- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Yohanna
Yohanna
Yohanna
Yoh
Yohanna
Kalman ya zama mutum
Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. Yana nan tare da Allah tun farar farawa. Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi. A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.
Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna. Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya. Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken.
Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya.1.9 Ko kuwa Wannan ne haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutumin da yake shigowa duniya Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba. Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam,1.13 Girik na jini ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.
Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.
(Yohanna ya ba da shaida game da shi. Ya ɗaga murya yana cewa, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya fi ni girma domin yana nan kafin ni.’ ”) Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka. Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi. Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi.
Yohanna Mai Baftisma ya ce ba shi ne Kiristi ba
To, ga shaidar Yohanna sa’ad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne. Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.”
Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?”
Ya ce, “A’a, ni ba shi ba ne.”
“Kai ne Annabin nan?”
Ya amsa ya ce, “A’a.”
A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?”
Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ”1.23 Ish 40.3
To, waɗansu Farisiyawan da aka aika suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”
Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba. Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”
Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma.
Yesu Ɗan Rago na Allah
Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya! Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’ Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.”
Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa. Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”
Almajiran Yesu na farko
Kashegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa. Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”
Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu. Da juyewa, sai Yesu ya ga suna bin sa, sai ya tambaye, su ya ce, “Me kuke nema?”
Suka ce, “Rabbi” (wato, “Malam”), “ina kake da zama?”
Ya amsa musu ya ce, “Ku zo, za ku kuma gani.”
Saboda haka suka je suka ga inda yake da zama, suka kuma zauna a can tare da shi. Wajen sa’a ta goma ce kuwa.
Andarawus ɗan’uwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun nan da suka bi Yesu bayan da suka ji maganar Yohanna a kan Yesu. Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗan’uwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi). Ya kuma kawo shi wurin Yesu.
Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan1.42 Da Kefas (Arameyik) da kuma Bitrus (Girik) na nufin dutse.).
Yesu ya kira Filibus da Natanayel
Kashegari Yesu ya yanke shawara yă tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, “Bi ni.”
Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne. Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa, Yesu Banazare, ɗan Yusuf.”
Natanayel ya ce, “A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?”
Filibus ya ce, “Zo ka gani.”
Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, “Ga mutumin Isra’ila na gaske wanda ba shi da ha’inci.”
Natanayel ya yi tambaya ya ce, “A ina ka san ni?”
Yesu ya amsa ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yă kira ka.”
Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Isra’ila.”
Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.” Sai ya ƙara da cewa, “Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, mala’ikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.”
Yesu ya mai da ruwa ya zama ruwan inabi
A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can, aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren. Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”
Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.”
Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.”
Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.
Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.
Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.”
Suka yi haka. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”
Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.
Yesu ya tsabtacce haikali
Bayan wannan sai ya tafi Kafarnahum tare da mahaifiyarsa da ’yan’uwansa da kuma almajiransa. A can suka zauna ’yan kwanaki.
([Mattiyu 21.12],[13]; [Markus 11.15-17]; [Luka 19.45],[46])
Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima. A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi. Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu. Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!” Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.”2.17 Zab 69.9
Sai Yahudawa suka tambaye shi, “Wace abar banmamaki za ka nuna mana ka tabbatar mana ikonka na yin duk waɗannan?”
Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.”
Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?” Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne. Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi.
To, yayinda yake a Urushalima a Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa suka ga abubuwan banmamakin da yake aikata suka kuma gaskata da sunansa. Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane. Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum.
Yesu ya koyar da Nikodimus
Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa. Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”
Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu. Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu. Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’ Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”
Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?”
Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba? Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu. Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama? Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum.3.13 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Mutum, wanda yake cikin sama Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.
Shaidar Yohanna Mai Baftisma a kan Yesu
Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan Yahudiya, inda ya ɗan jima da su, ya kuma yi baftisma. To, Yohanna ma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salim, saboda akwai ruwa da yawa a can, mutane kuwa suka yi ta zuwa don a yi musu baftisma. (Wannan kuwa kafin a sa Yohanna a kurkuku.) Sai gardama ta tashi tsakanin waɗansu almajiran Yohanna da wani mutumin Yahuda3.25 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da da waɗansu Yahudawa a kan zancen al’adar tsarkakewa. Sai suka zo wurin Yohanna suka ce masa, “Rabbi, wancan mutumin da yake tare da kai a ƙetaren Urdun, wannan da ka ba da shaida a kansa sosai nan, yana baftisma, kuma kowa yana zuwa wurinsa.”
Ga wannan zancen Yohanna ya amsa ya ce, “Mutum yakan karɓi kawai abin da aka ba shi ne daga sama. Ku kanku za ku shaida cewa na ce, ‘Ba ni ne Kiristi ba, sai dai an aiko ni ne in sha gabansa.’ Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu. Dole ne yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa.
“Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa; wannan da ya zo daga ƙasa na ƙasa ne, yana kuma magana kamar wanda ya zo daga ƙasa ne. Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa. Yana ba da shaidar abin da ya gani da kuma ya ji, duk da haka ba wanda ya yarda da shaidarsa. Mutumin da ya yarda da ita ya tabbatar da cewa Allah mai gaskiya ne. Gama wannan da Allah ya aiko yakan faɗi kalmomin Allah ne, gama Allah yana ba da Ruhu babu iyaka. Uban yana ƙaunar Ɗan ya kuma danƙa kome a hannuwansa. Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”
Yesu da wata mutuniyar Samariya
Yesu ya ji labari cewa Yahudawa sun ji cewa ya wuce Yohanna samun masu bi, yana kuma yin musu baftisma, ko da yake ba Yesu ne yake baftismar ba, almajiransa ne. Da ya sami wannan labari, sai ya bar Yahudiya ya sāke koma Galili.
To, ya zama dole yă bi ta Samariya. Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf. Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen sa’a ta shida ne.
Sa’ad da wata mutuniyar Samariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha?” (Almajiransa kuwa sun shiga gari don sayi abinci.)
Sai mutuniyar Samariyar ta ce masa, “Kai mutumin Yahuda ne, ni kuwa mutuniyar Samariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa.)
Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, shi kuwa da ya ba ki ruwan rai.”
Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai? Ka fi mahaifinmu Yaƙub ne, wanda ya ba mu rijiyar ya kuma sha daga ciki da kansa, haka ma ’ya’yansa da kuma garkunan shanunsa da tumakinsa?”
Yesu ya amsa ya ce, “Kowa ya sha wannan ruwa, zai sāke jin ƙishirwa, amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”
Sai macen ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, in yi ta zuwa nan ɗiban ruwa.”
Sai ya ce mata, “Je ki zo da mijinki.”
Sai ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.”
Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji. Gaskiyar ita ce, kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.”
Sai macen ta ce, “Ranka yă daɗe, ina gani kai annabi ne. Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan, amma ku Yahudawa kun ce a Urushalima ne ya kamata a yi sujada.”
Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba. Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake. Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.”
Sai Yesu ya ce, “Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.”
Almajirai sun dawo inda suka bar Yesu
Suna gama magana ke nan sai almajiransa suka iso, suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma ba wanda ya ce, “Me kake so?” Ko “Me ya sa kake magana da ita?”
Sai macen ta bar tulunta na ruwa, ta koma cikin gari ta ce wa mutane, “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi. Shin, ko shi ne Kiristi?” Sai suka fita daga garin suka nufa inda yake.
Ana cikin haka, sai almajiransa suka roƙe shi suka ce, “Rabbi, ci abinci mana.”
Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku san kome a kai ba.”
Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?”
Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa. Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku ɗaga idanu ku dubi gonaki! Sun isa girbi. Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’ Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”
Samariyawa da yawa sun ba da gaskiya
Samariyawa da yawa daga wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” To, da Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi yă zauna da su, ya kuwa zauna kwana biyu. Saboda kalmominsa kuwa da yawa suka gaskata.
Sai suka ce wa macen, “Yanzu kam mun gaskata, ba don abin da kika faɗa kawai ba; yanzu mun ji da kanmu, mun kuwa san cewa wannan mutum tabbatacce shi ne Mai Ceton duniya.”
Yesu ya warkar da ɗan mai mulki
([Mattiyu 8.5-13]; [Luka 7.1-10])
Bayan kwana biyun nan sai ya bar can zuwa Galili. (To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa.) Da ya isa Galili, sai mutanen Galili suka marabce shi. Sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin Bikin Ƙetarewa, gama su ma sun kasance a can.
Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.
Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”
Ma’aikacin hukuman ya ce, “Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu.”
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.”
Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi. Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa. Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai.”
Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.
Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili.
Warkarwa a tafki
Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa. To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda5.2 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Betzata; waɗansu kuma suna da Betsaida ne a nan. an kuma kewaye shi da shirayi biyar. A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu.5.3 Waɗansu rubuce-rubucen hannu marar muhimmanci sosai suna da shanyayyu, kuma suka jira a motsa ruwaye. 4 Lokaci-lokaci mala’ikan Ubangiji yakan sauko ya motsa ruwaye. Mutum na farko da ya shiga tafkin bayan motsawa zai warke daga kowace cutar da yake da ita. Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas. Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?”
Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.”
Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.” Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya.
A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce, saboda haka kuwa Yahudawa suka ce wa mutumin da aka warkar, “Yau Asabbaci ne; doka ta hana ka ɗauki tabarmarka.”
Amma ya amsa ya ce, “Mutumin da ya warkar da ni shi ya ce mini, ‘Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’ ”
Sai suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan da ya ce maka ka ɗauke ta ka yi tafiya?”
Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can.
Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.” Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
Rai ta wurin Ɗan
To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa. Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.” Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.
Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi. Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma. Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama. Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan, don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.
“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu. Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa. Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.
“Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci. Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.
Shaidu game da Yesu
“In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce. Akwai wani mai ba da shaida mai kyau a kaina, na kuma san cewa shaidarsa game da ni gaskiya ce.
“Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya. Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto. Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci.
“Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni. Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba, maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba. Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina, duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai.
“Ni ba na neman yabon mutane, na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku. Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi. Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici?
“Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni. Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”
Yesu ya ciyar da dubu biyar
([Mattiyu 14.13-21]; [Markus 6.30-44]; [Luka 9.10-17])
Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya), sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya. Sa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa. Bikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa.
Sa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?” Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.
Sai Filibus ya amsa ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!”
Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana, “Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan.”
Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar. Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace.” Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.
Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.” Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.
Yesu ya yi tafiya a kan ruwa
([Mattiyu 14.22-27]; [Markus 6.45-52])
Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki, inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna. Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka. Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata. Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.” Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.
Kashegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai. Sai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya. Da taron suka lura cewa Yesu da almajiransa ba sa can, sai suka shiga jiragen ruwa suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
Yesu burodin rai
Da suka same shi a wancan ƙetaren tafkin, sai suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, yaushe ka kai nan?”
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi. Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.”
Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?”
Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne, a gaskata da wanda ya aiko.”
Sai suka tambaye shi, “Wace abin banmamaki ce za ka yi don mu gani mu kuwa gaskata ka? Me za ka yi? Kakannin-kakanninmu sun ci Manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce, ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’6.31 Fit 16.4; Neh 9.15; Zab 78.24,25”
Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama. Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”
Sai suka ce, “Ranka yă daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi.”
Sa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba. Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba. Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan. Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni. Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe. Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”
Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.” Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ”
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku. Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’6.45 Ish 54.13 Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina. Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban. Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami. Ni ne burodin rai. Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu. Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba. Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”
Sai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?”
Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa. Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni. Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada.” Ya faɗi wannan ne lokacin da yake koyarwa a cikin majami’a a Kafarnahum.
Almajirai masu yawa sun bar bin Yesu
Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?”
Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne? Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā! Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai. Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi. Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”
Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.
Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”
Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami. Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!” (Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)
Yesu ya tafi Bikin Tabanakul
Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yă je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi. Amma sa’ad da Bikin Tabanakul na Yahudawa ya yi kusa, sai ’yan’uwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi. Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.” Domin ko ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba.
Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne. Duniya ba za tă iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne. Ku ku tafi Bikin, ba zan haura zuwa wannan Bikin ba yanzu, domin lokacina bai yi ba tukuna.” Da ya faɗa haka, sai ya dakata a Galili.
Amma fa, bayan ’yan’uwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye. A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?”
A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.”
Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ai, ruɗin mutane yake.” Amma ba wanda ya ce kome a fili game da shi don tsoron Yahudawa.
Yesu ya koyar a bikin
Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa. Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?”
Yesu ya amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni. Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana. Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi. Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?”
Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yă kashe ka?”
Yesu ya ce musu, “Na yi abin banmamaki ɗaya, dukanku kuwa kuka yi mamaki. Duk da haka, domin Musa ya bar muku kaciya (ko da yake a gaskiya, ba daga wurin Musa ne ya fito ba, sai dai daga wurin kakannin kakanninku), ga shi kuna yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci. To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci? Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci.”
Shin, Yesu shi ne Kiristi?
A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba? Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi? Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma sa’ad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.”
Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “I, kun san ni, kun kuma san inda na fito. Ban zo don kaina ba, sai dai shi da ya aiko ni mai gaskiya ne. Ba ku san shi ba, amma na san shi, domin ni daga wurinsa ne, kuma shi ya aiko ni.”
Da jin haka, sai suka yi ƙoƙari su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna. Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Sa’ad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?”
Farisiyawa suka ji taron suna raɗe-raɗen waɗannan abubuwa game da shi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin haikalin su kama shi.
Sai Yesu ya ce, “Ina tare da ku na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, sa’an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni. Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba; inda nake kuwa, ba za ku iya zuwa ba.”
Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina mutumin nan yake niyyar tafiya da ba za mu iya samunsa ba? Zai je wurin mutanenmu da suke zaune warwatse a cikin Hellenawa, yă kuma koya wa Hellenawa ne? Me yake nufi da ya ce, ‘Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba,’ da kuma ‘Inda nake, ba za ku iya zuwa ba’?”
A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yă zo wurina yă sha. Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.” Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.
Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.”
Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.”
Waɗansu har wa yau suka ce, “Yaya Kiristi zai fito daga Galili? Nassi bai ce Kiristi zai fito daga zuriyar Dawuda, daga kuma Betlehem garin da Dawuda ya zauna ba?” Sai mutanen suka rabu saboda Yesu. Waɗansu suka so su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi.
Rashin bangaskiyar shugabannin Yahudawa
A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?”
Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.”
Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan? Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi? A’a! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba, la’anannu ne.”
Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce, “Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?”
Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.”
[Rubuce-rubucen farko-farko da kuma mafi ingancin da aka fi dogara da su tare da waɗansu shaidu na dā ba su da Yoh 7.53–8.11. Kaɗan daga cikin rubuce-rubucen hannu na dā sun ƙunshi waɗannan ayoyi, ko gaba ɗayansu ko kuma sashensu kawai bayan Yoh 7.36, Yoh 21.25, Luk 21.38 ko kuwa Luk 24.53.]
Sai kowannensu ya koma gidansa.
Amma Yesu ya tafi Dutsen Zaitun.
Da sassafe ya sāke bayyana a filin haikali, inda dukan mutane suka taru kewaye da shi, sai ya zauna don yă koya musu. Sai malaman dokoki da Farisiyawa suka kawo wata macen da aka kama a zina. Suka sa ta tsaya a gaban taron suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina. A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?” Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi.
Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa. Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, “In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse.” Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa.
Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin. Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, “Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”
Ta ce, “Ba kowa, ranka yă daɗe.”
Sai Yesu ya ce, “Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.”
Gaskiyar shaidar Yesu
Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”
Sai Farisiyawa suka tambaye shi suka ce, “Ga kai dai, kana yi wa kanka shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.”
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, gama na san inda na fito da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ko inda za ni ba. Kuna shari’a bisa ga ma’aunin mutane; ni kuwa ba na yin wa kowa shari’a. Amma ko da zan yi shari’a, shari’ata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni. A cikin Dokarku a rubuce yake cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce. Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”
Suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka?”
Sai Yesu ya ce, “Ba ku san ni ko Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.” Ya faɗi waɗannan kalmomi ne yayinda yake koyarwa a filin haikali, kusa da inda ake ajiye baye-baye. Duk da haka ba wanda ya kama shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.
Har wa yau Yesu ya sāke ce musu, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba.”
Wannan ya sa Yahudawa suka yi tambaya suka ce, “Zai kashe kansa ne? Shi ya sa yake cewa, ‘Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba’?”
Amma ya ci gaba da cewa, “Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa daga bisa ne. Ku na duniyan nan ne; ni kuwa ba na duniyan nan ba ne. Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”
Suka ce, “Wane ne kai?”
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne wannan da na sha faɗi muku. Ina da abubuwa masu yawa da zan faɗa game ku in kuma yi muku shari’a. Amma wanda ya aiko ni mai aminci ne, abin da kuma na ji daga gare shi, shi nake gaya wa duniya.”
Ba su gane cewa yana yin musu magana game da Ubansa ba ne. Saboda haka Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini. Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.” Sa’ad da yake cikin magana, da yawa suka ba da gaskiya gare shi.
’Ya’yan Ibrahim
Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske. Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”
Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?”
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne. Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada. Saboda haka in Ɗan ya ’yantar da ku, za ku ’yantu da gaske. Na dai san ku zuriyar Ibrahim ne. Duk da haka kuna shiri ku kashe ni, don maganata ba ta da wurin zama a cikinku. Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.”
Suka ce, “To, ai, Ibrahim ne mahaifinmu.”
Yesu ya ce, “Da ku ’ya’yan Ibrahim ne, da za ku aikata abubuwan da Ibrahim ya yi. Ga shi kun ƙudura, sai kun kashe ni, ni mutumin da ya faɗa muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi irin waɗannan abubuwa ba. Kuna yin abubuwan da ubanku yake yi ne.”
Suka ce, “Mu fa ba shegu ba ne. Uba guda kaɗai da muke da shi, shi ne Allah kansa.”
’Ya’yan Iblis
Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni. Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi. Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata! Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni? Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”
Shaidar Yesu game da kansa
Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Aha, ai, gaskiyarmu da muka ce kai mutumin Samariya ne, kana kuma da aljani.”
Yesu ya ce, “Ni ba mai aljani ba ne, ni dai ina girmama Ubana, ku kuwa ba kwa girmama ni. Ba na nema wa kaina ɗaukaka, amma akwai wani wanda yake neman mini, shi ne kuma alƙali. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.”
Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam. Ka fi Ibrahim mahaifinmu ne? Ya mutu, haka ma annabawa. Wa kake ɗauka kanka ne?”
Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni. Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamar ku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa. Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yă sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.”
Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin tukuna ba fa, har ka ga Ibrahim!”
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!” Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali.
Yesu ya warkar da mutumin da aka haifa makaho
Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?”
Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa. Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki. Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”
Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin. Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.
Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Kai, ba wannan mutum ne ya saba zama yana bara ba?” Waɗansu suka ce shi mana.
Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ya dai yi kama da shi.”
Amma shi ɗin ya ce, “Ƙwarai kuwa ni ne.”
Sai suka ce, “To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?”
Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.”
Suka tambaye shi suka ce, “Ina mutumin yake?”
Ya ce, “Ban sani ba.”
Farisiyawa sun bincike warkarwar
Sai suka kawo mutumin da dā yake makaho wurin Farisiyawa. To, a ranar da Yesu ya kwaɓa laka ya buɗe idanun mutumin ranar Asabbaci ce. Saboda haka Farisiyawa suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Mutumin ya amsa, “Ya shafa laka a idanuna, sai na wanke, ina kuwa gani.”
Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.”
Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai ra’ayinsu ya sha bamban.
A ƙarshe suka sāke koma ga makahon suka ce, “Kai fa, me ka gani game da shi? Idanunka ne fa ya buɗe.”
Sai mutumin ya ce, “Tab, ai, shi annabi ne.”
Yahudawa dai ba su yarda cewa dā shi makaho ne ya kuma sami ganin gari ba, sai da suka kira iyayen mutumin. Suka tambaye su, “Wannan ɗanku ne? Shi ne wanda kuka ce an haife shi makaho? To, ta yaya yake gani yanzu?”
Iyayen suka amsa suka ce, “Mun dai san shi ɗanmu ne, mun kuma san cewa an haife shi makaho. Sai dai yadda yake gani yanzu, ko kuma wa ya buɗe idanunsa, ba mu sani ba. Ku tambaye shi. Ai, shi ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.” Iyayensa sun faɗa haka ne saboda suna tsoron Yahudawa, gama Yahudawa sun riga sun yanke shawara cewa duk wanda ya yarda cewa Yesu shi ne Kiristi, za a kore shi daga majami’a. Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”
Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka ɗaukaka Allah, mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”
Sai ya amsa ya ce, “Ko shi mai zunubi ne ko babu, ni dai ban sani ba. Abu ɗaya fa na sani, dā ni makaho ne, amma yanzu ina gani!”
Sai suka tambaye suka ce, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe idanunka?”
Ya amsa ya ce, “Na riga na gaya muku ba ku kuwa saurara ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?”
Sai suka hau shi da zagi suna cewa, “Kai ne dai almajirin mutumin! Mu almajiran Musa ne! Mun dai san cewa Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum ba mu san inda ya fito ba.”
Sai mutumin ya ce, “Cabɗi, yau ga abin mamaki! Ba ku san inda ya fito ba, ga shi kuwa ya buɗe idanuna. Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa. Ba wanda ya taɓa ji cewa an buɗe idanun wanda aka haifa makaho. Da mutumin nan ba daga Allah ba ne, da ba abin da zai iya yi.”
Sai suka amsa suka ce, “Kai da aka haifa cike da zunubi; za ka yi karambanin koyarwar da mu!” Sai suka kore shi.
Makanta ta ruhaniya
Yesu ya ji labari cewa sun kore shi, da ya same shi kuwa, sai ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum?”
Sai mutumin ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, wane ne shi? Gaya mini, don in gaskata da shi.”
Yesu ya ce, “Yanzu ka gan shi; tabbatacce ma, shi ne yake magana da kai.”
Sai mutumin ya ce, “Ubangiji, na gaskata,” ya kuma yi masa sujada.
Yesu ya ce, “Saboda shari’a ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.”
Da Farisiyawan da suke tare da shi suka ji ya faɗi haka sai suka yi tambaya suka ce, “Mene? Mu ma makafi ne?”
Yesu ya ce, “Ai, da ku makafi ne ma, da ba ku da zunubi, amma da yake kun ce, kuna gani, zunubanku suna nan daram.
Makiyayi da garkensa
“Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne. Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje. Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa. Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.” Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.
Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ’yan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba. Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo. Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin. Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su. Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.
“Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni, kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin. Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma. Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma. Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”
Saboda waɗannan kalmomi fa, sai ɓaraka ta sāke shiga cikin Yahudawa. Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”
Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?”
Rashin bangaskiyar Yahudawa
Bikin Miƙawa10.22 Wato, Hanukka a Urushalima ya kewayo, lokacin sanyin hunturu ne kuwa. Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon, sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.”
Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni. Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne. Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na. Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana. Da ni da Uba ɗaya ne.”
Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku ayyukan alheri masu yawa da Uba ya aiko ni in yi, a kan wanne kuke so ku jajjefe ni?”
Yahudawa suka amsa suka ce, “Ai, ba don wani daga cikin waɗannan ayyukan alheri ne muke so mu jajjefe ka ba, amma don saɓon da kake yi, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.”
Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’
10.34
Zab 82.6
? Mun dai san Nassi ba ya ƙarya, In har ya kira su waɗanda maganar Allah ta zo musu, ‘alloli,’ to, game da wanda Uba ya keɓe a matsayin nasa ne ya kuma aiko shi duniya. Don me kuke ce saɓo nake, domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’ In ba ayyukan da Ubana yake yi ne nake yi ba, to, kada ku gaskata ni. Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.” Sai suka sāke yin ƙoƙari su kama shi, amma ya kuɓuce musu.
Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.
Mutuwar Lazarus
To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta. Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya.”
Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.” Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ’yar’uwarta da kuma Lazarus. Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.
Sai ya ce wa almajiransa, “Mu koma Yahudiya.”
Sai suka ce, “Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?”
Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan. Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske.”
Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.” Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.
Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, “Lazarus ya mutu, amma saboda ku na yi farin ciki da ba na can, domin ku gaskata. Amma mu dai je wurinsa.”
Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.”
Yesu ya yi wa ’yan’uwan Lazarus mata ta’aziyya
Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari. Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima, Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu. Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.
Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba. Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.”
Yesu ya ce mata, “Ɗan’uwanki zai sāke tashi.”
Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.”
Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu; kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”
Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”
Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.” Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa. Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi. Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can.
Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.”
Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu. Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?”
Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.”
Yesu ya yi kuka.
Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?”
Yesu ya tā da Lazarus daga matattu
Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse. Sai Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.”
Marta, ’yar’uwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.”
Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?”
Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni. Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”
Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!” Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi.
Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”
An ƙulla shawara a kashe Yesu
([Mattiyu 26.1-5]; [Markus 14.1],[2]; [Luka 22.1],[2])
Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi. Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa.
Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa. In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.”
Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba! Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”
Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa, ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya. Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.
Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa. Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?” Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi.
An shafe Yesu da mai a Betani
([Mattiyu 26.6-13]; [Markus 14.3-9])
Kwana shida kafin Bikin Ƙetarewa, sai Yesu ya iso Betani, inda Lazarus yake, wanda Yesu ya tā da daga matattu. A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi. Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.
Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce, “Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.” Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki.
Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar jana’izata. Kullum za ku kasance da matalauta, amma ba kullum za ku kasance tare da ni ba.”
Ana cikin haka sai babban taron Yahudawa suka sami labari Yesu yana can suka kuwa zo, ba kawai don shi ba amma don su kuma ga Lazarus, wanda ya tā da daga matattu. Saboda haka manyan firistoci suka ƙulla su kashe Lazarus shi ma, gama dalilinsa Yahudawa da yawa suna komawa ga Yesu suna kuma ba da gaskiya gare shi.
Shiga mai nasara
([Mattiyu 21.1-11]; [Markus 11.1-11]; [Luka 19.28-40])
Kashegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima. Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa,
“Hosanna!”
“Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”12.13 Zab 118.25,26
“Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!”
Yesu ya sami ɗan jaki, ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Kada ki ji tsoro, ya Diyar Sihiyona;
duba, ga sarkinki yana zuwa,
zaune a kan aholaki jaki.”12.15 Zak 9.9
Da fari almajiransa ba su gane dukan wannan ba. Sai bayan da aka ɗaukaka Yesu, sa’an nan suka gane cewa an rubuta waɗannan abubuwa game da shi ne, har ma suka yi masa waɗannan abubuwa.
Taron da suke tare da shi a sa’ad da ya kira Lazarus daga kabari ya kuma tā da shi daga matattu suka yi ta baza labarin. Mutane da yawa kuwa suka fita taryensa, saboda sun ji labarin abin banmamakin da ya yi. Saboda haka Farisiyawa suka ce wa juna, “Duba, wannan ba ya kai mu ko’ina. Ga shi, duk duniya tana bin sa!”
Yesu ya yi maganar mutuwarsa
To, akwai waɗansu Hellenawa a cikin waɗanda suka haura don su yi sujada a Bikin. Suka zo wurin Filibus, wanda yake daga Betsaida ta Galili, da roƙo. Suka ce, “Ranka yă daɗe, muna so mu ga Yesu.” Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawus, Andarawus da kuma Filibus suka gaya wa Yesu.
Yesu ya amsa ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum. Gaskiya nake gaya muku, sai ƙwayar alkama ta fāɗi ƙasa ta mutu, in ba haka ba za tă kasance ƙwaya ɗaya tak. Amma in ta mutu, za tă ba da ’ya’ya da yawa. Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami. Duk wanda zai bauta mini dole yă bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.
“Yanzu kuwa na damu, amma me zan ce? ‘Uba, ka cece ni daga wannan sa’a’? A’a, ai, saboda wannan dalili ne musamman na zo. Uba, ka ɗaukaka sunanka!”
Sai wata murya ta fito daga sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.” Taron da suke a wurin suka ji, suka ce an yi tsawa; waɗansu kuwa suka ce mala’ika ne ya yi masa magana.
Yesu ya ce, “An yi wannan muryar saboda amfaninku ne, ba don nawa ba. Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne za a tumɓuke mai mulkin duniyan nan. Amma ni, sa’ad da aka ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni.” Ya faɗa haka ne don yă nuna irin mutuwar da zai yi.
Sai taron suka ce, “Ahab, Dokarmu ta gaya mana cewa, Kiristi zai kasance har abada, to, yaya za ka ce, ‘Dole ne a ɗaga Ɗan Mutum?’ Wane ne wannan ‘Ɗan Mutum’?”
Sai Yesu ya ce musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yă cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba. Ku dogara ga hasken yayinda kuke da shi, don ku zama ’ya’yan haske.” Da Yesu ya gama magana, sai ya tafi ya ɓuya daga gare su.
Yahudawa sun ci gaba da rashin bangaskiya
Ko bayan Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwan banmamaki a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba. Wannan ya faru ne, don a cika maganar annabi Ishaya cewa,
“Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu,
ga wa kuma aka bayyana hannun ikon Ubangiji?”12.38 Ish 53.1
Saboda haka ba su iya gaskatawa ba, domin, kamar yadda Ishaya ya faɗa a wani wuri cewa,
“Ya makantar da idanunsu
ya kuma taurare zukatansu,
don kada su gani da idanunsu,
ko su fahimta a zukatansu,
ko kuwa su juyo, har in warkar da su.”12.40 Ish 6.10
Ishaya ya faɗi haka ne, saboda ya hangi ɗaukakar Yesu, ya kuwa yi magana a kansa.
Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi. Amma saboda Farisiyawa ba su furta bangaskiyarsu ba, don tsoron kada a kore su daga majami’a; gama sun fi son yabon mutane, fiye da yabon Allah.
Sa’an nan Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Duk wanda ya gaskata da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne. Duk mai dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne. Na zo cikin duniya a kan ni haske ne, don duk wanda ya gaskata da ni, kada yă zauna a cikin duhu.
“Duk mai jin kalmomina bai kuwa kiyaye su ba, ba ni ba ne nake shari’anta shi. Gama ban zo domin in yi wa duniya shari’a ba, sai dai domin in cece ta. Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za tă hukunta shi a rana ta ƙarshe. Gama ba don kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ne ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa da kuma yadda zan faɗe shi. Na san cewa umarninsa yana kai ga rai madawwami. Saboda haka duk abin da na faɗa na faɗe shi ne kamar dai yadda Uba ya ce in faɗa.”
Yesu ya wanke ƙafafun almajiransa
Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yă koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.
Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yă bashe Yesu. Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah; saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa. Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura.
Ya zo kan Siman Bitrus, wanda ya ce masa, “Ubangiji, kai za ka wanke ƙafafuna?”
Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.”
Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.”
Yesu ya amsa ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.”
Sai Siman Bitrus ya ce, “To, Ubangiji, ba ƙafafuna kaɗai ba har ma da hannuwana da kaina kuma!”
Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yă wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.” Gama ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba kowa ba ne yake da tsabta.”
Da ya gama wanke ƙafafunsu, sai ya sa tufafinsa ya koma wurin zamansa. Ya tambaye su ya ce, “Kun fahimci abin da na yi muku? Kuna ce da ni ‘Malam’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake. Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna. Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku. Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi. Yanzu da kuka san waɗannan abubuwa, ku masu albarka ne, in kuka yi su.
Yesu ya yi maganar bashe shi
“Ba dukanku nake nufi ba; na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa don a cika Nassi ne da ya ce, ‘Wanda ya ci burodina tare da ni ya tasar mini.’
13.18
Zab 41.9
“Ina faɗa muku yanzu tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata cewa ni ne Shi. Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ ”
([Mattiyu 26.20-25]; [Markus 14.17-21]; [Luka 22.21-23])
Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
Almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake. Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi. Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?”
Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?”
Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman. Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi.
Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.” Amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka. Da yake Yahuda ne ma’aji, waɗansunsu suka ɗauka Yesu yana ce masa yă sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yă ba wa matalauta wani abu. Nan da nan da Yahuda ya karɓi burodin, sai ya fita. A lokacin kuwa dare ya yi.
Yesu ya yi zancen mūsun Bitrus
Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa. In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikin Ɗan, Allah kuwa zai ɗaukaka Ɗan zuwa ga zatinsa, zai kuma ɗaukaka shi nan take.
“’Ya’yana, zan kasance da ku na ɗan ƙanƙani lokaci ne. Za ku neme ni. Kuma kamar yadda na gaya wa Yahudawa, haka nake gaya muku yanzu. Inda zan tafi, ba za ku iya zuwa ba.
“Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”
([Mattiyu 26.31-35]; [Markus 14.27-31]; [Luka 22.31-34])
Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?”
Yesu ya amsa ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.”
Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.”
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku!
Yesu ya ta’azantar da almajiransa
“Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”
Yesu shi ne hanyar zuwa gun Uba
Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?”
Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.”
Filibus ya ce, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan kuwa zai biya bukatarmu.”
Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’? Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa. Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba. Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban. Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.
Yesu ya yi alkawarin Ruhu Mai Tsarki
“In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina. Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku. Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku. Ba da daɗewa ba, duniya ba za tă ƙara ganina ba, amma za ku gan ni. Don ina raye, ku ma za ku rayu. A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku. Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”
Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, “Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?”
Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi. Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni.
“Duk wannan na faɗa ne yayinda ina tare da ku. Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
“Kun dai ji na ce, ‘Zan tafi in kuma sāke dawo wurinku.’ In har kuna ƙaunata, za ku yi farin ciki cewa za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. Na faɗa muku tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata. Ba zan ƙara yi muku magana ba, gama mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Ba shi da iko a kaina, amma dole duniya ta koya cewa ina ƙaunar Uba, ina kuma yin yadda Ubana ya umarce ni.
“Ku zo, mu bar nan.
Itacen inabi da kuma rassa
“Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin. Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya. Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku. Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.
“Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone. In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.
“Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata. In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya. Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana. Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna.
Duniya ta ƙi jinin almajirai
“In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’15.20 Yoh 13.16 In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma. Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba. Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu. Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma. Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana. Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’15.25 Zab 35.19; Zab 69.4
Aikin Ruhu Mai Tsarki
“Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni. Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko.
“Na faɗa muku wannan duka, domin kada ku bauɗe. Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne. Za su yi waɗannan abubuwa ne domin ba su san Uba ko ni ba. Na faɗa muku wannan, domin in lokacin ya yi, ku tuna na gargaɗe ku. Ban faɗa muku wannan tun da fari ba domin ina tare da ku.
Aikin Ruhu Mai Tsarki
“Yanzu zan tafi wurin wanda ya aiko ni, duk da haka ba waninku da ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ Saboda na faɗa waɗannan abubuwa ga shi kun cika da baƙin ciki. Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku. Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci, a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba; a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba; a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan.
“Ina da sauran abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ba za ku iya ɗauka a yanzu ba. Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna. Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku. Duk abin da yake na Uba nawa ne. Shi ya sa na ce, ‘Ruhun zai ɗauko daga abin da yake nawa, yă bayyana muku.’ ”
Baƙin cikin almajirai zai koma farin ciki
Yesu ya ci gaba da cewa, “Jim kaɗan, ba za ku ƙara ganina ba, sa’an nan bayan an jima kaɗan kuma, za ku gan ni.”
A nan fa sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da cewa, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni,’ da kuma, ‘Domin zan tafi wurin Uba’?” Suka yi ta tambaya, “Me yake nufi da ‘jim kaɗan’? Ba mu fahimci abin da yake faɗi ba.”
Yesu ya gane suna so su tambaye shi game da wannan, sai ya ce musu, “Kuna tambayar juna game da abin da nake nufi da na ce, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, da kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni’? Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya. Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku. A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana. Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.
“Ko da yake ina magana da misalai, lokaci yana zuwa da ba zan ƙara yin magana da misalai ba, sai dai in faɗa muku a fili game da Ubana. A ranan nan, za ku roƙa a cikin sunana. Ban ce zan roƙi Uba a madadinku ba. Ai, shi Uban kansa yana ƙaunarku domin kun ƙaunace ni kun kuma gaskata cewa daga Allah na fito. Na fito daga wurin Uba, na kuma shigo duniya, yanzu kuwa zan bar duniya in koma wurin Uba.”
Sai almajiran Yesu suka ce, “Haba, yanzu ne fa kake magana a sarari ba tare da misalai ba. Yanzu mun gane cewa ka san kome ba sai wani ya tambaye ka ba. Wannan ya sa muka gaskata ka fito daga Allah.”
Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata! Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni.
“Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
Yesu ya yi addu’a
Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce,
“Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka. Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko. Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni. Yanzu ya Uba, ka ɗaukaka ni a gabanka da ɗaukakar da dā nake da ita tun kafin a kafa duniya.
Yesu ya yi addu’a saboda almajiransa
“Na bayyana ka ga waɗanda ka ba ni a duniya. Su naka ne; kai ka ba ni su sun kuma yi biyayya da maganarka. Yanzu sun san cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka ya fito. Na ba su kalmomin da ka ba ni sun kuwa karɓa. Sun san tabbatacce daga wurinka na fito. Sun kuma gaskata kai ka aiko ni. Ina addu’a dominsu. Ba domin duniya nake addu’a ba, amma domin waɗanda ka ba ni, gama su naka ne. Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. Na kuwa sami ɗaukaka ta wurinsu. Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika.
“Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu. Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne. Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan. Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya. Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya. Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske.
Yesu ya yi addu’a saboda dukan masu bi
“Addu’ata ba saboda masu bina kaɗai ba ne. Ina addu’a kuma saboda waɗanda za su gaskata da ni ta wurin maganarsu. Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni. Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.
“Uba, ina so waɗanda ka ba ni su kasance tare da ni a inda nake, su kuma ga ɗaukakata, ɗaukakar da ka ba ni domin kana ƙaunata kafin halittar duniya.
“Ya Uba Mai Adalci, ko da yake duniya ba tă san ka ba, ni na san ka, sun kuma san kai ka aiko ni. Na bayyana ka a gare su, zan kuma ci gaba da bayyana ka domin ƙaunar da ka yi mini ta kasance a cikinsu ni ma in kasance a cikinsu.”
An kama Yesu
([Mattiyu 26.47-56]; [Markus 14.43-50]; [Luka 22.47-53])
Da ya gama addu’a, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki.
To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa. Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu ma’aikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai.
Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce, “Wa kuke nema?”
Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.”
Yesu ya ce, “Ni ne shi.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.) Da Yesu ya ce, “Ni ne shi,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa.
Sai ya sāke tambayar su ya ce, “Wa kuke nema?”
Suka ce, “Yesu Banazare.”
Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku ni ne shi. In kuma ni ne kuke nema, to, sai ku bar waɗannan su tafi.” Wannan ya faru ne don a cika kalmomin da ya yi cewa, “Ban yar da ko ɗaya daga cikin waɗanda ka ba ni ba.”18.9 Yoh 6.39
Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama (Sunan bawan kuwa Malkus ne.)
Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?”
An kai Yesu a gaban Annas
([Mattiyu 26.57],[58]; [Markus 14.53],[54]; [Luka 22.54])
Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma ma’aikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka daure shi sa’an nan suka kawo shi da farko wurin Annas, wanda yake surukin Kayifas, babban firist a shekaran nan. Kayifas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa zai fi kyau mutum ɗaya yă mutu saboda mutane.
Mūsun Bitrus na farko
([Mattiyu 26.69],[70]; [Markus 14.66-68]; [Luka 22.55-57])
Siman Bitrus da kuma wani almajiri suna bin Yesu. Domin almajirin nan sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu a filin gidan babban firist ɗin, Bitrus kuwa ya dakata a waje a bakin ƙofa. Almajirin nan da yake sananne ga babban firist, ya dawo ya yi magana da yarinyar mai aiki a can, ya kuma shigo da Bitrus.
Yarinyar da take bakin ƙofar ta ce wa Bitrus, “Kai ba ɗaya ne daga cikin almajiran mutumin nan ba ne?”
Bitrus ya amsa ya ce, “A’a, ba na ciki.”
To, ana sanyi, bayi da ma’aikatan suna tsattsaye kewaye da wutar da suka hura don su ji ɗumi. Bitrus ma yana tsaye tare da su, yana jin ɗumi.
Babban firist ya yi wa Yesu tambayoyi
([Mattiyu 26.59-66]; [Markus 14.55-64]; [Luka 22.66-71])
Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa.
Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majami’u ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba. Don me kake tuhumata? Ka tambayi waɗanda suka ji ni. Ba shakka, sun san abin da na faɗa.”
Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin ma’aikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”
Yesu ya amsa ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?” Sai Annas ya aika da shi, a daure, wurin Kayifas babban firist.
Mūsun Bitrus na biyu da na uku
([Mattiyu 26.71-75]; [Markus 14.69-72]; [Luka 22.58-62])
Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?”
Sai ya yi mūsu, yana cewa, “Sam, ba na ciki.”
Sai wani daga cikin bayin babban firist dangin wanda Bitrus ya sare wa kunne, ya tambaya shi ya ce, “Kana tsammani ban gan ka tare da shi a gonar zaitun ba?” Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara.
Yesu a gaban Bilatus
([Mattiyu 27.1],[2],[11-14]; [Markus 15.1-5]; [Luka 23.1-5])
Sa’an nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa. Saboda haka Bilatus ya fito wajensu ya ce, “Wace ƙara kuke kawowa game da mutumin nan?”
Suka amsa suka ce, “Da a ce shi ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bashe shi gare ka ba.”
Bilatus ya ce, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga dokarku.”
Sai Yahudawa suka ƙi suka ce, “Ba mu da ikon yanke wa wani hukuncin kisa.” Wannan kuwa ya faru ne don a cika kalmomin da Yesu ya yi da suka nuna irin mutuwar da zai yi.
Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?”
Yesu ya yi tambaya ya ce, “Wannan ra’ayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?”
Bilatus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne? Ai, mutanenka ne da kuma manyan firistoci suka bashe ka gare ni. Me ka yi?”
Yesu ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.”
Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!”
Yesu ya amsa ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”
Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?”
([Mattiyu 27.15-31]; [Markus 15.6-20]; [Luka 23.13-25])
Da ya faɗi haka, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce, “Ni fa ban sami wani abin zargi game da shi ba. Amma fa kuna da wata al’ada in lokacin Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku ɗaya. To, kuna so in sakar muku ‘sarkin Yahudawa’?”
Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye.
An yanke wa Yesu hukuncin mutuwar gicciye
Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala. Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya. Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.
Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.” Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”
Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!”
Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”
Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”
Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi, sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba. Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”
Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”
Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”
Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata). Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida.
Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.”
Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!”
Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?”
Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”
A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi.
Gicciyewa
([Mattiyu 27.32-44]; [Markus 15.21-32]; [Luka 23.26-43])
Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu. Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota). Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.
Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne,
Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa.
Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik. Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.”
Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.”
Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.
Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.”
Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce,
“Suka rarraba tufafina a junansu,
suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.”19.24 Zab 22.18
Abin da sojojin suka yi ke nan.
To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
Mutuwar Yesu
([Mattiyu 27.45-56]; [Markus 15.33-41]; [Luka 23.44-49])
Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu. Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.
To, ranan nan fa, ranar Shirye-shirye ce, kashegari kuma muhimmin Asabbaci ne. Domin Yahudawa ba sa so a bar jikunan a kan gicciyoyi a Asabbaci, sai suka roƙi Bilatus a kakkarye ƙafafunsu kuma sauko da jikunan. Sai sojoji suka zo suka karya ƙafafun mutum na farko da aka gicciye tare da Yesu, da kuma na ɗayan. Amma sa’ad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba. A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito. Mutumin da ya gani ɗin shi ya ba da shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya san gaskiya yake faɗa, yana kuma ba da shaidar domin ku ma ku gaskata. Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,”19.36 Fit 12.46; Ƙid 9.12; Zab 34.20 kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
Jana’izar Yesu
([Mattiyu 27.57-61]; [Markus 15.42-47]; [Luka 23.50-56])
Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin. Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari. Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza. A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba. Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.
Kabarin da ba kowa
([Mattiyu 28.1-10]; [Markus 16.1-8]; [Luka 24.1-12])
Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin. Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!”
Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin. Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin. Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba. Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can, haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin. A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata. (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.) Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama.
Yesu ya bayyana ga Maryamu Magdalin
([Mattiyu 28.1-10]; [Markus 16.1-8]; [Luka 24.1-12])
Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin, sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu.
Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?”
Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.” Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba.
Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?”
Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.”
Yesu ya ce mata, “Maryamu.”
Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”).
Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ”
Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.
Yesu ya bayyana ga almajiransa
([Mattiyu 28.16-20]; [Markus 16.14-18]; [Luka 24.36-49])
Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!” Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji.
Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.” Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”
Yesu ya bayyana ga Toma
Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo. Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!”
Amma ya ce musu, “Ina, ai, sai na ga ramin ƙusa a hannuwansa na sa yatsata a inda ƙusoshi suka kasance, na kuma sa hannuna a gefensa, in ba haka ba, ba zan gaskata ba.”
Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!” Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”
Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”
Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”
Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba. An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.
Yesu da kamun kifin banmamaki
Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya.21.1 Wato, Tekun Galili Ga yadda ya faru. Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare. Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.
Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.
Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?”
Suka amsa suka ce, “A’a.”
Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.
Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.
Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.” Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba. Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne. Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin. Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.
Yesu ya sāke tabbatar da Bitrus
Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?”
Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”
Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.”
Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?”
Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”
Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”
Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?”
Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.”
Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina. Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.” Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”
Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”) Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”
Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.” Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”
Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce.
Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.