- Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
2 Korintiyawa
2 Korintiyawa
2 Korintiyawa
2Kor
2 Korintiyawa
Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,
Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, tare da dukan tsarkaka a ko’ina a Akayya.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
Allah na dukan ta’aziyya
Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.
’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa. Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu, yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.
Canja shirye-shiryen Bulus
Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba. Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa, kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.
Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu. Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya. Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “A’a”?
Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce. Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum. Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah. Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu, ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.
Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korint ba. Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi.
Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba. Gama in na sa ku baƙin ciki, wa ya rage yă faranta mini zuciya, in ba ku waɗanda na sa baƙin cikin ba? Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka. Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.
Gafara don mai zunubi
In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne. Irin wannan mutum, horon da yawancin mutane suka yi masa ya isa haka. Yanzu fa, a maimako, gara ku yafe masa, ku kuma ta’azantar da shi, don kada baƙin ciki mai yawa yă sha kansa. Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku. Abin da ya sa na rubuta muku shi ne don in ga ko za ku jimre da gwajin nan, kuna kuma yin biyayya ta kowace hanya. In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi, don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.
Masu hidimar sabon alkawari
To, sa’ad da na tafi Toruwas don in yi wa’azin bisharar Kiristi, ko da yake na tarar cewa Ubangiji ya buɗe mini ƙofa, duk da haka, ban sami salama a zuciyata ba domin ban sami ɗan’uwana Titus a can ba. Sai na yi bankwana da su na wuce zuwa Makidoniya.
Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina. Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka. Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin? Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.
Yabon kanmu ne kuma muka fara yi? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi? Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă santa, yă kuma karanta ta. Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane.
Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah. Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne. Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.
Ɗaukakar sabon alkawari
To, in hidimar da ta kawo mutuwa, wadda an rubuta a kan allon dutse, ta zo da ɗaukaka har Isra’ilawa suka kāsa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ko da yake mai shuɗewa ce, ashe, hidimar Ruhu ba za tă fi wannan ɗaukaka ba? In hidimar da take jawo wa mutane hukunci tana da ɗaukaka haka, to, lalle, hidimar da take kawo adalci za tă fi ta ɗaukaka nesa! Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu. In kuma aba mai shuɗewa ta zo da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwammame, lalle ne yă kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa!
Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan. Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Isra’ilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa. Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi. Har yă zuwa yau, duk sa’ad da ake karatun littattafan Musa, lulluɓin nan yakan rufe zukatansu. Amma duk sa’ad da wani ya juyo ga Ubangiji, akan kawar da lulluɓin. Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ’yanci yake. Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka.
Dukiya cikin tulunan yumɓu
Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba. Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa. Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu. Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,”4.6 Far 1.3 ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.
Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba. A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.
A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana. Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku. Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.
Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
Wurin zamanmu a sama
Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. Kafin nan muna nishi, da marmari a yi mana sutura da gidanmu na sama, don sa’ad da aka yi mana sutura, ba za a same mu tsirara ba. Sa’ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, sai dai don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa. Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.
Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba. Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji. Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan. Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.
Hidimar sulhuntawa
To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku. Ba ƙoƙari muke mu yabe kanmu a gare ku ba ne, sai dai muna ba ku damar yin taƙama da mu ne, don ku sami amsar da za ku ba wa waɗanda suke taƙama da abin da ake gani ne, a maimakon abin da yake cikin zuciya. In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne. Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu. Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.
Saboda haka, daga yanzu zuwa nan gaba, ba mu ƙara ɗaukan wani mutum bisa ga ganin duniya ba. Ko da yake a dā, mun ɗauki Kiristi haka, amma yanzu mun daina yin haka. Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo! Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu, wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu. Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah. Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.
A matsayinmu na abokan aikin Allah, muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza. Gama ya ce,
“A lokacin samun alherina, na ji ka,
a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.”6.2 Ish 49.8
Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.
Wahalolin Bulus
Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi. A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu. Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa. Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya, da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu, ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya, mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba, cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.
Ya ku Korintiyawa, mun yi muku magana a sake, muka kuma saki zuciya da ku ƙwarai. Ba mu ƙi nuna muku ƙaunarmu ba, sai dai ku kuka ƙi nuna mana. A wannan zance kam, ina magana da ku kamar ’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu.
Kada ku haɗa kai da marasa bi
Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi? Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce,
“Zan zauna tare da su,
in yi tafiya a cikinsu,
zan zama Allahnsu,
su kuma za su zama mutanena.”6.16 Fir 26.12; Irm 32.38; Ezk 37.27
Saboda haka,
“Sai ku fito daga cikinsu,
ku keɓe kanku,
in ji Ubangiji.
Kada ku taɓa wani abu marar tsabta,
zan kuma karɓe ku.”6.17 Ish 52.11; Ezk 20.34,41
Kuma,
“Zan zama Uba a gare ku,
ku kuma za ku zama ’ya’yana, maza da mata,
in ji Ubangiji Maɗaukaki.”6.18 2Sam 7.14; 2Sam 7.8
Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.
Farin cikin Bulus
Ku saki zuciya da mu. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba. Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa. Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.
Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro. Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus, ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai.
Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai. Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba. Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa. Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi. To, ko da yake na rubuta muku, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana. Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa.
Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka. Na yi taƙama da ku a wurinsa, ba ku kuwa ba ni kunya ba. Kamar dai yadda dukan abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka ma taƙamarmu a kanku a gaban Titus ya zama gaskiya. Ƙaunar da yake yi muku ya ƙaru ƙwarai, duk sa’ad da yake tunawa da biyayyarku duka, da kuma irin yawan bangirman da kuka nuna masa lokacin da kuka karɓe shi. Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.
An ƙarfafa bayarwa
To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya. Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci. Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu, sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka. Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah. Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi. To, da yake kun fiffita a kowane abu cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin dukan ƙwazo, da kuma cikin ƙaunarku dominmu, sai ku fiffita a wannan aikin alheri ma.
Ba umarni nake ba ku ba, sai dai ina so in gwada gaskiyar ƙaunarku ne, ta wurin kwatanta ta da aniyar waɗansu. Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.
Ga shawarata a kan abin da ya fi muku kyau a wannan al’amari. Bara ku kuka fara bayarwa, kuka kuma zama na farko wajen niyyar yin haka. Yanzu sai ku ƙarasa aikin da irin niyyar da kuka fara, ku yi haka gwargwadon ƙarfinku. Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.
Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.”8.15 Fit 16.18
An aika Titus zuwa Korint
Ina gode wa Allah, wanda ya sa a zuciyar Titus, irin kula da nake da shi dominku. Ba kawai ya yarda yă je wurinku kamar yadda muka roƙe shi yă yi ba, amma ya so yă zo kamar yadda ya riga ya yi niyya. Ga shi mun aiko ɗan’uwanmu nan tare da shi, wanda ikkilisiyoyi duka suna yabo saboda hidimarsa ga bishara. Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yă riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu. Muna gudu kada wani yă zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake. Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma.
Ban da wannan kuma, mun aiko da ɗan’uwanmu tare da su, wanda ya sha tabbatar mana da ƙwazonsa ta hanyoyi iri-iri, musamman yanzu, domin ya amince da ku da gaske. Game da Titus kuma, shi abokin tarayyata ne, da kuma abokin aikina a cikinku; game da ’yan’uwanmu kuwa, su wakilai ne na ikkilisiyoyi, kuma su masu ɗaukaka Kiristi ne. Saboda haka, ku nuna wa waɗannan mutane shaidar ƙaunarku, da kuma dalilin taƙamarmu da ku, domin ikkilisiyoyi su gani.
Babu wata bukata in rubuta muku game da hidiman nan ga tsarkaka. Gama na san aniyarku na yin taimako, ina kuma taƙama a kan wannan ga Makidoniyawa, ina faɗin musu cewa tun bara, ku da kuke a Akayya a shirye kuke ku bayar. Ƙoƙarinku kuwa ya zuga yawancinsu ga aiki. Amma ina aika ’yan’uwan nan don kada taƙamar da muke yi da ku, a kan wannan al’amari ta zama a banza, sai dai domin yă zama kuna nan a shirye, kamar yadda na faɗa za ku kasance. Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku. Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.
Shukin yardar rai
Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Ya ba gajiyayyu hannu sake,
ayyukansa na alheri madawwama ne.”9.9 Zab 112.9
To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.
Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake. A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku. Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!
Bulus ya kāre aikinsa
Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali’u da sanyin hali na Kiristi, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” a cikinku, amma “mai matsawa” sa’ad da nake rabe da ku! Ina roƙonku cewa sa’ad da na zo kada ku tilasta ni in matsa muku, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha’anin duniya ne. Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi. Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.
Kuna duban abubuwa bisa-bisa ne kawai. In wani ya ganin cewa shi na Kiristi ne, ya kamata yă sāke lura cewa kamar yadda yake na Kiristi, haka mu ma muke. Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba ni da abin jin kunya a ciki. Ba na so yă zama kamar ina ƙoƙari in tsorata ku ne da wasiƙuna. Gama waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa suna da nauyi da kuma ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi, ba shi da wani kwarjini, maganarsa kuma ba kome ba ce.” Ya kamata irin waɗannan mutane su gane cewa abin da muke faɗa a cikin wasiƙunmu sa’ad da ba ma nan tare da ku, shi muke aikatawa sa’ad da muke nan.
Ba za mu yi ƙarfin halin lissafta kanmu, ko mu kwatanta kanmu da waɗansu masu yabon kansu ba. Sa’ad da suke gwada kansu da kansu, da kuma kwatanta kansu da kansu, ba su da hikima. Amma mu kam, ba za mu yi taƙama mu zarce iyakarmu ba, sai dai za mu yi taƙama cikin filin da Allah ya ƙayyade mana, filin kuwa ya kai har zuwa wurinku. Ba mu wuce gona da iri a taƙamarmu ba, kamar yadda zai zama, da a ce ba mu zo wurinku ba, gama mun kai har wurinku da bisharar Kiristi. Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba tă kuma shafi aikin waɗansu ba. Sai dai muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku yă riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske. Saboda mu iya yin wa’azin bishara a yankunan da suke gaba da ku. Gama ba ma so mu yi taƙama game da aikin da aka riga aka yi a sashen wani. Amma, “Duk mai yin taƙama, sai ya yi taƙama da Ubangiji.” Ai, ba mai yabon kansa ake amincewa da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.
Bulus da manzannin ƙarya
Ina fata za ku yi haƙuri da ’yar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri. Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa zalla. Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi. Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai. Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba. Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya.
Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta? Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima. Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka. Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa. Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku!
Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su. Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.
Bulus ya yi taƙama game da wahalarsa
Ina sāke faɗa, kada wani yă ɗauka ni wawa ne. Amma in kun ɗauke ni haka, to, sai ku karɓe ni kamar yadda kuke karɓan wawa, domin in ɗan in yi taƙama. A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa. Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi. Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna! Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska. Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba!
Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne. In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka. In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu. Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya. Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi. Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?
In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina. Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni. Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.
Wahayin Bulus da ƙayarsa
Dole in ci gaba da yin taƙama. Ko da yake ba za tă amfane ni ba, zan yi magana a kan ru’uyoyi da wahayoyi waɗanda na karɓa daga Ubangiji. Na san wani a cikin Kiristi wanda shekaru goma sha huɗu da suka wuce an ɗauke zuwa sama ta uku. Ko a cikin jiki ne, ko kuwa ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, Allah ne ya sani. Na kuma san cewa wannan mutum, ko a cikin jiki ne, ko kuma ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, amma Allah ne ya sani, an ɗauke shi ne zuwa aljanna. Ya ji waɗansu abubuwa waɗanda ba zai iya faɗarsu da kalmomi ba, abubuwan da ba a ba wa mutum damar faɗi. Zan yi taƙama game da mutum irin wannan, sai dai ni ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai a kan rashin ƙarfina. Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata. Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
Damuwar Bulus domin Korintiyawa
Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kāsa waɗannan mafiffitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne. Abubuwan da suke tabbatar da manzo, alamu, abubuwa da kuma ayyukan banmamaki, an aikata su a cikinku da matuƙar nacewa. Ta yaya ne darajarku ba tă kai ta sauran ikkilisiyoyi ba, ko kuwa don dai ban nawaita muku ba ne? Ku gafarta mini wannan laifi!
Yanzu a shirye nake in ziyarce ku sau na uku, ba zan kuma nawaita muku ba, don ba kayanku nake so ba, ku nake so. Gama ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran. Don haka ina farin ciki in kashe dukan abin da nake da shi a kanku, har in ba da kaina ma dominku. In na ƙaunace ku fiye da haka, za ku rage ƙaunarku gare ni ne? To, shi ke nan, ban nawaita muku ba. Ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara! Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku? Na roƙi Titus ya zo wurinku. Na kuma aiki ɗan’uwanmu tare da shi. Ko Titus ya cuce ku ne? Ba ruhu ɗaya yake bi da mu ba? Ba kuma hanya guda muka bi ba?
Ko tun dā can, kuna tsammani muna kāre kanmu a gare ku ne? A gaban Allah muke magana, kamar waɗanda suke cikin Kiristi. Ƙaunatattuna, kome da muke yi, muna yi ne don inganta ku ne. Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi. Ina tsoro kada sa’ad da na sāke zuwa, Allahna zai ƙasƙantar da ni a gabanku, kuma in yi baƙin ciki saboda waɗanda suka yi zunubi a dā, ba su kuma tuba daga aikin ƙazanta, da na fasikanci, da kuma lalata da suka sa kansu a ciki ba.
Gargaɗin ƙarshe
Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.”13.1 M Sh 19.15 Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan, da yake kuna neman tabbaci cewa Kiristi yana magana ta wurina ne. To, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku. Ko da yake tabbatacce an gicciye shi cikin rashin ƙarfi, duk da haka, yana rayuwa bisa ga ikon Allah. Haka mu ma marasa ƙarfi ne a cikinsa, amma ta wurin ikon Allah za mu rayu tare da shi don mu yi muku hidima.
Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin. Ina fata za ku gane cewa ba mu fāɗi gwajin ba. Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne. Kai, ba dama mu saɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar. Murna muke sa’ad da ba mu da ƙarfi, ku kuwa kuna da ƙarfi. Addu’armu ita ce, ku zama cikakku. Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
Gaisuwa ta ƙarshe
A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.
Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki.
Dukan tsarkaka suna gaishe ku.
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.