- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Titus Titus Titus Tit Titus Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi, da lokacin da Allah ya zaɓa ya cika sai ya bayyana maganarsa a sarari ta wurin wa’azin da aka danƙa mini amana ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu, Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya. Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu, su kasance tare da kai. Aikin Titus a Kirit Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka. Dole dattijo yă kasance marar aibi, mijin mace guda, mutumin da ’ya’yansa masu bi ne, waɗanda kuma ba a san su da lalata ko rashin biyayya ba. Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse. Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi. Tsawata wa waɗanda suka ƙi yin nagarta Gama akwai ’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya. Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba don neman ƙazamar riba. Wani daga cikin annabawansu ma ya ce, “Kiretawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye haɗamammu.” Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka, sai ka tsawata musu sosai, don su zama sahihai a wajen bangaskiya, ba za su kuma mai da hankalinsu ga tatsuniyoyin Yahudawa ko ga umarnan waɗanda suke ƙin gaskiya ba. Ga tsarkaka kuwa, kome mai tsarki ne, amma ga waɗanda suke marasa tsarki da kuma marasa ba da gaskiya, ba abin da yake da tsarki. Gaskiya dai, hankulansu da lamirinsu duk marasa tsarki ne. Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba. Abin da ya kamata a koyarwa wa ƙungiyoyi dabam-dabam Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri. Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah. Haka kuma, ka ƙarfafa samari su zama masu kamunkai. Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu. Ka koya wa bayi su yi wa iyayengijinsu biyayya cikin kowane abu, su yi ƙoƙari su gamshe su, kada su mayar musu da magana, kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali. Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi, wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari. Waɗannan kam, su ne abubuwan da ya kamata ka koyar, ka ƙarfafa ka kuma tsawata da dukan iko. Kada ka yarda wani yă rena ka. Yin abin da yake mai kyau Ka tuna wa mutane su zama masu biyayya ga masu mulki da kuma hukumomi, su zama masu biyayya suna kuma a shirye su yi kowane abin da yake mai kyau, kada su zama masu ɓata sunan kowa, su zama masu salama da kulawa, su kuma zama masu matuƙar tawali’u ga dukan mutane. A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna. Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana, sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki, wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu, wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami. Wannan magana tabbatacciya ce, ina kuma so ka nanata waɗannan abubuwa ƙwarai, domin waɗanda suka dogara ga Allah su himmantu ga aiki mai kyau. Waɗannan abubuwa suna da kyau sosai suna kuma da amfani ga kowane mutum. Amma ka guji jayayyar banza da ƙididdigar asali da gardandami da faɗace-faɗace game da Doka, gama ba su da riba kuma aikin banza ne. Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi. Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci. Maganar ƙarshe Da zarar na aika Artemas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina a Nikofolis, domin na yanke shawara in ci damina a can. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan da Afollos a hanyarsu ka kuma tabbata ba su rasa kome ba. Dole mutanenmu su koyi ba da kansu ga aikata abin da yake nagari, domin su iya biyan bukatunsu na yau da kullum kada kuma su yi rayuwar marar amfani. Dukan waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gaggai mini da masoyanmu, masu bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku duka.