ɗaya da rabi ne. An yi ƙafafun kamar ƙafafun keken yaƙi ne; gindin, da’irar, gyaffan da kuma cibiyar duk an yi su da ƙarfe ne. Kowane dakali yana da hannuwa huɗu, ɗaya a kowane gefe, da yake nausawa daga dakalin. A bisa dakalin akwai da’irar da ta yi kamar gammo mai zurfi kamar rabin kamu7.35 Wato, kamar inci 9 ko kuma kamar sentimita 23. Abubuwan da suke riƙewa da kuma sassan, an haɗa su da bisa dakalin. Ya zāna siffofin kerubobi, zakoki da itatuwan dabino a saman abubuwan riƙewa da kuma a kan ɓangarorin, a kowane abin da ya ga akwai ɗan fili, ya zāna furanni. Haka ya yi dakalai goma. Duk an yi zubinsu iri ɗaya ne, girmansu da fasalinsu kuma iri ɗaya. Sa’an nan ya yi kwanoni goma na tagulla, kowane yana cin garwa arba’in, kuma kamu huɗu daga wannan zuwa wancan, kowane dakali yana da daro ɗaya. Ya sa dakalai biyar a gefen kudu na haikali, biyar kuma a arewa. Ya sa kwanon a gefen kudu, a gefen kudu maso gabas na haikalin. Ya kuma yi kwanoni da manyan cokula da kuma kwanonin yayyafawa. (2 Tarihi 4.11–5.1) Ta haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sarki Solomon a haikalin Ubangiji. Ya yi ginshiƙai biyun; dajiyoyi biyu masu fasalin kwano a kan ginshiƙan; ya yi yanar kashi biyu wa dajiyoyi masu fasalin kwano guda biyu a kan ginshiƙai; ya yi rumman guda ɗari huɗu na sashi yanar biyun (jeri biyu na rumman don kowace yanar, yana adon dajiyoyi masu fasalin kwano a kan ginshiƙai); ya yi dakalai goma da kwanoninsu goma; ya yi kwanon da ya kira Teku, da bijimai goma sha biyu a ƙarƙashinsa; ya yi tukwane, manyan cokula da kwanonin yayyafawa. Dukan waɗannan abubuwan da Huram ya yi wa Sarki Solomon saboda haikalin Ubangiji, an dalaye su da tagulla. Sarki ya sa aka yi zubi a abin yin tubalin laka a filin Urdun, tsakanin Sukkot da Zaretan. Solomon ya bar dukan waɗannan abubuwa ba tare da an auna su ba, domin sun yi yawa sosai; ba a san nauyin tagullar ba. Solomon ya kuma yi dukan kayayyakin da suke cikin haikalin Ubangiji. Ya yi bagaden zinariya; teburin zinariya, inda ake ajiye burodin Kasancewa; ya yi alkukai na zinariya zalla (Biyar a dama, biyar kuma a hagu, a gaban wuri mai tsarki na can cikin); ya yi zāne-zānen furannin zinariya da fitilu da kuma arautaki; ya yi kwanonin zinariya zalla, hantsuka, kwanonin yayyafawa, kwanoni, da kuma farantan wuta; ya yi wurin ajiye fitila na zinariya domin ƙofofi na ɗakin can ciki-ciki, da na ƙofofin Wuri Mafi Tsarki, da kuma domin ƙofofin babban zauren haikali. Sa’ad da aka gama aikin da Sarki Solomon sa a yi domin haikalin Ubangiji, sai ya kawo kayayyakin da mahaifinsa Dawuda ya keɓe, azurfa da zinariya da kayayyaki, ya sa su a ma’ajin haikalin Ubangiji. An kawo akwatin alkawari a haikali (2 Tarihi 5.2–6.2) Sai Sarki Solomon ya tattara dattawan Urushalima a gabansa, da dukan shugabannin kabilu, da shugabannin iyalan Isra’ilawa, domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda. Dukan mutanen Isra’ila suka tattaru a gaban Sarki Solomon a lokacin biki, a watan Etanim, wato, wata na bakwai. Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka iso, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin, suka haura da akwatin alkawarin Ubangiji da kuma Tentin Sujada, da dukan kayayyaki masu tsarkin da suke cikinsa. Firistoci da Lawiyawa suka ɗauko su, sai Sarki Solomon da dukan taron Isra’ila da suka tattaru kewaye da shi a gaban akwatin alkawari, suka yi ta miƙa hadayar tumaki da bijimai masu yawa da ba a iya lissaftawa, ko ƙirgawa. Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji inda aka shirya masa, can ciki cikin haikali, a Wuri Mafi Tsarki, aka kuma sa shi a ƙarƙashin fikafikan kerubobin. Kerubobin sun buɗe fikafikansu a bisa wurin da akwatin alkawarin yake, suka inuwartar da akwatin alkawarin da sandunan ɗaukansa. Waɗannan sandunan sun yi tsawo har ana iya ganin bakinsu daga Wuri Mai Tsarki a gaban wuri mai tsarki na can ciki, amma ba a iya ganinsu daga waje na Wuri Mai Tsarki ba. Suna nan kuwa a can har wa yau. Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da Isra’ilawa bayan sun fito Masar. Sa’ad da firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya cika haikalin Ubangiji. Firistocin kuwa ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalinsa. Sai Solomon ya ce, “Ubangiji ya ce zai zauna a gizagizai masu duhu; ga shi na gina haikali mai daraja dominka, inda za ka zauna har abada.” (2 Tarihi 6.3-11) Yayinda dukan taron Isra’ila suke tsattsaye a can, sai sarki ya juya ya albarkace su. Sa’an nan ya ce, “Ku yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannunsa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce, ‘Tun ran da na fitar da mutanena Isra’ila daga Masar, ban zaɓi wani birni a cikin wata kabilar Isra’ila a gina haikali domin Sunana yă kasance a can ba, amma na zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’ “Mahaifina Dawuda ya yi niyya a cikin zuciyarsa yă gina haikali saboda Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Saboda yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka yi niyyar wannan a zuciyarka. Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikali, amma ɗanka, wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’ Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina, yanzu kuma ga shi na zauna a kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya yi alkawari, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Na tanada wuri saboda akwatin alkawari, akwatin da ya ƙunshi alkawarin da Ubangiji ya yi da kakanninmu sa’ad da ya fitar da su daga Masar.” Addu’ar Solomon ta miƙawa (2 Tarihi 6.12-42) Sai Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji, a gaban dukan taron Isra’ila, ya ɗaga hannuwansa sama, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu. Ka kiyaye alkawarinka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina. Da bakinka ka yi alkawari, da hannunka kuma ka cika shi, yadda yake a yau. “Yanzu, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari ka cika wa bawanka Dawuda mahaifina alkawaran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza sun yi hankali cikin dukan abubuwan da suke yi, don su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi.’ Yanzu fa, ya Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina tă cika. “Amma anya, Allah, za ka zauna a duniya? Sammai, har ma da saman sammai ba za tă iya riƙe ka ba, balle wannan haikalin da na gina! Duk da haka ka ji addu’ar bawanka da kuma roƙonsa don jinƙai, ya Ubangiji Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka a wannan rana. Bari idanunka su buɗe, su fuskanci wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce, ‘Sunana zai kasance a can,’ saboda ka ji addu’ar bawanka in yana fuskantar wannan wuri. Ka ji roƙon bawanka da kuma na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a, suka fuskanci wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka, kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta. “Sa’ad da mutum ya yi abin da ba daidai ba ga maƙwabcinsa, an kuma bukace shi yă yi rantsuwa, sai ya zo ya rantse a gaban bagade a cikin haikalin nan, sai ka ji daga sama, ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, ka hukunta mai laifi, ka mai da laifinsa a kansa, mai gaskiya kuma ka nuna shi marar laifi ne bisa ga gaskiyarsa. “Sa’ad da abokan gāba suka ci mutanenka Isra’ila a yaƙi saboda sun yi maka zunubi, sa’ad da kuma suka dawo gare ka don su furta sunanka, suna addu’a suna roƙo gare ka a wannan haikali, ka ji daga sama, ka gafarta zunubin mutanenka, ka kuma dawo da su ƙasar da ka ba wa kakanninsu. “Sa’ad da sammai sun kulle, babu kuma ruwan sama domin mutane sun yi maka zunubi, sa’ad da suka yi addu’a suna fuskantar wannan wuri, suka kuma furta sunanka, suka juye daga zunubinsu domin ka hore su, ka ji daga sama, ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace ta rayuwa, ka kuma aika da ruwan sama a ƙasar da ka ba wa mutanenka gādo. “Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, ko kuwa abokan gāba sun yi musu kwanto, a wani daga cikin biranensu, duk wata cuta, ko ciwon da ya zo, in suka yi addu’a ko roƙo ta wurin wani daga cikin mutanenka Isra’ila, kowa ya san wahalar zuciyarsa, ya kuma buɗe hannuwansa yana fuskantar wannan haikali, sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi wani abu. Ka yi da kowane mutum bisa ga dukan abin da ya yi, tun da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan dukan mutane), saboda su ji tsoronka a kowane lokacin da suke zaune a ƙasar da ka ba wa kakanninmu. “Game da baƙo kuwa wanda shi ba na mutanenka Isra’ila ba, amma ya zo daga ƙasa mai nisa saboda sunanka, gama mutane za su ji game da girman sunanka, da ƙarfin hannunka, da kuma hannunka mai iko, sa’ad da ya zo, ya yi addu’a yana fuskantar wannan haikali, ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi dukan abin da baƙon ya tambaye ka, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, bari kuma su san cewa wannan gidan da na gina, ya amsa Sunanka. “Sa’ad da mutanenka suka tafi yaƙi da abokan gābansu, a duk inda ka aike su, sa’ad da kuma suka yi addu’a ga Ubangiji suna fuskantar birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka, ka ji addu’arsu da roƙonsu daga sama, ka kuma biya musu bukatansu. “Sa’ad da suka yi maka zunubi, gama babu wanda ba ya zunubi, ka kuwa yi fushi da su, ka kuma ba da su ga abokin gāba, wanda ya kwashe su kamammu zuwa ƙasarsa, nesa ko kusa; in suka canja zuciyarsu a ƙasar da aka riƙe su kamammu, suka tuba, suka kuma roƙe ka a ƙasar waɗanda suka ci su da yaƙi, suka ce, ‘Mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba, mun yi mugunta’; in sun juye gare ka da dukan zuciyarsu, da dukan ransu a ƙasar abokan gābansu waɗanda suka kwashe kamammu, suka yi addu’a gare ka, suka fuskanci wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, waje birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka; sai ka ji daga sama, mazauninka, ka ji addu’a da roƙonsu, ka kuma biya musu bukatansu. Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi; ka gafarta dukan laifofin da suka yi maka, ka kuma sa waɗanda suka ci su a yaƙi su ji tausayinsu. Gama su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fitar daga Masar, daga tanderu mai narken ƙarfe. “Bari idanunka su buɗe ga roƙon bawanka, ga roƙon mutanenka Isra’ila, bari kuma ka saurare su sa’ad da suka yi kuka gare ka. Gama ka ware su daga dukan al’umman duniya su zama abin gādonka, kamar yadda aka furta ta wurin bawanka Musa sa’ad da kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka ka fitar da kakanninmu daga Masar.” Da Solomon ya gama dukan waɗannan addu’o’i da roƙe-roƙe ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda ya durƙusa da hannuwansa a buɗe waje sama. Ya tashi ya kuma albarkaci dukan taron Isra’ila da babbar murya, yana cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya ba wa mutanensa hutu kamar dai yadda ya yi alkawari. Babu magana guda da ta kāsa cika cikin dukan alkawaransa masu kyau da ya yi ta wurin bawansa Musa. Bari Ubangiji Allah yă kasance tare da mu kamar yadda ya kasance da kakanninmu; kada yă taɓa rabu da mu, ko yă yashe mu. Bari yă juye zukatanmu gare shi, don mu yi tafiya a cikin dukan hanyoyinsa, mu kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa, da kuma farillan da ya ba wa kakanninmu. Bari kuma waɗannan kalmomina, waɗanda na yi addu’a a gaban Ubangiji, su yi kusa da Ubangiji Allahnmu, dare da rana, don yă biya bukatan bawansa da na mutanensa Isra’ila, bisa ga bukatan kowa, saboda dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji, shi ne Allah, babu kuma wani. Amma dole ku miƙa zukatanku ga Ubangiji Allahnmu, don ku rayu, ta wurin bin ƙa’idodinsa, ku kuma yi biyayya da umarnansa, kamar yadda kuke yi a wannan lokaci.” Keɓewar haikali (2 Tarihi 7.4-10) Sai sarki da dukan Isra’ila, suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji. Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji. A wannan rana sarki ya tsarkake sashe na tsakiyar fili a gaban haikalin Ubangiji, a can kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, da kitsen hadaya ta salama, gama bagaden tagulla a gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta sosai da za a miƙa hadayun ƙonawa, hadayun hatsi, da kuma kitsen hadayun salama. Ta haka Solomon da dukan Isra’ila, wato, babban taro, suka yi bikin a lokacin. Mutane suka zo, tun daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar. Suka yi biki a gaban Ubangiji Allahnmu, kwana bakwai. Suka kuma ƙara kwana bakwai, kwanaki goma sha huɗu gaba ɗaya. A rana ta biye sai ya sallame mutane. Suka sa wa sarki albarka, sa’an nan suka watse zuwa gida, da farin ciki, da murna a zukatansu saboda kyawawan abubuwan da Ubangiji ya yi domin bawansa Dawuda, da kuma mutanensa Isra’ila. Ubangiji ya bayyana ga Solomon (2 Tarihi 7.11-22) Sa’ad da Solomon ya gama ginin haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki, ya kuma yi dukan abin da yake so yă yi, sai Ubangiji ya bayyana gare shi sau na biyu, kamar yadda ya bayyana masa a Gibeyon. Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu’arka da kuma roƙon da ka yi a gabana; na tsarkake wannan haikali wanda ka gina, ta wurinsa Sunana zai kasance a can har abada. Idanuna da zuciyata kullum za su kasance a can. “Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina, zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’ “Amma in kai, ko ’ya’yanka maza, suka juye daga gare ni, ba ku kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da na ba ku ba, kuka yi gaba, kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka kuma yi musu sujada, sai in yanke mutanen Isra’ila daga ƙasar da na ba su, in kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Isra’ila kuwa za tă zama abin gori da abin dariya a cikin dukan mutane. Wannan haikali zai zama tarin juji. Duk wanda ya wuce ta hanyan nan kuwa zai ji tausayi, yă kuma yi tsaki yana cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka ga wannan ƙasa da kuma wannan haikali?’ Mutane za su amsa su ce, ‘Saboda sun yashe Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna yin musu sujada, suna bauta musu ne, ya sa Ubangiji ya kawo dukan masifan nan a kansu.’ ” Waɗansu ayyukan Solomon (2 Tarihi 8.1-18) A ƙarshen shekaru ashirin da Solomon ya ɗauka yana gina haikalin Ubangiji da fadan sarki, sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki. Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya don yă ga garuruwan da Solomon ya ba shi, sai bai ji daɗi ba. Sai ya ce, “Wanda irin garuruwa ke nan ka ba ni, ɗan’uwana?” Saboda haka ya kira su Ƙasar Kabul9.13 Kabul ya yi kamar kalmar Ibraniyanci na abu marar amfani., sunan da suke da shi har wa yau. Hiram kuwa ya aika wa sarki talenti 1209.14 Wato, kamar ton 4 da 1/2 ke nan na zinariya. Ga lissafin ma’aikatan gandun da Sarki Solomon ya ɗauka don ginin haikalin Ubangiji, da fadarsa, da madogaran gini, da katangar Urushalima, da kuma Hazor Megiddo da Gezer. (Fir’auna sarkin Masar ya kai wa Gezer hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Ya sa mata wuta, ya kashe Kan’aniyawanta mazaunan wurin, ya kuma ba da ita a matsayin kyautar aure ga ’yarsa, matar Solomon. Solomon kuwa ya sāke gina Gezer.) Ya gina Bet-Horon ta Kwari, da Ba’alat, da Tadmor a hamada, na cikin ƙasarsa. Haka kuma ya gina dukan biranen ajiyarsa, da garuruwa domin kekunan yaƙinsa, da garuruwa domin dawakansa. Ya gina duk abin da ya so yă ginawa a Urushalima, da Lebanon, da kuma ko’ina a dukan yankin da ya yi mulki. Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa da Yebusiyawan da suka ragu a ƙasar (waɗanda ba Isra’ilawa ba ne), wato, waɗanda suka ragu a ƙasar, waɗanda Isra’ilawa ba su iya hallakawa ba, su ne Solomon ya ɗauka su zama bayinsa don aikin gandu, kamar yadda yake har wa yau. Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi ba; su ne mayaƙansa, shugabannin gwamnatinsa, dogarawansa, shugabannin sojojinsa, da shugabanninsa na kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙinsa. Su ne kuma manyan shugabanni masu lura da ayyukan Solomon, su ne shugabanni 550 masu lura da mutanen da suke aiki. Bayan ’yar Fir’auna ta haura daga Birnin Dawuda zuwa fadan da Solomon ya gina mata, sai ya gina madogaran gini. Sau uku a shekara Solomon kan miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji, yana ƙone turare a gaban Ubangiji haɗe da su, ta haka ya cika abin da ake bukata na haikali. Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku. Hiram kuwa ya aiki mutanensa, masu tuƙan jirgin ruwa waɗanda suka san teku, don su yi hidima a jerin jiragen ruwa tare da mutanen Solomon. Suka tafi Ofir suka kuma dawo da talenti 420 na zinariya, wanda suka ba wa Sarki Solomon. Sarauniyar Sheba ta ziyarci Solomon (2 Tarihi 9.1-12) Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji game da sunan da Solomon ya yi, da kuma dangantakarsa da Ubangiji, sai ta zo tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso Urushalima da tawaga mai yawa, tare da raƙuma masu ɗauke da kayan yaji, da zinariya masu yawa, da duwatsu masu daraja. Ta zo wurin Solomon ta kuwa yi magana da shi game da dukan abin da take da shi a ranta. Solomon ya amsa dukan tambayoyinta, ba abin da ya yi wa sarki wuyan bayyanawa mata. Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina. Da irin abincin da yake kan teburinsa, da irin zaman fadawansa, da irin rigunan masu hidimarsa, da irin masu shayarwarsa, da kuma hadayun ƙonawar da yake yi a haikalin Ubangiji, sai ta yi mamaki ƙwarai. Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da abin da ka yi da kuma hikimarka gaskiya ne. Amma ban gaskata waɗannan abubuwa ba sai da na zo na gani da idanuna. Tabbatacce, ba a ma faɗa mini ko rabi ba. Gama cikin hikima da arziki, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba. Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka! Yabo ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗinka, ya kuma sa ka a kujerar sarautar Isra’ila. Ubangiji ya naɗa ka sarki saboda madawwamiyar ƙaunar wa Isra’ila, don ka yi shari’a da adalci.” Ta kuma ba sarki talenti 120 na zinariya, da kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa haka kamar yadda sarauniyar Sheba ta ba wa Sarki Solomon ba. (Jiragen ruwan Hiram suka kawo zinariya daga Ofir. Daga can kuma suka kawo kaya masu yawa na katakon almug, da kuma duwatsu masu daraja. Sarki ya yi amfani da almug don yă yi kayan ado wa haikalin Ubangiji da kuma don fadan sarki, don kuma yă yi molaye, da garayu saboda mawaƙa. Ba a taɓa yin jigilar katakon almug ko a gani irin yawan katakai haka ba har wa yau.) (2 Tarihi 9.13-28) Sarki Solomon ya ba wa sarauniyar Sheba dukan abin da take so, da kuma duk abin da ta nema, ban da abin da ya ba ta daga yalwar fadan sarki. Sa’an nan ta koma tare da tawagarta zuwa ƙasarta. Ɗaukakar Solomon Nauyin zinariya da Solomon yake samun kowace shekara, talenti 666 ne. Ban da haraji daga ’yan kasuwa, da fatake, da kuma daga dukan sarakunan Arabiya, da gwamnonin ƙasar. Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu na zinariya. An yi kowace garkuwa da zinariya bekas ɗari shida. Ya kuma yi ƙananan garkuwoyi ɗari uku na zinariya. An yi kowane garkuwa da zinariya minas uku. Ya sa su a cikin Fadar Kurmin Lebanon. Sa’an nan sarki ya yi kujerar sarauta mai nauyin giram na hauren giwa, aka kuma dalaye ta da zinariya zalla. Kujera sarautar ta kasance da matakai shida, kuma bayanta tana da bisa mai kamannin gammo. A kowane gefen kujerar akwai wurin sa hannu, da kuma zaki tsaye kusa da kowannensu. Zakoki goma sha biyu suna tsaye a matakai shida, ɗaya a kowane gefen ƙarshen mataki. Babu ƙasar da an taɓa gina irin wannan kujerar mulki. Dukan kwaf Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon, zinariya ce zalla. Babu wani abin da aka yi da azurfa, domin ba a ɗauki azurfa a bakin kome ba a zamanin Solomon. Sarki yana da jerin jiragen ruwan kasuwanci10.22 Da Ibraniyanci na jiragen Tarshish a teku, tare da jiragen ruwan Hiram. Sau ɗaya kowace shekara uku jerin jiragen yakan dawo ɗauke da zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai marasa wutsiya, da kuma gogon biri. Sarki Solomon ya yi suna a wadata fiye da dukan sarakunan duniya. Dukan duniya ta nemi su zo wurin Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. Kowace shekara, kowa da ya zo wurinsa yakan kawo kyautai, kayayyakin azurfa da na zinariya, riguna, makamai, da kayan yaji, dawakai da alfadarai. Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai; ya kasance da kekunan yaƙi dubu goma sha huɗu, da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, ya kuma ajiye tare da shi a Urushalima. Sarki ya mai da azurfa barkatai a cikin Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir na jumaiza a gindin tuddai. An yi jigilar dawakan Solomon daga Masar10.28 Mai yiwuwa Muzur, wani yanki a Silisiya; haka ma a aya 29. da kuma daga Kuye10.28 Mai yiwuwa Silisiya, ’yan kasuwan fadan sarki sun sayo su daga Kuye. Suka yi jigilar kekunan yaƙi daga Masar a bakin shekel ɗari shida na azurfa, doki ɗaya kuma a kan ɗari da hamsin. Sun kuma yi jigilarsu suna sayarwa ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa. Matan Solomon Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da ’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa. Sun fito daga al’ummai da Ubangiji ya ce wa Isra’ilawa, “Kada ku yi aurayya da su, domin tabbatacce za su juye zukatanku zuwa ga waɗansu alloli.” Duk da haka Solomon ya manne musu, ya nace, yana ƙaunarsu. Ya auri mata ɗari bakwai, haifaffun gidan sarauta, da kuma ƙwarƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa suka karkatar da shi. Yayinda Solomon yake tsufa, matansa suka juye zuciyarsa ga bin waɗansu alloli, zuciyarsa kuwa ba tă bi Ubangiji Allahnsa ɗungum kamar yadda zuciyar Dawuda mahaifinsa ta kasance ba. Ya bi Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Molek11.5 Da Ibraniyanci Milkom; haka ma a aya 33., allahn da aka hana na Ammonawa. Saboda haka Solomon ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Bai bi Ubangiji gaba ɗaya kamar yadda Dawuda mahaifinsa ya yi ba. A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa. Ya yi haka domin dukan baƙin matansa, waɗanda suka ƙone turare suka kuma miƙa hadayu ga allolinsu. Ubangiji ya yi fushi da Solomon domin zuciyarsa ya juye daga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bayyana masa sau biyu. Ko da yake ya hana Solomon bin waɗansu alloli, Solomon bai kiyaye umarnin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya ce wa Solomon, “Da yake halinka ke nan, ba ka kuma kiyaye alkawarina, da ƙa’idodina da na umarce ka ba, tabbatacce zan yage masarautar daga gare ka, in ba da ita ga ɗaya daga cikin bayinka. Amma saboda Dawuda mahaifinka, ba zan yi haka a zamaninka ba. Zan yage ta daga hannun ɗanka. Amma ba zan yage dukan masarautar daga gare shi ba, zan ba shi kabila ɗaya saboda Dawuda bawana, da kuma saboda Urushalima, wadda na zaɓa.” Abokan gāban Solomon Sai Ubangiji ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Hadad, mutumin Edom daga gidan sarautar Edom. A shekarun baya Dawuda ya ci Edom da yaƙi. Yowab, shugaban sojojinsa ya tafi can domin yă binne Isra’ilawa waɗanda suka mutu a yaƙi. Sa’ad da suke a can, sojojin Isra’ila suka kashe kowane ɗa namiji a Edom. Yowab da dukan Isra’ilawa suka zauna a can, wata shida, sai da suka hallaka dukan mutane a Edom. Amma Hadad yana ɗan yaro a lokaci, wanda ya gudu zuwa Masar tare da shugabannin mutanen Edom waɗanda suka yi wa mahaifinsa hidima. Suka taso daga Midiyan suka tafi Faran. Sa’an nan suka ɗauki mutane daga Faran suka tafi Masar, zuwa wurin Fir’auna wanda ya ba wa Hadad gida da ƙasa, ya kuma tanada masa da abinci. Fir’auna ya ji daɗin Hadad har ya ba shi ’yar’uwar matarsa, Sarauniya Tafenes, aure. ’Yar’uwar Tafenes ta haifi masa ɗa wanda ya kira Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a fadan sarki. A can, Genubat ya yi zama da ’ya’yan Fir’auna. Yayinda yake a Masar, Hadad ya ji Dawuda ya huta tare da kakanninsa, ya kuma ji cewa Yowab shugaban mayaƙa ya mutu. Sai Hadad ya ce wa Fir’auna, “Bari in tafi, don in koma ƙasata.” Fir’auna ya tambaye shi, ya ce, “Me ka rasa a nan da kake so ka koma garinka?” Ya ce, “Ba kome, amma ka dai bar ni in tafi!” Allah kuwa ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Rezon, ɗan Eliyada, wanda ya gudu daga maigidansa, Hadadezer sarkin Zoba. Rezon ya tattara mutane kewaye da shi, ya zama kuma shugaban ’yan tawaye sa’ad da Dawuda ya hallaka mayaƙan Zoba; ’yan tawayen suka tafi Damaskus, inda suka zauna, suka kuma yi mulki. Rezon ya zama babban abokin gāban Isra’ila cikin dukan kwanakin mulkin Solomon. Ya ƙara rikici a kan rikicin Hadad. Rezon ya ƙi mulkin Isra’ila da dukan ransa. Saboda haka Rezon ya yi mulki a Aram ya kuma ƙi jinin Isra’ila. Yerobowam ya yi wa Solomon tawaye Haka ma Yerobowam, ɗan Nebat, shi ma ya yi wa sarki tawaye. Shi ɗaya ne daga shugabannin Solomon, shi mutumin Efraim ne daga Zereda, mahaifiyarsa kuwa gwauruwa ce, mai suna Zeruwa. Ga yadda ya tayar wa sarki Solomon. Sarki Solomon ya gina madogaran gini11.27 Ko kuwa Millo, ya ciccika wurare a katangar birnin Dawuda mahaifinsa da ƙasa. To, Yerobowam mutum ne mai fasaha. Sa’ad da Solomon ya ga yadda matashin yake aiki da himma, sai ya sa shi yă lura da dukan aikin gandu na gidan Yusuf. Da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahiya, mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahiya yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai. Sai Ahiya ya kama sabuwar rigar da yake saye da ita ya yage ta gida goma sha biyu. Sa’an nan ya ce wa Yerobowam, “Ɗauki gida goma wa kanka, gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce ke nan, ‘Duba, zan yage masarauta daga hannun Solomon in ba ka kabilu goma. Amma saboda bawana Dawuda da kuma birnin Urushalima, wadda na zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila, zai sami kabila guda. Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba. “ ‘Amma ba zan ɗauki dukan masarautar daga hannun Solomon ba; na naɗa shi sarki, dukan kwanaki ransa saboda Dawuda bawana, wanda na zaɓa, wanda kuma ya kiyaye umarnai da farillaina. Zan ɗauke masarautar daga hannuwan ɗansa ne, in ba ka kabilu goma. Zan ba da ɗaya ga ɗansa don kullum Dawuda bawana yă kasance da fitila a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa Sunana. Amma fa, ga kai, zan ɗauke ka, za ka kuwa yi mulki bisa dukan abin da zuciyarka take so; za ka zama sarki a bisa Isra’ila. In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka. Zan ƙasƙantar da zuriyar Dawuda saboda wannan, amma ba har abada ba.’ ” Solomon ya yi ƙoƙari yă kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tsere zuwa Masar, zuwa wurin sarki Shishak, ya zauna a can sai bayan mutuwar Solomon. Mutuwar Solomon (2 Tarihi 9.29-31) Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, da dukan abubuwan da ya yi, da hikimar da ya nuna, an rubuta su a littafin tarihin Solomon. Solomon ya yi mulki a Urushalima, a bisa dukan Isra’ila, shekaru arba’in. Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda mahaifinsa. Sai Rehobowam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Isra’ilawa sun yi wa Rehobowam tawaye (2 Tarihi 10.1-19) Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ila sun je can don su naɗa shi sarki. Sa’ad da Yerobowam ɗan Nebat ya ji labari (gama har yanzu yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon), sai ya dawo daga Masar. Saboda haka mutane suka aika Yerobowam yă zo, sai shi da dukan taron Isra’ila suka tafi wurin Rehobowam, suka ce masa, “Mahaifinka ya sa mana kaya mai nauyin gaske, amma yanzu ka sassauta wannan aiki mai zafi, da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.” Rehobowam ya amsa, “Ku tafi, bayan kwana uku, ku dawo.” Sai mutane suka watse. Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawa waɗanda suka yi wa mahaifinsa Solomon, hidima a kwanakinsa. Ya ce, “Wace shawara ce za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?” Suka amsa, “In a yau za ka zama bawan waɗannan mutane, ka kuma yi musu hidima, ka ba su amsa mai kyau, kullum za su kasance bayinka.” Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawarar matasa waɗanda suka yi girma tare, waɗanda kuma suke masa hidima. Ya tambaye su, “Mece ce shawararku? Yaya za mu amsa wa waɗannan mutane masu cewa, ‘Ka sassauta nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?” Matasan, waɗanda suka yi girma tare da shi, suka amsa, “Faɗa wa waɗannan mutanen da suka ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sassauta kayanka.’ Ka ce musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri. Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.’ ” Bayan kwana uku, Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam yadda sarki ya faɗa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” Sai Sarki ya amsa wa mutane da zafi. Yana ƙin shawarar da dattawa suka ba shi. Ya bi shawarar matasa, ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.” Saboda haka sarki bai saurare mutane ba, gama wannan abin da ya faru daga wurin Ubangiji ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya, mutumin Shilo. Da dukan Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, “Ina ruwanmu da Dawuda! Ai! Ba mu da gādo wurin ɗan Yesse. Ya Isra’ila, kowa yă koma tentinsa! Dawuda, sai ka lura da gidanka!” Saboda haka Isra’ilawa suka watse zuwa gida. Amma ga Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da mulki a kansu. Sarki Rehobowam ya aiki Adoniram wanda yake shugaban aikin gandu, amma Isra’ila suka jajjefe shi da dutse har ya mutu. Sarki Rehobowam, ya sullale ya hau keken yaƙinsa ya tsere zuwa Urushalima. Tun daga wannan ranar ne mutanen Isra’ila suka shiga gāba da gidan Dawuda har wa yau. Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ji Yerobowam ya dawo, sai suka aika, suka kira shi zuwa taro, suka kuma naɗa shi sarki bisa dukan Isra’ila. Kabila Yahuda kaɗai ta kasance mai biyayya ga gidan Dawuda. (2 Tarihi 11.1-4) Da Rehobowam ya isa Urushalima, ya tattara dukan gidan Yahuda da kabilar Benyamin, ya sami sun kai mayaƙa dubu da tamanin. Sai aka shirya don su yaƙi gidan Isra’ila, su kuma mayar da masarautar wa Rehobowam ɗan Solomon. Amma waɗannan kalmomin Allah suka zo wa Shemahiya, mutumin Allah, cewa, “Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon, sarkin Yahuda, ka faɗa wa dukan gidan Yahuda da Benyamin, da kuma dukan sauran mutane, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku, Isra’ilawa. Ku koma gida, kowannenku, gama wannan aikina ne.” ’ ” Saboda haka suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka sāke watse zuwa gida, yadda Ubangiji ya umarta. ’Yan maruƙan zinariya a Betel da Dan Sai Yerobowam ya ƙara gina Shekem a ƙasar tudu ta Efraim, ya zauna a can. Daga can ya tafi ya gina Fenuwel. Yerobowam ya yi tunani a ransa ya ce, “Mai yiwuwa mulkin yă koma gidan Dawuda. In waɗannan mutane sun riƙa haurawa don su miƙa hadayu a haikalin Ubangiji a Urushalima. Za su sāke nuna biyayya ga mai girma, Rehobowam, sarkin Yahuda. Za su kashe ni su kuma koma ga Sarki Rehobowam.” Bayan ya nemi shawara, sai sarki ya yi siffofin ’yan maruƙa biyu na zinariya. Ya ce wa mutane, “Kun daɗe kuna haurawa zuwa can Urushalima. Ga allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga ƙasar Masar.” Sai ya kafa ɗaya a Betel, ɗaya kuma a Dan. Wannan ya zama zunubi, gama mutane suna tafiya yin wa wannan da yake a Betel sujada, su kuma je har Dan don su yi wa ɗayan sujada. Yerobowam ya gina masujadai da suke kan tuddai, ya kuma naɗa firistoci barkatai daga cikin mutanen da ba na zuriyar Lawi ba. Ya kafa biki a rana ta goma sha biyar ta watan takwas, kamar bikin da ake yi a Yahuda, ya kuma miƙa hadayu a bisa bagade. Ya yi haka a Betel, yana miƙa wa siffofin maruƙan da ya yi hadayu. A Betel kuma ya naɗa firistoci a wuraren tudun da ya yi. A rana ta goma sha biyar ta watan takwas, watan da ya zaɓa, ya miƙa hadayu a bisa bagaden da ya gina a Betel. Saboda haka ya kafa biki don Isra’ilawa, ya kuma haura zuwa bagade don yă miƙa hadayu. Mutumin Allah daga Yahuda Bisa ga umarnin Ubangiji, sai wani mutumin Allah ya zo daga Yahuda zuwa Betel, yayinda Yerobowam yake tsaye kusa da bagade don yă miƙa hadaya. Sai mutumin Allah ya tā da murya a kan bagade bisa ga umarnin Ubangiji ya ce, “Ya bagade, bagade! Ubangiji ya ce, ‘Za a haifi ɗa mai suna Yosiya wa gidan Dawuda. A kanka zai miƙa firistoci na masujadai kan tuddai masu miƙa hadayu a nan, za a kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kanka.’ ” A wannan rana mutumin Allah ya ba da alama, “Ga alamar da Ubangiji ya furta. Wannan bagade zai tsage yă rabu kashi biyu, tokar da yake a kansa za tă zuba a ƙasa.” Sa’ad da Yerobowam ya ji abin da mutumin Allah ya tā da murya ya faɗa game da bagaden Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden ya ce, “Ku kama shi!” Amma sai hannun da ya miƙa ya yanƙwane, har bai iya janye shi ba. Haka ma, bagaden ya rabu, tokarsa kuma ya zuba, bisa ga alamar da mutumin Allah ya bayar, ta wurin kalmar Ubangiji. Sai sarki ya ce wa mutumin Allah, “Ka roƙi Ubangiji Allahnka, ka kuma yi addu’a domina don hannuna ya warke.” Saboda haka mutumin Allah ya yi roƙo ga Ubangiji, hannun sarki kuwa ya warke, ya kuma zama kamar yadda yake a dā. Sai sarki ya ce wa mutumin Allah, “Zo gida tare da ni, ka sami wani abu ka ci, zan kuwa yi maka kyauta.” Amma mutumin Allah ya amsa wa sarki, “Ko da za ka ba rabin mallakarka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuwa zan ci abinci, ko in sha ruwa a can ba. Gama an umarce ni ta wurin kalmar Ubangiji, aka ce, ‘Kada ka ci abinci, ko ka sha ruwa, ko ka koma ta hanyar da ka zo.’ ” Saboda haka ya ɗauki wata hanya, bai kuwa koma ta hanyar da ya zo Betel ba. To, fa, akwai wani tsohon annabi yana zama a Betel, wanda ’ya’yansa suka zo suka faɗa masa dukan abin da mutumin Allah ya yi a can, a ranar. Suka kuma faɗa wa mahaifinsu abin da ya faɗa wa sarki. Mahaifinsu ya tambaye su ya ce, “Wace hanya ce ya bi?” Sai ’ya’yansa suka nuna masa hanyar da mutumin Allah daga Yahuda ya bi. Sai ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Da suka yi wa jakin shimfiɗa, sai ya hau. Ya bi bayan mutumin Allah. Ya same shi yana zama a ƙarƙashin itace oak, sai ya tambaye shi ya ce, “Kai ne mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda?” Ya amsa, “Ni ne.” Saboda haka annabin ya ce masa, “Zo gida tare da ni ka ci abinci.” Mutumin Allah ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba, ko in ci abinci, ko in sha ruwa tare da kai a can ba. An faɗa mini ta wurin maganar Ubangiji, ‘Kada ka ci abinci, ko ka sha ruwa a can, ko ka koma ta hanyar da ka zo.’ ” Sai annabin ya amsa, “Ni ma annabi ne, kamar ka. Kuma mala’ika ya ce mini ta wurin kalmar Ubangiji, ‘Dawo da shi zuwa gidanka saboda yă ci abinci, yă kuma sha ruwa.’ ” (Amma yana masa ƙarya ne.) Sai mutumin Allah ya koma tare da shi ya kuma ci ya sha a gidansa. Yayinda suke zaune a teburi, sai maganar Ubangiji ta zo wa tsohon annabin da ya dawo da mutumin Allah. Sai tsohon annabin ya tā da murya wa mutumin Allah wanda ya zo daga Yahuda, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ƙazantar da maganar Ubangiji, ba ka kuma kiyaye umarnin Ubangiji Allahnka ba. Ka dawo ka ci abinci, ka kuma sha ruwa a wurin da na faɗa maka kada ka ci, ko ka sha. Saboda haka ba za a binne jikinka a kabarin kakanninka ba.’ ” Sa’ad da mutumin Allah ya gama ci da sha, sai annabin da ya dawo da shi ya yi wa jakin mutumin Allah shimfiɗa. Yayinda yake kan hanyarsa, sai wani zaki ya sadu da shi ya kashe shi, aka kuma jefar da jikinsa a kan hanya, jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar. Waɗansu mutane masu wucewa suka ga an yar da gawar a can, zaki yana tsaye kusa da gawar, sai suka tafi suka ba da labarin a birni inda tsohon annabin nan yake zama. Sa’ad da annabin da ya dawo da mutumin Allah ya ji, sai ya ce, “Mutumin Allah ne, wanda ya ƙazantar da maganar Ubangiji. Ubangiji ya bashe shi ga zaki, wanda ya yayyage shi ya kuma kashe shi, kamar yadda maganar Ubangiji ta gargaɗe shi.” Sai annabin ya ce wa ’ya’yansa, “Ku yi wa jakina shimfiɗa.” Sai suka yi. Sai ya fita ya sami an jefar da gawar a hanya, jakin da zakin suna tsaye kusa da shi. Zakin bai ci gawar ko yă yayyage jakin ba. Saboda haka annabin ya ɗauki gawar mutumin Allah, ya shimfiɗa shi a kan jaki, ya koma da shi cikin birninsa don yă yi makokinsa yă kuma binne shi. Sai ya kwantar da gawar a kabarinsa, suka yi makoki a kansa, ya kuma ce, “Ayya, abokina!” Bayan an binne shi, sai ya ce wa ’ya’yansa, “Sa’ad da na mutu, ku binne ni a kabarin da aka binne mutumin Allah; ku kwantar da ƙasusuwana kusa da ƙasusuwansa. Gama annabcin da ya yi ta maganar Ubangiji gāba da bagaden da yake cikin Betel da kuma wuraren sujada a tuddan da suke a biranen Samariya, ba shakka zai cika.” Har ma bayan wannan, Yerobowam bai canja daga mugayen hanyoyinsa ba, amma ya ƙara naɗa firistoci domin masujadai da suke kan tuddai daga kowane irin mutane. Duk wanda ya so yă zama firist sai yă naɗa shi don aiki a masujadai da suke kan tuddai. Wannan ne zunubin gidan Yerobowam da ya kai ga fāɗuwarsa da kuma hallakarsa daga fuskar duniya. Annabcin Ahiya a kan Yerobowam A lokacin Abiya, ɗan Yerobowam ya kamu da ciwo, sai Yerobowam ya ce wa matarsa, “Ki tafi, ki ɓad da kama, don kada a gane ke a matsayin matar Yerobowam. Ki je Shilo. Annabi Ahiya yana a can, wannan wanda ya ce mini zan zama sarki a bisa wannan mutane. Ki ɗauki dunƙulen burodi goma tare da ke, da waina, da tulun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.” Saboda haka matar Yerobowam ta yi abin da ya faɗa, ta kuma tafi gidan Ahiya a Shilo. Yanzu dai Ahiya ba ya gani; idanunsa sun tafi saboda tsufa. Amma Ubangiji ya ce wa Ahiya, “Matar Yerobowam tana zuwa tă tambaye ka game da ɗanta, gama yana ciwo, za ka kuwa ba ta amsa kaza da kaza. Sa’ad da ta iso za tă yi kamar wata ce dabam.” Saboda haka sa’ad da Ahiya ya ji motsin sawunta a ƙofa, sai ya ce, “Ki shigo, matar Yerobowam. Me ya sa kike yi kamar wata ce dabam? An aiko ni wurinki da labari marar daɗi. Je ki faɗa wa Yerobowam cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na tā da kai daga cikin mutane, na mai da kai shugaba a bisa mutanena Isra’ila. Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba da shi gare ka, amma ba ka zama kamar bawana Dawuda wanda ya kiyaye umarnaina ya kuma bi ni da dukan zuciyarsa, yana yin abin da yake daidai kaɗai a idanuna ba. Ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka rayu kafin kai. Ka yi wa kanka waɗansu alloli, gumakan da aka yi da ƙarfe; ka tsokane ni na yi fushi, ka kuma juye mini baya. “ ‘Saboda wannan, zan kawo masifa a gidan Yerobowam. Zan yanke kowane ɗa na ƙarshe a Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan ƙone gidan Yerobowam kamar yadda mutum yakan ƙone juji, sai duk ya ƙone ƙurmus. Karnuka za su ci waɗanda suka mutu na Yerobowam a cikin birni, kuma tsuntsayen sararin sama za su cinye waɗanda suka mutu a jeji. Ni Ubangiji na faɗa!’ “Ke kuma, ki koma gida. Sa’ad da kika taka ƙafa a birninki, yaron zai mutu. Dukan Isra’ila kuwa za su yi makoki dominsa. Shi ne kaɗai na Yerobowam wanda za a binne, domin shi ne kaɗai a gidan Yerobowam wanda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya sami wani ɗan abu mai kyau a kansa. Ubangiji zai tā da wani sarki wa kansa a bisa Isra’ila wanda zai hallaka iyalin Yerobowam. Ko yanzu ma, wannan zai fara faruwa. Ubangiji kuma zai bugi Isra’ila, har tă zama kamar kyauro mai girgiza a bakin rafi. Zai tumɓuke Isra’ila daga wannan ƙasa mai kyau da ya ba wa kakanninsu, yă watsar da su gaba da Kogin Yuferites domin sun tsokane Ubangiji har ya yi fushi, ta wurin yin ginshiƙan Ashera. Zai kuma ba da Isra’ila saboda zunuban da Yerobowam ya yi, da ya kuma sa Isra’ila suka yi.” Sai matar Yerobowam ta tashi ta tafi, ta kuwa tafi Tirza. Nan da nan da ta taka madogarar ƙofar gidan, sai yaron ya mutu. Suka binne shi, dukan Isra’ila kuwa suka yi makoki dominsa, yadda Ubangiji ya faɗa ta wurin bawansa annabi Ahiya. Sauran ayyukan sarautar Yerobowam, da yaƙe-yaƙensa, da yadda ya yi mulki, ba a rubuce suke a littafin tarihi na sarakunan Isra’ila ba? Ya yi mulki shekaru ashirin da biyu, sai ya huta tare da kakanninsa. Sai Nadab ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Rehobowam sarkin Yahuda (2 Tarihi 11.5–12.16) Rehobowam ɗan Solomon ya zama sarki a Yahuda. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekaru goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra’ila don yă sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita mutuniyar Ammon ce. Yahuda ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Ta wurin zunuban da suka yi, sun tā da fushin kishinsa fiye da yadda kakanninsu suka yi. Sun kuma kafa wa kansu masujadai da suke kan tuddai, da a kan keɓaɓɓun duwatsu, suka kuma gina ginshiƙan Ashera a kowane tudu, da kuma a ƙarƙashin kowane duhuwar itace. Har ma akwai maza karuwai na masujada. Mutane suka sa kansu ga yin kowane abin ƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora kafin Isra’ilawa. A shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam, Shishak sarkin Masar ya kai wa Urushalima yaƙi. Ya kwashe dukiyar haikalin Ubangiji da kuma dukiyar fadan sarki. Ya ɗauki kome, har da dukan garkuwoyi na zinariya da Solomon ya yi. Saboda haka sarki Rehobowam ya yi garkuwoyin tagulla ya mayar da su. Ya kuma naɗa waɗannan shugabannin matsara ya sa su aiki a ƙofar zuwa fadan sarki. Duk sa’ad da sarki ya tafi wurin haikalin Ubangiji, matsara sukan riƙe garkuwoyinsu, daga baya kuma sai su mai da su ɗakin tsaro. Game da sauran ayyukan mulkin Rehobowam kuwa, da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka ci gaba da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam. Sai Rehobowam ya huta da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita kuwa mutuniyar Ammon ce. Sai Abiyam14.31 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da Seftuwajin (duba kuma 2Tar 12.16); yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci suna da Abiya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Abiya sarkin Yahuda (2 Tarihi 13.1-22) A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yerobowam ɗan Nebat, Abiyam ya zama sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara uku. Sunan mahaifiyarsa Ma’aka ne, ’yar Abisalom. Shi ma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Zuciyarsa ba tă bi Ubangiji Allahnsa, kamar yadda zuciyar Dawuda kakansa ta yi ba. Duk da haka, saboda Dawuda Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima ta wurin ta da wani da ya gāje shi, ta wurinsa kuma Urushalima ta yi ƙarfi. Gama Dawuda ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, bai kuma fasa kiyaye wani daga umarnan Ubangiji ba dukan kwanakinsa, sai dai a batun Uriya mutumin Hitti. Aka yi yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam a duk kwanakin Abiya. Game da sauran ayyukan mulkin Abiyam kuwa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka yi yaƙi tsakanin Abiyam da Yerobowam. Sai Abiyam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki. Asa sarkin Yahuda (2 Tarihi 15.16–16.6,11-13) A shekara ta ashirin ta Yerobowam sarkin Isra’ila, Asa ya zama sarkin Yahuda, ya yi mulki a Urushalima shekara arba’in da ɗaya. Sunan mahaifiya mahaifiyarsa, Ma’aka ne ’yar Abisalom. Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi. Ya kori dukan maza karuwai na masujadai daga ƙasar, ya kuma yi waje da dukan gumakan da mahaifinsa ya yi. Ya tuɓe mahaifiya mahaifiyarsa Ma’aka daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, gama ta gina ƙazantaccen ginshiƙin Ashera. Asa ya yanke ginshiƙin, ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron. Ko da yake bai cire masujadai da suke kan tuddai ba, zuciyar Asa ta kasance da aminci ɗungum ga Ubangiji dukan kwanakinsa. Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyakin da shi da mahaifinsa suka keɓe a haikalin Ubangiji. Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu. Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda. Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.” Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali. Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza. Sai Sarki Asa ya ba da umarni ga dukan Yahuda, kuma babu wanda aka ware, kowa yă taimaka a kwashe duwatsu da katakan da Ba’asha yake amfani da su daga Rama. Da duwatsu da katakan ne Sarki Asa ya gina Geba a Benyamin da kuma Mizfa. Game da sauran ayyukan mulkin Asa, dukan nasarorinsa, dukan abin da ya yi, da kuma biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. A tsufansa, sai ƙafafunsa suka kamu da cuta. Sai Asa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin kakansa Dawuda. Sai Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Nadab sarkin Isra’ila Nadab ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a shekara ta biyu ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekara biyu. Ya yi mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin mahaifinsa da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi. Ba’asha ɗan Ahiya na gidan Issakar ya yi maƙarƙashiya gāba da shi, ya buge shi a Gibbeton, a wani garin Filistiyawa, yayinda Nadab da dukan Isra’ila suke wa garin kwanto. Ba’asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma gāje shi a matsayin sarki. Nan da nan da ya fara mulki, sai ya kashe dukan iyalin Yerobowam. Bai bar wa Yerobowam wani da rai ba, amma ya hallaka su duka, bisa ga maganar Ubangiji da ya ba wa bawansa Ahiya, mutumin Shilo. Wannan abu ya faru saboda zunuban da Yerobowam ya yi, ya kuma sa Isra’ila ya yi, kuma saboda ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya yi fushi. Game da sauran ayyukan mulkin Nadab da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu. Ba’asha sarkin Isra’ila A shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, Ba’asha ɗan Ahiya ya zama sarkin dukan Isra’ila a Tirza, ya kuma yi sarauta shekara ashirin da huɗu. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Yehu ɗan Hanani game da Ba’asha, “Na ɗaga ka daga ƙura na mai da kai shugaban mutanena Isra’ila, amma ka yi tafiya a hanyoyin Yerobowam, ka kuma sa mutanena Isra’ila suka yi zunubi, ka tsokane ni na yi fushi ta wurin zunubansu. Saboda haka ina gab da cinye Ba’asha da gidansa, zan kuma mai da gidanka kamar na Yerobowam ɗan Nebat. Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ba’asha da suka mutu a birni, tsuntsaye kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.” Game da sauran ayyukan mulkin Ba’asha, abin da ya yi, da kuma nasarorinsa, an rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Ba’asha ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Tirza. Sai Ela ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam. Ela sarkin Isra’ila A shekara ta ashirin da shida ta Asa sarkin Yahuda, Ela ɗan Ba’asha ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Tirza shekaru biyu. Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza. Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki. Nan da nan sai ya fara mulki ya kuwa zauna a kujerar sarauta, ya kashe dukan iyalin Ba’asha. Bai bar namiji guda ɗaya ba, ko dangi, ko aboki. Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu. Wannan ya faru saboda dukan zunuban Ba’asha da waɗanda ɗansa Ela ya yi, da ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani. Game da sauran ayyukan mulkin Ela, da dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Zimri sarkin Isra’ila A shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda, Zimri ya yi mulki a Tirza kwana bakwai. Mayaƙa suka yi sansani kusa da Gibbeton, wani garin Filistiyawa. Sa’ad da Isra’ilawa a cikin sansani suka ji cewa Zimri ya yi maƙarƙashiya a kan sarki, ya kuma kashe shi, sai suka yi shela, suka naɗa Omri, shugaban mayaƙa ya zama sarki a bisa Isra’ila, a wannan rana a cikin sansani. Sai Omri da dukan Isra’ilawa suka janye daga Gibbeton, suka yi wa Tirza kwanto. Da Zimri ya ga cewa an kame birnin, sai ya je ya shiga hasumiya fadan sarki ya sa wa fadan wuta wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu. Wannan ya faru saboda zunuban da ya yi, ya yi mugunta a gaban Ubangiji ya kuma yi tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubin da Yerobowam ya yi da ya sa Isra’ila suka yi. Game da sauran ayyukan mulkin Zimri, da tawayen da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Omri sarkin Isra’ila Sai mutanen Isra’ila suka rabu kashi biyu; rabi guda sun goyi bayan Tibni ɗan Ginat yă zama sarki, ɗayan rabin kuma sun goyi bayan Omri. Amma mabiyan Omri suka nuna sun fi na Tibni ɗan Ginat ƙarfi. Sai Tibni ya mutu, Omri kuwa ya zama sarki. A shekara ta talatin da ɗaya na Asa sarkin Yahuda, Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu, shekaru shida a Tirza. Ya saya tudun Samariya daga Shemer, a bakin talentin biyu na azurfa, ya kuma gina birni a kan tudun, ya kira shi Samariya, bayan Shemer, sunan mai tudun a dā. Amma Omri ya yi mugunta a gaban Ubangiji, ya kuma yi zunubi fiye da dukan waɗanda suka kasance kafin shi. Ya yi tafiya a dukan hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat da kuma cikin zunubinsa wanda ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani. Game da sauran ayyukan mulkin Omri, abin da ya yi, da kuma abubuwan da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Omri ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Samariya. Sai Ahab ya gāje shi a matsayin sarki. Ahab ya zama sarkin Isra’ila A shekara ta talatin da takwas ta Asa sarkin Yahuda, Ahab ɗan Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Samariya a kan Isra’ila, shekara ashirin da biyu. Ahab ɗan Omri ya yi mugunta sosai a gaban Ubangiji fiye da wani daga cikin waɗanda suka riga shi. Bai zama masa wani abu mai wuya ba, yă yi zunuban Yerobowam ɗan Nebat, har ma ya auri Yezebel ’yar Etba’al sarkin Sidoniyawa, ya kuma fara bauta wa Ba’al, ya yi masa sujada. Ya kafa bagade domin Ba’al a haikalin Ba’al da ya gina a Samariya. Ahab ya gina ginshiƙin Ashera, ya kuma aikata abubuwa masu yawa don yă tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra’ila da suka riga shi. A lokaci Ahab ne, Hiyel mutumin Betel ya sāke gina Yeriko. Ya kafa tushensa a bakin ran ɗan farinsa Abiram, ya kuma kafa ƙofofinsa a bakin ran autansa Segub, bisa ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Yoshuwa ɗan Nun. Iliya ya sanar cewa za a yi babban fari To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.” Hankaki sun ciyar da Iliya Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce, “Ka bar nan, ka nufi wajajen gabas, ka ɓuya a Rafin Kerit, gabas da Urdun. Za ka sha daga rafin, zan kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.” Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can. Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin. Gwauruwa a Zarefat Ana nan sai rafin ya bushe saboda ba a yi ruwan sama a ƙasar ba. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya cewa, “Je ka, nan take, zuwa Zarefat na Sidon, ka zauna a can. Na umarci wata gwauruwa a can tă ciyar da kai.” Saboda haka sai ya tafi Zarefat. Sa’ad da ya isa ƙofar gari, sai ga wata gwauruwa tana tattara ’yan itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa a tulu don in sha.” Da ta kama hanya za tă tafi tă kawo, sai ya sāke kiranta ya ce, “Ina roƙonki, ki kuma kawo mini ɗan abinci.” Sai ta ce masa, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da wani abinci, sai dai ɗan gari hannu guda a tulu, da kuma ɗan mai a kwalaba. Ina tattara ’yan itacen nan ne don in kai gida in yi abinci wa kaina da ɗana, don mu ci, mu mutu.” Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Ki tafi gida, ki yi yadda kika ce. Amma da farko ki yi mini ’yar wainar burodi daga abin da kike da shi ki kawo mini, sa’an nan ki yi wani abu wa kanki da kuma ɗanki. Gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Tulun garin ba zai ƙare ba, kwalabar man kuma ba zai bushe ba sai ranar da Ubangiji ya bayar da ruwan sama a ƙasar.’ ” Sai ta tafi, ta yi yadda Iliya ya faɗa mata. Saboda haka aka kasance da abinci kowace rana wa Iliya da kuma don macen da iyalinta. Gama tulun garin bai ƙare ba, kwalabar man kuma bai bushe ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Iliya. Ana nan sai ɗan matan, wato, gwauruwan nan ya fara ciwo. Ciwon ya ƙara muni, daga ƙarshe sai ya daina numfashi. Sai ta ce wa Iliya, “Mutumin Allah, yaya haka? Ka zo ne domin ka nuna wa Allah zunubaina, ka kuma jawo mutuwar ɗana?” Iliya ya ce, “Ki miƙa mini ɗanki.” Sai ya ɗauke shi daga hannuwanta, ya kai shi ɗakin sama inda yake zama, ya kwantar da shi a gadonsa. Sa’an nan ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wannan masifa a kan gwauruwan nan? Kai ka ce in zauna tare da ita, ga shi yanzu ɗanta ya mutu.” Sai ya kwanta, ya miƙe kansa a kan yaron sau uku, ya kuma yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka mai da ran yaron nan!” Ubangiji kuwa ya ji kukan Iliya, sai ran yaron ya dawo masa, ya kuma rayu. Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga ɗakin sama zuwa cikin gida. Ya ba da shi ga mahaifiyarsa, ya ce, “Duba, ɗanki yana da rai!” Sai matar ta ce wa Iliya, “Yanzu na san cewa kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuma yana magana ta wurinka.” Iliya da Obadiya Bayan dogon lokaci, a cikin shekara ta uku, maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce, “Tafi, ka gabatar da kanka ga Ahab, zan kuwa aika da ruwan sama a ƙasar.” Saboda haka Iliya ya tafi ya gabatar da kansa ga Ahab. Yanzu dai yunwa ta tsananta a Samariya, Ahab kuma ya aika a kawo Obadiya, sarkin fadansa (Obadiya dai cikakken mai gaskata da Ubangiji ne. Yayinda Yezebel tana kisan annabawan Ubangiji, Obadiya ya ɗauki annabawa ɗari ya ɓoye a kogwanni biyu, hamsin a kowanne, ya kuma tanada musu abinci da kuma ruwa.) Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka ratsa ƙasar zuwa dukan maɓulɓulai da fadamu. Mai yiwuwa ka sami ciyawa mu ba dawakai da alfadarai don su rayu, don kada mu kashe dabbobinmu.” Saboda haka suka raba ƙasar da za su ratsa, Ahab zai tafi gefe ɗaya, Obadiya kuma yă bi gefe ɗaya. Yayinda Obadiya yana tafiya, sai Iliya ya sadu da shi. Obadiya ya gane shi, ya rusuna har ƙasa, ya ce, “Kai ne, shugabana, Iliya?” Iliya ya amsa, ya ce, “I, je ka faɗa wa maigidanka cewa, ‘Iliya yana a nan.’ ” Obadiya ya yi tambaya, “Me na yi da ba daidai ba, da kake miƙa bawanka ga Ahab don yă kashe? Na rantse da Ubangiji Allahnka, babu al’umma ko masarauta da mai girma sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka can, sai yă sa mulkin ko al’ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba. Amma yanzu kana faɗa mini in tafi wurin mai girma in ce, ‘Iliya yana a nan.’ Ban san inda Ruhun Ubangiji zai kai ka sa’ad da na bar ka ba. In na tafi na faɗa wa Ahab bai kuma same ka a nan ba, zai sa a kashe ni. Tuna fa, ni bawanka, na yi wa Ubangiji sujada tun ina saurayi. Ranka yă daɗe, ashe, ba a faɗa maka abin da na yi lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji ba? Yadda na ɓoye annabawa ɗari, na sa su hamsin-hamsin a kogwanni biyu, na yi ta ba su abinci da ruwa. Yanzu fa, kana ce in tafi wurin mai girma sarki, in ce, ‘Iliya yana a nan.’ Ai, zai kashe ni!” Iliya ya ce, “Na rantse da Ubangiji Maɗaukaki, wanda nake bauta wa, tabbatacce zan gabatar da kaina ga Ahab a yau.” Iliya a Dutsen Karmel Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya. Sa’ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne wannan, kai mai tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila?” Iliya ya amsa, ya ce, “Ban tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila ba. Amma kai da iyalin mahaifinka, ku kuka tā-da-na-zaune-tsaye. Ka ƙyale umarnai Ubangiji, ka bi Ba’al. Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.” Sai Ahab ya aika a duk fāɗin Isra’ila, ya kuma tattara annabawan a kan Dutsen Karmel. Iliya ya je gaban mutane ya ce, “Har yaushe za ku yi ta yawo tsakanin ra’ayoyi biyu? In Ubangiji ne Allah, ku bi shi; amma in Ba’al Allah ne, ku bi shi.” Mutane dai ba su ce uffam ba. Sai Iliya ya ce musu, “Ni ne kaɗai annabin Ubangiji da ya rage, amma Ba’al yana da annabawa ɗari huɗu da hamsin. Ku samo mana bijimai biyu. Bari su zaɓa ɗaya wa kansu, bari kuma su yanka shi kucu-kucu su sa a itace, sai dai, kada su sa wuta a kansa. Ni kuwa zan shirya ɗaya bijimin in sa a kan itace, ni ma, ba zan sa wuta a kansa ba. Sa’an nan ku kira bisa sunan allahnku, ni kuwa zan kira bisa sunan Ubangiji. Duk allahn da ya amsa ta wurin wuta, shi ne Allah.” Sai dukan jama’a suka ce, “Abin nan da faɗa yana da kyau.” Iliya ya ce wa annabawan Ba’al, “Ku ku fara zaɓi bijimi ɗaya, ku shirya, da yake kuna da yawa. Ku kira a bisa sunan allahnku, amma kada ku ƙuna wuta.” Sai suka ɗauki bijimin da aka ba su suka shirya shi. Sa’an nan suka kira bisa sunan Ba’al daga safe har tsakar rana. Suna ihu, “Ya Ba’al, ka amsa mana!” Amma babu wata amsa, babu wani da ya amsa. Suka yi ta rawa kewaye da bagaden da suka yi. Da tsakar rana, Iliya ya fara yin musu ba’a. Ya ce, “Ku yi ihu da ƙarfi, tabbatacce shi allah ne! Mai yiwuwa yana cikin zurfin tunani, ko dai aiki ya yi masa yawa, ko ya yi tafiya. Mai yiwuwa yana barci ne, dole a tashe shi.” Sai suka yi ta ihu da ƙarfi suna tsattsaga kansu da takuba da māsu, yadda al’adarsu take, sai da jininsu ya yi ta zuba. Tsakar rana ta wuce, suka ci gaba da ƙoƙari, suna annabci har lokacin miƙa hadayar yamma ya yi. Amma babu wani da ya tanƙa, babu wani da ya amsa, babu wanda ya kula. Sa’an nan Iliya ya ce wa dukan mutane, “Ku zo nan wurina.” Suka zo wurinsa, ya kuma shirya bagaden Ubangiji, da ya riga ya zama kufai. Iliya ya ɗauki duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowace kabila zuriyar Yaƙub, wanda maganar Ubangiji ta zo masa, cewa, “Sunanka zai zama Isra’ila.” Da waɗannan duwatsun ya gina bagade cikin sunan Ubangiji, ya kuma haƙa wuriya kewaye da shi, isashe da zai ci garwa biyu na irin ƙwayar gyada. Ya shirya itace, ya yayyanka bijimin kucu-kucu, ya shimfiɗa shi a itacen. Sa’an nan ya ce musu, “Ku cika manyan tuluna da ruwa, ku zuba a kan hadayar da kuma a kan itacen.” Suka zuba. Ya ce, “Ku sāke yin haka,” sai suka sāke yin haka. Ya umarta, “Ku yi haka sau na uku,” suka kuma yi haka sau na uku. Ruwan ya gangara kewaye da bagaden har ma ya cika wuriyar. A lokacin hadaya, sai annabi Iliya ya zo gaba ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Ibrahim, na Isra’ila da kuma na Yaƙub, bari a sani a yau cewa kai Allah ne a cikin Isra’ila, a kuma san cewa ni bawanka ne, na kuma yi dukan waɗannan abubuwa bisa umarninka. Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, saboda waɗannan mutane su san cewa kai, ya Ubangiji, kai ne Allah, su kuma san cewa kana sāke juye zukatansu zuwa gare ka.” Sai wutar Ubangiji ya fāɗo, ya cinye hadayar, itacen, duwatsun da kuma ƙasar, ya lashe ruwan da yake cikin wuriyar. Sa’ad da mutane suka ga wannan, sai suka rusuna, suka sunkuyar da kai suka ce, “Ubangiji, shi ne Allah! Ubangiji, shi ne Allah!” Sa’an nan Iliya ya umarce su, ya ce, “Ku kama annabawan Ba’al, kada ku bar waninsu yă tsere!” Suka kama su, Iliya kuwa ya sa aka gangara da su zuwa Kwarin Kishon, aka yayyanka su a can. Sai Iliya ya ce wa Ahab, “Ka haura gida, ka ci, ka sha, gama ina jin motsin ruwan sama mai yawa.” Sai Ahab ya ruga don yă ci, yă sha, amma Iliya ya hau kan ƙwanƙolin Karmel, ya rusuna ƙasa, ya sa fuska a tsakanin gwiwarsa. Ya ce wa bawansa, “Tafi ka dubi wajen teku.” Sai bawan ya haura ya duba. Ya ce, “Ba kome a can.” Sau bakwai Iliya ya ce, “Koma.” Sau na bakwai, bawan ya ce, “Wani girgije ƙarami kamar hannun mutum yana tasowa daga teku.” Sai Iliya ya ce, “Je ka faɗa wa Ahab, ‘Shirya keken yaƙinka, ka gangara kafin ruwan sama yă tare ka.’ ” Ana cikin haka, sarari ya ƙara duhunta da girgije, iska ta taso, sai ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauko, Ahab kuwa ya hau zuwa Yezireyel. Ikon Ubangiji ya sauko a kan Iliya, ya sha ɗamara, ya ruga a guje a gaban Ahab har zuwa Yezireyel. Iliya ya gudu zuwa Horeb Ahab fa ya faɗa wa Yezebel kome da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe dukan annabawan da takobi. Saboda haka Yezebel ta aika da ɗan aika wa Iliya yă faɗa masa, “Bari alloli su hukunta ni da tsanani, in war haka gobe ban mai da ranka kamar na ɗaya daga cikin annabawan Ba’al ba.” Iliya ya ji tsoro, ya gudu don yă ceci ransa. Sa’ad da ya kai Beyersheba a Yahuda, sai ya bar bawansa a can. Shi kuma ya yi tafiya yini guda zuwa cikin hamada. Ya zo wurin wani itacen tsintsiya, ya zauna a ƙarƙashinsa, ya roƙa yă mutu. Ya ce, “Ya ishe ni haka, Ubangiji, ka ɗauki raina; ban fi kakannina ba.” Sa’an nan ya kwanta a ƙarƙashin itacen ya yi barci. Farat ɗaya sai wani mala’ika ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci.” Ya duba kewaye, sai ga wainar burodi kusa da kansa a bisa garwashin wuta mai zafi, da kuma tulun ruwa. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya sāke kwanta. Mala’ikan Ubangiji ya sāke dawowa sau na biyu ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci, gama tafiyar za tă yi maka yawa.” Saboda haka ya tashi ya ci, ya kuma sha. Ta wurin ƙarfin da ya samu saboda wannan abinci, ya yi tafiya yini arba’in da dare arba’in, sai da ya kai Horeb, dutsen Allah. A can ya shiga kogo ya kwana. Ubangiji ya bayyana wa Iliya Sai maganar Ubangiji ta zo masa, ta ce, “Me kake yi a nan, Iliya?” Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.” Sai Ubangiji ya ce, “Fita ka tsaya a kan dutse a gaban Ubangiji, gama Ubangiji yana shirin wucewa.” Sai ga babbar iska mai ƙarfi ta tsage duwatsu, ta kuma ragargaza duwatsu a gaban Ubangiji, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai aka yi girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasa. Bayan girgizar ƙasa, sai ga wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wuta. Bayan wutar kuma sai ga wata ’yar murya. Sa’ad da Iliya ya ji ta, ya ja mayafinsa ya rufe fuskarsa, ya fita ya tsaya a bakin kogon. Sai ya ji murya ta ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?” Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.” Sai Ubangiji ya ce masa, “Ka koma ta hanyar da ka zo, ka tafi Hamadan Damaskus. Sa’ad da ka kai can, ka shafe Hazayel yă zama sarki bisa Aram. Ka kuma shafe Yehu ɗan Nimshi yă zama sarkin Isra’ila, ka shafe Elisha ɗan Shafat daga Abel-Mehola yă gāje ka a matsayin annabi. Yehu zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Hazayel, Elisha kuwa zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Yehu. Duk da haka zan bar mutane dubu bakwai na Isra’ila waɗanda ba su rusuna da gwiwansu wa Ba’al ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.” Kiran Elisha Sai Iliya ya tafi daga can ya sami Elisha ɗan Shafat, yana noma da shanu goma sha biyu masu garman noma, shi kansa yana jan na goma sha biyun. Iliya ya tafi wurinsa ya jefa mayafinsa a kan Elisha. Sai Elisha ya bar shanun, ya ruga ya bi Iliya. Ya ce, “Bari in sumbace mahaifina da mahaifiyata, in yi musu bankwana, sa’an nan in zo in bi ka.” Iliya ya ce, “Koma! Me na yi maka?” Sai Elisha ya bar shi, ya koma, ya ɗauki shanunsa ya yayyanka. Ya ƙone kayan garman noman don yă dafa naman, ya kuma ba wa mutane naman, suka kuwa ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya kuma zama mai hidimarsa. Ben-Hadad ya yaƙi Samariya Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tattara mayaƙansa gaba ɗaya. Sarakuna talatin da biyu suka tafi tare da shi haɗe da dawakansu da kekunan yaƙinsu. Ya haura ya yi wa Samariya kwanto, ya kuma yaƙe ta. Ya aika da ’yan aika zuwa cikin birnin wurin Ahab sarkin Isra’ila yana cewa, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Mafi kyau cikin matanka da ’ya’yanka nawa ne.’ ” Sarkin Isra’ila ya amsa, ya ce, “Kamar dai yadda ka faɗa, ranka yă daɗe, sarki. Ni da dukan abin da nake da shi, naka ne.” Sai ’yan aikan suka sāke dawo suka ce, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Na aika ka ba da azurfarka da zinariyarka, matanka da kuma ’ya’yanka. Amma war haka gobe zan aika shugabannina su bincika fadanka da kuma gidajen shugabanninka. Za su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi.’ ” Sarkin Isra’ila ya tattara dukan dattawan ƙasar, ya ce musu, “Ku duba fa, wannan mutum yana neman tsokana! Sa’ad da ya aika in ba shi matana da ’ya’yana, azurfana da zinariyana, ban hana masa ba.” Dattawa da dukan mutane suka amsa, suka ce, “Kada ka saurare shi ko ka yarda da abin da yake bukata.” Saboda haka ya ba wa ’yan aikan Ben-Hadad amsa, ya ce, “Ku faɗa wa ranka yă daɗe, sarki, ‘Bawanka zai yi dukan abin da ka bukaci da farko, amma wannan na ƙarshe ba zan iya yin ba.’ ” Suka tafi suka kai amsar wa Ben-Hadad. Sai Ben-Hadad ya aika da wani saƙo wa Ahab, ya ce, “Bari alloli su yi da ni yadda suke so, su kuma yi haka da tsanani, in isashen ƙura ta rage a Samariya da za a iya ba wa mutanena a tafin hannu.” Sarki Isra’ila ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, ‘Wanda ya sa kayan yaƙinsa bai kamata yă yi fariya ba sai ya tuɓe su.’ ” Ben-Hadad ya ji wannan saƙo yayinda shi da sarakunan suke sha a cikin tentunansu, sai ya umarce mutanensa, ya ce, “Ku shirya don yaƙi.” Saboda haka suka shirya don su yaƙi birnin. Ahab ya ci Ben-Hadad da yaƙi Ana cikin haka sai wani annabi ya zo wurin Ahab sarkin Isra’ila ya sanar masa cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan ɗumbun mayaƙa? Zan ba da su cikin hannunka a yau, sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ” Ahab ya ce, “Amma wa zai yi haka?” Annabin ya amsa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Sojoji matasa na shugabannin yankuna za su yi haka.’ ” Ya tambaya, “Wa kuma zai fara yaƙin?” Annabin ya amsa, “Kai za ka fara.” Saboda haka Ahab ya kira sojoji matasa na shugabannin yankuna, mutum 232. Sa’an nan ya tattara sauran Isra’ilawa su 7,000 gaba ɗaya. Suka fita da tsakar rana yayinda Ben-Hadad tare da sarakuna 32 masu goyon bayansa suke cikin tentunansu suna sha, suna buguwa. Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka fara fita. Ben-Hadad kuwa ya riga ya aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka ce, “Mutane suna zuwa daga Samariya.” Ya ce, “In sun fito don salama, ku kamo su da rai; in sun fito yaƙi ne, ku kamo su da rai.” Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka taka suka fita daga birnin da mayaƙa a bayansu. Kowannensu kuwa ya buge abokin gābansa. Ganin wannan, sai Arameyawa suka gudu, Isra’ilawa suna bi. Amma Ben-Hadad na Aram ya tsere a kan dokinsa tare da waɗansu mahayan dawakansa. Sarki Isra’ila ya bi, ya kuma sha ƙarfin dawakan da keken yaƙin, ya kashe Arameyawa da yawa. Daga baya, annabin ya zo wurin sarkin Isra’ila ya ce, “Ka ƙarfafa matsayinka ka kuma ga abin da za a yi, gama a bazara mai zuwa sarkin Aram zai sāke kawo yaƙi.” Ana cikin haka, shugabannin sarkin Aram suka ba shi shawara, “Allolinsu, allolin tuddai ne. Shi ya sa suka fi mu ƙarfi. Amma in mun yaƙe su a fili, tabbatacce za mu fi su ƙarfi. Ka yi wannan. Ka cire dukan sarakuna daga matsayinsu ka sa waɗansu shugabanni a maimakonsu. Dole kuma ka tā da waɗansu mayaƙa kamar waɗanda ka rasa, doki don doki, keken yaƙi kuma don keken yaƙi, saboda mu iya yaƙe Isra’ila a fili. Ta haka tabbatacce za mu fi ƙarfinsu.” Sai ya yarda da su, ya kuma yi haka. Bazara na biye Ben-Hadad ya tattara Arameyawa, ya haura zuwa Afek don yă yaƙi Isra’ila. Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin. Sai mutumin Allah ya zo ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Domin Arameyawa suna tsammani Ubangiji allahn tuddai ne, ba allahn kwari ba, zan ba da wannan ɗumbun mayaƙa a hannuwanka, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ” Kwana bakwai suka yi sansani ɗaura da juna, a rana ta bakwai sai yaƙi ya haɗu. Isra’ilawa suka kashe sojojin kafa na Arameyawa dubu ɗari a rana ɗaya. Sauransu suka tsere zuwa birnin Afek, inda katangar ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai. Sai Ben-Hadad ya gudu zuwa birni ya ɓuya a ciki cikin ɗaki. Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin sarkin Isra’ila, wataƙila zai bar ka da rai.” Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’ ” Sarki ya amsa, “Har yanzu yana da rai? Shi ɗan’uwana ne.” Da ma abin da fadawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan’uwanka, Ben-hadad!” Sarki ya ce, “Ku je ku kawo shi.” Da Ben-Hadad ya fita, sai Ahab ya sa aka kawo shi cikin keken yaƙinsa. Ben-Hadad ya ce, “Zan mayar da biranen mahaifinka da na ƙwace daga mahaifinka. Za ka iya sa wurin kasuwarka a cikin Damaskus, kamar yadda mahaifinka ya yi a Samariya.” Ahab ya ce, “Bisa wannan yarjejjeniya zan sake ka.” Saboda haka ya yi yarjejjeniya da shi, sai ya bar shi ya tafi. Annabi ya yi wa Ahab Allah wadai Ta wurin maganar Ubangiji, ɗaya daga cikin ’ya’ya maza na annabawa ya ce wa abokinsa, “Ka buge ni da makaminka,” amma mutumin ya ƙi. Sai annabin ya ce, “Domin ba ka yi biyayya da Ubangiji ba, da zarar ka bar ni zaki zai kashe ka.” Daga baya mutumin ya tafi, zaki ya same shi, ya kuma kashe shi. Annabin ya sami wani mutum ya ce, “Ka buge ni, ina roƙonka.” Sai mutumin ya buge shi, ya ji masa ciwo. Sa’an nan annabin ya tafi ya tsaya a bakin hanya yana jiran sarki. Ya ɓad da kamanni da ƙyalle a kansa. Ƙyallen ya sauka zuwa bisa idanunsa. Yayinda sarki yake wucewa, sai annabin ya yi kira da ƙarfi gare shi ya ce “Ni bawanka na tafi yaƙi, sai ga wani ya kawo mini wani mutum, ya ce, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi yă kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta, a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’ Yayinda bawanka yana fama, yana kai da kawowa, sai mutumin ya ɓace.” Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Hukuncinka ke nan, ka furta shi da kanka.” Sai annabin ya cire ƙyallen da sauri daga kansa, da ya rufe idanunsa, sarkin Isra’ila kuwa ya gane shi a matsayi ɗaya daga cikin annabawa. Sai ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka saki mutumin da na ƙudura yă mutu. Saboda haka ranka zai zama a maimakon ransa, mutanenka a maimakon mutanensa.’ ” Cike da fushi, sarkin Isra’ila ya tafi fadarsa a Samariya. Gonar inabin Nabot Ana nan bayan haka sai waɗannan abubuwa suka faru. Nabot mutumin Yezireyel yana da gonar inabi a Yezireyel, a yankin Samariya, kusa da gidan Sarki Ahab. Sai Ahab ya ce wa Nabot, “Ka ba ni gonar inabinka in yi amfani da ita don kayan lambu, da yake tana kusa da fadana. Zan ba ka wata gonar inabin da ta fi wannan, ko kuma in ka gwammace, sai in biya ka duk abin da ya dace da ita.” Amma Nabot ya amsa wa Ahab ya ce, “Ubangiji yă sawwaƙe in ba ka gādon kakannina.” Ahab ya cika da fushi saboda Nabot, mutumin Yezireyel ya ce, “Ba zan ba ka gādon kakannina ba.” Ya kwanta a gadonsa yana zub da hawaye, ya kuma ƙi cin abinci. Matarsa Yezebel ta shiga ciki ta tambaye shi, ta ce, “Me ya sa ka kumbura? Me ya sa ba za ka ci abinci ba?” Sai ya amsa mata, ya ce, “Domin na ce wa Nabot mutumin Yezireyel, ‘Ka sayar mini gonar inabinka; ko kuwa in ka gwammace, zan ba ka wata gonar inabi a maimakonta.’ Amma ya ce, ‘Ba zan ba ka gonar inabina ba.’ ” Yezebel matarsa ta ce, “Yaya kake yi kamar ba kai ne sarki Isra’ila ba? Tashi ka ci abinci! Ka yi farin ciki. Zan ba ka gonar inabin Nabot mutumin Yezireyel.” Sai ta rubuta wasiƙu a sunan Ahab, ta buga hatiminsa a kansu, sa’an nan ta aika su ga dattawa da manyan gari waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake. Cikin waɗannan wasiƙu ta rubuta, “Ku yi shelar ranar azumi, ku zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane. Amma ku zaunar da waɗansu ’yan iska biyu ɗaura da shi, ku sa su ba da shaida cewa ya zagi Allah da sarki. Sa’an nan ku ɗauke shi ku jajjefe shi da dutse sai ya mutu.” Sai dattawa da manyan gari, waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake, suka yi kamar yadda Yezebel ta umarta a cikin wasiƙun da ta rubuta. Suka yi shelar azumi, suka kuma zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane. Sa’an nan ’yan iska biyu suka zo, suka zauna ɗaura da shi, suka kawo zarge a kan Nabot a gaban mutane, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.” Saboda haka aka ɗauke shi waje da birnin, aka jajjefe shi da dutse har ya mutu. Sa’an nan suka aika wa Yezebel. “An jajjefe Nabot, ya kuma mutu.” Nan da nan sa’ad da Yezebel ta ji cewa an jajjefe Nabot da dutse ya kuma mutu, sai ta ce wa Ahab, “Tashi ka mallaki gonar inabin Nabot mutumin Yezireyel wanda ya ƙi ya sayar maka. Ba shi da rai, ya mutu.” Da Ahab ya ji cewa Nabot ya mutu, sai ya tashi ya gangara don yă mallaki gonar inabin Nabot. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe. Ta ce, “Gangara don ka sadu da Ahab sarkin Isra’ila, wanda yake mulki a Samariya. Yanzu yana a gonar inabin Nabot, inda ya tafi yă mallake ta. Ka ce masa, Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba ka kashe mutum ka kuma ƙwace kayansa ba?’ Sa’an nan ka ce masa ga abin da Ubangiji ya ce, ‘A inda karnuka suka lashe jinin Nabot, karnuka za su lashe jininka, I, naka!’ ” Ahab ya ce wa Iliya, “Wato, ka same ni kuma, abokin gābana!” Sai ya amsa ya ce, “Na same ka, domin ka sayar da kanka ga yin mugunta a gaban Ubangiji. ‘Zan kawo masifa a kanka. Zan kawar da zuriyarka, in kuma yanke daga Ahab kowane ɗa namiji na ƙarshe cikin Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan mai da gidanka kamar gida Yerobowam ɗan Nebat, da na Ba’asha ɗan Ahiya, domin ka tsokane ni har na yi fushi, ka kuma sa Isra’ila ya yi zunubi.’ “Game da Yezebel kuwa Ubangiji ya ce, ‘Karnuka za su cinye Yezebel a katangar Yezireyel.’ “Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ahab waɗanda suka mutu a cikin birni, tsuntsayen sararin sama kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.” (Babu wani mutum kamar Ahab, wanda ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Yezebel matarsa ce ta zuga shi. Ya yi abar ƙyama ƙwarai ta wurin bin gumaka, kamar Amoriyawan da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ila.) Sa’ad da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, sai ya yage rigarsa, ya sa rigunan makoki, ya kuma yi azumi. Ya kwanta a kayan makoki, ya kuma yi tafiya cikin sauƙinkai. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe, ta ce, “Ka lura da yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana kuwa? Domin ya ƙasƙantar da kansa, ba zan kawo wannan masifa a kwanakinsa ba, amma zan kawo ta a kan gidansa a kwanakin ɗansa.” Mikahiya ya yi annabci a kan Ahab (2 Tarihi 18.2-27) Aka yi shekaru uku ba a yi yaƙi tsakanin Aram da Isra’ila ba. Amma a shekara ta uku, Yehoshafat sarkin Yahuda ya gangara don yă ga sarki Isra’ila. Sarkin Isra’ila ya ce wa shugabanninsa, “Ba ku san cewa Ramot Gileyad namu ne ba, duk da haka ba mu yi kome ba don mu sāke karɓanta daga sarkin Aram?” Saboda haka ya tambayi Yehoshafat, ya ce, “Za ka tafi tare da ni don in yi yaƙi da Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa sarkin Isra’ila, ya ce, “Ni ma kamar ka ne, mutanena kuwa kamar mutanenka, dawakaina kamar dawakanka.” Amma Yehoshafat ya ce wa sarkin Isra’ila, “Da farko mu nemi nufin Ubangiji.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa, kamar ɗari huɗu, ya tambaye su, “In kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada in kai?” Suka amsa, “Ka tafi, gama Ubangiji zai ba ka ita a hannunka.” Amma Yehoshafat ya yi tambaya, ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?” Sarkin Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, ya ce, “Akwai mutum guda har yanzu wanda ta wurinsa za mu iya nemi nufin Ubangiji, amma na ƙi jininsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai dai mummuna kullum. Shi ne Mikahiya ɗan Imla.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya ce haka.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin shugabanninsa ya ce, “Kawo Mikahiya ɗan Imla nan take.” Saye da rigunansu na sarauta, sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zama a kujerun sarautarsu a masussuka ta mashigin ƙofar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu. Zedekiya ɗan Kena’ana kuwa ya yi ƙahonin ƙarfe ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka tunkuyi Arameyawa har su hallaka.’ ” Dukan sauran annabawan suka yi annabci iri abu ɗaya. Suka ce, “Ka yaƙi Ramot Gileyad, ka kuma yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.” Ɗan aikan da ya je yă kawo Mikahiya, ya ce masa, “Duba, sauran annabawa suna maganar nasara wa sarki, sai ka ce mutum guda. Bari maganarka tă yarda da tasu, ka kuma yi maganar alheri.” Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji mai rai, zan faɗa masa kawai abin da Ubangiji ya faɗa mini.” Da suka kai, sai sarki ya tambaye shi, ya ce, “Mikahiya, mu kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada mu kai?” Ya amsa ya ce, “Yaƙe ta, za ka kuwa yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.” Sai sarki ya ce masa, “Sau nawa ne zan sa ka rantse cewa ba za ka faɗa mini kome ba sai dai gaskiya a cikin sunan Ubangiji?” Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowa yă tafi gida cikin salama.’ ” Sai sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka cewa bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni, sai mummuna kawai ba?” Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka ka ji maganar Ubangiji. I, na ga Ubangiji zaune a kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye kewaye da shi a dama da hagunsa. Kuma Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab zuwa yaƙi da Ramot Gileyad, yă kuma kai shi mutuwarsa a can?’ “Wani ya ce wannan, wani ya ce wancan. A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “Ubangiji ya yi tambaya ‘Ta wace hanya?’ Ya ce, “ ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’ “Saboda haka yanzu Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawanka. Ubangiji ya zartar maka da masifa.” Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya hau ya mari Mikahiya a fuska. Ya yi tambaya, “A wace hanya ce ruhu daga Ubangiji ya bar ni ya yi maka magana?” Mikahiya ya amsa, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a ciki cikin ɗaki.” Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ku kama Mikahiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki. Ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku sa wannan mutum a kurkuku, kuma kada ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa, sai na dawo lafiya.’ ” Mikahiya ya furta, “Idan har ka dawo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana ta wurina ba.” Ya kuma ƙara da cewa, “Ku lura da maganata, dukanku mutane!” An kashe Ahab a Ramot Gileyad (2 Tarihi 18.28-34) Sai sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad. Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama in shiga wurin yaƙi, amma ka sa kayan sarautarka.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya ɓad da kama, ya shiga cikin yaƙi. Sarkin Aram kuwa ya umarci shugabanni kekunan yaƙinsa talatin da biyu, ya ce, “Kada ku yaƙe kowa, ƙarami ko babba, sai dai sarkin Isra’ila.” Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙin suka ga Yehoshafat, suka yi tsammani, suka ce, “Tabbatacce wannan shi ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juye don su yaƙe shi, amma sa’ad da Yehoshafat ya yi ihu, sai shugabannin kekunan yaƙin suka ga ashe ba sarkin Isra’ila ba ne, sai suka daina binsa. Amma wani ya ja bakansa kawai ya bugi Ahab sarkin Isra’ila a tsakanin sassan kayan yaƙinsa. Sai sarki ya ce wa mahayin keken yaƙinsa, “Juye, ka fitar da ni daga yaƙin. An ji mini rauni.” Dukan yini aka yi ta yaƙi, aka kuma riƙe sarki a keken yaƙinsa yana fuskanci Arameyawa. Jini daga mikinsa ya yi ta zuba a ƙasan keken yaƙin, a wannan yamma kuwa ya mutu. Da rana tana fāɗuwa, sai kuka ta bazu cikin mayaƙa, “Kowane mutum ya tafi garinsu; kowa ya tafi ƙasarsa!” Sai sarki ya mutu, aka kuwa kawo shi Samariya, aka binne shi a can. Suka wanke keken yaƙi a tafki, a Samariya (inda karuwai suke wanka), sai karnuka suka lashe jininsa, kamar yadda maganar Ubangiji ta furta. Game da sauran ayyukan mulkin Ahab, haɗe da dukan abin da ya yi, da fadan da ya gina ya kuma shimfiɗa da hauren giwa, da biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. Ahab ya huta da kakanninsa. Ahaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Yehoshafat sarkin Yahuda (2 Tarihi 20.31–21.1) Yehoshafat ɗan Asa ya zama sarkin Yahuda a shekara ta huɗu ta Ahab sarkin Isra’ila. Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa, Azuba ’yar Shilhi. A cikin kome ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa, bai kuma kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Amma bai rurrushe masujadai da suke kan tuddai ba, mutane kuwa suka ci gaba da miƙa hadayu suna kuma ƙone turare a can. Yehoshafat kuma ya zauna lafiya da sarkin Isra’ila. Game da sauran ayyukan mulkin Yehoshafat da abubuwan da ya yi, da kuma yaƙe-yaƙensa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Ya kawar da karuwai maza na masujadai da suke kan tuddai waɗanda suka rage tun mulkin mahaifinsa Asa. Babu sarki a lokacin Edom, saboda haka sai mataimaki ya yi mulki. To, Yehoshafat ya gina jerin jiragen ruwan kasuwanci22.48 Da Ibraniyanci na jiragen Tarshish don su je Ofir saboda zinariya, amma ba su yi tafiya ba, gama sun farfashe a Eziyon Geber. A lokacin Ahaziya ɗan Ahab ya ce wa Yehoshafat, “Bari mutanena su tafi tare da mutanenka,” amma Yehoshafat ya ƙi. Yehoshafat kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin Dawuda kakansa. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi. Ahaziya sarkin Isra’ila Ahaziya ɗan Ahab ya zama sarkin Isra’ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta Yehoshafat sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekaru biyu. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, domin ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa da na mahaifiyarsa, da kuma a hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi zunubi. Ya bauta, ya kuma yi wa Ba’al sujada, ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi, kamar yadda mahaifinsa ya yi.