- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ 1 Tarihi 1 Tarihi 1 Tarihi 1Tar 1 Tarihi Rubutaccen tarihi daga Adamu zuwa Ibrahim Zuwa ’Ya’yan Nuhu Maza (Farawa 5.1-32; 10.1-32; 11.10-32) Adamu, Set, Enosh, Kenan, Mahalalel, Yared, Enok, Metusela, Lamek, Nuhu. ’Ya’yan Nuhu maza su ne,1.4 Seftuwajin; Ibraniyanci ba su da ’Ya’yan Nuhu maza. Shem, Ham da Yafet. Mutanen Yafet ’Ya’yan1.5 ’Ya’ya suna iya nufin zuriya Ko kuwa magāda ko al’ummai; haka ma a ayoyi 6-10, 17 da 20. Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras. ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat1.6 Yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da na Bulget (dubi kuma Seftuwajin da Far 10.3); yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci suna da Difat da Togarma. ’Ya’yan Yaban maza su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. Mutanen Ham ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar1.8 Wato, Masar; haka ma a aya ta 11. Fut da Kan’ana. ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza su ne, Sheba da Dedan Kush shi ne mahaifin1.10 Mahaifi na iya nufin kaka ko wanda ya riga Ko kuwa wanda yake tushe; haka ma a ayoyi 11, 13, 18 da 20. Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya. Masar shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa, Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa. Kan’ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa, Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa. Semiyawa ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram. ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Meshek. Arfakshad shi ne mahaifin Shela, Shela kuwa shi ne mahaifin Eber. Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka kira ɗaya Feleg domin a lokacinsa ne aka raba duniya; sunan ɗan’uwansa kuwa shi ne Yoktan. Yoktan shi ne mahaifin Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera Hadoram, Uzal, Dikla, Ebal, Abimayel, Sheba, Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne. Zuriyar Shem (Farawa 11.10-26) Shem, Arfakshad,1.24 Da Ibraniyanci; waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin suna da Arfakshad, Kainan (dubi kuma sharhi a Far 11.10). Shela, Eber, Feleg, Reyu Serug, Nahor, Tera da Abram (wato, Ibrahim). Iyalin Ibrahim (Farawa 25.1-4,12-16) ’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel. Zuriyar Hagar Waɗannan su ne zuriyarsu. Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam, Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema Yetur, Nafish da Kedema. Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza. Zuriyar Ketura ’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. ’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan. ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a. Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura. Zuriyar Saratu Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. ’Ya’yan Ishaku maza su ne, Isuwa da Isra’ila. ’Ya’yan Isuwa maza (Farawa 36.1-14) ’Ya’yan Isuwa maza, su ne, Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz, da Timna wanda aka haifa wa Amalek.1.36 Waɗansu rubuce-rubucen hannun Seftuwajin (dubi Far 36.12); Ibraniyanci yana da Gatam, Kenaz, Timna da Amalek ’Ya’yan maza Reyuwel su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Mutanen Seyir a Edom (Farawa 36.20-43) ’Ya’yan Seyir maza su ne, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan. ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ita ce ’yar’uwar Lotan. ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Ɗan Ana shi ne, Dishon. ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran. ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Ya’akan. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran. Masu mulkin Edom Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba. Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki. Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki. Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit. Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki. Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki. Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki. Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab. Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet Oholibama, Ela, Finon Kenaz, Teman, Mibzar, Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom. ’Ya’yan Isra’ila maza Waɗannan su ne ’ya’yan Isra’ila maza. Ruben, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Zebulun, Dan, Yusuf, Benyamin, Naftali, Gad da Asher. Zuriyar Yahuda ’Ya’yan Hezron maza ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan da Shela. Waɗannan mutum uku Bat-shuwa mutuniyar Kan’ana ce ta haifa masa. Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi. Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera. Yahuda ya haifi ’ya’ya maza biyar ne. ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul. ’Ya’yan Zera maza su ne, Zimri, Etan, Heman, Kalkol da Darda, su biyar ne. ’Ya’yan Karmi maza su ne, Akar2.7 Akar yana nufin masifa; Akar an kira shi Akan a cikin Yoshuwa. wanda ya kawo masifa wa Isra’ila ta wurin yin abin da aka haramta. Ɗan Etan shi ne, Azariya. ’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne, Yerameyel, Ram da Kaleb. Daga Ram ɗan Hezron Ram shi ne mahaifin Amminadab, Amminadab kuwa shi ne mahaifin Nashon, shugaban mutanen Yahuda. Nashon shi ne mahaifin Salma, Salma shi ne mahaifin Bowaz, Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse. Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya, na huɗun Netanel, na biyar Raddai, na shidan Ozem na bakwai kuma Dawuda. ’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel. ’Ya’yan Zeruhiya maza guda uku su ne Abishai, Yowab da Asahel. Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel. Zuriyar Kaleb ɗan Hezron Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne ’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon. Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur. Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel. Daga baya, Hezron ya kwana da ’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub. Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad. (Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad. Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa. Zuriyar Yerameyel ɗan Hezron ’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne, Ram shi ne ɗan fari, sai Buna, Oren, Ozem da Ahiya. Yerameyel yana da wata mata, wadda sunanta Atara; ita ce mahaifiyar Onam. ’Ya’yan Ram maza ɗan farin Yerameyel su ne, Ma’az, Yamin da Eker. ’Ya’yan Onam maza su ne, Shammai da Yada. ’Ya’yan Shammai maza su ne, Nadab da Abishur. Sunan matar Abishur ita ce Abihayil, wadda ta haifa masa Aban da Molid. ’Ya’yan Nadab maza su ne, Seled da Affayim. Seled ya mutu babu yara. Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan. Sheshan shi ne mahaifin Alai. ’Ya’yan Yada maza, ɗan’uwan Shammai su ne, Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu babu yara. ’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel. Sheshan ba shi da ’ya’ya maza, sai ’ya’ya mata kawai. Yana da bawa mutumin Masar mai suna Yarha. Sheshan ya ba da ’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai. Attai shi ne mahaifin Natan, Natan shi ne mahaifin Zabad, Zabad shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne mahaifin Obed, Obed shi ne mahaifin Yehu, Yehu shi ne mahaifin Azariya, Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa, Eleyasa shi ne mahaifin Sismai, Sismai shi ne mahaifin Shallum Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma shi ne mahaifin Elishama. Gidan Kaleb ’Ya’yan Kaleb maza, ɗan’uwan Yerameyel su ne, Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif, da ɗansa Maresha, wanda shi ne mahaifin Hebron. ’Ya’yan Hebron maza su ne, Kora, Taffuwa, Rekem da Shema. Shema shi ne mahaifin Raham, Raham kuma shi ne mahaifin Yorkeyam. Rekem shi ne mahaifin Shammai. Ɗan Shammai shi ne Mawon, Mawon kuma shi ne mahaifin Bet-Zur. Efa ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Haran, Moza da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez. ’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af. Ma’aka ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Sheber da Tirhana. Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna da kuma Shewa, mahaifin Makbena da Gibeya. ’Yar Kaleb ita ce Aksa. Waɗannan su ne zuriyar Kaleb. ’Ya’yan Hur maza, ɗan farin Efrata su ne, Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim, Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader. Zuriyar Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim su ne, Harowe, rabin Manahatiyawa, kuma gidan Kiriyat Yeyarim su ne, Itrayawa, Futiyawa, Shumatiyawa da Mishratiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito. Zuriyar Salma su ne, Betlehem, Netofawa, Atrot Bet Yowab, rabin Manahatiyawa, Zoriyawa, kuma gidan marubuta waɗanda suke zama a Yabez su ne, Tiratiyawa, Shimeyatiyawa da Sukatiyawa. Waɗannan su ne Keniyawa waɗanda suka zo daga Hammat, mahaifin gidan Rekab. ’Ya’yan Dawuda maza Waɗannan su ne ’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron. Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel; na ukun, Absalom ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur; na huɗun, Adoniya ɗan Haggit; na biyar, Shefatiya ɗan Abital; da kuma na shida, Itireyam ta wurin matarsa Egla. Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida. Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku, kuma waɗannan su ne yaran da aka haifa masa a can. Shimeya,3.5 Da Ibraniyanci Shimeya, wani suna na Shammuwa Shobab, Natan da Solomon. Waɗannan huɗu ne Bat-shuwa3.5 Bat-shuwa. Waɗansu tsofaffin fassarori biyu (duba kuma 2Sam 11); Ibraniyanci yana da “Batsheba” ne a nan. ’yar Ammiyel ta haifa. Akwai kuma Ibhar, Elishama, Elifelet, Noga, Nefeg, Yafiya, Elishama, Eliyada da Elifelet, su tara ne duka. Dukan waɗannan ’ya’yan Dawuda ne maza, ban da ’ya’yansa maza ta wurin ƙwarƙwaransa. Tamar ita ce ’yar’uwarsu. Sarakuna Yahuda Zuriyar Solomon su ne Rehobowam, da Abiya, da Asa, da Yehoshafat, da Yoram3.11 Da Ibraniyanci Yoram, wani suna na Yehoram, da Ahaziya, da Yowash, da Amaziya, da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya da Manasse, da Amon, da Yosiya. ’Ya’yan Yosiya maza su ne, Yohanan ɗan fari, Yehohiyakim ɗa na biyu, Zedekiya ɗa na uku Shallum ɗa na huɗu. Magādan Yehohiyakim3.16 Da Ibraniyanci Yekoniya, wani suna na Yekoniya; haka kuma a aya 17. su ne, Yekoniya ɗansa, da Zedekiya. Zuriyar sarauta bayan zaman bauta Zuriyar Yekoniya kamamme su ne, Sheyaltiyel, Malkiram, Fedahiya, Shenazzar, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya. ’Ya’yan Fedahiya su ne, Zerubbabel da Shimeyi. ’Ya’yan Zerubbabel maza su ne, Meshullam da Hananiya. Shelomit ce ’yar’uwarsu. Akwai kuma waɗansu biyar, Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya da Yushab-Hesed. Zuriyar Hananiya su ne, Felatiya da Yeshahiya, Refahiya, Arnan, Obadiya da Shekaniya. Zuriyar Shekaniya su ne, Shemahiya da ’ya’yansa maza. Hattush, Igal, Bariya, Neyariya da Shafat, su shida ne duka. ’Ya’yan Neyariya maza su ne, Eliyohenai, Hezekiya da Azrikam, su uku ne duka. ’Ya’yan Eliyohenai su ne, Hodawiya, Eliyashib, Felahiya, Akkub, Yohanan, Delahiya da Anani, su bakwai ne duka. Sauran gidajen Yahuda Zuriyoyin Yahuda su ne, Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal. Reyahiya ɗan Shobal shi ne mahaifin Yahat, Yahat shi ne mahaifin Ahumai da Lahad. Waɗannan su ne gidajen Zoratiyawa. Waɗannan su ne ’ya’yan Etam. Yezireyel, Ishma da Idbash. ’Yar’uwarsu ita ce Hazzelelfoni. Fenuwel shi ne mahaifin Gedor, kuma Ezer shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata da mahaifin Betlehem. Asshur mahaifin Tekowa yana da mata biyu, Hela da Na’ara. Na’ara ta haifi Ahuzzam, Hefer, Temeni da Hawahashtari. Waɗannan su ne zuriyar Na’ara. ’Ya’yan Hela maza su ne, Zeret, Zohar, Etnan, da Koz. Koz ne mahaifin Anub da Hazzobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum. Yabez ya fi ’yan’uwansa martaba. Mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, tana cewa, “Na haife shi da azaba.” Yabez ya yi kuka ga Allah na Isra’ila ya ce, “Ka yi mini albarka ka fadada yankina! Bari hannunka yă kasance tare da ni, yă kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni, don kada in shiga wahala.” Sai Allah ya ji roƙonsa. Kelub, ɗan’uwan Shuha, shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton. Eshton shi ne mahaifin Bet-Rafa, Faseya da Tehinna wanda ya haifi Ir Nahash. Waɗannan su ne mutanen Reka. ’Ya’yan Kenaz maza su ne, Otniyel da Serahiya. ’Ya’yan Otniyel maza su ne, Hatat da Meyonotai. Meyonotai shi ne mahaifin Ofra. Serahiya shi ne mahaifin Yowab, mahaifin Ge-Harashim. An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne. ’Ya’yan Kaleb ɗan Yefunne maza su ne, Iru, Ela da Na’am. Ɗan Ela shi ne, Kenaz. ’Ya’yan Yahallelel su ne, Zif, Zifa, Tiriya da Asarel. ’Ya’yan Ezra maza su ne, Yeter, Mered, Efer da Yalon. Ɗaya daga cikin matan Mered ta haifi Miriyam, Shammai da Ishba wanda ya haifi Eshtemowa. (Matarsa mutuniyar Yahuda kuwa ta haifi Yared mahaifin Gedor, Heber mahaifin Soko, da kuma Yekutiyel mahaifin Zanowa.) Waɗannan su ne ’ya’yan Bitiya ’yar Fir’auna, wadda Mered ya aura. ’Ya’yan matar Hodiya, ’yar’uwar Naham su ne, suka haifi Keyila Bagarme, da Eshtemowa mutumin Ma’aka. ’Ya’yan Shimon maza su ne, Amnon, Rinna, Ben-Hanan da Tilon. Zuriyar Ishi su ne, Zohet da Ben-Zohet. ’Ya’yan Shela ɗan Yahuda maza su ne, Er mahaifin Leka, La’ada mahaifin Maresha da kuma gidajen masu aikin lilin a Bet-Ashbeya, da Yokim, mutanen Kozeba, da Yowash da Saraf wanda ya yi mulkin Mowab da kuma Yashubi Lehem (Waɗannan rubutattun tarihi ne na tun dā.) Su ne maginan tukwane waɗanda suka zauna a Netayim da Gedera; sun zauna a can suka kuma yi wa sarki aiki. Zuriyar Simeyon Zuriyar Simeyon su ne, Nemuwel, Yamin, Yarib, Zera da Shawulu; Shawulu ya haifi Shallum, Shallum ya haifi Mibsam. Mibsam ya haifi Mishma. Zuriyar Mishma su ne, Hammuwel ɗansa, wanda ya haifi Zakkur, shi Zakkur kuma ya haifi Shimeyi. Shimeyi yana da ’ya’ya maza goma sha shida da ’ya’ya mata shida, amma ’yan’uwansa ba su da ’ya’ya da yawa; saboda haka gidansu gaba ɗaya ba tă zama mai mutane da yawa kamar mutanen Yahuda ba. Sun zauna a Beyersheba, Molada, Hazar Shuwal, Bilha, Ezem, Tolad Betuwel, Horma, Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susim, Bet-Biri da Sha’arayim. Waɗannan su ne garuruwansu har lokacin mulkin Dawuda. Ƙauyukan da suke kewayensu su ne Etam, Ayin, Rimmon, Token da Ashan, garuruwa biyar; da kuma dukan ƙauyuka kewaye da waɗannan garuruwa har zuwa Ba’al. Waɗannan ne wuraren zamansu. Suka kuma ajiye tarihin zuriya. Zuriyar Simeyon ta ƙunshi Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya. Akwai Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya. Yoshibiya ɗan Seraya ne. Serahiya kuma ɗan Asiyel ne. Akwai Eliyohenai da Ya’akoba, da Yeshohahiya, da Asahiya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benahiya. Akwai Ziza ɗan Shifi. Shifi ɗan Allon ne. Allon ɗan Yedahiya ne. Yedahiya ɗan Shimri ne. Shimri kuma ɗan Shemahiya ne. Mutanen da aka jera sunayensu a bisa, shugabannin gidajensu ne. Iyalansu sun ƙaru sosai, suka tafi bayan garin Gedor wajajen gabashin kwari suna neman makiyaya domin garkunansu. Suka sami makiyaya mai ciyawa mai kyau, ƙasar kuma tana da fāɗi, da salama, kuma zaman lafiya. A dā waɗansu mutanen Ham sun zauna a can. Mutanen da aka jera sunayensu sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Suka yaƙi mutanen Ham a wuraren zamansu, haka kuma suka yi da Meyunawa da suke can, suka hallaka su ƙaƙaf, yadda yake har yă zuwa yau. Sa’an nan suka zauna a wurin, gama akwai makiyaya domin garkunansu. Mutum ɗari biyar na waɗannan mutane Simeyon, waɗanda Felatiya, Neyariya, Refahiya da Uzziyel, ’ya’yan Ishi maza suka jagorance, sun mamaye ƙasar tudu ta Seyir. Suka karkashe raguwar Amalekawan da suka tsere, suka kuma zauna a can har yă zuwa yau. Zuriyar Ruben ’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila (shi ne ɗan fari, amma sa’ad da ya ƙazantar da gadon auren mahaifinsa, sai aka ba wa ’yancin ɗan farinsa wa ’ya’yan Yusuf maza ɗan Isra’ila; don kada a lissafta shi a tarihin zuriya bisa ga matsayin haihuwarsa, ko da yake Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin ’yan’uwansa kuma mai mulki ya fito daga gare shi, ’yancin zaman ɗan fari na Yusuf ne), ’ya’yan Ruben ɗan farin Isra’ila maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi. Zuriyar Yowel su ne, Shemahiya, Gog, Shimeyi, Mika, Reyahiya, Ba’al, da Beyera, wanda Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya ɗauka zuwa zaman bauta. Beyera shi ne shugaban mutanen Ruben. Danginsu bisa ga iyalansu da aka jera bisa ga tarihin zuriyarsu su ne, Yehiyel shi ne sarki, akwai Zakariya, da Bela ɗan Azaz. Azaz ɗan Shema daga dangin Yowel. Yowel ya yi zama a yankin Arower har zuwa Nebo da Ba’al-Meyon. Ta waje gabas sun zauna a ƙasar har zuwa bakin hamadan da ya nausa zuwa Kogin Yuferites, domin dabbobinsu sun ƙaru a Gileyad. A zamanin Shawulu zuriyar Ruben sun yi yaƙi da Hagirawa, suka ci su da yaƙi, suka zauna a wuraren zaman Hagirawan ko’ina a dukan yankin gabashin Gileyad. Zuriyar Gad Mutanen Gad sun zauna kusa da mutanen Ruben a Bashan, har zuwa Saleka. Yowel shi ne babba, sai Shafan na biyu, sa’an nan Yanai da Shafat, su ne tushen Bashan. Danginsu, bisa ga iyalai su ne, Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka. Waɗannan su ne ’ya’yan Abihayil ɗan Huri, ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Mika’ilu, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz. Ahi ɗan Abiyel, ɗan Guni, shi ne kan iyalinsu. Mutanen Gad sun zauna a Bashan da ƙauyukan da suke kurkusa da shi, da kuma a dukan makiyayan Sharon har zuwa iyaka inda suka kai. Dukan waɗannan sun shiga tarihin zuriya a lokacin mulkin Yotam sarkin Yahuda da Yerobowam sarkin Isra’ila. Mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse sun kasance da mutane 44,760 shiryayyu don aikin soja, jarumawan da za su iya riƙe garkuwa da takobi, waɗanda suke iya yin amfani da baka, waɗanda kuma aka horar don yaƙi. Suka yi yaƙi da Hagirawa, Yetur, Nafish da Nodab. Aka taimake su a yaƙin, Allah kuma ya ba da Hagirawa da dukan abokansu gare su, domin sun yi kuka gare shi a lokacin yaƙin. Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi. Suka ƙwace dabbobin Hagirawa, raƙuma dubu hamsin, tumaki dubu ɗari biyu da hamsin da kuma jakuna dubu biyu. Suka kuma kame mutane dubu ɗari ɗaya, waɗansu suka mutu, domin yaƙin na Allah ne. Suka zauna a ƙasar har lokacin da aka kai su zaman bauta. Rabin kabilar Manasse Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon). Waɗannan su ne kawunan iyalansu. Efer, Ishi, Eliyel, Azriyel, Irmiya, Hodawiya da Yadiyel. Su jarumawa ne, sanannu, su ne kuma kawunan iyalansu. Amma ba su yi aminci da Allahn kakanninsu ba, suka kuma yi karuwanci ga waɗansu allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu. Saboda haka Allah na Isra’ila ya zuga ruhun Ful sarkin Assuriya (wato, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya), wanda ya kwashe mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse zuwa zaman bauta. Ya kwashe su zuwa Hala, Habor, Hara da kuma kogin Gozan, inda suke har wa yau. Zuriyar Lawi ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari. ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam. ’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar. Eleyazar shi ne mahaifin Finehas, Finehas mahaifin Abishuwa, Abishuwa mahaifin Bukki, Bukki mahaifin Uzzi, Uzzi mahaifin Zerahiya, Zerahiya mahaifin Merahiyot, Merahiyot mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub, Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Ahimawaz, Ahimawaz mahaifin Azariya, Azariya mahaifin Yohanan, Yohanan mahaifin Azariya (shi ne ya yi hidima a matsayin firist a haikalin da Solomon ya gina a Urushalima), Azariya mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub, Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Shallum, Shallum mahaifin Hilkiya, Hilkiya mahaifin Azariya, Azariya mahaifin Serahiya, Serahiya kuwa mahaifin Yehozadak. Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershom, Kohat da Merari. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Gershom. Libni da Shimeyi. ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. Waɗannan suke gidajen Lawiyawan da aka jera bisa ga kakanninsu. Na Gershom su ne, Libni, Yahat, Zimma, Yowa, Iddo, Zera da Yeyaterai. Zuriyar Kohat su ne, Amminadab, Kora, Assir, Elkana, Ebiyasaf, Assir, Tahat, Uriyel, Uzziya da Shawulu. Zuriyar Elkana su ne, Amasai, Ahimot, Elkana, Zofai, Nahat, Eliyab Yeroham, Elkana da Sama’ila. ’Ya’yan Sama’ila maza su ne, Yowel ɗan fari da Abiya ɗa na biyu. Zuriyar Merari su ne, Mali, Libni, Shimeyi, Uzza, Shimeya, Haggiya da Asahiya. Mawaƙan haikali Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can. Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu. Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da ’ya’yansu maza. Daga mutanen Kohat akwai, Heman, mawaƙi ɗan Yowel, ɗan Sama’ila, ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyel, ɗan Towa, ɗan Zuf, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai, ɗan Elkana, ɗan Yowel, ɗan Azariya, ɗan Zefaniya ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila; da kuma Asaf ’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa. Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya, ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya, ɗan Malkiya, ɗan Etni, ɗan Zera, ɗan Adahiya ɗan Etan, ɗan Zimma, ɗan Shimeyi, ɗan Yahat, ɗan Gershom, ɗan Lawi; da kuma daga ’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa. Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi, ɗan Malluk, ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya, ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer, ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi. Aka ba ’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah. Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta. Waɗannan su ne zuriyar Haruna, Eleyazar, Finehas, Abishuwa, Bukki, Uzzi, Zerahiya, Merahiyot, Amariya, Ahitub, Zadok da Ahimawaz. (Yoshuwa 21.1-42) Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne): Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta. Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne. Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa, Hilen, Debir, Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu. Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu. Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka. Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse. Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan. Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun. Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu. Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata. Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim. A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer, Yokmeyam, Bet-Horon, Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu. Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat. Mutanen Gershom suka sami waɗannan. Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat, Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon, Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu. Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan. Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza, Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu; daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim, Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu. Zuriyar Issakar ’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yashub da Shimron, su huɗu ne duka. ’Ya’yan Tola maza su ne, Uzzi, Refahiya, Yeriyel, Ibsam da Sama’ila, su ne kuma kawunan iyalansu. A zamanin mulkin Dawuda, an rubuta zuriyar Tola a matsayin mayaƙa a cikin tarihinsu, sun kai 22,600. Ɗan Uzzi shi ne, Izrahiya. ’Ya’yan Izrahiya maza su ne, Mika’ilu, Obadiya, Yowel da Isshiya. Dukansu biyar manya ne. Bisa ga tarihin iyalinsu, sun kai mutane 36,000 shiryayyu don yaƙi, gama suna da mata da ’ya’ya da yawa. Dangin da suke maza masu yaƙi sun kasance na dukan gidajen Issakar ne, kamar yadda aka rubuta a cikin tarihi, su 87,000 ne duka. Zuriyar Benyamin ’Ya’ya uku maza na Benyamin su ne, Bela, Beker da Yediyayel. ’Ya’yan Bela maza su ne, Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot da Iri, su ne kawunan iyalai, kuma su biyar ne duka. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna mazan da sun isa yaƙi 22,034. ’Ya’yan Beker maza su ne, Zemira, Yowash, Eliyezer, Eliyohenai, Omri, Yeremot, Abiya, Anatot da Alemet. Dukan waɗannan ’ya’yan Beker maza ne. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna da kawunan iyalai da mazan da suka isa yaƙi 20,200. Ɗan Yediyayel shi ne, Bilhan. ’Ya’yan Bilhan maza su ne, Yewush, Benyamin, Ehud, Kena’ana, Zetan, Tarshish da Ahishahar. Dukan waɗannan ’ya’yan Yediyayel maza kawunan iyalai ne. Akwai mazan da suka isa yaƙi waje 17,200. Shuffiyawa da Huffiyawa zuriyar Ir ne, kuma Hushiyawa zuriyar Aher ne. Zuriyar Naftali ’Ya’yan Naftali maza su ne, Yaziyel, Guni, Yezer da Shallum, su zuriyar Bilha ne. Zuriyar Manasse Zuriyar Manasse su ne, Asriyel zuriyarsa ne ta wurin ƙwarƙwararsa mutuniyar Aram. Ta haifa wa Makir mahaifin Gileyad. Makir ya auri mata daga cikin Huffiyawa da Shuffiyawa. ’Yar’uwarsa ita ce Ma’aka. Wani daga zuriyar, sunansa Zelofehad, shi yana da ’ya’yan mata ne kawai. Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa ta kuma ba shi suna Feresh. Sunan ɗan’uwansa Sheresh, ’ya’yan Feresh maza kuwa su ne Ulam da Rakem. Ɗan Ulam shi ne, Bedan. Duka waɗannan zuriyar Gileyad ne. Gileyad ɗan Makir ne, Makir kuma ɗan Manasse. ’Yar’uwarsa Makir mai suna Hammoleket ta haifi Ishod, Abiyezer da Mala. ’Ya’yan Shemida maza su ne, Ahiyan, Shekem, Liki da Aniyam. Zuriyar Efraim Zuriyar Efraim su ne, Shutela, Bered, Tahat, Eleyada, Tahat Zabad da Shutela. Wani ɗan ƙasa haifaffen mutanen Gat ya kashe Ezer da Elad, sa’ad da suka gangara don su ƙwace dabbobinsu. Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya. Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa. ’Yarsa ita ce Sheyera, wadda ta gina Bet-Horon na kwari da na tudu da kuma Uzzen-Sheyera. Zuriyarsa ita ce, Refa, Reshef, Tela, Tahan, Ladan, Ammihud, Elishama, Nun da kuma Yoshuwa. Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta. A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa. Zuriyar Asher ’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishwi da Beriya. ’Yar’uwarsa ita ce Sera. ’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel, wanda yake mahaifin Birzayit. Heber shi ne mahaifin Yaflet, Shomer da Hotam da kuma ’yar’uwarsu Shuwa. ’Ya’yan Yaflet maza su ne, Fasak, Bimhal da Ashwat. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaflet maza. ’Ya’yan Shemer maza su ne, Ahi, Roga, Yehubba da Aram. ’Ya’yan ɗan’uwansa Helem su ne, Zofa, Imna, Shelesh da Amal. ’Ya’yan Zofa maza su ne, Suwa, Harnefer, Shuwal, Beri, Imra, Bezer, Hod, Shamma, Shilsha, Itran da Bera. ’Ya’yan Yeter maza su ne, Yefunne, Fisfa da Ara. ’Ya’yan Ulla maza su ne, Ara, Hanniyel da Riziya. Dukan waɗannan zuriyar Asher ne, kawunan iyalai, zaɓaɓɓun mutane, jarumawa sosai da kuma fitattun shugabanni. Yawan mutanen da suke a shirye don yaƙi, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, 26,000 ne. Zuriyar Shawulu mutumin Benyamin Benyamin shi ne mahaifin, Bela ɗansa na fari, Ashbel ɗansa na biyu, Ahara na uku, Noha na huɗu da Rafa na biyar. ’Ya’yan Bela maza su ne, Addar, Gera, Abihud Abishuwa, Na’aman, Ahowa, Gera, Shefufan da Huram. Waɗannan su ne zuriyar Ehud, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Geba waɗanda aka kuma kwasa zuwa Manahat. Na’aman, da Ahiya, da Gera. Gera ne shugabansu lokacin da aka kai su bauta, shi ne ya haifi Uzza da Ahilud. An haifa ’ya’ya maza wa Shaharayim a Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba’ara. Ya haifi Yobab, Zibiya, Hodesh, Malkam, Yewuz, Sakiya da Mirma ta wurin Hodesh matarsa. Waɗannan su ne ’ya’yansa, kawunan iyalai. Ya haifi Abitub da Efa’al ta wurin Hushim. ’Ya’yan Efa’al maza su ne, Eber, Misham, Shemed (wanda ya gina Ono da Lod tare da ƙauyukan kewayensu), da Beriya da Shema, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Aiyalon waɗanda kuma suka kori mazaunan Gat. Ahiyo, Shashak, Yeremot Zebadiya, Arad, Eder, Mika’ilu, Isfa da Yoha su ne ’ya’yan Beriya maza. Zebadiya, Meshullam, Hizki, Heber, Ishmerai, Izliya da Yobab su ne ’ya’yan Efa’al maza. Yakim, Zikri, Zabdi, Eliyenai, Zilletai, Eliyel, Adahiya, Berahiya da Shimra su ne ’ya’yan Shimeyi maza. Ishfan, Eber, Eliyel, Abdon, Zikri, Hanan, Hananiya, Elam, Antotiya, Ifdehiya da Fenuwel su ne ’ya’yan Shashak maza. Shamsherai, Shehariya, Ataliya, Ya’areshiya, Iliya da Zikri su ne ’ya’yan Yeroham maza. Dukan waɗannan su ne kawunan iyalai, manya kamar yadda aka lissafta a cikin zuriyarsu, suka zauna a Urushalima. Yehiyel na Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Sunan matarsa Ma’aka, ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab, Gedor, Ahiyo, Zeker da Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima. Ner shi ne mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al. Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al8.34 Aka kuma sani kamar Mefiboshet wanda ya zama mahaifin Mika. ’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tereya da Ahaz. Ahaz shi ne mahaifin Yehowadda, Yehowadda shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza. Moza shi ne mahaifin Bineya; Rafa, Eleyasa da kuma Azel. Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Dukan waɗannan ’ya’yan Azel maza ne. ’Ya’yan ɗan’uwansa Eshek su ne, Ulam ɗan farinsa, Yewush ɗansa na biyu da Elifelet na uku. ’Ya’yan Ulam maza jarumawa ne sosai waɗanda suke iya riƙe baka. Suna da ’ya’ya maza masu yawa da jikoki, 150 gaba ɗaya. Dukan waɗannan zuriyar Benyamin ne. Haka aka lissafta dukan Isra’ila a tarihin zuriyoyi a littafin sarakunan Isra’ila. Aka kwasa mutanen Yahuda zuwa zaman bauta a Babilon domin rashin aminci. Mutanen Urushalima To, na farkon da aka sāke zaunar da su a mallakarsu a garuruwansu, su ne waɗansu Isra’ilawa, firistoci, Lawiyawa da kuma masu hidimar haikali. Waɗanda suke daga Yahuda, daga Benyamin, da kuma daga Efraim da Manasse waɗanda suka zauna a Urushalima su ne, Uttai ɗan Ammihud, ɗan Omri, ɗan Imri, ɗan Bani, zuriyar Ferez ɗan Yahuda. Na mutanen Shilo kuwa su ne, Asahiya ɗan fari da ’ya’yansa maza. Na mutanen Zera su ne, Yewuyel. Mutane daga Yahuda sun kai 690. Na Benyamin su ne, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Hodawiya, ɗan Hassenuwa; Ibnehiya ɗan Yeroham; Ela ɗan Uzzi, ɗan Mikri; da Meshullam ɗan Shefatiya, ɗan Reyuwel, ɗan Ibniya. Mutane daga Benyamin, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, sun kai 956. Dukan waɗannan mutane kawunan iyalansu ne. Na firistoci su ne, Yedahiya; Yehoyarib; Yakin; Azariya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, shugaban da yake lura da gidan Allah; Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya; da Ma’asai ɗan Adiyel, ɗan Yazera, ɗan Meshullam, ɗan Meshillemit, ɗan Immer. Firistocin da suke kawunan iyalai, sun kai 1,760. Dukansu ƙwararru ne, masu hakkin hidima a cikin gidan Allah. Na Lawiyawa su ne, Shemahiya ɗan Hasshub, ɗan Azrikam, ɗan Hashabiya, mutumin Merari; Bakbakkar, Heresh, Galal da Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zikri, ɗan Asaf; Obadiya ɗan Shemahiya, ɗan Galal, ɗan Yedutun; da Berekiya ɗan Asa, ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofawa. Matsaran ƙofofi su ne, Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman da ’yan’uwansu. Shallum ne babbansu da aka ajiye a Ƙofar Sarki a gabas, har zuwa wannan lokaci. Waɗannan su ne matsaran ƙofofi na sansanin Lawiyawa. Shallum ɗan Kore, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, da ’yan’uwansa matsaran ƙofofi daga iyalin (mutanen Kohat) su suke da hakkin tsaron madogaran ƙofar Tenti kamar dai yadda kakanninsu suka kasance da hakkin tsaron mashigin mazaunin Ubangiji. A dā Finehas ɗan Eleyazar ne yake lura da matsaran, kuma Ubangiji ya kasance tare da shi. Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada. Duka-duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai 212. Aka rubuta su zuriya-zuriya a ƙauyukansu. Dawuda da Sama’ila mai duba ne suka sa matsaran a wurarensu na aminci. Su da zuriyarsu, su suke lura da tsaron ƙofofin gidan Ubangiji, gidan da ake kira Tenti. Matsaran suna a kusurwoyi huɗu, gabas, yamma, arewa da kudu. ’Yan’uwansu a ƙauyukansu sukan zo lokaci, lokaci su yi ayyukansu kwana bakwai, bakwai. Amma manyan matsara huɗu, waɗanda suke Lawiyawa, an danƙa musu hakkin lura da ɗakuna da kuma wuraren ajiya a gidan Allah. Sukan kwana a kewayen gidan Allah, domin dole su tsare shi; kuma su suke lura da mabuɗi don buɗewa a kowace safiya. Waɗansunsu su ne suke lura da kayayyakin da ake amfani da su a hidimar haikali; sukan ƙirga su sa’ad da ake shigar da su da sa’ad da ake fitar da su. An sa waɗansu su lura da kayayyakin da kuma dukan waɗansu kayan wuri mai tsarki, da kuma gari da ruwan inabi, da mai, turare da kuma kayan yaji. Amma waɗansu firistoci ne suke harhaɗa kayan yajin. Wani Balawe mai suna Mattitiya, ɗan farin Shallum mutumin Kora ne aka danƙa masa hakkin toya burodin miƙawa. Waɗansu ’yan’uwansu Kohatawa ne suke lura da shiryawa burodin da ake kaiwa a tebur a kowane Asabbaci. Waɗanda suke mawaƙa, kawunan iyalan Lawiyawa, sukan zauna a ɗakunan haikali kuma ba sa yin waɗansu ayyuka domin su suke da hakkin aiki dare da rana. Dukan waɗannan su ne kawunan iyalan Lawiyawa, manya kamar yadda aka lissafta su a zuriyarsu, kuma suna zama a Urushalima. Zuriyar Shawulu (1 Tarihi 8.29-38) Yehiyel mahaifin Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Matarsa ita ce Ma’aka ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab, Gedor, Ahiyo, Zakariya da Miklot. Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima. Ner shi mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.9.39 Aka kuma sani da Ish-Boshet Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda shi ne mahaifin Mika. ’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tareya da Ahaz. Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza. Moza shi ne mahaifin Bineya; Refahiya, Eleyasa da kuma Azel. Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Waɗannan su ne ’ya’yan Azel maza. Shawulu ya ɗauke ransa (1 Sama’ila 31.1-13) To, fa, Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa; Isra’ilawa kuwa suka gudu a gabansu, da yawa kuma suka mutu a kan Dutsen Gilbowa. Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kuma kashe ’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa. Yaƙin ya yi tsanani kewaye da Shawulu, kuma sa’ad da maharba suka rutsa shi, sai suka ji masa rauni. Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa. Da mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya fāɗi a kan takobinsa ya mutu. Ta haka Shawulu da ’ya’yansa maza uku suka mutu, dukan gidansa kuwa suka mutu tare. Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu. Kashegari, da Filistiyawa suka zo don su tuttuɓe waɗanda suka mutu, sai suka sami Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu a Dutsen Gilbowa. Suka tuttuɓe shi suka yanke kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka kuma aika ’yan aika ko’ina a ƙasar Filistiyawa, a yi shela labarin a cikin gumakansu da kuma mutanensu. Suka sa kayan yaƙinsa a haikalin allahnsu suka kuma rataye kansa a haikalin Dagon. Sa’ad da mazaunan Yabesh Gileyad suka ji dukan abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu, sai dukan jarumawa suka tafi suka ɗauki jikunan Shawulu da na ’ya’yansa maza suka kawo Yabesh. Sa’an nan suka binne ƙasusuwan a ƙarƙashin babban itace oak a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai. Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba, bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse. Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila (2 Sama’ila 5.1-3) Dukan Isra’ila fa suka taru wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu jiki da jininka ne. A dā, ko a lokacin da Shawulu yake sarki, ai, kai ne kake shugabantar Isra’ila a yaƙe-yaƙe. Kuma Ubangiji Allahnka ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayin mutanena Isra’ila, za ka kuma zama mai mulkinsu.’ ” Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, suka yi yarjejjeniya da shi a gaban Ubangiji, suka kuwa shafe Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila, yadda Ubangiji ya yi alkawari ta wurin Sama’ila. Dawuda ya ci Urushalima (2 Sama’ila 5.6-10) Dawuda tare da dukan Isra’ilawa suka taka zuwa Urushalima (wato, Yebus). Yebusiyawan da suke zama a wurin suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka, Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, Birnin Dawuda. Dawuda ya ce, “Duk wanda ya jagoranci yaƙi a kan Yebusiyawa zai zama babban shugaban mayaƙa.” Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba. Dawuda zauna a kagarar, ta haka aka kira ta Birnin Dawuda. Sai ya gina birni kewaye da shi, daga madogaran gini zuwa katangar da take kewaye, yayinda Yowab ya maido da sauran birnin. Dawuda kuwa ya ƙara ƙarfi, domin Ubangiji Maɗaukaki yana tare da shi. Jarumawan Dawuda (2 Sama’ila 23.8-17) Waɗannan su ne manyan jarumawan Dawuda, su ne, tare da dukan Isra’ila, suka ba wa mulkinsa goyon baya mai ƙarfi da ya kai bisa dukan ƙasar, yadda Ubangiji ya yi alkawari. Ga jerin sunayen jarumawan Dawuda. Yashobeyam wani ɗan Hakmoni, shi ne babban shugaba; ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe a ƙarawa guda kawai. Biye da shi, shi ne Eleyazar ɗan Dodo mutumin Aho, ɗaya daga cikin jarumawa uku. Yana tare da Dawuda a Fas Dammim sa’ad da Filistiyawa suka taru can don yaƙi. A wani wuri inda akwai gona cike da sha’ir, sojoji suka gudu daga Filistiyawa. Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha’ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuma ya kawo babban nasara. Wata rana uku cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara wurin Dawuda zuwa dutse a kogon Adullam, yayinda ƙungiyar Filistiyawa suke sansani a Kwarin Refayim. A lokacin Dawuda yana cikin mafaka, sojojin Filistiyawa kuma suna a Betlehem. Dawuda ya ji marmarin ruwan sha sai ya ce, “Kash, a ce wani zai sami mini ruwan sha daga rijiya kusa da ƙofar Betlehem mana!” Sai Ukun suka kutsa kai cikin sansanin Filistiyawa, suka ja ruwa daga rijiyar da take kusa da ƙofar Betlehem suka ɗauko shi suka kawo wa Dawuda. Amma ya ƙi yă sha; a maimako, sai ya zubar da shi a gaban Ubangiji. Ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka, ya kamata in sha jinin waɗannan mutanen da suka yi kasai da rayukansu?” Domin sun yi kasai da rayukansu don su dawo da shi, Dawuda bai sha shi ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan. (2 Sama’ila 23.18-39) Abishai ɗan’uwan Yowab shi ma babba ne cikin Ukun nan. Ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe, ya kuma zama sananne kamar Ukun. Aka ninka girmama shi bisa Ukun, sai ya zama shugaba, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba. Benahiya ɗan Yehohiyada shi ma wani barden yaƙi ne daga Kabzeyel, wanda ya yi manyan abubuwa. Ya bugi gwanayen Mowab biyu. Ya kuma gangara zuwa cikin rami a ranar da aka yi dusar ƙanƙara ya kashe zaki. Ya kuma kashe wani mutumin Masar mai tsayi ƙafa bakwai da rabi. Ko da yake mutumin Masar yana da māshi kamar sandan masaƙa a hannunsa, Benahiya ya yaƙe shi da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannun mutumin Masar ya kuma kashe shi da māshin nan nasa. Irin abubuwan da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma sananne ne kamar waɗannan jarumawa uku. Aka ɗauka shi da bangirma fiye da Talatin nan, amma ba a haɗa shi cikin Ukun ba. Dawuda kuwa ya sa shi yă lura da masu tsaron lafiyarsa. Jarumawan nan su ne, Asahel ɗan’uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem, Shammot mutumin Haror, Helez mutumin Felon, Ira ɗan Ikkesh daga Tekowa, Abiyezer daga Anatot, Sibbekai mutumin Husha, Ilai mutumin Aho, Maharai mutumin Netofa, Heled ɗan Ba’ana mutumin Netofa, Ittai ɗan Ribai daga Gibeya a Benyamin, Benahiya mutumin Firaton, Hurai daga kogunan Ga’ash, Abiyel mutumin Arba, Azmawet mutumin Harum, Eliyaba mutumin Sha’albo, ’ya’yan Hashem mutumin Gizon maza, Yonatan ɗan Shageye mutumin Harar, Ahiyam ɗan Sakar mutumin Harar, Elifal ɗan Ur, Hefer mutumin Mekerat, Ahiya mutumin Felon, Hezro mutumin Karmel, Na’arai ɗan Ezbai, Yowel ɗan’uwan Natan, Mibhar ɗan Hagiri, Zelek mutumin Ammon Naharai Baroti, mai ɗaukar kayan yaƙin Yowab ɗan Zeruhiya, Ira mutumin Itra, Gareb mutumin Itra, Uriya mutumin Hitti Zabad ɗan Alai, Adina ɗan Shiza mutumin Ruben, wanda shi ne babba na mutanen Ruben, kuma talatin suna tare da shi, Hanan ɗan Ma’aka, Yoshafat mutumin Mit, Uzziya mutumin Ashtarot, Shama da Yehiyel ’ya’yan Hotam mutumin Arower maza, Yediyayel ɗan Shimri, ɗan’uwansa Yoha mutumin Tiz, Eliyel mutumin Ma’aha, Yeribai da Yoshawiya ’ya’yan Elna’am maza, Itma mutumin Mowab, Eliyel, Obed da Ya’asiyel mutumin Mezob. Jarumawa sun haɗa kai da Dawuda Waɗannan su ne mutanen da suka zo wurin Dawuda a Ziklag, yayinda aka kore shi daga gaban Shawulu ɗan Kish (suna cikin jarumawan da suka taimake shi a yaƙi; suna da baka suna kuma iya harba kibiya, ko majajjawa da hannun dama ko na hagu; su ’yan’uwan Shawulu ne daga kabilar Benyamin): Ahiyezer babbansu da Yowash ’ya’yan Shema’a maza daga Gibeya; Yeziyel da Felet ’ya’yan Azmawet; Beraka, Yehu daga Anatot, da Ishmahiya daga Gibeyon, wani jarumi a cikin Talatin nan, wanda shi ne shugaban Talatin; Irmiya, Yahaziyel, Yohanan, Yozabad daga Gedera, Eluzai, Yerimot, Beyaliya, Shemariya da Shefatiya daga Haruf; Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezer da Yashobeyam daga Kora; da Yoyela da Zebadiya ’ya’yan Yeroham maza daga Gedor. Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu. Ezer shi ne babba, Obadiya shi ne mai binsa a shugabanci, Eliyab na uku, Mismanna na huɗu, Irmiya na biyar, Attai na shida, Eliyel na bakwai, Yohanan na takwas, Elzabad na tara, Irmiya na goma da kuma Makbannai na goma sha ɗaya. Waɗannan mutanen Gad shugabannin mayaƙa ne; ƙarami a cikinsu zai iya ƙara da mutum ɗari, kuma babba a cikin zai iya ƙara da dubu. Su ne suka haye Urdun a wata na farko sa’ad da kogin ya yi ambaliya, suka kuma kori duk mai rai a kwarin, na wajen gabas da na wajen yamma. Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa. Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.” Sai Ruhu ya sauko a kan Amasai, shugaban Talatin nan, sai ya ce, “Mu naka ne, ya Dawuda! Muna tare da kai, ya ɗan Yesse! Nasara, nasara gare ka, nasara kuma ga waɗanda suke taimakonka. Gama Allahnka zai taimake ka.” Saboda haka Dawuda ya karɓe su ya kuma mai da su shugabannin ƙungiyoyin maharansa. Waɗansu mutanen Manasse suka haɗa kai da Dawuda sa’ad da ya tafi tare da Filistiyawa don yă yaƙi Shawulu (Shi da mutanensa ba su taimaki Filistiyawa ba domin bayan shawarwari, shugabanninsu suka salame shi. Sun ce, “Za mu biya da kawunanmu in ya koma ga maigidansa Shawulu.”) Da Dawuda ya tafi Ziklag, waɗannan mutanen Manasse ne suka haɗa kai da shi. Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika’ilu, Yozabad, Elihu da Zilletai, shugabannin ƙungiyoyi na dubu a cikin Manasse. Suka taimaki Dawuda a kan ƙungiyoyin hari, gama dukansu jarumawa ne sosai, kuma su shugabanni ne a cikin mayaƙansa. Kowace rana mutane suka riƙa zuwa don su taimaki Dawuda, sai da ya kasance da runduna mai girma, kamar mayaƙan Allah. Saura sun haɗa kai da Dawuda a Hebron Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa. Mutanen Yahuda, masu riƙe garkuwa da māshi, su 6,800 shiryayyu don yaƙi; mutanen Simeyon, jarumawa shiryayyu don yaƙi, su 7,100; mutanen Lawi, su 4,600, haɗe da Yehohiyada, shugaban iyalin Haruna tare da mutane 3,700, da Zadok, matashi jarumi sosai, tare da shugabanni su 22 daga iyalinsa; mutanen Benyamin, ’yan’uwan Shawulu, su 3,000, yawanci waɗanda suke biyayya ga gidan Shawulu sai lokacin; mutanen Efraim, jarumawa, sanannu cikin gidajensu, su 20 800; mutanen rabin kabilar Manasse, sanannu da sunaye suka zo suka mai da Dawuda sarki, su 18,000; mutanen Issakar, masu fahimtar lokuta suka kuma san abin da ya kamata Isra’ila ya yi, manya 200, tare da danginsu a ƙarƙashin shugabancinsu; mutanen Zebulun, ƙwararru sojoji shiryayyu don yaƙi da kowane irin makami, suka zo don su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya, su 50,000; mutanen Naftali su 1,000 shugabanni, tare da mutane 37,000 masu riƙe garkuwa da masu; mutanen Dan, shiryayyu don yaƙi, su 28,600; mutanen Asher, ƙwararrun sojoji shiryayyu don yaƙi, su 40,000; kuma daga gabashin Urdun, mutanen Ruben, Gad da kuma rabin kabilar Manasse, masu kayan yaƙi iri-iri, su 120,000. Dukan waɗannan mayaƙa ne waɗanda suka ba da kansu da yardar rai su yi hidima. Suka zo Hebron da cikakken niyya don su naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila. Duka sauran Isra’ilawa su ma suka goyi baya a naɗa Dawuda sarki. Mutanen suka yi kwana uku a can tare da Dawuda, suna ci suna sha, gama iyalansu sun yi musu tanadi. Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila. Dawowa da akwatin alkawari (2 Sama’ila 6.1-12) Sai Dawuda ya tattauna da kowane ɗaya daga cikin shugabanninsa, shugabannin sojoji na dubu-dubu da na ɗari-ɗari. Sa’an nan ya ce wa dukan taron Isra’ila, “In ya yi muku kyau kuma in nufin Ubangiji Allahnmu ne, bari mu aika da saƙo nesa da kuma ko’ina zuwa ga sauran ’yan’uwanmu a duk iyakokin Isra’ila, da kuma zuwa ga firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a garuruwansu da makiyayansu, su zo wurinmu. Bari mu ɗauko akwatin alkawarin Allahnmu mu kawo wurinmu, gama ba mu neme shi a lokacin mulkin Shawulu ba.” Dukan taron jama’a suka yarda su yi haka, domin ya yi daidai ga dukan mutane. Saboda haka Dawuda ya tattara dukan Isra’ilawa, daga Kogin Shihor a Masar zuwa Lebo Hamat, don su kawo akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim. Dawuda da dukan Isra’ilawa tare da shi suka tafi Ba’ala na Yahuda (Kiriyat Yeyarim) don su haura daga can su kawo akwatin alkawarin Allah Ubangiji, wanda yake zama tsakanin kerubobi, akwatin alkawarin da ake kira da Sunan. Suka ɗauki akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab a kan sabon keken shanu, Uzza da Ahiyo ne suke lura da shi. Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi shagali da dukan ƙarfinsu a gaban Allah, tare da waƙoƙi da garayu, molaye, ganguna, kuge da ƙahoni. Sa’ad da suka kai masussukar Kidon, Uzza ya miƙa hannunsa don yă gyara akwatin alkawarin, gama shanun sun yi tuntuɓe. Sai fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Uzza, ya kuma buge shi domin ya sa hannunsa a kan akwatin alkawarin. Sai ya mutu a can a gaban Allah. Ran Dawuda ya ɓace domin Ubangiji ya husata a kan Uzza, kuma har wa yau ana ce da wannan wuri Ferez Uzza.13.11 Ferez Uzza yana nufin hasala a kan Uzza. Dawuda ya ji tsoron Allah a wannan rana ya kuma yi tambaya, “Yaya zan taɓa kawo akwatin alkawarin Allah gare ni?” Don haka bai ɗauki akwatin alkawarin ya kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka, ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat. Akwatin Alkawarin Allah ya zauna tare da iyalin Obed-Edom a gidansa wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkaci gidan Obed-Edom da kome da yake da shi. Gida da iyalin Dawuda (2 Sama’ila 5.11-16) To, fa, Hiram sarkin Taya ya aika da ’yan aika zuwa wurin Dawuda, tare da gumaguman al’ul, maginan duwatsu da kafintoci, don su gina wa Dawuda fada. Dawuda kuwa ya san cewa Ubangiji ya kafa shi a matsayin sarki a bisa Isra’ila kuma cewa an ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa Isra’ila. A Urushalima, Dawuda ya ƙara auren waɗansu mata, ya kuma zama mahaifin ƙarin ’ya’yan maza da mata. Ga sunayen yaran da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon, Ibhar, Elishuwa, Elfelet, Noga, Nefeg, Yafiya, Elishama, Beyeliyada da Elifelet. Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi (2 Sama’ila 5.17-25) Sa’ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila, sai suka haura da cikakken mayaƙa don su neme shi, amma Dawuda ya ji game da wannan ya kuwa fita don yă ƙara da su. To, fa, Filistiyawa suka zo suka kai wa Kwarin Refayim hari; sai Dawuda ya roƙi Allah ya ce, “In tafi in yaƙi Filistiyawa? Za ka ba da su gare ni?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ka tafi, zan ba da su gare ka.” Saboda haka Dawuda da mutanensa suka haura zuwa Ba’al-Ferazim, a can kuwa suka ci Filistiyawa da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa kan raraki ƙasa, haka Allah ya raraki abokan gābana ta wurin hannuna.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim. Filistiyawa suka yashe allolinsu, Dawuda kuma ya ba da umarnai a ƙone su a wuta. Filistiyawa suka sāke kai hari wa kwarin; sai Dawuda ya sāke roƙi Allah, Allah kuwa ya amsa masa, “Kada ka tafi kai tsaye, amma ka yi zobe kewaye da su, ka kuma fāɗa musu a gaban itatuwan tsamiya. Da zarar ka ji motsin takawa a sama itatuwan tsamiya, ka fita don yaƙi, domin wannan zai nuna cewa Allah ya fita a gabanka don yă bugi mayaƙan Filistiyawa.” Saboda haka Dawuda ya yi kamar yadda Allah ya umarce shi, suka kuma bugi mayaƙan Filistiyawa, tun daga Gibeyon har zuwa Gezer. Sai sunan Dawuda ya bazu ko’ina a ƙasar, Ubangiji kuwa ya sa dukan al’ummai suka ji tsoronsa. An kawo akwatin alkawari a Urushalima Bayan Dawuda ya yi gine-gine wa kansa a Birnin Dawuda, sai ya shirya wuri domin akwatin alkawarin Allah, ya kuma kafa tenti dominsa. Sa’an nan Dawuda ya ce, “Babu wani sai ko Lawiyawa kaɗai za su ɗauka akwatin alkawarin Allah, gama Ubangiji ya zaɓe su su ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji su kuma yi hidima a gabansa har abada.” Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa. Ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya da kuma Lawiyawa. Daga zuriyar Kohat, Uriyel shugaba da dangi 120; daga zuriyar Merari Asahiya shugaba da dangi 220; daga zuriyar Gershom, Yowel shugaba da dangi 130; daga zuriyar Elizafan, Shemahiya shugaba da dangi 200; daga zuriyar Hebron, Eliyel shugaba da dangi 80; daga zuriyar Uzziyel, Amminadab shugaba da dangi 112. Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa. Ya ce musu, “Ku ne kawunan iyalan Lawiyawa; ku da ’yan’uwanku Lawiyawa, sai ku tsarkake kanku ku hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila, zuwa wurin da na shirya dominsa. Domin ku, Lawiyawa ba ku haura da shi da farko ba ne ya sa Ubangiji Allahnmu ya husata a kanmu. Ba mu tambaye shi game da yadda za mu yi shi a hanyar da aka ƙayyade ba.” Saboda haka firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu don su hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila. Sai Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah da sanduna a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji. Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa ’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna. Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berekiya daga cikin ’yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kushahiya. Tare da su kuma ’yan’uwansa da suke biye bisa ga matsayi. Wato, Zakariya,15.18 Rubuce-rubucen Ibraniyanci guda uku da kuma yawancin rubuce-rubucen Seftuwajin (duba kuma aya 20 da 1Tar 16.5); yawancin Rubuce-rubucen Ibraniyanci Zakariya ɗan da kuma ko Zakariya, Ben da Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ben, Ma’asehiya, Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom da Yehiyel,15.18 Da Ibraniyanci; Seftuwajin (duba kuma aya 21) Yehiyel da Azaziya matsaran ƙofofi. Mawaƙan nan Heman, Asaf da Etan, ne za su buga kugen tagulla. Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot. Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom, Yehiyel da Azaziya, ne za su ja garayu masu murya ƙasa-ƙasa bisa ga sheminit. Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni. Berekiya da Elkana, ne za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin. Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin. (2 Sama’ila 6.12-22) Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-Edom, da farin ciki. Domin Allah ya taimaki Lawiyawan da suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, aka miƙa hadayar bijimai bakwai da raguna bakwai. To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin. Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu. Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal ’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta. Yin hidima a gaban akwatin alkawari Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah. Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji. Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace. Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila. Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna, Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah. Zaburar Dawuda ta godiya (Zabura 105.1-15; 96.1-13; 106.1,47,48) A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji. Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi. Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa. Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki. Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum. Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke, Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa. Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya. Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu, alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku. Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari. “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.” Sa’ad da suke kima, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta, suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga wannan mulki zuwa wancan. Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna. “Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.” Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane. Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli. Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai. Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa. Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji, ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa. Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba. Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!” Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri; bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki! Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce. Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.” Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.” Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana. Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi. Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila. Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa. Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka. Alkawarin Allah ga Dawuda (2 Sama’ila 7.1-17) Bayan Dawuda ya zauna a fadansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti.” Natan ya amsa wa Dawuda ya ce, “Duk abin da kake tunani a zuciya, ka yi, gama Allah yana tare da kai.” A daren nan maganar Allah ta zo wa Natan cewa, “Ka tafi ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ba kai ba ne za ka gida mini gidan da zan zauna a ciki. Ban taɓa zama a gida daga ranar da na fito da Isra’ila daga Masar ba har wa yau. Na yi ta yawo daga gefen da aka kafa tenti zuwa wani, daga wannan wuri zuwa wancan. Duk inda na tafi tare da Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani daga cikin shugabanninsu waɗanda na umarta su yi kiwon mutanena, “Don me ba ku gida mini gidan al’ul ba?” ’ “Yanzu, ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauke ka daga makiyaya da kuma daga bin garke, don ka zama mai mulki a bisa mutanena Isra’ila. Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya. Zan kuma tanada wuri domin mutanena Isra’ila, zan kuma kafa su saboda za su kasance da gidan kansu ba kuwa za a ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zaluntar su ba, yadda suka yi da farko da kuma suka yi tun lokacin da na sa shugabanni a bisa mutanen Isra’ila. Zan rinjaye dukan abokan gābanka. “ ‘Na furta maka cewa Ubangiji zai gina maka gida, sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin ’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka. Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada. Zan zama Ubansa, zai kuma zama ɗana. Ba zan taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi, kamar yadda na ɗauke ta daga wanda ya riga ka ba. Zan sa shi a bisa gidana da mulkina har abada; kujerar sarautarsa za tă kahu har abada.’ ” Natan ya faɗa wa Dawuda dukan kalmomin wahayin nan. Addu’ar Dawuda (2 Sama’ila 7.18-29) Sai Sarki Dawuda ya shiga ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, kuma wane ne iyalina, da ka kawo ni har zuwa nan? Kuma sai ka ce wannan bai isa ba a idonka, ya Allah, ka yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Ka dube ni sai ka ce ni ne mafi ɗaukaka cikin mutane, ya Ubangiji Allah. “Me kuma Dawuda zai ce maka saboda girmamawar da ka yi wa bawanka? Gama ka san bawanka, Ya Ubangiji. Gama saboda bawanka da kuma bisa ga nufinka, ka yi wannan babban abu, ka kuma sanar da dukan manyan alkawura. “Babu wani kamar ka, ya Ubangiji, babu kuma Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu. Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar? Ka mai da mutanenka Isra’ila na kanka har abada, kuma kai, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu. “Yanzu kuwa, Ubangiji, bari alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa yă kahu har abada. Yi kamar yadda ka yi alkawari, saboda zai kahu kuma sunanka zai zama mai girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki, Allah a bisa Isra’ila, Allahn Isra’ila ne!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka. “Kai, Allahna, ka bayyana ga bawanka cewa za ka gina gida dominsa. Ta haka bawanka ya sami ƙarfin gwiwa ya yi addu’a gare ka. Ya Ubangiji, kai ne Allah! Ka yi alkawari abubuwa masu kyau wa bawanka. Yanzu ka ji daɗi don ka albarkace gidan bawanka, don yă ci gaba har abada a gabanka; gama kai, ya Ubangiji, ka albarkace shi, ya kuma sami albarka ke nan har abada.” Nasarorin Dawuda (2 Sama’ila 8.1-14) Ana nan sai Dawuda ya ci Filistiyawa ya kuma rinjaye su, ya ƙwace Gat da ƙauyukan kewayenta daga mulkin Filistiyawa. Dawuda ya kuma ci Mowabawa, suka zama bayinsa suka kuma biya haraji. Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer sarkin Zoba, har can Hamat, sa’ad da ya je don yă kafa mulkinsa a wajen Kogin Yuferites. Dawuda ya kame keken yaƙinsa dubu ɗaya, da mahayan kekunan yaƙi dubu bakwai da sojojin kafa guda dubu ashirin. Ya yayyanke dukan agaran dawakansa, amma ya bar dawakai da suka isa jan kekunan yaƙi ɗari. Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu. Ya sa ƙungiyoyin sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus. Arameyawan kuwa suka zama bayinsa, suka kuma kawo haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi. Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariyan da shugabannin sojojin Hadadezer suke riƙe, ya kawo su Urushalima. Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam. Sa’ad da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci mayaƙan Hadadezer sarkin Zoba gaba ɗaya, sai ya aiki ɗansa Hadoram zuwa wurin Sarki Dawuda yă gaishe shi yă kuma yi masa barka da nasara a yaƙi a kan Hadadezer, wanda yake yaƙi da Towu. Hadoram ya kawo kowane irin kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla. Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek. Abishai ɗan Zeruhiya ya bugi mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri. Ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi. Manyan ma’aikatan Dawuda (2 Sama’ila 8.15-18) Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa. Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci; Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci; Shafsha shi ne magatakarda; Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa; ’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki. Dawuda ya ci Ammonawa da yaƙi (2 Sama’ila 10.1-19) Ana nan, sai Nahash sarkin Ammonawa ya mutu, sai ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. Dawuda ya yi tunani, “Zan nuna jinƙai ga Hanun ɗan Nahash, domin mahaifinsa ya nuna alheri gare ni.” Saboda haka Dawuda ya aika da tawaga don yă yi wa Hanun ta’aziyya game da mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka iso wurin Hanun a ƙasar Ammonawa don su ta’azantar da shi, sai manyan Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aika mutanen nan wurinka su ta’azantar da kai? Ba mutanensa sun zo ne su bincika su kuma leƙi ƙasar su tumɓuke ta ba?” Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda, ya yi musu aski, ya yayyanka rigunansu a daidai ɗuwawunsu, sa’an nan ya sallame su. Da wani ya zo ya faɗa wa Dawuda game da mutanen, sai ya aiki ’yan aika su sadu da su, gama an ƙasƙantar da su ainun. Sarki ya ce, “Ku zauna a Yeriko har sai gemunku sun yi girma, sa’an nan ku dawo.” Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba. Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi. Da jin haka, Dawuda ya aiki Yowab tare da dukan mayaƙa masu yaƙi. Ammonawa suka fito suka ja dāgā a ƙofar birninsu, yayinda sarakunan da suka zo, su kansu suka ware suna a fili. Yowab ya ga cewa akwai dāgā a gabansa da bayansa; sai ya zaɓi waɗansu mayaƙa mafi kyau a Isra’ila ya sa su a kan Arameyawa. Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin kulawar Abishai ɗan’uwansa, aka sa a kan Ammonawa. Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ni ƙarfi, sai ka kawo mini ɗauke da ni; amma in Ammonawa sun fi ka ƙarfi, sai in kawo maka ɗauke. Ka yi ƙarfin hali bari mu yi yaƙi da jaruntaka saboda mutanenmu da biranen Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da ya ga ya yi masa kyau.” Sai Yowab da ƙungiyoyin mayaƙan da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Arameyawa, Arameyawan kuwa suka gudu a gabansa. Sa’ad da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka guda a gaban ɗan’uwansa Abishai suka shiga cikin birni. Sai Yowab ya koma Urushalima. Bayan Arameyawa suka ga cewa Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka aiki ’yan aika suka sa aka kawo Arameyawan da suke hayen Kogi waɗanda Shobak shugaban mayaƙan Hadadezer yake shugabanta. Sa’ad da aka faɗa wa Dawuda wannan, sai tattara dukan Isra’ila ya haye Urdun; ya tafi wurinsu ya kuwa ja dāgā ɗaura da su. Dawuda ya ja dāgārsa don yă sadu da Arameyawa a yaƙi, su kuwa suka yi yaƙi da shi. Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, mutanen Dawuda kuwa suka kashe masu hawan keken yaƙinsu dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya kuma kashe Shobak shugaban mayaƙansu. Da abokan tarayyar Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka nemi salama da Dawuda suka kuma zama bayinsa. Saboda haka Arameyawa ba su ƙara yarda su taimaki Ammonawa ba. An ci Rabba (2 Sama’ila 11.1; 12.26-31) Da bazara, a lokacin da sarakuna kan tafi yaƙi, Yowab ya jagorance mayaƙa. Ya lalatar da ƙasar Ammonawa ya kuma tafi Rabba ya yi mata kwanto, amma Dawuda ya zauna a Urushalima. Yowab ya yaƙi Rabba, ya kuma bar ta kango. Dawuda ya ɗauki rawani daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti na zinariya, aka kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, sai Dawuda kuwa ya sa a kansa. Ya kuma kwashi ganima mai yawa daga birnin ya kuma fitar da mutanen da suke can, ya sa su aiki da zartuna da makamai masu kaifi da kuma gatura. Dawuda ya yi haka da dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da mayaƙansa gaba ɗaya suka koma Urushalima. Yaƙi da Filistiyawa (2 Sama’ila 21.15-22) Ana nan, sai yaƙi ya ɓarke a Gezer tsakanin Isra’ila da Filistiyawa. Sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin zuriyar Refahiyawa, ta haka kuma aka ci Filistiyawa da yaƙi. Yaƙi kuma ya sāke tashi tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, Elhanan ɗan Yayir ya kashe Lahmi ɗan’uwan Goliyat mutumin Gat, wanda yake riƙe da māshi mai sandan masaƙa. Aka sāke yin wani yaƙin kuma, wanda ya faru a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu da kuma yatsotsi shida a kowace ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriyar Rafa ce. Sa’ad da ya yi wa Isra’ila ba’a, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda ya kashe shi. Waɗannan su ne zuriyar Rafa a Gat, Dawuda da mutanensa sun kashe su. Dawuda ya ƙidaya mayaƙansa (2 Sama’ila 24.1-9) Sai Shaiɗan ya tashi gāba da Isra’ila, ya zuga Dawuda ya ƙidaya Isra’ila. Saboda haka Dawuda ya ce wa Yowab da shugabannin mayaƙa, “Ku tafi ku ƙidaya Isra’ilawa daga Beyersheba zuwa Dan. Ku kawo mini labarin saboda in san su nawa ne.” Amma Yowab ya amsa ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya mayaƙansa fiye da sau ɗari. Ranka yă daɗe sarki, dukansu ba bayin shugabana ba ne? Me ya sa ranka yă daɗe yake so yă yi haka? Me zai sa ka kawo laifi a kan Isra’ila?” Amma sarki ya nace a kan maganar da ya yi wa Yowab. Sai Yowab ya tashi ya tafi cikin dukan Isra’ila, ya kewaye sa’an nan ya dawo Urushalima. Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda. Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba. (2 Sama’ila 24.10-17) Wannan umarnin mugu ne a gaban Allah; saboda haka ya hukunta Isra’ila. Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai ta wurin yin wannan. Yanzu, na roƙe ka, ka ɗauke laifin bawanka. Na yi wauta sosai.” Sai Ubangiji ya ce wa Gad, mai duba na Dawuda, “Tafi ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina ba ka abubuwa uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata a kanka.’ ” Saboda haka Gad ya tafi wurin Dawuda ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka yi zaɓi, shekara uku na yunwa, wata uku na shan ɗibga a gaban abokan gābanka, sa’ad da za su bi suna kakkashe ku, ko kuwa kwana uku na takobin Ubangiji, ranakun annoba a cikin ƙasar, mala’ikan Ubangiji zai hallaka kowane sashe na Isra’ila.’ Yanzu sai ka yanke shawara yadda zan amsa wa wanda ya aiko ni.” Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Bari in fāɗa a hannuwan Ubangiji, gama jinƙansa yana da girma sosai; amma kada ka bari in fāɗa a hannuwan mutane.” Sai Ubangiji ya aiko da annoba a kan Isra’ila, mutane duba saba’in na Isra’ila suka mutu. Allah kuwa ya aiki mala’ika yă hallaka Urushalima. Amma yayinda mala’ikan yana gab da yin haka, sai Ubangiji ya gani ya kuma yi nadama saboda masifar, sai ya ce wa mala’ikan wanda yake hallaka mutane, “Ya isa! Janye hannunka.” Mala’ikan Ubangiji kuwa yana tsaye a masussukar Ornan mutumin Yebus. Sai Dawuda ya ɗaga ido ya ga mala’ikan Ubangiji tsaye tsakanin sama da duniya, da takobi a zāre a hannunsa ya miƙa a kan Urushalima. Sai Dawuda da dattawa, saye da rigunan makoki suka fāɗi rubda jiki. Dawuda ya ce wa Allah, “Ba ni ba ne na umarta a ƙidaya mayaƙan? Ni ne wanda ya yi zunubin da kuma abin da ba daidai ba. Waɗannan dai tumaki ne. Me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, bari hannunka ya fāɗi a kaina da kuma iyalina, amma kada ka bar wannan annoba ya kasance a kan mutanenka.” (2 Sama’ila 24.18-25) Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya umarci Gad yă faɗa wa Dawuda yă haura yă gina bagade wa Ubangiji a masussukar Ornan mutumin Yebus. Saboda haka Dawuda ya haura cikin biyayya ga maganar da Allah ya yi da sunan Ubangiji. Yayinda Ornan yake sussukar alkama, sai ya juya ya ga mala’ika; ’ya’yansa maza guda huɗu da suke tare da shi suka ɓuya. Sai Dawuda ya kusato, sa’ad da Ornan ya duba sai ya gan shi, ya bar masussukar ya rusuna a gaban Dawuda da fuskarsa har ƙasa. Dawuda ya ce wa Ornan, “Ka ba ni masussukarka saboda in gina bagade wa Ubangiji, don annobar da take kan mutane tă daina. Ka sayar mini ita a cikakken kuɗinta.” Ornan ya ce wa Dawuda, “Ka karɓa! Bari ranka yă daɗe, sarki yă yi duk abin da ya ga ya yi masa kyau. Duba, zan ba da shanu domin hadaya ta ƙonawa, da itacen sussuka, da kuma alkama domin hadaya ta gari. Zan ba da dukan wannan.” Amma Sarki Dawuda ya amsa wa Ornan ya ce, “A’a, na nace zan biya cikakken kuɗinta. Ba zan karɓi abinka kawai don Ubangiji ba, ko in miƙa hadaya ta ƙonawar da ba tă ci mini wani abu ba.” Saboda haka Dawuda ya biya Ornan shekel ɗari shida na zinariya saboda wurin. Dawuda ya gina bagade wa Ubangiji a can ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wuta daga sama a kan bagaden hadaya ta ƙonawa. Sa’an nan Ubangiji ya yi magana ga mala’ikan, ya kuma mayar da takobinsa a kube. A lokacin, sa’ad da Dawuda ya ga cewa Ubangiji ya amsa masa a masussukar Ornan mutumin Yebus, sai ya miƙa hadayu a can. Tabanakul na Ubangiji da Musa ya yi a hamada, da kuma bagaden hadaya ta ƙonawa a lokacin suna a tudun Gibeyon. Amma Dawuda bai iya zuwa gabansa don yă yi tambaya ga Allah ba, gama yana jin tsoron takobin mala’ikan Ubangiji. Sai Dawuda ya ce, “Gidan Ubangiji Allah zai kasance a nan, haka kuma bagaden hadaya ta ƙonawa don Isra’ila.” Shirye-shirye don haikali Dawuda kuwa ya umarta a tattara baƙin da suke zama a Isra’ila, daga cikinsu ya sa masu farfasa duwatsu don su shirya duwatsun da aka sassaƙa saboda ginin gidan Allah. Ya tanada ƙarfe mai yawa don ƙusoshi saboda ƙyamaren hanyoyin shiga da kuma saboda mahaɗai, da ƙarin tagulla fiye da ƙirge. Ya kuma tanada gumaguman al’ul masu yawa fiye da ƙirge, gama Sidoniyawa da mutanen Taya sun kawo su wa Dawuda da yawa. Dawuda ya ce, “Ɗana Solomon matashi ne kuma bai gogu ba, kuma gidan da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, sananne da kuma mai daraja a idon dukan al’ummai. Saboda haka zan yi shirye-shirye saboda shi.” Sai Dawuda ya yi ɗumbun shirye-shirye kafin mutuwarsa. Sa’an nan ya kira ɗansa Solomon ya umarce shi yă gina gida domin Ubangiji, Allah na Isra’ila. Dawuda ya ce wa Solomon, “Ɗana, na yi niyya a zuciyata in gina gida saboda Sunan Ubangiji Allahna. Amma wannan maganar Ubangiji ta zo mini, ‘Ka zub da jini mai yawa ka kuma yi yaƙe-yaƙe masu yawa. Ba za ka gina gida domin Sunana ba, domin ka zub da jini da yawa a duniya a idona. Amma za ka haifi ɗa wanda zai zama mutumin salama da kuma hutu, zan kuma ba shi hutu daga dukan abokan gābansa a kowane gefe. Za a kira shi Solomon, zai kuma kawo wa Isra’ila salama da natsuwa a zamanin mulkinsa. Shi ne wanda zai gina gida saboda Sunana. Zai zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan kafa kujerar sarautarsa a bisa Isra’ila har abada.’ “Yanzu, ɗana, Ubangiji ya kasance tare da kai, bari kuma ka yi nasara ka kuma gina gidan Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya ce za ka yi. Bari Ubangiji ya ba ka basira da fahimi sa’ad da ya sa ka shugaba a bisa Isra’ila, saboda ka kiyaye dokar Ubangiji Allahnka. Ta haka za ka yi nasara in ka mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa saboda Isra’ila. Ka yi ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya. “Na sha wahala da yawa don in yi tanadi talentin dubu ɗari na zinariya, talenti miliyon na azurfa, ɗumbun tagulla da ƙarfe da suka wuce ƙirge da katako da dutse saboda haikalin Ubangiji. Za ka iya ƙara su. Kana da ma’aikata masu yawa, masu fafarshe duwatsu, masu gini da masu aikin katako, da kuma gwanaye a kowane irin aikin zinariya da azurfa, tagulla da ƙarfe, masu sana’a waɗanda suka wuce ƙirge. Yanzu ka fara aiki, Ubangiji kuma ya kasance tare da kai.” Sai Dawuda ya umarta dukan shugabannin Isra’ila su taimake ɗansa Solomon. Ya ce musu, “Ba Ubangiji Allahnku yana tare da ku ba? Bai kuma ba ku hutu a kowane gefe ba? Gama ya ba da mazaunan ƙasar gare ni, ƙasar kuma ta Ubangiji ce da mutanensa. Yanzu fa sai ku sa zuciyarku da ranku ga neman Ubangiji Allahnku. Ku fara ginin wuri mai tsarki na Ubangiji Allah, don ku kawo akwatin alkawarin Ubangiji da kayayyaki masu tsarki na Allah a cikin haikalin da za a gina saboda Sunan Ubangiji.” Lawiyawa Sa’ad da Dawuda ya tsufa yana kuma da cikakken shekaru, ya sa ɗansa Solomon sarki bisa Isra’ila. Ya kuma tattara dukan shugabannin Isra’ila a wuri ɗaya, haka kuma ya yi da firistoci da Lawiyawa. Aka ƙidaya Lawiyawan da suke ’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas. Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai. Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.” Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga ’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari. Gershon Na Gershonawa, Ladan da Shimeyi. ’Ya’yan Ladan maza su ne, Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka. ’Ya’yan Shimeyi maza su ne, Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka. Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan. ’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne, Yahat, Zina, Yewush da Beriya. Waɗannan su ne ’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka. Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi ’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki. Kohatawa ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka. ’Ya’yan Amram maza su ne, Haruna da Musa. Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada. An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi. ’Ya’yan Musa maza su ne, Gershom da Eliyezer. Zuriyar Gershom su ne, Shebuwel ne ɗan fari. Zuriyar Eliyezer su ne, Rehabiya ne ɗan fari. Eliyezer ba shi da waɗansu ’ya’ya maza, amma ’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa. ’Ya’yan Izhar maza su ne, Shelomit ne ɗan fari. ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu. ’Ya’yan Uzziyel maza su ne, Mika na fari da Isshiya na biyu. Merariyawa ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. ’Ya’yan Mali maza su ne, Eleyazar da Kish. Eleyazar ya mutu ba ’ya’yan maza, yana da ’ya’ya mata ne kawai. ’Yan’uwansu, ’ya’yan Kish maza, suka aure su. ’Ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka. Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji. Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada, Lawiyawa ba sa ƙara bukata su ɗauki tabanakul ko kuwa waɗansu kayayyakin da ake amfani da su a hidima.” Bisa ga umarnin ƙarshe na Dawuda, za a ƙidaya Lawiyawa daga ’yan shekara ashirin ko fiye. Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah. Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa. Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu. A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin ’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji. Sassan firistoci Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza. ’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar. Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci. Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima. Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar. Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar. Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar. Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib, na biyu a kan Yedahiya, na uku a kan Harim, na huɗu a kan Seyorim, na biyar a kan Malkiya, na shida a kan Miyamin, na bakwai a kan Hakkoz, na takwas a kan Abiya, na tara a kan Yeshuwa, na goma a kan Shekaniya, na goma sha ɗaya a kan Eliyashib, na goma sha biyu a kan Yakim, na goma sha uku a kan Huffa, na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab, na goma sha biyar a kan Bilga, na goma sha shida a kan Immer, na goma sha shida a kan Hezir, na goma sha takwas a kan Haffizzez, na goma sha tara a kan Fetahahiya, na ashirin a kan Ezekiyel, na ashirin da ɗaya wa Yakin, na ashirin da biyu a kan Gamul, na ashirin da uku wa Delahiya da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya. Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi. Sauran Lawiyawa Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya. Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari. Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat. ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu. Ɗan Uzziyel shi ne, Mika; daga ’ya’yan Mika maza, Shamir. Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya. ’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi. Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno. ’Ya’yan Merari su ne, daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri. Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza. Daga Kish, ɗan Kish shi ne, Yerameyel. Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu. Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane. Mawaƙa Dawuda tare da shugabannin mayaƙa, suka keɓe waɗansu daga ’ya’yan Asaf, Heman da Yedutun don hidimar yin annabci, suna amfani da garayu, molaye da ganguna. Ga jerin mutanen da suka yi wannan hidima. Daga ’ya’yan Asaf, Zakkur, Yusuf, Netaniya da Asarela. ’Ya’yan Asaf sun kasance a ƙarƙashin kulawar Asaf, wanda ya yi annabci a ƙarƙashin kulawar sarki. Game da Yedutun kuwa, daga ’ya’yansa maza. Gedaliya, Zeri, Yeshahiya, Shimeyi, Hashabiya da Mattitiya, su shida ne duka, a ƙarƙashin kulawar mahaifinsu Yedutun, wanda ya yi annabci, yana amfani da garaya a yin godiya da yabon Ubangiji. Game da Heman kuwa, daga ’ya’yansa maza. Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot; Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da Mahaziyot. Dukan waɗannan ’ya’yan Heman ne mai duba na sarki. An ba shi su ta wurin alkawarin Allah don yă ɗaukaka shi. Allah ya ba Heman ’ya’ya maza goma sha huɗu da ’ya’ya mata uku. Dukan waɗannan mutane suna a ƙarƙashin kulawar mahaifansu don kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a cikin haikalin Ubangiji, da ganguna, molaye da garayu, don hidima a gidan Allah. Asaf, Yedutun da Heman suna ƙarƙashin kulawar sarki. Da su da danginsu, dukansu su 288 ne kuma horarru da ƙwararru ne a kaɗe-kaɗe da bushe-bushe domin Ubangiji. Baba ko yaro, malami ko ɗalibi, duk suka jefa ƙuri’a saboda ayyukan da za su yi. Ƙuri’a ta fari, wadda take don Asaf, ta fāɗo a kan Yusuf, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta biyu a kan Gedaliya, danginsa da ’ya’yansa maza, 12 ta uku a kan Zakkur, ’ya’yansa da danginsa, 12 ta huɗu a kan Izri, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta biyar a kan Netaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta shida a kan Bukkiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta bakwai a kan Yesarela, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta takwas a kan Yeshahiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta tara a kan Mattaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma a kan Shimeyi, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha ɗaya a kan Azarel, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha biyu a kan Hashabiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha uku a kan Shubayel, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha huɗu a kan Mattitiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha biya a kan Yeremot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha shida a kan Hananiya, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha bakwai a kan Yoshbekasha, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta goma sha takwas a kan Hanani, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa 12 ta goma sha tara a kan Malloti, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin a kan Eliyata, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin da ɗaya a kan Hotir, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin da biyu a kan Giddalti, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin da uku a kan Mahaziyot, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta ashirin da huɗu a kan Romamti-Ezer, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa 12. Matsaran ƙofofi Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne, Daga Korayawa, Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin ’ya’yan Asaf maza. Meshelemiya yana da ’ya’ya maza. Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu, Elam na biyar, Yehohanan na shida da Eliyehoyenai na bakwai. Obed-Edom shi ma yana da ’ya’ya maza. Shemahiya ɗan fari, Yehozabad na biyu, Yowa na uku, Sakar na huɗu Netanel na biyar, Ammiyel na shida, Issakar na bakwai da Feyuletai na takwas. (Gama Allah ya albarkace Obed-Edom.) Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da ’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai. ’Ya’yan Shemahiya maza su ne, Otni, Rafayel, Obed da Elzabad; danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne. Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da ’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka. Meshelemiya yana da ’ya’ya maza da kuma ’yan’uwa, waɗanda jarumawa ne, su 18 ne duka. Hosa dangin Merari yana da ’ya’ya maza. Shimri na fari (ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, mahaifinsa ya sa shi na fari), Hilkiya ne na biyu, Tabaliya ne na uku sai kuma Zakariya na huɗu. ’Ya’ya da dangin Hosa su 13 ne duka. Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi. Aka jefa ƙuri’u don kowace ƙofa bisa ga iyalansu, ƙarami da babba. Ƙuri’a don Ƙofar Gabas ta fāɗo a kan Shelemiya. Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa. Ƙuri’a don Ƙofar Kudu ta fāɗo a kan Obed-Edom, ƙuri’a don ɗakin ajiya kuwa ta fāɗo a kan ’ya’yansa maza. Ƙuri’u don Ƙofar Yamma da kuma Ƙofar Shalleket a hanyar bisa suka fāɗo a kan Shuffim da Hosa. Aikin tsaro bisa ga mai tsaro. Akwai Lawiyawa shida da suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu-biyu suke tsaron ɗakunan ajiya. Game da filin waje ta yamma kuwa, akwai masu tsaro huɗu a hanya da kuma biyu a filin26.18 Ma’anar wannan a Ibraniyanci babu tabbas. kansa. Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari. Masu ajiya da sauran manyan ma’aikata ’Yan’uwansu Lawiyawa kuwa su ne26.20 Seftuwajin; Ibraniyanci Game da Lawiyawa kuwa, Ahiya ne suke lura da ma’ajin gidan Allah da kuma baitulmali don kayayyakin da aka keɓe. Ladan ɗan Gershon ne, kuma kaka ga iyalai masu yawa, har ma da iyalin ɗansa Yehiyeli, ’ya’yan Yehiyeli maza su ne, Zetam da ɗan’uwansa Yowel. Su ne suke kula da ma’ajin haikalin Ubangiji. Daga zuriyar Amram, Izhar, mutanen Hebron da kuma Uzziyel, su ma aka ba su aiki. Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami’i mai lura da baitulmali. Danginsa na wajen Eliyezer su ne, Rehabiya, Yeshahiya, Yoram, Zikri da Shelomit. Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa. Sun keɓe waɗansu ganimar da aka kwaso a yaƙi don gyaran haikalin Ubangiji. Shelomit da ’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe. Daga mutanen Izhar, Kenaniya da ’ya’yansa maza su aka sa a ayyukan da ba na haikali ba, su suka zama manya da kuma alƙalai a bisa Isra’ila. Daga zuriyar Hebron, Hashabiya da danginsa, su jarumawa dubu ɗaya da ɗari bakwai ne, su suke lura da Isra’ila yamma da Urdun don dukan aikin Ubangiji da kuma hidimar sarki. Game da zuriyar Hebron kuwa, Yeriya ne babba bisa ga tarihin zuriyar iyalansu. A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka yi binciken tarihi, aka tarar jarumawa cikin zuriyar Hebron suna zama a Yazer cikin Gileyad ne. Yeriya yana da ’yan’uwa guda dubu biyu da ɗari bakwai, jarumawa da kuma kawunan iyalai, sai Sarki Dawuda ya sa su lura da mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse game da kome da ya shafi Allah da kuma al’amuran sarki. Ɓangarorin mayaƙa Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000. Wanda yake lura da sashe na fari, na wata na farko, shi ne Yashobeyam ɗan Zabdiyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Shi zuriyar Ferez ne kuma babba na dukan shugabannin mayaƙa don wata na farko. Wanda yake lura da sashen don wata na biyu shi ne Dodai mutumin Ahowa; Miklot ne shugaban sashensa. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist. Shi ne babba kuma akwai mutane 24,000 a sashensa. Wannan shi ne Benahiya wanda yake ɗaya daga cikin jarumawa Talatin nan kuma shi ne yake babba a cikin Talatin ɗin. Ɗansa Ammizabad ne yake lura da sashensa. Na huɗu, don wata na huɗu, shi ne Asahel ɗan’uwan Yowab; ɗansa Zebadiya shi ne magājinsa. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na biyar don wata na biyar, shi ne Shamhut mutumin Izhar shugaban mayaƙa. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na shida, don wata na shida, shi ne Ira ɗan Ikkesh mutumin Tekowa. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na Bakwai, don wata na bakwai, shi ne Helez mutumin Felon, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na takwas, don wata na takwas, shi ne Sibbekai mutumin Husha, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na tara, don wata na tara, shi ne Abiyezer mutumin Anatot, mutumin Benyamin. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na goma, don wata na goma, shi ne Maharai mutumin Netofa, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na goma sha ɗaya, don wata goma sha ɗaya, shi ne Benahiya mutumin Firaton, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Na goma sha biyu don wata goma sha biyu, shi ne Heldai mutumin Netofa, daga iyalin Otniyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa. Manyan shugabannin Kabilu Shugabannin da suke bisa kabilan Isra’ila, bisa mutanen Ruben su ne, Eliyezer ɗan Zikri; bisa mutanen Simeyon shi ne, Shefatiya ɗan Ma’aka bisa mutanen Lawi shi ne, Hashabiya ɗan Kemuwel; bisa mutanen Haruna shi ne, Zadok; bisa mutanen Yahuda shi ne, Elihu, ɗan’uwan Dawuda; bisa mutanen Issakar shi ne, Omri ɗan Mika’ilu; bisa mutanen Zebulun shi ne, Ishmahiya ɗan Obadiya; bisa mutanen Naftali shi ne, Yerimot ɗan Azriyel; bisa mutanen Efraim shi ne, Hosheya ɗan Azaziya; bisa rabin kabilar Manasse shi ne, Yowel ɗan Fedahiya; bisa ɗayan rabi kabilar Manasse a Gileyad shi ne, Iddo ɗan Zakariya; bisa mutanen Benyamin shi ne, Ya’asiyel ɗan Abner; bisa mutanen Dan shi ne, Azarel ɗan Yeroham. Waɗannan su ne shugabanni a bisa kabilan Isra’ila. Dawuda bai ƙirga mutanen da suke ’yan shekara ashirin ko ƙasa ba, domin Ubangiji ya yi alkawari zai sa Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama. Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. Hasala ta sauko a kan Isra’ila saboda wannan ƙirge, ba a kuma shigar da adadin a littafin tarihin Sarki Dawuda ba. Masu lura da kayan sarki Azmawet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ɗakuna ajiyar fada. Yonatan ɗan Uzziya shi ne mai lura da ɗakunan ajiya a yankuna, cikin garuruwa, ƙauyuka da kuma hasumiyoyin tsaro. Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da ma’aikatan gona waɗanda suke nome ƙasar. Shimeyi mutumin Ramat shi ne mai lura da gonakin inabi. Zabdi mutumin Shifam shi ne mai lura da amfanin gonakin inabi don matsin ruwan inabi. Ba’al-Hanan mutumin Geder shi ne mai lura da itatuwan zaitun da na al’ul a gindin tuddan yamma. Yowash shi ne mai lura da tanadin man zaitun. Shitrai mutumin Sharon shi ne mai lura da garkuna masu kiwo a Sharon. Shafat ɗan Adlai shi ne mai lura da garkuna a kwari. Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma. Yedehiya mutumin Meronot shi ne mai lura da jakuna. Yaziz mutumin Hagiri shi ne mai lura da tumaki. Dukan waɗannan shugabanni ne masu lura da mallakar Sarki Dawuda. Yonatan, kawun Dawuda, shi ne mashawarci, mutum mai hangen nesa kuma marubuci. Yehiyel ɗan Hakmoni ne ya lura da ’ya’yan sarki maza. Ahitofel shi ne mashawarcin sarki. Hushai mutumin Arkitawa shi ne abokin sarki na kud da kud. Yehohiyada ɗan Benahiya da Abiyatar ne suka gāji Ahitofel. Yowab shi ne shugaban mayaƙan masarauta. Shirye-shiryen Dawuda don haikali Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini. Sarki Dawuda ya miƙe tsaye ya ce, “Ku saurare ni, ’yan’uwana da kuma mutanena. Na yi niyya in gina gida a matsayin wurin hutu domin akwatin alkawarin Ubangiji, domin zatin Allahnmu, na kuma yi shiri don in gina shi. Amma Allah ya ce mini, ‘Ba za ka gina gida domin Sunana ba, saboda kai mayaƙi ne ka kuma zub da jini.’ “Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga ’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila. Cikin dukan ’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila. Ya ce mini, ‘Solomon ɗanka shi ne wanda zai gina gidana da filayen da suke kewaye da shi, gama na zaɓe shi yă zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan kafa mulkinsa har abada in bai kauce ga kiyaye umarnaina da dokokina ba, yadda ake yi a wannan lokaci.’ “Saboda haka yanzu ina umartanku a gaban dukan Isra’ila da na taron jama’ar Ubangiji, da kuma a kunnuwan Allahnmu. Ku yi hankali ku kiyaye dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa ku kuma bar wa zuriyarku gādo har abada. “Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada. Ka lura fa, gama Ubangiji ya zaɓe ka don ka gina haikali a matsayin wuri mai tsarki. Ka yi ƙarfin hali ka kuma yi aiki.” Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Solomon tsari domin shirayin haikalin, gine-ginensa, ɗakunan ajiyarsa, ɓangarorin bisansa, ɗakunan cikinsa da kuma wurin kafara. Ya ba shi tsarin dukan abin da Ruhu ya sa a zuciyarsa saboda filayen haikalin Ubangiji da ɗakunan kewaye, da ma’ajin haikalin Allah da kuma baitulmali na kayayyakin da aka keɓe. Ya ba shi tsari game ɓangarori na firistoci da Lawiyawa, da game dukan aikin hidima a cikin haikalin Ubangiji, da kuma game da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a hidima. Ya kimanta yawan zinariya don dukan kayayyakin zinariyar da za a yi amfani a kowane irin hidima, da yawan azurfa don dukan kayayyakin azurfan da za a yi amfani a kowace irin hidima. Da yawan zinariya don wurin ajiye fitilan fitilu da fitilunsu, da yawan zinariyan da za a yi amfani don kowace fitila da wurin ajiye fitilanta; da kuma yawan azurfa don kowane wurin ajiye fitila da fitilunsa bisa ga yadda za a yi amfani da kowane wurin ajiye fitila; yawan zinariya don kowane tebur saboda burodi mai tsaki; da kuma yawan azurfa saboda teburin azurfa; yawan zinariya zalla, don cokula masu yatsu, kwanonin yayyafawa ruwa da kuma tuluna; yawan zinariya don kowane kwanon zinariya; yawan azurfa don kowane kwanon azurfa; da kuma yawan tacecciyar zinariya don bagaden turare. Ya kuma ba shi tsari don keken yaƙi, wato, kerubobin zinariyar da suka miƙe fikafikansu suka inuwantar da akwatin alkawarin Ubangiji. Dawuda ya ce, “Dukan wannan, ina da shi a rubuce daga hannun Ubangiji zuwa gare ni, ya kuma ba ni ganewa cikin dukan tsarin fasalin, filla-filla.” Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, “Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya, gama Ubangiji Allah, Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ko yă yashe ka ba, sai an gama dukan aikin saboda hidimar haikalin Ubangiji. Sassan firistoci da na Lawiyawa suna a shirye domin dukan aiki a haikalin Allah, kuma kowane gwani mai niyya a kowace sana’a, zai taimake ka a cikin dukan aikin. Shugabanni da dukan mutane za su yi biyayya da kowane umarninka.” Kyautai don ginin haikali Sa’an nan Sarki Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ɗana Solomon, wanda Allah ya zaɓa, matashi ne, kuma bai gogu ba. Aikin yana da yawa, domin wannan ƙasaitaccen ginin ba na mutum ba ne, na Ubangiji Allah ne. Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim. Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali, talenti dubu uku na zinariya (zinariyar Ofir) da tacecciyar azurfa dubu bakwai; don adon bangon gine-ginen, don aikin zinariya da kuma aikin azurfa, don kuma dukan aikin da gwanaye za su yi. Yanzu fa wa yake da niyya yă miƙa kansa a yau don Ubangiji?” Sai shugabannin iyalai, shugabannin kabilan Isra’ila, manyan hafsoshin mayaƙa dubu-dubu da manyan hafsoshi mayaƙa ɗari-ɗari, da shugabannin lura da ayyukan sarki suka yi bayarwa da yardar rai. Suka bayar talenti dubu biyar na zinariya, talenti dubu goma na azurfa, talenti dubu goma sha takwas na tagulla da talenti dubu ɗari na ƙarfe don aiki a haikalin Allah. Duk waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka ba da su ga Yehiyel mutumin Gershon ma’ajin haikalin Ubangiji. Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai. Addu’ar Dawuda Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa, “Yabo gare ka, ya Ubangiji, Allah na mahaifinmu Isra’ila, har abada abadin. Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka. Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka. Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka, muna kuma yabon ɗaukakar sunanka. “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne. Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya. Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne. Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka. Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya. Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.” Sa’an nan Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ku yabi Ubangiji Allahnku.” Saboda haka suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu; suka rusuna suka kuma fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji da kuma sarki. An yarda da Solomon a matsayin sarki Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma ’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila. Suka ci suka sha da farin ciki mai girma a gaban Ubangiji a wannan rana. Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist. Saboda haka Solomon ya zauna a kujerar sarautar Ubangiji a matsayin sarki a maimakon mahaifinsa Dawuda. Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya. Dukan shugabanni da jarumawa, har ma da dukan ’ya’yan Sarki Dawuda maza, suka yi alkawari za su yi wa Sarki Solomon biyayya. Ubangiji ya ɗaukaka Solomon sosai a idon dukan Isra’ila, ya kuma ba shi darajar sarauta yadda babu sarki a Isra’ilan da ya taɓa samu. Mutuwar Dawuda Dawuda ɗan Yesse ya zama sarki a bisa dukan Isra’ila. Ya yi mulki a bisa Isra’ila shekaru arba’in, shekaru bakwai a Hebron da kuma shekaru talatin da uku a Urushalima. Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki. Game da ayyukan mulkin Sarki Dawuda, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin Sama’ila mai duba, tarihin annabi Natan da kuma tarihin Gad mai duba, tare da yadda mulkinsa da ikonsa da yanayin da suka kewaye shi da Isra’ila da kuma dukan masarautai na dukan sauran ƙasashe.